UBAYD MALEEK 32

 

***************

Da sauri ta dago ta kallesa lokacinda ya jinginata da kofar dakin bayan ya rufe, ta kalli faffadan kirjinsa dake bayyane sbd fitowarsa wanka kenan daure da brown towel ta ‘dan juyar da kanta ahankali ta iya bude Baki tace”

Afia na Palo tare muke…

Wani kallo yayi Mata da idanuwansa dake kan fuskarta ya sake matseta jikin kofar har jikinta na mannuwa da nashi ta ja wani guntun numfashi tana Dora tafin hannunta kan qirjinsa batareda tasaniba 

Hakan yasa maganar dazaiyi ta bace masa yayi shiru Yana kallonta 

Ta sake dagowa ahankali sai suka hada idanuwa taji wani sanyi da kwanciyar hankali na shigarta sai fuskarta tafara yunqurin bayyanarda murmushi tayi saurin sauke Kai Tana motsawa ahankali sbd qamshinsa daya Gama cika hancinta Yana neman sage qafafunta.

Motsawar datake yasa qirjinta ringa gogarsa ya rintse idanuwansa Yana budesu akanta tareda yin baya Yana sakinta sbd Jin zata iya jawo damuwa.

Closet ya nufa batareda ya waiwayo ba bare ta iya gane halinda fuskarsa take ciki.

Bayansa tabi da kallo zuciyarta da dukkanin gangar jikinta na karbuwar da kowane irin sako ne yasoma isar mata.

Waiwayowa yayi ahankali ya kalleta idanuwansu suka shiga cikin na juna ta dauke kanta tana sakin wani boyayyan murmushi Wanda yasashi juyowa gabaki daya Yana Mata kallonda yasata bude dakin ta fito da gudu tanajin gabaki daya jikinta na daukar vibration Kai tsaye dakin farhat ta nufa ta zauna bakin gado tana sauke numfashi tana warware daurin gashinta Dan tasamu iska Tako Ina ya shigeta.

Farhat dataga shigowarta tabiyota dakin itama tana tsayawa gabanta tana kallon fuskarta da mamaki tace”

Aunt NURU you’re smiling???

Dagowa NURU tayi ta kalli farhat din tana zuba Mata idanuwanta tana kallo kamanninta da mahaifinta ta janyota jikinta tayi kissing Kumatunta ahankali Yana rungumeta ahankali tace”

I love you sweetie.

Da farin ciki farhat ta maqale NURUn tana cewa”

I love you more my Aunt.

Zamansu sukayi a dakin saida kowa yashige sallar magriba tukuna ta fito ta haye saman batareda kowa yaganta ba taje sharp sharp tayo aikinta ta fito batareda shima yaganta ba sbd yafita sallah baya saman.

Kodata sauko takaiwa mum Sarah kayan gyaran dakin farhat Takoma acan tayi sallah tukuna ta fito Takoma kicin tasaka hannu a aikin hada abincin maleek din na dare ta jera a tray takai saman tadawo ta nufi dakinsu tashiga tanajin nauyi da kunyar afia nason shigarta Amma ta daure ta danne tashigo dakin tana kallon afian dake zaune da littafi a hannunta tace”

Karatu Kuma ayanxu afia?.

Kasa kallonta afia tayi tace”

Eh wani Abu na dauko Ina dubawa.

Ok kitashi anyi sallah tun dazu.

Toilet ta wuce tayo wanka tana fitowa afia tabita da satar kallo tana cewa”

Kingama aikin?

Dakatawa NURU tayi daga shafa spray ajikinta ta ‘dan waiwayo ta kalli afian tace”

Eh na gama na yau dai.

Cigaba tayi da abinda takeyi tagama tasaka kayan bacci ta fita dakin ta nufa dakin farhat acan sukasha oat suka sallar ishai sukai kwanciyarsu.

Washe gari tunda safe dakin padima ta nufa dan tayata shiri saidai padimar Bata buqata Kamar yanda tafada Mata Dan haka bata takura kantaba ta juya ta ficewarta ta nufa kitchen aikin breakfast tana gamawa ta nufi daki ta tada farhat tayi Mata wanka tareda Shirin school suka fito tabata breakfast da kanta ta rakata bakin mota driver ya wuce kaita tadawo ciki ta hadawa padima kayan breakfast a tray ta nufi dakin datake takai Mata sbd dama bakowa ke cin abincin a dining din gidan ba daga maleek sai iyalansa.

Tana shiga ajiye Mata kawai tayi ta fice 

Qarfe goma driver ya kawo mota bakin kofar shigowa Palo Yana jiran fitowarsu jekadi wadda dukkanin saqon Anneti na miqawa NURU sauran Wanda ya rage ta shanye da safiyar suka fito NURU na gefen padima data matsu su Isa gizah rayuwarta itama ta canza gaba daya.

Shiga mota tayi ta zauna tareda kallon NURU tace”

Allah yabawa kowa rayuwar daya cancanta Dan haka gamo na alkhairi uwar renon farhat.

Wani qayataccen murmushi NURU tayi zancen padiman Bai tabataba ta dago tace”

Idan kinje Ina gaidasu abal da meryam, Jekadi zata Baki saqo a gizah da nawa Dana MALEEK duka kafin ki wuce delah,

Allah ya tsare hanya.

Maida kallonta kan jekadi tayi cikin kulawa tace”

Jekadi a sauka lafiya.

Da girmamawa jekadi tace”

Allah yasa mushrah Kuma godiya muke Allah ya qaro girma.

Shiga mota jekadi tayi aka shigar da kayansu motar driver yaja suka fice NURU na juyawa Takoma ciki direct ta nufi daki ta tube tafada wanka.

Tana fitowa ta zauna gaban madubi tana kallon fuskarta datakeson shafawa janbaki Dan Bata taba sawaba Sam ita Bata kwalliya iyakacinta shafa bronzer itama sama sama sai lip balm shima Mara Kara Amma yanzu son yin kwalliyar taji Kamar ya shigeta tana ra’ayi Dan haka tana gama shafa oils da creams dinta saita shafa face primer ta shafa powders kawai da liner cikin idonta ta dauki Nude lipstick tashafa akan lips dinta me sirkin pink pink.

Kallon fuskarta tayi aga kwalliyar tayi Mata sbd batai yawaba Kuma sbd Bata taba yiba sai tayi Mata kyau sosai.

Tashi tayi ta dauko doguwar English grown tasaka peach kala ta Sanya Sanya Dan kunne qarami ta fice daga dakin tabar afia da idanuwanta suka fara yaji yaji sbd kallon ikon Allah.

Tashi afian tayi itama ta nufi toilet tayo wanka tafito ta shirya cikin doguwar riga kusan irinta NURUn Dan dama kusan duk kayansu iri dayane.

Makeup tayi me kyau itama ta fito Palo daukeda laptop tazo ta zauna tareda bude laptop din tafara wani aikin tanashan tea data saka Fana hado Mata.

Murmushi kawai NURU dake zaune tayi tareda janyo musu firar wani program sunayi sbd kada shedan yasamu Shiga ranta.

Suna cikin firar Kiran lailah yashigo wayar afia 

Suka kalli wayar atare kafin NURU ta dauke Kai tana miqewa tace”

Bari naje nataya Fana aikin abincin lunch.

Tana barin gurin afia ta maida kallonta kan wayarta tana tunanin daukan Kiran sbd tasani Babu wani abin kwanciyar hankali a wayar mum saina buqatarta wadda ita koyaushe abinda takeso shi zaayi Dole akuma lokacinda takeso din.

Kasa daukan wayar tayi ta saka wayar silent tareda Miqewa tabar palon ta nufi daki sbd kada NURU ta fahimci Bata dauki numbern mum dintaba.

Koda tashiga daki kashe wayar take kokarin Yi wani Kiran yasake shigowa  ta sauke numfashi tareda dauka cikin sanyi tace”

Mum.

Dagacan bangaren lailah ta amsa da cewa”

Afia since when did you become this foolish dazan Kira kina ganin kirana bazaki daukaba?.

Ajiyar zuciya afian ta sauke tana Jin gajiya da halayen mum din tace”

Mum bana kusa Kuma Dan Allah mum kidaina wannan fadan kina bani tsoro ne sai inringa tunanin kina cikin wani halin ne sbd gabaki daya kinayi kaman bakya cikin kwanciyar hankali.

Wani baqin cikin afia ne ya tasowa lailah taji kaman ta zageta ko zata rage Jin abinda takeji na abinda yake gabanta na contact data rasa bayan dukkanin dukiyar data kwashe ta zuba Dan kawai ta samu contact din wanda zai sauya rayuwarta gabaki daya tazama abin gogayyar maleek saigashi ta rasa babban abin damuwar shine a qarqashin maleek contact din yatafi shiyasa yanzu a haukace take da buqatar komawa maleek kafin abinda take dashi yafara yin qasa Amma wannan wawuyar Yar tata tanayi kaman batasan abinda takeson tayi Mata ba.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button