Labarai

Sadiya Haruna Ta Kammala Islamiyyar Gyaran Tarbiyya Da Kotu Ta Tura Ta

Sadiya Haruna matashiyar nan da ta shahara a shafukan sada zumunta, inda take wallafa bidiyo da hotuna na harkokin ƙashin kanta da kuma tare da wasu fitattun matasa a wasu lokutan, musamman a Youtube da Instagram ta kammala ɗaurin-talalar da wata kotun shari’a da ke Jihar Kano ta yi mata.

Muryoyi ta ruwaito an yi wa matashiyar daurin-talala ne bayan da a watan Agustan da ya wuce rundunar Hisbah ta kama ta bisa zargin “yaɗa hotunan batsa” a shafukanta na sada zumunta.

Inda Alkalin kotun Mai shari’a Ali Jibrin ya yanke mata hukuncin ɗaurin-talala na wata shida, sannan ya yi umarni ta riƙa zuwa makarantar Islamiyya domin koyon “tarbiyya” da kuma “sanin yadda za ta riƙa mu’amala a matsayinta na Musulma”.

Da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Jibrin ya umarci jami’an hukumar Hisbah su riƙa raka ta makaranta sannan su kai masa rajista domin ya tabbatar tana zuwa.

Sai dai a yau Talata ne hukumomi suka fitar da sanarwar cewa matashiyar ta kammala zuwa Islamiyyar kuma a tsawon lokacin da ta kwashe ta koyi kur’ani da Hadisi da sauran litattafai na koyar da tarbiyya da zamantakewa a musulunci


Post Views:
1

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button