Labaran Duniya

DA DUMI DUMI, Kasar Amurka ta sanar da kashe shugaban al-Qaeda

DA DUMI DUMI, Kasar Amurka ta sanar da kashe shugaban al-Qaeda

 

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya sanar a yammacin jiya Litinin cewa, wani hari da jiragen yaki mara matuki suka kai a birnin Kabul na kasar Afganistan a karshen mako, ya kashe shugaban kungiyar al-Qaeda Ayman al-Zawahiri.

 

Biden ya bayyana cikin wani jawabi da ya gabatar kai tsaye daga fadar White House cewa, “shi ne ya bayar iznin kai harin, da zai kawar da shugaban na al-Qaeda daga fagen fama,” kuma babu wani farar hula da aka jikkata.”

 

Sanarwar ta Biden na zuwa ne kusan shekara guda, bayan da sojojin Amurka suka kammala janyewa daga Afganistan da ta mamaye, a matsayin mayar da martani ga hare-haren ta’addanci na ranar 11 ga Satumban shekarar 2001, da ake zargin ‘yan kungiyar al-Qaeda da kaiwa a kan Amurka, hare-haren da ake zaton sun halaka kusan mutane 3,000.

 

Fiye da mutane 929,000 ne dai suka mutu a yake-yaken da suka biyo bayan harin ranar 11 ga watan Satumba da ake kira 9/11, biyo bayan tashe-tashen hankulan yaki kai tsaye, da kuma sau da dama tasirin yakin. Alkaluman da jami’ar Brown ta fitar sun irin makuden kudaden da aka kashe a yakin.

 

Rahotanni na cewa, kamar yadda CRI HAUSA ta Samu tabbacin hakan, kudaden da gwamnatin tarayyar Amurka ta kashe a yake-yaken bayan harin na 9/11, ya haura dalar Amurka tiriliyan 8, baya ga yadda aka rika take hakki da ‘yancin bil adam a ciki da wajen Amurka. (Ibrahim Yaya)

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button