Uncategorized

SALON SO 43-44

 ????????????????????????????????????????            ???? SALON SO ????

????????????????????????????????????????

    BOOK ONE ????

Story & written by

Mommyn fareesa

   ????️ 43&44

“Ahankali mr Aliyu yace”.kinsan bana son kuka ko?”to nidai bana son tafiyar nan taka kace kafasa pls”

    idan zakiyi farin ciki da hakan zan gwada fasa tafiyar” idan daddy ya yarda shikenan?”

Amma meyasa bakyaso natafi ne?”

yaya Aliyu zanyi kewarka! kuma ban manta abinda yafaruba dakayi wancan tafiyar”

kada kisaka hankalina yakasa kwanciya idan nayi tafiyar nan yasmeen”sbd wannan mgn”amma ai aymaan d’in baya gidan ko?”

Hakane yaya Aliyu amma nidai banaso kayi nisa damu”yana k’okarin mgn wayarsa tayi ringing”

ganin khaleel ne yasakashi d’agawa”sbd atare zasuyi tafiyar ma”

Kashigo ina parlou na”yafad’a yana kashe wayar”

Tashi tsaye yasmeen tayi “ina zakije kuma kibarni?”

Ba bak’o zakayi bane?”khaleel fane”dukda haka yaya Aliyu ina gun imaan Idan kun gama mgn”

Okay yafad’a yanata kallon ta harta fice”

Ko 2 minit yasmeeen batayi da fitaba khaleel ya shigo”

zama yyi gefen mr Aliyu”kafin yace”.kaga yanzun 3 tama wuce”nina nayi sallama dasu hjy”kashirya komai damunyi la’asar sai muce air port ko?”

mr Aliyu yace”.gsky nifa da wuya namayi tafiyar nan”saidai kaje kai d’aya”zanyiwa daddy mgn”

    banganeba MAI NASSARA?”akan me zaka fasa to?”bayan kasan company d’in nan zai k’aru sosai akan tafiyarmu”

cikin sub’ututar baki mr Aliyu yace”.yasmeen batason tafiyar nan ai gara kawai nahak’ura ko?”

   murmushin anzo wajen khaleel yasaki kafin yace”.yasmeen fa kace?nazata kace imaan ma”amatsayin ta nawa taka da sbd ita zakak’i tafiya?”

“shiru mr Aliyu yyi sbd beda amsar tambayar”

Hmmmm abokina kenan!idan nafahimceka soyayya kukeyi da yasmeen d’in kenan?”

kaga mlm nibbu wata soyayya atsakaninmu sai mutunci”tana girmamani da kulawa da imaan”

tana tsoron abinda yafarune awancan tafiyar danayi”shine bataso natafi zaka mana wata fassa daban”

wani murmushi khaleel yasaki kafin yace”.komai nisan jifa zai dawo k’asa”

yanzun ashawarance tunda ka yarda da ita “me zai hana suje da imaan gidansu har zuwa gobe kadawo”kokuwa ka kai imaan hotoro(gidan ka kanninsu na wajen uwa)tunda nalura bakason barinsu agidan”ga security gakomai”

Eh to”zan cewa daddy kawai imaan nacan saitabi yasmeen d’in”sun d’ebewa juna kewa”banaso taje hotoro da sunan kwana”yaron nan Faisal(d’an yayan mahaifiyarsu)

yana son imaan”itakuma bata sonsa”gashi  agidan yake, tunda bata sonsa meye amfanin had’uwar su waje guda?”gara adaiyi gaisuwar zumunci kawai”

Ajiyar zuciya khaleel yasaki jin imaan d’in ance batason faisal”

Ok nafahimceka abokina yanzun muje muyi salla ko?”okay bara nasaka yasmeen tashiryamun kayana”

yafad’a suna fitowa dg parlourn”khaleel yyi waje”mr Aliyu ya wuce bed room d’in imaan”yasamesu suna sallah”

“Ahankali yace”.yasmeen idan kingama kije kishiryamun kayana ak’aramin trolley zanje nayo salla nadawo”

yana fad’in hakan yajuya ya fita”

suna shafa addua yasmeen ta tashi ta wuce sashensa”

bayan ta bud’e k’ofar parlourn da key” tashiga cikin bed room d’in”

k’aramin trolley d’in sa ta duba”kafin ta wuce gun ward rope tafara d’aukar masa abinda yadace”

tana k’okarin rufe trolley d’in yaturo k’ofar yashigo”

d’ago kanta tayi suka had’a ido”my yasmeeen tafiyar nan dolece”muna tare awaya karki damu”sannan tare da baby zakuje gida”har zuwa gobe insha Allah”

k’asa tayi da kanta ta wuce gurin mirror da nufin ta d’auki wayarta”

bayanta yabi ,yatsaya gab da ita kamar zai rungumeta ta baya”komai yatuna yafasa”

Atsorace ta d’ago kanta suka had’a ido ta cikin mirro d’in”harara ta galla masa”

yasaki murmushi har fararen hak’oransa suka bayyana yace”. matsoraciya dake”

nidai kabarni naje nasanarwa imaan sai mutafi”idan nak’i fa?”yafad’a murya can k’asa”

kukan shagwab’a tasaka tana turo baki batayi mgn ba”

kafeta yyi da lumsassun idanuwansa”cikin soft voice yace”.yasmeen meyasa rigimarki bata tashi ba, saida kikaga zanyi tafiya?”

    banida time d’in rarrashinki”amma zamuyi voice& vedio call sai na rarrasheki sosai  ko?”

nanma shiru batayi mgn ba”dafe kansa yyi yace”.yasalam!yakikeso nayi wai?”tafiyar nan daddy yace”.dole nayi….nifa yaya Aliyu nahak’ura”musammun dakace zanje da imaan gidanmu”

Hakan na nunamun ka yarda dani da family nawa nagode sosai”

Hmmm !shine kikak’i mgn kikamun shiru ko?”bacin kin hak’ura”

yasmeen na juyowa da nufin tayi mgn wayarsa tayi ringing”

kallonta mr Aliyu yyi yace”.muje kirakani get” kinga khaleel najirana”

bazaka komayin wanka ba?”babu time yasmeen”

batace komaiba ta d’auki trolley d’in,suka fito atare”

A parlou suka had’u da imaan”mr Aliyu yasanar mata taje ciki ta d’auki abinda takeda buk’ata da yasmeen zasu tafi gidansu”

Imaan na murna ta wuce bed room d’in ta”

Mr Aliyu yarufe sashen sa harda windows”sbd tsaro”imaan na fitowa suka wuce bakin get atare”

Khaleel da driver suka zauna a front sit”mr Aliyu da imaan da yasmeeen suka zauna a back sit”imaan na atsakkiyar su”

motar tayi shiru bbu me mgn”yasmeen kanta ak’asa tana wasa da yatsun hannuwanta”

yayinda mr Aliyu keta kallonta da duk wani motsinta”

da haka suka iso anguwar sarki”yasmeen ta fara fita dg motar”kafin imaan Ta fito”

Amamakin khaleel yaga mr Aliyu shima yafito”

yasmeen bazan samu darajar,ki tsaya kimun addua ba zaki juya kitafi?”

Juyowa tayi suka had’a ido ya banko mata harara”

murmushi tasaki yyinda imaan tace”.inane gidan anty yasmeen?

Da hannu yasmeen tanuna mata kafin ta juyo suka had’a ido da mr Aliyu”

Yaya Aliyu ai namaka acikin zuciya ta ko?”

ban yardaba da baki nakeson naji”to shikenan Allah yakaiku lafiya yadawo daku lafiya”kuma yabada sa’a abinda kukaje yi…

Ameen yah Allah thank you”yafad’a yana lumshe idanuwansa…..MAI NASSARA wai meye haka ne??”khaleel yafad’a yana zuro kansa ta glass”

bud’e idanuwansa mr Aliyu yyi yakalli yasmeen”itama shitake kallo”kaje yana jiranka sai munyi waya ko?”

da gaske bakida damuwa  ko kad’an?”d’aga mishi kanta tayi tana murmushi”

bece komaiba yajuya yatafi”yasmeen bata shiga gidaba,yana bud’e motar yad’ago kansa yakalli k’ofar gidansu yasmeen”tana atsaye”

Hannu ta d’aga masa ,tana mishi bye bye”shima bye bye d’in yamata kafin yashige mota”

sai asannan itama ta shige cikin gidan”

atsakar gidan tasami imaan da asma’u sunacin awara da yaji”

Imaan tasaki jikinta sunata fira dasu umma da asma’u”tamkar sun saba”

bata nuna wani girman kan ganinsu atalakawaba”dukda ayanzun sun wuce wannan sunan”sai dai ace musu masu rufin asiri.

Anty yasmeen yayan yatafi ko?”Eh yatafi sarkin k’wadayi”kinsamu yaji ko?”

duk sukayi dariya”yasmeen tace”.umma sannu da gida”

yauwa yasmeen,saiga imaan tafe”bamu gajetaba saida tamana bayani”

Eh umma yaya Aliyu yace”.mutaho tare zuwa gobe idan yadawo”

Allah yamaidoshi lafiya”

yasmeen ta amsa da Ameen….

B’angaren su mr Aliyu kuwa” jirgin k’arfe 5:pm suka hau”sai kusan 6:30 pm suka iso Abuja”

Kaitsaye hotel suka wuce”suka kama masauki”

bayan sunyi sallah kowa yawuce d’akinsa”

Wanka mr Aliyu yyi yaci abinci”

gaba d’aya yasmeen na aransa”kasan zuciyarsa yaji haushin bata kirasa ba taji sun sauka”

Wayarsa yad’auka,aikuwa yaga message nata data turo masa tun 6 pm”

Bud’e message d’in yyi kamar haka”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button