Labaran Duniya

Akwai rade-radin kulluwar wata alaka mai karfi tsakanin Dangote da diyar Sunusi Lamido Sunusi

A yan kwanakin baya-bayan nan ne aka sami bullar wadansu hotuna, na diyar sarki Sunusi Lamido Sunusi tare da shahararren dan kasuwa Alhaji Aliko Dangote kuma wanda yafi kowa kudi a Africa, wadanda aka dauka a jihar Legas.

 

An yada hotunan ne a dandalin Facebook na magoya bayan sarki Sunusi Lamidon, mai suna (Sunusi II fans ) wanda ya sami mabiya da dama wadanda suka tofa albarkacin bakinsu.

A cewar rahoton, Maryam Sanusi Lamido tana aikine na sanin makamar aiki a kamfanin na Dangote dake jihar Legas, inda ta sami damar daukar hotuna da shi.

 

Duba da yadda aka dauki hotunan, zasu nuna wa mai kallo cewa Lallai na cikin hoton suna da kyakkyawar alaka.

Matsayin Sunusi Lamido Sunusi a kasa

Mahaifin Maryam, Sunusi Lamido Sunusi, tsohon sarki ne wanda kuma yana daya daga cikin sarakuna da ake girmamawa, sannan kuma aboki ne na kud-da-kud ga Aliko Dangote.

 

Haka kuma, wadannan hotuna sun janyo sharhi da dama daga mutane masu yawa.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button