Labarai

Wata Sabuwa Yan bindiga a Jahar Zamfara Sun bukaci Kudin Fansan Wasu Mutane da Sabon Kudade.

Wata Sabuwa Yan bindiga a Jahar Zamfara Sun bukaci Kudin Fansan Wasu Mutane da Sabon Kudade.

Jaridar Alfijir Hausa ta ruwaito yadda Wasu Yan ta’adda da suka yi garkuwa da mutane huɗu da suka hada da namiji da mace da yara biyu a ƙauyen Kolo da ke ƙaramar hukumar Gusau a jihar Zamfara.

An tattaro cewa bayan sace waɗanda aka yi garkuwa da su, ‘yan bindigar sun buƙaci a biya su Naira Miliyan (Goma) N10m, kuma tare da gindaya sharaɗin rashin amincewa da tsoffin takardun naira.

Wani ɗan asalin yankin mai suna Mohammed Ibrahim, ya ce daga baya ‘yan fashin sun rage kuɗin fansa zuwa Naira Miliyan (Biyar) N5m, inda ya ce mutanen ƙauyen sun yi ta ƙoƙarin tara kuɗin fansar domin a sako waɗanda lamarin ya shafa.

A yayin da muke ƙoƙarin tattara kuɗaɗen da ‘yan ta’addan suka nema, sun sake aike da wani saƙon a safiyar yau cewa ba za su karɓi tsoffin takardun naira ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button