Labaran Duniya

Majalisar dokokin Indonesiya ta amince da hukuncin dauri kan yin jima’i kafin aure

Majalisar dokokin Indonesiya ta amince da hukuncin dauri kan yin jima’i kafin aure

 

Majalisar dokokin Indonesiya ta amince da dokar aikata laifuka da ta haramta jima’i a wajen aure tare da hukuncin daurin shekara guda a gidan yari.

 

A ranar Asabar ne jami’an gwamnatin kasar suka yi tir da amincewa da dokar yayin da Edward Hiariej, mataimakin ministan shari’a na Indonesia ya ce kudurin ya yi daidai da kimar kasar.

 

Indonesiya ita ce kasa mafi yawan musulmi a duniya.

 

A yau Talata, ƴan majalisar dokokin kasar suka amince da kudurin dokar, lamarin da ya haifar da bore daga kungiyoyin ƴan kasuwa, da masu rajin kare hakkin bil’adama, wadanda su ka bayyana hakan a matsayin tauye ‘yanci.

 

A cikin sabuwar dokar, iyaye ko ƴaƴa za su iya kai rahoton ma’auratan da ba su yi aure ba ga ƴan sanda idan sun zarge su da yin jima’i.

 

Dokar da ta shafi duk mazauna Indonesiya za ta ladabtar da mutanen da aka samu da laifin yin jima’i kafin aure da kuma yin zina da daurin shekara guda a gidan yari ko tara.

 

Za a yanke hukuncin yin lalata ga masoya na tsawon watanni shida a gidan yari ko tara.

 

Har ila yau, tuhumar cin mutuncin shugaban kasa mai ci na da daurin shekaru uku a gidan yari.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button