Uncategorized

HEEDAYAH 17

 Mami ta bude kofar parlonta jin ana knocking, suka yi ido hudu da Shuraim, sauke idonsa yyi da sauri, murya can kasa yace “Ina kwana” A takaice tace “Lafiya…. 

Ya aka yi?” Yace “Karatu xa mu yi?” Mami tace “Da wa?” Ya d’an yi shiru sannan yace “Ban san sunanta ba” Mami tace “Toh sai kayi kokarin sanin sunan nata coz gida daya ku ke ynxu” daga haka ta juya ta koma ciki ya bi ta da wani irin kallo, Mami ta karasa sa ma Heedayah kayanta don har tayi wanka, ta dau hula ta sa mata a kanta sannan tace “You listen and pay attentive kin ji, Kuma kiyi kokari sosai, idan kin dawo xaki koya min nima” tace “Toh Mami” Mami ta kama hannunta suka fita xuwa parlor, har sannan yana tsaye, dai dai kusa da shi Mami ta tsayar da Heedayah, sannan ta juya ta koma ciki ta kulle kofarta, Heedayah ta kai hannu tana laluba wajen ta ji inda yake, hannunsa ta ta6a, bbu bata lkci kamar jira yake ya buge mata hannun yace “Are you stupid” Ta janye hannunta da sauri kamar xata yi kuka tace “Ni me na maka??” Ya kalli left sannan ya kalli right ya fixgo hannunta ya fara tafiya, bin sa take hawaye cike idonta tace “Ni ka sake ni bana so, baxan yi karatun ba kuma, baxan yi ba….” Ko saurarenta bai yi ba har ya isa wani area cikin parlon wanda ya kasance study area din Abba, sannan ya saketa yana mata wani kallo yace “Kika ce baxa ki yi karatun ba??” Cikin kuka tace “Ehh ni baxan yi ba, ka kai ni wajen Mami” ya ja kujera ya xauna yace “Sai ki kai kanki ai” durkushewa tayi a kasa ta fashe da kuka sosai tace “Ni sai na gaya ka da Abba wllh….” bude kofa aka yi Shuraim ya juya da sauri bai jira ya ga wanda ya bude kofar ba ya xamo kasa kusa da ita ya dake cike da karfin hali yace “Okay, sorry mu yi karatun ynxu” ta make kafada tace

 “Ban so” satan kallon cikin parlon yyi duk da bai ga wanda ya fito ba har sannan, ya wani hade rai yace “I said sorry” Kamar jira take tace “Ban so nace” sai kuma ta fashe da wani sabon kuka, kamshin turaren Abbansa da ya ji yasa yasan Abba ne a parlon, ya dawo kusa da ita ya kamo hannunta a hankali yace “But nace kiyi hakuri, I’m sorry” ta turo baki tace ”

To me yasa xaka buge min hannu sbda bana ganin ka, kuma shine kake ja na don in fadi in ji ciwo” Ya kara satan kallon parlon cikin dakiya yace “To rama” ta kai hannu ta laluba kafarsa sannan ta maka mashi duka a nan, kallonta kawai yake da mamaki xuciyarsa na tafarfasa, still controlling himself yace “Shkkn?” 

Ta gyada masa kai a hankali tana goge idonta, ya koma saman kujera yace “To fara karatun” tayi kasa da murya ta fara karatun a hankali, har Heedayah ta tsaya a aya na 15 bai ji inda xa ayi mata gyara ba, her recitation was perfect and cool for her age, sai dai wayarsa kawai yake dannawa, Ya saci kallonta ganin tayi shiru sai dai bai ce komai ba still pressing his phone, ta turo baki tace “To ai a nan mu’allimata ta tsaya min” yace “Toh sai ki tsaya a nan din” yana fadin haka ya mike ya tafi kitchen, Sabuwar me aikin da Mumy ta dauka ne a kitchen din tana ta gyare gyare da goge goge, yace “Wancan yarinyar xaki dauka ki kai ta wancan part din…”

 Gaishesa tayi da ladabi tace “Wace yarinya yallabai?” Fita yyi kitchen din yace “Ki taho ki ganta” sai da ya tabbatar ta ga Heedayah sannan yayi wucewarsa sama, har part din Mami mai aikin ta kai ta, duk da sai faduwa gabanta yake don ba karamin warning Mumy tayi mata ba kan cewa ko bangaren Mami kar ta kuskura ta bi balle ta shiga, Mami ta bude kofa ta amsa gaisuwan mai aikin sannan ta kama hannun Heedayah suka koma ciki ta kulle kofar, Mami na kallon Heedayah tace “Ina me koya maki karatun?” Heedayah tace “Mami bai koya min komai ba” Mami tace “Me yasa?” Heedayah ta 6ata fuska tace “Mami mugu ne, I don’t like him to teach me anymore….” 

Mami dai bata ce komai ba ta wuce can bedroom da ita, Heedayah tace “Mami he is wicked, ni nafi son wannan din nan ya koya min” Mami tace “Wa?” Shiru Heedayah tayi sai kuma tace “Yace min sunansa Fatima shi ma, kilan baya son gaya min sunansa” Mami na kallonta tace “A ina yake?” Heedayah tace “Wanda ya xo jiya ya tafi da ni” Mami tace “Sunansa Junaid, but you call him Yaya” tace “To, na fi son Yaya ya dinga koya min” Mami bata kuma cewa komai ba ta xaunar da ita saman gado tace “Kwanta kiyi baccin ki xan je in hada maki breakfast” daga haka ta fita dakin, 

Heedayah ta kwanta. Mami na tsaye kitchen su Rabi’ah suka shigo ajiye plates da cups da suka yi breakfast duk suka fice bbu wanda yace mata komai, ta gama dafa Indomie da kwai da shayi da take yi ma Heedayah ta fito kitchen din, a parlor ta tadda Abba alamar he is going out kuma ita yake jira ta fito kitchen, yana kallonta yace “Ina Heedayah, bata gaisheni ba yau” Mami tace “Let me bring her” daga haka ta wuce bangarenta, 

Duk wannan abun Mumy na ta kai komo parlon kai kace wani abu take yi, Abba dai bai ce mata komai ba don har ranan bata gaishesa bata masa magana a gidan, Yana ta tsaye parlon Shuraim ya fito shi ma xai fita, Abba yace “Yaushe rabon ka je gaida kaka Aliyu?” Ya d’an yi shiru kafin yace “Abba bana dawowa da wuri ne ynxu” Abba yace “Ohk yau ka je ko da kuwa tsakar dare ka dawo, and you go with Heedayah ita ma ta gaisheta, she is complaining ba a kai ta ba jiya da naje….”

 Shuraim ya kalli Abba, amma bai ce komai ba, Abba yace “Su Khadijah ma nace idan sun dawo islamiyya su wuce can, so idan ka je sai ku dawo tare gaba daya” Mami ce ta karaso rike da Heedayah, Abba na kallonta ya dafa kanta yace “How are you dear?” Tace “Good morning Abba” yace “Morning Daughter, kun yi karatun yau koh?” Ai ko rufe baki Abba bai yi ba Shuraim ya nufi kofa, Heedayah tace “A’a bai min ba” Abba ya kalli Shuraim da har ya isa kofa cikin tsawa yace “Aliyu” Mumy ta karaso cikin parlon da sauri tace “Ba gane Aliyu ba?? Shi Aliyun malami ne ko kuma makafi na haifosa ya xo ya dinga yi ma karatu, kaga a gaskiya barrister ku tsaya iya Lane din ku kai da Sabuwar matarka da makauniyar ka a gidan nan, ku fita harkarta da ta ‘ya yana, Yaushe aka sa Shuraim ya dinga koya mata karatu bani da labari? Kanninsa da suka fito ciki daya ma an ga yana koya masu karatu balle makauniya, to wllh ni a kiyayeni a gidan nan, ku bar ni kawai yanda ku ka gan ni ayi ta tafiya a haka kar ku kai ni bango….” 

Abba yana kallon Shuraim da kyau yace “Me na ce maka jiya da asuba?” Yyi kasa da kai bai ce komai ba, Abba yace “Good, idan kana son ganin the other side of me ka sake tsallake magana ta a gidan nan, wllh sai dai ka tafi wani gidan uban amma ba wannan gidan ba, yanda uwarka ta isa ta fada maka kaji, haka nima, idan kuwa watsar da maganata xaka dinga yi a kan wani banxa son xuciya na uwarka to you have to change anoda father and anoda home, Kuma ni nayi instructing dinka ka dinga koya ma Heedayah karatun qur’ani in har ka isa ka tsallake instruction din in gani” A mugun fusace Mumy tace “To sai me don kace ya canja uba ya bar gidan nan?? Kansa farau barrister? Ai ba abun mamaki bane don ka fadi haka tunda an gama da kai an shanye ka, 

nan gaba mu ma duk kora mu xaka yi ka cika gidan nan da agololi da ‘ya yan tsintuwa, Kuma in har ni na haifesa baxai koya ma wata makauniya karatu ba tunda ban ce yaje xai gani ba” Dariya Mami tayi ta kama hannun Heedayah ta koma bangarenta tana girgixa kai, Shuraim dai bai iya yace komai ba, ya juya ya nufi kofa ya fice daga parlon, Banda kallon Mumy bbu abinda Abba yake as if thinking of how to punish her, cike da neman fitina tace 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button