MAKAUNIYAR KADDARA 46

*Page 46*
………Koda akazo yin breakfast yau gaba ɗaya gidan aka haɗu harsu
Momie domin nuna murnar dawowar Hajiya iya. Aiko taji matuƙar jin daɗi
dan bakinta yaƙi rufuwa. Little na jikinta tana bashi da kanta. Ita
Zinneerah ma har mamakin yanda ya saki jiki da kowa takeyi, gashi yanzu
ta fahimci dai yana neman zama ɗan gidan. Har ranta tanajin daɗin yanda
kowa bai taɓa gano alaƙarta da little ɗinba. Amma idan ta tuna randa
zasu iya sanin abin na damunta da sakata a fargaba.
Tunda ta zauna bata yarda ta kalli inda AK yake ba, dan ta samu
ta ɗan maƙale ne jikin aunty Safiyya ba sosai ake iya ganinta kamar kowa
ba. Garama Huzaifa da yazo zai zauna sai da ya tsokaneta. Murmushi kawai
tayi dan ita kam ba iya irin wannan wasan tayiba saboda miskilancin ta.
Shima dai ya fahimci miskilarce, hakan ya sashi faɗin, “Like Husband
like wife”.
Murmushi su Baffah duk sukayi, yaran kuwa kowa yay ƙasa da kai yana
gumtse dariya. Ita dai Zinneerah ba sanin inda ya dosa tai ba. AK kuwa
yi yayi kamarma baiji mi Huzaifa ya faɗaba, ya maida hankali gacin
abincinsa kawai dan hajiya iya ta riga tai musu sabon idan suka zauna
gaban abinci shi kaɗai suke bama dukan nutsuwarsu har sai sun kammala.
Shine farkon tashi, kamar an tsikari little shima ya miƙe daga
jikin hajiya iya yana faɗin, “Abbana zanje”.
Yanda yay zaram ɗin ya miƙe da maganar tasa data fita raɗam ya
saka kowa yin dariya, banda Zinneerah da aranta take raya (kajimin yaro
da shegen ɗafa, wai Abbana).
AK kam dawowa yay da baya yasa hannu ya ɗaukesa yana murmushi, ba
komai kesa little na ƙara manne masaba sai yawon da yake fita da shi,
shiko yaro dama akwai son yawo shiyyasa duk inda sukaga maza koda basu
da wayo suke maƙale musu. Balle little dake da wayo masha ALLAH.
“Sweetheart kaima fa ka iya yawo na lura”. AK ya faɗa lokacin da
suke nufar ɗakinsa shi da little.
Mommy dake binsu da kallo ita da Baffah tace, “Ƙuruciyar little
tamkar Adnan, har wayon tsiyar ya kwaso bai rageba. Wani irin bugawa
ƙirjin Zinneerah yayi a take, har takai ta ɗago ta kalli Mommy batare
data saniba. Haɗa ido sukai da Hajiya iya dake kallonta cike da nazari
ita, tai saurin maida kanta ƙasa. Harga ALLAH maganar ta daketa shiyyasa
duk abincinma ya fita mata a rai.
Ganin yanda taketa faman juya cokali a cikin abincin Hajiya iya
tace, “Inno kin ƙoshi ko?”. Da sauri tako ɗaga kanta jin ta samu mafita,
kafinma Hajiya iya ta sake cewa wani abu ta miƙe da sauri. Sauran da duk
basu san mike faruwaba basu fahimci komaiba. Da wannan damar Zinneerah
ta samu ta silale daga wajen ta koma ɗaki.
Tayi zurfi a tunani sosai Hajiya iya ta shigo, harta zauna
Zinneerah batasan da zuwantaba, sai da ta gama mata kallon nazari tsaf
sannan ta taɓata. Nufashi Zinneerah ta kawo a zabure, sai dai ganin
hajiya iya ya sakata sauke ajiyar zuciya da ɗan ƙaƙaro murmushi.
“Granny ashe kin shigo? Bara na ɗauka miki maganinki kisha”. Tai
maganar tana ƙoƙarin tashi. Kamo hannunta Granny tayi ta maida ta ta
zaunar. Hakan yasa Zinneerah ɗan kallonta. Amma ganin itama kallonta
Granny keyi saita maida kanta ƙasa dan kallon ya banbanta da wanda ta
sani. “Kamannin Abdul-Mutallab da Moddibo na ruɗaki ko? Muma haka suke
ruɗamu a koda yaushe. Sai dai nasan jinine kawai yasa Hauwa’u haifo mai
kama da Moddibo”.
Ɗan murmushin yaƙe kawai Zinneerah tayi kanta a ƙasa har yanzu,
Hajiya iya taci gaba da magana batare da ta damu da yanayin Zinneerah
ɗin ba. “Ki shirya zuwa anjima da yamma hajiya Zulai zatazo ku wuce
katsina akwai wani aike da zaku kaimin amma ke da ita kawai zakuje”.
Saurin ɗagowa Zinneerah tai ta kalli Hajiya iyan a karo na farko,
dan itafa tama kanta alƙawarin bazata ƙara taka ƙafarta katsina ba
saboda tsoron karsu Hajiya su ganta. Duk da a yanzu tafi ƙarfin a ƙara
kaita inda aka kaitan, kuma tasan ba gidan yankan kai baneba kamar yanda
ƙuruciya ta sata kiran wajen a baya.
Cike da basarwa Hajiya iya tai ɗan dariya, “Oh wai kokin taɓa zuwa
Katsina ne Inno?”.
Murya a raunane Zinneerah tace, “Sau ɗaya Granny”.
“Kai, duk da kasancewarki bakatsina? A to karma ki faɗa gaban su
Jamal sumiki dariyar Danya kawai kika sani”.
Ƴar dariya tayi saboda yanda hajiya iya tai maganar cike da raha.
Batare da tunanin komaiba tace, “Granny ai shima aiki Inna tasa wata
mata taje dani nayi bama yawo naje ba”.
“Aiki kuma? Kina nufin aikatau fa kenan?”.
A take damuwa ta bayyana akan fuskar Zinneerah, ƙwalla suka ciko
mata idanu, murya a raunane tace, “Eh aikatau Granny, ni bansan miyasa
Inna bata sonaba. Dagafa wata ƙawarta tazo ta bata labarin kuɗin da ake
samu shikenan tasa na bita ko baba bai saniba. Amma tsabar sharri dana
dawo sai tace wai yawon banza naje, wlhy kuma ba yawo najeba”.
“Toke miyasa baki faɗama Babanki gaskiyar abinda ya faruba?”.
“Haka kawai naji inajin tsoro Granny, koma nayi niyyar faɗa masa
saina kasa dan Baba tsoron Inna yakeji saboda masifarta wlhy, bama shi
kaɗaiba ƴan garinmu da yawa tsoronta sukeji dan jarababbiyace sosai”.
“Kai wannan mata ALLAH ya wadaran halinta, ina daɗi ace miji na
tsoronka. To amma ke miya faru har tasa aka tafi dake aikatau babu wanda
ya sani, harma ta samu damar miki sharri kinje yawo?”.
Hannu Zinneerah tasa ta share hawayenta daketa sakkowa saboda tuna a
yanda tabar Danya wancan lokacin, babu wani tunanin wayon manya Hajiya
iya ke mata ta fara zayyana mata yanda abin ya kasance.
“Hajja lanti ƙawar inna ce sosai, dan nidai tare na sansu tunda na
fara wayo, dan Hajja Lanti dillaliyace a garinmu, tana kuma saida
abubuwa iri-iri. Daga baya kuma ta koma ɗaukar yara tana kaiwa aikatau a
birni. Hajja lanti ba sona takeba itama, shiyyasa bana murna da zuwanta
gidanmu, dan duk randa tazo da wahala kaga harta tafi Inna bata dakeniba
saboda tsaban iya haɗa gulmanta. A wata ranar asabar na dawo daga tallan
gyaɗa da riɗi a gajiye na iskesu zaune a tsakar gidanmu suna magana da
ban san kota micece ba. Ni dai na gaidasu na bama Inna kuɗin tallar na
shige ɗaki dan tace karna sake zama a tsakar gida idan tayi baƙi. Ban
jima da shiga ba ta ƙwalamin kira. Koda na fito sai da suka gama min
kallo na wani lokaci ne naji hajja Lantin na cewa “Ai wannan ma itace
dai-dai a yanzu. Dan za’a jima ana samu tattare da ita”. Bansan ina
zancen nasu ya dosaba. Ni dai Inna tacemin naje na canja kaya nawuce can