TAYI MIN KANKANTA COMPLETE HAUSA NOVEL

TAYI MIN KANKANTA 8

 

???????????????????????????????? *TAYI MIN ƘANƘANTA*

????????????????????????????????

*Zahra Surbajo*

*8*

A harabar gidan yayi parking,tun kan ya gama tsayawa Hajiya da Muhammad suka fito,cike da damuwa yafito daga motar,sannan yayi umarnin da a ɗaukota akaita boysquater dake gidan.

Ba musu masu tsaron lafiyar tashi suka ɗauketa kamar yadda ya buƙata,ba hajiya ba hatta Muhammad ya kaɗu dajin warin da takeyi,haka aka wuce da ita ciki.

Jummai da Asabe Masu aykin gidan hajiya ta kira bayan sunzo tace”ku kwashi kayan wanka maza kuje kui mata wanka,ku tabbatar da cewa komai na jikinta kun wanke ganinan zuwa”

Amsawa sukayi da sauri suka wuce aywatar da abinda tace.kallonta takai gun Muhammad wanda gaba ɗaya Babu annuri a fuskarsa tace”Muhammad bari inje in dubata bazan jimaba zan dawo”

“Mummy wannan warin fa ze iya cutar dake,gaskiya da aba direba ita yakaita asibiti,nan akwai matsala”ya faɗi cikin yanayin damuwa.

“karka damu bari in dubata ba abinda ze sameni”ta faɗi sannan ta juya ta bi bayan su jumman.

Se a lokacin Muhammad ya ƙarasa gun mahaifinshi yana murmushi ya ɗan rusuna yace “sannu daddy”

Dafoshi yayi yana murmushi yace “Yauwa ɗan gidan daddy ya hanya,ya kuma hajiya da jikin”

“hanya Alhmdllh,hajiya kuma ta warke sosai”

Daga haka suka shiga ɗan taɓa hira kaɗan suna jiran hajiya ta fito suji in agidan zata diba mara lafiyar ko asibitin zaa tafi.

Hajiya lokacin data shiga toilet ɗin kusan kukane yakusa kwace mata ganin yadda gaban mara lafiyar ke shirin lalacewa.

Safa tasaka sannan ta tara ruwa me zafi,tasa detol,sannan ta tsomata acikin ruwan ta fara wanke gurin,wayyo Allah na gurin yauƙi yake gashi har wani kore kore yake,ga uban wari.

Hajiya na fara wankewa tsananin azabar da zahra taji yasa ta farkawa daga suman da tayi ta kwalla wata ƙara.

A gigice Daddy da Muhammad suka nufi boysquater ɗin,sede suna shiga jummai ta dakatar dasu a falo ta hanyar shaida musu wanka ake mata.

Kimanin awa guda Hajiya ta kwashe tana sauya ruwa tana wanke gurin Zahra kuka take iya ƙarfinta tana kiran sunan Allah.

Kan kace me tuni wannan azababben wari ya tafi se ɗan wanda baa rasa ba,doguwar riga ta marasa lafiya hajiya tasa mata sannan suka ɗaukota zuwa ɗakin da hajiya ta ware domin kula da marasa lafiya na gida,ba abinda babu aciki.

Kan gado ta ɗorata,sannan ta fara wanke duk inda taji rauni sakamakon bigeta da mota tayi.seda tagama tsab sannan ta buɗe gaban nata ta kawo fitilar likitoci ta haska,sosai tausayinta ya kamata,wannan sashin ba ɓangarenta bane shiyasa bata fahimci ko matsalar menene ba.

Kashe fitilar tayi sannan ta rufeta,tasa jummai ta kawo mata abinci,ayko kamar tsohuwar mayunwaciya haka takecin abincin har ta cinye tasha ruwa,

Magunguna hajiya ta bata,sannan ta kwantar da ita ayko kamar jira bacci yayi awon gaba da ita,sosao tausayinta ya taɓa zuciyar hajiya,yarinya ƙarama amma ta haɗu da matsalar  taɓin hankali,dan atunaninsu su dika mahaukaciyace.

Falo ta dawo gun su muhammad  da Alhaji tace cikin damuwa “Alhaji ni nayi nawa,sede yarinyar nada matsala a al’aurarta,shine nake ganin ko de A kaita Hammad Hospital ne,kaga can akwai kayan ayki zata fi samun kulawa,tunda can dama na ɓangaren mata ne”hajiya tace cike da damuwa.

“wanne irin Hammad hospital,menene zaay mata acan wanda ɗanki Muhammad baze iyaba,ko kin raina kwarewarsa ne,da har kike cewa akaita wani guri bayan ga abu agida”cewar Alhaji yana duban Muhammad.

“Mummy zan dubata ingani insha Allahu baze gagara ba,abinda zaay mata a wancan asibitin nima shi zanyi insha Allahu”cewar Muhammad.

juyawa hajiya tayi yabita abaya zuwa inda Zahra take kwance tana bacci.

Safa yasaka a hannu sannan ya kunna fitilar likitoci ya matsa da ita gabanta hajiya ta buɗe masa gaban na zahra.

A Hankali ya duƙa yana kallon gurin,yasa hannu ya ruƙo wannan tsoka dake lilo itama ya ƙare mata kallo, tsawon mintuna arba’in ya kwashe yana karantar gurin sannan ya ɗago ya cire glass ɗin fuskarsa,sosai damuwa ta bayya na a fuskarsa idanunsa sukayi ja,tsigar jikinshi har tashi take yace “mummy fyaɗe aka mata,kuma a ƙalla ya kwashe watanni da yi matan,kuma anji mata ciwo agurin,wanda sanadin hakan ta kamu da yoyon fitsari,ga infection me ƙarfi daya kama gurin wanda in baayi da gaske ba ze iya rikiɗewa yakoma cancer”

.Salati mummy tayi sannan tace”oh ni jamaa yaushe zasu fara tsorom Allah ,yarinya ƙarama a haike mata wannan wanne irin cin zarafine”

“mummy muje inyi list na abinda zaa buƙata,dan akwai buƙatar ayi mata ayki yau ɗinnan ayi mata plushing ɗin infection ɗin sannan a ɗorata akan magani”cewar Muhammad bayan ya cire safar dake hannunsa ya wanke Hannunsa suka fito ransa Aɓace ya rasa dalili,ko kaɗan baya ƙaunar akawo masa yara an musu fyaɗe ransa ɓaci yake ji yake da ze ga wanda ya aykata musu ba makawa seya kasheshi .

Muje zuwa

Surbajo for life.

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button