MAKAUNIYAR KADDARA 45

*Page 45*
………..Sai da ya kai zaune sannan ya ɗan dubeta ya kauda kansa yana
maidawa ga Hajiya iya mamaki har yanzu shimfiɗe a fuskarsa. Kansa ta
shafa tana murmushi. “Mamaki ko?”. Ta faɗa tana kamo hannunsa cikin
nata.
Cikin ɗacin murya yace, “Amma Granny yanz……”
“Shiii” ta faɗa tana girgiza masa kanta alamar kar yace komai.
Badan yasoba dole yay shiru yana binta da kallo. Barin wajen Zinneerah
tayi dan kasancewarsa a wajen yasa taji ya cika mata fili kamar yanda
takeji a duk sanda yana a waje. Handbag ɗin Hajiya iya ta ɗauka tabi
bayan su Bahijja da har sun shige, barci da gajiyar da take ciki ya
haddasama tafiyar tata sanyi sosai fiye da ko yaushe.
Shigowar Khalipha ya sanya Ak dake binta da kallo juyawa ya dubesa.
Murmushin ƙarfin hali Khalipha yayi da matsowa ya rungumesa yana jera
masa kalmar “I’m sorry yayanmu”.
Komai baice masaba, sai kansa kawai daya ɗan kaɗa yana miƙewa. “Dare
yariga yayi nisa, yakamata ku kwanta ku rage gajiya”. Daga haka ya nufi
ɗakinsa ransa duk babu daɗi da dawowar tasu, dan shi ba haka yaso ba.
Ƴan gidan babu wanda yasan da dawowar ƴan london sai washe
gari, a take suka rikice da murnar dawowar Granny, yayinda Baffah kuma
keta mamaki, sai dai dariyar da yaga Huzaifa nayi suna magana da
Khalipha ƙasa-ƙasa ya sashi fahimtar sune suka ƙulla komai. Uffan
baiceba ya shiga layin ƴan murnar ganin hajiya iya shima.
Sai da duk suka lafa da gaishe-gaishe da tambayar jiki sannan su
Zinneerah suka fito suka gaida Baffah suma. Cike da jin daɗi da kulawa
yake amsa, dan ƴan kwanakin da sukai acan harsun ƙara canja kala.
Sai da kowa ya nutsa sannan Baffah ya samu zama da Granny shi
da Mommy da hajiya iya keta murnar ganinta da kiranta autarta. Yanda
Mommy ke nane da hajiya iya sai hakan ya birge Zinneerah har little
ɗinta ya faɗo mata a rai da mamanta itama da baba. Murmushi tayi a
zuciyarta tana mai begen ganinsu.
Kamo hannunta Mommy tayi ta zaunar kusa da ita tana faɗin, “Masha
ALLAHU, lallai yarona ya iya zaɓe, dan ɗiyar tawa kam badaga nanba”.
Kunyace ta kama Zinneerah duk da bata fahimci inda zancen na Mommy
ya dosaba. Sai kuma can gefen zuciyarta ke raya mata ko dai Moos’ab ya
faɗa musu wani abune?. Sosai gabanta ya faɗi, taɗan saci kallon Khalipha
dake ƙoƙarin fita zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Bata gama kammala
tunanintaba ta miƙe ganin kowa ya fice a yaran sai ita kaɗai. Itama
ficewa tai tabar su Granny dan taga alamar magana zasuyi.
Kayan barcine wando da riga a jikinta, sai dai ta ɗora hijjab
mai hannu a sama kalar pink mai haske daya kai mata har gwiwa, gashi ya
ɗau guga dan da zatai salla ta cirosa ta saka.
Fitowarta dai-dai da shigowar AK ɗauke da little a hannu, kamar
daga sama taji muryar gudan jininta na ambaton, “Aunty! Aunty!”.
Da sauri ta ɗago ta kalli hanyar shigowar duk da zuciyarta bata
yarda da abinda tajin ba. Cikin sa’a kuwa sai a kan little daketa zillo
daga jikin AK alamar zaizo wajenta. Shiko yaƙi sakinsa sai ma kafeta yay
da idanu kai tsaye hankalinsa kwance.
A hankali ta motsa laɓɓanta wajen ambaton “Little” da mamaki
shimfiɗe a saman fuskarta. Ga wani bugawa da ƙirjinta keyi saboda
matsanancin kamannin yaron nata da Yayansu da suke ƙara bayyana kansu a
koda yaushe. Musamman yau da fuskarsu ke gab da juna kuma little ɗin
tamkar ya ƙara girma da wayo.
Duk yanda taso ɗaga ƙafarta zuwa garesu ta amshi little ɗin ta
kasa, haka ta cigaba da tsayuwa harshi ya fara takowa a hankali yana
nufota. Tsitt falon yayi kowa ya zuba musu idanu ƙasa-ƙasa, musamman su
Mas’ood da sukasan mike tsakani yanzun. Su Jamal dai yanda Yayan nasu ke
kallon Zinneerah ɗinne da yanda tayi itama ya basu kala suka tsaya kallo
dan son ganin mike shirin faruwa.
Gab da ita ya tsaya, batare da yayi maganaba ya kamo hannunta
ɗaya ya ɗaura na little akai. Kafin ya saki yaron gaba ɗaya gareta yana
motsa laɓɓansa a hankali yanda ita kaɗai zata iya jinsa, itama ɗin sai
da taimakon motsin laɓɓansa. “Sai na tsone wannan idanun”.
Sosai taji wani irin shock saboda jin hannayensa da nata na neman
sarƙewa waje guda lokacin da yake sake mata little, magarsa da yanayin
da ta ji ya sata tura baki da ɗan juya kwayoyin idon dazai tsokale
batare da tasan tayiba.
Leɓensa na ƙasa ya wani cije ganin yanda ta tura baki ga
idanunta sun fara tara ƙwalla suna wani farfar. Ya saki wani munafikin
murmushi da ya nema sakata sakin little ɗin ƙasa yana ja da baya. Da
wani irin slow tafiya ya raɓata ya wuce ƙamshin turarensa na sake bugun
hancinta.
Babu shiri ta ƙanƙame little jin zai suɓuce mata. Suko su Saifudden
suka shiga sunne kawuna ƙasa suna dariyar shaƙiyanci ƙasa-ƙasa. Su
Bahijja kuma da basusan dawan garinba bakuna suka saki cike da mamaki da
al’ajabin abinda Yayan nasu yayi yanzun, amma ya fiske ya wucesu tamkar
baisan da zamansu a wajen ba.
Yana shigewa ɗakin Hajiya iya su Mas’ood suka shiga tafawa da
juna. Khalipha yay ƙasa da kansa yana sakin murmushi da ƙoƙarin kauda
komai dake ransa dan yasan dai ta ƙare. Koda ace ya furtama Zinneerah so
Yayansu ya nuna yanaso wlhy zai iya sadaukar masa. Ballema ALLAH ya
soshi bai taɓa koda nuna mataba duk da kuwa tun sanda ya haɗu da ita a
gidan tai caraf da zuciyarsa. Dan bazai saka haɗuwarsu ta farko a
lissafi ba, saboda kallon matar aure yake mata. Duk abinda yay mata kuma
tausayine a wancan lokacin ba so ba.
Moos’ab ma dai daurewa yake matuƙa wajen danne komai, dan yayi
alƙawarin koda yaƙi sai ya cire Zinneerah a ransa ta koma matsayin matar
Yaya da ƙanwarsa har cikin zuciya.
Zinneerah kam ƙanƙame little tayi a jikinta da sauri mamakin
abinda Yayansu yayi na neman kasheta da ranta. Ta bisa da kallo harya
shige ɗakin hajiya iya ko waiwayosu baiyiba. “Aunty!!” little ya faɗa da
ƙarfi cikin kunnenta yana bubbuga mata kafaɗa. Babu shiri ta juyo garesa
tana sauke tagwayen ajiyar zuciya. Sai kuma ta saki murmushi da lakace
hancin little ɗin tana faɗin, “Haba bawan ALLAH kashemin dodon kune
zakayi ne? Waya kawoka nan?”.
Bata da mai bata amsa. Danshi little ma dariyarsa ya saki maiban
sha’awa saboda lakace masa hanci da tayi, ya kwanta a kafaɗarta yana
zagayo hannunsa ɗaya a wuyanta zuwa ɗayar kafaɗarta. Hannunta ta ɗora
akan gadon bayansa tana shafawa a hankali da murmushi, murya ƙasa-ƙasa