HAUSA NOVEL

A Bari Ya Huce Complete Ebooks

KAUYEN GURIN-GAWA, 1988
Gurin-gawa karamin kauye ne mai tsohon tarihi da ya kunshi al’umma masu sana’o’i daban-daban, amma
duka tushensu daya. Galiban malamai ne da manoma, kuma kauye ne da manyan malaman da a halin yanzun
suka barwa duniya abin da ba za a mance da su ba suka fito. Gurin Gawa na nan cikin karamar hukumar
Kumbotso, yankin Fanshekara ta jihar Kano. Karamin kauye ne, wanda ya samu tallafin gwamnati ta hanyar
wutar lantarki, ruwan sha mai tsabta, da takin zamani, wanda ke taimaka musu kwarai wajen bunkasa harkar
nomansu.
Akwai sanannen hadin kai tsakanin al’ummar garin mazansu da matansu. Sai dai kuma babu titi mai kyau a
Gurin-Gawa. Idan mota ce zata shiga kauyen sai ta yi futuk da kura, mutanen cikinta sun gwaggwara
kawunansu sabida rashin kyawun birjin.
Duk da haka wannan bai hana al’ummar cikinta jin dadin zamanta ba, motar haya ba ta shiga cikin kauyen, sai
dai ta aje ka a titin ka hau achaba ko bayan akori-kurar Rake ta mutanen garin ka karasa ciki. Don haka da
wuya ka ga mutanen birni na shiga kauyen, don a ganinsu ba su ga mai zasu tsinto cikin wannan kalataccen
kauyen ba.
Samarin garin Gurin-Gawa kan fita cikin Fanshekara da wajenta domin neman kwabo, ta hanyar ga-ruwa,
sayar da rake, dukanci, dako da sauransu. Don kalilan ne suka damu da makaranta wadda dama idan dai ta
boko ce, to ba a zancenta cikin garin Gurin-Gawa. Makarantun allo da na Buzu su ne Allah Yai yawa da su a
garin.
Malam Bedi, yana daya daga cikin dattawan garin Gurin Gawa, haifaffen nan ne iyayensa da kakanninsa.
Sana’arsa shi ne noma, yana da gonar rake da gyada, sannan yana nome dankalin Hausa, makani da gurjiya.
Bedi da matarsa Hure, fulanin Gurin-Gawa ne na usul. Mutanen kwarai ne da duk Gurin Gawa ba wanda bai
sansu ba, tare da yi musu kyakkyawar shaida. Babban dansu shi ne Habibu, wanda tun yana karami Malam
Bedi ya dankawa kaninsa mai bi masa a haihuwa ya ke taya shi sana’ar fataucin goron da yake yi daga
Shagamu zuwa Kano, wanda daga baya shi Habibu ya shiga makarantar horas da malamai (SAS) tun daga
wancan lokacin kuwa ya koma Kano kwata-kwata. Shi da Gurin-Gawa sai dai yazo da yawo idan ya zo gaida
mahaifansa wanda yakan dauki dogon lokaci bai yi hakan ba.
Su ma su Malam Habibu ba su wani damu da shi ba, don ba wata cikakkiyar shakuwa ce a tsakaninsu ba. Duk
wani burinsu na duniya yana kan ‘yar autarsu “MAIRO”, wadda ba su samu ba sai bayan shekaru sha takwas
da haihuwar Habibu. Don haka idan ya zo a tura mai kujera ya zauna, ana lale da shi, idan bai zo ba ma
falillahil hamdu.
Inna Hure ce duke tana faman firfita wutar iccenta, domin ta samu ta kammala abincin rana kamin Malam
Bedi ya dawo daga gona. Idanunta sun yi jawur sai zuba suke, ga dukkan alamu irin azababben itacen nan ne
Allah Ya hadata da shi. A gefe ‘yar lelen ce zaune bisa tabarma tana dandasawa ‘yar bebin karanta kwalliyar
juma’a da wani tsalelen yankin yadin mamar-mamar da ta tsinto a shagon tela. Ta daga ‘yar bebin tana
cillawa tana cafewa tana wakarta cikin nishadi, ga dukkan alamu babu yarinyar da ke cikin farin ciki a gidansu
a gaba dayan kauyen Gurin Gawa kamarta, sabida daurin gindin sangarta da cikakken gata da ta ke samu daga
Innarta.
“Ke kam ‘yar gata ce, Ta-Ummule.
Ni uwarki “MAIRO” na tsaya miki.
A taba ki a tabo bala’i,
A duke ki, in rama miki.
Innata ta tsaya min,
Ni kuma na tsaya miki……..”
Sallamar Habibu ce ta katse ta daga wakar da ta ke rerawa ‘yar bebinta, cikin zazzakar muryarta kamar gyare.
Ta yi cilli da Ta-ummulen ta kwasa da gudu ta makalkale shi, tana cewa,
“Yaya Habibu oyoyo!”
Ya ce “Ke da Allah kazamar banza, cika ni, dubi bakinki damale-damale da busasshen koko, hanci duk
busasshiyar majina, sannan kalli hannunki duk bakin tukunya, kin zo kin goge su duka a jikina. Wallahi duk
sanda na doso garin nan cikin fargabar cakumon da zaki yi min da kazantarki nake, shashashar banza an girma
ba a san an girma ba”.
Ya rabata da jikinsa ta karfi, ita ko ko a jikinta, dariya ma ta ke abinta kamar ba da ita yake ba. Inna Hure ta
cika fam, kiris ta ke jira ta sauke mishi kwandon bala’in da ke cike taf a bakinta, sabida wannan tijara da yake
yiwa autarta.
A ganinta Habibu ya tsani Mairo ne kawai, don shi yana birni, ita tana kauye, duk da matsananciyar kaunar da
Mairon ke masa. Babu ranar Allah da zata fito ta fadi, Mairo ba ta ambaci sunan Yaya Habibu ba. Shi kuma da
zarar ya zo irin tarbar da yake yi mata ke nan, ita kuwa kamar dada tunzura ta yake ta yi masa oyoyon, da
dukkan zuciyarta.
Ya matsa gaban Innar ya kai gwiwoyinsa kasa, ya ce
“Inna barkanku da gida, mun wuni lafiya?”
Ba ta juyo daga fifita wutarta ba, haka ba ta kalle shi ba, ta ce “Lafiya kalau”. Cikin danne bacin ranta.
Ya yi shiru cikin zargin kansa. Ya san tabbas ya tabo Innar, don ta sha ce masa idan ba zai daina kyarar mata
auta ba, to ya daina zuwa, babu dole.
Cikin kasada ya ce “Amma Inna ga wannan katuwar yarinyar ki zauna kina hura wuta, ita tana wakar ‘yar
bebi? Duk wani dan arziki kamarta ai yanzu ya dawo ne daga makaranta, yana haramar tafiya islamiyya,
amma ban da wannan, ban da karare ba ta san komai ba, shi yasa duk wasu abubuwa na yara masu hankali,
ba ta san shi ba…………”
A fusace ta juyo ta zuba masa jajayen idanunta, ta ce “Kai saurara. Wai me ye gaminka da yarinyar nan ne?
Me ta tare maka? In don oyoyon da ta ke yi maka ne ba ka so, zan hanata, amma wannan sababin da kake yi
mata ya ishe ni. Ka zo gidan su ka uzzireta babu gaira babu sabar? Ba ta zuwa makarantar, idan kai ka haife ta
sai ka dauketa ka kai ta”.
Ya sunkuyar da kai ya ce, “Allah Ya ba ku hakuri Inna, Inna Allah Ya huci zuciyarku”.
Ta ja tsaki, “Tsuuuu!” Ta ci gaba da aikinta tana ta sababi, shi kuma bai kara tofawa ba, bai kuma tashi daga
durkuson shi ba. Malam Bedi ya yi sallama ya shigo, rataye da fartanyarsa da alama a gajiye ya ke likis, sai
gumi ke disa daga wuya da goshinsa. Yana ganin Habibu sai ya fadada far’arsa, amma jin Inna Hure na ta
sababi sai ya maida fuskarsa ya dinke. Ya dade yana sauraronta ba ta san ma ya shigo ba, tana ta fadan idan
Habibu ba zai daina tsangwamar mata Mairo ba, to ya daina zuwa, don ba ita ta kirawo shi ba.
Malam Bedi ya yi gyaran murya, sai a nan tasan da tsayuwarsa. Ta ce “Ai gara da ka zo, dama binka zan yi
yanzun, ka ja wa yaron nan kunne ya sakar wa diyata mara ta yi fitsari, tunda ba a gidansu ta ke zaune ba,
balle ya ji kunya don an ce kanwarsa ce”.
Malam Bedi ya ce, “Anya Hure? Kina kyautawa abin da kike yi wa Habibu? Ina laifinsa don ya zo gaishe ki?
Wannan yarinya da kike ta tada jijiyar wuya akan an gaya mata gaskiya, wane ne majibincin al’amarin ta nan
gaba a bayan mu? Wannan din dai da kike cewa ya fita harkarta shi ne ba wani ba. To idan ya fita harkar tata
ranar da babu mu, wane ne zai shiga?
Shin ma me ya yi mata da zafi? Don kurum ya ce ta dinga wanka? To ki yi hakuri, Habibu ya daina cewa ‘yar ki
ta yi wanka, don Allah ta shekara ba ta yi ba. Kai taso mu tafi masallaci kar mu rasa jam’i”.
Ai jin haka ta yi daki da gudu ta yayibo mayafinta da takalmin robarta, a gujen ta sake fitowa, “Yaya Habibu ni
ma zani masallacin, dama tun jiya ban yi sallah ba”.
Wani takaici ne ya sake kama shi, ya hadiye ya ce, “To mu je, amma sai ki tsaya a wajen masallacin daga
gindin bishiya kina bin jam’in, don mata ba sa zuwa masallacin maza”.
Ta ce “To idan mun fito zaka rakani mu je mu tsinko wa Inna tsamiyar kunu? Dama Rabe shi yake dora ni, kai
kuwa ka ma fishi tsawo”.
Ya kama baki, “Yanzu Mairo bishiyar tsamiya kike hawa?”
Cikin son ta burge shi, da alfaharin hakan sosai a kwayar idonta, ta ce
“Mu hau tsamiya mu sauko, mu hau magarya, mu hau dinya, mu tsallaka goba. Rannan Lanto ta fado tim! Ta
karya kashin baya, ni kuwa idan na makale a jikin reshen bishiya kamar ‘yar Birrai nake. Bana fadowa, sai dai
in ciko bujena da goba da tsamiya………”
Ya yi gaba ya rabu da ita don takaicinta kamar ya amayo zuciyarsa, amma sai ya yi tunanin to ita me ye
laifinta? Innarta ce ta daure mata gindi.
Habibu saurayi ne dan kimanin shekaru ashirin da biyar. Ya kammala kwalejin horas da malamai ta Kano,
wato (SAS), yana jiran sakamako ne ya wuce babbar makaranta, kodayake ma abin da ya kawo shi GurinGawa kenan yanzun, wanda yake son su tattauna da mahaifinsa.
Alhaji Abbas Mai goro kanin Malam Bedi ne ciki daya, uwa daya uba daya, shi ke rike da Habibu da hidimar
karatunshi, ko da yake morar juna suke tunda kuwa duk wahalar kasuwancinsa na goro, a wuyan Habibun ta
ke, wadda ya ke gudanarwa idan ya dawo daga makaranta da ranakun karshen mako.
Suna zaune a unguwar Yakasai a cikin birnin Kano. Yana da matan aure biyu da ‘ya’ya bila adadin maza da
mata. Saidai ‘ya’yanshi kanana ne da ake haifa akan idon Habibu. Cikinsu duka babu mai shekaru goma.
Babbar diyarshi Ladidi sa’ar mairo ce. Don haka Habibu tamkar wani jigo ne ga iyalin Alh. Abbas wanda duk
suke kauna sabida zumuncinsa da rikon amana.
A rayuwar Alh. Abbas bai taba ganin yaro mai kwazon neman na kai da amana irin Habibu ba. Tunda ya ke
tare da shi, kwandala wannan bata taba bata cikin lissafinsa ba, kimanin shekaru ashirin ke nan. Watau tun
Habibun yana dan shekara biyar. Wannan ne dalilin da ya sa ya maida Habibu dan cikinsa ba Dan dan uwansa
ba.
Taimako dai-dai gwargwado Alh. Abbas na yi ma yayan shi Malam Bedi, kamar ta samar mai ingantaccen
takin zamani, da taimaka mai da motocin noma a yayin girbi, wadanda yake dauko masa haya daga KNARDA.
Bayan wannan sallah da azumi shi ne sutturarsu, haka ta fannin abinci lokacin azumi, tun daga kan sukari,
lipton, madara, da su taliya ba abin da ba ya taso Habibu ya kawo musu, sai dai idan suna nomansa a nan
Gurin-Gawa.
Zumunci ne mai karfi a tsakaninsu, wanda iyayensu suka dora su a kai, har gida Alh. Abbas ya sayawa Mal.
Bedi a Yakasai ya ce ya dawo su zauna tare, inda shi kuma ya ce shi da rabuwa da Gurin-Gawa sai dai
mutuwarsa. Ko ita ba ya fatan a fitar da gawarsa daga Gurin-Gawa, su je can su tsinci abin da suke tsinta a
birnin, shi kam a gareshi kwanciyar hankali shi ne komai.
To amma wannan zumunci na mazan ne banda matan. Babu shiri ko kadan tsakanin Inna Hure da matan Alh.
Abbas wato Habiba da Hajara. Tun sanda daya daga cikinsu ta taba cewa a bata Mairo ta dinga taimaka mata
hidimar ‘ya’yanta ta kulla gaba da su. Ta ce kuma wadda duk ta kara tako mata gida, Allah Ya isa. Ta rasa
dalilin da ‘yar tata ta tsolewa kowa ido. Ba abin da ta ke so a rayuwarta irin ta budi ido ta ga Mairo na wasan
‘yar tsanarta a tsakar gida, suna harkokinsu gwanin ban sha’awa.
Don haka ne ko makarantar firamare da ake sa yara a kauyen taki yarda ta sakata, ita dai su zauna abinsu.
Sai da Mal. Bedi ya yi da gaske kamin Mairo ta dinga zuwa karatun allo a makwabtansu, daga takwas na safe
zuwa sha biyun rana. Nan din ma ba wani abin arziki ta ke tabukawa ba da ya wuce tsokana, jan fada, surutu
da guduwa idan Malam ya soma gyangyadi.
Abin da Mairon Hure ta kware akai shi ne hawa bishiya. Yadda kasan kadangaruwa koko Gorilla haka ta ke
makalewa a jikin bishiya. kusufa-kusufa ta iya kurdawa ta tsinko abinda ranta ke so ta cika bujenta. Duk
girman bishiya Mairo zata iya dafe ta, ko tsoron irin aljannun nan da ake ce suna zama a bishiyoyi ba ta yi. Ta
tsinko musu su ci abinsu, ita da Innarta, wannan ya fi komai dadi ga Hure.
Mairo yarinya ce ‘yar kimanin shekaru takwas cif. Amma kaifin bakinta ya fi na dan shekaru ashirin. Kyau kam
ba a magana, tsurarshi na Inna Hure, doguwa shafal-shafal da shafaffar mara gami da lafiyayyen kugu, wanda
tun tana jaririya haka yake. Sumar kai yalwatacciya, yalo-yalo kamar ta hada jinsi da Larabawa. Sai dai fa
dankare take da kwarkwata da amosani wanda ya bi ya cinye rabin gashin.
Wani aiki sai Hure Innar Mairo, don tunda Mairo kukan kitso ta ke, aka shafe yi mata kitso a doron kasa. Kai
wata kila ma ta manta akwai suma akan Mairo, don kullum kulle ta ke tamau cikin wani bakin dankwali mai
masifar dauda. Sai idan kwarkwatar ta ishe ta da cizo ne ta ke tube dankwalin ta samu gefe guda ta yi ta susa
da hannu bibbiyu har sai jini ya bubbugo.
Wannan shi ne babban takaicin rayuwar Habibu, yana matukar bakin-ciki da tsarin rayuwar kanwarsa tilo,
wadda kuma Allah Ya sanya masa matsananciyar kaunarta da tausayinta. Ta wani bangaren ba ya ganin laifin
Inna Hure, domin haihuwar ce Allah Ya ba ta a tsufanta, bayan ta riga ta fidda rai da samunta.
Sannan yawan aiyukan gida da ke kanta ba zasu barta ta kula da irin wadannan kananun abubuwan game da
yarinyar ba.
Duk ba wannan ya fi damunsa ba, kamar jahilcin Mairo. A ganinsa Mairo jahila za a kirata kai tsaye, ba arabi
ba boko. A ganinsa da tana zuwa makaranta, wannan duk wani abu ne da ita kanta zata yi wa kanta nan gaba,
ba tare da kowa ya sata ba.
Bayan sun fito masallacin ya duba inda ya ce Mairo ta tsaya ta yi sallah, ba ta ba alamunta, balle dardumar
karauninta. Ya juya gabas da yamma, Kudu da Arewa babu Mairo. Ransa ya sosu, ya kira wata ‘yar yarinya mai
tallan rogo, ya ce “Don Allah ko kinga Mairon Hure?”
Ta ce, “Na ganta ta mika kwanar gidan su”.
Ya ce, “To madallah. Ta yi gaba abunta dai-dai sanda Malam Bedi ya cimmasa da cazbaha a hannunsa ya ce,
“Mai kake tambaya ne?”
Ya ce “Mairo mana, sama ko kasa na nemeta na rasa?”
Dariya ya ba wa Malam Bedi, ya ce “Mairon ce zata zauna maka waje daya? Ai yadda kasan tsuntsuwa haka ta
ke. Idan dai ba gaban Innarta ba ne babu inda zata zauna. Ai jin ku kawai nakeyi da ka ce wai ta zauna nan mu
fito”.
Ya girgiza kai suka ci gaba da tafiya yana ba shi labarin Mairo. Wanda duk mai bakanta zuciya ne ga Habibu.
Ya ce “A rana in ba a kawo min kararta sau hudu ba, a kawo sau shida. Malaminsu ya gaji da sulalewar da ta
ke yi, ya ce ta yi zamanta gida. Ni al’amarin Mairo ai sai addu’a. Kuma duk Hure ce ta jawo”.
Habibu ya yi kankan da murya ya ce “A gaskiya Baba kai ma da naka laifin. Mai yasa idan Innar ta yi hukunci
akan Mairon ba ka ketarewa? Yanzu sabida Allah kamar Mairo ace har yanzu ba ta shiga makarantar boko ba,
sai yaushe? Sai karatun ya wuce lokacinta? Fisabilillahi ina matukar takaicin rayuwar Mairo. Ina tausaya mata,
domin dai ita ‘ya mace ce, gidan wasu zata je ba da jimawa ba.
Babu mijin da zai iya zama da ita da wannan rashin tarbiyyar wadda ni ba haka aka yi mun ba”.
Ya yi shiru kamar zai yi kuka, zuciyarshi na matukar kuna.
Malam Bedi da alama zancen Habibu na shigarsa. Ya ce “Yanzu ni me zan iya akai Habibu? Ba karamin abu ba
ne Hure ta amince akai Mairo makarantar book ba. Ni kuma bana son tashin hankali balle abin da zaya bata
mini rai, ina zamana lafiya”.
Habibu ya dubi mahaifinsa cikin ido, ya ce “Shin Baba kai ko Inna wa ke auren wani?”
Malam Bedi ya ce
“Ni ne”.
Ya ce “To matukar kai ke da iko da ita dole ka ba ta umarni. Kuma dole ta bi idan dai ita matar kwarai ce. Ka
daina tsoron sababinta, kai ma ka bude mata murya. Ita ma ta iya ta bude maka makogwaro balle kai?”
Ya yi murmushi ya ce “To yanzu me za a yi?”
Ya ce, “Ni zan je na samu hukumar makarantar in musu bayani har halayenta duka zan fada musu, don su yi
hakuri da ita, su kuma san matakin da za su dauka a kanta idan ta gudo ba tare da sun yi la’akari da fadan
Inna ba. Ga kuma makarantar islamiyya da na ga yara suna zuwa da hijabinsu da uniform, nan ma zan je in ba
da sunanta su sanyata ajin da ya dace da ita.
Kai kuma aikinka shi ne ka tabbatar tana zuwa akan lokacin, da son ranta da na Innar ko babu?”
“Malam Bedi ya ce “Sha Allahu za a yi kokari. Allah dai Ya yi maka albarka Habibu, idan ban da kai dan uwanta
wa ya damu da ita balle har ya ce a sanyata makarantar?”
Habibu ya ce “Sai abin da ya kawo ni, amma ina ganin mu samu gindin bishiyar can mu zauna, maganar ta
zaune ce”.
Malam Bedi ya ce “Inji dai ALHERI ne?”
Ya ce “Alheri ne, idan Allah Ya so Ya yarda, kai ma ka yarda”.
Suka samu kututturen bishiyar wata goriba mai duhu da inuwa mai sanyi suka zauna. Malam Bedi ya tattara
dukkan hankalinsa akan Habibu, yana zake da son jin mai zai fito daga bakinsa. Shi kuwa Habibun in banda
addu’ar neman rinjaye babu abin da yake dannawa Malam din daga zuciyarsa.
Malam Bedi ya ce
“Kai na ke saurare, kuma ka yi shiru”.
Habibu ya ce “Eh to, dama Alhaji ne ya ce in zo in shawarce ka, ko kuwa in nemi izninka, idan ka yarda shi ke
nan. Idan ma ba ka yarda ba babu damuwa sai na hakura”.
Ya ce (a dan kufule) “Wai mene ne ka ke ta kwana-kwana? Daga ji ba abin arziki ba ne, don abu idan na arziki
ne ba a kumbiya-kumbiyar fadarsa”.
Ya yi murmushi ya ce “Yi hakuri Baba. Wani abu ne na zamani ya shigo mana cikin na’ura mai kwakwalwa wai
shi yanar-gizo (internet). Ta cikinshi babu inda ba zaka sadu da shi ba a duniya. To rannan ina lalube na, sai na
ci karo da tallan wata makaranta a Malaysia suna neman dalibai. Kamar da wasa na cike form dinsu na tura
musu.
To kwatsam har na manta, shekaran jiya sai ga sako sun turo cewar sun dauke ni, na zo na biya kudin
makaranta na fara karatu. Na samu Alhaji na fada masa, ya tayani murna kwarai, to amma shi kansa ba ya da
kudin da zai iya daukar nauyin karatun, amma yace zai yi min hanyar da zan mika neman taimako daga
gwamnati ta hanyar wani abokinshi mai baiwa gwamna shawara akan harkokin matasa wai shi ALHAJI
GAMBO ADO, kuma ya tabbatar min za a samu insha Allahu, ragowar shi Alhajin ya yi alkawarin cikasawa
daga aljihunshi.
Shi ne ya ce na zo na fada maka tun kamin komi ya yi nisa, kada sai an gama wahala ka zo ka ce ba ka yarda
ba. Yanzu kuwa ba abin da aka yi, sai da amincewarka”.
Shiru Malam Bedi ya yi kamar ruwa ya cinye shi, yayinda Habibu ya ci gaba da jifansa da, “Innahu ala raja’ihi
la-kadir”. Bai gushe ba yana maimaita addu’arsa sai jin muryar malam Bedi ya yi tana tambayarsa har tsayin
shekaru ko watanni nawa za a yi ana karatun?
Ya yi godiya ga Allah a zuciyarsa, domin da alama akwai nasara, ya ce “Abin ya fi karfin watanni. Shekaru
shidda ne zan yi ina karatu akan na’ura mai kwakwalwa”.
Malam bedi ya ce “To daga nan kuma fa?”
Habibu ya murmusa ya ce “Sai na dawo gida na nemi aiki”.
Malam Bedi ya ce “A’ah, ba haka nake son ji ba, sai ka dawo ka yi aure ka tara min ‘ya’yan da ni Allah bai bani
da yawa ba”.
Habibu ya sunkuyar da kai yana murmushi, ya ce “Insha Allahu Baba”.
Malam Bedi ya ce “To ka je, Allah Ya tabbatar da ALHERI………..”
Dai-dai nan Habibu ya ji “tim!” A tsakiyar kansa an nannako masa katuwar goriba a tsakar ka. Kwakwalwarsa
ta daure, kansa ya yi dumm!! Kamar an kwala masa dutse. Wata azaba ta ziyarce shi tun daga tsakiyar kansa
har yatsar kafarsa. Kamin ya gama farfadowa daga takaitaccen suman da ya yi, sai jiyo zazzakar muryarta yayi
kamar zata tsige masa dodon kunnuwa tana fadin “Yaya Habibu sanya min a aljihunka, nawa aljihun bujen ya
cika……..”.
Suka daga kai su duka biyun suna kallonta, Mairo ce kwance abinta akan reshen bishiya, a kalla ta fi karfin
awanni biyu akan bishiyar. Tunda liman ya tada kabbarar sallah ta yi raka’a daya ta dago, ta hango goshin
kowa a kasa, babu mai kallonta, ta yayibo tabarmarta da zummar tahowa gida. Sai kuma ta hango nunannun
goriba ai kuwa ta daka tsalle ta dare.
Duk abin da suke cewa akan kunnenta, sai dai ba wani fahimta ta ke yi ba sabida hankalinta ba ya jikinta. Ita
dai tana tsinkar goribar ta gutsira ta ji idan da zaki ta sa a buje, idan ba zaki ta cillar. Sai da bujen ya cika ne ga
shi kuma ba ta iya barin wannan zazzakar, ta cillowa Habibu ajiya.
Ya bude baki da kyar ya ce “To sauko mu tafi”.
Ta ce “Bari na tsinkowa Baba”.
Ya ce “A’ah, shi baya da karkon hakori”.
Ta kamo reshe bayan reshe tana bin jikin bishiyar cikin kwarewa har ta sauko suka taho gida.
A ranar da ciwon kai ya kwana, amma bai daina yi wa malam Bedi magiya da naci akan makarantar Mairo ba,
ko baya nan. Malam din ya yi masa alkawarin kada ya damu, da yardar Allah kamin ya dawo Mairo ta kimtsu.
Washegari ya je ya ba da sunanta a makaranta aka sata aji uku. Ya yi musu bayaninta dalla-dalla wani malami
da yake makocinsu ne ya ce ya san Mairo farin sani, ko shi yana takaicin rashin sa ta makaranta, to amma
kowa ya san sababin Inna Hure, idan dai akan Mairo ne, shi yasa kowa ya sa mata ido. Amma insha Allah zai
tsaya a kanta kamar yadda zai tsayawa ‘yar cikinsa.
Habibu ya yi godiya mai tarin yawa, ya nemi taimakonshi a kan ya taimaka ya bayar a dinka mata uniform, ya
kirgo kudi ya ba shi har na littattafai da jakar makaranta. Sannan ya nufi islamiyyar yaran Gurin-Gawa, nan ma
ya ba da sunanta. Sun tabbatar mishi ba komai ai irin su Mairon ake son a gyara.
Hankalinsa bai kwanta ba, sai da ya ga Mairo ranar litinin cikin kayan makaranta da jakarta a rataye ta tafi
makaranta. Duk da Inna Hure na kumbure da shi, bai damu ba, tunda ya cika kudurin da ya dade yana damun
zuciyarsa. Don haka koda ya je yi mata sallama zai komo Kano ta yi masa kunnen uwar shegu.
Hure ta ga tijarar Malam Bedi irin wadda ba ta taba gani ba, ba ta kuma taba tsammanin ya iya ba, domin
cewa ya yi idan Mairo ba zata je makaranta safe da yamma ba, to dukkaninsu su zo su fice masa a gida, su tafi
duk duniyar da za su.
Ba ta yi magana ba, amma a cikin ranta tasan wannan aikin Habibu ne, don yadda Malam din ke jin maganar
Habibu ko ubansa sai haka. Abin da ta ce da shi kawai shi ne, “Saboda ka tabbata tsohon bakauye ka zauna
dan ka ya fi karfin ka”.
Ya ce “Eh, koma mai zaki ce ki ce, amma Mairo da uwarta ba su zama min cikin gida muddin Mairo ba zata
nemo ilimi ba. Me ye marabarta da dabba? Babu! Dabba ce aka sani da hawa bishiya da cin abincinta daga
‘ya’yan itace, amma ba dan mutum ba”.
Habibu ya karkace kai ya yi ta ba Innarshi hakuri, ya ce “Inna ku yarda da ni, ba ni da nufin cutarku, sai dai ma
na yi kokarin ganin duk abin da zai zamto cuta a gare ku na yake shi iya karfina. Ina nufin Maironki da alheri
ne, bayan wannan ba wani abu. Ke da kanki wata rana za ki gane gata na yiwa rayuwar Maryam. Don Allah
Inna ki sauko ki yafe min, kisa min albarka!”.
Zuciyarta ta yi sanyi lakwas, ta ce “Ai shi ke nan, nasan iyakar gaskiyar ke nan, laifina shi ne, ina son Mairo da
yawa”.
Ya yi murmushi ya ce “Hakan ma ba laifi ba ne. Sai dai ki yi kokari kada son da kike mata ya sa ki kasa
lankwasata. Ni ma ina son Mairon ki, son da bana yi wa kowa a duniya, amma idan har da gaske ina sonta,
dole in inganta mata rayuwa da gishirin zamani, wanda idan babu shi miya duk dadinta lami ce. Wannan
gishirin kuwa ba komi ba ne, face wannan ilimin dana ke so Mairo tayi. Shi ne zai haskaka mata ragowar
bangarorin rayuwarta, tasan kanta, tasan inda ta sa gaba.
Amma a yanzu wallahi Mairo ba ta da maraba da ‘ya’yan birrai”.Dariya Inna ta yi, ta ce “To Allah Ya taimake
mu ta kimtsu”.
Ya ce, “Amin–amin, ko ke fa Innata? Ni ma karatun zan tafi…” Ya warware mata zare da abawa.
Ga mamakinsa sai ya ga damuwa karara ta bayyana a kyakkyawar fuskarta, ita da a kullum, ta ke nuna ba ta
damu da shi ba. Ya shiga kwantar mata da hankali cikin tausasan kalami, yana nuna mata shekaru shida
kamar yau ne, idan da rai da lafiya. Da kyar ya samu ta sa ma abin albarka.
Da wannan Habibu ya koma Kano ya ci gaba da shirye-shiryensa, da taimakon Baffansa. Cikin watanni uku
kacal komi ya kammala, ya zo wa iyayenshi sallama.
Ya ji dadin yadda ya ga Mairo cikin wankanta fes! Ba ta kuma yi masa wannan damuken oyoyon ba, an fara
nutsuwa ke nan.
Ya yi murmushi, ya ce, “Mairon Inna ‘yan makaranta, ya ya dai?”
Ta yi murmushi ta kawar da kai ba ta ce komi ba. Ya kamo hannayenta ya ce “Ba ki ga yadda kika soma
sauyawa ba? Ina fatan duk runtsi za ki dage da zuwa makaranta? Zan tafi karatu Mairo, sai Allah Ya dawo da
ni kimanin shekaru shidda a nan gaba. Ki kula da Innarki, ki dinga tayata aiki, ba wasan ‘yar bebi ba kin ji
Mairo nah?”
Ta shiga damuwa sosai, nan da nan sai ga hawaye rau-rau a idanunta. Ta ce “Yanzu Yaya Habibu shekaru
shidda zan yi ban ganka ba? Ina zaka je? Mai yasa ba zaka ci gaba da zama gidan Baba Abbas ba kana zuwa
makarantar a can?”
Ya ce “Kamar yau ne Mairo za ki ga na je na dawo, idan dai da rai da lafiya. Ki kula da kanki, ki dinga wanka
kullum, ki dinga yanke akaifarki ta kafa da hannu duk sati. Ki kuma dinga wanke gashin kanki shi ma duk sati,
kin ji?”
Ta ce, “Na ji Yaya Habibu, Allah Ya dawo da kai lafiya”.
Ya ji dadi sosai, bai zaci Mairo tana da dan hankali ba ko yaya ne, har ta yi wa mutum addu’a. Ya sa hannu a
aljihunsa ya ciro naira ashirin ya bata, ta yi ta murna ta je tana nunawa Innarta.
Haka Habibu ya tafi cike da tunanin Mairo. Yana addu’a, Allah Ya sa ta dore da hakan. Watau turbar da ya
sanyata.
Washegari ya tashi zuwa Malaysia, inda ya samu gurbi a Unibersity of Malaya.
Ya sha wuya matuka kamin ya samu ya mance da tunanin gida. Da taimakon abokinshi Amiru wanda shi ma
dan Kano ne ya samu ya soma fuskantar karatun, amma babu ranar Allah da zata fito ta fadi bai tuna Mairo
ba.
***
BAYAN TAFIYAR HABIBU
M
alam Bedi tsaye yake akan kafafunshi kan karatun Mairo don cika alkawarin da ya daukarwa Habibu. Da
taimakon Allah Mairo ta saba da zuwa makaranta, kuma lokuttan makarantar sai ya shafe lokacin da ta ke
samu ta hau bishiya ko ta yi wasan ‘yar tsana.
Idan ta dawo makaranta karfe daya na rana wanka zata yi ta ci abinci, ta yi sallah. Karfe biyu cikin ajinsu na
islamiyya ya ke mata. Ba kuma za su taso ba sai goshin magriba, don haka ranakun alhamis da juma’a da
yamma kadai ta ke samun hutu. A cikinsu kuma tana tare da Innarta suna ayyukan gida wadanda ta alkawarta
wa Yaya Habibu taimakawa Innar.
Rannan Mairo na surfen masara Inna Hure tana bakacewa, Mairo ta aje tabaryar ta ce “Oh Inna, Yaya Habibu
yau watanninsa bakwai ke nan, yana can a cikin Turawa”.
Inna ta ce “Wa ya ce miki a Turai yake? Kasar Larabawa ne”.
Mairo ta yi murmushi, ta ce “A’ah Inna, rannan na tambayi malaminmu na makarantar book, a ina Malaysia ta
ke? Ya ce min Asia ne, can wajejen India da Pakistan”.
Inna ta kama baki ta ce “Ke Mairo, yaushe kika iya Turanci haka?”
Mairo ta ce “Ba Turanci na yi miki ba Inna, sunan kasashe na fada miki”.
Wani dadi ya kama Inna Hure, ba tasan sanda ta ce “Kai Allah Ka sakawa Habibu da alheri”
MARYAM BEDI, ta ci gaba da karatunta cike da himma da kwazo. Takan sanya wa ranta cewa, kawai Habibu
na kallonta, yana jin dadin kwazonta. Yana kara mata karfin gwiwa. Ba ta yarda wai shekaru shidda zai yi bai
dawo ba. A ganinta shi ne Habibu na iya dawowa yau, ko gobe, don kawai ya rutsa ta, ya ga irin kwazonta.
Saboda haka cikin shekara guda kacal, Maryam Bedi, ta zama zarrah a ajinsu na boko, kan gaba a ajin
islamiyyah, wadda ke da haddar izfi ashirin na Alkur’ani a cikin kanta.
Sauran littattafan addini kuwa idan ta bude su tana karantawa tana fassarawa Inna tsarki da alwala, da irin
sallar khashi’ai da sallar da ake dunkulewa a jefowa bawa kayarsa, tun kamin ya tashi akan dardumarsa. Sai
Inna ta sa habar zaninta tana share hawaye, ta ce “Ba karamar cuta na so na yi miki ba Mairo”.
Shekaru uku ke nan cif da tafiyar Habibu, kuma a yau ne ranar saukar su Mairo. Ta sha wanka da sabon dinki
na atamfa (hitarget) da suka yi anko gaba dayansu. Ta dora wani sabon farin hijabi akai, wanda ya tabo har
gwiwarta. Ta azalzali Innarta ta yi sauri ta gama shiryawa su tafi kada wajen zama ya cika ta rasa inda za ta
zaunar da ita. Innar kuwa sai sake murza kwalli ta ke a idanunta yadda zata fito radau!
Ta kuwa fito din, sai kyallin wanka da basilin ta ke. Suka jera abinsu Mairo na ta addu’ar samun nutsuwa cikin
zuciyarta sakamakon ganin cincirodon al’ummar kauyensu wadanda ake nufin ta yi karatu a gabansu.
Tuni Malam Bedi ya isa wajen tun kamin su zo, yana cikin rumfar iyaye maza, a sahun gaba, yana ta ware ido
don ganin ta inda Mairo zata bullo.
Can ya hangota rike da hannun Innarta, ta samu wajen zaman da ya dace da Innar ta zaunar da ita, sannan ta
karasa cikin ‘yan group dinsu suka yi sansani.
Taro ya yi taro, mai gabatarwa ya fara gabatarwa bayan bude taron da addu’a, daga limamin garin GurinGawa. Maryam Bedi, ita ce wadda aka fara kira ta bude taron da karatun Alkur’ani cikin daddadar kira’arta kai
ka ce diya ce ga Khusairi, inda ta karanto karshen suratul Fathi, wato ayar nan ta
“Muhammadurrasulullah…….”
Gaba dayan jama’ar dake wajen jikinsu ya yi sanyi, sai ga Malam Bedi yana kuka. Da ta dasa aya aka dauki
kabbara kowa na cewa “Ai Mairon Hure ce, diyar Malam Bedi”.
Innar kuwa sai washe baki ta ke, bakinta ya ki rufuwa don kuwa duk matan da suka san ita ce babar Mairo, sai
gaisawa suke da ita. Yayin da ‘yan bakin-ciki, wato wadanda ke da ‘ya’ya a makarantar ba a kuma kirawo
‘ya’yansu ba sai zumbure-zumbure suke yi mata, ko a jikinta wai an tsikari kakkausa.
Haka nan Mairo ce dalibar da aka fara kira ta amshi allonta daga hannun Mai girma shugaban karamar
hukumar Kumbotso. Malaminsu ya karanto mata farkon suratul Bakara tana bi tiryan-tiryan cikin kira’ar da ta
fi ta malamin.
Bayan nan Mairo ta karbi kyautar dalibar da ta fi kowa iya Tajwidi, sannan daliba mafi da’a a gaba dayan
daliban shekararsu. A sa’ilin da maigirma Chairman ya amshi lasifika domin gabatar da jawabinsa na babban
bako mai jawabi. Budar bakinsa sai cewa ya yi
“Na dauki nauyin karatun wannan yarinya MARYAM BEDI a makarantar sakandiren ‘yammata ta gwamnatin
tarayyah da ke Minjibir”.
Gabadaya aka sa kabbara. Abokan Malam Bedi suka shiga taya shi murna, ya rasa inda zai sa kansa don farin
ciki. Mairo ta riga su komawa gida domin an ce su tsaya za su gana da Chairman.
Inna Hure na shigowa ta suri Mairo ta goya a baya, ta sa zane ta daure ta, ta sa majanyi ta kara daurewa. Ta
shiga zagaye dakin da ita, ita kuwa sai dariya ta ke. Kamin su zauna gabadayansu. Malam Bedi ya gabatar
musu da bayanin da maigirma chairman ya yi masa na cewa, zai tallafawa karatun Mairo a babbar makaranta
ta gwamnatin tarayya. Zai mika komai ta hannun shugaban makarantarsu ta boko tunda dama gab ta ke da
zana jarrabawar fita firamare. Ya kare da cewa.
“Amma fa makarantar ta kwana ce”.
Nan da nan farin cikin da ke makale a fuskar Inna Hure ya yaye, Mairo ta lura da hakan, ta ce “Haba Inna,
wannan ba wani abu ba ne. Zan dinga zuwa hutu kuma ana zuwa ziyara. Kin san Lanto ma ta gidan Kado tana
makarantar kwana a Kwa. Duk bayan watanni uku dawowa ta ke. Sannan bayan kowanne wata ana zuwa
ziyara”.
Inna ta ce “To ni wa zai kai ni birni? Har in gano ki a kowanne wata?”
Ta ce “Allah Shi zai kai ki, ga iyalin Baba Abbas za su iya raka ki”.
Nan da nan Hure ta yi kicin-kicin da fuska ta ce “Ke, raba ni da wadannan mutanen. Ni dai na yi hakuri har ki
zo hutun”.
Mairo ta yi murmushi ta ce “Shi ke nan Inna”.
Malam dai jinsu yake a zuciyarshi yana mamakin dalilin Hure na kin son yin zumunci da iyalin dan uwansa. Bai
sani ba ita a ra’ayinta shi ne, idan har zata ke shiga shirginsu wata rana za su sake yin yunkurin rabata da
Maironta don taje tayi masu bauta amma ba don Allah ba.
Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah, su Mairo aka kammala zana common entrace, aka zauna gida zaman jiran
sakamako. Ba jimawa ya fito, shugaban makarantarsu ya mikawa Chairman. Cikin sati uku sai ga takardar
daukar Maryam Bedi, cikin sabbin daliban FGGC Minjibir na shekarar.
A na so kuma ta isa makaranta cikin sati biyu, hedimasta ya kira Malam Bedi ya damka masa ya kuma gaya
masa ya hadawa Mairo kayan abinci da ake hadawa dan makarantar kwana, ya kuma ba shi katifar Mairo da
filo, domin makarantar ba sa bukatar akwatun karfe.
Malam Bedi ya dawo gida shi da Hure aka hau shawarar abin da za a hadawa Mairo, Hure ta daka mata kulikuli ta kuma shanya mata Rama mai yawan gaske, da zata dinga jikawa idan ta yi sha’awa ta kwada ta ci,
kwaki kwano biyar, kanzo kwano uku, yaji rabin kwano, omon wanki da sabulun wanka. Man shafawa da man
kitso, man kuli da manja. Mairo ta ce, su sayo mata brush da maclean, aka siyo a Fanshekara. Shi ke nan kaya
sun hadu sai tafiya.
A daren Inna Hure ta kwaba lalle ta yaba mata a kafafunta aka daure aka kuma zura hannun dama cikin
dumar lalle, shi ma kan safe ya yi jawur kamar jini, duk adon tafiya makaranta ne.
Aka tsefe kai aka yi mata kitson doka guda takwas. Babanta da Hedimasta su za su kai ta Minjibir, don haka
tun karfe bakwai hedimasta ya ke buga musu zaure da yake shi ma Chairman ya cika shi da abin arziki duk
don ya kula da karatun Mairo.
Mairo na kuka Innarta na yi, a haka suka rabu. Hedimasta dauke da katifar kwanan Mairo, malam Bedi rike da
dindimemiyar (Ghana Must Go), a haka suka doshi tasha. Hedimasta na ce da Bedi daga wannan zuwan da
zamu yi da kai, duk hutu kai kadai zaka dinga kawota, don haka ka dinga kula da duk abin da na yi”.
Malam Bedi ya ce “To, angode dai”.
Suka samu bayan motar rake suka dane, ta fito da su Fanshekara, daga nan suka hawo motar Bata/Kuroda. A
nan suka hau motar Minjibir, Mairo a maleji su kuma a kujerun gaban motar. Tafiyar awanni biyu ta kawo su
Minjibir, aka sauke su a tasha. Daga nan suka hau tasi aka kai su har kofar FGGC. Suka gaisa da maigadi, suka
ba shi ajiyar kayan su suka karasa cikin makarantar. Jikin Mairo ya yi sanyi matuka ganin irin tsaleliyar
makarantar da aka kawo ta.
Ta daga ido tana hangen dalibai cikin kayan makaranta iri daya, cikin tsari da nutsuwa. Kowacce a nutsenta ta
ke tsaf, tana tafe cikin kamala. Ba ka jin hayaniyar komi sai sautin malamai suna koyarwa cikin azuzuwa, shi
ma din a tausashe.
Mairo ta kalli kanta sama zuwa kasa, ta hango bambanci a farrake tsakaninta da irin jefi-jefin daliban da ta ke
ganin suna wulgawa.
Gabadaya sai ta ga kanta kamar wata almajira, duk da kuwa ta kure adaka, ta sha lalle. Ga jambaki jawur ta
rambada ta yi kuma jagira da digo a tsakiyar goshinta. Duk da hakan ba ta ji ko dar na zama a wannan
makarantar ta yi karatu ba. Ta yi tunanin cewa, ba wannan ne abinda ya kawota ba, darasin da za a koya mata
ne, Yaya Habibu ya dawo ya yi alfahari da ita.
Suka tambayi ofishin shugaba aka nuna musu. Kai tsaye can suka dosa, Mairo na kallon yadda daliban wani aji
da babu malami a ciki suka yi cincirodo a taga suna kallonta. Sai hankalinta ya tashi matuka, don haka har ta
riga Hedimasta tura kai ofishin shugaba, don dai ta tsira daga kallon wadannan yara.
Shugaban makarantar Halima Dukku, ta yi tsai da ranta ta cikin gilashinta tana kallon harbatsatstsiyar dalibar
da aka kawo mata. Ta jinjina kai ba tare da ta tofa ba, ta karbi takardun hannun Hedimasta ta sa hannu bayan
ta duba ta kuma shigar da sunan Maryam Bedi cikin jerin daliban da makarantar ta karba a wannan shekarar.
Ta sa aka ba ta uniform, house-wear da sauransu. Ta kalli takalmin da ke kafar Mairo ta ga silifa ne, wani
bakikkirin da shi, ya kuma hadu da wata kafa jawur kamar gauta. Ta ce ba sa ba da takalmi don haka aje a
sayo mata sandal ko cambus.
Hedimasta ya ce su yi masa alfarma ya bada kudin a siya mata, su baki ne a garin ba su san ko ina ba. Ta kira
leburanta, ta hadasu dashi, ya gaya masa sandal dari takwas ne, kambas dubu daya da dari biyar mai saukin
kudin kenan. Gabadayan su shi da Malam Bedi suka hada baki suka ce, “Mai ka ce?”
Ya sake maimaitawa. Malam Bedi ya hau salati amma shi Hedimasta da yake da dan karatunsa na yaki da
jahilci sai ya ce”Au to, ba mu sani ba ne, domin yanzu a aljihuna kwata-kwata naira dari hudu ne, ga shi a ciki
zamu hau mota. Amma ga wannan”. Ya mika masa dari biyu, ya ce, “Ko irin na dankon nan ne mai igiya a saya
mata idan zata dawo sai a nemo”.
Haushi ya ishi leburan ya juya zai fita abinsa, shugaba ta yi gyaran murya ta dauko gudar naira dari biyar guda
hudu ta mika masa, ba tare da ta ce komi ba.
Malam Bedi ya dinga zuba mata godiya, ta ce, “Babu komi, ai da na kowa ne”. Ta sa aka kira mata wata
prefect ta hadata da Mairo da kayanta gami da littattafai wadanda suke cikin kudin makarantarta, amma
babu jaka, ta ce su sayo mata daga baya, ta ce ta kai ta hostel.
Sai a lokacin ne kuka ya zo wa Mairo, shi ma Malam Bedi duk da dauriyarsa sai da ya sa habar babbar rigarsa
yana share hawaye. Suna dagawa juna hannu har su Mairo suka kule cikin hostel.
Bayan prefect din nan ta damka Mairo a hannun house-captain dinsu sai ta koma aji. House-captain ta
nunawa Mairo dakinsu ta ba ta gado ta shimfida katifarta ta ce, to ta sanya uniform ta tafi aji don kowa yana
aji. Sai dai fa a ranta tana mamakin yadda aka yi wannan bakauya ta zo makarantarsu.
Mairo ta tube kayanta ta sanya na makaranta ta bi bayan captain har ajin da aka ba ta, wato JSS 1A. Ta je staff
room ta nemo class master dinsu ta hada shi da Mairo, ta koma nasu ajin.
Mairo ta yi tsuru a gaban allo, a lokacin da Uncle ke gabatar da ita a matsayin sabuwar daliba a ajin. Abin da
Mairo ta lura da shi shine, gabadaya ‘yan ajin wani irin kallo suke mata na raini da kyama, suna kyabe baki
duk sai ta ji ta muzanta.
Uncle ya nuna mata kujerar zama gefen wasu fararen yara ‘yan gayu guda biyu, da ba su fice tsaranta ba. Ai
kuwa suka soma matsawa jikin junansu suka takure suka ba ta katon fili.
Malamin ya lura da irin karbar da Mairo ta samu a ajinsa, duk sai ya ji tausayinta ya kama shi. Ya dube ta ya
ce, “Sake gaya min sunanki, ban gane abin da principal ta rubuta sosai ba”.
A hankali ta bude dan kankanin bakinta ta ce
“Maryam Bedi”.
Ya ce “What a nice name, maryama, saki jikinki ki zauna a inda na umarce ki. Ba ruwanki da kowa sai abin da
ya kawo ki, kina ji na?”
Ta gyada kai, amma ba ta amsa ba.
Ta karasa inda ya nuna mata ta zauna a darare. Yarinyar kusa da ita ta ja tsaki, tsuuu! Ta murguda baki ta juya
mata keya. Ta dauki tulin littattafanta ta zura su cikin lokar kujerarta tunda ba ta da jaka.
Uncle ya fita cike da tunanin wannan yarinya. Yana daga cikin malaman da ba sa son ganin rashin walwala ko
yaya daga dalibansu. Abin da ya lura shi ne, Maryama ta shigo makarantar da ta fi karfinta. Ya fi kowa sanin
girman kai da ji da kai na daliban FGGC don haka ya samu kansa da tausayin ‘yar yarinya, Maryama.
Ya alkawarta wa ransa taimaka mata iyakar iyawarsa, har sai ya ga ta saki jikinta tamkar sauran dalibai ‘yan
uwanta.
Da aka tashi daga aji Mairo ba ta san dawar garin ba. Ta dai ga kowa na fita da littattafansa babu wanda ya
kulata, kai ba ta ma ishi kowa a ajin kallo ba. Sai ta kwaikwayi yadda suka yi, wato ta kwaso littattafanta masu
yawa da matukar nauyi ta nufi hostel kamar yadda ta ga sun yi.
Tana shiga dakin sai ta ga wadannan fararen yaran sun rigata isa har sun tube uniform sun sa na hostel, ashe
su ma a dakin suke. Suna ganinta ta shigo suka kara yin kicin-kicin da fuska kamar an aiko musu da sakon
mutuwa, musamman da suka fahimci a kusa da gadonsu ta ke.
Dayar ta yi tsaki ta canza harshe tana cewa da kawarta, “See this girl, i donno what she is looking for
here…”(kalli wannan yarinyar bansan me take nema a nan ba).
Kawar ta ce, “Kaddararmu ke nan, daki daya, aji daya, mts!”
Jikin Mairo ya kara yin la’asar, amma sai ta dasa wa ranta ta rabu da wadannan yaran ta yi abin da ya kawo ta.
Ta ajiye litattafanta ita ma ta tube uniform tasa na hostel irin wanda taga sun sanya, ta nufi famfunan da ta
ga ana alwala, ita ma ta yi ta nufi masallacin da ta ga ana shiga da sauri ta samu jam’in sallar azahar.
Da aka fito yunwa ta addabe ta, ta soma tunanin ta je ta kwada kwadon kwaki sai ta ji wata senior na fadin a
fita ‘dining’ za’a rufe hostel. Ta dinga maimaita kalmar ‘dining’ a ranta, ko mene ne? Ta ga dai kowa fita yake
yi sai ta bi bayan wasu yara ba tare da sun san binsu ta ke ba, har zuwa wani katon dakin cin abinci inda ta ga
dalibai a zazzaune kowa da filet dinshi ana ta cin abinci.
Yawun bakinta ya tsinke, ta bi layin da ake bi a karba ita ma ta karba, jallof din shinkafa ce da yankan nama
biyu da soyayyar ayaba (plaintain) sala uku. Ta zauna ta ci ta koshi, ta sha ruwa ta yi hamdala ta mike ita ma
ta nufi hostel ta kwanta a gadonta don ta huta zuwa la’asar.
Da aka yi sallar la’asar kuma suka koma aji zuwa karfe shida. Haka dai ta yi ta bin abin da ta ga ana yi, har
lokacin barci.
A sannan ne ta samu damar kwashe kayanta da ke cikin (Ghana Must Go) ta jera a loka, kamar yadda ta ga
kowa ya yi. Yaran nan makotanta suka fito da wani irin abu cikin kwali da ba ta taba gani ba suna ci, suna
korawa da lemon gwangwani suna hira da Turanci, suna kallonta, ita da kullin kayan kuli-kulinta suna ta
dariya. Duk ta bi ta sha jinin jikinta, amma ba ta daga kai ta kalle su ba, ta jika ramarta cikin ‘yar robarta ta
ajiye akan lokarta tana jira ta jiku ta kwada da kuli.
Tana ganinsu har lekowa suke da kai suna leka robar ta, amma ragowar jama’ar da ke dakin ba ruwansu da
ita, kowa gararin gabansa yake yi. Ta rasa dalilin wadannan yara na sa mata ido da wulakanci a gare ta, daga
baya ta fuskanci daya sunanta Nabilah, daya kuma Kausar.
Ta kwada ramarta ta ci ta koshi, ta sha ruwa ta kwanta a katifarta da ko zanin gado babu. Ta rufa da zanin
atamfar Innarta, wadancan yaran kuwa irin bargonta da hedimasta ya cinye suka rufa da shi. Hatta filon ya
dauke ya cinye saboda rashin tsoron Allah irin nasa. Aka yi (light-off) na gabadayan hostel din, ta shafe jikinta
da addu’o’i ta kwanta.
Washegari da aka yi sallar asubah ta ga kowa yana bin layin wanka, don haka ita ma ta bi ta yi wankanta ta yi
sallah a masallaci tare da Imam. Daga nan aka tafi aji.
Suna shiga aji ta ga mutanenta sun dauke bencin gabadaya sun maida shi wurin da ba kowa sun zauna, sun
kuma kira wata yarinya sun zaunar da ita a wajenta. Ta rasa inda za ta zauna, ta koma karshen ajin ta sanya
littafinta daya a kasa ta zauna akai. Zamanta da kamar minti biyar Uncle din ajin ya shigo. Yana ta jefa ido ya
hango Mariaman da ya kwana ya tashi da tunaninta jiya, amma bai ganta ba.
Gabadaya ajin aka mike, ita ma sai ta mike kamar yadda suka yi, suka hada baki gabadaya suka ce “Good
morning Uncle”.
Ya ce, “Morning class, how are you all?”
Suka sake hada baki gaba daya suka ce “We are fine Uncle”. Sannan ya yi umarni da a zauna.
A sannan ne ya hangota makure a can layin karshe kamar mujiya, kuma a dandaryar kasa. Bai ce komi ba ya
bude rajista ya yi kiran lambar kowa, ya amsa, sai a karshe ya ce “No. 40”. Shiru ba a amsa ba, a lokacin ya
gane lambar Mairo ce, sai ya ce, “Mariama daga yau ke ce no.40”.
Ta ce “To”.
Ya rufe rajistar ya dinke fuska sosai, ya ce
“Kausar!”
Ta amsa, “Yes Uncle”.
Ya ce “mene ne dalilinki na janye benci ki hana Mariama zama?”
Ta yi shiru ba ta amsa ba.
Ya dubi dalibar da suka zaunar a wajen, “Ke Laila ina wajen zamanki? Me ya kawo ki nan?”
Ta yi saurin mikewa ta koma wajenta.
Ya ce “Kausar fito nan”.
Ta fito tana gatsina ita a dole ga ‘yar masu kudi. Saura kadan ya zabga mata mari, sai dai ya yaki zuciyarshi ga
yin hakan, ya ce ta fita waje ta yi kneel down, har zuwa lokacin break.
Ta cika ta yi fam, kamar balam-balam, dama ga ta buleliya. Ta zobara baki, ta ce “Ai ba ni kadai na janye
bencin ba, har da Nabilah”.
Nabilah ta ce “Wallahi Uncle babu ruwana, ita ce ta ce wai ba zata zauna da billager ba”.
Bai yi mamaki ba, sai ya bude murya yana tambayar ‘yan ajin “Shin dama akwai banbanci tsakanin musulmin
kauye da musulmin birni?”
Suka ce “A’ah Uncle”.
Ya ce “To me ye laifin wannan yarinya da kuke kyamarta?”
Wasu daga ciki suka hau matsawa suna cewa “Ta zo ta zauna a kusa da mu”.
Amma Uncle sai cewa ya yi, babu inda zata zauna sai bencin su Nabilah, don haka idan Nabilah da Kausar
baza su zauna tare da Maryama ba, sai dai su koma gidan ubansu.
Mairo dai na sauraron ikon Allah. Tana tunanin yadda ta ke abar so a wurin Innarta da Babanta, amma wai
yau ake takaddama akan inda za ta zauna sabida ita an ga alamar ba ta da arziki.
A lokacin ta ji wata zuciya na shigarta (determination) akan rayuwa. Ta alkawarta wa ranta idan ilimi na kawo
arziki, to zata neme shi ko don ‘ya’yanta. Za ta nemi ilimi har sai ta ga karshensa, idan har ana gani. Ba zata so
a yi wa danta irin wannan wulakancin ba. Uncle ya lura Mairo kuka ta ke yi, sai zuciyarsa ta karye. Don haka
tunda ya gama kiran lambar sai ya fita, bayan ya tabbatarwa Kausar kada ta sake ta bar kneel down din da
yasa ta har sai ya dwo.
Malamin maths ya shigo ya fara ba su darasi, Mairo ta tattara hankalinta akan malamin gabadaya, ba ta damu
da hararar da Nabilah ke mata ba. Ya gama ya fita, sai ga Uncle ya dawo wanda kuma shi ne yake daukarsu
darasin Turanci.
Yana koyarwa, amma rabin hankalin sa na kan Mairo. Ya lura sabanin ragowar ‘yan ajin, Maryama ta ba shi
dukkan ‘attention’ dinta, da wani muradi cikin kwayan idanunta. A zahiri wannan yarinya bakauyiya ce
lakadan, amma ga dukkan alamu, ba haka Allah Ya yi nufin barinta ba.
Ya kammala darasinsa ya ba da aiki ‘Essay Writting’ mai take guda uku, ya ce kowacce ta zabi wanda za ta iya
yin sharhi a kansa. A rubuta a kawo masa washegari. Hankalin Mairo ya tashi, domin dan ilimin nata bai kai
nan ba. Magana ce ake so su rubuto da harshen Turanci akalla shafi daya da rabi na littafi.
Aka kada kararrawar fita break, amma Mairo ba ta yi niyyar fita ba. Ta kurawa aikin ‘assignment’ dinta ido
tana tunanin ta inda za ta bullo. Ba ta ankara ba ta ji wani sassanyan kamshi na dukan hancinta da kuma
alamun zaman mutum a bencin gabanta. Ta dago a hankali tana kallonsa, Uncle ne.
Ya ce “Yaya dai Maryama, kowa ya fita cin abinci, amma ke ban ga alamar kina da niyyar fita ba?”
Ta sadda kai cikin kankanuwar murya ta ce
“Ina tunanin yadda zan yi aikin da ka bayar ne”.
Ya yi murmushi ya ce “Aiki ne kuwa mai sauki, amma ga wanda ya gane tambayar. Wacce tambaya kika dauka
a ciki?”
Ta sunkuya tana kara nazarinsu, ta ce “Ina ganin ta daya za ta fi mun saukin amsawa, tunda daga karkara na
ke, ‘Yadda ake bikin sallah a karkararmu”.
Ya yi murmushi, ya ce
“Ni kuwa sai na ga tambaya ta biyu zata fi dacewa da ke ‘Ranata ta farko a sakandire’, za ki kawo ‘points’ sosai
wanda zai taimaka ki yi ‘scoring’ maki mai yawa. Kinga sauyin abubuwa da dama, a zuwanki babbar
makaranta. Haka ne ko ba haka ne ba?”
Ta yi murmushi, wanda ya lotsa kumatunta hagu da dama. Akwai wani asirtaccen kyau a tare da Mariama,
wanda rashin gyara da rashin gogewa ya boye shi. Yarinya ce kamar diyar Larabawa, sai dai fatarta a dafe ta
ke, kamar an shafa mata shuni, wanda kai tsaye ya banbantata da sauran yaran makarantar.
Ta ce “Haka ne Uncle. Na gane cewa, ashe mu ba mutane ba ne, ababen kyama ne ga wasu jinsin al’ummah.
Abin dariya ga wadanda Allah Ya yiwa falalar rayuwa. Ban san cewa ni ‘yar talaka ba ce sai yanzu, tunda kuwa
ban taba neman abin da zan ci na rasa ba, sai na dauka iyakarta ke nan. Ashe akwai masu shi fiye da ni, amma
idan da ace ni ce a matsayin mai shi din, ba haka zan yi wa mara shi ba!”.
Mamakin kalaman karamar yarinya kamar wannan ya kama shi. Sai dai ya kula magana ta ke tun daga
karkashin zuciyarta, ba wai tunaninta ba ne.
Ya ce “Mariama!”
Ta dago ta dube shi, amma ba ta amsa ba.
Ya ce “Ina son ki sa wa ranki cewa, ba duka mutanen da kika tarar halinsu daya ne ba. Kowa da kika gani a
duniya da irin halayyarsa. Wani yasan darajar kansa, yasan ta mutane, wani bai san darajar kansa ba, bai san
ta mutane ba. Wani yasan darajar kansa bai san ta mutane ba.To wannan ba cikakken mutum ba ne, kuma shi
ne wanda Allah Ubangiji Ya yi alkawarin dankafar da shi a duniya da lahira sabida girman kansa. Da zarar ka yi
tunani ko ya ya cewa, kai wani ne, to kai ba kowa ba ne a wurin Ubangiji.
Sabida haka a yadda kika dau kan naki a ba kowa ba, ci gaba da hakan. Amma kada ki yarda da cewa, sai wun
fi ki ne. Ido biyu gare su, kunne biyu, kafafu biyu, hannaye biyu, ke ma su gare ki. To akan me za ki yi tunanin
sun fi ki? Wanda ya fi ki kawai shi ne wanda ya fi ki tsoron Allah!”.
Jikinta ya yi sanyi, ranta ya yi fari. Tana dubanshi da kyawawan idanunta, ta ce “Uncle kana nufin ni ba abun
kyama ba ce?”
Ya girgiza kai “Ko daya Maryama. Da za ki daure ki fidda su a gabanki ki yi karatu sosai ki dinga gyara kanki, sai
kin fi su kyan gani. Ko a yanzu haka kin fi su, gyara suka fi ki. Ba kawa kika zo nema ba, ilimi kika zo nema, irin
wanda suka zo nema. To akan me za ki damu da su? Ai abu daya za ki damu da shi, shi ne ki dage ki ga cewa
ba su fi ki kokari ba”.
Ta yi murmushi ta ce “Uncle kana da kirki, sai na ke jinka kamar Yaya Habibu. Shi ma haka yake yi min irin
maganganunka. Da zai zo ya ganni a makarantar nan, ban san irin farin cikin da zai yi ba”.
Ya ce “Yaya Habibu yana ina yanzun? Ni kuwa inje in gaya masa, ga ki a babbar makaranta”.
Ta washe baki ta ce “Ayyah, yana da nisa, yana karatu ne a kasar waje, amma komi nake yi sai in yi ta ganin
kamar yana kallona, sabida shi ne ya dage, ya sani a makaranta”.
Ya ce “Ni kuwa gani na dage da yardar Allah sai kin yi karatun da Yaya Habibu zai dawo ya yi alfahari da ke,
amma hakan ba zai yiwu ba sai da goyon bayanki Maryama, wanda ba komi ba ne da ya wuce perserbearance
(jajircewa) da ba da himma”.
Ta sake yin murmushi har kumatunta suka lotsa, ta ce “Na gode Uncle, kuma na yi maka alkawarin I’ll
persebere”.
Ya yi mata tafi guda daya ya ce “Good Maryama, ina neman alfarmar ki rike ni a matsayin Yaya Habibu”,.
Wani farin ciki ya bayyana a fuskarta, ta ce “Kenan ka yarda na rinka kiranka da Uncle Habibu?”
Murmushi ya yi, “A’ah, UNCLE JUNAIDU. Sunana Junaidu Galadanchi”.
Ta ce “Galadanchi?”
Ya ce “Eh, kin santa ne?”
Ta ce “A’a, ban taba ji ba ne. Garinku ne Galadanchi ko sunan Babanka ne?”
Da alama Maryama matambayiya ce, kuma matambayi ba ya bata. Hazakar yaro na da alaka da yawan
tambayarsa (curiosity).
Ya ce “Galadanchi karamar unguwa ce a cikin birnin Kano. Sai dai tarihinta mai girma ne ga Kanawa. Duk wani
Ba-Kano ya san Galadanchi, sannan mu ‘ya’yan cikinta muna alfahari da ita da kasancewarmu ‘ya’yanta.
A Galadanchi ne aka fara samun Dr. a ilimi a jihar Kano. Haka idan kika bi tarihin manyan ‘yan bokon Kano, da
mayan malaman Jami’ar Bayero, wadanda suka fito da jihar Kano a tsakanin jihohi ‘yan uwanta, to duk ‘yan
Galadanchi ne. sannan gasu da kyau, ga Alkur’ani da Tajwidi a cikin kansu”.
Ta ce “Ina fatan wata rana, in ziyarci Galadanchi”.
Murmushi ya yi “Insha Allahu za ki je Galadanci Maryama. Yanzu dai jeki ci abinci kamar sauran dalibai, idan
kun fito ‘pref’ da yamma sai ki rubuta aikin gobe ki kawo mani”.
Ba musu ta mike ta nufi kofar fita. Bai daina kallonta ba har sai da ta kule ya daina ganinta.
Shi kam bai san dalilin da ya sa ya damu da yarinyar ba. Haka dan zaman da suka yi a yanzu ya kara sanya
mishi jin son taimakonta.
Mairo da ta fito ‘pref’ ta yagi takarda kamar da wasa, ta soma rubuta ‘essay’ dinta mai taken ‘My first day in
secondary school’. Da jagwalgwalallen turancinta mara ‘tenses’ har haduwarta da Uncle a aji ta rubuta, inda
ta ce, ba ta taba haduwa da mutum mai kirkinsa ba. A karshe ta ce “shin ko mutum nawa ne masu jin kai irin
UNCLE JUNAIDU? Ta ce, Uncle Junaidu ya sa mata burin son zama malamar makaranta, wanda a da ba
ra’ayinta ke nan ba.
Ta sake bin jagwalgwalonta ta yi dan gyaran da zata iya, ta sanya a tsakiyar littattafanta.
Washegari da karfin gwiwarta ta shiga aji, to amma Uncle bai tambayi ‘assignment’ din shi ba sai da period
dinsa ta shiga. Yana bi daya bayan daya yana marking har ya zo kan na Maryama Bedi. A zahiri duka ‘yan ajin
sun fi ta iya Turanci, da kula da ‘tenses’ sabida su sun sami kyakkyawan tushe daga makarantu masu tsada. To
amma idea da ke cikin rubutun Maryam fasaha ce tsagwaronta.
Ta yi rubutunta kamar da gasket, tana magana kamar akan idonsa abin ya faru. Ya kirata yana nuna mata
kura-kuranta, tare da cewa “Matsalarki daya ce a Ingilishi (tenses), don haka darasinmu na yau tenses ne”.
Nan da nan ya fara darasi inda Mairo ta dauki dukkan hankalinta ta likawa Uncle. A yau da aka fita break ma
ba ta yi saurin fita ba, ta zauna ne tana aikin lissafi (maths). Uncle Junaid ya kwankwasa desk dinta, ta yi
hamzarin dagowa kamin ta yi murmushi ta ce “Uncle dama ba ka fita ba ne?”
Ya ce “A’ah na fita, dawowa na yi. Tun daga staff room na hango ki kina rubutu, zuwa na yi na gaya miki ki
daina zama cikin aji yayin da kowa ya fita. Komi na makarantar nan cikin tsari yake, yanzu lokaci ne na cin
abinci ba na yin aiki ba. Idan wani bai ga abinsa ba yana iya cewa ke ce”.
Ta rufe littafin ta mike ba tare da ta ce dashi komi ba. Ta nufi hanyar fita, har ta kai bakin kofa ya ce,
“Maryama”.
Ta juyo cikin damuwa, ya ce, “Ina fatan ba ranki ne ya baci ba?”
Sai ta koma dariya, ta ce “A’ah Uncle”.
Ya ce “To mai yasa kika yi shiru?”
Ta ce “Ka yi hakuri Uncle Junaidu”.
Ya yi murmushi ya bi hanyar kofa shi ma ya na kissimawa a ranshi Maryam na daga cikin miskilan yara.
Cikin sati biyu kacal Mairo ta fahimci tsarin komi na makarantarsu, sai dai ma ta nuna wa wani. Babu ruwanta
da su Kausar, duk kuwa da basu fasa yi mata izgilanci ba, a daki ne ko a aji. Sai dai su kansu sun san akwai
wani aminci, ko kuwa shakuwa ta musamman tsakanin Maryam da Uncle, don haka basa yi mata a gabansa.
Saboda Maryam Uncle Junaid ya kirkiro tutorial class da yamma da yake yi akan darasinsa English da darasin
Uncle Wahhab (mathematics), wanda ba karamin taimakawa Mairon ya yi ba.
Duk wasu matsalolinta akan karatu Mairo ba ta shayin gayawa Uncle Junaidu shi kuma ya tsaya mata kamar
Yayanta. Shi kansa bai san mai yasa ya tsani Kausar da Nabilah ba, tun daga ranar da ya lura sune kawai
matsalar Maryama cikin makarantar.
Ita kuwa kullum kokarinta shi ne, ta boye abin da suke mata, kada ya gane. Don duk ranar da ya hora su
sabida ita, idan sun koma daki akanta suke hucewa. Rannan da ya sa su noma sabida sun karya bencin ta
karfin gaske, duk don kada ta zauna kusa da su, da suka komo hostel suna ta digar da gumi. Sun yi jawur
sabida wahala, Kausar ta yi kuka ta ce “Wai Nabilah wannan bakauyar kanwar uban Uncle ce ne?”
Nabilah ta ce “A’ah, ina jin tare aka haife su, don shi ma da alama dan talaka ne ya soma daukar albashi ya je
ya sayo gwanjo yana zanzarewa”.
Kausar ta ce “Uban wa ya gaya miki? Abokin Yayana ne tare sukai karatu, dan chief justice Atiku Galadanchi
ne. Har gidansu na sani sanda muka zo Kano daga Jos da Yaya Yusuf bikin wani abokinsu, abin da na kasa
ganewa shi ne, mai wannan billager din ta ke gaya masa yake damuwa da ita? Ni kam da nasan har da irin
wadannan a makarantar nan ai da ban yarda Daddy ya kawo ni ba”.
Nabilah ta ce “Ke kika ga zaki iya, amma ni nan idan an yi hutu bazan dawo ba, Edcel collage zan koma.
Minjibir ta rube, ta zama ta yaku-bayi”.
Suka kwashe da dariya, Mairo dai na jinsu ba ta dago ta dube su ba, sai rubutunta ta ke kamar alhudahuda.
Ranar ziyarar ‘yan makaranta, wato bisiting day ta zo. Kowanne dalibi ya sha wanka ya yi fes, ya fito neman
nasa. Mairo dama ba ta sa a ka ba, tasan Babanta da Innarta duka ba su san da wata ranar ziyara ba. Tunda
ko radiyo ba su damu da su saurara ba, don haka ta samu can wani gefe gindin wata bishiyar goba mai inuwa
ta zauna akan benci tana nazarin littafin the boy slabe da ta karbo a library.
Can anjima ta daga kai ta kalli motoci na gani na fada da ke ta fakin yara na rugawa su rungume iyayensu,
sannan a soma kokawar fito da manyan ma’adanan abinci da katon-katon na kayan masarufi ana ajiyewa.
Waje ya cakude kowa na nemawa ‘yan uwansa wurin zama, babu wanda yasan da ita, a lokacin ne ta ji babu
dadi, ta ji kewar Innarta. Idanunta suka cicciko da kwalla. Kamar daga sama ta ji muryar Uncle a kanta ya ce.
“Mariama”.
Da sauri ta dago tana kokarin boye kwallar idonta, Uncle ne rike da manyan ledoji guda biyu, a bayansa wata
yarinya ce budurwa da akalla zata girme ta da shekaru biyu da kuma wani yaro da zai yi tsara da ita, su kuma
niki-niki da manyan kulolin abinci da picknick cooler wato irin kular nan da ake zuba lemuka da kankara mai
hade da dan famfo a jiki. Ko ba ta tambaya ba tsabar kamanninsu da juna ya gaya mata wadannan yaran
kannen Uncle Junaid ne.
Ta zame kasa tana gaishe shi, ya ce “Kuka kike ko Maryama, sabida mene?”
Ta share kwallar idonta dai-dai lokacin da shi da budurwar suka zauna akan bencin nata, ta ce “Lah Uncle ba
kuka nake yi ba”.
Ya ce “Mai yasa ‘yan gidanku ba su zo ba?”
Ta ce “Ba su san ana yi ba”.
Ya ce “To ki fada min adires na garinku ni da kaina zan je na taho da su a bisiting na gaba. Yanzu dai ga
kannena Ilham da Sagir sun zo miki bisiting, are you o.k?”
Farin cikinta ya gaza boyuwa, bakinta ya gaza rufo don dadi. Ba tasan mai zata ce da Uncle Junaid ba, sai ta
kama hannun Ilham tana murmushi, ta ce, “Na gode Ilham”.
Ilham ta ce “Ba komi Maryam, yadda Yaya Junaid ke ba ni labarinki sai na dauka zan ga wata babbar budurwa,
ashe kamar Sagir ce Maryama?”
Ya mike yana cewa “Ki tabbata ta ci abincin, kuma ba ta yi kewar kowa nata ba, I know you Ilham. Zan dawo
nan da awa daya mu tafi”.
Ta ce “To Yaya Junaidu”. Tana murmushi.
Ilham ta ce “Amma ko kannenki ba su zo ba Maryam?”
Ta ce “Ba ni da kanne, ni ce auta a wurin Innata”.
Suka ci gaba da hira, Ilham na kokarin cika umarnin Yayanta na ganin cewa, ba ta bar Maryam da kewa ba
kamar yadda dan uwanta ya umarce ta. Ta zuba mata abinci mai rai da motsi cikin filet da kirjin kaza ta mika
mata tana cewa “Ci maza kamin Yaya Junaidu ya dawo ya tuhume ni da barinki da yunwa”.
Dariya ta yi, da ta lotsa kumatunta, tana tambayar kanta ko wane matsayi Uncle Junaid ya ba ta haka a wurin
‘yan uwansa? Girmansa da kimarsa ya karu a zuciyarta. Tana ganin bayan Baba da Inna da Yaya Habibu ba ta
da kamar Uncle Junaidu.
Ya dawo da wata leda mai dauke da ruwan (Faro) roba uku masu sanyi ya mikawa Ilham. Suka sha dukkansu
sannan suka yi haramar tafiya, Mairo ta ji babu dadi.
Cikin ‘yan awoyin da ta yi da Ilham sun saba sosai. Ta bude baki cikin al’ajabi tana kallon Uncle da ya ce duka
wannan kayan nata ne. Abinci kuma daga mahaifiyarsu ne sai ta rasa irin godiyar da zata yi wa Uncle din nata.
Bayan tafiyarsu ta kinkimi kayanta daya bayan daya ta nufi hostel. Cikin ledojin ba komi ba ne sai biskit na
kwali kala-kala da crackers na shan shayi irin wadanda ta ke ganin su Kausar na ci, dayar kuwa alawoyi ne,
cakulet kala-kala masu dan karen tsada da katon na irin taliyar da ta ga dalibai suna jikawa (indomie), sai
katon na lemon gwangwani (Rani).
Baki ta bude cikin matsanancin firgici, ba ta taba tsammanin wai ita Mairo zata taba cin irin wadannan abincin
ba a rayuwarta. Cikin kulolin kuwa bayan abinci akwai soyayyun kaji wadanda suka soyu rakau yadda za su
jima ba su lalace ba, cin-cin mai nama (meat pie), cake da sandwitch masu yawa sosai. Kenan godiya ga Uncle
Junaid wadda ba ta karewa.
Mutanenta suka shigo, wani abin mamaki kulolinsu duk iri daya ne da nata, sai kala da ta banbanta. Suka yi
kasake! Cikin mamaki ganin irin garar da ke gaban Mairo wadda ko a mafarkinsu ba su zata ba. Abin da suka
dauka shi ne, ramar da ta ke kwadawa mai tsamin tsiya da kanzo su za a karo mata. To sai ga sabani ga
tunaninsu, ina ruwan Allah Mai azurta bawa.
Mairo dai jeren kayanta ta ke a loka, ba ta kula su ba. Nabilah ta kasa shiru ta ce, “Kausar yau billager ta shigo
gari”.
Kausar ta ce “Ke ina jin ‘charity’ ne daga (MSS), ba ki san ta shiga MSS ba? Kungiyar ‘yan a bamu saboda
Allah?”
Ita yaran sai suka koma ba ta dariya sabida yadda suka sa mata ido babu gaira babu dalili, ko mai ya yi masu
zafi da ita? Allahu A’alam.
Bayan bisiting da sati biyu, rannan Mairo ta fito domin yin fitsari da daddare a lokacin Kausar ma ta fito ta
tsugunna a bakin rariyar hostel tana goge bakinta domin ta kwanta. Mairo na daga bandaki ta hangi wani
mulmulallen abu mai sheki da tsayi na sanda ya nufi Kausar. Ta ware idanunta gabadaya sai ta gane katon
maciji ne wanda ake rade-radin akwai a makarantar.
Ta yar da butarta ta sheko da gudu dai-dai sanda macijin ya fasa kai, ta angije Kausar tun karfinta ta wulwula
ta fada kwatami da baka, abin tsautsayi, sai kulbar (macijiyar) nan ta huce fushinta a kafar Mairo, wato ta
sare ta.
Kausar ta mike cike da bala’i a lokacin idanunta suka gane mata abin da ke faruwa, dai-dai lokacin kulbar ta
sulale tana komawa inda ta fito, ga kuma Mairon da ta angije ta kwance a kasa ba yadda ta ke. Ta daura
hannuwa aka ta rafsa ihu, wanda ya ratsa gaba dayan hostel din, student da metron suka fito. Kausar ta ce
“macijiya ce ta sare ta.”
Ai jin haka captain ta suri Mairo, sauran yara suka bi ta yuuu! Har da su Kausar sai gidan principal ana buga
mata kofa.
Ta fito a gigice ita ma nan take ta bugawa school doctor waya, nan da nan sai ga ta, aka wuce da Mairo
asibitin makaranta, Doctor ta dukufa ga son ceto ranta.
Kausar da Nabilah suka kasa komawa hostel ko babu komai akwai tausayin rai a zukatansu, balle ita Kausar da
tasan hakikanin yadda abinda ya faru. Nadamar abubuwan da ta ringa yi wa Maryam Bedi, suka shige ta. Ta ji
tausayin Maryam matuka, ta kuma tambayi kanta, shin ko wace irin zuciya ce da ita? Irin su Maryam ne masu
rama sharran da hairan, babu shakkah ta yi nadama.
Nabilah ta yi mamakin damuwar Kausar akan Maryam ta yi yawa, ta kasa ko magana. Ta ce “Kausar kowa ya
koma hostel sai mu, ni fa tsoro nake ji”.
A salube Kausar ta sa kafa cikin dan karamin asibitin ta samu benci ta zauna, ba ta da niyyar tashi. Nabilah ta
biyota cikin mamaki, ta ce “Wai me ya faru ne? Ba zaki zo mu tafi ba?”
Ta ce “Je ki abinki Nabilah. Amma ni a nan zan kwana”.
Nabilah ta kama baki, dai-dai lokacin da Mummy Dukku wato principal ta fito zata koma gidanta. Ta hango su
Nabilah ta ce, “Ku kuma me kuke a nan ba ku koma hostel ba?”
Kausar sai ta sa kuka. Ta matso ta dafa kanta domin ta santa farin sani sabida mahaifinta, ta ce “kawarku ce
ince ko?”
Nabilah ta yi saurin cewa “A’ah, dakinmu ne kawai daya”.
Mummy ta lura da kukan da Kausar ta ke sosai ta ce, “Ke kuwa tausayinki ya yi yawa Kausar, alhamdu lillahi
dafin bai shiga cikinta ba, kuma Doctor ta zuke shi. Insha Allah zuwa safiya za ta warware, tashi ku tafi dare ya
yi sosai”.
Sai da suka je daki ne Kausar ta ke gayawa Nabilah hakikanin yadda akai maciji ya sari Maryam. Ta ce “Yanzu
ni tashin hankalina shi ne, idan ta mutu ban nemi gafararta ba ina zan sa kaina?”
Jikin Nabilah ma ya yi sanyi, ta ce, “Allah Sarki, irin su ne ake cewa masu halin ‘yan aljannah”.
Suka yi jugum-jugum har wayewar gari ba su runtsa ba, nadama ta ishe su, sai kuma kaunar Maryam farat
daya ta bi zuciyoyinsu.
Washegari Uncle ya zo kiran suna kamar yadda ya saba, cike da mamakin rashin ganin Maryama a class don
kullum ya shigo idanuwanshi akan wurin zamanta yake. Duk da haka bai fasa kiran sunan ba, har ya zo No. 40,
shiru ba ta amsa ba.
Ya dago manyan idanunsa ya zubawa Kausar cike da zargi kamar ita ce ta boye Maryaman.
Ya ce “dakin ku daya, tana ina ban ganta ba?”
Kirjinsa har wani harbawa yake da sauri-da-sauri. Fargabarsa kada ace da shi iyayenta sun cire ta daga
makarantar sabida su Kausar. Bakin-cikinsa shi ne yau ace Maryama ta bar makarantar nan. Tashin hankalinsa
shine ko sunan kauyensu bai sani ba, alhalin yanzu yadda yake kaunar Ilham haka yake kaunar Maryama. Idan
zai iya rabuwa da ita, to hakika zai iya rabuwa da Ilham.
Cikin in-ina Kausar ta ce “Maciji ne ya sare ta, tana kwance a maternity…”
Tun kamin ta kai karshe Uncle ya fita. Ya doshi maternity cikin matsanancin tashin hankali, ko gani ba ya yi
sosai. Ya banka kofar da kafarsa babu neman izini.
A kwance ta ke, idanunta a rufe, rana daya kacal ta zabge, ta yi wani irin fari fat kamar babu jini a jikinta,
sannan ta kumbura kamar an hura balam-balam.
Nurse din da ke kokarin daura mata ‘drip’ ta juyo a razane ta dube shi, bai kula ta ba ya karisa gaban gadon da
Maryam ke kwance ya tsaya kurum yana kallonta. Kamar an ce da ita bude idonki, ko kuma alamar tsayuwar
mutum ta ji a kanta oho, ta bude fararen idanunta a hankali wadanda suka kumbura suka yi mata nauyin
budewa, a hankali ta ce “Uncle……..” Sai hawaye suka zubo ta gefen idonta.
Ya yi saurin kama hannun damanta, ya ce “Sannu Maryama, sannu kin ji. Allah Ya ba ki sauki”.
Ya juya ga nurse din ya ce “Edcuse me madam Serah, na yi miki shisshigi cikin aikin ki. Maryam na daga cikin
dalibai na masu muhimmanci a gare ni. Ki yi hakuri”.
Ta yi murmushi ta ce “Ai na ga alama, wannan patient din taka akwai raki da saurin kuka. Na dauka dadi zaki ji
da kika ga Uncle sai kuma ki kama kuka?”
Mairo ta maida idanunta ta rufe tana murmushi. Ta nemi ciwon da jikinta ke yi ta rasa, sabida kasancewar
Uncle Junaidu tare da ita.
Suna magana a kanta shi da Madam Serah ta gaya mishi wannan macijiya ta dade tana sarar dalibai, anyi duk
iya kokarin da za a yi don ganin an fitar da ita daga makarantar an rasa. Wani zubin sai a yi tsammanin ma ta
mutu don sai a yi shekaru biyu ba a ji duriyarta ba. Amma yanzu kam za a daukaka zancen zuwa federal da
yardar Allah za a fitar da ita.
Ya ce “Maryama ta kumbura, ta yi biyun yadda ta ke”.
Ta yi murmushi ta ce “Jini ne babu isashshe a jikinta, wanda aka zuke tare da dafin amma already an tafi a
sayo wanda za a sanya mata a asibitin Aminu Kano”.
Hankalin Uncle ya tashi, ya ce yana son ganin Doctor Nanah, ta ce tana ofis ka karisa.
Ya samu Dr. Nanah a ofis cikin tashin hankali. Ta ce “Yaya dai Uncle Junaidu?”
Ya ce “So nike ki debi jinina idan ya yi dai-dai ki sanyawa student dina”.
Ta ce “To bari in diba kadan a auna a gani”.
Ta zuka kadan a sirinji ta mikawa lab asisstant ta auna, ya nuna (negatibe), ga duk wasu gwaje-gwaje da akayi,
sannan dukkansu a 0+. Ya kwanta ta debi leda biyu ta ce ya ci gaba da kwanciya ya huta. Ta ba nurse ta
sanyawa Mairo ta dawo tana fada mishi irin abincin da zai ringa ci har zuwa kwana bakwai.
Nan da nan labari ya watsu cikin FGGC cewa Uncle Junaid ya yi donating jini wa Maryam. A’ah, cece-kuce ya
soma (round) zagaye makarantar musamman daga ‘yan ajinsa da daman suna hankalce da su. Yara kanana da
su amma sun iya gulma. ‘Yan manyan aji kuwa masu yi masa asirtacciyar soyayyah, wadanda a da ba su san
da Maryam din ba suka zo suna kallonta, duk ta takura ta rasa inda zata sa kanta, balle da ta lura har da masu
yi mata mugun kallo.
Ranar da ta dawo hostel Kausar kunyarta ta ke ji, ko ido ta kasa hadawa da ita. Daga baya da ta ga Maryam
din ma ba ta damu ba harkar gabanta kawai ta keyi, sai ta zo bakin gadonta ta zauna ba ta ce komai ba.
Nabilah ta shigo itama ta zauna a katifarta abin da ko da wasa ba su taba yi ba. Suka ce “Don Allah don
Annabi Maryam ki yafe mana. Wallahi sharrin shaidan ne, kuma mun gode da sacrifice (sadaukar da kan) da
kika yi mana. Muna rokonki daga yau mu zama daya a makarantar nan, wato mu zama mu uku cikin amana”.
Mairo ta yi murmushi ta ce “Babu komi, ni dama ban taba kullatarku ba, mamaki dai kuke ba ni. Amma shi ke
nan, komi ya wuce”.
Daga ranar Maryam, Nabilah da Kausar ba a kara jin kansu ba.
To sai kuma ciwon ciki ya kama Kausar, kullum ba ta iya barci, sai murkususu da kuka cikin dare, haka suke
kwana tsaye a kanta har asubah sannan zata samu barci.
Da suka ga abin ya fi karfinsu sai suka yi reporting ga hukumar makaranta. Aka dauki Kausar zuwa maternity
inda aka gano kabar ciki ke damunta. Nan da nan aka yi hamzarin mikata gida, domin abin ya fi karfin asibitin
makaranta.
Suka koma kewar Kausar tare da yi mata addu’a, kullum, har lokacin jarabawa ya matso. Kokarin Uncle shi ne
Maryam ta saki ranta ta yi abin kirki a jarrabawarta, amma ina! Tunanin Kausar da halin da ta ke ciki ya
hanata zama lafiya.
Ranar da suka soma jarrabawa suka dawo hostel sai suka ga babu ko allurar Kausar a dakin. Captain da
Metron sun kwashe sun bai wa iyayenta.
A gigice Mairo ta fita kafarta ko takalmi babu, kanta babu kallabi. Nabilah ma ta bi ta dakin Metron suna
tambayarta yaushe aka kwashe kayan Kausar?
Ta ce “Allah sarki, wannan yarinyar diyar Gwamnan Jos, ta rasu. Tun satin da ya wuce”.
Suka rushe da kuka, suka zube anan suna ta yi. Tsoron Allah Ya kara shigar Maryam da Nabilah. Tun daga
ranar suka koma wasu irin sukuku, ba fuss ba ass. Shi kansa Uncle ya girgiza da mutuwar Kausar, ya yi ta
lallashinsu yana ba su baki. Ya ce da Nabilah abin da yake ankarar da ita ke nan kan daukan duniya da zafi. Shi
Ubangiji ba ruwansa da ko kai wane ne, dan wane ne, wane ne ubanka face ayyukanka kyawawa.
Nabilah ta fi Maryam ramewa, ta fi ta gigicewa, domion dai ta fi ta shakuwa da Kausar. Sannan ta kara
rungumar Maryam a matsayin ‘yar uwarta don sai ta ke ganinta kamar Kausar.
Aka yi jarrabawa aka kare, sai hutu sati mai zuwa. Sai dai fa daga Maryam har Nabilah kowacce cike ta ke da
zullumin sakamakonta. Uncle ya yi fushi da Maryam sosai, domin ta dauko na talatin da takwas yayin da
Nabilah ta dauko na arba’in.
Ta kaskantar da kai ta dinga ba Uncle hakuri, ta tabbatar masa zango mai zuwa za ta dage ta yi abin da zai ji
dadi. Mutuwar Kausar ke nukurkusarta har zuwa lokacin.
Ranar hutu malam Bedi sammako ya yi domin hedimasta ya gaya masa tun ana saura kwana uku, don haka a
kwanakin nan barcin da suka yi kalilan ne sabida dokin dawowar Mairo. Barin ma Inna Hure da shiga goma,
fita goma sai ta siyo abin da zata ajiyewa Maironta. Tun daga kan goriba, kurna, goba, magarya, dinya da ireirensu wadanda tasan Mairon na so babu wanda ba ta nemo ta ajiye mata ba.
Duk sammakon Baban Mairo bai isa makarantar ba sai da aka soma dadewa.
Mairo da Nabilah na zaune karkashin dalbejiya dukkaninsu cikin damuwa suke na rashin ganin kowa nasu.
Nabilah ta ce “Da na san gidanku Maryam da na zo kamin na wuce Lagos hutu wurin Auntyna”.
Maryam ta jinjina kai ta ce “Ba zaki iya zuwa gidanmu ba, can ne cikin surkukin kauye, cikin Fanshekara”.
Nabilah ta ce “Don ba kisan yadda nake son zuwa kauye ba ne, idan kuma kin musanta hakan ki gaya min ki
gani”.
Ta dauko biro da jotter tana jiran ta bakin Mairon.
Mairo ta ce “Fanshekara, motar Gurin Gawa, idan an shiga Gurin Gawa, sai a tambayi gidan Malam Bedi kowa
ya sani. Idan kuwa yara ne kika ce musu ‘MAIRON HURE’ da gudu za su rako ki”.
Duka Nabilah ta dauke cikin jotterta, wanda ke bayansu ma ba su san da tsayuwarshi ba shi ma ya dauke cikin
kakkaifar kwakwalwarsa.
“Lah, ga Babana nan!”. Mairo ta fada cikin matsananciyar murna, kamin ta kwasa da gudu ta rungume Malam
Bedi. Nabilah ta dago daga rubutun da ta ke ta bi bayan Mairo da kallo, sai ta hango ta rungume da wani
yagulallen tsoho, sanye cikin yadin algarara, kanshi duk furfura. Ta ce a ranta, “Ya za a yi ace wannan ne ya
haifi Mairo? Ya fi kama da kakanta fiye da babanta”.
Ba tasan cewa ba wai shekarun da ya yi a duniya ba ne suka janyo masa wannan tsufan ba, a’a, wahalar
rayuwa ce kawai ta noma, girbi, da sussuka irin ta kowanne manomin kauye.
Tausayin Mairo ya kamata, ta tabbata ita ‘yar talaka ce futuk, amma she is contented with what she habe (a
gamshe ta ke da abin da ta ke da shi, ba ta taba kwadayin abin hannun wani ba).
Mairo ba ta taba tambayar Nabilah ita ‘yar waye ko daga ina ta fito ba. Wannan ya sa Nabilah tambayar
kanta, shin Maryam wace iri ce? A zahiri miskila ce, abin da tasa a gabanta shi ne kawai ya dame ta.
Ta mike ta tadda su tana gayas da Malam Bedi cikin tsananin girmamawa.
Mairo ta ce “Baba Nabilah sunanta, ajinmu daya, dakinmu daya. Da har da Kausar amma ita ta rasu”.
Fuskarshi ta nuna bai ji dadi ba, ya ce, “Sannunki Nabilah, Allah Ya jikan Kausar”.
Idanunta ya ciko da hawaye, ta juya tana sharewa ta ce, “Amin”.
Babu irin neman da ba ta yi wa Uncle ba, don su gaisa da Babanta, amma ba ta ganshi ba. A haka cikin rashin
jin dadi ta yi sallama da Nabila rike da ‘yar jakar kayanta ta buhu (Ghana Must Go) suka fita. Sun sha wuya
matuka irin ta motocin haya kamin Allah Ya kawo su gida.
Ganin irin wuyar da Babanta ya sha ya sa ta alkawarta wa ranta daga wannan hutun zata hutar da shi kai ta
makaranta da dawo da ita, tunda ta gane hanya zata dinga tafiya da kanta.
Tunda yaro ya shigo da jakar Mairo Hure ta biyo bayansa da saurinta. A soro suka yi kacibus, da Mairon nata.
Suka rungume juna kamin Hure ta soma hawaye ta ce “Ashe wannan ranar zata zo Mairo, ranar da zan kara
ganinki?”
Mairo kuwa baki ya ki rufuwa a haka suka karasa cikin gidan kamar wadanda suka shekara ba su ga juna ba.
Inda duk Inna ta mika hannu sai ta zarowa Mairo abin sawa a baka, ta ci ta yi nak! Ta ci girkin Innarta da ta yi
kewa, ba kadan ba. Duk da cewa abin da ta ke ci a makaranta ya fi na gidansu amfani a jikin dan Adam.
Hure ta kasa boye mamakinta, ta ce “Shin mai kike ci a makarantar nan ne Mairo? Kinga kuwa yadda kika
zama buleliya, kika yi fari sai sheki kike?”
Mairo ta sa dariya, ta ce, “Ba abin da bana ci Inna. Tun daga kan kwai, dankali, agada, doya, madara, nama da
kifi ba abin da ba a bamu. Har ‘ya’yan itace (fruits) ba dole in zama buleliya ba?”
A ranar dai Mairo da iyayenta kwanan zaune suka yi, tana ba su labarin rayuwarta a makaranta. Sai dai fa duk
rabin hirarta, “Uncle Junaidu” wanda ya yi ruwa ya yi tsaki wurin sama mata farin ciki da walwala a cikin
dalibai ‘yan uwanta.
Malam Bedi ya ce, “To Allah Ya saka mishi da alkhairi”.
Sai dai a cikin labarinta ba ta kawo labarin saran sa macijiya ta yi mata ba, don ta tabbata idan suka ji,
kidimewa za su yi su ce ba zata koma ba.
Hutun Mairo gwanin ban sha’awa a gidansu, gabadaya yanayin rayuwarta ya canza, ba ta barin Innarta da aiki
ko ya ya, sai ta karba ta yi. Haka ta ke bin babanta gona tana taya shi shuka da ban ruwa. Abokinta Rabe da ya
ji ta zo hutu daga makarantar kwanan da aka kai ta, sai ya aiko yaro rannan da yamma wai Mairo ta zo su je
su hau tsamiya. Malam na jin sanda ta maida dan aiken ya tambayo mata Rabe, shin yanzu ta yi masa kama
da ‘ya’yan birrai ne da zai ce ta zo ta hau bishiya?
Sai ya yi murmushi yana kara shi wa Habibu albarka a zuciyarsa.Rannan sun dawo gona ke nan ita da
Babanta, ta zuba ruwa a buta tana alwala a gindin rijiya sai ta ji rurin mota. Kamin ta kare alwallar sai jin
sallamar Nabilah ta yi a tsakar gidansu. Da ta yi wurgi da butar cikin rijiya ta kwaso da gudu ta cacume
Nabilah suna ta tsallen murna.
Inna ta fito da sabuwar tabarma ta shimfida mata a shararriyar rumfar hutawar su tana, “Lale da Nabilah,
muna murna da zuwan Nabilah”.
Shi ma malam ya fito daga turakarsa yana na shi marhabin da bakuwar Mairo domin dai labarin Nabilah
kamar na Uncle ne a cikin kansu.
Nan da nan ya fita ya shigo mata da damammiyar sabuwar fura da nono kindirmo gami da gasasshen nama.
Nabilah karamcin iyayen Maryam ya burge ta, rayuwarsu kuma ta ba ta sha’awa. Ta raba komai biyu ta kaiwa
direbanta wanda ya kawo ta. Ta dawo tana ci suna hirar bayan saduwa har goshin magriba, sannan suka yi
haramar tafiya.
Nabilah ta ba ta mamaki kwarai yadda ta iya ta sarkafo kai cikin surkukin kauyen su, ko da wasa ba ta kawo
zata iya cika alkawarin da ta dauka ba. Ta yi zaton dai ta karbi adireshin ne kawai. Direbanta ya sauke musu
kwandon dankalin Turawa da doya cikin (boot) wanda Nabilar ta kawo musu a matsayin tsaraba.
Hutu ya dauko karewa, Mairo ta soma shiri cikin nutsuwa. Tarkacen da ta tafi da su da farko, yanzu duk ta
rage, sai wanda zai amfane ta kadai.
Ta ce da Innar ta daina tara wannan uban kanzon da ta ke tara mata, ana ba su lafiyayyen abinci sau uku a
rana. Ta tsefe kanta ta wanke tas da shampoo ta je aka yarfa mata sabon kitso yiri-yiri. Ana saura kwana biyu
su koma makaranta. Ta yi wankan yammanta ta sanya sabuwar atamfarta ‘jaba’ ta zauna a rumfar tsakar
gidansu tana gyaran kumbarta. Wani yaro mai zakin muryar tsiya ya kwada sallama ya kara da cewa, “Wai ana
kiran Mairo a waje”,
Sai ta ji abin banbarakwai ta dago kai tana hararar yaron. Dai-dai lokacin da Inna ta fito daga bayan gida rike
da buta zata yi alwala a gindin rijiya, ta ce da yaron “Wane ne mai kiran Mairo?”
Yaron ya ce “Wani mutum ne dogo, fari ne kamar Balarabe, kayanshi masu kyau ne, ban taba ganin mutum
mai kyawunshi ba. Ga dukkan alamu daga birni ya ke”.
Mairo ta saki kunne tana mamakin surutun Ilu dan makotansu. Ita kuwa waye wannan? Ina za ta tsaya tana yi
wa mutum irin wannan kallon kowane ne shi, balle har ta iya yin sharhi a kansa?
Kanta ya daure, haka kawai ta ji tana son ganin wannan mutumin mai kiran nata. Inna ta ce “Mairo kuwa, wa
ta sani a birni? Ga shi ka ce namiji ne balle ince ko diyan baffanta ne, je ka ce ba zata zo ba, haka kawai
mutanen birnin nan ba abin yarda ba ne”.
Ilu ya juya da gudu don isar da sako, Mairo ta mike ta jawo hijabinta a jikin kyaure tana cewa “Bari na je Inna,
kika sani ko sako ne daga Yaya Habibu?”
Inna Hure ta ce, “Ai kuwa, maza je ki jiyo mana”.
Ta fita tana dariyar Inna, ganin yadda ta rikice daga ambaton Habibu.
Tsaye yake jikin bishiyar maina, wadda ke gaba kadan da gidansu, sanye da kufta da wando na farin yadin
boyel mai salki, kafarshi cikin rufaffen takalmi baki (cober) sumar kanshi kwance lub a kanshi, sai sheki yake.
Eh, gaskiyar Ilu ne, yana yanayi da jinsin Larabawa sabida murdaddiyar suma ke gare shi irin tasu. Mamakinta
da farin cikinta ya kasa boyuwa, bakinta ya kasa rufuwa. UNCLE JUNAIDU ne tsaye yau a kofar gidansu.
Ta kai hannuwanta biyu ta rufe bakinta ta kasa cewa komi. Shi kuwa murmushi ya yi, murmushin nan nasa
mai aji da tsada da ba kowa yake yimawa ba. Ta bude baki a hankali ta ce “Uncle……..”
Sai kuma ta juya gida da gudu ta yayibo sabuwar tabarma ta shimfida masa a tsakar gidansu, Innar na ta
tambayarta wane ne, amma ta kasa magana, ta komo ta ce “Inna debo ruwa mai sanyi, Inna Uncle Junaidu
ne”.
Ta fita da gudu ta shigo da shi. Lokacin Inna ta debo ruwa cikin kwanon sha mai tsafta, mai sanyi daga
randarsu. Ta tsugunna daga can gefe suna gaisawa da Uncle tana ta yi masa godiyar dawainiyar da Mairo ta
gaya masu yana yi da ita. Cikin girmamawa ya dukar da kai yana cewa “Babu komai Goggo. Maryam kanwa ce
a gare ni”.
Innar ta mike ta shige daki, ya dubi Mairo suka yi murmushi, sannan ta duka tana gayas da shi cikin ladabi.
Sau tari tana jin nauyin Uncle Junaidu kasancewarsa malaminta, duk da shakuwa da amincin da ke
tsakaninsu.
Ya ce “Zuwa na yi na ji shin sau nawa kika yi bita a tsawon hutunki, ko kuwa tunda kika shigo gida kika jingine
jakar shi ke nan?”
Ta ce “Wallahi Uncle kullum da dare ina yin karatu, kuma ka tambayi Innata”.
Ya ce “Shi ne kuma ranar hutu kikayi tahowarki ko ki neme ni in gaisa da Baba?”
Ta mike ta sa silifas tana cewa, “Jira ni in zaga gona in kira Baban, ya yi min shaida akan lokacin da na bata
mishi ina nemanka”.
Dariya ta ba shi sosai, yarinyar ta kan burge shi haka ta ke ‘frank’ komai da ke zuciyarta fade ta ke iyakar
gaskiyarta. Ya ce “Dawo zauna abunki, barshi ya dawo da kansa kada ki katse masa aiki. Na yarda kin neme ni
ba ki ganni ba, don ni kaina nasan na koma gida da wuri sabida ciwon Sagir, abin da ban yarda ba shi ne, ba ki
yi kewata ba Maryam, don ga ki nan kin yi kiba abinki. Ni kuwa dubi yadda duk nabi na rame sabida kewarki”.
Yana fada yana taba kashin wuyansa wai yana nuna mata ramar.
Dariya ta yi, wadda ta fiddo jerarrun hakoranta farare kal, da siririyar wushiryarta. Ta ce “Allah Shi ne
shaidana akan hakan. Babu ranar da zata fito ta fadi ban tunaka ba Uncle, ban kuma yi wa Inna da Baba
tadinka ba. Idan ba ka yarda ba na kira Inna yanzu ka tambaye ta”.
Ya kama baki “Ke kuma haka kike da son a yi miki shaida Maryama? Tunda kin ce Allah Shi ne shaida ai kin
gama magana. Na yi kewarki Maryama yadda ba kya zato, nayi-nayi in bari kwanaki biyun nan su cika ki koma
makaranta in ganki a can na kasa. Ban san mai yasa kika shiga raina har haka ba”.
Kalamanshi sun yi mata tsauri, kuruciyarta ta fito a fili, cikin halin ko’in kula ta yi murmushi kawai ta ce “Ina
Ilham? Wane irin ciwo ke damun Sagir?”
Ya ce “Ilham tana gaishe ki. Ga aike ma ta ce na kawo miki”.
Ya zura hannu cikin aljihunshi ya fiddo wani abu kulle cikin leda. Ya mika mata ta amsa cikin jin dadi tana
kuncewa, ya ce “Sagir sikila ce ke damunshi, tun yana yaro”.
Ta ce, “Ayya Allah Sarki, Allah Ya ba shi lafiya”.
Ga yadda ta lura Uncle na son ‘yan uwansa kamar yadda ta ke son Yaya Habibu. Awarwaraye ne na silba
sirara masu kyau guda shidda. Ta sanya a hannunta tana murmushi, ta ce “Ka ga Uncle sun yi min dai-dai, ka
ce da Ilham na gode”.
Shi dai kallonta kawai yake yi, shi kadai yasan abin da yake sakawa a zuciyarsa. Ba ta kula ba ta ke shaida
mishi jibi da kanta zata dawo makaranta.
Malam Bedi ya yi sallama ya shigo, kansa dauke da kullin hatsi, kafadarsa rataye da fartanya da lauje, su duka
biyun suka mike suka karbe shi suna yi mishi sannu da zuwa. Ya bi bakuwar fuskar da kallo cikin mamaki,
kamin ya tanka Mairo ta ce “Baba Uncle Junaidu ne”.
Da sauri Malam Bedi ya mika masa hannu suka yi musabiha, sannan suka zauna a tabarmar da Mairo ta
shimfidawa Junaidun suna kara gaisawa. Ya yaba kwarai da nutsuwar Uncle, haka kawai ya ji yaron ya shiga
ransa. Ya yi masa godiya mai tarin yawa kan hidimar da Mairo ta gaya masu yana yi mata.
Ya ce “Don Allah ka kula min da karatun Mairo ko bayan raina, na baka amanar Mairo a wannan makarantar,
ba ta da kowa sai Allah, Ba don alkawarin da na daukarwa Habibu ba, da bazan barta ta je ba”.
Jikin Uncle ya yi sanyi matuka da kalaman Baban Mairo. Ya ce “Insha Allah Malam lafiya Maryama za ta gama
karatunta ga dukkan alamu yarinya ce mai hazaka da nan gaba za a amfana da ita. Na dauki wannan amanar
ta tsayawa akan karatunta iyakar karfina. Ku dinga yi mana addu’a”.
Ya ce “Addu’a ga ‘ya’yan musulmi duka muna yinta kullum. Sai dai daga yau JUNAIDU kana cikin addu’ata ta
safe da dare, har zuwa ranar da na daina numfashi”.
Uncle Junaidu bai bar kauyensu Mairo ba sai yamma lis. Ya tafi cike da tunanin Baban Mairo da tausayinsu.
Bai san mai yasa yake jin tausayin Malam Bedin ba, bayan ba ya da hujja na yin haka, Tunda kuwa bai rasa ci
ba, bai rasa sha ba, kai a fadin kauyen Gurin-Gawa ma yana daga cikin attajiran garin.
Manomi ne mai zuciyar neman na kansa, bai dogara da kowa ba. Baya kuma nema a hannun kowa. To ko
Maryaman yake tausayi sabida iyayenta dattijai ne? Bai sani ba, abin da ya sani kawai shi ne, yana kaunar
Maryam da iyayenta. Wannan amanar kuwa da ya daukarwa Malam Bedi, yana rokon Allah Ya ba shi ikon rike
ta.
Litinin, Mairo ta yi shiri, tun da asubah Malam Bedi ya rakata tasha ya sata a mota sabida ta dage ita kadai
zata dinga kai kanta tana dawo da kanta, don ta saukakawa Babanta. Kafin azahar tana cikin Minjibir, suka
game da Nabilah suka gyare dakinsu suka durfafi karatu da kwarin gwiwar Uncle, da kulawarsa gare ta.
A karshen zangon sai ga Maryam Bedi da sakamakon (5th position), wato ta biyar a ajinsu. Ga yadda Uncle
dinta ya ce da ita, wannan alama ce mai nuna wata rana zata fi hakan. Haka nan ita kadai ce ta fito da (80%) a
darasin da ta fi so (Ingilishi). Sai dai a cewar ‘yan ajinsu, ba wani nan, sama da fadi ne Junaid ya yi mata,
kasancewarta ‘yar gaban goshinsa. Amma ina za a ce wannan bakauyar ta fi su iya Turanci daga zuwanta a
zangon baya? Koma dai me ye, Maryama ba sune a gabanta ba, burinta ta cimma burinta na cika alkawarin da
ta kaukarwa Yayanta Habibu.
Kwanci tashi ba wuya wurin Allah Maryam da Nabilah suka zana jarrabawar wucewa babbar sakandire (SS.1),
wato placement, suka fara shirin tahowa hutu. Sai dai kamin lokacin Maryama ke daukar na daya, Nabilah na
biyu, ko Nabilah na daya Maryam na biyu.
Kamin kuma su zana jarrabawar nan ba haka Uncle ya barta ba, sai da ya tabbatar ya tusa mata karatu cikin
kwanyar kanta ta yadda faduwa, sai wani babban ikon Allah.
Zuwa lokacin Maryama ta kara girma, matashiyar budurwa ‘yar kimanin shekaru goma sha biyar. Zama da
Nabilah ya sa Mairo tasan me ake kira ‘gyara’ na diya mace. Ta yi sharr ta yi ‘fresh’ jazur da ita. Kirjinta ya
soma cika dagwas haka kirarta ta soma fitowa na alamun budurci. Gashin kanta ya mike baki sidik na Fulanin
usuli sabida samun gyara. Duk wani abu da tasan zata yi amfani da shi a kantin makaranta ta ke saye ta tafi da
shi gida, wasu abubuwan kuma daga Nabilah ta ke samu duk da ko yaushe cogewa ta ke da karbar abin
hannun Nabilah, amma naci da mitar Nabilah ke sawa ta amsa wani zubin ko ta ki ko ta so, don ba zata barta
ta zauna lafiya ba da korafi da mitar ba ta dauke ta ‘yar uwa yadda ta dauke ta ba.
Suka kare jarrabawa ta dawo gida inda ta tarar da tashin hankalin da ba ta taba haduwa da shi ba a
rayuwarta. Malam Beddi ya fadi a gona rabin jikinsa ya mutu (paralysed), sai dai a kwantas a tayar.
Mairo ta yi ta kuka kamar ranta zai fita, kuka irin wanda ba ta taba yi ba a rayuwarta. Daga kwancen da yake
Malam Bedi, ya miko hannun shi mai lafiyar ya kamo hannunta yana dan girgizawa alamun lallashi. Mairo ta
soma damuwa kwarai da rashin zuwan Habibu, tana tunanin da yana nan, da tuni ya kai Babansu asibiti,
shekaru biyar curr ba aike ba sako, anya kuwa Yaya Habibu bai manta da su ba?
Daga ranar ta ajiye komi ta shiga taya Innarta jinyar Baban. Ita ce ke ba shi abinci safe, rana da kuma dare. Ita
ke yi masa alwala ta fuskantar da shi alkibla, yayin da Innar ke kula da tsaftar jikinsa da dahuwar abinci.
Maganar makaranta Mairo ta ajiye ta a gefe, ba ta jin tana da ranar komawa har sai Allah Ya baiwa Baba
sauki. Duk da shelar da ake ta yi a rediyo na cewa, a koma.
A karshen watan Allah ya jefo Alhaji Abbas ya tarar da halin da dan uwansa ke ciki, ya yi ta yi wa Hure fada
kamar ya doke ta ya ce, mai yasa ko da kanta ba zata je ta fada masa ba? Da dan uwansa ya mutu cikin
wannan halin da ba zai yafe mata ba.
Ya debo su duka a motarsa suka taho asibitin Murtala a Kano, aka ba su gado. Nan aka ci gaba da bai wa
Malam Bedi kulawa ta masu lalura irin tasa ‘Physiothearaphy’. Har zuwa watanni biyu, babu wani canji ko
hannunsa ba ya iya motsawa.
Mairo cikin asibitin ta zama ‘yar gari ba inda ba ta shiga. Rannan Malam Bedi ya bude baki ya yi magana, ita
da Hure suka matsa sosai cikin tsananin murna, suka kasa kunne don jin abin da zai fada. Babu abin da ya ke
ambato sai, “Habibu… ku kirawo min Habibu”.
Dukkansu babu abin cewa, dai-dai lokacin da Ladidi daya daga cikin ‘ya’yan Alhaji Abbas ta shigo dauke da
kwanukan abincinsu. Tana yatsina ta ajewa Innar kwanukan babu ina wuni, balle ya mai jiki. Ta juya zata fita,
wannan al’adar ‘ya’yan Alhaji Abbas ce ga su Hure, tun zuwansu asibitin don ba su ga dalilin da Alhajinsu zai
damu da wadannan shirgin kauyen ba akan wannan gawa-ta-ki-ramin Bedin, shi a wahale su a wahale. Kullum
dare da rana ana aikensu kawo abinci, tun daga Yakasai suke takowa a kasa har zuwa asibitin. Yanzu kam
yaran har buyarwa iyayensu suke idan lokacin kwashe abincin ya yi a neme su sama da kasa a rasa, wani
lokacin sai shi Alhajin ne ke kawowa da kansa.
Har ta kai bakin kofa sannan ta juyo ta ce “Ke Mairo, tare muke da wani mutum wai yana nemanki, Baba ne
ya hado ni da shi na nuna masa ku”.
Ta ce “Yana ina?”
Ladidi ta ce “Ga shi can a kofar shigowa ward din nan”. Ta kada kai ta fita abinta.
Mairo ta sanya gyale ta fito tana dube-dube, sai ji ta yi cikin taushin murya mai cike da damuwa an ce
“Sannunki Maryam, kin kyauta”.
Ta daga idanunta a hankali ta dube shi cikin mamaki, Uncle Junaidu ne, rungume da hannayenshi a kirji,
kafarshi ta dama jingine da bango, ya yi rama ainun cikin riga da wando na yadin siliki.
Suka zubawa juna ido na ‘yan dakikai, kamin ta sunkuyar da kanta hawaye na zuba, suna diga kan tafin
kafarta. Uncle ya kula, ya ce “Ni ne ya kamata na yi kuka ba ke ba. Ni da kika bari cikin zullumi da yawon
nemanki kusufa-kusufa. Idan har yanzu ba ki yi hankalin da za ki damu da damuwar masu kaunarki akan ki ba,
sai yaushe ne Mariama? Watanni uku Baba ba lafiya ba ki neme ni kin sanar da ni ba, ba ki sanar da hukumar
makaranta uzurinki ba. Na raina wayonki Mariama, kin bata min sosai, amma hakan da kika yi ya taimaka min
wurin gano matsayin da kika ba ni a zuciyarki. Na gane ba ni da wani muhimmanci, ni kadai na…….”
Muryarshi ta sarke sabida takaici, ya wuceta ya shiga ciki yana raba ido a cikin ward din, har ya hango Inna
Hure tana yi wa Malam firfita. Da sauri ya karasa ya rungume dattijon hawaye na fita mishi tararara! Bedi ya
mika hannunshi mai lafiyar yana shafar kanshi, ya ce, “Habibu….”
Ya zube a gabanshi ya kamo hannunshi ya rike tamau cikin nasa kai ka ce mahaifinsa ne. Ya ce “Baba ba
Habibu ba ne, Junaidu ne, Baba Allah Ya ba ka lafiya”.
Jikinshi na mazari da karkarwa ya ce, “Junaidun-Mairo?”
Ya ce “Shi ne Baba”.
Ya kama hannunshi da nashi hannun mai karkarwa ya ce “Ina Mairo?”
Mairo da ke rakube a gefe tana rasgar kuka maras dalili, ta karaso ta ce “Ga ni Baba”.
Ya ce “Miko min hannunki”.
Cike da fargabar abin da Baban ke shirin yi, ta daura hannunta na dama akan nashi. Ya zare nashi, nata ya
sauka akan na Junaidu, ya kama su duka biyun ya dunkule ya ce “Na ba ka amanar Mairo, ka rike min ita
amana kar ka bari a raba ta da mahaifiyarta. Idan Habibu ya dawo ka damka masa ita, shi kadai na yarda ya
rike min Mairo sai uwarta, kai kuwa dama amanata da kai…. ita ce karatunta…….”
Ya zare hannunshi ya yi shiru.
Jikinsa ya mace murus, daga shi har Mairo an rasa wanda zaiyi jarumtakar fara dauke hannunsa. Ita kuwa
Hure tana gefe akan tabarma tana ta sharar hawaye, ya yi ta maza ya zare hannunsa cikin karfin hali ya ce
“Baba Allah zai ba ka lafiya. Da yardar Allah kai zaka ci gaba da rikon Maironka, har ka daura mata AURE”.
Haka suka kasance har dare, jikin Malam ya ki dadi.
Bayan sallar isha’i Junaidu ya tafi gida da alkawarin gobe da sassafe zai zo ya nema masu (transfer) zuwa
asibitin Aminu Kano.
Da asubahin ranar Hure ta tashi ta ciko ruwa a buta ta dauko roba ta zo da niyyar yi wa Bedin alwala.
Allahu Akbar ashe Allah Ya amshi abinSa cikin dare. Ta ja mayafi ta rufe masa ido ta yi alwala tana hawaye ta
tada kabbarar sallah. Mairo ta tashi daga kan tabarmar da ta ke kwance ita ma ta yo alwalarta ta tada sallah.
Da ta idar ta juya tana gayas da Inna, a nan ta lura Innar lazimi ta ke tana kuka. Sai ta ja gefe ita ma ta soma
kukan da ba tasan dalilinsa ba.
Gari ya yi dan shaaa! Haka, Misalin karfe shidda da rabi na safe, Junaidu ya iso biye da shi, Ilham ce rike da
filas din ruwan zafi da filas din abinci. Shi kuma niki-niki da ledoji ya rusuna yana gayas da Inna, tare da
tambayarta lafiyar mai jiki. Ta daure ta ce “Ka taimaka ka je gidan nan na Yakasai, inda idan aka rakoka nan,
ka fadawa maigidan ya zo ya dauki gawar dan uwansa a yi masa suttura”.
A firgice Junaidu da Mairo suka dago, kamin dukkansu su karasa ga gadon Malam Bedi. Mairo ta sa hannu ta
yane zanin da Inna ta rufe shi da shi. Ta tabbatarwa kanta Innar ba wasa ta ke ba, sai ta sulale a kasa ita ma
babu alamun numfashi a tare da ita.*** ***
Uncle Junaidu ya yi mata halarcin da ba zata taba mantawa ba a rayuwarta. Tare da shi aka yi ta zaman
makoki har tsayin kwanaki bakwai, mahaifiyarshi da kannenshi duka ya kawo su sun yi wa Inna Hure gaisuwa.
Ranar da aka yi sadakar bakwai ya tura aka kira masa Mairo azure, ya kara yi mata ta’aziyya, ya kara da nasihu
masu sanyaya rai da karfafa gwiwa. Ya ce ta daure sati mai zuwa ta dawo makaranta har zangon ya yi nisa ba
tareda ita ba.
Ta rantse masa zata dawo amma tana tausayin Innarta, yadda zata barta cikin kewa. Ya ce “Wata rana aure
zaki yi Maryama, ke da Inna sai gani da yawo, ita kanta tasan hakan. Don haka ki taimake ni in rike nauyin da
marigayi ya aza mani akan karatunki”.
Bayan tafiyarsa Mairo da Innarta idan ka gansu gwanin ban tausayi. Tunanin Mairo shi ne, wa zai dinga
nomawa Innarta abin da zata ci? Idan wanda ke cikin rumbunsu ya kare? Allah maji kan bawa, washegari sai
ga Alhaji Abbas niki-niki da kayan abinci ya kawo musu. Ya kuma ce, wannan nauyin ya dauke shi insha Allahu.
Sai a nan hankalin Mairo ya dan kwanta duk da Innar ma ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba.
Shi ma Alhajin ya yi mata zancen makaranta ta ce, insha Allah karshen wannan satin zata koma.
Hakan kuwa aka yi, ranar litinin ta yi shiri ta koma makaranta. Nabilah ta yi mata ta’aziyyar babanta wanda ta
ji a bakin Uncle Junaidu.
Rayuwar Mairo ta sauya kwarai, ta zama babu walwala, akwai shakuwa da kauna mai tsanani tsakaninta da
mahaifinta, don haka ta ke jin kanta tamkar ita kadai ta rage a duniyar. Sai ta samu kanta da son yin abin da
zai debe mata kewa, don haka ta fara tunanin yin RUBUTU.
Tana yi tana gutsirewa ta ajiye, idan ta ji bai yi mata ba. Kamar da wasa, ta fara rubutun labarai cikin harshen
Turanci a kalla guda biyar tana yagawa. Lokacin da ta shiga aji biyar na babbar sakandire aka ba ta kallabin
‘AMIRA’ sabida hidimarta ga masallaci da kungiyar dalibai musulmai da Uncle Junaid ya sa ta. Haka nan ita ce
ja gaba a club din Uncle, watau English club.
Kowa yasan Uncle Junaid a Minjibir, yasan shi tare da Maryam Bedi. Mairo ce mai rubutawa club din DRAMA
Uncle ya yi gyara a gabatar da ita. Wannan wata hikima ce da Allah Ya yi mata wadda ke bai wa kowa
mamaki. Sai dai iyaka kwakkwafinka da sa ido, haka nan so kulla karya da sharri, ba zaka ce akwai soyayya
tsakanin Junaid da Mairo ba, sai mutunta juna.
A wannan hutun na zangonsu na biyun karshe a sakandire da Mairo ta zo gida. Ta tarar da ciwon kafar Inna ya
yi tsanani. Ko bayan gida ba ta iya takawa sai dai ta ajiye (foo) a kusa da ita. Don haka Mairo ta kara kadewa
ta rame, ta kuma soma tunanin jingine makaranta domin Innarta, tun tana tunanin Habibu har ta watsar ta
hakura da shi, shi da ya ce shekaru shidda kacal zai yi.
Ta tabbata inda duk Habibu ya ke tunda ya iya ya yi shekaru takwas bai neme su ba, to babu shakka ya manta
da su, ya samu sabuwar rayuwa a gaba. Ba zata taba amincewa da cewa wani mugun al’amari ne ya faru da
shi ba, tunda kuwa lafiya ita ke buya, amma ba rashinta ba.
Cikin watan January ne sanyi ya yi tsanani, hazo ya mamaye sararin samaniya, wanda duk ya yi kuskuren fita
babu shakka gashin ido dana girarsa fari fat za su koma. Mairo ta dawo daga wani chemist inda ta amsowa
Inna maganin mura tana tafe yafe da mayafin gyauton atamfa, ta dunkule hannuwanta wuri guda.Tana ta
sauri domin ta daura dafa-dukar taliya akan wuta, wadda zata bai wa Innar, kasancewar ba komi ta ke iya ci
ba, sai abu mai laushi, kuma mai dan ruwa-ruwa, duka Mairo na kokari a kai. Ta kada ta raya da Innar ta kai ta
asibiti, amma Innar ta ki, ta ce, ciwon kafa ba a kanta tsoffi suka fara shi ba.
Ta doso zauren gidansu ke nan ta hange shi, tsaye a kofar gidansu. Sanye yake da farar shirt (Armani) da
dogon bakin wandon jeans ya daura jibgegiyar rigar sanyi mai hade da hula bisa. Duk hazo ya ba ta tsararren
gashin idonsa, girarsa da sajensa. Mairo ta ce a ranta, Allah Sarki Uncle! Cikin wannan sanyin ya taho tun daga
Minjibir sabida rashin komawata makaranta.
Tun daga nesa ta ke yi masa murmushi amma shi fushi yake sosai. Ta kariso cikin nutsuwa, tana karasowa ta
russuna tana gayas da shi ya ce “Ni bana son wata gaisuwarki, kawai shiga ciki ki hado kayanki ki zo mu tafi”.
Ta girgiza kai kamin ta wuce cikin gidan ya bi ta a baya. Ta fara da sauke tukunyar daga kan wuta, kana suka
karasa dakin Innan da sallama. Shi kansa ya girgiza da ganin ramar da Innar ta yi, tana kwance bisa katifar
auduga ta amsa sallamar su. Nan ya gano amsarsa ta rashin komowar Mairo makaranta.
Jikinsa ya yi sanyi, ya daga manyan idanunsa ya dube ta suka yi wa juna kuri da ido.
Wani irin tausayinta ke ratsa zuciyarshi, wani sabon feelings ya shiga ratsa kowannensu. A yanzu kam ji ta ke
ba ta da kowa sai Uncle, babu wanda ya damu da rayuwarta sai shi. Duk da Alhaji Abbas na iya kokarinshi
akansu. Ta sauke kwayar idonta kasa a hankali, hawaye na disa bisa tafukanta. Ya sauke nasa idon akan Innan
cikin matsananciyar damuwa, ya ce “Sannunku da jiki Inna, amma ya dace ki daure yanzun nan mu tafi
asibiti”.
Ta ce “Kayya Junaidu, wadannan kafafun bana jin za su kuma takawa a doron kasa. Akwai likitan da ya isa ya
raba tsoho da ciwon kafa? Sai Allah!”
Ya ce “Inna ku daina fidda rai da rahmar Ubangiji, babu ciwon da Allah Ya saukar, ba tare da ya saukar dashi
tare da maganinsa ba”.
Ta ce “Ai ana shan maganin Junaidu. Watakila abin da nake gudu ne, dole sai ya faru……..”
Cikin matsananciyar damuwa ya ce “Wane abu ne kike gudu Inna?”
Ta ce
“Zaman Mairo da Iyalan Abbas”. Daga haka ta yi shiru.
Daga shi har Mairo su ma shirun suka yi. Mairo ta rasa dalilin da ya sa Inna ta tsani iyalan Alhaji Abbas, abin
kam ya wuce na cewa wai don sun so su dauke ta ne. Watakila dai akwai wani boyayyen abun don yadda ba
ta sonsu ba ta shiga shirginsu, haka su ma.
Tun tasowarta ba ta taba ganin wata cikin matan Alhaji Abbas a gidansu ba, haka ita ma Innar ba ta taba zuwa
ba. Ita duk ba wannan ya dame ta ba, illa samun lafiyar Innarta. Ba ta son jin irin maganganun da Innan ke yi a
kullum suna kara tayar mata da hankali.
Junaid ya yi musu sallama ya tafi, washegari sai ga shi ya zo da likita har kauyen wanda likitan gidan su ne. Ya
dade yana duba kafafun Innar, ya rubuta magunguna masu inganci da allurai ya ba Junaidu.
Ranar litinin ya dawo da magungunan ya nunawa Mairo tsarin shan su dalla-dalla. Ya je babban dakin shan
magani na kauyen ya tattauna da nurse da kullum zata zo har gida ta dinga yi wa Innan allura.
Cikin sati guda kafafun Inna sun yi kyau, har tana iya zagayawa bayan gida. Ranar wata alhamis da daddare
suna kwance ta ce “Mairo”, tace “Na’am Inna” “ ni ko ba don wani abu ba, da na ce Junaidu YA AURE KI”.
Gaban Mairo ya fadi damm! Ta dade bata saisaita tunaninta ba, cikin dabarbarcewa ta ce “Inna ke ko mai
yasa kika yi wannan tunanin?
Uncle Junaidu Yayana ne, yadda na dauki Yaya Habibu haka na dauki Uncle, babu wani tunani na daban ko ya
ya game da shi a zuciyata.
Allah ne Ya hada mu, Ya hada zumunci mai karfi a zuciyoyinmu. Babu wani abu makamancin wannan, sai
mutunta juna”.
Inna ta yi murmushi ta ce “Wannan zuciyar Mairo ce kike gaya mini, ba ta Junaid ba. Kin taba ganin inda
namiji zai yi ta wahala da mace da iyayenta babu gaira babu dalili? Idan kin ga kare na sunsunar takalmi,
wallahi dauka zai yi. Har yanzu ke yarinya ce da sauranki. In gaya miki gaskiya na hango miki abin da ke ba ki
hango ba, cikin kwayar idon Junaidu.
Na hango miki abubuwa da dama, wadanda a shekarunki bazaki iya hango su ba. Babu komai cikin kwayar
idanunsa sai sonki da kaunarki, ke ma sai dai ki karyata zuciyarki da gan-gan, amma kina son Junaidu. Adadin
soyayyarka da mutum, yana da nasaba da yawan ambatonsa. To gaya min tun haduwarki da shi, wace rana ce
ba ki ambace shi ba?
Ni ba wani abu na ce ba, kawai ina gano miki dacewar hakan. Ina gano miki mutumin da zai rike ki da kauna ta
gaskiya, har zuwa karshen rayuwarki. Wanda kuma shi ne wannan Junaidun. Duk runtsi, duk wahala da
tsanani kada ki bari a rabaku. Zan iya rantsuwa in fada miki Junaidu sonki yake yi, idan kuma ba ki yarda ba, ki
jira LOKACI ya fada miki…….”
Cikin gundura da zancen ta ce “Na ji Inna, amma don Allah don Annabi ki rufa min asiri kada ki ce wai ya aure
ni, ai kin zubar min da aji, sai ka ce wata wadda kike neman yadda za ki yi da ita? Ni kam gare ni har gobe
Uncle Junaidu Yayana ne”.
Inna ta yi murmushi ta ce “Neman yarda zan alkinta rayuwarki nake yi mana, ga shi kuma ina hango inda za a
alkinta min ke”.
Ta ce (kamar ta yi kuka), “Ni dai don Allah Inna ki bari……..”.
Ta ce “Na bari, amma wata rana idan kina shayar da jaririn Junaidu, ki tuna na gaya miki Junaidu na sonki, tun
ba ki mallaki hankalin kanki ba”.
Ta yi narai-narai da fuska, ta ce “Yanzu don Allah Inna ba zaki bar zancen nan ba?”
Ta ce “Na bari”.
Ashe karshen hirar tasu ke nan. Inna Hure ta tako da asubahi cikin dafa bango domin yin alwala, ta zo gittawa
ta gefen da rijiyarsu ta ke, santsin cabalbalin gindin rijiyar ya kwashe ta ga kafafun babu karfi, ta zame ta baya
sai ji kake cindummmm….! Ta fada rijiyar ita da butar da ke hannunta.
Mairo wadda ba ta yi barci ba tun daren jiya, tana tunanin zancen Inna akan Uncle Junaidu, ta kasa yakice
al’amarin a zuciyarta. Haka kawai ta samu kanta da fatan ina ma ace zancen Inna ya tabbata gaskiya? Uncle
Junaidu ya so ta? Ita kuwa da wace irin sa’a zata yi a rayuwarta?
A farkon shekatun karatunta ba ta tantance wane ne Junaid ba, sai da girma da hankali suka fara game mata
jiki.
Uncle Junaidu na daya daga cikin irin mazan da suka yi karanci a wannan zamanin. Ta fannin sura, halayya da
kyawawan dabi’u.
Ta kasance ma’abociyar karance-karancen littattafan nobels’ na Turanci. Littattafan Shakespear, Wole
Soyinka, Zainab Alkali, Abubakar Gimba, Ama Ata Aidoo da mabiyansu babu wanda bata karanta ba. A duk
lokacin da ta ke karatun, takan rasa dalilin da yasa ta ke danganta al’amarin jaruman littafin da Uncle da ita
kanta. Ba tasan dalilin da yasa a duk lokacin da aka ambaci managarcin mutum mai kyawun sura ta ke cewa
cikin ranta, “Kaman Uncle Junaidu”.
Eh, Junaidu kyakkyawa ne, ma’abocin kwarjini, zati da kamala, wanda kwata-kwata bai dace da matsayin da
yake kai ba, wato malamin makaranta. Saidai da yake ance (ra’ayi riga ne)
Mutum ne da yasan mene ne ‘dressing’ wanda kuma kowanne irin kaya ke karbarsa, su dace da da zubin
halittarsa. Kai kace don shikadai aka kirkiresu. Junaidu idan ya shigo waje dole kasan ya shigo, sabida
kwarjininsa da cikar zati. Yana da fara’a amma yana da zucciya, abu kadan sai ya bata mishi rai, haka abu
kadan zaka yi ya wanke laifinka nan take daga zuciyar shi. Ba ta san me yasa ba, komai Uncle ya yi burge ta
yake koda kuwa ace fada ne yake mata. Ta sha tambayar kanta, anya za a samu mutum mai kirkin Junaidu? Ta
taba ce da Nabilah matar duk da Uncle ya aura ta caba.
Nabilah ta ce “Dalili?”
Sai ta dauko mata littafin da ke boye a bayanta, GENDER STUDIES (wani bangare ne na sociology mai
banbance jinsin maza da mata). Shafin da aka fasalta halittar maza masu gamsar da diya mace a shimfida,
kuma irin mazan da matansu ba sa iya rabuwa da su komi wulakancin da zasu yi masu. Tana jan layi-bayanlayi tana fassarawa Nabilah.
Ta kare tana murmushi, ta ce “Edactly Uncle ko?”
Nabilah ta kama baki cikin mamaki, ita karance-karancen Maryam ya fara ba ta tsoro. Yadda ta nakalci
harshen Turanci ko goyon Birtaniya dole ya sara mata. Ta ce “Ke dai wallahi shegen karance-karancenki sai ya
lalataki. Yanzu ina ke ina littafin ‘yan jami’a? Tukunna ma ina kika samo shi?”
Ta yi dariya cikin nishadi ta ce “A wurin Uncle na dauke rannan daya aikeni in kai mishi littattafi staff-room na
ganshi cikin lokarsa shi ma bai sani ba na dauke”.
Nabilah ta ce “To wallahi ki bar karanta sociology za ki hauka ce”.
Maryam ta ce “Da Uncle bai hauka ce ba? Ya gaya mini digirinsa ya yi shi ne kan sociology. (With first-class
honour) Nima insha Allahu abin da zan karanta kenan”.
Nabilah ta ce “Sai ki yi azama, me ake da abin da zai juyawa mutum tunaninsa zuwa na Yahudu da Nasara?”
Ta ce “Eh, idan kin amince da abin da suke fada ba? Ni dai ina so tunda Uncle shi ya karanta”.
Nabilah ta kyabe baki ta ce “Kya karaci gulmarki dai, kina son mai abin kina cewa abin kike so”.
Ta bude baki cikin mamakin Nabilah, ta suri bokiti ta yi waje tana yi mata dariya, tana cewa, “Ku gama
kumbiya-kumbiyar taku a yi candy mu zo Galadanchi mu kawo amarya….”.
Ta bi ta da duka ita kuwa ta falla da gudu.
To sai ga shi yau Inna ta fadi wani abu kwatankwacin na Nabilah. Ta yi ajiyar zuciya, ta ce a ranta “Shin ko dai
Nabila da Inna gaskiya suka fada ne? I fall in lobe with Uncle Junaidu? Neman tabbacin hakan abu ne mai
matukar wahala a kwawalwarta”.
Ta mike ta fito ganin shiru-shiru Inna ba ta dawo ba daga fita alwala har gari ya waye, gabanta ya soma
bugawa da sauri da sauri, cikin matsananciyar faduwar gaba. Ta duba gabas da yamma, kudu da arewa, babu
Inna babu alamarta.
Ta matsa kofar bayin ta kasa kunne babu motsin Inna. Cikin karfin hali da matsanancin firgici ta ce, “Inna kina
ciki ne?”
Shiru babu amsa, ta ce “Inna ki yi min gyaran murya idan ba za ki magana ba”.
Nan ma shiru, sai amsa kuwwar raunanniyar muryarta da ginin kasa ya dauka, ya dawo mata da abinta cikin
kunnuwanta. A lokacin ne ta ankara da zanin da ke daure a jikin Inna wanda karfen guga ya makale ya yage.
Ba ta son gasgata abin da kwakwalwarta ke son ankarar da ita. Ta matsa ga rijiyar ta leka jikinta babu inda ba
ya kyarma. Kafafuwan Inna ta gani a sama, maganar motsi kuwa babu shi a tare da su.
Sai ta yiwo waje da gudu tana ihu tana kururuwa a kawo mata agaji, kanta ko kallabi babu, kafarta babu
takalmi, hawaye shabe-shabe a idanunta. Abinki da jama’ar kauye, ma’abota hadin kai da taimakon junansu,
nan da nan gidan ya cika makil da dan Adam, makotansu da abokan arziki kowa yana ta Allahu Akbar! Hure
Allah Sarki!!
Nan da nan wasu samari majiya karfi suka hada doguwar igiya suka cilla, biyu suka kama hancin suka rike,
daya ya bi ya dauko Hure suka fiddo su.
Mairo ta daga ido ta ga wai yau Innarta ce wannan babu numfashi, ta tafi har abada ta barta. Innan da ta rage
mata a duk fadin duniya, ita ma ta tafi. Sai ta fadi, wuni guda cur ba tasan inda kanta yake ba.
***
F
arkawa ta yi ta samu kanta a gidan makociyarsu Karime. A lokacin har an yi wa Innar sallah, an kai ta
makwancinta. Mairo ta ja jiki ta takure wuri guda sai a lokacin kuka ya zo mata. Ta yi ta kuka kamar ranta zai
fita. Karime na ba ta baki tana rarrashinta. Ta ce, “Wannan ba shi ne karshen rayuwarki ba Mairo. ‘Ya’ya nawa
ne iyayensu suka mutu tun a wurin haihuwarsu, kuma sun rayu? Ki godewa Allah da Ya nufe ki da tashi tare
da su, kika san dadinsu. Ni kin ganni nan ban taba sanin uwata da ubana ba, cikina da wata biyar Babana ya
rasu, lokacin haihuwata uwata ta rasu, amma gani nan da nawa ‘ya’yan goma sha uku. Ina yi miki ta’aziyya
Allah Ya jikan Hure, mutumiyar kirki, mai alheri”.
Mairo ba ta fasa kukanta ba, addu’a ta ke Allah Ya dauki ranta ita ma ta huta, maraici na uwa da uba ba
karamin abu ba ne. Tunaninta shi ne, ina zata kuma samun mai kaunarta a duniya kamar iyayenta? Ina zata
je? Da wa zata zauna? Mene ne amfanin sauran rayuwarta? Ba ta da kowa ba ta da komi sai Allah, domin ta
fidda lissafin Habibu a zuciyarta. Ta samu kanta cikin kullatar Yaya Habibu, kullata mai tsanani. Ba ta ga ranar
da haihuwarsa tai wa iyayensu ba.
Karime ta shigo da dambun masara a kwano da ruwa a kofi, ta sa ta gaba lallai sai ta ci. Ta dauki loma ta kai
bakinta tamkar mai taunar madaci, haka ta ke taunar abincin. Ta tsame hannunta tana sharce wasu
dunkulallun hawaye da suka zubo mata. A lokacin ta tuna babban kuskurenta a rayuwa, ba ta yi wa Inna
addu’a ba.
Ta mike ta je ta dauro alwala ta zo waje mai tsabta a dakin Karime ta shimfida sallaya, ta suturce jikinta ta
tayar da sallah. Tana sallah hawayenta ba su bar ambaliya ba. Da ta idar ta bude Alkur’ani mai Tsarki ta shiga
karantawa Inna suratul Yasin da suratul Rahman ta rufe da (du’a’ul mutawaffa) tana addu’ar Ubangiji Ya yi
mata masauki da aljannah.
Ranar kwana uku da rasuwar Inna Hure ta tattaro duk ajiyarta kudin mota kawai ta barwa kanta, ta ba wa
Karime aka yiwa Inna sadakar gumba, waina da kosai. Mijin Karime da Dagacin Gurin-Gawa suka zo suka
same ta har dakin Karime suka fara da yi mata ta’aziyyah, sanan Dagaci ya ce sun zo ne su kai ta gidan kanin
mahaifinta su damkata a hannunsa, wannan ita ce amanar da za su sauke.
Hankalin Mairo ya tashi, zancen Inna ya dawo mata sabo tar! A kwanyarta, “Wata kila abin da nake gudu ne
dole sai ya faru… Zaman Mairo da iyalan Abbas”.
Ta sunkuyar da kai tana kuka, ta ki ba su amsa, Malam Tanimu ya ce “Hakuri za ki yi Mairo, mutuwa riga ce
akan kowa, tafiyarki birni ya zama dole, domin ba ki da wanda ya fi shi. Sannan Abbas mutum ne mai
ZUMUNCI ki dubi yadda ya rayu yana kyautatawa mahaifinki. Ina da yakinin zai rike ki da amana tamkar
mahaifinki, har zuwa sanda zai miki aure”.
Sai ta mike cikin karfin zuciya, ta yafa mayafinta ta sa takalminta. Karime ta rakata gidansu tana hada kayanta
tana kuka.
Ta tattara zannuwan Inna da kayayyakinta ta sa a wata tsohuwar akwatun karfe ta rufe, ta tura karkashin
gadon bononta. Ta tattara ‘yan kudaden Innar irin wanda Junaidu ke ba ta ne a duk zuwan da ya yi, da kudin
motar da ta warewa kanta duka ta zuba cikin jakarta ta makaranta. Suka fito Karime ta datse dakin da kwado,
tana tafe tana waiwayen dakunansu da madafinsu da ta ke jin tana yi masu kallon karshe ne, wasu hawayen
suka zubo.
Tana bayan motar Dagaci wata (mitsubishi) mai hayaniyar tsiya, in banda karar injina da salansa ba abin da
kake ji, shi da Malam Tanimu suna gaba. Ta kama jikinta tsan-tsan sabida gwaruwar da kanta ke yi da jikin
motar sabida rashin kyawun birjin Gurin Gawa. Shi da Malam Tanimu suna ta hirarsu ba abin da ya dame su,
ita kuwa sake-saken da ta ke yi cikin ranta na abin da zata je ta tarar a gidan Baffanta da ‘ya’yansa marasa
adadi da rashin tarbiyya ta ke yi.
Sai da suka hau titin gidan zoo sosai sannan motar ta daidaita, tafi-tafi har suka iso gidan Sarki suka billa
Yakasai ta nan.
Kugin karshe da kwarababbiyar motar ta yi a kofar gidan Alhaji Abbas Maigoro ne. Gida ne ginin siminti mai
dakali hagu da dama da manyan zaure irin ginin masu kudin da. Yara kanana da samari suna ta shige da ficen
su. Gabanta ne ya soma dukan uku-uku sabida haka ta yi hamzarin jan Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un har ta
samu bugun zuciyarta ya yi dai-dai.
Suka ce ta shiga cikin gidan ta turo musu Alhajin suka fito kan dakalin gidan suka zauna. Cikin sanyin jiki Mairo
ta fito tana tafe tamkar macijiya sulu-sulu abin tausayi. Ta yi sallama a tsakar gidan, Uwargidan Hajiya Habiba
ta amsa, wadda ke tukin tuwon dare a bakin murhu.
Ta karasa inda ta ke ta tsugunna tana gaishe ta cikin nutsuwa. Ta amsa da alama ba ta gane ta ba, ta ce
“Yammata daga ina? Ban gane fuskar ba”.
Ta dukar da kai ta ce, “Gurin-Gawa”.
Habiba ta kalle ta sosai na ‘yan dakikai, nan da nan fara’ar da ke fuskarta ta bace. Ta juya ta ci gaba da tukin
tuwonta. Cikin halin ko’in’kula ta ce
“Auyo! Ce min zaki yi MAIRON HURE shalelen HURE, sai yau tasan mu mutane ne da ta turo ki ki gaishe mu?
Ce nake har jinya kuka yi anan ta tsayin watanni ba ku san hanyar gidanmu ba, sai dai kullum mu tuka mu ba
ku? Ince ko yanzun ma ba tasan kin zo ba kada mu moran mata ke?”
Mairo ta share hawayen idanunta, ta ce “Tare muke da baki suna zaure, sun ce suna son ganin Alhajin ne”.
Sai da ta mula ta ce “Ba ya nan, yana kasuwa, amma yana gab da dawowa”.
Ta taso sumui-sumui ta fito dakalin gidan ta fadawa su Malam Tanimu sakon Hajiyar.
Ta ci gaba da tsayuwa a zauren ba ta koma cikin gidan ba. Malam Tanimu ya ce “Bude motar ki kwaso kayanki
mana ki shiga da su?”
Jikinta ya yi sanyi lakwas ko numfashi da kyar ta ke shaka, ta ce “A’a, mu dai jira Baffan”.
Dagaci ya yi nazarinta yana taunar goronsa, ya ce “Mairo ki saki jikinki, nan fa gidanku ne, gidan ubanki ne”.
A ranta ta ce “Kayya Uba guda daya ne, na tabbata na rasa nawa”.
Suna nan zaune ita kuma tana tsaye daga cikin zauren kusan rabin awa, Ladidi diyar Alhaji Abbas wadda ta ke
kusan tsararta ta dawo daga unguwa rike da hannun kanwarta Rahma ta ci kwalliya kamar me? Tana yafe da
wani dan gyale mai kama da abin tatar koko, ta daga ido tana kallon Mairo kana ta kyabe baki ta ce “Ah! Yau
wace rana?”
Ta yi murmushi, ta ce “Ladidi ke nan, kuna lafiya?”
Ta sake kyabe bakin (ga alama al’adarta ne yin hakan a duk sanda zata yi magana), wanda kwata-kwata ba ya
mata kyau, don ko daya ba ta da kyawun fuska. Ta ce “Gidan namu ne bai ishe ki shiga ba da zaki tsaya a
zaure, ko kuwa wani sabon salon gulmar ne Hure ta koya miki, ta ce idan kin zo ki yi mana, don Baba ya ce
mun wulakanta ki?”
Ta bude baki tana kallonta kawai cikin mamaki, ba ta ce komai ba, ta yi ciki sai ta danne zuciyarta ta bi ta a
baya.
Suna shiga Habiba ta ce “Ai na dauka tafiya ta yi babu sallama, saboda uban nata ba ya nan”.
Ta sake kyabe baki, ta ce “Can soro na ganta a tsaye, salon ta ja mana magana wajen Baba”.
Amarya Aunty Hajara ta yane labulenta jin cece kucensu, ta ce “Wa nake gani kamar ‘yar gidan Hure?”
Habiba ta ce “Ke ma dai kya fada, ai ni na dauka batan kai ta yo”.
Hajara ta saki labulenta tana cewa, “Allah Sarki! Alhajin yana kan hanya don nasan dai ba wajenmu kika zo
ba”.
Mairo dai na tsaye tamkar mutum-mutumi. Tana mamakin rashin mutumci irin na matan Alhaji Abbas.
Babban mamakinta daga Habiba har Hajara babu wadda ta ce ta shigo daki.
Haka Ladidi ta shige dakinsu na ‘yammata ba ta kara bi ta kan Mairo ba. Ta ci gaba da tsayuwa sororo!
Wannan yaro ya shiga, wannan ya fita duk ba su santa ba. Wannan ita ce rayuwar da Innarta ta ke guje mata
ke nan ta matan birni marasa karah da rayuwar kowa yai ta kansa, ko kuwa abin nan da Bahaushe ke cewa,
kowa tasa ta fishshe shi.Sai ta jiyo muryar Alhajin yana gaisawa da su Dagaci, ta yi ajiyar zuciya. Sun dade
suna magana tana jiyo tashin sautin Alhaji Abbas yana ta kiran Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, ita ma sai
hawayen ya zubo mata. Can anjima ya shigo dauke da jakar kayanta da kansa, nan ya ganta tsaye a tsakar
gida tana share hawaye.
Ya ce “Sannu kinji Mairo, sannu Allah Ya jikan Bedi da Hure, Allah Ya ba mu dangana mu kuma Ya kyautata
namu karshen. Ya ya zaki tsaya a tsakar gida kamar ba gidanku ba? Shige mu je wajen Habiba”.
Ta bi shi a baya. Ya shiga dakin yana cewa, “Habiba ‘yarki ta zo kin barta a tsakar gida, ko ba ki ganeta ba ne?”
Daga can kuryar daki ta amsa “A’ah ‘yar Hure dai, don sanda na ce da uwarta ta ba ni na hada da nawa na rike
cewa ta yi ba ita ba mu. Sai yanzu da ta zama budurwa gab gidan miji zata zo min? Wato na tattara jeren
dakina na yi mata kayan aure?”
Ya yi murmushi, ya ce “Ina abin ya ke? Wannan jeren naki ko dari biyu bazan iya sayenshi ba, sai ka ce yau
kika fara aurar da ‘ya’ya? Cewa nake ‘ya’yan yayyaenki duk kekika aurar dasu batareda kin taba kayan jeren
naki ba?”
Ta fito tana daura kallabinta, ta ce “Can dai, akai gaba. Da din ma da na ce a bani rashin godiyar Allah ne,
yanzu kuwa ni ma sun yi min yawa, neman kai nake da su”.
Ya nunawa Mairo kujera ya ce ta zauna, amma ita sai ta zame ta zauna akan leda tana gayar da Baban. Ya
kwalawa Hajara kira ta shigo tana tambayar “Lafiya? Bashi na ci ban biya ba ne?”
Ya ce “Duk ku zauna”. Sannan ya maida walwalar da ke fuskarsa ya ce “Hajara, Habiba, kowacce ta amsa da
“Na’am”.
Ya nuna Mairo wadda kanta ke sunkuye, ya ce “Wannan wace ce?”
Suka ce “Mairo”.
Ya ce “To madallah, tunda kun santa, wane ne ubanta?”
Suka ce “Bedi”.
Ya ce “Bedi wane ne a gare ni?”
Suka ce “Yayanka ne”.
Ya ce “A yau babu Bedi, wadda kuke gaba da ita itama babu ita a duniyar, wato Hure. Sabida haka duk
duniyar nan Mairo ba ta da inda zata je sai gidana, tunda ba aure aka yi mata ba, saboda haka ga amana nan
a hannunku, ku rike ta yadda za ku rike ‘ya’yanku har zuwa sanda Allah Zai kawo mata mijin aure.
Wannan yarinya marainiya ce, don haka wadda duk ta zalunce ta cikinku Allah ba zai barta ba. Idan ta yi ba
dai-dai ba ku kwaba mata, ku sa ido akan tarbiyyarta kamar yadda zaku yi wa ‘ya’yan cikinku. Ke kuma Mairo
wadannan iyayenki ne, ba ki da wanda ya fi su, don haka ki yi musu biyayyar da zaki yi wa iyayenki. Ki kai
kayanki dakin Ladidi ku zauna tare, Allah Ya jikan Bedi da Hure”.
Cikin zuciyarta ta ce “Ameen”. Hawaye suka kawo mata zarya.
Habiba ta ce “Dakata Alhaji, amanar maraya ka ce ka bani ko? Idan na ci Allah Ya ci tawa, to ban karba ba,
balle ace na ci amana. Sai dai zama na kinzo-na-zo kowa zaman kansa yake. Ita zaman uba ni zaman miji”.
Hajara ma ta ce “Ato! Gaskiyarki Yaya, ni ma abin da zan ce kenan sabida rikon maraya wuya gare shi. Da idan
ba wanda ka haifa ba ko goyonsa zaka rika yi kullum ba zaka fita ba. Dubi Mairo gansamemiyar budurwa ce
da tasan abin da ta ke yi. Don haka ta yi wa kanta fada, kada inyi ace don ba ‘yata ba ce”.
Suka karkade zannuwansu suka yi daka. Daga Mairo har Baffanta kowanne gwiwa a salube, ya dade kai a
duke, haka ita ma. Daga bisani ya ce,
“Ki yi hakuri Mairo, na rasa me ke tsakanin Hure da su Habiba, ki rabu da su ki yi rayuwarki cikin walwala, duk
wata matsalarki ki yi kokarin sanar da ni. Ya ya batun makaranta kuma?”
Ta ce “Nan da kwana uku nake son komawa idan na natsa”.
Ya ce “To gaya min abubuwan da kike da bukata gobe sai na sayo miki”.
Ta gaya mishi yana rubutawa, ya sanya takardar cikin aljihun gaban rigarshi ya mike ya ce, “Zo dauko kayan
na nuna miki dakin Ladidin”. Ta sungumi jaka ta bi shi ya nuna mata dakin ya fita.
***
MAIRO A GIDAN BAFFANTA
M
airo ta yi zugum ta zubawa jakar kayanta ido cike da tunanin yadda za ta yi rayuwa a wannan gida. A karshe ta
tattara komi ta mikawa Allah. Ta ji tausayin Baffanta Alh. Abbas da bai yi dacen matan aure ba. Da ganin shi
ba shi da katabus a gidan.
Ba ta gama tunaninta ba Ladidi ta yane labulen dakin ta shigo fuskar nan a turbune, kamar wadda aka yi wa
shegen duka. Wannan fushi ba na komai ba ne, sai don hadata da Mairo daki daya da Baban ya yi, ba ta kuma
da yadda zata yi.
Mairo ba ta kulata ba, ta maida kai ga littafin da ke hannunta tana karantawa.
Allah-Allah ta ke litinin ta zo ta koma makaranta, wannan ne kadai ta ke ji zai sanyaya mata zuciya. Washegari
tun bayan da ta yi sallar asuba ba ta koma barci ba, ci gaba ta yi da lazimi har gari ya soma haske. Ta mike ta
ninke sallayar ta fito tsakar gida ta tarar da tulin wanke-wanke a gindin famfo, ta nade zaninta ta ja kujera ta
zauna ta soma wanke kwanukan, duk gidan ba wanda ya fito, ta gama ta share tsakar gidan tas! Dai-dai
lokacin Habiba ta fito zata yi alwala ta ganta tana sharar ga kwanukan ta wanke mata, ranta ya yi dadi, ta dan
saki fuska, ta ce “Ah’ah Mairo daga zuwanki? Ai aikin gidan nan ya fi karfinki, kada ki dorawa kanki abinda ba
zaki iya ba”.
Ta yi murmushi, ta ce “Ai babu komai Mama, abin da jibi zan koma makaranta har ina aikin ya ke?”
Ta wuce bayan gida ranta ya yi dan sanyi da Mairo, tunda da alamun za a yi zaman lafiya da ita, tunda ba ta
da kiwa.
Da ta gama ta yi wanka, ta shafa mai ta sanya atamfa nichem wad, ta ci gaba da karance-karancenta. Ladidi ta
shigo musu da kwanon koko da kosai, ta debi nata ta turawa Mairo ragowar ba ta ce ko uffan ba.
Mairo ta rasa wace irin yarinya ce Ladidi kamar ita ba jininta ba ce. Ta ga ba ta da alamun yi mata magana
kamar ba daki daya suka kwana ba. Wannan sam ba ya daga cikin tsarin musulunci, don haka ita ta sauke kai
ta ce “Mun kwana lafiya Ladidi?”
A lalace ta ce “Lafiya lau”.
Da haka Mairo ta ja bakinta ta yi shiru, ita kuma Ladidi ta yi wanka ta fice daga gidan.
Da yamma Baba ya dawo, har dakin ya bi ta, ya same ta da ledoji niki-niki ya yo mata sayayyar komawa
makaranta. Ta yi hamzarin mikewa ta karbe shi, ya ce “Duba ki gani, idan da abin da babu ki gaya min na
koma na karo”.
Tana bude kayan tana dubawa ta ce, “A’ah komai ya yi Baffa, madalla na gode, Allah Ya kara budi”.
Ya fita yana cewa “Ki dai saki jikinki a gidanku, don Allah Mairo”.
Tana kokarin hada kayan don ta maida su cikin ledarsu. Tsulum! Aunty Hajara ta bankado labulen dakin ta
shigo. Idanunta akan kayan ta kama haba ta ce “Iye! Gata maganinka Allah! Mu yaushe aka taba saya mana
kayan masarufi haka a gidan nan? To wallahi ba zata sabu ba, biyu zan raba su na dauki rabi”.
Ta soma kasa kayan bayan ta zazzage su daga ledojinsu. Ta kwashe rabi ta zuba a leda guda ta yi waje da su,
ko kunya babu.
Mairo na zaune tana kallon ikon Allah, ashe ba ta gama mamaki ba, don Habiba ganin Hajara ta fito da kaya
fal leda ita ma ta zabura ta yi dakin, ta ce “Mairo miko kayan nan a cire na Ladidi”.
Ba musu Mairo ta mika mata buhun baccon, ta kwashe na arzikin su kayan shayi da sabulai, ta tura mata
sauran da ko sati ba zasu yi mata ba. Ita ma ta fice tana fadin “Gara mu ci arzikin albarkacinki, don idan namu
‘ya’yan ne ai ba za a siya musu haka ba, ita ma Ladidi ta sha shayi ta ji ya dandanonsa ya ke”.
Da ta ga idan ta biyewa wadannan mutanen za su sanyata kuka, sabida rashin imaninsu, sai ta dauko littafin
addu’o’i na Hisnul Muslim ta soma karantawa idanuwanta cike taf da kwallah. Wadannan su ne ‘MATAN
BIRNI’ ke nan.
Wato duk matan birni ba su da kirki, daga na masu kudinsu har talakawansu. Al’ummar kauye ba haka suke
ba, mutane ne masu kara da karimci. Matan birni dansu shi ne nasu, dan wani kuma ko oho! Ta yarfe
hawayen idanunta.
Wajejen karfe sha biyu na rana, Hajara ta kwaso jibgin wankin yaranta ta jibge a gindin famfo, ta kwalawa
Mairo kira wadda wani matsiyacin barci ya soma fizga kadan-kadan. Nan da nan ta gyagije ta amsa, ta fito “Ga
kayan kannenki nan ki taimaka ki wanke musu kan la’asar, saura ki zauna kailula har uban naki ya dawo ya ce
don me na saki aiki”.
Ba musu Mairo ta amsa da “Zan yi sauri Aunty Hajara”.
Ta soma dirzar dukunkunannun kayan wanda kamin ta wanke wando daya ya fita, sai an yi minti ashirin
sabida tsabar daudar da suka yi. Don haka wankin ya kai ta har karfe hudu. A lokacin an gama abincin rana,
kowa ya ci nasa amma banda ita, sai da ta gama gaba daya, bayanta ya amsa, kugunta ya rike, ‘yan yatsunta
suka shiga zafi da radadi sabida ba ta taba yin wanki irin wannan ba.
Ta dawo daki ta kwanta, Habiba ta aiko dan autanta Hadi da filet din dafadukar shinkafa wadda duk ta bushe
babu kuma alamun zata toshe mata dunkulalliyar yunwar da ke cinta.
Ta gabatar da sallar azhar da la’asar a tare, sannan ta zauna tana cin shinkafar. Dai-dai lokacin Baba ya yi
sallama ya shigo rike da kwanon samira, ya ce “Amshi nan Mairo ki kara, idan kuma kin koshi ki ajiye zuwa
anjima kafin a gama na dare idan kinji yunwa sai ki ci”.
Cike da tausayin Baffanta mai son faranta mata, Mairo ta karbi kwanon samirar, hakan ya yi dai-dai da
bayyanar Habiba a dakin tana huci kamar macijiya, ta ce
“Wannan salon da zaka fito da shi bazan yi na’am da shi ba. Yazan bai wa yarinya abinci kamar yadda na
baiwa kowa a gidan nan amma ka dauko naka ka kawo mata, cewa ta yi ba ta koshi ba, ko kuwa wani sabon
kinibibin ne don a zage ni?”
Ya ce “Idan ma kinibibin ne, ni ne mai kinibibin ba ita ba, tunda dai ni na dauko na kawo mata har inda ta ke,
ba zuwa ta yi wajena ta roka ba”.
Ta sa hannu ta dauke na filet din, ta ce “Wallahi ba zata ci rabon mutum biyu ba, kai dai da ka zabi ka zauna
da yunwar kai ta zama, amma na dauke wannan”.
Ko kulata bai yi ba, ya sa kai ya fice daga dakin, ta wani fannin kuma kunyar Mairon ya ji.
Mairo ba ta saba ganin irin wannan rayuwar ta matan birni ba. Wadanda suka dauki miji, ba a bakin komai ba.
A matsayinta na marubuciya ‘articles’ a take ta ji tana son yin rubutu akan mata irin Habiba da Hajara.
Wannan ne ya tuna mata da mutum ma fi muhimmanci a gare ta a yanzu (Uncle Junaidu). Ta yi ajiyar zuciya
mai nauyi, a take ta dauko full-scap da biro ta soma rubutun da tasan Uncle zai yaba da shi.
A tsayin kwanaki ukun da ta yi gidan Baffanta, ta ga rashin mutumci da rashin darajja miji kala-kala wajen
matan Baffanta. Sannan ta ga rashin tarbiyya da rashin mafadi wurin ‘ya’yan su, hart a soma yiwa kanta fatan
kada Allah Ya sa ta yi aure a birni. Gara ta koma can Gurin-Gawa ta yi aurenta kada ita ma ta zamo daya daga
cikin matan birni, wadanda ba su dauki mijinsu da ‘yan uwansa a bakin komai ba.
Wannan tunanin da ta yi, yasa ta yi murmushi. To idan ma auren zata yi wa zata aura? Babu wanda ya taba
cewa yana sonta. Babu wanda ta taba gani ta ji tana so a duniya, ba ya ga iyayenta da Yaya Habibu. Wata irin
faduwar gaba ta same ta, tare da jin wani dal-dal-dal a cikin kirjinta, gami da tashin da tsigar jikinta ta yi, duk
a lokaci daya. A lokacin da zuciyarta ta ambato mata UNCLE JUNAIDU. Wani irin matsayi ne da shi mai GIRMA
a zuciyarta, wanda a duk lokacin da tuninsa ya fado mata, ta ke tsintar kanta a cikin wannan yanayin.
Mu biyo Mairo da Junaidunta a littafin na biyu, wanda tare suke da dan uwansa.,
Maman SAFAH da MARWAH ce…….!
Ku nemi littafin FROM MY KITCHEN na HADIZA UMAR DOGON DAJI (Mrs. Jelani Aliyu) don samun kayatattun
girke-girke na zamani dana gargajiya da suka sha banban da sauran littattafan girke-girken da kuka saba
karantawa. Tuna sunan FROM MY KITCHEN (Daga Kichin Dina).(2)A
Ranar Litinin. Tun asuba da Mairo ta tashi ta yi sallah ba ta koma bacci ba, ruwa ta taro a famfo ta yi wanka ta
shafa mai, ta sanya uniform dinta ta shirya tsaf ta zauna jiran fitowar Baffa.
Ba shi ya fito ba sai karfe takwas dai-dai na safe. Ya yane labulen dakin su Mairo cikin sallama ya ce “Ya ya kin
gama kimtsawa mu tafi?”
Ta ce “Na gama Baffa tun dazu”.
Ya sa hannu ya daukar mata katuwar jakar, ita kuma ta dauki karamar suka fito. Ta leka dakin Habiba da
Hajara ta yi musu sallama suka amsa duk cikin yanayi daya, wato a yatsine, don ita Habiba ba ta so wannan
komawa makarantan na Mairo ba, so ta ke abar musu ita tai ta yi musu bauta, don Ladidi ko za a kashe ta ba
zata yi musu bautar da Mairo ta yi musu ba cikin kwanaki ukun da ta yi tare da su ba.
Shi kuwa Baffa Allah-Allah yake ya maida Mairo makaranta don ta huta da kwarzabar su. Idan ya tuno daga
wannan zangon Mairo ta gama makaranta hankalinsa tashi ya ke. Ya soma tunanin da ta gama makaranta
idan ta samu masoyi zai ganganda ya yi mata aure, idan ma ba ta samu ba ko cikin mutanensa ya nemi wani
wanda ya yaba da hankalinsa ya ba shi ita, shi dai ta bar gaban su Habiba, sai hankalinshi ya kwanta.
Ya bude boot ya zuba kayan, ita ma ta sanya jakar hannunta. Ya bude kofar wajen mai zaman banza ta shiga
ta zauna, sannan ya zagaya shi ma ya shiga ya tayar da motar suka mika kan titi.
Karfe goma dai-dai suna cikin Minjibir, duk wasu shige da fice na dawowar dalibi Mairo da Baffanta sun
kammala cikin dan lokaci. Suka yi sallama da Baffan ya kada kan motarshi ya tafi, ita kuma ta nufi ajinsu.
Tun daga nesa ta hango Uncle yana rubutu akan allo, wani irin dadi da farin ciki suka ziyarci zuciyarta. Ji ta yi
tamkar Baba da Innanta ne suka dawo.
Daga can mazauninsu Nabilah ta hango ta, ta kuwa sheko da gudu ta rungume ta, ba tare da la’akari da cewa
akwai malami a cikin ajinsu ba. Ya dakatar da rubutun ya juyo, juyowar da ta ke nufin al’amura da dama a
gare su a wannan ranar.
Mairo ba ta iya ta hada ido da Uncle ba saboda matsanancin kwarjinin da ya yi mata a yau, shi kuma kokari
yake ya kalli cikin kwayar idanunta cike da tuhuma da tarin laifuffukanta gareshi. Ya mannawa Nabilah harara
ba shiri ta koma cikin nutsuwarta, kai tsaye Mairo ta wuce wurin zamansu shi kuma ya cigaba da bada darasi
cikin wani sabon kuzari da nishadi gami da wani karfin gwiwa da ya same shi duk a lokaci daya.
Aka fita break amma ita da Nabilah ba su fita ba, sun nutsa hirar bayan rabo. Nabilah ta ce “Yaya Inna? Kusan
kullum sai na yi mafarkinku Mairo, tun bayan rasuwar Baba nake jin tausayin Inna, ina gayawa Mamana da
Daddy. Dama idan kika yi sati baki dawo makaranta ba zan bi sawunki ko makaranta ta yi min izini ko ba ta yi
ba”.
Idanun Mairo suka kawo kwallah, ta ce “Innar ma na rasata Nabilah … Ba ni da kowa a yanzu sai Baffana sai
Allah da Ya halicce ni. Na zama marainiya Nabilah, ba uwa ba uba…….”Hawaye suka kece mata, ta dukar da
kanta cikin cinyoyinta ta ci gaba da kuka.
Nabilah ma sai ta sa kuka, tana tuna Inna da kirkin da ta yi mata. Sun dauki mintuna suna kuka, kamar wasu
kananan yara. Ba su san yaushe Uncle ya shigo ba, har ya tsaya a kansu. Ya sanya hannu ya kwankwasa desk
din da suke sunkuye. Duk hirarrakin da suke yi ya ji su, ya rasa inda zai sa kansa da tausayin Mairo. Ba
kankanin abu ne ke sanya Junaidu kuka ba, amma a yau ya ce Maryama I cannot control my tears………..”Suka
dago ido suka dube shi cikin ido, Mairo da Junaid ke kallon juna, irin kallon da ba su taba yi a rayuwarsu ba.
Wani muhimmin al’amari na samun muhalli cikin kwayar idanunsu. Nabilah sai ta bude baki, galala! Tana
kallonsu, tana cewa cikin ranta “A yau dai, dole Mairo ta yarda Uncle Junaid yana sonta……..”.
Mairo kwana ta yi ba ta yi barci ba, baya ga dacin mutuwar iyayenta da ya dawo mata sabo fil, sai kuma
SOYAYYAR Junaid da ke dawainiyya da zuciyarta, amma ta kasa ganewa, sabida kuruciya da wauta. Ga dai
zahiri al’amarin ya sauya, amma ta sanya kafa tana takewa da gan-gan.
A ganinta mai Junaid zai ci da ‘yar kauye kamarta? Sai dai ta ce zuciyarta na yaudararta, tunda shi din bai furta
ba. To ita ma ba zata taba yarda da tunaninta ba.
Shirye-shiryen jarrabawar fita ya kankama. A wannan dan tsukin Uncle ya takura musu matuka da karatu,
musamman akan lissafi (mathematics) da Ingilishi (English). Burinsa kawai Mairo ta lashe dukkan takardunta.
Ta gama makaranta with flying colours’, ta samu gurbi a babbar makaranta, ta yi karatun da zata dogara da
kanta cikin kowanne hali. Idan hakan ta faru to shi kam Alhamdu lillahi… Ya sauke nauyin alkawarin da ya
daukar wa Malam Bedi, sannan ne yake jin zai fallasa mata soyayyar shi, don haka wannan ba lokaci ne da ya
dace ya fallasa asirtacciyar soyayyarsa ga Mairo ba. Ya manta masu iya magana sun ce “A BARI YA HUCE… Shi
ke kawo da rabon wani.
Ba ta da abin da zata ce da Uncle Junaidu sai godiya, domin da taimakonshi da kwarin gwiwar da ta ke samu
daga gare shi ne ta zana jarrabawar Jamb, Waec da Neco cikin kwanciyar hankali, tamkar ba jarrabawa ta
zana ba, sabida yadda komi ya zo mata da sauki. Sai dai kuma wannan gama jarrabawar na nufin al’amura da
dama cikin rayuwarta. Rabuwa da UNCLE JUNAIDU? Wani muhimmin al’amari ne da ke cinta a zuci, da zuciyar
ba zata iya jurewa ba, da harshe ba zai iya bayyanawa ba. Ina ma Uncle zai ce yana sonta ya aure ta? Ya
rabata da rayuwar maraicin da zata je ta fada a gidan Baffanta?
Hawaye suka ciko idanunta. A karo na farko da zuciyarta ta kawo shawarar ta nemi Uncle ta roke shi ya
aureta, ya tserar da ita daga rayuwar kunci da zata je ta fada, ko da ba ya sonta.
Ta shiga neman Uncle cikin makaranta, lungu-lungu, sako-sako, abun kamar wasa ko mai kama da Uncle
babu. Tuni dalibai sun soma tafiya, don duk wacce ta fito daga last paper daukar kayanta ta ke ta tafi, bayan
anyi sallama da kawaye da abokan arziki. Tana tsaye nan cikin tashin hankali Nabilah ta iskota,
“Ga can Baffanki ya zo daukarki yana ta aike a nemo mishi ke”.
Hankalinta ya kara tashi da ta tabbatar a yau zata tafi ne, tafiya ta har abada daga Minjibir, ba tare da ta yi
sallama da Uncle ba, wani mutum daga cikin mutane biyu da ke ba ta farin ciki da buri (hope) a cikin
rayuwarta.
Tabbas yau ya sauke nauyin alkawarin da ya yiwa mahaifinta. Ta kammala makaranta cike da kyakkyawan
zaton samun nasara. Muhimmin al’amarin da ke dawainiya da zuciyarta akan Uncle, ta ke so ta sauke, amma
babu Uncle a cikin Minjibir, babu alamarsa.
Sai ta sa fuskarta cikin tafukanta ta soma shesshekar kuka. Nabilah ta rungume ta suka ci gaba da kukan tare,
sai dai ita Nabilah ba ta san hakikanin dalilin kukan Mairo ba.
Ita kuka ta ke na kewa da rabuwa da Maironta, yayin da Mairo ke kuka na tausayawa rayuwarta. Ta kullaci
Uncle mummunar kullata, (irin kullatar data yiwa Habibu) ta tuhume shi da YAUDARA da wasa da rayuwarta.
Ba tasan inda za ta ganshi ba, ta gaya mishi shi kadai zuciya da ruhinta ke so. Ya taimake ta ya aure ta koda BA
YA SONTA. Shi kadai ne namijin da ta ke jin zata iya aure a rayuwarta. Shi kadai ne ta ke jin zai kula da
rayuwarta a bayan idon Baba da Inna. Shi kadai ne ta ke kalla ta ji shi kamar Yaya Habibu. Yau shekaru dai-dai
har shidda dai-dai da rana daya zuciyarta ba ta taba hutawa da kaunarshi ba.
A da kam ba ta gane ba, amma yanzu ta yarda ta amince da mahaukaciyar soyayyar da ta ke yi wa Uncle
Junaidu. A yau da ta yanke shawarar fada masa don su tallafi rayuwar juna ta neme shi ta rasa.
*****
K
arfe hudu dai-dai na yammacin ranar ta litinin suka iso gida, inda direban su Nabilah da ke biye da su don ya
ga gidan ya juya da Nabilah, da alkawarin bayan sati zata zo su je da Mairo gidansu, don ba ta taba zuwa ba.
Tun daga soro Mairo ta soma cin karo da kwanuka, da busasshiyar miyar kuka a jiki. Gabanta ya ci gaba da
faduwa don ta tabbatar ita da rayuwar farin ciki, sun yi hannun riga ke nan. Ta fado cikin wata sabuwar
rayuwa ta MARAICI, wadda Innarta ta ke jiye mata. Ta tabbata Inna tasan rashin kirki na matan Alhaji Abbas
shi yasa a lokacin rayuwarta ta ki yarda ta zauna da su. Mai za a yi da hali irin na Hajara da Habiba? Sai Allah
Ya kyauta.
Karatu dai an kare shi, yanzu zama ne za a yi na din-din-din. Kowacce waina za a toya? To bari mu bi Mairo da
iyayen rikon nata mu gani.
Habiba na daki lokacin da suka shiga, sai Hajara ce a tsakar gida tana tankaden garin tuwo. Baffa ne a gaba
rike da jakar mairo, ita kuma ta biyo bayansa rike da wata jakar.
Hajara ta amsa musu sallama fuskarta ba yabo ba fallasa. Bayan haka ba ta kara tofawa ba. Baffa cike da
takaici ya ce “Hajara baki ga ‘yar taki ba ne, ko sannu da zuwa babu? Ai ba a haka”.
Ta cira kai ta jefe shi da harara, “Cewa za ka yi tashi ki yi tsalle ‘yar gaban goshina ta dawo, ba sannu da zuwa
ba”.
Jin cece-kucensu sai Habiba ta leko. Ita kam tayi fara’a ta ce “Ah! ‘Yan makaranta an dawo? Lale-lale”. Ko ba
komai ta samu jakar da zata yi ta yi mata bauta.
A dakinsu ta cimma Ladidi ta yi dai-dai sai sharar barci ta ke, dakin kaca-kaca ko’ina kayan Ladidi ne a watse,
nan pant, can brazier dukun-dukun da su. Ba ta ga inda zata dosana duwawunta ba a dakin, don haka ta aje
jaka ta soma tattara mata shirgin waje guda ta gyare dakin tsaf ta share ta kwashe ta zubar.
Ta gabatar da sallar azahar da la’asar da suka wuce ta, ta dauko karamin Alkur’aninta ta soma tilawa. Ko aya
biyar ba ta yi ba cikin suratul Ma’idah, Hajara ta kwalla mata kira. Ta rufe Alkur’anin ta ajiye mayafi ta fita. Ta
nuna mata tulin wanke-wanke ta ce “Kina ganin aiki ya kacame min amma kika tafi kika kule a daki ko uwar
me kike? Oho! Maza wanke su yanzun nan cikinsu zan kwashe tuwon dare”.
Ta ja kujera ta soma wanke-wanken, Hajara ta sake cewa “Ki dinga iza min wutar nan, sallah zan yi”.
Ta ce “To”.
Hajara na shiga bayi Habiba ta fito, ta ce “Cika min randar can da ruwa, ga kuma tsummokaraina ba yawa, ki
dauraye min su”.
Ta zube mata tulin atamfofinta a gefe, ta ce “To bari in karisa wa Aunty Hajara wanke-wanken, ta ce tuwo
zata kwashe”.
Habiba ta ce “Inye, wato aikin Hajara ya fi nawa don ni kin raina ni, sabida ina sakar miki fuska?”
Ta tsame hannunta daga wanke-wanken zata fara yi mata wankin Hajara ta fito daga bayi ta ce “Au, bar min
wanke-wanken za ki yi sabida kina tsoronta? To ba zaki yi wankin ba, sai kin gama mini”.
Suka soma bala’i a tsakaninsu, Mairo dai tsayawa ta yi kawai tana kallonsu.
Baffa ya shigo yana “Kaiconku! Harshenku a matsayinku na matan aure, amma har a makota ana jiyo ku,
asararru wadanda ba su san mutumcin kansu da martabar da Allah Ya yi musu na matan aure ba”.
Ya dubi tulin aikin da suka tilawa Mairo yana salati, ya ce “Habiba waye zai yi miki wannan wankin?”
Ta yi shiru, ya ce “Da ke nake magana fa”.
Ta soma rawar murya amma ba ta fasa tsiwa ba, ta ce “Au… to, kana nufin haka zamu aje gansamemiyar
budurwa kamar Mairo sai dai mu tuka mu bata ta ci ta side hannu ta mike a katifa?”
Ya ce “Ina almajirin da nake biya yake yi muku wankin?”
Cikin rashin gaskiya ta ce “Bai zo ba”.
Ya ce “To kwashe kayanki maza-maza tun kafin mu sa kafar wando daya da ke, idan ya zo ya yi miki, ko ki tura
‘ya’yanki su kirawo shi ya yi miki, amma bazan lamunci wannan rashin arzikin ba. Mairo ba baiwar uwar kowa
ba ce a cikinku, wallahi-wallahi bazan yarda ku maidata baiwa ba. Bazan hanata ta taimaka muku da ayyukan
gida ba, amma banda wankau da dakau. Ke Ladidi!”
Ya kwala mata kira, ta fito a razane, “Zauna nan don ubanki, ku yi wanke-wanken tare ko in kwashe miki
hakora yanzun nan”.
Ta ja kujera ta zauna tana zumbure-zumbure, suka soma wanke-wanken tare.
Wannan tsayawa tsayin daka da Alhaji Abbas ke yi akan Mairo da al’amarinta, ya sayo mata matsananciyar
kiyayya a gurin iyalansa, sun dauki tsanar duniya sun daurawa marainiyar Allah, daga su har ‘ya’yansu, su suyi
mata, ‘ya’yansu su yi mata, amma ba zasu kwabe su ba. Barin Ladidi da ji ta ke da da hali, da ta cakawa Mairo
wuka ta mutu kowa ya huta da bala’in Baffa a kanta.
Kwana bakwai kacal da dawowar Mairo daga makaranta, duk ta bi ta kare kamar kudin guzuri, sai karan hanci
da idandunan kadai, sabida rashin dadin rai da rashin kwanciyar hankali. Bata taba ganin mutane marasa
imani da rashin darajja dan Adam irin Habiba da Hajara ba.
Amma a kullum tana yi musu uzuri da yafe musu cikin zuciyarta. Ba kowa ne zai iya rike dan mutum ba a
wannan zamanin, tunda dai sun yarda su zauna da ita, to ba zata kasa yi musu biyayya ba iyakar iyawarta.
Wata mota kirar Kia-Rio ta yi fakin a kofar gidan Alhaji Abbas, misalin karfe goma dai-dai na safe. Lokacin
Alhajin bai kai ga fita kasuwa ba. Nabilah Bebeji, ta fito daga mazaunin direba tana duba agogon hannunta, ta
doshi kofar gidan Alhaji Abbas, tana mai addu’ar Allah dai Ya sa Baffan Mairo bai fita ba.
Ta yi sallama a tsakar gidan, Habiba ta amsa yayin da ta bi ta da kallon mamaki. Sanye ta ke da atamfa mai
karshen tsada shudiya ta karkata dauri mai ban sha’awa kamar nadin inji, a hannunta ‘yar matsakaiciyar jaka
ce, samfarin Louis Buittion da takalminta marar tudun dunduniya. In ban da kamshin turaren Rasasi (blueroyale) ba abin da ke tashi a jikinta, ta yane jikinta da gyale kalar atamfarta, daure a hannunta agogo ne shudi
samfurin polo.
Jiki na rawa Habiba ta dauko sabuwar tabarma ta shimfida mata, ta tsugunna har kasa ta gaishe ta, ta gaya
mata ta zo wajen Mairo ne. A lokacin Mairon tana bayi tana wanka, cikin bakin-ciki karara Habiba ta yi mata
nuni da dakin su Mairo kamar ba ita ce mai yi mata fara’ar da ta ke yi mata ba.
Dakin tsaf ya ke, da yake Mairo ba ta wasa da tsaftarsa, sau dubu Ladidi zata bata, sau dubu zata gyara.
Ta samu gefen katifar Mairo ta zauna, ta dauki wani littafi na Mairon da Mairon ta aje, da alama shi ta ke
karantawa kamin ta shiga wankan na Dynasties the Ashtons (Condition of marriage), ta ce “Maryama na nan
da karance-karancenta”.
Dai-dai lokacin da Mairon ta shigo, kanta na yararin ruwa domin wankan sallah ta yi, zata soma sallah. Ta
harari Nabilah ta ce, “karfe taran ke nan?”
Ta yi murmushi ta ce “Go-slow ya tare ni, amma ai na yi kokari, ke fa da sai yanzu kika yi wanka, ni tun asuba
Momi ta tashe ni wai inyi maza in shirya in dauko mata Mairo ta ganta”.
Ta yi murmushi, ta ce “Yau dai da yardar Allah zan ga Momi”.
Ta ce “kwarai kuwa”.
Mairo na shiryawa Nabilah na kallonta cikin yin tazbihi ga Sarkin halitta da Ya kaga halittar Mairo.
“MAIRO MATAR MANYA CE”. Nabilah ta ayyana a zuciyarta. Wani irin jiki lukui-lukui kamar mai shiga wankan
inji, ga kwantaccen gashi na fulanin usuli, wanda ke kwance lambam akan dogon wuyanta yala-yala da shi
kamar ba zai kitsu ba, alhalin ba ta taba shafa masa relader ba koda wasa. Idanuwanta dara-dara, farare kal
masu wani irin maiko da sheki (oily-eyes). Kai ita ba ta taba ganin mace mai lafiyayyen kugu da shafaffar mara
irin Mairo ba. Kai ka ce idan ta sunkuya karyewa zata yi. Tana sharce kanta ta lura Nabilah kallonta ta ke, ta ce
“Ke don Allah wannan kallon fa?”
Ta ce “ke din ce, abun kallon ce Mairo, duk mijin da ya aure ki ya caba, ai ban san haka kike da kyau ba sai
yau”.
Ta yi murmushi ta ce “Ni kuma ban taba ganin mai kyau irin naki ba Nabilah”.
Ta ce “Kayya! Gyara ne kawai Mairo, ina maganar natural beauty ne”.
Sai Mairo ta ja bakinta ta tsuke, ba ta kara cewa komai ba.
Ta kammala shiryawa tsaf cikin atamfarta ta ganin sarki (Ghana wad), wani tausayi ya kama Nabilah, mace
har mace, sai dai ba kayan ado, da da suttura ya ya za a ga Mairo? A hakan ma Mairo abin a juyo a kalla ce,
ina ga ta samu sutturu da kayan gyara? Sai dai duk yadda ta so ta dinga taimakawa Mairon tun a makaranta
Mairon ba ta yarda, cike ta ke da wadatar zuci, kuma cikin godiyar Allah.
Mairo ta yi wa Nabilah jagora zuwa dakin Baffa. Ta zube a kasa ta gaishe shi, ya amsa cikin far’a da cewa,
“Lafiya kalau Nabilah, an gama karatu sai aure ko, ko kuwa babbar makaranta za ki wuce kamar kawarki?”
Ta ce “Eh, makaranta zan wuce”.
Ya ce “To Allah Ya ba da sa’a”.
Sannan ta gaya mishi ta zo ta dauki Mairo su je gidansu, iyayenta su ganta. Ya ce “Babu damuwa, don Allah
kada Mairo ta kai dare”.
Suka ce “Insha Allah”.
Cikin nutsuwa Nabilah ke tuki har suka hau kan titin sakateriyar Audu-Bako, Mairo ta dauka Tarauni suka
nufa, sai ta ga Nabilah ta karya akalar motar ta sha round ta hau kan titin state library, ba ta kai karshen titin
ba ta yi kwana ta shiga unguwar Ahmadu Bello Way, ta tsaya a harabar gidansu mai lamba dari da biyu (No.
102), suka rufe motar suka karasa cikin gidan.
Tun Mairo na mamakin tangama-tangaman falullukan da suke wucewa har ta daina mamaki, sai tazbihi ga
Allah Mai azurta wanda ya so. Ba ta taba shiga gida irin wannan ba ko a mafarkinta. Ba su tsaya a ko’ina ba sai
a babban falon Momin Nabilah, wadda ta fito tana tafa hannu tana ‘Lale da Mairon Nabilah”.
Ta yi murmushi ta zamo daga cikin kujera tana gayas da Momin, kamin ai haka tuni Nabilah da wata dattijuwa
wadda da alama mai aiki ce sun cika gaban Mairo da kayan tande-tande da lashe-lashe irin wadanda ba ta
taba ci ba a rayuwarta.
Shi ma Daddyn Nabilah ya sauko yana marhaban da Maryam. Ya zauna a cikin su, Mairo duk ta kasa sakewa
sabida bakunta da rashin sabo. Saukin kan iyayen Nabilah ya burge ta. Ta tabbatar Nabilah ‘yar gata ce ta
karshe, ita kadai ce kwallin kwal, a wurin iyayenta. Daddy ya ce da Mairo da zarar takardunsu sun fito ta kawo
mishi zai taimaka su samu gurbi a jami’a ita da Nabilah, ta yi godiya sosai.
Karfe biyar na yamma Mairo ta yi haramar tafiya. Akwati guda Momi ta shake mata da kayan shafa da
dogayen riguna kala-kala, Nabilah ta maidota gida.
Tana shigowa idanun Hajara da Habiba akan jakar hannunta. Jikin Habiba har rawa yake, ta bi bayan Mairo
tana son ta ji ina Mairo ta samo wannan diyar arzikin, har ga shi ta dawo da galleliyar jaka cike taf da kaya.
Har karo suke ita da Hajara wajen shigowa dakin. Habiba ta ce “Bude jakar mu gani, me muka samu?”
Hajara kuma ta ce “Wannan bakauyar ta iya bude irin wannan jakar ne? Gafara nan ki gani”.
Ta jawo jakar ta soma kici-kicin budewa. Ta zazzago duk kayan da ke ciki tana al’ajabi. Habiba ta ce “Ina kika
samo wannan diyar arzikin kuma?”
Mairo ba ta yi magana ba suka soma kasawa, Habiba ta daga rigar da ta fi kowacce kyau a ciki, ta ce “Wannan
zata yi wa Ladidi”. Ta sake daga skirt da rigarshi ta ce, “Wannan sai a bar wa Batulu idan ta kara girma zata yi
mata dai-dai, ke ki rike wannan din”.
Ta tura mata wata ‘yar yaloluwar rigar barci suka tattara kashi uku bisa hudu na kayan suka yi waje da sauri
har suna tuntube tareda karo da juna kada Baffa ya jiyo su suka gudu dakinsu.
Mairo ta ce, “Allah na tuba, suttura tsumma, mene da zan damu kaina?”
Duk da Baffa ya hana a bata aikin wahala wanda ya fi karfinta ba su fasa ba a bayan idonsa. Mairo na hakuri
da su da kokarin kyautata musu su da ‘ya’yansu a kullum, amma ta rasa dalilin da yasa mutanen nan suka ki
jininta, ko zata wuni tana aikin bauta, shara, wanke-wanke, wanki da wankin bandaki ba zata taba yi musu
gwaninta ba, balle kalmar “madallah” ko “an gode” ta gitta a tsakani.
Watanni uku cif da gama makarantar su ta samu labarin fitowar jarrabawarsu, don haka ta soma shirin zuwa
gidan su Nabilah don su je makaranta su karbo sakamakonsu.
Baffa da kanshi ya kaita gidan su Nabilah tana yi masa kwatance tana nuna masa hanya har suka iso gidan. Ya
sauke ta ya juya da cewa, idan sun dawo Nabilar ta maidota gida.
Amma Allah sarki, sai ta tarar da Nabilah kwance ba ta jin dadi. Ta zauna a gefen gadon da ta ke kwance ta
dora hannu akan goshinta, zafi rau! Momi ta shigo da filet a hannunta mai dauke da soyayyar plaintain da
dankali da kwai, ta ce “Ungo ba ta Maryam da kanki, watakila zata ci, tunda ni nayi-nayi ta ki karba”.
Mairo ta ce “Haba Nabilah, ciwo da rashin cin abinci ai abin ba kyau, ki daure ki ci ko kadan ne don Allah”.
Ta karba tana kokarin mikewa, Mairo ta tusa mata filo a bayanta don ta ji dadin jingina. Momi ta fita ta bar
su. Tana fita Nabilah ta fashe da kuka mai tsanani. Hankalin Mairo ya tashi, ta ce “Lafiya Nabilah? Wani abu ya
faru ne?”
Cikin kuka ta ce, “Me ye bai faru ba? Hajiyar Daddy ce ta zo ta ce ba ta yarda na ci gaba da karatu ba, aure za
a yi min da wani cousin dina. Bayan kuma bana sonsa, kuma sati mai zuwa za a daura auren, shi ma bai ce
yana sona ba, wai wata Igbo ya zo musu da ita daga can inda yake karatu a Kudu, shi ne ba su amince masa
ba, suka ba shi ni. Allah na tuba auren soyayya ma bai tsira ba a wannan zamanin balle auren tushe? Sabida
Allah na yi kama da matar tushen iyaye?”
Mairo ta rasa abin da zata ce “Ki ce ba ciwo kike ba, tunanin aure ne. Ni ban ga aibu a nan ba, tunda iyaye ne
suka hada, ai ALHERI ne, kuma alherin suke nufin ki da shi. Ki yi biyayya ga iyayenki Nabila za ki ga da kyau a
rayuwa.
Soyayya aikin banza ce, don watakila yadda kike son mutum shi ba haka ba ne a zuciyarshi ba. Na gani akan
kaina Nabilah. Har yanzu kuma ban ga inda soyayya ta kaini ba, sai kunci a zuci, ruhi da gangar jiki. Nabilah
yau zan gaya miki abin da ke raina shekara da shekaru. Wato soyayyar Uncle Junaidu. Na dauka yadda na ke
azabtuwa a zuci, da gangar jiki da soyayyarsa, shi ma haka yake sona, ashe ni ban sani ba, Uncle ba haka ba
ne a zuciyarshi ba.
A ranar da na yanke shawarar fallasa mishi asirin zuciyata, a ranar ya zame, ya gudu ya barni, ba tare da ya
sanar da ni komi a kanshi ba. Wanda ke nufin ba ya bukatar anymore mu’amala da ni. Har yau ni kadai nasan
abin da nake ji a zuciyata Nabilah. Hasashenku ke da Innata, bai zamo gaskiya ba, Uncle Junaidu ba SO NA
yake yi ba, tausayina ne da taimako”.
Nabilah ta yi shiru cikin mamaki, yau Allah Ya nuna mata ranar da Mairo ta bude bakinta da kanta ta fada
mata cewar tana son Uncle Junaidu.
Ina ma ace shi ma hakan ne a zuciyarshi? Duk duniya ba ta taba ganin mijin da ya dace da Mairo ba, irin
Uncle, wanda yasan zahirinta da badininta, jinin jikinsu ke gauraye guri guda yana circulating. Amma ba zata
taba yarda cewa wai Junaidu ba son Mairo yake ba.
Babu wanda zaka bai wa jinin jikinka sai wanda kake matukar so.
Ta dago a hankali ta dubi Mairo ido cikin ido, ta ce “Wallahi Mairo yadda kike son Uncle, shi ma haka yake
sonki. Zan yi rantsuwa in dafa Alkur’ani akan hakan. Sai dai ban san dalilinshi na janye kafa a ranar da zaku
rabu ba. Zan yi mishi uzuri da wani abu mai muhimmanci a gare shi, amma haka kawai Uncle ba zai ki yi miki
sallama ba, sai ko sakamakon wani muhimmin abu da ya faru gare shi.
Rashin haduwarku ya zama rahma ke nan ga mutumcinki da martabarki a idanunsa…….”
Ta yi saurin duban Nabilah, tana mai daga gira ta ce, “Yes, gara da Allah bai baki ikon ki furta masa ba, wai ya
aure ki koda ba ya sonki. Duk inda yake, Mairo ni na gaya miki ko ba dade ko bajima WATARANA zai neme ki,
ki rike wannan a zuciyarki ki ce, ni na gaya miki”.
Ta mike ta fada bandaki tana cewa, “Bara na shirya mu tafi, ni har ma na warke da ganinki Mairo”.
Ta yi dariya, cikin samun nutsuwa a zuciyarta da kalaman Nabilah, ta ce “Dama ba wani ciwo ke damunki ba,
sai shagwaba da gata, da suka taru suka lullube ki”.B
Sun isa Minjibir ana sallar azahar, zuwan da ya tuna musu da dabdalar kuruciyarsu. Shekaru shida cur, cikin
dalibtaka da al’amura masu dama, da suka faru cikin rayuwarsu, suka tuno Kausar suka yi mata addu’a. Suka
karasa Edam office suka amso sakamakonsu. Ba abin da suka fadi, sun cinye sun lashe 9 credits ris. Ina ma
Uncle na nan, ya zo ya ga girbin abin da ya shuka?
Nabilah ta kasa daurewa ta tambayi Mr. Kayode malamin lissafinsu, ko ina Uncle Junaidu? Cike da alhini ya ke
sanar da ita cewa, “Yau watanninsa uku kenan da tafiya karo karatu (in-serbice) zuwa kasar Russia (Ukhrain).
Yana daga cikin malaman da federal ta dauki nauyin karo karatunsu a kasashen duniya talatin da biyar”.
Mairo ta samu wani kututturen bishiya ta zauna ta yi kukanta mai isarta, kuka irin wanda ba ta taba yi ba a
rayuwarta, ko a rashin iyayenta kuwa. Ta tabbatar wani bigiren nata ya kuma faduwa. Ta dubi takardunta,
wahalar shekaru shidda da Uncle ya yi, yau ga shi Allah Ya cika mishi burinsa, amma ashe ba zai gani ba.
Kuka ta ke kukan sabo, soyayya da kewa. Ta tabbatar ta rabu da Junaidu ke nan har abada! Ya yi mata nisan
da ba zata taba kamo shi ba. ALHERINSA da kyautayinsa masu yawa ne a gareta da ba zata taba mantawa ba.
Soyayyarsa da kaunarsa wani abu ne da ba zai taba gushewa daga zuciyarta ba. Shi kadai ta fara so, kuma shi
kadai zata ci gaba da so har zuwa karshen rayuwarta, yana sonta ko ba ya sonta. Ta tabbatar ita ke son Uncle,
amma shi ba hakan ba ne a zuciyarsa ba, ai yasan inda zai same ta, da yana sonta da ya neme ta.
Ciwon kana so ba a sonka, matukar ciwo ne da shi. Ya san ba ta da kowa a duniya a halin yanzu, daga Baffa sai
shi, amma ya yi mata haka, ya ki tallafar rayuwarta a dai-dai lokacin da ta fi bukatar tallafinsa. Ta kullaci Uncle
Junaidu kullata mai tsanani, irin kullatar da ta yi wa Habibu tare da alkawarta wa ranta yin kokari ta yakice shi
daga zuciyarta, ta fuskanci rayuwa ta karbeta a duk yadda ta zo mata…..!!!
*** ***
B
ikin Nabilah bai yi armashi ba, sabida amaryar da angon duk sun ki ba da hadin kai, sai iyaye da ‘yan uwa ke ta
sha’aninsu cikin farin ciki. Ko yaushe Mairo na tare da Nabilah, don ita kadai ce zata yi mata magana ta ji.
Abinci ma sai Mairo ta lallashe ta sannan za ta ci, don wai fushi ta ke da Momi da Daddy. Ranar lahadi aka kai
amarya gidanta da ke Nassarawa GRA. Tana kuka, Mairo na yi suka rabu, don wata irin kauna ce shakikiya
Allah Ya hada a tsakaninsu.
Mairo ta dawo gida, ta kwanta a yagulalliyar katifarsu. Ta runtse idonta tana tunanin al’amuran rayuwa. Yau
dai ga Nabilah ta yi aure ta barta, ita kuma ko sai yaushe ne Allah Zai kawo mata nata Mr. Right din? Tunda
Uncle ba ya sonta? A zahiri aure ta ke so, ba kuma da kowa ba da UNCLE JUNAIDU. Karatun ya fice mata a rai,
tunda babu Junaidu mai karfafawa. Tana daga cikin halittattun mata masu tsananin bukatar da namiji, amma
ba da kowa ba, da wanda ruhi, zuciya da gangar jikin su ke so. Haka kawai tunanin unguwar GALADANCHI ta
fado mata a rai. Idan har ba kuskure ta yi a tunaninta ba, Uncle ya taba gaya mata shi dan unguwar
Galadanchi ne, da ke cikin birnin Kano. To idan ta je Galadanchi ta ce tana neman waye? Alhalin ma an ce
Uncle Junaidu yana Russia? Zata je ta nemi gidan su Uncle, iyayenshi da ‘yan uwanshi musamman Ilham, wai
an ce Gaida mai gaisheka…!’
Zumbur ta mike, ta jona ruwa a heater tana jiran ya yi dumi ta yi wanka, sabida sanyin da ake cikin watan
Junairu.
Daga can gefe Ladidi ta tashi tana yatsina fuska, ba a jima ba kuma ta soma kelaya amai a tsakar dakin. Mairo
na yi mata sannu amma ko kallonta ba ta yi ba. Ta gama aman ko kurkure baki babu ta koma ta kwanta.
Mairo ta dauko tsintsiya da abin kwashe shara ta soma gyara wajen don tasan idan ta Ladidi ne, to a bar
wajen a haka,. Ta dauko tsumma da omo klin ta goge dakin tas! Ta kunna turaren wuta na tsinke.
Idan ba ta manta ba wannan aman Ladidi na shidda ke nan cikin kwana uku, amma ko tunanin ta je asibiti ba
ta yi. Ta matsa jikinta a hankali, abinki da dan uwa, ta ce, “Ladidi ki shirya na rakaki asibiti mana, ko magani ne
a baki, wannan aman ya tsaya?”
Ta yi shiru ba ta ce uffan ba, kuma ba ta kalle ta ba, can kuma ko mai ta tuna? Ta ce “Mu je”.
A gurguje ta yi wankan ta fito, Ladidi ko wanka babu suka fito. Habiba na tsakar gida ta daga ido ta dube su.
Wani irin kishi da bakin-ciki ya tushe mata a kahon zucci, ganin irin kyau da kwarjini na musamman a fuskar
Mairo tamkar diyar larabawan Turkiya. Ladidi kuwa kamar a rufe ido don muni da rashin tsafta.
Ta ce “Ke Ladidi, ina zaki je da wannan mai kama da kabewar?”
Ta kyabe baki kamar yadda ya ke a al’adarta, ta ce “Asibiti wai zata kai ni”.
“Ciwon me kike da za a kai ki asibiti?”
Ta sake kyabe bakin ta ce “Wai don ina amai, ko ta gaji da kwashewa ne? Oho!”.
Ta gallowa Mairo harara ta ce “Kin ga ni bana son kinbibi da son nuna iyawa, waye ba ya amai idan ya ci abin
da ranshi bai so ba? Wuce da Allah ki ba ni waje, ke kuma ungo goro ki ci tashin zuciyar zai lafa”.
Mairo ta koma daki tana jinjina hali irin na Habiba. Karfe biyar na yamma ta ji karar motar Baffa tabbacin ya
dawo. Sai da ta ba shi lokaci ya kimtsa sannan ta je dakinsa, ta same shi yana cin abinci ga Hajara da autarta
Umma a gefe, ban da harararta ba abin da Hajara ke yi, amma ita ba ta kula ba, tsugunnawa ta yi har kasa ta
gaida Baffan, ya amsa cikin walwala, ya ce “Yaya dai Mairo, babu wata matsala ince ko?”
Kanta a kasa ta ce “Babu Baffa, ina so in je Galadanchi ne”.
Bai tambayi wajen wanda zata ba, ya dauko naira dari biyu a aljihunsa ya mika mata, ya ce “Ga shi ayi kudin
mota, amma kada ki bari dare ya riske ki waje”.
Ta ce “Insha Allahu Baffa”.
Mairo tana tafe tana tunanin rigima irin tata, ya za a yi ta nemi gidansu Uncle alhalin ba tasan komi a kanshi
ba? Ace ma ta sani, me zata je ta ce, kuma me zata je ta yi? Wata zuciyar ta ce “Gaida mahaifiyarsa kamar
yadda yake gaida naki”. Wannan tunani ne mai kyau.
Ta fito daga Yakasai zuwa Bakin Rimi, ta tari tasi ta ce “Galadanchi”. Ya bude mata kofa ta shiga.
Ba a fi minti goma ba ya sauke ta a unguwar Galadanchi. Ta fito ta ba shi dari biyun Baffa ya ba ta canji, ta
gangara dai-dai makarantar gidan Galadima ta tsaya nan tana rarraba ido, ta rasa wanda zata tambaya.
Daga can gefe wajen masallaci dandazon matasa ne a zaune suna haramar shiga sallar magriba, ba zata iya
shiga cikin wadannan samarin ba don haka ta ci gaba da tsayuwa cikin rashin sanin abin yi. Tana nan tsaye
wani saurayi ya zo gittawa ta gabanta ta yi mishi sallama, ya juyo ya amsa, ta ce “Don Allah Yayana tambaya
nake”.
Ya ce “Allah Ya sa na sani kanwata”.
Ta ce “Gidan su Junaid nake tambaya”.
Ya ce “Junaid? Ya ya sunan maigidan?”
“Gaskiya ban sani ba”.
“Babba ne ko yaro ne?”
“Babba ne, don zai girme ka”.
Ya yi dan tunani “Kwatanta min shi”.
Nan ta shiga kwatanta mishi, ya ce “Ke ko gidan Justice Atiku kike tambaya?”
Kwarai ta taba jin sunan Chief Justice Atiku Galadanchi a bakin Kausar mai rasuwa, (Alkalin-alkalai) na Jihar
Kano. Ta ce “Ina jin nan ne”.
Ya ce “Mu je na nuna miki”.
Abinka da karamar unguwa, kowa yasan kowa. Ya yi mata nuni da gida ginin manyan ‘yan bokon da, mai
malalen suminti, dakali biyu sun sa gidan a tsakiya, ko ina a share tas ko tsinke babu. Ta yi wa saurayin godiya
ta sa kai zauren gidan.
Ashe yadda wajen yake ba haka cikin gidan yake ba, cikin gidan gini ne sosai na zamani, mai ban al’ajabi,
sabida yadda aka kwalmada karfe da rodi aka yi irin wannan ginin ba kasafai ake samun irinshi cikin Nijeriya
ba. Ko’ina gilashi sai daukar ido yake hatta kofar shiga falon gidan ta gilashi ce. Ta tsaya a kofar falon tana
sallama.
Wata dattijuwa da alama mai aiki ce, ta fito tana mata kallon rashin sani. Mairo ta tsugunna ta gaishe ta, ta
amsa, ta ce “Yammata wa kike nema?”
Ta ce “Babar su Ilham”.
Ta bude mata kofar falon, ta ce “Zauna a nan, Hajiya tana zuwa yanzu”.
Ba ta zauna a kujerar ba, a kan wani tattausan kilishi da ke tsakiyar dakin ta zauna. Talabijin na ta aiki cikin
tasoshin tauraron dan Adam. In banda kamshin turaren wuta na (Bakhour) ba abin da ke tashi a falon,
gauraye da ni’imtaccen sanyin na’urar sanyaya daki duk da sanyin da ake fama da shi kuwa.
Ta daga kai a hankali zuwa gabas maso kudu na dakin. Tangamemen hoton Uncle Junaidu ya yi mata sallama,
yana murmushi. Wata matsananciyar faduwar gaba ta same ta, ta kura mishi ido ba ta ko kyaftawa. Dai-dai
lokacin da ta ji muryar Hajiyar tana yi mata sallama.
Ta daga kai ta kai dubanta ga mahaifiyar Uncle Junaidu. Nan ta ga inda Junaid ya debo kyau, tsurarsa. Mace
ce ma’abociyar zati da kamala gami da gogayya cikin zuzzurfan ilmin boko. A idanunta farin gilashi ne
(medicated). A kiyasce zata yi shekaru hamsin. Amma a idaniyarka ba zata fi shekaru talatin da biyar ba.
Ta zauna a kujera fuska cike da annuri, Mairo ta duka tana gayas da ita. Ta amsa cikin murmushi ta ce,
“Yammata daga ina? Ban gane ki ba”.
Itama Mairon sai ta rasa abin da zata ce. Wata zuciyar ta ce “Akul! Kika ce danta kika zo nema, wannan ba
mutumcin diya mace ba ne. Kin zo ki gaishe ta ne sabida Allah, da kuma soyayyar danta da Allah Ya dasa miki.
Amma ba don kamun kafar neman soyayyar ba”.
Hajiyar ta sa mata ido tana nazarinta, ta rasa inda ta san fuskar. Haka kawai Allah Ya sanya mata kaunar
yarinyar a zuciyarta. Duk inda ake neman kyau da nutsuwa, haiba da kamala to wannan yarinyar ta zarce, ga
shi da alamunta ilmi ya ratsata ta ko ina. Amma shirun da ta yi mata ya sanya ta diga mata ayar tambaya
(kuestion mark?). Ta sake maimaita mata tambayarta “Yammata daga ina kike ban gane ki ba?”
A sannan ne Mairo ta cira kai, wasu irin fararen idanu, gauraye da wani irin blue-blue suka haske Hajiyar, ta yi
wa Allah sarkin halitta tazbihi, ta tsarkake Shi, ta tsarkake iko da iyawarSa. Cikin sassanyan sautinta ta ce “Na
zo wurin Ilham ne”.
Ta ce “Ke kawarta ce halan? Don na ga kamar nasan fuskarki”.
Ta ce “Eh”. A takaice.
Ta ce “To amma kuwa na yi mamaki da ba ta kawo miki katin bikinta ba, an yi bikinta watanni uku da suka
wuce. Suna zaune a Wales din kasar Ingila inda mijinta ke karatu”.
Mairo ta ce “Allah Sarki, Allah Ya yi ba zamu hadu ba”.
Ta sake juyawa ta dubi hoton Uncle. Ta sake juyowa ta dubi mahaifiyarsa, wata irin soyayya da kauna na sake
mamayar zuciyarta. Ba ta ki ta zauna a nan tare da Hajiyar Junaidu ba, tana yi mata bauta, har karshen
rayuwarta koda Junaid ba zai aure ta ba. Wannan ita ce kauna ta hakika, wadda ba a samunta a wannan
zamanin. Da gaske Junaid ya yi mata nisan da ba tasan ranar da zata kamo shi ba.
Tsigar jikinta ya tashi, ganinta ya dushe, wani duhu ya gilma mata ta daina ganin abin da ke gabanta na wucin
gadi.
Hajiyar ba ta lura ba, don a lokacin hankalinta ya tafi ga amsa kiran wayar da ya shigo mata yanzu-yanzu. Ta
mike tana gyara lullubinta ayayinda ta fuskanci da Uncle Hajiyar ke magana. Hajiyar ta yi mata alama da
hannu ta jirayeta. Sai da ta gama wayar ta ajiyeta akan centre table, ta ce da Mairo “dan jiraye ni ina zuwa”.
Ta koma matattakalar da ta fito, jim kadan ta dawo da leda mai tambarin shagon country mall ta mika mata.
Mairo ta girgiza kai alamar ba zata karba ba, don tasan ko ta karba rabon su Ladidi ne, dama ace za su gode
ne, to a’a, zagi da bakar magana ne zai biyo baya.
Hajiyar ta ce “Ni ba babarki ba ce? Ba zan yi miki ihsani ki karba ba?”
Ta sake kai dubanta ga Uncle Junaid da ke cikin hoto yana murmushi. Sai ta ga kamar ya turbune mata fuska,
cikin rashin jin dadi. Ta maido ga dubanta ga Hajiyar, kallonta ta ke tsakaninta da Allah da matsananciyar
kauna cikin kwayar idanunta.
Ji ta yi kamar ta kwantar da kai a kafadunta ta yi kukan da ke cin ranta, ta gaya mata matsananciyar kaunar
danta da Allah Ya dora mata. Ta ji dumin da Junaid ya ji, a jikin wannan nagartacciyar UWA, ganin hawaye na
neman tona mata asiri ta yi hamzarin karba ta ce “Na gode”.
Har ta kai bakin kofa zata fita, Hajiyar ta kirata jikinta a sanyaye, don daga dukkan alamu akwai abin da ke
damun wannan yarinya, ta ce “Har za ki tafi, ba ki gaya min sunanki ba, idan Ilham din ta yi waya in gaya
mata”.
Mairo ta ce
“Ki ce mata Maryam ce”.
“Maryam-Maryam!” Tana ji a bakin su Ilham, amma a wannan karon Allah bai bata ikon ganewa ba.
Har yarinyar ta fita, ba ta motsa daga inda ta ke ba, ta dade tana tunanin inda tasan yarinyar. Mai yasa ba ta
tambaye ta daga inda ta ke ba? To akan me zata tambaye ta? Don kwaita zo wajen Ilham? Amsar shi ne, don
zuciyarta tana sonta. Ta koma falon ta zauna cike da tunani.
Sai ana kiran isha’i ta iso gida, Baffa na alwalar sallah a nan kofar gida, ta tube takalminta sannan ta wuce shi,
zuciyarta cike da jin haushin dadewar da ta yi. Ya ce “Ban ce kada ki kai dare ba Mairo?”
Cikin matsanancin ladabi ta rausayar da kai tace “Ka yi hakuri Baffa, mota ce ban samu da wuri ba”.
Ya ce “Ni dai duk inda za a je aje ido na ganin ido, amma bana son ayi dare. Idan kin shiga ki turo min Lawan”.
Ta ce “To”.
Habiba na kwasar tuwon dare sanda ta shigo, ta dago kai ta dube ta a ranta ta ce, “Kai wannan yarinya da
kashin arziki ta ke, kullum ta fita ba ta dawowa haka nan, sai bakin jini har yau babu wanda ya taba sallama
da ita, duk kyawun nan nata. Ladidi kuwa kullum idan mutum biyu ba su yi sallama da ita ba, hudu za su yi”.
Ta dubi Lawan wanda ke bin ledar hannunta da kallo, ta ce “Ka je Baffa na kira”.
Ya ce “In an ki fa?”
Ba ta yi magana ba ta wuce wajen Habiba ta durkusa ta ce “Mama Na dawo, sannunku da aiki”.
Lawan ya ce “Wani feleke wai ‘Baffa’, mu ‘Baba’ mu ke cewa Babanmu, ba wani Baffa ba. Wai mama yarinyar
nan ta fara bin maza ne ta ke shigowa gidan nan da manyan ledoji?”
Habiba ta ce “Idan ta bi sun ina ruwanka, ko mace ba don namiji aka halicceta ba? Me muka samu ne Mairo?
Miko nan in gani”.
Ta mika mata ledar ta tusa karkashin kujerar da ta ke zaune kada Hajara ta fito ta gani, ta ce sai an raba da
ita.
Ta dauki tuwon da ta saka mata a wani kwano duk lamba, ta zuba miyar karkashi akai ta mika mata. Ta karba
ta wuce daki cike da takaici.
Ashe wani takaicin ke jiranta. Tana sanya kai dakin wani mugun karni ya dake ta. Ladidi ta kelaya amai tun
daga bakin kofa har bakin katifarsu. Tana kwance a katifa tana barci kamar mushe ba abin da ya dame ta. Ta
fita ta dauko tsintsiya da abin kwashewa ta soma aikin aman kamar zuciyarta ta yo waje don bakin ciki.
Tuwon da ba ta iya ci ba ke nan sabida karnin da dakin ke yi, haka ta kwana da yunwa.
Washegari Ladidi da kanta abin duniya ya ishe ta, ta rarrafa katifar Mairo ta tashe ta, misalin karfe bakwai na
safe. Mairo ta bude ido tana kallonta, yawu ya ciko mata baki ta juya bayan kofa ta tsartar ta ce
“Zo ki raka ni asibitin don Allah, na kasa gane abin da ke damuna, amma da gaske ba ni da lafiya”.
Sai Mairon ta ce “Ki fara zuwa ki tambayo mama tukunna, idan ta amince sai na rakaki”.
Ta ce “Rabu da ita kawai, zo mu fice tana daki”.
Mairo ta ce “A’ah, ba za a yi haka da ni ba”.
Ba da son ran Ladidin ba ta fita ta tambayo Habiba za su je asibiti. Habiba ta dubi diyarta ta ce “Bana so ku
dinga jerawa ne kada a ga muninki”.
Ladidin ta kyabe baki, ta ce “Lallai ma Mama, ni ce ma mummunar?”
Habiba ta ce “Sai idan ba ku jera da wannan mai kama da aljannun ba”.
Ladidi ta ce “Ke wannan ya dama, ni da munin nawa dai ai na fi ta farin jini, kin taba jin ko bera ya aiko yana
sallama da ita?”
Ta ce “Haka kuwa, ku je sai kun dawo”.
Suna tafe a gefen hanya har asibitin Murtala, Mairo ta yanko mata kati suka hau layi. Suna nan zaune har aka
kirasu
B
Sun isa Minjibir ana sallar azahar, zuwan da ya tuna musu da dabdalar kuruciyarsu. Shekaru shida cur, cikin
dalibtaka da al’amura masu dama, da suka faru cikin rayuwarsu, suka tuno Kausar suka yi mata addu’a. Suka
karasa Edam office suka amso sakamakonsu. Ba abin da suka fadi, sun cinye sun lashe 9 credits ris. Ina ma
Uncle na nan, ya zo ya ga girbin abin da ya shuka?
Nabilah ta kasa daurewa ta tambayi Mr. Kayode malamin lissafinsu, ko ina Uncle Junaidu? Cike da alhini ya ke
sanar da ita cewa, “Yau watanninsa uku kenan da tafiya karo karatu (in-serbice) zuwa kasar Russia (Ukhrain).
Yana daga cikin malaman da federal ta dauki nauyin karo karatunsu a kasashen duniya talatin da biyar”.
Mairo ta samu wani kututturen bishiya ta zauna ta yi kukanta mai isarta, kuka irin wanda ba ta taba yi ba a
rayuwarta, ko a rashin iyayenta kuwa. Ta tabbatar wani bigiren nata ya kuma faduwa. Ta dubi takardunta,
wahalar shekaru shidda da Uncle ya yi, yau ga shi Allah Ya cika mishi burinsa, amma ashe ba zai gani ba.
Kuka ta ke kukan sabo, soyayya da kewa. Ta tabbatar ta rabu da Junaidu ke nan har abada! Ya yi mata nisan
da ba zata taba kamo shi ba. ALHERINSA da kyautayinsa masu yawa ne a gareta da ba zata taba mantawa ba.
Soyayyarsa da kaunarsa wani abu ne da ba zai taba gushewa daga zuciyarta ba. Shi kadai ta fara so, kuma shi
kadai zata ci gaba da so har zuwa karshen rayuwarta, yana sonta ko ba ya sonta. Ta tabbatar ita ke son Uncle,
amma shi ba hakan ba ne a zuciyarsa ba, ai yasan inda zai same ta, da yana sonta da ya neme ta.
Ciwon kana so ba a sonka, matukar ciwo ne da shi. Ya san ba ta da kowa a duniya a halin yanzu, daga Baffa sai
shi, amma ya yi mata haka, ya ki tallafar rayuwarta a dai-dai lokacin da ta fi bukatar tallafinsa. Ta kullaci Uncle
Junaidu kullata mai tsanani, irin kullatar da ta yi wa Habibu tare da alkawarta wa ranta yin kokari ta yakice shi
daga zuciyarta, ta fuskanci rayuwa ta karbeta a duk yadda ta zo mata…..!!!
*** ***
B
ikin Nabilah bai yi armashi ba, sabida amaryar da angon duk sun ki ba da hadin kai, sai iyaye da ‘yan uwa ke ta
sha’aninsu cikin farin ciki. Ko yaushe Mairo na tare da Nabilah, don ita kadai ce zata yi mata magana ta ji.
Abinci ma sai Mairo ta lallashe ta sannan za ta ci, don wai fushi ta ke da Momi da Daddy. Ranar lahadi aka kai
amarya gidanta da ke Nassarawa GRA. Tana kuka, Mairo na yi suka rabu, don wata irin kauna ce shakikiya
Allah Ya hada a tsakaninsu.
Mairo ta dawo gida, ta kwanta a yagulalliyar katifarsu. Ta runtse idonta tana tunanin al’amuran rayuwa. Yau
dai ga Nabilah ta yi aure ta barta, ita kuma ko sai yaushe ne Allah Zai kawo mata nata Mr. Right din? Tunda
Uncle ba ya sonta? A zahiri aure ta ke so, ba kuma da kowa ba da UNCLE JUNAIDU. Karatun ya fice mata a rai,
tunda babu Junaidu mai karfafawa. Tana daga cikin halittattun mata masu tsananin bukatar da namiji, amma
ba da kowa ba, da wanda ruhi, zuciya da gangar jikin su ke so. Haka kawai tunanin unguwar GALADANCHI ta
fado mata a rai. Idan har ba kuskure ta yi a tunaninta ba, Uncle ya taba gaya mata shi dan unguwar
Galadanchi ne, da ke cikin birnin Kano. To idan ta je Galadanchi ta ce tana neman waye? Alhalin ma an ce
Uncle Junaidu yana Russia? Zata je ta nemi gidan su Uncle, iyayenshi da ‘yan uwanshi musamman Ilham, wai
an ce Gaida mai gaisheka…!’
Zumbur ta mike, ta jona ruwa a heater tana jiran ya yi dumi ta yi wanka, sabida sanyin da ake cikin watan
Junairu.
Daga can gefe Ladidi ta tashi tana yatsina fuska, ba a jima ba kuma ta soma kelaya amai a tsakar dakin. Mairo
na yi mata sannu amma ko kallonta ba ta yi ba. Ta gama aman ko kurkure baki babu ta koma ta kwanta.
Mairo ta dauko tsintsiya da abin kwashe shara ta soma gyara wajen don tasan idan ta Ladidi ne, to a bar
wajen a haka,. Ta dauko tsumma da omo klin ta goge dakin tas! Ta kunna turaren wuta na tsinke.
Idan ba ta manta ba wannan aman Ladidi na shidda ke nan cikin kwana uku, amma ko tunanin ta je asibiti ba
ta yi. Ta matsa jikinta a hankali, abinki da dan uwa, ta ce, “Ladidi ki shirya na rakaki asibiti mana, ko magani ne
a baki, wannan aman ya tsaya?”
Ta yi shiru ba ta ce uffan ba, kuma ba ta kalle ta ba, can kuma ko mai ta tuna? Ta ce “Mu je”.
A gurguje ta yi wankan ta fito, Ladidi ko wanka babu suka fito. Habiba na tsakar gida ta daga ido ta dube su.
Wani irin kishi da bakin-ciki ya tushe mata a kahon zucci, ganin irin kyau da kwarjini na musamman a fuskar
Mairo tamkar diyar larabawan Turkiya. Ladidi kuwa kamar a rufe ido don muni da rashin tsafta.
Ta ce “Ke Ladidi, ina zaki je da wannan mai kama da kabewar?”
Ta kyabe baki kamar yadda ya ke a al’adarta, ta ce “Asibiti wai zata kai ni”.
“Ciwon me kike da za a kai ki asibiti?”
Ta sake kyabe bakin ta ce “Wai don ina amai, ko ta gaji da kwashewa ne? Oho!”.
Ta gallowa Mairo harara ta ce “Kin ga ni bana son kinbibi da son nuna iyawa, waye ba ya amai idan ya ci abin
da ranshi bai so ba? Wuce da Allah ki ba ni waje, ke kuma ungo goro ki ci tashin zuciyar zai lafa”.
Mairo ta koma daki tana jinjina hali irin na Habiba. Karfe biyar na yamma ta ji karar motar Baffa tabbacin ya
dawo. Sai da ta ba shi lokaci ya kimtsa sannan ta je dakinsa, ta same shi yana cin abinci ga Hajara da autarta
Umma a gefe, ban da harararta ba abin da Hajara ke yi, amma ita ba ta kula ba, tsugunnawa ta yi har kasa ta
gaida Baffan, ya amsa cikin walwala, ya ce “Yaya dai Mairo, babu wata matsala ince ko?”
Kanta a kasa ta ce “Babu Baffa, ina so in je Galadanchi ne”.
Bai tambayi wajen wanda zata ba, ya dauko naira dari biyu a aljihunsa ya mika mata, ya ce “Ga shi ayi kudin
mota, amma kada ki bari dare ya riske ki waje”.
Ta ce “Insha Allahu Baffa”.
Mairo tana tafe tana tunanin rigima irin tata, ya za a yi ta nemi gidansu Uncle alhalin ba tasan komi a kanshi
ba? Ace ma ta sani, me zata je ta ce, kuma me zata je ta yi? Wata zuciyar ta ce “Gaida mahaifiyarsa kamar
yadda yake gaida naki”. Wannan tunani ne mai kyau.
Ta fito daga Yakasai zuwa Bakin Rimi, ta tari tasi ta ce “Galadanchi”. Ya bude mata kofa ta shiga.
Ba a fi minti goma ba ya sauke ta a unguwar Galadanchi. Ta fito ta ba shi dari biyun Baffa ya ba ta canji, ta
gangara dai-dai makarantar gidan Galadima ta tsaya nan tana rarraba ido, ta rasa wanda zata tambaya.
Daga can gefe wajen masallaci dandazon matasa ne a zaune suna haramar shiga sallar magriba, ba zata iya
shiga cikin wadannan samarin ba don haka ta ci gaba da tsayuwa cikin rashin sanin abin yi. Tana nan tsaye
wani saurayi ya zo gittawa ta gabanta ta yi mishi sallama, ya juyo ya amsa, ta ce “Don Allah Yayana tambaya
nake”.
Ya ce “Allah Ya sa na sani kanwata”.
Ta ce “Gidan su Junaid nake tambaya”.
Ya ce “Junaid? Ya ya sunan maigidan?”
“Gaskiya ban sani ba”.
“Babba ne ko yaro ne?”
“Babba ne, don zai girme ka”.
Ya yi dan tunani “Kwatanta min shi”.
Nan ta shiga kwatanta mishi, ya ce “Ke ko gidan Justice Atiku kike tambaya?”
Kwarai ta taba jin sunan Chief Justice Atiku Galadanchi a bakin Kausar mai rasuwa, (Alkalin-alkalai) na Jihar
Kano. Ta ce “Ina jin nan ne”.
Ya ce “Mu je na nuna miki”.
Abinka da karamar unguwa, kowa yasan kowa. Ya yi mata nuni da gida ginin manyan ‘yan bokon da, mai
malalen suminti, dakali biyu sun sa gidan a tsakiya, ko ina a share tas ko tsinke babu. Ta yi wa saurayin godiya
ta sa kai zauren gidan.
Ashe yadda wajen yake ba haka cikin gidan yake ba, cikin gidan gini ne sosai na zamani, mai ban al’ajabi,
sabida yadda aka kwalmada karfe da rodi aka yi irin wannan ginin ba kasafai ake samun irinshi cikin Nijeriya
ba. Ko’ina gilashi sai daukar ido yake hatta kofar shiga falon gidan ta gilashi ce. Ta tsaya a kofar falon tana
sallama.
Wata dattijuwa da alama mai aiki ce, ta fito tana mata kallon rashin sani. Mairo ta tsugunna ta gaishe ta, ta
amsa, ta ce “Yammata wa kike nema?”
Ta ce “Babar su Ilham”.
Ta bude mata kofar falon, ta ce “Zauna a nan, Hajiya tana zuwa yanzu”.
Ba ta zauna a kujerar ba, a kan wani tattausan kilishi da ke tsakiyar dakin ta zauna. Talabijin na ta aiki cikin
tasoshin tauraron dan Adam. In banda kamshin turaren wuta na (Bakhour) ba abin da ke tashi a falon,
gauraye da ni’imtaccen sanyin na’urar sanyaya daki duk da sanyin da ake fama da shi kuwa.
Ta daga kai a hankali zuwa gabas maso kudu na dakin. Tangamemen hoton Uncle Junaidu ya yi mata sallama,
yana murmushi. Wata matsananciyar faduwar gaba ta same ta, ta kura mishi ido ba ta ko kyaftawa. Dai-dai
lokacin da ta ji muryar Hajiyar tana yi mata sallama.
Ta daga kai ta kai dubanta ga mahaifiyar Uncle Junaidu. Nan ta ga inda Junaid ya debo kyau, tsurarsa. Mace
ce ma’abociyar zati da kamala gami da gogayya cikin zuzzurfan ilmin boko. A idanunta farin gilashi ne
(medicated). A kiyasce zata yi shekaru hamsin. Amma a idaniyarka ba zata fi shekaru talatin da biyar ba.
Ta zauna a kujera fuska cike da annuri, Mairo ta duka tana gayas da ita. Ta amsa cikin murmushi ta ce,
“Yammata daga ina? Ban gane ki ba”.
Itama Mairon sai ta rasa abin da zata ce. Wata zuciyar ta ce “Akul! Kika ce danta kika zo nema, wannan ba
mutumcin diya mace ba ne. Kin zo ki gaishe ta ne sabida Allah, da kuma soyayyar danta da Allah Ya dasa miki.
Amma ba don kamun kafar neman soyayyar ba”.
Hajiyar ta sa mata ido tana nazarinta, ta rasa inda ta san fuskar. Haka kawai Allah Ya sanya mata kaunar
yarinyar a zuciyarta. Duk inda ake neman kyau da nutsuwa, haiba da kamala to wannan yarinyar ta zarce, ga
shi da alamunta ilmi ya ratsata ta ko ina. Amma shirun da ta yi mata ya sanya ta diga mata ayar tambaya
(kuestion mark?). Ta sake maimaita mata tambayarta “Yammata daga ina kike ban gane ki ba?”
A sannan ne Mairo ta cira kai, wasu irin fararen idanu, gauraye da wani irin blue-blue suka haske Hajiyar, ta yi
wa Allah sarkin halitta tazbihi, ta tsarkake Shi, ta tsarkake iko da iyawarSa. Cikin sassanyan sautinta ta ce “Na
zo wurin Ilham ne”.
Ta ce “Ke kawarta ce halan? Don na ga kamar nasan fuskarki”.
Ta ce “Eh”. A takaice.
Ta ce “To amma kuwa na yi mamaki da ba ta kawo miki katin bikinta ba, an yi bikinta watanni uku da suka
wuce. Suna zaune a Wales din kasar Ingila inda mijinta ke karatu”.
Mairo ta ce “Allah Sarki, Allah Ya yi ba zamu hadu ba”.
Ta sake juyawa ta dubi hoton Uncle. Ta sake juyowa ta dubi mahaifiyarsa, wata irin soyayya da kauna na sake
mamayar zuciyarta. Ba ta ki ta zauna a nan tare da Hajiyar Junaidu ba, tana yi mata bauta, har karshen
rayuwarta koda Junaid ba zai aure ta ba. Wannan ita ce kauna ta hakika, wadda ba a samunta a wannan
zamanin. Da gaske Junaid ya yi mata nisan da ba tasan ranar da zata kamo shi ba.
Tsigar jikinta ya tashi, ganinta ya dushe, wani duhu ya gilma mata ta daina ganin abin da ke gabanta na wucin
gadi.
Hajiyar ba ta lura ba, don a lokacin hankalinta ya tafi ga amsa kiran wayar da ya shigo mata yanzu-yanzu. Ta
mike tana gyara lullubinta ayayinda ta fuskanci da Uncle Hajiyar ke magana. Hajiyar ta yi mata alama da
hannu ta jirayeta. Sai da ta gama wayar ta ajiyeta akan centre table, ta ce da Mairo “dan jiraye ni ina zuwa”.
Ta koma matattakalar da ta fito, jim kadan ta dawo da leda mai tambarin shagon country mall ta mika mata.
Mairo ta girgiza kai alamar ba zata karba ba, don tasan ko ta karba rabon su Ladidi ne, dama ace za su gode
ne, to a’a, zagi da bakar magana ne zai biyo baya.
Hajiyar ta ce “Ni ba babarki ba ce? Ba zan yi miki ihsani ki karba ba?”
Ta sake kai dubanta ga Uncle Junaid da ke cikin hoto yana murmushi. Sai ta ga kamar ya turbune mata fuska,
cikin rashin jin dadi. Ta maido ga dubanta ga Hajiyar, kallonta ta ke tsakaninta da Allah da matsananciyar
kauna cikin kwayar idanunta.
Ji ta yi kamar ta kwantar da kai a kafadunta ta yi kukan da ke cin ranta, ta gaya mata matsananciyar kaunar
danta da Allah Ya dora mata. Ta ji dumin da Junaid ya ji, a jikin wannan nagartacciyar UWA, ganin hawaye na
neman tona mata asiri ta yi hamzarin karba ta ce “Na gode”.
Har ta kai bakin kofa zata fita, Hajiyar ta kirata jikinta a sanyaye, don daga dukkan alamu akwai abin da ke
damun wannan yarinya, ta ce “Har za ki tafi, ba ki gaya min sunanki ba, idan Ilham din ta yi waya in gaya
mata”.
Mairo ta ce
“Ki ce mata Maryam ce”.
“Maryam-Maryam!” Tana ji a bakin su Ilham, amma a wannan karon Allah bai bata ikon ganewa ba.
Har yarinyar ta fita, ba ta motsa daga inda ta ke ba, ta dade tana tunanin inda tasan yarinyar. Mai yasa ba ta
tambaye ta daga inda ta ke ba? To akan me zata tambaye ta? Don kwaita zo wajen Ilham? Amsar shi ne, don
zuciyarta tana sonta. Ta koma falon ta zauna cike da tunani.
Sai ana kiran isha’i ta iso gida, Baffa na alwalar sallah a nan kofar gida, ta tube takalminta sannan ta wuce shi,
zuciyarta cike da jin haushin dadewar da ta yi. Ya ce “Ban ce kada ki kai dare ba Mairo?”
Cikin matsanancin ladabi ta rausayar da kai tace “Ka yi hakuri Baffa, mota ce ban samu da wuri ba”.
Ya ce “Ni dai duk inda za a je aje ido na ganin ido, amma bana son ayi dare. Idan kin shiga ki turo min Lawan”.
Ta ce “To”.
Habiba na kwasar tuwon dare sanda ta shigo, ta dago kai ta dube ta a ranta ta ce, “Kai wannan yarinya da
kashin arziki ta ke, kullum ta fita ba ta dawowa haka nan, sai bakin jini har yau babu wanda ya taba sallama
da ita, duk kyawun nan nata. Ladidi kuwa kullum idan mutum biyu ba su yi sallama da ita ba, hudu za su yi”.
Ta dubi Lawan wanda ke bin ledar hannunta da kallo, ta ce “Ka je Baffa na kira”.
Ya ce “In an ki fa?”
Ba ta yi magana ba ta wuce wajen Habiba ta durkusa ta ce “Mama Na dawo, sannunku da aiki”.
Lawan ya ce “Wani feleke wai ‘Baffa’, mu ‘Baba’ mu ke cewa Babanmu, ba wani Baffa ba. Wai mama yarinyar
nan ta fara bin maza ne ta ke shigowa gidan nan da manyan ledoji?”
Habiba ta ce “Idan ta bi sun ina ruwanka, ko mace ba don namiji aka halicceta ba? Me muka samu ne Mairo?
Miko nan in gani”.
Ta mika mata ledar ta tusa karkashin kujerar da ta ke zaune kada Hajara ta fito ta gani, ta ce sai an raba da
ita.
Ta dauki tuwon da ta saka mata a wani kwano duk lamba, ta zuba miyar karkashi akai ta mika mata. Ta karba
ta wuce daki cike da takaici.
Ashe wani takaicin ke jiranta. Tana sanya kai dakin wani mugun karni ya dake ta. Ladidi ta kelaya amai tun
daga bakin kofa har bakin katifarsu. Tana kwance a katifa tana barci kamar mushe ba abin da ya dame ta. Ta
fita ta dauko tsintsiya da abin kwashewa ta soma aikin aman kamar zuciyarta ta yo waje don bakin ciki.
Tuwon da ba ta iya ci ba ke nan sabida karnin da dakin ke yi, haka ta kwana da yunwa.
Washegari Ladidi da kanta abin duniya ya ishe ta, ta rarrafa katifar Mairo ta tashe ta, misalin karfe bakwai na
safe. Mairo ta bude ido tana kallonta, yawu ya ciko mata baki ta juya bayan kofa ta tsartar ta ce
“Zo ki raka ni asibitin don Allah, na kasa gane abin da ke damuna, amma da gaske ba ni da lafiya”.
Sai Mairon ta ce “Ki fara zuwa ki tambayo mama tukunna, idan ta amince sai na rakaki”.
Ta ce “Rabu da ita kawai, zo mu fice tana daki”.
Mairo ta ce “A’ah, ba za a yi haka da ni ba”.
Ba da son ran Ladidin ba ta fita ta tambayo Habiba za su je asibiti. Habiba ta dubi diyarta ta ce “Bana so ku
dinga jerawa ne kada a ga muninki”.
Ladidin ta kyabe baki, ta ce “Lallai ma Mama, ni ce ma mummunar?”
Habiba ta ce “Sai idan ba ku jera da wannan mai kama da aljannun ba”.
Ladidi ta ce “Ke wannan ya dama, ni da munin nawa dai ai na fi ta farin jini, kin taba jin ko bera ya aiko yana
sallama da ita?”
Ta ce “Haka kuwa, ku je sai kun dawo”.
Suna tafe a gefen hanya har asibitin Murtala, Mairo ta yanko mata kati suka hau layi. Suna nan zaune har aka
kirasu
B
Sun isa Minjibir ana sallar azahar, zuwan da ya tuna musu da dabdalar kuruciyarsu. Shekaru shida cur, cikin
dalibtaka da al’amura masu dama, da suka faru cikin rayuwarsu, suka tuno Kausar suka yi mata addu’a. Suka
karasa Edam office suka amso sakamakonsu. Ba abin da suka fadi, sun cinye sun lashe 9 credits ris. Ina ma
Uncle na nan, ya zo ya ga girbin abin da ya shuka?
Nabilah ta kasa daurewa ta tambayi Mr. Kayode malamin lissafinsu, ko ina Uncle Junaidu? Cike da alhini ya ke
sanar da ita cewa, “Yau watanninsa uku kenan da tafiya karo karatu (in-serbice) zuwa kasar Russia (Ukhrain).
Yana daga cikin malaman da federal ta dauki nauyin karo karatunsu a kasashen duniya talatin da biyar”.
Mairo ta samu wani kututturen bishiya ta zauna ta yi kukanta mai isarta, kuka irin wanda ba ta taba yi ba a
rayuwarta, ko a rashin iyayenta kuwa. Ta tabbatar wani bigiren nata ya kuma faduwa. Ta dubi takardunta,
wahalar shekaru shidda da Uncle ya yi, yau ga shi Allah Ya cika mishi burinsa, amma ashe ba zai gani ba.
Kuka ta ke kukan sabo, soyayya da kewa. Ta tabbatar ta rabu da Junaidu ke nan har abada! Ya yi mata nisan
da ba zata taba kamo shi ba. ALHERINSA da kyautayinsa masu yawa ne a gareta da ba zata taba mantawa ba.
Soyayyarsa da kaunarsa wani abu ne da ba zai taba gushewa daga zuciyarta ba. Shi kadai ta fara so, kuma shi
kadai zata ci gaba da so har zuwa karshen rayuwarta, yana sonta ko ba ya sonta. Ta tabbatar ita ke son Uncle,
amma shi ba hakan ba ne a zuciyarsa ba, ai yasan inda zai same ta, da yana sonta da ya neme ta.
Ciwon kana so ba a sonka, matukar ciwo ne da shi. Ya san ba ta da kowa a duniya a halin yanzu, daga Baffa sai
shi, amma ya yi mata haka, ya ki tallafar rayuwarta a dai-dai lokacin da ta fi bukatar tallafinsa. Ta kullaci Uncle
Junaidu kullata mai tsanani, irin kullatar da ta yi wa Habibu tare da alkawarta wa ranta yin kokari ta yakice shi
daga zuciyarta, ta fuskanci rayuwa ta karbeta a duk yadda ta zo mata…..!!!
*** ***
B
ikin Nabilah bai yi armashi ba, sabida amaryar da angon duk sun ki ba da hadin kai, sai iyaye da ‘yan uwa ke ta
sha’aninsu cikin farin ciki. Ko yaushe Mairo na tare da Nabilah, don ita kadai ce zata yi mata magana ta ji.
Abinci ma sai Mairo ta lallashe ta sannan za ta ci, don wai fushi ta ke da Momi da Daddy. Ranar lahadi aka kai
amarya gidanta da ke Nassarawa GRA. Tana kuka, Mairo na yi suka rabu, don wata irin kauna ce shakikiya
Allah Ya hada a tsakaninsu.
Mairo ta dawo gida, ta kwanta a yagulalliyar katifarsu. Ta runtse idonta tana tunanin al’amuran rayuwa. Yau
dai ga Nabilah ta yi aure ta barta, ita kuma ko sai yaushe ne Allah Zai kawo mata nata Mr. Right din? Tunda
Uncle ba ya sonta? A zahiri aure ta ke so, ba kuma da kowa ba da UNCLE JUNAIDU. Karatun ya fice mata a rai,
tunda babu Junaidu mai karfafawa. Tana daga cikin halittattun mata masu tsananin bukatar da namiji, amma
ba da kowa ba, da wanda ruhi, zuciya da gangar jikin su ke so. Haka kawai tunanin unguwar GALADANCHI ta
fado mata a rai. Idan har ba kuskure ta yi a tunaninta ba, Uncle ya taba gaya mata shi dan unguwar
Galadanchi ne, da ke cikin birnin Kano. To idan ta je Galadanchi ta ce tana neman waye? Alhalin ma an ce
Uncle Junaidu yana Russia? Zata je ta nemi gidan su Uncle, iyayenshi da ‘yan uwanshi musamman Ilham, wai
an ce Gaida mai gaisheka…!’
Zumbur ta mike, ta jona ruwa a heater tana jiran ya yi dumi ta yi wanka, sabida sanyin da ake cikin watan
Junairu.
Daga can gefe Ladidi ta tashi tana yatsina fuska, ba a jima ba kuma ta soma kelaya amai a tsakar dakin. Mairo
na yi mata sannu amma ko kallonta ba ta yi ba. Ta gama aman ko kurkure baki babu ta koma ta kwanta.
Mairo ta dauko tsintsiya da abin kwashe shara ta soma gyara wajen don tasan idan ta Ladidi ne, to a bar
wajen a haka,. Ta dauko tsumma da omo klin ta goge dakin tas! Ta kunna turaren wuta na tsinke.
Idan ba ta manta ba wannan aman Ladidi na shidda ke nan cikin kwana uku, amma ko tunanin ta je asibiti ba
ta yi. Ta matsa jikinta a hankali, abinki da dan uwa, ta ce, “Ladidi ki shirya na rakaki asibiti mana, ko magani ne
a baki, wannan aman ya tsaya?”
Ta yi shiru ba ta ce uffan ba, kuma ba ta kalle ta ba, can kuma ko mai ta tuna? Ta ce “Mu je”.
A gurguje ta yi wankan ta fito, Ladidi ko wanka babu suka fito. Habiba na tsakar gida ta daga ido ta dube su.
Wani irin kishi da bakin-ciki ya tushe mata a kahon zucci, ganin irin kyau da kwarjini na musamman a fuskar
Mairo tamkar diyar larabawan Turkiya. Ladidi kuwa kamar a rufe ido don muni da rashin tsafta.
Ta ce “Ke Ladidi, ina zaki je da wannan mai kama da kabewar?”
Ta kyabe baki kamar yadda ya ke a al’adarta, ta ce “Asibiti wai zata kai ni”.
“Ciwon me kike da za a kai ki asibiti?”
Ta sake kyabe bakin ta ce “Wai don ina amai, ko ta gaji da kwashewa ne? Oho!”.
Ta gallowa Mairo harara ta ce “Kin ga ni bana son kinbibi da son nuna iyawa, waye ba ya amai idan ya ci abin
da ranshi bai so ba? Wuce da Allah ki ba ni waje, ke kuma ungo goro ki ci tashin zuciyar zai lafa”.
Mairo ta koma daki tana jinjina hali irin na Habiba. Karfe biyar na yamma ta ji karar motar Baffa tabbacin ya
dawo. Sai da ta ba shi lokaci ya kimtsa sannan ta je dakinsa, ta same shi yana cin abinci ga Hajara da autarta
Umma a gefe, ban da harararta ba abin da Hajara ke yi, amma ita ba ta kula ba, tsugunnawa ta yi har kasa ta
gaida Baffan, ya amsa cikin walwala, ya ce “Yaya dai Mairo, babu wata matsala ince ko?”
Kanta a kasa ta ce “Babu Baffa, ina so in je Galadanchi ne”.
Bai tambayi wajen wanda zata ba, ya dauko naira dari biyu a aljihunsa ya mika mata, ya ce “Ga shi ayi kudin
mota, amma kada ki bari dare ya riske ki waje”.
Ta ce “Insha Allahu Baffa”.
Mairo tana tafe tana tunanin rigima irin tata, ya za a yi ta nemi gidansu Uncle alhalin ba tasan komi a kanshi
ba? Ace ma ta sani, me zata je ta ce, kuma me zata je ta yi? Wata zuciyar ta ce “Gaida mahaifiyarsa kamar
yadda yake gaida naki”. Wannan tunani ne mai kyau.
Ta fito daga Yakasai zuwa Bakin Rimi, ta tari tasi ta ce “Galadanchi”. Ya bude mata kofa ta shiga.
Ba a fi minti goma ba ya sauke ta a unguwar Galadanchi. Ta fito ta ba shi dari biyun Baffa ya ba ta canji, ta
gangara dai-dai makarantar gidan Galadima ta tsaya nan tana rarraba ido, ta rasa wanda zata tambaya.
Daga can gefe wajen masallaci dandazon matasa ne a zaune suna haramar shiga sallar magriba, ba zata iya
shiga cikin wadannan samarin ba don haka ta ci gaba da tsayuwa cikin rashin sanin abin yi. Tana nan tsaye
wani saurayi ya zo gittawa ta gabanta ta yi mishi sallama, ya juyo ya amsa, ta ce “Don Allah Yayana tambaya
nake”.
Ya ce “Allah Ya sa na sani kanwata”.
Ta ce “Gidan su Junaid nake tambaya”.
Ya ce “Junaid? Ya ya sunan maigidan?”
“Gaskiya ban sani ba”.
“Babba ne ko yaro ne?”
“Babba ne, don zai girme ka”.
Ya yi dan tunani “Kwatanta min shi”.
Nan ta shiga kwatanta mishi, ya ce “Ke ko gidan Justice Atiku kike tambaya?”
Kwarai ta taba jin sunan Chief Justice Atiku Galadanchi a bakin Kausar mai rasuwa, (Alkalin-alkalai) na Jihar
Kano. Ta ce “Ina jin nan ne”.
Ya ce “Mu je na nuna miki”.
Abinka da karamar unguwa, kowa yasan kowa. Ya yi mata nuni da gida ginin manyan ‘yan bokon da, mai
malalen suminti, dakali biyu sun sa gidan a tsakiya, ko ina a share tas ko tsinke babu. Ta yi wa saurayin godiya
ta sa kai zauren gidan.
Ashe yadda wajen yake ba haka cikin gidan yake ba, cikin gidan gini ne sosai na zamani, mai ban al’ajabi,
sabida yadda aka kwalmada karfe da rodi aka yi irin wannan ginin ba kasafai ake samun irinshi cikin Nijeriya
ba. Ko’ina gilashi sai daukar ido yake hatta kofar shiga falon gidan ta gilashi ce. Ta tsaya a kofar falon tana
sallama.
Wata dattijuwa da alama mai aiki ce, ta fito tana mata kallon rashin sani. Mairo ta tsugunna ta gaishe ta, ta
amsa, ta ce “Yammata wa kike nema?”
Ta ce “Babar su Ilham”.
Ta bude mata kofar falon, ta ce “Zauna a nan, Hajiya tana zuwa yanzu”.
Ba ta zauna a kujerar ba, a kan wani tattausan kilishi da ke tsakiyar dakin ta zauna. Talabijin na ta aiki cikin
tasoshin tauraron dan Adam. In banda kamshin turaren wuta na (Bakhour) ba abin da ke tashi a falon,
gauraye da ni’imtaccen sanyin na’urar sanyaya daki duk da sanyin da ake fama da shi kuwa.
Ta daga kai a hankali zuwa gabas maso kudu na dakin. Tangamemen hoton Uncle Junaidu ya yi mata sallama,
yana murmushi. Wata matsananciyar faduwar gaba ta same ta, ta kura mishi ido ba ta ko kyaftawa. Dai-dai
lokacin da ta ji muryar Hajiyar tana yi mata sallama.
Ta daga kai ta kai dubanta ga mahaifiyar Uncle Junaidu. Nan ta ga inda Junaid ya debo kyau, tsurarsa. Mace
ce ma’abociyar zati da kamala gami da gogayya cikin zuzzurfan ilmin boko. A idanunta farin gilashi ne
(medicated). A kiyasce zata yi shekaru hamsin. Amma a idaniyarka ba zata fi shekaru talatin da biyar ba.
Ta zauna a kujera fuska cike da annuri, Mairo ta duka tana gayas da ita. Ta amsa cikin murmushi ta ce,
“Yammata daga ina? Ban gane ki ba”.
Itama Mairon sai ta rasa abin da zata ce. Wata zuciyar ta ce “Akul! Kika ce danta kika zo nema, wannan ba
mutumcin diya mace ba ne. Kin zo ki gaishe ta ne sabida Allah, da kuma soyayyar danta da Allah Ya dasa miki.
Amma ba don kamun kafar neman soyayyar ba”.
Hajiyar ta sa mata ido tana nazarinta, ta rasa inda ta san fuskar. Haka kawai Allah Ya sanya mata kaunar
yarinyar a zuciyarta. Duk inda ake neman kyau da nutsuwa, haiba da kamala to wannan yarinyar ta zarce, ga
shi da alamunta ilmi ya ratsata ta ko ina. Amma shirun da ta yi mata ya sanya ta diga mata ayar tambaya
(kuestion mark?). Ta sake maimaita mata tambayarta “Yammata daga ina kike ban gane ki ba?”
A sannan ne Mairo ta cira kai, wasu irin fararen idanu, gauraye da wani irin blue-blue suka haske Hajiyar, ta yi
wa Allah sarkin halitta tazbihi, ta tsarkake Shi, ta tsarkake iko da iyawarSa. Cikin sassanyan sautinta ta ce “Na
zo wurin Ilham ne”.
Ta ce “Ke kawarta ce halan? Don na ga kamar nasan fuskarki”.
Ta ce “Eh”. A takaice.
Ta ce “To amma kuwa na yi mamaki da ba ta kawo miki katin bikinta ba, an yi bikinta watanni uku da suka
wuce. Suna zaune a Wales din kasar Ingila inda mijinta ke karatu”.
Mairo ta ce “Allah Sarki, Allah Ya yi ba zamu hadu ba”.
Ta sake juyawa ta dubi hoton Uncle. Ta sake juyowa ta dubi mahaifiyarsa, wata irin soyayya da kauna na sake
mamayar zuciyarta. Ba ta ki ta zauna a nan tare da Hajiyar Junaidu ba, tana yi mata bauta, har karshen
rayuwarta koda Junaid ba zai aure ta ba. Wannan ita ce kauna ta hakika, wadda ba a samunta a wannan
zamanin. Da gaske Junaid ya yi mata nisan da ba tasan ranar da zata kamo shi ba.
Tsigar jikinta ya tashi, ganinta ya dushe, wani duhu ya gilma mata ta daina ganin abin da ke gabanta na wucin
gadi.
Hajiyar ba ta lura ba, don a lokacin hankalinta ya tafi ga amsa kiran wayar da ya shigo mata yanzu-yanzu. Ta
mike tana gyara lullubinta ayayinda ta fuskanci da Uncle Hajiyar ke magana. Hajiyar ta yi mata alama da
hannu ta jirayeta. Sai da ta gama wayar ta ajiyeta akan centre table, ta ce da Mairo “dan jiraye ni ina zuwa”.
Ta koma matattakalar da ta fito, jim kadan ta dawo da leda mai tambarin shagon country mall ta mika mata.
Mairo ta girgiza kai alamar ba zata karba ba, don tasan ko ta karba rabon su Ladidi ne, dama ace za su gode
ne, to a’a, zagi da bakar magana ne zai biyo baya.
Hajiyar ta ce “Ni ba babarki ba ce? Ba zan yi miki ihsani ki karba ba?”
Ta sake kai dubanta ga Uncle Junaid da ke cikin hoto yana murmushi. Sai ta ga kamar ya turbune mata fuska,
cikin rashin jin dadi. Ta maido ga dubanta ga Hajiyar, kallonta ta ke tsakaninta da Allah da matsananciyar
kauna cikin kwayar idanunta.
Ji ta yi kamar ta kwantar da kai a kafadunta ta yi kukan da ke cin ranta, ta gaya mata matsananciyar kaunar
danta da Allah Ya dora mata. Ta ji dumin da Junaid ya ji, a jikin wannan nagartacciyar UWA, ganin hawaye na
neman tona mata asiri ta yi hamzarin karba ta ce “Na gode”.
Har ta kai bakin kofa zata fita, Hajiyar ta kirata jikinta a sanyaye, don daga dukkan alamu akwai abin da ke
damun wannan yarinya, ta ce “Har za ki tafi, ba ki gaya min sunanki ba, idan Ilham din ta yi waya in gaya
mata”.
Mairo ta ce
“Ki ce mata Maryam ce”.
“Maryam-Maryam!” Tana ji a bakin su Ilham, amma a wannan karon Allah bai bata ikon ganewa ba.
Har yarinyar ta fita, ba ta motsa daga inda ta ke ba, ta dade tana tunanin inda tasan yarinyar. Mai yasa ba ta
tambaye ta daga inda ta ke ba? To akan me zata tambaye ta? Don kwaita zo wajen Ilham? Amsar shi ne, don
zuciyarta tana sonta. Ta koma falon ta zauna cike da tunani.
Sai ana kiran isha’i ta iso gida, Baffa na alwalar sallah a nan kofar gida, ta tube takalminta sannan ta wuce shi,
zuciyarta cike da jin haushin dadewar da ta yi. Ya ce “Ban ce kada ki kai dare ba Mairo?”
Cikin matsanancin ladabi ta rausayar da kai tace “Ka yi hakuri Baffa, mota ce ban samu da wuri ba”.
Ya ce “Ni dai duk inda za a je aje ido na ganin ido, amma bana son ayi dare. Idan kin shiga ki turo min Lawan”.
Ta ce “To”.
Habiba na kwasar tuwon dare sanda ta shigo, ta dago kai ta dube ta a ranta ta ce, “Kai wannan yarinya da
kashin arziki ta ke, kullum ta fita ba ta dawowa haka nan, sai bakin jini har yau babu wanda ya taba sallama
da ita, duk kyawun nan nata. Ladidi kuwa kullum idan mutum biyu ba su yi sallama da ita ba, hudu za su yi”.
Ta dubi Lawan wanda ke bin ledar hannunta da kallo, ta ce “Ka je Baffa na kira”.
Ya ce “In an ki fa?”
Ba ta yi magana ba ta wuce wajen Habiba ta durkusa ta ce “Mama Na dawo, sannunku da aiki”.
Lawan ya ce “Wani feleke wai ‘Baffa’, mu ‘Baba’ mu ke cewa Babanmu, ba wani Baffa ba. Wai mama yarinyar
nan ta fara bin maza ne ta ke shigowa gidan nan da manyan ledoji?”
Habiba ta ce “Idan ta bi sun ina ruwanka, ko mace ba don namiji aka halicceta ba? Me muka samu ne Mairo?
Miko nan in gani”.
Ta mika mata ledar ta tusa karkashin kujerar da ta ke zaune kada Hajara ta fito ta gani, ta ce sai an raba da
ita.
Ta dauki tuwon da ta saka mata a wani kwano duk lamba, ta zuba miyar karkashi akai ta mika mata. Ta karba
ta wuce daki cike da takaici.
Ashe wani takaicin ke jiranta. Tana sanya kai dakin wani mugun karni ya dake ta. Ladidi ta kelaya amai tun
daga bakin kofa har bakin katifarsu. Tana kwance a katifa tana barci kamar mushe ba abin da ya dame ta. Ta
fita ta dauko tsintsiya da abin kwashewa ta soma aikin aman kamar zuciyarta ta yo waje don bakin ciki.
Tuwon da ba ta iya ci ba ke nan sabida karnin da dakin ke yi, haka ta kwana da yunwa.
Washegari Ladidi da kanta abin duniya ya ishe ta, ta rarrafa katifar Mairo ta tashe ta, misalin karfe bakwai na
safe. Mairo ta bude ido tana kallonta, yawu ya ciko mata baki ta juya bayan kofa ta tsartar ta ce
“Zo ki raka ni asibitin don Allah, na kasa gane abin da ke damuna, amma da gaske ba ni da lafiya”.
Sai Mairon ta ce “Ki fara zuwa ki tambayo mama tukunna, idan ta amince sai na rakaki”.
Ta ce “Rabu da ita kawai, zo mu fice tana daki”.
Mairo ta ce “A’ah, ba za a yi haka da ni ba”.
Ba da son ran Ladidin ba ta fita ta tambayo Habiba za su je asibiti. Habiba ta dubi diyarta ta ce “Bana so ku
dinga jerawa ne kada a ga muninki”.
Ladidin ta kyabe baki, ta ce “Lallai ma Mama, ni ce ma mummunar?”
Habiba ta ce “Sai idan ba ku jera da wannan mai kama da aljannun ba”.
Ladidi ta ce “Ke wannan ya dama, ni da munin nawa dai ai na fi ta farin jini, kin taba jin ko bera ya aiko yana
sallama da ita?”
Ta ce “Haka kuwa, ku je sai kun dawo”.
Suna tafe a gefen hanya har asibitin Murtala, Mairo ta yanko mata kati suka hau layi. Suna nan zaune har aka
kirasu
C
Likitan yana rubuce-rubuce a file lokacin da suka shiga, Mairo ta tsaya ta harde hannuwa a kirji a bakin kofa.
Ladidi ta karasa ta zauna a kujerar da marasa lafiya suke zama. Ya gama ya dube ta ta karkashin gilashinsa ya
ce “Me ke damunki?”
Ta ce “Ina fama da haraswa, zazzabi da ciwon kai mai tsanani, ga wani yawu da yake taruwar min a baki, bana
jin dadin bakina”.
Likitan ya dau abin awonsu ya sanya a hannunta yana sauraro, sannan ya yi rubutu a wata ‘yar takarda ya ce,
su je laboratory su kawo masa result. Suka fita suka tambayi lab aka nuna musu. Nan aka bai wa Ladidi robar
fitsari aka ce ta je toilet ta yi ta kawo. Nan da nan result ya fito suka koma ofishin likita. Ita dai Mairo tunda ta
ga an rubuta positibe hankalinta yai matukar tashi. Likitan ya dube su bayan ya duba takardar ya ce da Ladidi,
“Ina mijinki?”
Ladidi ta ce “Ba ni da aure”.
Ya kura mata ido na ‘yan sakonni ya ce, “Amma you are pragnant,(kinada juna biyu) watanni biyu cif?”
Ladidi ta fiddo ‘yan idanunta gaba daya suka yi kuru-kuru, wannan bai damu likitan ba ya ci gaba da aikin da
ke gabansa bayan ya rubuta mata magani a wata ‘yar takarda.
Suka fito jikin Mairo har rawa yake, saboda dimuwa da razana, ita kuwa Ladidi in banda kuka ba abin da ta ke,
wai likitan sharri yai mata, duk girman kan nan ta sauke shi tana rokon Mairo wai su je wani asibitin a sake
dubawa.
Mairo ta sa mata ido, ta ce “Wannan asibitin specialist ne, duk Kano daga Aminu Kano sai shi, hakikanin
gaskiya suka gaya miki. Don haka ni babu inda zan kuma zuwa”.
Ta yi shiru hawaye na zubar mata. Ba tausayin Ladidi ta ke ji ba, tausayin Alhaji Abbas ne, bawan Allah, Baffa
bai cancanci ‘ya’ya irin wadannan ba.
Sun kusa Yakasai Ladidi ta ce “Wallahi Mairo duk abin da kike so zan baki, ki rakani a zubar min da cikin, in
Baba ya ji wallahi-wallahi kashe ni zai yi”.
Mairo ta ce
“Ni kuwa mai za ki ba ni Ladidi in rakaki a kashe rai? Tukunna ma ni ban san inda ake zubar da ciki ba. Kin bata
wayonki! Amma bana tausayinki, Baffa nake tausayawa. Iyakacin tarbiyya da ilmi ya baku, daga boko har na
Arabiyyah, ya tsare muku cinku da shanku, da suttura dai-dai karfinshi. Bai cancanci wannan sakayyar daga
gare ku ba…..”
Ta kai gefen mayafinta ta share hawaye, ta fyace majina, ta ce “Ladidi ke kuwa mai ya kai ki ga yin haka? Idan
aure kike so mai yasa ba ki tsayar da daya cikin tulin samarin naki kin aura ba? Mai za ki ce da Baffa ranar da
ya gane kin yi cikin shege?”
Ladidi ta kufula wai Mairo ta ce ta yi cikin shege, ta ce “Kinga malama bana son wani dogon Turanci, idan ba
zaki rakani ba ne mu raba hanya, wancan karon ma da aka ce na yi cikin ai nasan inda na je aka kwakule shi.
Ko ance da ke kowa ma kidahumi ne, bakauye irinki? Mtsew!!!”
Ta yayyaga takardar likitan da takardar maganin, ta ce
“Ki je ki gayawa Baffan naki ya yi duk abin da zai yi kada ya barni da rai idan shi ne………..”
Mairo ta sanya ‘yan yatsu ta toshe kunnenta, ita kuma Ladidi ta tare dan A dai-daita sahu ta shige, ta ce, ya
kai ta Sabon Gari.
Tana shigowa gida Habiba ta ce “Ina kika baro Ladidin?”
Ba tare da ta dubeta ba ta ce “Tana zuwa yanzu”. Ta shige dakinsu ta danno kofa. Ta rasa inda zata sa kanta
da tausayin Baffa. Ta soma kuka kamar ita ce abin ya faru a kanta.
Wani sassanyan kamshi ya doki hancinta, irin wanda ba ta taba ji ba a rayuwarta. Daga nan ta jiyo muryar
Baffa yana salati, yana sallamewa. Ta sake saurarawa sosai sai ta ji ya ce “HABIBU? Wa nake gani kamar
Habibu?”
Tamkar wadda aka cakawa mashi. Ta ji wani kululun bakin ciki ya taso ya soketa a kahon zucci. Amma hakan
bai hanata mikewa ta fito ba, don gasgata kunnuwanta.
Wani magidanci ne dan kimanin shekaru talatin da takwas, wankan tarwada, mai zarkadeden dogon karan
hanci da yalwar idanu farare kal. Da ganin fuskarshi ka ga Malam Bedi, ta wani fannin kuma Alhaji Abbas sak!
Yana sanye da kaftan na shadda Getzner kar-kar da ita, baka wul! Dinkin tazarce, sumar kansa a kwance luf
baka sidik, kasancewar ba hula a kansa. Da gani babu tambaya, ka ga mutum da ya dama, ya kutsa cikin
ilmummuka daban-daban. Wasu kyawawan yara guda uku, maza biyu da mace daya, sai rarraba ido suke na
rashin sabo.
Mairo dai tana nan rike da labule tana kallonsu, wasu irin hawaye suka zubo mata, ta yi saurin sakin labulen
ganin zai juyo sashen da ta ke. Tana ji su Hajara duk suka firfito suna ta karadi da sallallami, ita kuwa ba ta
kara lekowa ba. Mai ya dawo da shi cikin rayuwarsu yanzun? Bayan masu bukatarshi sun shude a doron kasa?
Mai zai ce, mai zai yi, ya wanke mugun tabon da ya yi mata a zuciyarta?
Mairo kuka ta ke tamkar ranta zai fita, ba ta son ganin Habibu ko kadan a rayuwarta. Gara ta bar gidan, kada
ace da shi yana da ‘yar uwa, mai zai yi mata wanda ALLAH da UNCLE JUNAID ba su yi mata ba?
Ta soma harhada kayanta cikin jakarta da sauri-da-sauri, tana yi tana fyace hanci da hawaye duka. Ba ta
ankara ba sai ji ta yi Baffa na kwala mata kira daga tsakar gida “Mairo! Mairo!! Ko Mairo ba ta nan ne?”
Ta yi bakam, ta ki amsawa, ta jawo hijabinta ta zurma ta sungumi akwatinta ta yo waje, suka ci karo da Baffa
a bakin kofa.
Ya ce “Zo Mairo, yau ga Habibu Allah Ya dawo mana da shi”.
Ta sa kuka, ta ce “don Allah Baffa ka bani hanya in wuce, bana son ganinshi, ba abin da ya hada ni da shi. Idan
dai zai zauna a gidan nan to ni zan koma wajen Nabilah”.
Baffa ya ce “Haba Mairo, waye ba ya kuskure? Ki dinga yi wa dan Adam uzuri cikin kowanne hali, uzuri sau
saba’in, kafin ki kama shi da laifi. Ki saurare shi ki ji da wacce ya zo, sannan ki yanke mishi hukunci”.
Da haka ya lallabata suka nufi dakinshi, inda Habibu da su Habiba su ke.
Habibu ya hada kai da gwiwa sai kuka ya ke, kamar karamin yaro. Ba kuma kukan komai yake ba, sai kukan jin
rasuwar iyayensa daga bakin Habiba. Baffa ya fada su da fada kamar ya rufe su da duka “Ke kam Habiba ba ki
ji dadin halinki ba, ko ruwa ba ki barshi ya kurba ba zaki ce Uwa da Uba sun mutu, gatsar, babu sakayawa,
babu nuni da daukan hakuri da YAKANAH (Sunan Littafin TAKORI mai zuwa). Ku tashi ku fita ku ba ni waje,
iyayen banza, wadanda ban san yaushe za su san Annabi Ya faku ba”.
Sum-sum-sum suka mike suka fita. Habibu ya dago kai yana kallon Mairo. Kyakkyawar budurwa ‘yar shekara
sha takwas, wadda ya tafi ya bari tana shekaru takwas. Ita ma ta kalle shi cikin ido, sai kuma ta dauke kanta.
Ta daure fuska sosai. Ya ce “Mairo Yaya Habibun?” Sai ta fada jikinsa ta sa kukan da ke cinta a zucci.
Allah Ya riga ya halicci zuciyarta da kaunar Habibu, babu yadda zata yi, shi ne dolenta a rayuwa. Suka
rungume juna suka yi ta kuka, Baffa ma tunanin dan uwansa ya dawo masa sabo. Ya soma share ido da habar
babbar rigarsa.
Sai da suka yi kukansu mai isarsu, sannan Baffan ya soma lallashinsu. Ya ce “Ni ina nan Habibu, zan zame
muku uwa, uba, kuma abokin shawara. Dukkaninmu na haka ne, kowa jiran wa’adinsa ya ke”.
Habibu ya ce “Kaicona Baffa! Dukiyar da na zauna ina tarawa don Baba ya daina noma, Inna ta daina girki da
icce, Mairo ta yi karatu mai kyau sun tashi a banza!
Na kintata ne zuwa sanda zata gama sakandire sannan in dawo, ashe bazan tadda Baba da Inna ba, sannan
Mairon ba ta ji dadin dawowata ba!!”
Baffa ya ce “Wai haka Mairo? Ba ki ji dadin dawowarsa ba in sallame shi?”
Ta yi murmushi, ta sake sunne kanta a kirjin Yaya Habibun. Ya ja karan hancinta, ya ce “Ko kallon ‘ya’yanki ba
ki yi ba, balle mai sunanki, mai kama da ke”.
Sai a lokacin hankalinta ya koma ga yaran. Cikin murmushin kaunarsu da ta mamaye zuciyarta farat daya, ta
ce “Ya’yanka ne Yaya Habibu?”
Ya gyada mata kai, “Ya’yana ne. Na yi aure da mamarsu tun sanda na kammala karatun digiri na farko. Ga
Abbas, ga Muhammad (Bedi), sannan ga Mairo”.
Baffa ya yi murmushi, ya ce “Taho takwarana”.
Abbas ya matsa gare shi, dan kimanin shekaru hudu, Muhammad shidda, Mairo kuma ‘yar shekara biyu ce.
Babban wato Muhammad ya ce “Daddy wannan ne Babanka?”
Ya ce “Eh, shi ne Babana”.
Ya kuma cewa, “Wannan ce Aunty Mairo?”
Ya ce “Eh ita ce Aunty Mairo”.
Ya matso jikin Mairo ya jingina da kafadunta, ita kuma sai kokarin daukar takwararta ta ke, amma ta ki, ta like
jikin babanta. Ya ce “Ai ita kiwar tsiya gare ta, wanda yake kulaki ba ki kula shi ba”.
Ta yi murmushi ta ce “Abbana, Muhammad”.
Ya yi murmushi ya ce “Anti Mairo za ki je gidanmu?”
Ta ce “Insha Allahu”.
“Za ki yi min tatsuniyya ta gizo da koki irin wadda Daddy ke mana?”
Ta ce “A’ah, ni ban iya tatsuniya ba, ni sai dai na karanta maka labarin jaruman maza, irin su Ilya dan mai karfi,
da Malukussaif Ibn Ziyyazanun”.
Ya yi dariya ya ce “Ni kuma zan tuka ki a jirgina (helcopter) wanda Daddy ya sayo min”.
Ta rungume shi ta ce “To Abbana”.
Baffa ya ce “Amma Habibu na yi mamaki da ka iya yin wadannan shekarun ba ka waiwayi gida ba, ko gaisuwa
ce ai ka aiko mana, idan ba ka zo ba (a lokacin ba kowa ke da wayar hannu ba, sai wane da wane)”.
Habibu ya ce “Kuskuren da na yi ke nan, amma kusan kullum ba a rasa masu zuwa Najeriya daga Malaysia. To
sai dai ita kanta Maleshiyar na dade da barinta, tun bayan da na kammala karatun digirina na farko.
Dina abokiyar karatuna ce, diyar Ambassadan Nijeriya a kasar Maleshiya. Mun dade muna soyayya,
mahaifinta ya so mu dawo gida ayi auren gaban iyayena, na nuna masa ni ba yanzu zan koma gida ba, ina da
babban uzurin da ya rabo ni da gida, idan na koma mawuyaci ne Babana ya barni na dawo. Don haka ya tsaya
tsayin daka har muka yi aure.
Da taimakon mahaifinta na samu aiki na wucin gadi (temporary) ina yi a wani kamfanin kera takalman fata.
Na dade ina aiki a nan kuma na samu alheri yadda ba kwa zato. Daga baya wani abokina Amiru da taimakon
mahaifinsa ya yi min hanyar da na samu gurbin karo karatu a Michigan din Amurka, akan kwamfuta da duk
abin da ya shafe ta. Ina gamawa ba da jimawa ba na samu aiki a Bankin Barclays reshen kasar Amurka, don
haka muka koma can. A can aka haifi Alhaji da Mairo, Muhd ne kadai aka haifa a Kuala-Lampur (Malaysia). To
kun ji, don haka bazan dade ba, don wajen aikina suna bukatana, ina so zan tafi da Mairo”.
Mairo ta yi azamar dago kai ta dube shi, da gaske ya ke ko wasa ya ke? Babu alamun wasa ko kankani a fuskar
Habibun. Shi kuma ya kafa mata ido cike da tsoron, kada ta ce ba zata zauna da shi ba. Shi kam nan duniya bai
ga abin da zai sake raba shi da ‘yar uwarshi ba, wadda ta rage mishi kwal a duniya. Baffa ya ce, “Anya a yi
haka? Ni dai na fi so inyi mata aure, hankalina zai fi kwanciya. In lissafina dai-dai ne shekarunta goma sha
takwas cif, aure shi ne ya dace da ita”.
Cikin murmushi Habibu ya ce “Ta fitar da mijin ne?” Ya fadi yana kallon Mairon, ta yi hamzarin sunkuyar da
kanta. Baffa ya ce, “A’ah, ita ko zancen nan da samari irin na su Ladidi ba ta yi, idan ka ganta ta fita, to
muhimmin abu ne ya fitar da ita. Amma akwai wani abokina Alh. Salisu da ya yi min maganarta tun wancan
watan na ce ya dakace ni sai na yi shawara da ita tukunna”.
Habibu ya ce “Har nawa Mairon ta ke? Ka yi hakuri Baffa ka ba ni ita makaranta zan sa ta, idan ta soma ko ba
ta kare ba idan mijin ya fito sai a yi auren, amma Alh. Salisu ai ya yi mata tsufa”.
Baffa ya ce “Ni ma abin da na yi la’akari dashi kenan, shi yasa ban baiwa zancen wani muhimmanci ba, sai ka
yi mata fasfo ku tafi, Allah Ya sa hakan shi ne alkhairinta”.
Habibu ya ce “Amin”. Ya dubi Mairo ya ga ta sunkuyar da kai, ba ta dago ba ya ce “Mairo ko ba kya son zama
da ni da ‘ya’yanki?”
Ta yi murmushi ta ce “Mamarsu zata yarda?”
Shi ma ya tayata murmushin, ya ce “Kada ki damu. Dina mace ce mai fahimta, ga kirki da hankali. Na yi mata
kyakkyawar shaida. Ta sanki, ta san labarinki ba tun yau ba. Ta fi ni damuwa da a dauko ki, ina gaya mata
akwai lokacin da nake jiran isowarsa ga shi Allah Ya kawo”.
Baffa ya ce “Ita tana ina?”
Ya ce “Tana garin Dutsinma, can home town dinsu, gobe insha Allah zan je na dauko ta”.
Rahma diyar Hajara ta shigo da kular abinci da farantai ta aje ta fita, Mairo ta matso ta zubawa Habibu, ya
karba yana cewa, “Yaushe rabona da cin dan wake?”
Baffa ya yi dariya ya ce “Ai ga Mairo nan sai ta dinga yi maka dan wake, idan matarka ba ta iya ba”.
Ya ce, “Tana yi min na fulawa (gudun kurna), amma ba irin shi nake so ba, wannan da ake yi da rogo da kuka
shi na fi so, don ya fi sulbi, yafi saukin wucewa a makogaro”.
Mairo ta zuba filet daya da yaran ta ja su suna ci, Baffa na bai wa Habibu labarin bayan rabo. Habibu ya
kammala ya ajiye farantin, ya tsiyayi ruwa a jug ya sha, ya ce “Na zo da ma’aikata Baffa, gobe insha Allahu za a
rushe gidannan a yi ginin zamani yadda su Inna Habiba da sauran yara za su fi sakewa”.
Baffa ya yi murmushi ya ce “Allah Ya ba da iko Habibu”.
Ya juya ga Mairo ya ce “Je ki share min dakina na zaure, anan zan sauka zuwa gobe, yaran ki kwana da su, ni
zan shiga cikin gari wajen tsoffin aminai, gobe idan Allah Ya kaimu sai mu je can immigration maganar fasfo”.
Ta ce “Ita kuma Anti Dinan a ina zata sauka idan ta zo?”
Ya ce “Tana da inda ya fi nan ne? Duk nan zamu sauka”.
Ta tasa yaran a gaba suka nufi cikin gida. Habiba da Hajara dai duk kunyar Habibu ta ishe su, sakamakon
rashin arzikin da suka san suna yi wa Mairo. Ba su taba zaton Habibu zai dawo ba, ga wata irin galleliyar mota
da ya iso da ita mai nuni da lallai Habibu ya kama kasa, ga ‘ya’ya firda-firda kamar ‘ya’yan kajin gidan gona, da
gani babu tambaya iyayensu sun gama samun nasibin rayuwa.
Habiba ta karbi ‘yar daga hannun Mairo, ta sa zani ta goyata, ta ce da Mairo “Ladidi har yanzu shiru, ina kika
barota ne?”
Ta ce “Tana can asibitin ta ce zata dan jima”.
Baffa ya fita ya dawo da gyararrun kaji guda goma, ya ce a yi wa Habibu girki. Mairo ta je ta share dakin
Habibun da ke soro, ta kunna turaren wuta ta gyare ko’ina. Ta shigar da kayan Habibun, bayan ta ware kayan
yaran. Daga Hajara har Habiba sun shiga hankalinsu musamman ganin yadda ake sauke buhunhunan
shinkafa, katon-katon na taliya, garewanin mai, katon na juices, na gwangwani da na kwali, buhunan sugar,
doya, dankali da sauransu, duk aka jibge musu a store.
Ladidi ba ta dawo gidan ba sai dare, wujiga-wujiga da ita, ba wanda ya ga shigowarta sai Mairo don duk sun yi
barci, ta lallaba ta kwanta a katifarta, ga dukkan alamu ta je an cire mata cikin. Ladidi sai ta daina bai wa
Mairo mamaki, ta koma ba ta tsoro.
Washegari ta shirya ta yi wa yaran wanka ta shirya su, Hajara ta ba su abin kari koko ne da kosai da agada, da
suka kammala suka tadda Habibu a dakin Baffa suna kalaci shi da Baffan. Yaran suka nufi Babansu suka
baibaye shi, ya ce “Ba ku gaida Baffa ba Muhammad”.
Suka hada baki suka ce, “Baffa ina wuni?”
Ya ce “Ina kwana dai takwara na, kamar ba haihuwar Turai ba, Hausa ras a bakinku”.
Habibu ya ce “Ai ni bana yi musu Turanci, Mamarsu ce ta ke musu. Ita ma ina hanata don kowa yabar gida
gida ya barshi”.
Baffa ya ce “Wannan haka ya ke, Allah Ya raya mana su cikin addinin islam, amin”.
Suka bar yaran wurin Habiba, suka nufi Immigration office, can hanyar farm center cikin dan lokaci aka yi wa
Mairo passport aka ce su dawo bayan kwana uku su karba.
A hanyarsu ta dawowa Habibu yana tuki cikin nutsuwa Mairo tasa ido tana kallon shi yana burge ta, ya yi kyau
ya yi girma, ya zama ingarman cikakken mutum ma’abocin kwarjini na musamman da cikar zati. Ta fadi a
ranta gaskiya wannan Dina ta caba miji. A ranta kuma tana kissima shin ita kuma Dinar yaya zata kasance?
Jikinshi ya ba shi Mairo kallonshi ta ke, ya yi wani irin murmushi mai ban sha’awa har fararen hakoranshi suka
fito. Ya dan juyo ya ce
“Ya ya dai Mairo? Irin wannan kallo haka? Ko na yi kama da saurayinki ne?”
Kunya ta kama Mairo, ta rufe fuska tana dariya, “Ni ba ni da wani saurayi. Ka yi kyau ne da yawa Yaya Habibu,
ka zama babban mutum mai ban mamaki, don Allah mai Anti Dinar nan take ba ka ne?”
Ya yi murmushi ya kai hannun hagunshi ya shafi kwantacciyar sumar kanshi, ya ce “Soyayya ta ke ba ni Mairo.
Duk wata kauna ta duniya Dina ta ba ni tun a lokacin da nake dalibi, ba ni da komai, ba ni da ko kwabon da
zan aure ta, a matsayina na dan kauye da matsayinta na diyar Ambassador. Habibun kawai ta ke so ba wai
wani abu da Habibun ya mallaka ba”. Mairo ta ce cikin zuciyarta, “Kamar ni da Uncle Junaidu”. Ba tasan cewa
furucin ya subuto ya shiga kunnensa ba
D
Ya rage gudun motar ya dube ta sosai, hawaye ne fal idanunta “Kika ce mun ba ki da saurayi, Mairo”. Ta kai
‘yan yatsu ta share hawayen idanunta “Kuka Mairo? Mairo me ya sanya ki kuka?”
Ba amsa, karewa ma, sai ta soma shesshekar kukan sosai.
Ya sauka gefen titi ya kashe motar. Ya mika hannu ya kama hannunta, ya damke cikin nasa “Daga yau ba zaki
sake kuka ba Mairo, tunda ga ni. Babu abinda Allah bai mallaka min ba. Gida a America, gida a Abuja, motocin
hawa sai wadda ranki yake so. Ga babban aiki da BARCLAYS BANKS, ga takardun ilmi har zuwa PhD, wanda
nake da yakinin daga mu har jikokinmu da ‘ya’yan jikokinmu babu mu babu talauci.
Jami’a sai wadda kika zaba cikin kasar America. Gaya min wane ne Junaidu? Ni kuwa in aura miki shi ko shi ne
beran masallaci sabida talauci, ko shi ne Bill Gates sabida arziki, amma fa sai idan yana da ilmi, ya kuma yi
alkawarin zai rike min ke da amana”.
Mairo ta sunkuyar da kai, ta ce “Ai bai taba cewa yana sona ba!”.
Habibu ya ce “Ke ce kike sonshi ke nan?”
Ta ce “Ni ma ban sani ba ko son nasa nake yi. Alherinsa da kyautayinsa masu yawa ne a gare ni. Ya tsaya
tsayin daka akan karatuna, ya tsaya tsayin daka akan lafiyar Baba da Inna, ya ce nima cikakkar mutum ce a
lokacin da nake jin kaina cikin inferiority compled. Don haka bazan iya ce maka Uncle Junaidu saurayina ba
ne, sai dai duk duniya babu wanda nake jin zan iya aure sai shi…….”
Ta shiga baiwa Habibu labarin tun bayan tafiyarsa, yadda akai ta je FGGC, haduwarta da Junaid, Kausar da su
Nabilah, saran da maciji ya yi mata, ba da jininsa da ya yi gare ta, karfafa mata gwiwa da kwarin gwiwar da
yake ba ta a karatunta, amanar da Malam Bedi ya ba shi a kanta, tsayawa da ya yi akan lafiyar iyayensu, har
zuwa gama makaranta da nemansa da ta yi ranar candy ba ta ganshi ba. Ta kare labarinta da ba shi labarin
zuwansu karbo sakamakonsu a makarantar inda aka gaya musu ya tafi karo karatu Russia. Ta dakata ta share
hawaye, ta cigaba da ba shi labarin zuwanta gidansu wajen mahaifiyarsa, amma ba ta gaya mata ko ita wace
ce ba.
Habibu ya yi shiru, cikin zuzzurfan tunani na ma’abota hankali. Ya rasa ta inda zai bullowa al’amarin Mairo.
Tabbas soyayya ke dawainiya da kanwarshi tilo, ba tareda ita din ta sani ba. Dole ya tsamota, ya ba ta (hope)
na yadda zata manta, ta fuskanci sabuwar rayuwar da ke gabanta.
Neman Junaid agareshi ba wahala ba ne, zai iya kai ta kasar Russia, to amma ba zai iya cewa da Junaid don
Allah ya aureta ba, tunda shi din ba sonta ya ke yi ba.
Da yana sonta da ya nemeta, tunda ta ce yasan da Alhaji Abbas. A ganinshi ma, a wannan sabon zamanin da
muka shigo. Mairo ta yi kankanta da aure, yana sonta da ilimi mai zurfi ba soyayya ba. To amma shi kansa ya
kasa yanke hukuncin cewa Junaidun yana son Mairo ne ko ba ya sonta?
Idan ba sonta yake ba haka kawai ba zai yi ta dawainiya da rayuwarta har haka ba. Allah ne kadai Ya san wane
ne mijinta. Don haka ya kada harshe ya ce “Za ki yi min wata alfarma, Mairo?”
Ta dago a hankali ta dube shi “Ta mece ce Yaya Habibu?”
“So nake ki manta da Uncle Junaidu. Ba wai ki manta da alherinsa gare ki ba, a’ah, ki manta da soyayyar da
zuciyarki ke yi masa, da tunaninki na ba zaki iya auren kowa ba sai shi. Amma kullum kika yi sallah ki dinga yi
masa addu’ar budi da nasarar rayuwa kamar yadda ya zama sanadin da kika samu ingantaccen ilimi.
Ni ma zan tayaki, zan dinga yi wa Junaid addu’a, wannan shi ne kawai alherin da za ki yi ki rama mishi, ba lallai
sai kin aure shi ba. Da yana sonki da ya zo neman aurenki. Ko bai zo neman aurenki ba, da ya zo ya yi miki
sallama a lokacin da zai tafi, ya gaya miki wata kwakkwarar magana, mai nuni da yana son aurenki a nan
gaba.
Ko ya ce ku yi alkawarin aure, don haka ki manta da soyayyarsa, ki tsaya ki yi karatu irin na Junaidu, ke ma ki
taimaki mutane kamar yadda Junaid ya taimake ki. Ki zama malamar makaranta, mai nagarta irin Junaidu.
Idan Junaid mijinki ne, wata rana ni na gaya miki zai zo inda ki ke, Allah Zai hada ku, amma hakan ba yana
nufin za ki zauna zaman jiransa ba ne, a’ah, matar mutum kabarinsa.
Na ji dadi da ba ki gaya wa mahaifiyarsa ko ke wace ce ba, da ina nan ma, da ba zaki je ba, koda yake ba
wajenshi kika je ba, wajen wadda ta yi SANADIN kawo shi duniya ne, gaishe ta da zuciya daya ba laifi ba ne.
Ita darajar diya mace a wurin da namiji guda daya ce, don haka yi min alkawarin mantawa da soyayyar Uncle
Junaidu. Ki bude file ki sanyata a ciki, ki rufe, ki adana. Ki fuskanci rayuwarki ta gaba, kin ji Mairona?”
Cikin shesshekar kuka ta ce “Na ji Yaya Habibu, na yi maka alkawari”.
Ya tayar da motar suka harba kan titi. Mairo na addu’a cikin ranta, Allah Ya ba ta ikon rike wannan muhimmin
alkawari da ta yi wa Habibu, domin ba karamin nauyi ba ne ya azawa zuciyarta ba, da ta ke fatan Allah Ya ba
ta ikon saukewa.
*** ***
“KUDI” Aka ce su ne ‘KARE MAGANA’. Suna zuwa gida me zata gani? Ma’aikatan Julius Berger. Sun sa katafila
sun murkushe gidan Alhaji Abbas, sai fili fetal. Tuni har sun fara auna rodi sun kakkafa matattakalar katako
sun fara aikinsu. Su Habiba da yaransu duk suna gidajen iyayensu, sai an gama ginin zasu dawo. Can gidan su
Habiba suka je suka dauki yaran, Habibu ya zuba su a mota suka wuce Dutsinma.
Mairo da takwararta da Muhammad da ta ke kira Abbana suna baya, Abbas yana gaba tare da Habibu, wanda
ke tuki cikin kwarewa da sukuni. Abba yana ta yi mata tambayoyi tana ba shi amsa dai-dai yadda
kwakwalwarshi zata dauka.
Sanyin A.C gauraye da ni’imtaccen kamshin turaren Yaya Habibu na ‘Miyaki’ ya gauraye motar. Ya sanyawa
Mairo wata irin nutsuwa cikin zuciyarta.
Habibu bai tsaya ba sai a garin Funtuwa, ya sai masu gasassun kaji da lemunan kwali da ruwan Faro, suka
mika. Bai kara tsayawa ba sai a kofar gidan kakannin matarshi da ke cikin garin na Dutsinma.
Habibu ya fidda waya yana kiran Dina, ya ce “Ga mu nan mun iso”.
Mairo na gefe, harde da hannuwanta a kirji. Idanunta kur, akan kofar fitowa gidan, tana zuba idon ganin wace
ce wannan Dina, da ta mamaye zuciyar Habibu haka?
Wace ce Allah Subhana Ya yiwa baiwar samun wannan Habibun? ‘Yar Katsinawan sai ta fito, kyakkyawar
fuskar fal far’a. Sanye da doguwar bakar riga da mayafinta kirar Bahrain. Fara ce, amma ba sol ba, ta ma fi daidai da a kirata choculate colour. Mai wadatar giran ido, gashin ido da sumar kai. Ba ta taba ganin mace mai
kyawun fata irin matar Habibu ba. Gayun ne ya hadu da jin dadi, ya gauraya da hutu, ya cakude da
wadataccen ilmi, sannan kwanciyar hankali da zaman kasar sanyi ya biyo baya. Suka yi wa juna wani irin
sassanyar kallo ita da Habibu, sannan ta karaso ta rungume Mairo, tamkar ta tsaga kirjinta ta sanyata don
kauna. Wani irin matsiyacin kamshi da Mairo ba ta taba ji ba ya ziyarci hancinta.
“Lallai wasu tun a duniya Allah Ya ke ba su Hurul’eeni”. Mairo ta ce a zuciyarta.
Da tana ganin Dinan ce mai sa’a da ta samu Yaya Habibu, ashe shi ma Habibun mai sa’ar ne, don cikin mata
dubu, da kyar zaka samu biyu irin Dina. Da tana ganin Nabilah ‘yar gaye, ashe Nabilah ‘yar dukununu ce. Ba ta
gama zancen zucinta ba, tattausan hannun Dina kamar na jariri ya kama nata, ta ja ta cikin gida. Bayan ta bi
‘ya’yanta daya bayan daya da kisses da runguma.
Wata dattijuwa ce tsohuwa tukuf, sanye da atamfa super holland zaune a can kuryar kayataccen falon bisa
darduma tana lazimi. Da gani babu tambaya, ita ce uwar Baban Dina. Habibu da yaran suka zauna a kujera
yayin da Dina da wata yarinya budurwa da alama mai aiki ce suka shiga hidimar fito da warmers, plates, da
cokulla. Ba ta katse laziminta ba, shi ma Habibun fita ya yi don samun jam’in sallar la’asar. Mairo tana fashin
sallah, don haka suka zauna ita da yaran da Dina suna cin abinci.
Dina ta rasa ina taka-saka-ina-taka-aje da Mairo? Soyayyar Habibu ta shafe ta. Ganinta ta ke tamkar kanwarta
ta jini.
Sai wajejen karfe biyar Habibun ya shigo, lokacin Hajiya ta idar da laziminta, suka soma gaisawa da Habibu.
Itama Mairo ta duka tana gaishe ta. Dina ta ja ta dakin da ta sauka, ta hada mata ruwan zafi a baf da
turarukan wanka, ta ce ta shiga ta yi wanka. Mairo ta ce, “Ai na yi wanka da safe”.
Ta yi murmushi, ta ce “Sakewa za ki yi, ita mace so ake ta yi wanka sau uku a rana. Idan hakan bai samu ba, ta
yi sau biyu. Sannan na ji smelling din jikinki bai min yadda nake so ba”.
Don haka Mairo ta hau wanka, cikin kwami da ruwa mai dumi, da kamshin bathrobb din desire-dunhill mai
sanyaya zuciya da ni’imtata. Da sabulun da ko a mafarkinta ba ta taba gani ba, wanda in ka yi wanka da shi, ba
sai ka shafa mai ba. Ta ji fatarta har wani santsi ta ke da sheki. Jikinta ya yi laushi tubus. Ta dauro alwala ta
fito, ta samu Dina na jiranta zaune a bakin gado.
Ta zube mata kayan shafa da turarukanta, ta ce ta shafa, sannan ta dauko riga da siket masu kauri na Bersace
ta ce ta sanya.
Ta zaunar da ita a gabanta ta sa dryer tana busar mata da gashi, sannan ta bi layi bayan layi na gashin ta shafe
shi da Indian hemp ta taje ta matse da bound, ta bi jelar ta jere da ribbons kala uku masu taushi. Nan da nan
sai ga Mairo ta fito kamar Sushmita Sen. Dina ta yi murmushi ta ce “Maryama, haka kike da kyau kamar
Habibu?”
Mairo ta ji kunya, ta sunne kanta tana dariya, ta ce “Anti Dina ai ke kin fi Yaya Habibu kyau, fari kawai ya fi ki”.
Ta ce “Allah Ya nuna min ranar da tawa Mairon, zata girma ta tashi kamar wannan Mairon. Kinga yadda na
ganki yanzun nan, haka nake so kullum na ganki. Ita mace ba abin da ya fiye mata jikinta daraja. Idan ta gyara
shi, to ta gyara martaba da mutumcinta, mijinta zai like mata tamkar kaska, ya ji ba abin da ya ke so ya
kusanta a duniya sai ita.
Shi kamshi wata rahma ne da Allah Ya saukar mana mu mata, kuma shi ne babban sirrin rike da namiji. Kin ji
ko Mairo?”
Mairo na dariya ta ce “To ai ni ba ni da mijin”.
Ita ma ta tayata dariyar ta ce “Zai zo ne, gallele kuwa, ni na gaya miki”.
Can dakin baki suka iske Habibu, shi ma ya sake fesa wanka, ya yi shiri cikin T. shirt din DKNY fara sol da ratsin
jaja-jaja da wandon jeans kai ka ce saurayi ne dan shekaru ashirin da biyu, babu mai yarda ya aje ‘ya’ya uku a
duniya, ya bi Mairo da kallo don da fari bai ganeta ba, ya ce “Kai! Halitta!!”
Suka kyalkyale da dariya ita da Dina. Ya soma hararar Dinan cikin wata irin soyayyarta da ta kara ratsa
zuciyarshi, ya ce “Shikenan kuma don kin yi kanwa ni kin yaye ni?”
Ta soma yi masa alama da ido, Mairo na jinsa. Itama Mairon juyawa ta yi ta fice a ranta tana ce, ‘Ku cinye
kanku da soyayyar”.
Ai kuwa tana fita ya yi super ya suri Dinan yana cewa “Gaya min wanda ya ce da ke kanwa ta fi miji????”
Mairo wajen Hajiyar su Dina ta koma tana goga goro a magoginsu na tsoffi, da gani ka ga ‘yar gatan tsohuwa
da da ya hucewa takaicin duniya. Ga wasu mulmulallun awarwarayen zinari a hannunta guda uku, sai walwali
suke, tufafin jikinta kadai, sun ishi karamin talaka jari. Ta zauna gefenta ta ce “Hajiya kawo goron in goga
miki”.
Ta mika mata dankwalelen goron fari sol da magogin ta soma gogawa, in ya taru ta mika mata ta hambuda a
baki. Tana bai wa Mairo labarin Dina.
Ta ce “Kin ganta nan, duk cikin jikoki na ashirin da biyar na fi sonta. Sabida halayenta na kwarai da rashin
daukar rayuwa da fadi. Babanta shine da na biyar cikin ‘ya’ya biyar da na haifa suna mutuwa, shi kadai ya
tsaya. Kuma daga shi Allah bai kara ba ni da namiji ba, sai kannensa mata guda biyar.
Ita ce ‘yarsa ta fari, sai tarin kanne guda bakwai. Ta kawo Yayanki dalibi da ba shi da komai ta ce ita shi ta ke
so ta aura. Da fari ba mu yarda ba, tunda ba mu ga iyayenshi ba, shi kuma ya ce, ba zai koma gida a wancan
lokacin ba.
Ya fito neman ilmi da arziki ne sai Allah Ya yi mishi zai koma, don haka muka saduda muka yi musu aure. Da
ya ke abokiyar arzikinshi ce ga shi Allah Ya azurta su, da ‘ya’ya da dukiya. Allah Sarki, ashe iyayen da ya nema
don su huta, kamar yadda nake hutawa a tsufana, Allah bai yi za su mori arzikinsa ba.
Ki saki jikinki, ki kwantar da hankalinki da Dina, zata zame miki uwa, abokiya, kuma Yayar kwarai, kin ji
Maryamu?”
Ta girgiza kai, ta ce “Na ji Hajiya, Yaya Habibu ma ya gaya mini”.
Dina da Habibu suka shigo, sun jero, tsawonsu daya, takunsu iri daya, sai annuri ke fita daga fuskokinsu, ga
dukkan alamu an ci soyayya an koshi. Ta dubi Hajiya da Mairo da ta takarkare sai nika goro ta ke yi, ta yi
dariya ta ce “kawa da kawa, hirar me ake yi?”
Hajiya ta ce “Ina ruwanki da hirarmu? Ko mu mun tambaye ki hirar me kika je taya mijinki?”
Habibu ya nitse cikin leather yana amsa waya da thuraya dinsa, cikin wani dan bantan uban Turanci kamar
Karl Mad sabida yadda Turancinshi ke fita tar-tar irin wanda Mairo ba ta taba ji ba. A da, tana tsammanin a
duniya babu wanda ya iya Turanci irin Uncle Junaidu, ashe Junaid rarrafe yake yi, ga wadanda suka mike suke
dabo, suka tsaya da kafafunsu.
Kwanansu uku a Dutsinma suka tattaro suka yo Kano, Mairo dai kamar ba zata tafi ba sabida jin dadin zama
da Hajiya, har hawaye ta ke da suka fito za su tafi, Habibu da Dina na mata dariya.
Hajiya ta cika mata Bacco fal da atamfofin edclusibes irin wadanda ‘ya’yanta ke kawo mata, don ta dinka,
amma ta tattara ta bai wa Mairo. Wannan a jinin Mairon yake, FARIN JINI da shiga zucci. Idan ka zauna da ita
yini guda, zaka so ka kwana da ita. Idan ka kwana da ita, zaka so kayi wata tare da ita, idan ka yi wata tare da
ita zaka so ka yi zaman shekara da ita, haka idan ka yi shekara da ita, zaka so ka zauna da ita har zuwa karshen
rayuwarka.
Karfe uku dai-dai na rana suna cikin Kano, Habibu ya karya kan mota suka shigo Yakasai. Tun daga nesa wani
dankareren European Billa (Bungalour) ya dauki hankalinta, ya karkada mata ‘ya’yan hanji. Abin mamaki a get
din gidan Habibu ya sanya hancin motarsa kirar Porsche. Zuciyarta na gaya mata, wai wannan gidan Baffa ne?
Amma wani sashen na karyatawa. To idan ba shi ba ne, wanne ne? A nan dai gidan Baffa ya ke, ga makotansu
nan ba su motsa daga inda suke ba, su ma sun samu arzikin sabon fenti irin na gidan. Dama dai gidan Baffan
babba ne, ga kuma bene an daura, ko ina gilashi da tile ke zagin idonka.
An fidda sashen baki daga gaban gidan, a cikin gidan kuma sashe biyu ne na matan gidan, sashe guda na yara,
Baffan yana sama, sai dakin ‘yammata. Kowanne daki an kafe plasma a sama tana ta aiki cikin tasoshin
tauraron dan Adam, ga dindima-dindiman kujeru masu nishi ‘yan Italy da labulaye masu garai-garai da gani
tafiyayyu ne tun daga China. Abin dai ba a cewa komai sai a gaida Habibu, a gaida ma’aikatan Julius Berger. A
gaida Habibu da aikin ZUMUNCI, da rama hairan da hairan.
Suna tsayuwa su Rahma suka diba yuuu! Suka yi cikin gida suna ta ihu, “turawan sun dawo da Mairo, ba su
sace ta ba. Baba ga Mairon nan sun dawo da ita”.
Baffa dai baki ya ki rufo, ya fito ya taro su, Abbas ya gane shi, ya je ya kama hannunsa, Hajara da Habiba
kowacce ta fito daga bangarenta bakin nan kamar gonar auduga, har rige-rigen daukar Mairo karama su ke.
Mairo fa ta fara jin tsoron al’amarin Habibu. Allah dai Ya sa ba kungiyoyin nan na matsafa da sassan jikin
mutum ya shiga ba. Allah Sarki! Da tasan Barclays da ba ta ce haka ba.
Hankalinta na kan ‘yar uwarta Ladidi da halin da ta tafi ta barta a ciki. Don haka suna shigowa ta tambayi
Habiba “Ina Ladidi?”
Habiba wadda ke jin kamar ta suri Mairo ta goya don ta samu fada wajen Baffa wanda ya daure musu fuska
tam ya ki kula su don yasan duk borin kunya suke yi. Ta nuna mata dakin da Ladidi ta ke, ta ce “Halan Mairo a
inji matar Habibu ta sakaki ta wanke?”
Mairo ta yi murmushi ta ce “A’ah, a lagireto ne”.
Ta wuce ta barta nan, tana ta sosa keya don kunya.
A dakin ta cimma Ladidi, an yi dai-dai cikin Italian bed, ana shan lemon Safari ana kallon tashar Zee-Aflam, ba
tasan sanda dariya ta kubuce mata ba, don kwata-kwata ba ta yi matching da gadon ba da dakin gaba daya, ta
fi dacewa da mai aikin dakin ba mamallakiyarshi ba.
Tana ganin Mairo ji kake kat, ta kware. Ta dinga tari ba kakkautawa. Mairo ta zauna a bakin gadon tana yi
mata sannu. Ta mutsittsike ido ta ce “Mairo ke ce kuwa?”
Ta ce “A’ah, ba ni ba ce, Ladidi ce”.
Ladidi ta soma kuka ta ce “Don Allah Mairo ki yafe mini. Ga shi dai tun a gidan duniya mun ga ishara, dan uwa
duk lalacewarshi ba abun wasa ba ne, sai dai nasan kome zan fada miki a yanzu ba zaki yarda ba, za ki ce don
na ga Habibu ne, ko don abin da ya yi mana, amma wallahi ba haka ba ne. Yadda kuma kika rufa min asiri a
duniya, Allah Ya rufa naki duniya da lahira”. Ta sa habar zaninta ta share ido.
Mairo ta ce “Duk ba wannan ba Ladidi. Ki tuba ga Allah, ki sani cewa, Yana kallonki, idan su Baffa ba sa
kallonki. Yau idan Baffa ya samu labarin kin cire ciki har sau biyu a wane yanayi kike tunanin zai tsinci kansa?
Idan ba kya tsoron Allah, ai kya ji wa kanki tsoron cututtukan zamanin nan da ba su da magani. Idan aure kike
so ki fidda daya daga cikin manemanki ki aura mana?”
Ladidi ta ce “Na tuba, na bi Allah na bi ki. Wallahi daga yau bazan sake ba…”
“……Ki ma sake din mana don ubanki”.
Suka juya a razane, Habiba ce tsaye a kansu, ashe ta dade da shigowa ba su ankara da ita ba. Ta kwance
dankwalinta ta yi damara, ta yo kan ladidi ta hau ruwan cikinta ta soma kirba mata naushi tana ihu tana “Na
tuba Mama, wallahi bazan sake ba”.
Wannan bai ishi Habiba ba, sauka ta yi ta nufi kicin ta dauko tabarya ta yo kanta tana fadin, “Gara na kashe ki
kafin kanjamau ta kashe ki, kibar mana abin fadi cikin zuri’armu”.
Ganin ta yo kanta da tabaryar Ladidi ta yo waje da gudu don tserar da rayuwarta, wannan ya janyo hankalin
kafatanin jama’ar gidan yara da manya, suka fito tsakar gida har Dina da Habibu da Baffa. Ganin Ladidin zata
yi waje da rigar bacci, kafarta ko takalmi babu, kanta ko dankwali, Habibu ma ya rufa da gudu ya kamota tana
ta kuka, tana “Na tuba wallahi ba zan sake ba……..”
Habiba ta fito tana sharar hawaye, ta ce, “Ni fa ince, wannan aman da wannan kwanciyar nakin na Ladidi, ba
na lafiya ba ne, na zama shashashar Uwa, yanzu Mairo da kunnawana ba su jiye min ba, haka zaki biye mata
ku binne mu?”
Mairo na kukan tausayin Ladidi ba ta ce komai ba.
Baffa ya ce “Mai Ladidin ta yi ne?” Ya tambaya yana kallon Mairo.
Ta yi tsuru-tsuru ba ta yi magana ba. Ya sake tambayarta, ta ki magana. Habiba cikin kuka ta ce “Ciki suka je
aka cire mata, wai wannan shi ne na biyu, na ji su tana yi wa Mairon godiyar ta rufa mata asiri”.
Baffa ya ce “Mairon? Da ita aka je aka cire cikin?”
Mairo ta girgiza kai cikin kuka ta ce “Wallahi ba ni na rakata ba, ita kadai ta je abunta. Ni asibiti na kaita ta ga
likita”.
Dariya ta kama Habibu, wai asibiti ta kaita, sai ka ce wata uwarta? Habibu ya ce “Ke ma sai mu je a duba ki,
don abokin barawo ai barowo ne”.
Ya hankada Ladidi da ke hannunsa ya tankado keyar Mairon, ya ce, “Oya! Lets go, har gwajin kanjamau duk za
a yi muku tunda kun zama karuwai”.
Mairo ta soma rantsuwar, wallahi babu ruwanta, ba ta da saurayi, ba ta taba yin zance da namiji ba. Babu
wanda ba ta baiwa dariya a wajen ba. Baffa ya kamo hannunta ya ce
“Share hawayenki Mairo. Babu inda za ki, kanwarshi ce karuwa ba ke ba”. E
Ya juya ga Ladidi, idonsa ya ciko da kwallah. Ya ce
“Bazan yi miki baki ba, Allah Ya shirye ki. Amma bazan sa wa raina bakin cikinki har ya shafi lafiyata ba. Idan
wannan ita ce rayuwar da kika zabawa kanki, sai ki je ki yi ta yi, Allah Ya ba da sa’a”.
Ladidi ta durkushe a nan tana kuka. Tun daga ranar rayuwar gidan ta yi mata kunci, duk da murnar sabon gida
da kowa ke yi kuwa, daga Mairo sai Dina kadai ke yi mata magana cikin gidan, amma Habiba tsinuwa ce kadai
ba ta yi mata ba.
Ranar asabar suka yi shirin tafiya Gurin-Gawa, Habibu, Dina da Mairo, Baffa da yaransu. A yadda suka yo
shirin tafiyar da kulolin abinci da na ruwa kamar masu zuwa picnic. Dina cike da dokin son ganin mahaifar
Habibu.
Suna tafe akan burjin kansu na gwaggwaruwa da mota sabida rashin kyawun burjin. Dina ta ce
“Ya kamata idan gwamnati ba zata sanya kwalta a titin nan ba, kai ka saka Habib, albarkacin iyaye da
kakanni”.
Ya ce, “Kin riga ni a baki na riga ki a zuci, insha Allah kamin mu tafi za a sanya da famfuna da (bore-holes).
Sannan zan sake ginin gidanmu, na yi gidan gona da gonar Baba”.
Ta ce “Wannan tunani ne mai kyau”.
Gidan Dagaci suka fara isa, da farko bai gane Habibu da Mairo ba, sai Alhaji Abbas. Ya shiga lale da baki, ya
kawo sabuwar karauni katuwa ya shimfida musu. Ya shiga cikin gida ya kawo musu ruwan randa mai sanyi da
damammiyar fura ta ji kindirmo. Sai da suka sha suka nitsa, sannan aka soma gaggaisawa. Ya dubi Alhaji
Abbas ya ce
“Ina labarin Habibu? Ko har yanzu bai dawo ba? Mairo an kare makaranta ko, ko har anyi aurenta ne?”
Alhaji Abbas ya ce “Wane Habibun da wace Mairon kake nema, bayan wadannan da suke gabanka? Ga
matarsa ga ‘ya’yansa”.
Dagaci ya soma salati ya ce “Iko sai Allah! Allahu Akbar!! Habibu kai ne? Ba ka kyautawa Bedi ba Habibu”.
Ya soma sharar hawaye sakamakon tunowa da tsohon amini, su ma duk sai suka yi shiru jikin kowa ya yi
sanyi. Da kyar Baffa ya lallashe shi ya daina kukan. Tare da shi suka nufi gidan Liman da gidan Malam Tanimu,
suka rankaya gidan su Mairo.
Malam Tanimu ya sa mukulli ya bude kwadon da aka rufe gidan da shi suka shiga. Mairo sai ta rushe da kuka,
ganin komai nasu yana nan yadda ya ke, sai kura da ko’ina ya yi.
Karime ta shigo suka rungume juna ita da Mairo suna kuka. Kafin ka ce me ye wannan? Labarin zuwan
MAIRON HURE da Habibu daga turai ya baza dan karamin kauyen. Abinka da jama’ar karkara ma’abota
karimci da zumunci nan da nan aka cikasu da kwanuka da abinci nau’i-nau’i. Suka ci suka koshi, sannan suka
shiga cikin gari.
Suna tafe Habibu yana bai wa Dina labarin kuruciyar Mairo tana shan dariya. Suka iso dai-dai wata bishiyar
goriba, ya juya ya dubi Mairo, ya ce “Mairo ko za a tsinko mana ne? Ko bujen ya cika ne?”
Ta kyalyale da dariya ta ce “Kai Yaya Habibu, na yi maka kama da ‘ya’yan Birrai ne?”
Ya ci gaba da bai wa Dina labarin ranar da ta nannako masa katuwar goriba aka, wai ya saka mata a aljihunsa,
bujenta ya cika. Dina har da hawaye don dariya. Suka je makarantar firamare din su Mairo, suka nemi
hedimasta, Habibu ya yi masa ALHERI da ya gigita shi, ya kuma bai wa makarantar tallafi na wasu makudan
kudade, haka makarantar islamiyyar su Mairo ma Habibu bai manta da ita ba.
Dagaci da Malam Tanimu sun fi kowa samun ihsani. Mairo ta cire dan kunnen gwal da ke kunnenta da Dina ta
bata ta bai wa Karime da kafatanin kayanta da ta ke amfani da su kafin zuwan Habibu.
Habibu ya bar maganar gini, famfuna, bore-hole, da gidan gonarsa a hannun Dagaci da Malam Tanimu, da
kwalta da yake so a shimfida tun daga titin Gurin-Gawa har zuwa babban titin da zai hadaka da babban titin
Fanshekara. Ya ce gobe insha Allah zai turo ma’aikata su fara aiki. Suka baro kauyen with nostalgia, bayan
motarsu cike da tsarabobin kauye iri-iri, musamman rake, kwan zabbi, nono-kindirmo, aya da dankali. Abin
gwanin ban sha’awa.
Habibu ya wuce Abuja a washegari don yi wa Mairo cuku-cukun bisa. A ranar da misalin karfe sha biyu na
rana Baffa ya sauke su a sabuwar Golf dinshi da Dina ta ba shi a gidan Nabilah da ke cikin unguwar
Nassarawa.
Nabilah ta yi hamdala ga Allah da Mairo ta gaya mata Yaya Habibu ya dawo, ga ‘ya’yanshi ta kawo mata, har
ga shi zai tafi da ita, tafiya da ba ranar dawowa.
Nabilah hawaye ta ke sharewa tana mamakin ikon Allah. Koda yake an ce ba a mamaki da ikon Allah, Mai
azurta bawa, buwaya gagara misali. Ta tuno kwadon ramar Mairo, jikakken kanzonta da kwaki da kuli-kulinta
da suke wa dariya, yau ga Mairo ta fi ta arziki.
Ta tuno kalaman Uncle Junaidu da yake nusar da su cewa, duniya RAWAR ‘YAMMATA CE, ba su san arzikin da
Allah Zai wa yarinyar a nan gaba ba. Suna can kule a daki suna kukkulla labarin rayuwarsu ta baya. Isma’el
mijin Nabilah ya dawo, ya tsaya daga bakin kofa, hannuwanshi cikin aljihu yake jifan Nabilah da wani irin
asirtaccen kallo da su kadai suka san ma’anar abinsu. Ta yi murmushi tana yi mishi sannu da dawowa, ya ce
“Duk da ban sani ba, wannan ce Mairo?”
Mairo ta yi murmushi, ta ce “Mairon Nabila ce”.
Wannan kadai ya tabbatarwa da Mairo Nabila ta shirya da mijinta.
Ranar talata sha biyu ga watan biyu na shekarar alif dari tara da cas’in da biyar. Jirgin American Airways ya
lula da Habibu da iyalinsa kasar America, sai da suka tsaya a Frankfurt. Daga nan suka hawo jirgi zuwa
Michigan.
Gidan Habibu yana nan a Detroit. Flat ne hawa daya, kewaye da grass-carpet, wadanda suka lullube gidan ruf,
tun daga sama har kasa. Mairo tun tana kauyanci, har ta mika wuya, ta yarda ba mutuwa ta yi Allah Ya sa ta a
aljanna ba. A’ah, tana nan a raye. Aljannar ce Allah Ya bata tun a gidan duniya. Mai zata yi? Mai zata ce?
Banda kullum ta kasance cikin godiyarSa, da yi wa iyayenta da Yaya Habibu addu’ar neman samun gindin
zama a wajen Maiduka…….
***
MAIRO A GIDAN YAYA HABIBU!
L
itinin ce babbar rana. Habibu ya yi shirin ofis cikin suit din ma’aikatan bankin Barclays, da jibgegiyar rigar
sanyi, hand-socks, da leg-socks yana so zai fita aiki, ga yara sun yi shirin makaranta, misalin karfe bakwai na
safe. Amma babu hanya, don tashi suka yi suka tarar da kankara ta rufe kofar gidan ruf da tagogi baki daya.
Dina ma ta fito cikin shirin ofis cikin kayanta na lauyoyin banki, tana ta korafi akan snow. Dole Habibu ya fiddo
waya ya kira ma’aikatan sare kankara, nan da nan suka zo cikin minti goma, suka banbare kankarar sannan
suka samu hanya suka fita.
Mairo ta fito daga dakinta ta yi wa sanyi mugun shiri, ba ka ganin komai nata sai shacin kayatacciyar fuskarta,
kai ka ce Balarabiyar Morocco ce. Ta yi kiran Lynder dattijiyar da ke musu aikace-aikace ta ba ta wayar tafi da
gidanka, ta ce ta sanya mata a caji, socket din dakinta ya lalace.
Ta sa yaran a gaba suka fito tana dauke da Little Mairo, suka zo bakin hanya suka tsaya, tana rike da
hannayensu. Tsayuwar minti biyar suka yi, motar makarantarsu ta iso suka shiga suka tafi suna daga mata
hannu, ita ma tana daga musu.
Ta komo gida ta zauna a tebir tana kalaci da pizza da ruwan lipton. A gurguje ta kammala ta mike ta sunkuci
jakarta ta fito, ta yi wa ‘yar kankanuwar motarta key ta harba kan titi. Tana duba bakin agogon swatch da ke
daure a hannun damanta.
(Wannan shine tsarin rayuwar gudan Yayya Habibu a kullum).
Mairo na karantar zamantakewar dan Adam (sociology) a Jami’ar Michigan (Michigan State University). Yau
kimanin shekara biyu da rabi. Idan ka ga Mairo a wannan lokacin aka ce maka ita ce Mairon Hure, ‘yar kauyen
Gurin-Gawa, wallahi karyatawa zaka yi. Ba ta da abin da zata ce da Yaya Habibu da matarsa, sai addu’a.
Duk wani gata na duniya sun gama yi mata shi, duk wani alheri na rayuwa sun gama yi mata shi. Don haka ita
ma ta kama ‘ya’yansu ta rike, ita ce uwarsu, ita ce nanninsu, ita ce malamarsu, idan sun dawo daga
makaranta, karatun Alkur’ani a bakinsu abin sai ya baka mamaki duk da suna zuwa islamiyya ta wasu
Larabawan Egypt a weekend, amma karfin karatunsu na addini a wuyan Mairo ya ke.
Mairo zaune a study-room da farin gilashin karatu a idanunta, tana nazarin littafin Haralarambus and
Horlborn, (sociology, themes and Perspectives), domin wani assignment mai matukar wuya da aka ba su akan
hedonism za su yi submitting a washegari.
Misalin karfe shidda na yamma, Aunty Dina ta murda kofar ta shigo fuskarta dauke da kankanin murmushi,
tana sanye da thick-coat da dogon wandon Cherokee. Sassanyan kamshinta na turaren Ybes saint laurent shi
ya fara bakuntar hancin Mairo. Ta ja kujera ta zauna, sannan ta ce
“Mairo London zan je gobe, ko zan samu ‘yar rakiya?”
Mairo ta ce “Ina da aiki mai yawa a Makaranta Anty Dina, sannan zan yi submitting assignment duka a goben,
me zaki je ki yi?”
Ta ce “Kallon film-fare award na wannan shekarar, gara in gani vivid fiye da a talabijin. Tun wancan satin ake
ta sanarwa za a yi”.
Mairo bata san son kallon Indiyan na Dina yakai har haka ba, da zata niki gari kasa-ya-kasa don kawai ta ga
Gala, ta ce “Sai kin dawo, ni kam bazan samu zuwa ba”.
Habibu d taya bera bari, ya yankowa Dina ticket ta tafi London a washegari. Gidan ya saura sai su kadai. Tun
safe Mairo na makaranta tana ta fama da ayyukan gabanta, ita da awarta Ir’eesh ‘yar asalin kasar Somalia. Ba
ta dawo gida ba sai yamma lis. Tuni Yaya Habibu ya rigata dawowa, zaune suke a babban falonshi shi da yaran
suna aikin makaranta yana nuna musu. Mairo ta yi sallama ta shigo suka yi tsalle suka daneta suna yi mata,
“Oyoyo!”
Yaya Habibu ya dago ido ya kalle ta, yana mamaki cikin ranshi wai wannan Mairo ce, Mairon Gurin-Gawa,
Mairon Hure… Abu daya ya tuno yayi a wannan lokacin (goruba daga kan bishiya a kauyen Gurin-gawa) yayi
murmushi ya ce “Mairo ‘yan makaranta, Mairon Dina, Mairon Yaya Habibu…”
Ta yi dariya, kirarin da yake mata kenan idan ya so nishadi. Ta wuce dakinta don ta kimtsa.
Bayan ta yi sallar magriba ta canza kayan jikinta ta fito falo ta zauna tare da su. Zuwa can Yaya Habibu ya fito
daga dakinsa cikin shiri, sai kamshi ya ke. Ga dukkan alamu cikin sauri yake, ya dube ta ya ce “Maza a shirya
dinner, amma African dish Mairo ina da babban bako. Babban abokina Amiru zai sauka yanzu daga
Washington D.C. Zan je filin jirgi na dauko shi”.
Daga yadda ya ke maganar cikin rawar jiki kadai kasan wannan bakon mai matukar muhimmanci ne da
matsayi na musamman a gare shi. Ba tun yau ba, Mairo na jin sunan Amiru a bakin Yaya Habibu da Dina. Zata
iya cewa rana bata fitowa ta fadi wani cikinsu bai ambaci Amiru ba.
Ta amsa da “To, sai kun iso”.
Yana fita ta fada kichin, Lynder na goge-goge, ta bata hanya ta wuce. Ta bude deep-freezer tana tunanin me
zata dafa? Zuciyarta ta tsaya akan tuwon shinkafa miyar danyar kubewa tunda dai suna da Okora (danyar
kubewar gwangwani).
Nan da nan ta dora sanwa. Ta yi amfani da dried fish da mushroom curry cikin miyar, duk kicin din sai ya dau
kamshi. Suna da zobo don haka ta tafasa shi ta tace, ta markada abarba ta hade da zobon da fulebo din
abarba ta juye a jug ta sanya a firji don ya yi dan sanyi.
Ba tun yau ba tasan Yaya Habibu da son dan wake. Kai shi duk wani abinci ma na burgewa na Africa to ya bi
bayan dan wake. Don haka nan da nan ta jika kanwa ta kwaba ta jejjefa cikin tafasasshen ruwa, sannan ta
bude freezeer ta fiddo kankararriyar kaza ta daddatsa ta dora farfesu. Cikin dan lokaci ta kammala komai. Ta
jere komai a dining har filet da cokulla da tambulan na shan ruwa. Ta koma dakinta ta fada bandaki ta sake
wanka. Ta shirya cikin baki da farin suwaita masu kauri, ta koma gefen gado ta kwanta ta fiddo novel din
Emilie Rose (condition of marriage) tana karantawa.
Wayarta ta yi kira cikin daddadan sauti, ta aje novel din ta dauka. Sunan ‘Nabilah-ta’ ke yawo a fuskar wayar.
Ta yi murmushi ta amsa. Nabilah ta ce “Kunnenki nawa?”
Da sauri ta ce “Hudu”.
“To kara hudu ki sha labari”.
Ta ce “Na kara”.
Ta kanga mata kukan baby a kunne, Mairo ta yi wani dan ihu don ba ta san Nabilah na da ciki bama, ta ce
“Amma ba ki kyauta min ba Nabilah…”
Ta ce “Yi hakuri. I just want to surprise you….”.
Ta ce “Turo min hoton baby yanzu, Allah Ya raya mana, Ya sa cikon musulunci ne”.
Nabilah ta ce “Ameen, ke kuma aure sai yaushe, Mairo?”
Mairo ta yi murmushi, wani abu ya dan daki zuciyarta. Banda abun Nabilah ta gaya mata tana sha’awar aure
ne? Ita babu aure, babu soyayya a lissafinta, tun daga lokacin da ta daukarwa Yaya Habibu alkawari. Karatun
nan shi tasa a gaba, shi kadai ta ke buri, amma aure? Tunda ta rasa Uncle Junaid baya cikin lissafinta.
Ta kashe wayar ba tare da ta bai wa Nabilah amsa ba. Dai-dai nan ta ji motsin shigowar Yaya Habibu da
bakonsa a falo. Da alama ba su biyu ba ne, don tana jin muryoyin maza daban-daban. Ta sake kudundunewa a
cikin bargonta. Sama-sama ta ke jiyo tashin sautinsu, ana ta Turanci kamar tashin duniya. Kira ya sake
shigowa wayarta. Ta amsa, Dina ce.
Ta ce “ya ya kuke Mairo? Hope ba matsala, ina nan tahowa gobe insha Allahu”.
Mairo ta ce “Mun yi missing dinki Aunty, duk gidan babu dadi da ba ki”.
Ta yi murmushi, ta ce “Ni ma haka, ji na nake kamar na yi shekara ban ganku ba. Me ya samu wayar Habib?
Na kasa kama shi”.
Ta ce “Yana falo, ya yi baki ne”.
Ta ce “Su waye?”
Mairo ta ce “Na dai ji ya ce Amiru ne”.
Dina ta ce “Wow! Amiru yau a gidanmu? Maza kai wa Habib wayar ina son magana da shi”.
Ta mike ta fito, shaf! Ta manta ba ta rufe kanta ba, tsabar yadda Dina ta azalzaleta a kaiwa Habibu wayar. In
kaga Mairo a wannan lokacin kamar wata balarabiyyar Morocco haka komai nata ya koma, baka taba hada ta
da jinsin kasar haihuwarta. A haka ta isa falon a sanda ta ke mikawa Yaya Habibu wayar batare da ta kai ido
kan kowa ba banda Habibun. Juyowar nan da zata yi sai idonta cikin na Amiru, wanda ke sanye cikin Italian
suit bakake wul, ya sassautawa wuyanshi ruwan tokar tie da ke wuyanshi. Ya dago kansa daga wayar da yake
dubawa don ya yiwa Habibu magana. Suka samu kansu cikin matsananciyar faduwar gaba a lokaci daya. Ga
ita Mairo, kwarjini ne da kyawun Amirun ya haifar mata da faduwar gaban, amma ga AMIRUN, bazan iya
cewa ba.
Habibu ya dubi Amiru yana murmushi
ya ce “Amiru meet my belobed sister ‘MAIRO’, da nake baka labari”.
Yana kokarin saita lumsassun idanunsa akan Habibu, don kawar da su daga nacewa da kafewar da da suka yi
akan Mairon ya ce “Ita ce Mairon? Mairo zo mu gaisa…….”.
Amiru dai Hausa yayi, amma wani ‘accent’ ne da Mairo bata taba jin mai gardinsa cikin kunnuwanta ba.
Kamar yadda bata taba ganin mutum mai kyau da kwarjininsa ba. Ilhamomin dake tare da shi bata taba
haduwa da mai irin su ba! Bata taba ganinsu tareda kowa a duniya ba! Wannan shine AMIRUN Yaya
HABIBUN???
(The beginning of everything kenan).
*****
Ya mika mata hannun damanshi wanda ke daure da agogo na zallar diamond. Ta yi murmushi, beauty point
din suka lotsa ciki sosai, kafin ta yi baya da hannunta ta sarkesu a baya. Akan me zata yi hannu da katon
namiji? Mr Raymond baturen Ingila da suke tare kuma (secretary) na Amirun, ya kyalkyale da dariya ya ce.
“Ta boye hannunta abin ta, ba ta shan hannu da maza”.
Amiru ya lumshe ido ya bude su dukka a kanta, sun juye, sun rikide gaba daya da abin nan da ake kira luv at
first-sight. Cikin sassanyar murya ya ce “Wai haka Mairo? Mairo ni ma Yaya Habibu ne, ba za ki hannu da
Habib ba?”
Habib ya ture filet din gabanshi ya harare shi “Kai bana son iskanci, ba zata yi hannun ba! Wuce Mairo ki tafi,
rabu da wannan baturen banza ne!”.
Amiru ya maida hannunshi cikin aljihu yana gimtse fuska, bayan Mairo ta wuce ta koma daki, ya ce. “Don me
zaka yi mun haka? Cewa nake ni har da matata hand shaking kake ban ce maka baturen banza ba sai ni don
na ga matar aure?”
Habibu ya ce “Yo wannan matar taka har wata mace ce da namiji zai tsaya yana kishi a kanta? Me ke cikin
hannun nata banda kafurci? A ina ka ga matar auren? Ba dai a gidana ba ta je a burma mata wuka babu gaira
babu dalili”.
Raymond da Franklyn suka yi dariya, ban da Amirun, wanda ya sha kunu sosai ya zama serious ya ce “Ka daina
yi mun magana in this manner. Sabida yanzu kai ba abokina ba ne, surukina ne. Na ga Mairo ina so, sujjada ce
kadai bazan yi maka ba don ka ba ni ita. Ba maganar wasa nake ba, za ka bani Habibu???”
Habibu ya daga ido yana kallonsa, duk ya bi ya marairaice masa ya manta a gaban yaransa ya ke irin wannan
magana, da gani ka ga wanda tsumagiyar soyayya ta yi wa mugun fyada, ina Mairo ina Amiru? Ai ya fi
karfinta, igiyar rakumi ta yi nesa da kasa, an ce yaro tsaya matsayinka…. kada zancen ‘yan duniya ya rude ka,
ba zai sanya kankanuwar kanwarshi cikin rayuwar Amiru ba, ba zai sanya Mairo cikin problem (matsala) ba,
auren kwanciyar hankali yake sonta da shi, ba auren irin su Amiru ba, don haka ya share kamar bai ji shi ba.
*****
Haduwar shi da Amiru ta faro ne a Malaysia, can inda ya fara karatu, ajinsu daya da shi, amma Amiru ba ya
kwana cikin makaranta, gida guda mahaifinshi ya kama mishi a wajen makaranta da tsaleliyar motar zamani.
Sai dai ya shigo, in ya gama abin da zai yi ya fita.
Rannan sun zauna waje daya daukar lacca shi da Habibun, bayan sun tashi Amirun ya riga shi fita, ya kuma
manta wayar hannunshi a nan inda ya tashi, wadda a lokacin sai ‘ya’yan wane da wane ne kadai ke rikewa.
Habib din ya dauka, washegari da suka hadu ya ba shi. Amiru ya yi mamaki sabida tsadar wayar ba karamin
mai imani ba ne zai tsince ta ya iya neman mai ita ya ba shi ba, sai mai tsananin tsoron Allah. A nan ya nemi
sanin sunan Habibun da kasar da ya fito.
Tun daga nan suka kulla abota kullum suna tare. Sai dai ba yadda Amirun bai yi da Habib ba akan ya kwashe
kayanshi daga hostel su zauna tare a gidanshi, amma Habibun ya ki.
Da suka kammala karatun digiri na farko mahaifin Amirun ya dauki nauyin ci gaba da karatunsu a Oakland
University da ke Michigan. Bayan sun kammala PhD ne suka raba kafa, inda shi Amirun ya samu aiki da World
Bank da ke Washington yana kuma harkokin shigo da kwamfutoci nau’i-nau’i daga U.S. Fadin iyakacin abinda
Amirun ya mallaka a wannan duniyar bata baki ne. Mahaifin Amiru ya rike mukamai da dama a gida Nijeriya,
kama daga Commissioner, Governor, EFFC har zuwa wanda ya ke kai a halin yanzu wato (Director of Currency
and Branch Operations). Ta wani fannin suna da sarauta a Gaya (home-town dinsu) Suna da siraran tsagin
biyu-biyu a gefen fuskarsu na fulanin Gaya.
Mahaifiyar Amiru da mahaifinsa fulanin Gaya ne na usul. Watakila a nan ne Amiru ya debo wannan kyawun
wanda ya firgita kanwar Habibu (Mairo), dama duk wata lafiyayyar mace da ta dora ido a kansa.
A duba na farko, ba zaka kira shi baki ba, sabida wani irin baki ne da shi mai sheki da daukar hankali. Ga
mikakken hanci kamar karas. Babban sirrin kyawun Amirun, na cikin sajen da ke gefen fuskarsa, wanda ya
taho ya hade da siririn gashin bakin nan da ake kira man’s pride. Dogo ne sosai, don tsayi har ya rankwafa,
mai fadin kirji da alamun karfi ta ko ina. Ma’abocin yawan saisaye da shaving sabida yawan gargasa. Hakora
gare shi farare kal, kai ka ce ba a tauna komi da su. Jerarru reras a cikin wasu siraran labba masu taushi, da ke
bayyanar da dukkan hakoran, a duk sanda ya yi dariya.
Dan kimanin shekaru talatin da bakwai . Shi da Habibu kusan a komai suna da ra’ayi daya, kamar kalar suit da
suke sawa, sun fi son yin amfani da black, ash and white (baki, ruwan toka da fari). Suna son shafa turaren
Miyaki, tsawonsu daya, ilminsu daya, sai dai Amirun ya fi Habibu samu nesa ba kusa ba. Sabida Habibu da
aikinsa kawai ya dogara, kuma ko kusa baka taba hada World Bank da Barclays.
Shi kansa Habibu na yabawa da halayen kwarai na Amirun. Ba ya shan giya, ba ya neman mata, duk da yadda
matan ke rubdugu a kansa kuwa. Sai dai yana smoking wannan din ma ba sosai ba, don sai ya yi sati bai sha
ba. Babu yadda Habibun bai yi ba don ya raba shi da taba ya kasa, sai dai kala daya kawai yake sha, wato
Aspen. Wannan din ma ba da sanin iyayenshi ba, domin har Amir ya kai wannan munzalin ba su daina sanya
ido akan tarbiyyarsa ba, kasancewarshi da namiji kadai da Allah Ya ba su. Cikin ‘ya’ya mata goma sha biyu.
Yau shekaru biyu kenan da Amiru ya yiwa iyayenshi wani gagarumin laifi, wato auren wata abokiyar aikinshi
baturiyar Philippines da ya yi ba da saninsu ba. Ya san babu yadda za a yi su amince masa ya aure ta, shi kuma
da ya yi zina, ya gwammace ya aure ta a boye, don yana sonta. Babu yadda Habibu bai yi ba don ya nuna
mishi illar hakan, amma Amirun bai gani ba. A cewarshi ai bazai taba kaita gida ba balle su sani. Suna tare a
Washington D.C don ita ma Harrit din ma’aikaciyar ‘world bank’ ce.
Amiru yana son Da, kamar-kamar me, Harrit ba ta son haihuwa. Ba da saninsa ba ma ta je asibiti gabadaya
aka juya mata mahaifa. A tunanin Amiru idan har tsakaninshi da Harrit aka samu albarkar ‘ya’ya duk ranar da
ya bayyanata ga iyayensa dole za su hakura su kyale su tare.
To sai kuma yau da ya dora idanunshi akan Mairon Habibu. A yau Amiru ya kalubalanci kansa da tunaninshi
na da cewa yasan soyayya. Ashe so daban, sha’awa daban. Idan an gusar da sha’awar nan shikenan son ke
‘vanishing’. Shi ‘so’ din, ba yinsa ake ba, shi ya ke sarrafa kansa. Ba ganinsa ake ba, jinsa ake a gabadayan
sassan jiki, musamman ‘ZUCIYA’. Inda duk ya juya a wannan daren kyakkyawar fuskar Mairo da murmushinta
ke gilma mishi. Jikinshi har wani irin kaduwa yake. Karfe bakwai na safe shi ne mutun na farko daya dannawa
Habibu kararrawa, kasancewar ranar lahadi ce, Habibun ba zai je ofis ba.
Ya zo ya bude kofar da kanshi, don Mairo da yaran suna daki ba su fito ba, don a irin wannan lahadin suna
samun isasshen barci wani lokacin sai su kai karfe goma sannan su fito yin karin-kumallo.
Lynder ce kawai ta tashi ta ke aikace-aikacenta cikin gidan. Habibun na sanye da kayan barci ne riga da wando
masu kauri ya mutsittsika idonshi cikin mamaki ya ba shi hanya ya wuce ciki.
Ga dukkan alamun Amirun ma ko wanka bai yi ba, shi ma shirt ce da wando na barci a jikinshi. Wani abu da
Habibu bai taba gani ba tun suna makaranta, Habibu ya kasa boye mamakinsa, ya ce “Halan cikin magagin
barci kake?”
Ya harare shi da wata katuwar harara ya ce “A’ah, makuwa na yi”.
Ya nufi resting chair ya yi kwance, ya tallafe kanshi da hannayenshi. Ya lumshe lumsassun idanunsa. Habibu
ya zauna a gefenshi, dai-dai kafafunsa. Ya tsura wa kyakkyawan tafin kafarshi ido, ya ce.
“Ka zo ka kwanta ba ka ce da ni komai ba???”
A hankali Amirun ya bude ido yana kallonshi, bai ce komai ba, sai kuma ya sauke kwayar idonshi kasa. Ya ce
“A irin yadda na dauka tsakaninmu shi ne yarda da aminci ne ginshikin abotarmu. Ban zaci akwai boye-boye
ko rashin yarda ba.
Ban zaci zan iya ganin wani abu naka ina so kana da iko da shi ka kasa mallaka min ba, duk sonka da abin nan
kuwa, muddin zai amfane ni. Kamar yadda nake da yakinin babu wani abu nawa da bazan iya mallaka maka
ba, amma tunda kai a gare ka hakan ne, babu komai, shi ke nan, nagode”.
Habibu ya daga ido ya yi mishi duban rashin fahimta “Ka ba ni magana a dunkule, mene ne nawa kake so Amir
da na ki mallaka maka?”
Ya ce “Kana nufin ban gane irin karbar da ka yi wa zancena jiya ba? Your I don’t care attitude… gashi ya fito
baro-baro, tunda kai har ka manta ma.
To ni jiya ban yi barci ba throughout rayuwata ta shiga cikin wata jarabta, ban taba tsintar kaina cikin kwatankwacin irin wannan halin ba.
Ka dade kana zargin abubuwa daban-daban game da aurena da Harrit, ina gaya maka cewa, nasan abun da
nake yi. Ban yi niyyar gaya maka ba, amma a yau zan gaya maka, na auri Harrit ne don kare kaina daga ZINA a
iyakacin zamana a America, amma ba don ta zama uwar ‘ya’yana ba.
A nawa tunanin shi ne har yau ba a haifi matar da zan ji ina so ba, wadda ta hada wasu muhimman abubuwa
da nake so ga diya mace. Sai jiya na gani a gidanka, kuma jininka. Sai dai a dan zamana da Harrit na shekaru
biyu ya sauya ra’ayina a game da ita, ta yadda har nake jin zan iya haihuwa da ita, sabida karbar musulunci da
ta ce zata yi. Da kuma wasu boyayyun halayenta na kwarai da na fahimta a hankali. Sai dai komi ya zo late
daga lokacin da na dora idona akan MAIRO.
Zan rabu da Harrit na koma gida na auri Mairo, cikin iyaye, dangi, al’ada da addininmu. Lokaci ya yi da zan
gina iyali na kwarai kamar yadda ka gina naka. Amma hakan ba zai yiwu ba sai da goyon bayanka, wanda na
lura kamar bazan samu ba”.
Habibu ya yi shiru yana sauraronsa. Bai katse shi ba, sai da ya kai aya yace “Ameer!”
Ya ce “Na’am, sunan kenan”.
Ya sake cewa “Amiru!!”
Ya ce “Ba ka yi kuskure ba, shi din ne”.
Ya ce “Ka yarda ina sonka, ina kaunarka, ba ni da aboki sama da kai a duniya. Ba ni da wanda na yarda da shi
sama da kai a duniya, amma am sorry to say… Ba zan iya ba ka kanwata ba!!!”.
Cikin matsanancin mamaki Amiru ya ce “Ina da wasu halaye ne da ba ka yarda da su ba? Duk dan Adam tara
yake, don haka bazan shaidi kaina ba”.
Ya ce “100% halayenka na kwarai ne, sai dai ina sara ne ina duban bakin gatari. Mu din nan ba wasu ba ne
Amiru, face wasu ‘yan wani surkukin kauye. Sabida haka ajin rayuwarka da na Mairo ba daya ba ne. Mairo ba
ta da kowa a duniya, daga ni sai Allah, sai Baffanta. Ta fada cikin maraici a kanan shekaru wanda nake so ta
huta kamin na yi mata aure. Na dade ina shan wahala bayan dawowar mu nan kafin in samu ta samu farin
cikin da take ciki a yanzu.
A kalla ta samu ta hada digirinta yadda ko babu ni watarana zata iya tsayawa da kafafunta. Sannan ina so na
aura mata yaro dan makaranta wanda za su ci gaba da fafutukar neman ilmi tare, su tsarawa kansu rayuwa
dai-dai ilminsu kamar ni da Dina. Sannan ina so ta je inda za a so ta, a mutuntata, ba inda za a ga kwadayinta
da wautarta ba. Ina fatan ka fahimce ni?”
Amiru ya tsura mishi kyawawan idanunsa ya ce “Na fahimce ka, ban fahimce ka ba.
Abin da na fahimta shi ne, kana nufin na yi wa Mairo tsufa, sannan iyayena ko dangina ba zasu so ta ba,
sabida kun fito daga kauye, to gaya min wane ne asalinshi ba kauyen ba? Idan kuma kana nufin na fi karfinta
ne, wallahi-wallahi aikin sai na daina, na koma gida tunda bazan rasa abin da zan ciyar da ita ba”.
Habibu ya ce “I don’t wish so, amma kana tunanin Harrit da sauran ‘yammatanka za su bar Mairo ta zauna
lafiya? Idan iyayenka da ‘yan uwanka sun karbe ta?”
Amiru ya ja wani matsiyacin tsaki, tsuuuuu!!! Ya ce “Muhimmin abin da ya kawo ni garin nan wajenka ke nan.
Na zo ne don mu yi wata muhimmiyar shawara wadda tafi karfin a yita a waya.
Habibu ina so mu tattara mu koma gida, mu hada karfi mu kafa bankinmu na kanmu, wanda zamu yi wa
reshe a dukkan 36 states da muke da su a gida Najeriya, mu daina amfanar da bature haka nan, mu koma mu
tsayawa kasarmu ita ma ta amfana da experience dinmu akan banking, amma ya ya ka gani?”
Habibu ya ce “Wannan shawara ce mai kyau. Amma kuma ba ta bukatar gaggawa, sai mun bi komai a hankali.
Na kuma amince da shawararka”.
Amiru ya langabar da kai abin tausayi, ya ce “Allah Yaya Habibu ka ba ni Mairo. Za ka sha mamakina. I
promise to make her happy a gaba daya tsayin rayuwarmu. Jikina yana ba ni Mairo ce uwar ‘ya’yana a duniya
da lahira. Hajiyata zata yi farin ciki da Mairo, irin auren da ta ke fata inyi kenan, auren yarinya ‘yar usli mai
tarbiyyar addinin musulunci.
Ban mata tsufa ba Yaya Habibu, am 37, garau na ke, kar a ledata. Babu abinda Harrit ta dauka a jikina, sai
kwararon roba. Ina killace da wannan ‘yan mazancin mai daraja da na ajiye ga macen da nake so kadai”.
Habibu ya kama baki “Kai dai baka da kunya wallahi. Ni da ka ce surukinka ne kake gaya min wannan
maganar?”
Ya yi wani irin murmushi ganin ya soma samo kan Habibun, ya ce “Yaya to? In fara zance, an bani izini yaya
Habibu?”
Ya ce “Ban yarda ba, ba zaka lalata min kanwa da soyayya ba. Kai ko waya ma ban yarda ka dinga yi mata ba,
ka barta ta yi karatu ka je ka kashe lalurorin gabanka, ni da kaina idan lokacin da na ga ya dace na aurar da ita
ya yi, zan maka magana”.
Amiru yana girgiza kai ya ce “Ban yarda da wannan takunkumin ba, ina nan na bari YA HUCE…… wani ya je ya
siye zuciyarta. Don dai ‘yar gaisuwa cikin waya ai ba aibu ba ce, kuma gaskiya ba zan iya hakuri har nan da
shekaru biyu a gaba kamin ta kammala digiri ba, sanda muka gama shirye-shiryenmu na komawa gida da mun
koma nake addu’ar Allah Ya mallaka min Mairo”.
Habibu ya ce “Ba sai in tana sonka ba, wani malaminsu ta ke so kamar ranta, don na kashe zancen ne, amma
nasan har yanzu tana sonshi, ta dai daina zancenshi ne kawai don na ce da ita karatu nake so ta yi”.
Cikin takaici Amiru ya ce, “To ka ji ba, shi ne ni zaka hanani in nemi soyayyarta, a’a da sake!”.
Dariya ta kama Habibu ganin yadda lokaci daya kyakkyawar fuskarshi ta canja sabida kishi. Can kuma ya kuta
ya ce “A ina malamin nasu ya ke?”
Ya ce “Ina ruwanka da inda ya ke? Idan ka yarda da kanka ka ci a soka ba shikenan ba?”
Ya ce “A’ah gaya min dai, rokonshi zan yi ya daina sonta, ya zo gidanmu in ba shi ‘yammata zuka-zuka guda
hudu kuma kyauta, babu lefe, bare kayan toshi”.
Habibu ya kyalkyale da dariya ya ce “Idan kuma ba ya sonsu fa? Ita din kadai ya ke so?”
Ya ce “Sai mu zuba ni da shi, shege ka fasa. Yanzu haka kalaman soyayya yake gaya mata har ta so shi, shi ne
ni zaka hanani sabida mugunta da rashin tausayi, Allah Ya shirye ka Habibu”.
Ya sake yin dariya ya ce “Ya shirye mu tare, mayen fararen mata kawai, wallahi ko sau daya ka kama
hannunta ban yafe maka ba”.
Ya ce “Ni ko aura min ita ma ka yi, ko farcenta ba zan kama ba, sakata zan yi a gaba in yi ta kallo, in tai kuka in
goyata in rarrashe ta in ba ta feeder tunda Yayanta ba ya taba ‘yar wani, don me za a taba mishi tashi?”
Habibu ya yi murmushi ya san zambo yake mishi, ya ce “A’ah idan an aure ta ni ban isa in hana a tabata ba,
amma yanzun dai bazan yarda ba”.
Ya ce “Na yi alkawari ni Amiru zan rike amanar Yaya Habibu, ranar da na ci ta Allah Ya ci tawa”.
Dariya ta kama Habibu, ya ce “Yauwa, da ka ji kana son taba ta, sai ka garzaya wajen mai jajayen kunnuwa”.
Ya rausayar da kai, ya ce “Bashi ka ci, Allah akwai ranar da zaka biya shi”.
Dai-dai sanda Mairo ta fito daga dakinsu, kanta cikin shower cap da rigar tawul a jikinta iya kauri, ga dukkan
alamu kicin zata don hada abin da zasu yi karin kumallo da shi, don ba sa baiwa Lynder girki ko da wasa, ko ita
ko Dinan ke yi, ba girkin zamani da na gargajiya da Mairo ba ta koya a wurin Dina ba, ba tasan suna zaune a
falon ba ga shi ta riga ta fito sun ganta, don haka ta koma ciki da sauri dama wanka ta fito.
Ta shafa mai ta fesa spray ta sanya wata shirt mai dogon hannu wadda ta manne a lafiyayyar fatar jikinta
sosai, sai ta hada da budadden siket fari sol, yayin da rigar ta kasance launin ja.
Ta fake gashin a tsakiyar ka, baki sidik da shi, sannan ta tura shi cikin jar hular sanyi ta sake fitowa, ta russuna
ta gaishe su ba tare da ta dube su ba, don ba ta ma san ko waye suke tare da Yayan ba. Ta wuce kicin inda
Lynda ta hada mata kayan girki a gefe, ta nade hannun riga ta shiga sarrafa girke-girkenta cikin kwarewa da
gwaninta.
A can falo Habib ya dubi Amiru wanda ya wani narke cikin kujera yana lumshe ido da azabar soyayya, ya ce
“Kai wallahi ka ja girmanka, wannan idan ta ga kana wannan ai sai ta rainaka, a haihuwar karkararmu ka haifi
Mairo, ni wallahi fararen mata ba sa gabana, bakake nake so, don sun fi juriya, kuma ba sa saurin tsufa”.
Amiru ya ce “Ai kai fari ne ina ce? Ni kuwa baki ne, don haka nake neman sirki, kuma laushin jiki da taushinsa
ai sai farar mace malam, mai farar aniya”.
Habibu ya ce “Ba zaka daina yi min zancen banza ba, ni tawa bakar wato mai bakar aniya kake kallonta?”
Ya ce “Ban ce ba malam, kada ka yi min sharri, ka hada ni da baiwar Allah. Dina. Ra’ayi riga, wadda kake so shi
zaka saka, abin da na gaya ma kenan”.
Suka mike a tare, Habibu ya ce, zai shiga wanka ne, shi kuma ya ce, zai je kicin ya taya Mairo girki.
Ta dukufa a kicin tana gashin french bread cikin even ta ji kamshin turaren Yaya Habibu, ba ta juyo ba, don a
zatonta shi ne ya shigo daukar wani abu, ya shiga juya mata chips da ta ke soyawa a fryer. Jikinta ne ya ba ta
ba Yaya Habibu ba ne cikin kicin din don da shi ne zuwa lokacin da ya dauka cikin madafin da ya yi mata
magana. Da sauri ta juyo, a karo na biyu suka sake yin arba da dan Abdurrahman Gaya. Wani dan gaye danye
sharaf, mai yawan gargasa da ginannan jiki irin na Junaidu. Ba yau ta fara ganin irin wannan kallon ba, don ta
kan gani cikin kwayar idon Uncle a duk sanda ta yi wani abu da ya burge shi. Sai dai na Uncle ba ya kassarata
haka, har ta kasa yin abin da ke gabanta.
Wannan ya kassarata, ya kashe duk wata laka da ke cikin gangar jikinta. Ya haifar da kasala gami da tashin
tsigar jikinta duk a lokaci daya. Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki, sai ta ja sagaggun kafafunta don barin
kicin din.
Ya yi murmushi a sanda ta kai bakin kofa, ya ce “Gashin naki zai kone”.
Ta dakata, amma ba ta juyo ba, ya ce, “Mairo sabida na zo in tayaki aiki shi ne zaki tafi ki barni?”
A yadda ya yi maganar cikin sanyi, ya sa ta juyowa? To amma ba ta son ganin wannan mutumin, domin
kwarjininshi da kyawun shi suna firgitata. Shi kadai cikin kicin din, amma ji ta ke kamar cincirindon mutane ne
cikin kicin din suna kallonsu. Ita ba ta taba kebewa da katon namiji ba, don haka ba zata fara yau ba. Da kyar
ta ce “Don Allah ka kashe”.
Ta ja dogayen kafafunta da sassarfa ta fice ta gudu dakinsu, ta rufe kofa.
Ta zauna bakin gado tana maida numfashi, kamar wadda ta yi gudun 1000 metre. Wai me ke faruwa da ita ne
akan bakon Yaya Habibu? Mai yasa ya ke firgitata, kamar ba ta taba ganin namiji ba? Idan kyau ne ai ta sha
ganin mazan da suka fi shi kyau ko a ajinsu, Turawa, Indiyawa da Larabawa, kai har da black American ma,
half-caste da ‘yan Somali, amma mai yasa su ba ta jin wadannan abubuwan da ta ke ji akan Amiru? Jiya ba ta
yi barci ba, da tunaninshi ta kwana, da ta runtse ido shi ta ke gani, idan ta bude idon sassanyar muryarshi ke
tashin amo cikin kunnuwanta.
“Mairo ni ma yaya Habibu ne…. Mairo zo mu gaisa…….”
Ta debi hannuwa ta rafka uban tagumi, har zuwa lokacin numfashinta bai dawo dai-dai ba, bai daina racing
ba.
Muryar Yaya Habibu ta jiyo daga falo yana kiranta. Ta sake rikicewa, ga shi ba ta da hujjar kin amsawa. Dole ta
sake janyo kafa ta fito ba tare da ta amsa ba.
A bakin kofar dakin nasu ta tsaya tana dubanshi ba ta ce komi ba. Ya ce “Yaya? An kammala kalacin?”
Ta girgiza kai.
Ya ce “Yi min magana mana, ko wani abu ne ya faru?”
Nan ma ta girgiza kai. Dai-dai lokacin ya fito rike da katon tire, Lynda ta biyo shi da flask din ruwan zafi suka
dire bisa dining ya ce “Ga kalacin Yaya! Ka titsiyeta sai tambaya kake yi, ba kasan wasu ba sa son yawan
tambaya ba ne?”
Ya ce “Ai to, kai ne ka girka ke nan? To ba na cin girkin maza, tun daga sanda Allah Ya mallaka min mata, don
ba ta nan kuma ba zan fara ba”.
Ya ce “Kada Allah Ya sa ka ci, Mairo taho kinji mu yi kalacinmu, cikin wa zai zuba abincin ba cikinshi ba?”
Ta saki baki kawai tana kallonshi, wai da shi zata ci abinci, ita ko da Yaya Habibu ba ta cin abinci. Ta zo Turai
kam, amma ba ta yarda ta yada al’adun ta na alkunya na malam Bahaushe ba. Maimakon ta ba shi amsa, sai
ta wayance da cewa Yaya Habibu “Ka ci, Allah ni na yi girkin”.
Ta shige daki ta barsu nan, ko ya ci ko bai ci ba su suka sani.
Ta tada yaran suka shiga bandaki ta yi musu wanka, ta shirya su cikin kayan sanyi, kamar kullum. Sannan ita
ma ta shiga ta yi fitsarin da ya cika mata mara, tana sharce gashin kanta Yaya Habibu ya leko “Ya ya kin gama
shiryawa mu wuce?”
Ta ce “Eh, amma ni ban yi break fast ba”.
Ya ce “To na baki minti biyar kada ta sauka ta yi ta jira”.
(Za su je airport dauko Dina ne).
Ta dawo falo a lokacin Amiru da Habibu suna tsakiyar falo suna ta aiki cikin kwamfutocinsu, ta wuce dining ta
zauna kusa da Abbas ta dan tsattsakura kadan ta sa tissue ta goge hannu da baki, suka mike. Shi da Amiru
suna gaba, ita da yaran suna baya cikin motar Habibu Cadillac srd. Amiru ya mika hannu yana karkata
mudubin ‘side’ dinshi dai-dai santar Mairo, yadda zai ke kallon duk wani ‘motion’ nata sosai. Fuskarta ta yi
sayau, babu wata kwalliya, cikin farin gilashi (prada), ‘yan labbanta sirara jazur da su, sai kyalli suke cikin wetlips, suna ratsa shimfidaddun titunan garin Michigan marassa tudu, balle gargada, har suka iso airport din
Detroit-Metro.
Already jirgin ya yi landing suka hango Dina tana daga musu hannu tana tura ‘yar kankanuwar troller dinta, ba
da bata lokaci ba suka nufo gida.
F
Little Mairo tana ta murnar ganin mamarta da ta kwana biyu ba ta gani ba. Shi kanshi Yaya Habibun idan ka
lura zaka ga annurin fuskarshi ya karu sosai. Oh! Ashe haka auren so yake? Mairo ta ce a zuciyarta. Kai ka ce
sun shekara ba su ga juna ba.
A otel din da Amiru ya sauka (Best Western) suka ajiye shi, da alkawarin sai ya shigo da daddare yin dinner.
Kuma Mairo yake so ta yi mishi girki. Dina ta yi murmushi ta ce “Ban fa gane ba, kada ka sa Harrit ta bindige
min kanwa”.
Ya yi murmushi ya ce, “Allah babu wasa cikin maganata Aunty Dina, don ni yanzu kin zama Auntyna, alfarma
nake nema ku yi min ke da mijinki, kokon bara na yana gidanku, duk da mijinki is not hundred percently
agreed (bai yarda gabadaya ba) sabida wasu hujjojinshi marasa makama. Nasan ke za ki dube ni da idon
rahma. Zan ba ku mamaki, zan nemi soyayyar Mairo ba campaign nake so ku yi min ba”.
Har suka iso gida, Dina na jinjina kalaman Amiru a zuciyarta. Ta sanshi, ta san halinshi kamar yadda tasan
mijinta. Karya ko joking ba sa cikin halayyarsa, idan ya ce yes, to da gaske yana nufin yes din babu gudu babu
ja da baya. Babu kuma abin da zai sa shi ya janye abin da ya sa gaba.
Wani irin mutum ne mai nasara akan duk abin da ya sa gaba, wato dai irin mutanen nan ne masu ra’ayin
kansu, ba masu fadin karya don wani ya ji dadi ba. Hakanan ba sa iya boye abin da ke zuciyarsu.
Ta dade tana addu’ar zuwan ranar da Allah zai nuna mata mijin Mairo, ta sha kissima yaya mijin Mairo zai
kasance? Domin ita din ‘yar baiwa ce kamar Habibu. To amma ba ta taba tunanin Amiru ne zai ce yana so ba.
Kololuwar ilmi, nasaba, arziki, kyau, nagarta duk shine. Bankin duniya yana hannunsu, kudin Najeriya gaba
daya yana hannun ubansa, sai ya rattaba hannu a kansu za a yi amfani da su, ko ‘yar shugaban kasa yake so
zai aura. Duk kalar macen da yake so da gudu za a ba shi, amma ya ce; MAIRO, a ganinta wannan abin alfahari
ne a gare su, ita da Habibu domin Amiru ba zai yi karya ba, ba zai yaudare su ba. Ba zai fadi abinda ba haka
yake a zuciyar shi ba. To mai yasa Habib cogewa?
Ta san abin da yake gudu ba zai wuce Harrit da ‘yammatan Amirun ba, domin iyayenshi mutanen kwarai ne,
‘yan jiya, bana yau ba, kuma Habibu kamar Da ne a wajen Abudrrahman Gaya. Da irin wanda ya tsugunna ya
haifa. Shi ya dau nauyin karatunshi tun daga master har PhD da sauran kwasa-kwasan da ya halarta. Yasan
kuma amintarsu da Amiru ba tun yau ba, don haka ta ke ganin ta wannan fannin ba za a samu matsala ba.
Idan ma akwai matsalar ta fannin Harrit ai shi Amirun ba yaro ba ne, yasan yadda zai tsarawa kanshi rayuwa.
Suna kicin ita da Mairo lokacin da Amiru ya iso. Dina ba ta ce mata komai ba, sai ta yi ma kamar ba tasan
zancen ba. Shi da Raymond ne sakatarenshi, suna hira kan harkokinsu shi da Habibu, amma duk hirar ta
gundire shi, sai baza ido yake don ganin ta inda Mairo zata bullo, amma shiru. Habibun na hankalce da shi,
yau surukuta sosai yake nunawa, duk sai dariya ta kama Habibu, sabida wani ‘respect’ na musamman da ya
lura Amirun na bashi. Ya yi fes cikin ta-zarce, na farar shadda excellencior duk da kullum cikin kwalisarshi ya
ke amma Habibun bai taba ganin ya yi mishi kyau irin yau ba, to ina ga ‘yammata?
Wadanda ke jin kamar su ja shi ta karfi, to amma fa banda kanwar Habibu ‘Mairo’, wadda kallon fuskarshi ma
ba zata iya yi ba idan ba dole ba.
Hakurinshi ya kare, tare da duban agogon hannunshi. Shi dai kawai so yake ya ganta, ko hankalinshi ya
kwanta, amma Habibu ya share shi kamar bai san halin da yake ciki ba.
Cikin ikon Allah sai ga Dina ta fito daga kicin ya ce “Wai Dina ina kanwarkin nan ne?”
Ta murmusa ta ce “Tana aiki ne”.
Tsam! Ya mike, kanshi tsaye ya doshi kicin din. Ta juya baya tana yayyanka fruits cikin wata katuwar silba,
daga bakin kofa ya tsaya ya tokare hannunshi a kofar. Ya shagala sosai a cikin kallonta har ya manta abin da
yake yi, bai san kuma iyakacin mintunan da ya bata a tsayen ba.
Dina ta dawo ta ce “Ba ni hanya malam”.
Ya matsa, ta wuce ciki tana murmushi kasa-kasa, a sannan ne ma Mairon tasan da mutum a tsaye. Ta cira kai
ta dube shi, shi ma duban nata yake cikin lumsassun idanunsa. Bai san me zai ce mata ba ta fahimci masifar
sonta da Allah Ya dora masa. Yana daga cikin mutanen da harshensu bai iya bayyana abin da ke karkashin
zuciyarsu. Sai dai action da emotion dinsu ya nuna. Da Mairon zata daure ta dube shi, da ta gane yadda ya yi
laga-laga cikin SOYAYYAH. To amma ta ki, kallo daya ta yi mishi ta dauke kanta, bata sake marmarin
maimaitawa ba.
Ya karaso ya karbi wukar da ke hannunta ya ci gaba da yanka mata gwanda (paw-paw). Dina ta dau abinda
zata dauka ta fita. Ta mika hannuwa cikin sink ta wanke hannu ta juya zata fita.
Ya dago a galabaice, muryarshi har ba ta fita sosai, ya ce “Idan kika fita zan yi miki Allah Ya isa ne…, tunda
Manzo ma ya ce, “BAKONKA, ANNABINKA…” Idan kika fita kin wulakanta ni, shin ma mene ne gare ni da kike
guduna? Na yi miki kama da dodon da zai cinye ki ne?”
Ta ja turus, ta tsaya, ita ba ta fita ba, ita ba ta juyo ba. Ya ajiye gwandar ya sha gabanta sosai har tana jin
hucin numfashinsa. Wanda ke sauka da sauri-da-sauri. Kwayar idanun sun rikide, sun haukace da soyayya.
Ban da alkawarin da ya daukarwa Habibu, da wallahi rungumeta zai yi, sannan ne yake jin zai iya gaya mata
ko mene ne ke cin ransa, zuciyarsa da gangar jikinsa a kanta. Amma a haka ba zai iya bata bakinsa ba, ba zai
iya ce mata komi ba. Da kyar ya daure ya langabar da kai, ya ce “Yi min magana mana, don Allah, Mairo?
Mairo ko ba kya SO na?”
Nan ma shiru, kai ka ce da gunki yake magana. Don ita jin abin ta yi banbarakwai, wai namiji da suna Hajara,
tunda dai babu wanda ya taba tararta da wannan kalmar, wai….. Ya katse tunaninta da cewa, “Mairo Allah Ya
jarrabce ni da sonki, tun daga lokacin da Allah Ya dora idanuna a kanki. Duk wani saukar numfashina a yanzu
da sunanki yake fita, duk wani tunanina a yanzu na yadda zan mallake ki ne a matsayin matata, uwar ‘ya’yana.
Sunana Ameeru Abdurrahman Gaya, ni kadai ne da namiji a wurin iyayena, ina da kanne mata goma sha biyu.
Na yi dukkan karatuna tare da Habibu. Iyayena ‘yan Gaya ne suna zaune a Abuja, amma mu ‘yan asalin garin
Gaya ne da ke cikin jihar Kano, ina aiki a Washington, sai dai kwanan nan zan bari in koma gida.
Ina da mace daya da ‘ya’ya zero. Duk wani abu da kike son ji game da ni, ki tambayi Habibu, zan samu
karbuwa Mairo? Mairo ko ba kya so na?”
Ya tsare ta da wani irin kallo daga can karkashin kasan lumsassun idanunsa.
Mairo ta rasa inda zata sa kanta. Ga kunya da ta baibaye ta, ga jin nauyi, don ganinshi ta ke kamar Yaya
Habibu. Idan ta ce ba ta sonshi ta yaudari zuciyarta, haka idan ta ce tana sonshi ta yi karya. Mutum daya ta ke
wa ‘SO’ na hakika, wato UNCLE JUNAIDU. To amma shi wannan jinsa ta ke har cikin kasusuwa da bargonta ba
zuciya kadai ba, da wani al’amari mai ban mamaki da ba zata iya fassarawa ba.
Tunaninta shi ne, ba zata iya hada rayuwarta da kowa ba, idan ba Uncle Junaid ba. Ta dauki al’amarin da ta ke
ji akan Amiru da BURGEWA da SHA’AWA, wato yana burge ta, yana bata sha’awa, yana daukar hankalinta,
yana bijiro mata da sha’awar tayi aure. Zata iya aurenshi don ta mallaki gangar jikinshi, amma ba don so ba.
Idan aure ne kadai hanyar da zata samu mallakar abin da zuciyarta da gangar jikinta ke so daga gare shi, to
zata iya aurenshi don ta samu, amma SO guda daya na UNCLE JUNAIDU ne!
Wata irin kunya ta kamata, da ta yi wannan tunanin, don gani ta ke kamar ya hango abin da ta ke sakawa da
warwarewa cikin zuciyarta. Tana tunanin idan ta yi hakan kuma ai ya zama yaudara. babbar yaudara kuwa,
don haka ta soma tunanin yadda zata yi ta gudu, ba tare da ta ce da shi komai ba.
Yadda Uncle Junaid ya yaudare ta, ta san ciwon hakan, ko ba don komi ba don amintarsu da Yaya Habibu da
mutumcin da ke tsakaninsu kamar yadda Yaya Habibu ya gaya mata, mahaifin Amiru shi ya dauki nauyin
karatunsa daga masters har PhD. Sabida haka ba yadda za a yi ta yaudari Amiru wata rana ta rabu da shi idan
ta samu Uncle Junaidu.
Haka nan idan ta ce ta yarda tana sonsa ita ma ta yi sallama da burinta na WATA RANA zata hadu da
Uncle Junaid su yi aure a lokacin da Allah Ya nufa. Gara ta ci gaba da dakon soyayyarsa, don idan ta yi aure ya
tabbata ita da Junaid kenan HAR ABADA!
BURGEWA da SHA’AWA ba tubala ne na kwarai da za a gina aure a kansu ba. Idan aka yi hakan, ba da jimawa
ba ginin zai rushe tamkar ba a taba ginawa ba.
Don haka gara ta hakura da rudin zuciya don shaidaniya ce, ta fuskanci gaskiya. Ta yi aure don Allah, ba don
kyale-kyalen Amiru da rayuwa bakidaya ba. Ta ci gaba da jiran Uncle ya gaya mata da bakinsa cewa ba sonta
yake ba, sannan ne zata hakura, ta yi addu’ar Allah Ya kawo mata mijin da zata so da gaskiya, ta kaunata
saboda Allah, kamar yadda ta ke yi wa Junaidu.
Ta daga kai a hankali ta dubi Amiru, wanda har zuwa wannan lokacin bai dauke kyawawan idanunshi daga
kanta ba, binta yake da ido, da zuciya. Idan Mairo ta ce ba ta sonshi, bai san inda zai sa kanshi ba.
Ta ce (cikin kaskantacciyar murya) “Don Allah ka ba ni hanya in wuce”.
Ya ce “Ai ba ki ba ni amsa ba, ko na yi miki tsufa ne Mairo?”
“Ni ban ce ba”.
“To mai kika ce?”
“Cewa na yi ni ba sonka nake yi ba!”.
Wannan ita ce kalma mafi muni da wani ya taba gaya mishi a rayuwarshi. Ji ya yi kamar ta soka mishi mashi a
kahon zucci. Hajijiya ta kamashi. Ta wani fannin kuma sai ta BURGE shi, sabida kai tsaye ta gaya mishi kalmar
da babu wata diya mace da ta taba gaya mishi. Wannan ya tabbatar mishi da cewa, ita ta daban ce.
Sai dai yadda ta yi maganar da yanayinta kadai zai nuna maka tsabar kuruciyarta karara. Don haka bai yi fushi
ba, ance wai, ‘Mai nema yana tare da samu’. Ya lumshe ido ya bude su dukka a kanta “Amma mai yasa Mairo?
Komi yana da dalili, kamar ni, na so ki ne sabida wasu abubuwa guda uku, wadanda bazan iya gaya miki ba. To
ke mene ne naki dalilin?”
Ta so ta ce da shi “Sabida ina da wanda nake so”. Sai ta tuno alkawarin da ta daukarwa Yaya Habibu, na barin
soyayyar Junaid da mantawa da al’amarinshi. Don haka sai ta ce.
“Sabida wasu dalilan nima, da bazan iya gaya maka ba!!”.
Sun dauki mintina uku shiru, babu wanda ya sake cewa da dan uwansa uffan. Kamin ya dauke ido daga kanta,
ya ce.
“Ni kuma na yarda ki aure ni ko da ba kya sona…!!!”.
Ta ce “Ba zan yi hakan ba, idan na yi hakan na yaudare ka, na ci amanar kaunar da nake yi wa Uncle
Junaidu……….!!!”
Ta yi saurin kai hannu ta toshe bakinta da karfi, ba ta san yaushe furucin ya subuto daga zuciyarta ba, ga shi
an ce ‘magana zarar bunu’ ta riga ta fita.
Sai ya kauce da zafin nama ya ba ta hanya sabida wani masifaffen KISHI da ya taho ya tokare masa a kirji. Ai
tana samun hanya ta arce. Da kyar ya iya dago matattun kafafunsa bayan mintina goma sha biyar, ya nufo
falon inda ya tarar da Raymond da Habibu akan tebur suna cin abinci, Dina na tsakiyar falon tana canza
channel a talabijin. Abincin da bai ci ba ke nan, ya zauna cikin doguwar kujera fuskarshi babu walwala, ya ce.
“Raymond idan ka gama sai mu wuce”.
Habibu ya juyo ya dube shi yana nazarinsa, ya ce “Ba zaka ci abincin ba? Mairo ce ta girka maka………..”
Ya dago idanuwanshi da suka canza launi luuuu! Yana kallon Habibu a kankance, ya ce “Ba zan iya ba!!”.
Dina ta ce “Haba don Allah Amiru? Ba ka ga wahalar da ta sha wajen girkin nan ba? Idan ba ka ci ba bazata ji
dadi ba”.
Bai san lokacin da ya ce “Ba don ni ta girka ba, don Yayanta ne”.
Daga haka ya mike ba tare da ya iya hada ido da kowa ba. Ya sake ce da Raymond, “If you finish, meet me
outside….”.
Shima Habibu sai ya ajiye cokalin don jikinshi ya yi sanyi, don bai taba ganin Amirun cikin kwatankwacin irin
wannan halin ba.
Don haka ya mike ya bi shi wajen ya dafa kafadunshi da ya juya baya. Ya ce.
“Mai ya faru ne?”
Ya kalle shi kawai bai amsa ba, tambayar duniyar nan Habibu ya yi, amma ya ce “Babu komai”. Don ba
burinshi ba ne a takurawa Mairo ta aure shi. So na hakika ya ke nema, ba da tallafin wani ba.
Mairo da ta koma daki kwanciya ta yi, rigingine cikin nadama. Kai tsaye ka dubi kwayar idon mutum mai kima
kamar Amiru da ya ce yana sonka, ka ce ba ka son shi, ya zama wulakanci da cin fuska. To amma ita a ganinta
dai-dai ta yi, don ba ta iya karya da yaudara ba. Amma dai duk da haka ta san ba ta kyauta ba, sai dai a
ganinta gara hakan, da ta yi irin auren da zuciyarta ta raya mata.
Dina ta yi sallama ta shigo, dauke da faranti tana cewa “Kin yi barci ne?”
Ta girgiza mata kai, alamar “A’ah”.
Ta ce “To tashi, abincin da kike gudu ne na biyoki da shi”.
Ta tashi ta zauna sosai, ta karbi farantin ta soma ci, Dinan na kallonta. Can kuma ta ce “Mairo mai kika ce da
Amiru ne? Ya shigo cikin walwalarsa, ya fita cikin yanayin da bamu taba ganinsa a ciki ba. Ina laifin wanda ke
son ka?”
Ta cira kai ta dube ta, sai kuma ta sunkuyar. Can kuma ta dago ta dube ta, ta ce “Yana magana ne akan wai
yana sona, ni kuma na gaya mishi cewa, bana son shi!”
Dina ta yi murmushi. Daga jin kalaman Mairo, da yanayin maganarta kasan kuruciya ke dawainiya da ita. Ta ce
“Sabida mai ba kya sonshi Mairo?
Ga shi kyakkyawa, son kowa, kin wanda ya rasa. Ga shi da ilimi kamar Yaya Habibun da kike cewa yana burge
ki. Yana da mata Baturiya, amma ya tsallakota ya zo ya ce yana sonki. Zai iya rabuwa da ita sabida ya aure ki.
Ga shi da kirki, ga addini. Ke kuwa mai kike nema a da namiji da ya wuce wannan?”
Sai Mairo ta sa kuka. Ta kwantar da kai a cinyoyin Dina, tana kuka mai tsuma zuciya.
“Na kasa mance Uncle Junaidu ne Aunty Dina. Na kasa mance dumbin alherin da ya yi min a rayuwa. Shi ne
tsanin duk wani matsayi da matakin da nake kai a yau. Idan na auri wani ba shi ba, na ci amanarsa…….”
Dina ta katse ta “Akwai hanyoyi da yawa da zaka saka wa mutum alherin da ya yi maka ba dole sai ta hanyar
aure ba. Misali shi ne, ka dinga binshi da kyakkyawar addu’a ba tare da shi din ya sani ba. Wannan addu’ar
Allah Ya yi alkawarin karbarta. Kada ki yi mamakin zuwa yanzu shi Junaidun ya samu wata da yake so ya aura.
Ni na kasa gane kan wannan soyayyar da kike yi wa Junaid, maras dalili. Kin ce bai taba cewa yana sonki ba.
Kin ce ba ku yi alkawarin aure ba, kin ce yasan gidan Baffa, amma bai neme ki ba. To ki gaya min wacce hujja
gare ki da zata tabbatar da cewa yana sonki?
Ba ki san akwai masu taimako sabida Allah ba, ba don a aure su ko a saka musu da soyayya ba? Haba Mairo,
ki yi tunani mana? Ki yi aiki da hankalinki. Ki so mai sonki a zahiri da badini. Ki yi aure saboda Allah da raya
sunnar ma’aiki, amma ba don abin da zuciyarki ta afu akai ba.
Mai yiwuwa ne shi wannan abun da kika kwallafawa ran ba alheri ba ne a gare ki, wanda ba kya so din shi ne
alherin. Idan kika fauwalawa Allah a hankali za ki so abun, tunda shi ma Junaid ba lokaci daya kika fara sonshi
ba, so na soyayya, kin ce sai da tafiya ta yi tafiya kika mallaki hankalin kanki, sabida fahimtar halayenshi da
kika yi.
Shi ma Amiru a hankali za ki fahimce shi, kuma ki so shi wallahi fiye da son da kike wa Junaid ma. Ba ki ci
amanar Junaid ba, ba ki yaudare shi ba tunda ba alkawari kuka yi ba. Iyakar soyayya ta gaskiya kin yi wa
Junaidu, ko ba ki aure shi ba Allah Ya shaida ya yi alkawarin sanya masoyan gaskiyan da suka mutu ba tare da
sun auri juna ba a aljanna. Ina tunanin Junaid ya yi abin nan ne da Hausawa ke cewa, “A BARI YA HUCE… SHI
KE KAWO DA RABON WANI”.
Ta dubi Dina sosai, ta ce “Idan haka ne Aunty Dina, kema kin yarda Uncle Junaid yana sona? Furtawa ce bai yi
ba, kamar yadda Inna da Nabilah ke cewa?”
Gyada kai Dina ta yi, ta ce “Eh, yana sonki, amma ya bari YA HUCE… Don babu wata mu’amala ta mutumci da
tausayi tsakanin mace da namiji sai SOYAYYAH!
Idan ma mutumcin ne da farko, to daga baya rikidewa ya ke ya koma soyayya. Kuma dama ita irin wannan
dadaddiyar soyayyar ba a fiya auren juna ba. Wasu ma har su mutu, ba sa kara ganin juna.
Wasu kuma daya ne yake mutuwa ya bar dayan cikin soyayyar, kuma babu yadda dayan zai yi, a karshe dole
zai hakura ya auri wani, wasu kuma hakura suke da auren har zuwa sanda nasu ajalin zai riske su.
Amma Ubangiji ba ya son hakan, don haka bana son ki zamo daga cikin wadanda za su kyamaci sunnar
Ma’aiki sabida soyayya. Manzon Allah (S.A.W) cewa ya yi “Ku yi aure don ku hayayyafa… Bai ce ku yi aure don
soyayya ba. Karewama, duka matan ma’aiki da dalilin da ya yi sanadin da ya aure su, ba soyayya ba.
Soyayyarsu tana kafuwa ne a hankali cikin gidan aurensu. Ki yi koyi da Nana Khadijah wadda halayen amana
na Ma’aiki ya kwadaitar da ita ga son aurensa, shi ma kuma ya aure ta don dukiyarta, addininta da nasabarta.
Ki auri Amiru don yana da nasaba, addini, ilmi da arzikin ma, ku raya sunnah ku haifi ‘ya’ya ku yi musu
tarbiyyar musulunci in gaya miki karshen soyayya ke nan.
Ke nan har wata soyayya kika sani ko halarci? Wallahi HALACCI kike yi mawa ba SOYAYYA ba. Amirun shi kike
so da gaske, na gani a kwayar idonki, na gani a gangar jikinki. Kina jin abubuwan da kike ji kan Amiru a Uncle
Junaidun? Kina neman Junaid ya aure ki ne don ya tallafi rayuwarki a lokacin da kike neman matallafi, amma
ba don kin san hakikanin me aure ya kunsa ba.
Kina so ki ramawa Junaid halaccin da ya yi miki ne ta hanyar ‘aure’ don da shi kika saba, ya sanki, kin sanshi, a
tunaninki wannan shi ne karshen soyayya, to ba shi ba ne, soyayyar aure daban ta ke, Allah ke hadata, kuma
bata fassaruwa.
Haka ita ma kauna daban ta ke, sai kin auri Junaidun za ki ji kamar kin auri Babanki. A sa ma shi din ya ce yana
son naki, balle bai ce ba. Tsayin shekara biyun nan wallahi da duk inda kike ya neme ki, da fa ya damu da ke.
Ita zuciya an halicce ta ne da son mai kyautata mata, wannan shi ne tsakaninki da Junaid ba soyayyar aure ba.
Idan kuma mata sun fara zuwa neman aure ne, to sai mu je gidansu mu neme shi mu kai kudin aure, mu gaya
mishi yadda kike sonshi har kina gayawa masu sonki da auren, ke ba kya sonsu, sabida kar ki ci amanar
soyayyar sa da ya ba ki……G
Ala dole ta murmusa, don tasan zambo ne take mata. Duka wannan bata lokacin da Dina ta yi tana bayani, ba
duka abin da ta ce ne ta yarda da su ba.
Ta dauki Dina a matsayin mai campaign ga Amiru, sabida shi ta sani, shi ne mai irin tsarinm rayuwarsu. Ita
kudin Yaya Habibu ma tsoro ya ke bata, balle na Amirun da ta sha jin suna cewa yana world bank, karewar
Barclays.
Ta yarda ta hakura da Junaid sabida kwararan hujjoji masu karfi da kowa yake gaya mata, hatta Nabilah. Ta ce
da ita lokaci ya yi da ya kamata ta manta da soyayyar da ta ke wa Uncle Junaid ta yi aure. Ta dubi irin auren
da ita ta yi, amma ga shi ya zame mata ALHERI, don yanzu ba abin da ta ke so a duniya sama da mijinta, kuma
shi ma hakan har ga albarkar haihuwa.
Ta sauke ajiyar zuciya, ta koma ta kwanta a gadonta, ta ja bargo har kanta. Barci ta ke so ya zo ya dauke ta,
amma ya ki zuwa. Al’amarin na neman tarwatsa mata kwakwalwa, tareda wargaza mata tunani. Tana son ta
yarda da Dina, halaccin da ke zuciyarta na karyatawa. Amma abubuwan da ta zana ai duk haka suke, zata je
neman auren Uncle Junaid ne? Ko haka zata kare da zaman jiran tsammanin warabbuka?
Zata iya ci gaba da zaman jiran ranar da Junaid zai neme ta, ya bayyana mata soyayyarshi, ya ba ta uzurin da
ya hana shi yin hakan har nan gaba da abada. Amma ba zata iya jure bukatar gangar jikinta da zuciyarta ba,
kamar kowanne lafiyayyen dan Adam. Idan haka ne tana bukatar aure, domin kare kanta daga ZINA, da
sauran ayyukan ALFASHA, cikar mutunci a idon duniya, da karuwar matsayi a fadar Ubangiji.
Wayarta da ke karkashin filo ta soma dan kidi mai sanyi, alamar shigowar sako (text). Cike da mamakin wanda
ya yo mata sako a dai-dai wannan lokacin, karfe biyu na sulusin dare agogonsu na can. Ta mika hannu ta
lalubo wayar ta danna, ba tasan lambar ba, don bakuwa ce. Ga abin da ke rubuce.
‘… When life change, and we go our separate ways, U will still be in my heart till my dying days… My world
has never meet a person like U………!
(A yayin da rayuwa ta canza , ni da ke muka bi hanyoyin mu mabambanta (muka rabu), za ki cigaba da zama a
xuciyata har karewar numfashi na. Duniyata bata taba haduwa da mutum irin ki ba).
Haka ta sa sakon a gaba, tana ta karantawa. Har aka yi kiran assalatu. Don ta tabbatar ba kowa ba ne, Amiru
ne, duk da bai sa suna ba. Allah sarki ko YA HUCE ne? Ta fada a fili. Tana so ta ba shi amsa, ba ta san me zata
ce masa ba.
Da safe ta ke nunawa Dina, ta karanta, ta yi dan miskilin murmushinnan nata, ta ce.
“Ke kuma kika ce mene?”
Ta zumburi baki. “Ni ko kulasa ma na yi?”
Ta yi dariya, ta na kwaikwayon ‘yar muryar ta tace, “Haba Mairo? Yi hakuri ki dan kula sa. Kinga shi ya yi
fushin amma ya sauko, saboda ya gane ba son sa ne ba kya yi ba, kawai ke mai aminta amana da alkawari
ce!”.
Ta yi dariya har kumatun ya lotsa, Dina kam akwai shegen wayo, kanwa ce uwar gami.. Ta ce “To me zan
rubuta?”
“Ki ce kawai ya zo yayi joining dinmu break fast…..”.
Ta rubuta ta tura, amsar da ya ba ta ta sata yin murmushi. Domin ya ambato rabin-ranta (uncle Junaidu).
“…A’ah kirawo Junaid….”.
“He is far-away…!!”(Amsar Mairo )
“And am not closer too… am far-away either, and I’ll not come back…!!! On my way to Detroit Metro……”.
Hankalin Mairo yayi mummunan tashi, da sauri ta jefar da wayar, da gudu ta yi daki ta dauko mukullinta, Dina
na kira amma ba ta juyo ba, cikin rishin kuka ta ce.
“Shi ma zai tafi ya barni, kamar yadda Junaid ya gudu ya barni. Bayan sun kimsa min soyayyarsu. Bana son in
samu wannan heart break (karyewar zuciyar) a karo na biyu”.
Dina ta ce “Bishi Mairo, shi ne ZABIN ALLAH!!”
Gudu ta ke shararawa akan titin da zai kai ta airport din Detroit. Cikin kankanuwar motarta GMC Terrain.
Hawaye na sauka akan kundukukinta. Da gaske Dina ta ke, Wannan ita ce soyayyah! Da gaske Dina ta ke,
Amiru shine zabin Allah!! Da gaske Dina ta ke da ta ce ta kama mai sonta, ta rabu da JIRAN TSAMMANIN
WARABBUKA. Ta karbi ‘Soyayyah’ a hankali zata rikide ta zama ‘Kauna’. To gashi soyayyar ma zata tafi ta barta
da tsammanin warabbukanta wanda bata fata…….…
Koda ta iso airport din ko kulle motar ba ta yi ba, a jikin motar ta bar mukullin. Da gudu ta sheka cikin
reception tana dube-dube, babu Amiru, babu ko mai kama da AMIRU. Ta karasa terminal bayan ta hankade
ma’aikacin da ke kokarin hanata shiga. Dai-dai sanda aka rufe kofar jirgin (Lufthansa), wanda zai tashi zuwa
kasarmu mai dumbin albarka. Ba da jimawa ba kuma ya soma ruguginsa mai gigitarwa bisa kwaltarshi. Kafin
ya dai-daita sosai, a sararin samaniya.
Mairo ta durkushe a nan tana kuka, kukan da ta dade batayi irinsa ba tun bayan rashin BABANTA da INNAR
TA. Fita yake tun daga karkashin zuciyarta. Amiru ya tafi tareda dukkan farin cikin da ta samu cikin Michigan
wanda Habibu ya dade kafin ya assasa. Bai shigo rayuwarta da sauki ba ashe! Ashe ya shigo ne don ya rusa
komai . Ya tafiyar da sauran karfin zuciyarta. Ya dawo da rayuwa unbearable kamar Uncle Junaidun? Meyasa
ita ba ta da sa’a ko kankani a soyayya ???.
Ji ta yi kamar an tsugunna a gabanta, kamin ta dago kuma, an kai hannu a hankali an dafa kafadarta. Don
haka ta dago idanunta jage-jage da hawaye… don ganin ko wane ne wannan???
Masha Allahu La Kuwwata Illa Billah!
Mu biyo Mairo da Amiru da Junaidunta a littafi na uku. Kafin nan ina sauraron ra’ayoyinku kan jaruman namu,
AMIRUN ko JUNAIDUN???
Maman SAFAH da MARWA ce.
A
Ta dago idanunta jage-jage da hawaye, don ganin ko wane ne wannan? Da haka kawai zai zo ya dafata? Ko ta
ce da wani tana neman taimako ne? Wa za ta gani? Yaya Habibu ne!
Cikin matsanancin mamaki ya ce, “Mairo?”
Ba ta amsa ba, illa ta bi shi da kallo, da jajayen, idanunta. Ya sake cewa
“Me ya kawo ki nan? Ina za ki je?”
Nan ma shiru ta yi masa, sai kallonsa ta ke kamar ta rufe shi da duka don haushi. Ya ishe ta da tambaya, ya
barta ta ji da kukan zuci, da takaicin da ya dame ta. Don ji take kamar Amiru ya bula mata kura, ya ja motar
rayuwarshi, ya barta.
A nashi bangaren, shima Habibun, haushi ne ya kama shi, ya ce
“Kina ji ina magana kin yi kunnen uwar shegu da ni? Na ce me ya kawo ki nan, kuma gurin wa kika zo? Ina zaki
je?”
Nan ma shiru ta yi masa, kamar da dutse yake magana, kuma ba ta dauke idanunta daga kanshi ba. Ta kafe
shi dasu kurrrrr! Kamar shi ne ya kori Amirun. Iyakar fusata Habibu ya fusata, ya fizgi hannunta suka fito
harabar adana motoci na airport din, yana baza ido don gano inda ta yi fakin.
Daga can ya hango motar ta yi mata wani banzan fakin a inda aka rubuta no parking, Security ne cikin fararen
kayan ma’ikatan gurin tsaye jikin motar, wato sun kamata.
Ya yi tsaki, tsut…, suka doshi wajen, har yanzu yana rike da hannunta, sai janta yake kamar kayan wanki. Ya
mika hannu ya zare makullin ya soma ba su hakuri ya nuna musu Mairo ya ce ga dukkan alamu ba cikin
nutsuwarta ta ke ba, su yi mishi uzuri su ba shi motar.
Abinka da malam bature da bai san cin hanci da rashawa ba, gami da bin ka’ida da dokar duk da aka shimfida
masa, kememe sun ki yarda, sun dage dole su dangana da ofishinsu in har suna son motar su, don a ka’ida
mai matsala a kwakwalwa, ba a yarda ya tuka abin hawa ba, ya ce lafiyarta kalau, tension ne kawai, suka ce
idan haka ne ke nan tana sane ta karya musu doka? Don haka dole su dangana da ofishinsu, amma ba zasu
bada motar ba.
Cikin matsanancin fushi, Habibu ya dubi Mairo
“Kin kyauta, kin ga abin da kika jawo min ko?
Yau shekaruna goma cur cikin kasar America, ban taba zuwa ofishin ‘yan sanda ba, don haka sai ki bi su ku je,
ki yi musu bayanin dalilinki na karya dokarsu, tunda ni kin yi min banza, sai ki je ku karata…….”
Ya cika hannunta zai tafi, ta riko bayan rigarsa tana kuka. Ya ce
“Wallahi bazan je ofishin ‘yan sanda ba, sai dai ki hakura da motar, ki bar musu mu tafi, kuma wallahi-wallahi
ba zan sake siyan wata ba”.
Ta ce ta yarda, don haka suka bar motar a nan, suka nufi motar Habibun.
Allah Sarki, dan uwa rabin jiki! Sun yi nisa sosai danja ta tsaida su, ya saci kallon Mairo da ke kujerar gefensa,
ya ga har yanzu kuka ta ke mara sauti, ta rufe fuska da mayafinta. Sai ya hadiye fushinsa, ya soma lallashinta
cikin dabara.
“Ni dai idan don na tambaye ki inda za ki ne kike min wannan kukan, to ki yi hakuri. Mantawa na yi, ashe fa
Amiru ya fada min ba kya son tambaya.
Ban da abinki Mairo, idan wajen Junaid kike son zuwa, jirgi ya tashi ya barki, ai sai ki fada mini, na yi miki
booking din wani, amma ba ki sunkuya cikin dubban mutane kina rafka kuka ba, kamar wata mai tabin
hankali. Yana ina Junaid din? Nigeria ko Russia?”
Cikin kuka ta ce
“Ni fa tunda na yi maka wancan alkawarin, ban sake tuna zancen Uncle Junaid ba”.
Ya ce “To ina za ki? Ko AMIRU kika biyo?”
Hantar cikinta ta karta, ta rasa me zata ce masa, don haka ta ja bakinta ta yi shiru. Habibu ya kuta ya ce
“Hakan da kike yi, kina ganin mutumci za ki sayawa kanki?
Shi wancan bai ce yana sonki ba, sabida neman gindin zama kika kwashi jiki kika je gidansu don rashin hankali
da rashin mafadi. Shi wannan da ya ce yana sonki, kin ce ba kya sonshi, sabida kar ki ci amanar wanda bai ce
yana sonki ba. Ya hakura ya bar miki kasar ma baki daya ba garin ba.
To uban me kika biyo shi ki mishi? Da kin same shin me za ki ce masa? Yi hakuri na tuba, ka zo ka aure ni ko
me? To ni bana son rashin hankali da rashin mutunta kai, aikin zubar da kima, da wulakanta kai. Kin riga kin
ce ba kya sonshi, to a barshi a hakan. Allah Ya kawo miki wanda kike so.
Don wanda ya ce ba ya sonka tun farko, daga baya ya dawo ya ce yana sonka, to akwai dalilinshi na yin hakan.
Wato za ki yi A RASHIN UWA… akan yi UWAR DAKI…? To ba da abokina ba!
Idan auren kike so ki yi, ki je ki nemo Junaidun, tunda ba kya son karatun da nake sonki da shi.
Abu na dan lokaci kalilan, ba zaki maida hankali akai ba, mazan nan da kike gani, dukkansu matsala ne, shi
kansa auren idan ba a tsaya anyi shi cikin nutsuwa ba, babu inda ya ke zuwa. Don haka yarinya, kama kanki.
Wayar ma daga yau ba zaki sake rikewa ba, kamar yadda babu ke babu tukin mota. To kin ji”.
Dai-dai lokacin da ya yi fakin a harabar gidansu, ya juya bayan motar ya dauko falmaran din suit’ dinshi da
wayoyinshi ya fito, ita ma ta fita, ba tare da ta yarda sun kara hada ido ba.
Dina ta tari mijinta kamar yadda ta saba a kullum, amma ya sakar mata harara. Ya fincike jikinsa daga jikinta
ya juya ya kara hararar Mairon da ke shigowa sumui-sumui kai a kasa, kamar wata munafuka, ya dawo da
dubansa ga Dina.
“Da saninki Mairo ta dauki mota ta tafi airport?”
Dina ta yi shiru, ya ce “Magana nake, ko ke ma sullutun za ki mayar da ni ku barni na yi ta magana ni kadai?”
Ta ce “To me ya faru?”
“Ya zan tambaye ki kema ki tambaye ni? Amsa nake son ji kawai, kina sane ta tafi ko a’ah?
Yanzu na je kai Amiru zai tashi zuwa Najeriya na ganta tana kuka akan titi uban me ta je yi?”
Dina ta hau kame-kame ganin yadda ya hasala sosai, ta ce
“Am… Eh, ai sako zata kai wa Amirun”.
A fusace ya ce
“Sakon me?”
Ta ce “Ka ga Allah ban sani ba, can tsakaninsu”.
Ya yi dogon tsaki, ji kake ‘tsiiittt!’ Ya maida kallonshi ga Mairo
“Ba ni wayarki”.
Ta soma dube-dube a falon inda ta cillar da ita, can ta ganota bayan room heater, ta dauko ta mika mishi. Ya
kashe ta gaba daya ya jefa a aljihun wandonsa da sassarfa ya nufi bangarenshi ya barsu nan tsaye cirko-cirko
kamar an dasa su a wurin.
Dina ba ta yi gigin binsa ba, don tasan halin kayanta sarai, idan ya yi fushi yana bukatar a daga mishi kafa, har
sai ya sauko don kansa, wanda ba ya daukar dogon lokaci yake yin hakan. Ba ya son aje ana wani lallashin shi
ko ace za a ba shi hakuri.
Ta kama hannun Mairo suka nufi dakin Mairon suka zauna a bakin gado. Ta ce “Kin same shi?”
Ta girgiza kai, wasu hawayen suka zubo.
Dina ta sa yatsunta tana share mata, “Kada ki yi kuka Mairo, mika dukkan lamurranki ga Allah. Amiru yana
sonki, na kuma tabbata zai dawo. Shi ma Junaid yana sonki, ina tabbatar miki da shi ma akwai ranar da zai zo.
Allah kadai Ya san mijin ki a cikinsu, don haka ki dukufa ga neman ZABIN ALLAH ba zabin zuciyarki ba”.
Don haka Mairo ta tattara shawarwarin iyayen rikonta, wato masoyan nan nata guda biyu, da ba ta da ya su a
duniya: Yaya Habibu, da Maidakinsa, Dina. Ta karbi shawarwarin su da hannu bibbiyu, ta fuskanci jarrabawar
karshen shekara da ta tunkarota, wadda daga ita zata shiga shekara ta uku, kuma ta karshe da zata hada digiri
dinta.
***
A yau suna da tutorial class, kan wani kwas da zasu fara jarrabawa a kanshi. Mairo ta fi duk ‘yan ajin su
fahimtar wannan darasin, don haka suka bukaceta da ta yi musu karin bayani. Maryam Muhammad Bedi, ta
fito gaban ajinsu ta tsaya rike da takardu, domin wani abu ne da ta kware a kai, wanda Uncle Junaid ya koyar
da ita, wato dabarun speech in public, ba tare da jin ko da dar a zuciyarta ba.
Ta soma feso sassanyan Turanci daga makogaro zuwa harshe, sannan siraran labbanta su furta. Kai ka ce diya
ce ga Herbert Spencer. Tana bayani ne akan Segmund Freud’s stages of psycho-sexual development, tana
farke theory tana yin kaca-kaca da ita tun daga phallic-stage… Anal stage… da ‘yan uwansu.
Sannan ta koma kan SOCIAL CLASSES; the BOURGEOISIE and the PROLETARIAT………. !!! Habibu da ke cikin
‘yan ajin ya sanya mask (fuska) sai ya soma kuka.
Sannan ya taso ya fito, zuciyarshi cike da alhinin ina ma ace… Malam Muhammad Bedi, zai dawo duniya yau
ya ga Mairon shi na koyar da turawa, da sauran jinsin al’umma.
Don haka Mairo yau da ta dawo gida ta ga sauyi sosai daga Yayan nata. Domin dai ya tabbatar ta tsaida
hankalinta tana karatun, kamar yadda yake so. Yaje makarantar ne ya shiga cikin ‘yan ajinsu don yayi
supervising hakan.
Shi da Dina ne cikin three seater suna aiki cikin takardu da kwamfuta. Ya daga kai ya dube ta yana murmushi,
a lokacin da tayi sallama ta shigo.
“Mairo ‘yan makaranta……Mairon Dina….. Mairon Yaya Habibu”.
Ta yi murmushi, har kumatun ya lotsa. Za ta wuce cikin daki ya ce.
“Zo zauna, mota zan sake miki”.
Da hanzari ta dago ta dube shi. Ya daga mata gira (in affirmation) watau cikin tabbatarwa “Gaya min duk irin
motar da kike so ni kuma na yi alkawarin zan yi kaffara in saya miki. Sannan ki mai da walwalarki kamar da,
bana son ganin wannan shiru-shirun da kika koma. Sannan Dina ta fada min ko hira kin daina yi da ita, kullum
sai karatu. A dinga rage karatun, a dinga baiwa zuciya da kwakwalwa dama su huta, sai karatun ya fi zaunawa
sosai.
Zan tafi Nigeria gobe, akwai muhimman al’amura da zamu gabatar ni da Amiru a Abuja, zan yi sati daya, me
kike so in kawo miki?
Dina ta rubuta min kayan abincinmu na gargajiya su kuka, daddawa, rogo, kubewa da sauransu. Ke kuma fa?”
Ta yi murmushi kanta a kasa ta ce, “Ladidi nake son gani”.
Ya ce
“Ai an yi mata aure. Kina ganin zan rabo mace da gidan aurenta ne na kawo ta? Ai mijinta ba zai so ba, ki yi
hakuri ki kare karatun gida za mu koma gaba daya. Gobe sai ku je da Dina ki zabo motar da kike so, zan bar
komai a hannunta”.
Ta yi godiya, ta kama hannun Little Mairo suka nufi dakinta.
Dina da Habibu suka bita da kallo, dukkansu ba haka suke son ganinta ba. Gaba daya ta sauya, tun ranar da
Amiru ya tafi, daga daki sai daki, daga littafi sai littafi na gaggan malaman sociology. Habibu na addu’ar Allah
Ya sa ba sociology’n ne ya soma taba mata kwakwalwa ba. Shi yasa tun farko bai so ta zabi wannan kwas din
ba, amma ta dage ita nan duniya shi ta ke so, ba don komai ba sai don ta zama Uncle Junaidu. Ita Dina da
yake tasan dawan garin, wato Mairo ta soma kamuwa da matsananciyar soyayyar Amiru sai ba ta damu sosai
ba.
Habibu ya daga Nigeria a washegari, da tsarabar Baffa da iyalinshi rankatakaf! Da aiken Mairo ga Ladidi. Ita da
Dina suka shiga gari suka yo cefanen kayan abinci da kayan amfanin gida da ya kare, sannan suka nufi wani
kamfanin motocin (General Motors) dake nan cikin Michigan ta zabi mota irin tata ta da, watau GMC Terrain
ruwan makuba, suka shirya payment Dina ta biya, ta karbo rasidi da takardun mota aka biyo su da ita gida.
Duk a kokarinsa na son farantawa ‘yar uwarshi, yana sauka a gidan Baffa ya kira wayar Dina, ko gaisawa ba su
yi ba, ya ce ta hada shi da Mairo, ga Ladidi ga Baffa. Farin cikin da Mairo ta samu kanta da jin muryar Baffa da
Ladidi ba zai fadu ba.
Sun dade suna hira, inda Ladidi ke sanar da ita tsohon ciki ne da ita, ta yi mata fatan sauka lafiya, sannan ta
baiwa Dina suka ci gaba da hira ita da Habibu.
Washegari Dina ta kira shi don su gaisa, amma wayarshi a kashe, sai ba ta damu ba, ta ci gaba da ayyukan
gabanta.
Karfe biyu na rana agogonsu na can, ta sake gwadawa ko za ta samu, amma wannan karon ma an sanar da ita
wayar a kashe ta ke. Yinin ranar zungur, haka ta yi ta nemansa amma ba ta samu Habib ba.
Abu kamar wasa, har kwana uku ba su samu wayar Habibu ba, sannan ita ma idan ta buga ba ta shiga.
Hankalinta ya tashi, amma ba ta bari Mairo ta gane ba.
A rana ta hudu ne dabara ta zo mata. Ta kira layin Baffa, bayan sun gaisa ta ce, ko yana da labarin Habibu?
Sun kasa samunshi a waya.
Baffa ya yi gyaran murya ya ce
“Tun ranar da ya zo, ya samu sakon cewa amininshi Amiru ba lafiya, don haka ya tafi Abuja wajenshi ban san
halin da suke ciki ba”.
Dina ta yi zugum! Da waya a hannu, tunani iri-iri babu wanda ba ta yi ba. Ba ta fatan ya kasance ciwon Amirun
yana da alaka da soyayyar Mairo. Ta sanshi bai iya daukan al’amuran rayuwarshi da wasa ba. Idan ya ce, yes
to da gaske yana nufin yes din, babu gudu babu ja da baya, raba shi da abin nan da yake so sai wani babban
ikon Allah.
Sannan Amiru mai-nasara ne, bai taba sanya abu a gabanshi ya kasa samu ba.
Jin motsin fitowar Mairo daga kicin ta yi azamar sauke taguminta ta kakaro murmushi, wanda iyakacinsa fatar
bakinta, ta ce
“Baffa yana gaishe ki, yanzun nan muka yi waya da shi”.
Ta aje farantin da ke hannunta akan centre-table, ta ce “Ina amsawa. Ni Yaya Habibu lafiya dai ko? Tun ranar
da ya tafi har yau ban kara jin wayar shi ba”.
Dina ta shirga karya
“Am, eh, ya kira kina barci ne shi yasa ban tashe ki ba”.
Ta ja farfesun kifin da Mairo ta aje mata, ta soma shan romon da cokali. Tana satar kallon Mairo ta wutsiyar
idonta. Wadda ta maida hankali ga labaran CNN da Mu’azzam Kanti, ke kwararowa. (Alkawari bayan rai).
Amma a zahiri ba sauraronsa ta ke ba, kewar dan uwanta ne ya dame ta, da rashin jin dadin rayuwar ko ta
yaya, da ta samu kanta a ciki. Ba ta rasa ci ba, ba ta rasa sha ba, mai kyau kuma mai dadi, amma zuciyarta a
kuntace ta ke babu dadi. Tana ji a jikinta wani bakon al’amari mai GIRMA na shirin faruwa da ita, wanda ba
zata ce mene ne ko na mene ne ba.
Washegari da asuba bayan ta idar da sallah, ta yi azkar din safiya kamar yadda ta saba. Ta yaye labulen
dakinta tana kallon yadda snow ta yi musu lullubi. Amma hakan bai hana Bature yin harkokin gabansa ba.
Yau ranar ta kasance lahadi, don haka ba zata je makaranta ba, kai kofofi da tagogin gidan ma duk lullube
suke da dusar kankara. Room heater da ke aiki a dakin bata taimaka ba ko kankani wajen rage azabtaccen
sanyin da ta ke ji ba, wanda idan da sabo, to sun saba.
Ta hau kwamfuta don duba emails dinta. Bayan ta yi wa sanyi mugun shiri cikin bakaken coat da bakin
wandon jeans mai kauri, hand-socks (safar hannu) da leg-sock (safar kafa) duk bakake wul. Sakonnin suka
soma bayyana, inda welcome-screen ke tabbatar mata tana da sabbin sakonni guda goma sha biyar.
Ta soma budawa, yawanci duk daga Nabilah suke, tana tambayarta abin da ya samu wayarta ta kasa
samunta. Ta mayar mata da amsa cewa, ta yiwa Yaya Habibu laifi ya kwace, sai na Ir’eesh inda ita kuma ta ke
sanar da ita cewa akwai test’ karfe sha biyu na ranar washegari, wato litinin. Sai na wani dan ajinsu Henry
baturen Brussels inda yake sanar da ita ya wuce kasarsu don mamarshi ta rasu. Ta taimaka tayi masa wani
assignment, ya neme ta a wayarta bai same ta ba.
Ta yi mishi ta’aziyya ta tura, sai wani guda daya da ya yi matukar daukar hankalinta, kasancewar an yi shi ne
cikin harshen Hausa, da rubutu in italic, sannan babu sunan wanda ya aiko, sai logo na hular ilmi. Ta soma bin
rubutun a gurguje.
“Nasarar dan Adam a rayuwa, ana gane ta ne tun daga kuruciyarshi. Mutanen da suka samu kansu cikin
gwagwarmayar rayuwa daga yarintarsu zuwa giramansu ba sa karewa haka a banza.
Ina da yakinin cewa, kina daya daga cikinsu, ci gaba da kokari har sai kin cimma burinki na zama ‘malamar
makaranta’, kada ki bari soyayyar da ke zuciyarki ta zamo barazana ga ci gaban rayuwarki. Dora soyayyarki
akan turba ta hankali da tunani, ba don fita daga wani kunci ko matsatsi na rayuwa ba”.
-mai son ki.
Ta karanta ya fi cikin ‘ya’yan carbi, amma ba ta fahimci me mai sakon ke son isarwa gare ta ba. Wa ya ce da
shi tana cikin soyayya ko cikin matsin rayuwa? Ta yi tsaki mai karfi ta goge sakon daga cikin akwatun adana
sakonta, amma ba ta iya ta goge shi daga kwakwalwarta da zuciyarta ba.
To haka washegari, mai ‘logo’ na hular ilmi ya sake turo mata da gajeren sako.
“…….. Some one misses you!”.
Abin sai ya koma ba ta haushi, wannan karon ma ta goge ba tare da ta ba da amsa ba. A ganinta ko waye,
yana son yi mata yawo da hankali ne. Ta so ta fadawa Dina, amma ganin Dinar kwana biyun nan ba ta cikin
walwala sai ta kyale ta.
Karfe tara na daren ranar, suna bisa tebir dukkaninsu, har yaran, suna cin abincin dare, daga can kicin Lynder
ke ta goge-gogenta. Wayar Habibu ta shigo wayar Dina, kar ku so ku ga mazari a wurin Dina garin rawar jiki ta
datse kiran da hannunta. Ya sake kira a karo na biyu, wannan karon Allah Ya ba ta ikon amsawa.
Muryarshi ba ta fita sosai, kamar mai fama da mura ya ce “Yaya kuke? Ya Mairo da yaran?”
Ta yi ajiyar zuciya ta ce “Duk lafiya muke. Haba Habib? Ka barmu cikin fargaba. Akalla ko mene ne ya faru da
kai ka daure ka sanar da ni, sannan ka kulle wayar. Duk kwanakin nan hankalina a tashe ya ke”.
Ya ce “Ki yi hakuri, bana cikin hayyacina ne, I don’t want to lose AMEERU. (bana so in rasa Ameeru). Ki debo
passport dinku a dakina, daga gobe zuwa jibi ku nemi jirgi ku taho, ki kai yaran gidan Sultana sabida
makaranta, ku taho ke da Mairo”.
Dina ta kidime “Lafiya? Me ya faru da Amirun?”
Bai ba ta amsar ko daya ba, ga dukkan alamu kuka Habibun ke yi kasa-kasa, wanda ba ya so ta jiyo. Hankalinta
idan ya yi dubu ya tashi. Ba kankanin abu ke sa Habibu kuka ba. Kada Allah Ya sa abin da ya darsu a zuciyarta
yanzun ya zam tabbatacce.B
Cikin dauriya ta ce “Habib, me ya faru da shi? Ka gayamin don Allah. Sai dai na taho ni kadai, Mairo jarrabawa
zata fara zanawa, wadda idan ba ta yi ba, sai ta maimaita shekarar”.
Da budaddiyar murya ya ce.
“Karatun ma, ai ina jin ta barshi kenan. AURE zan yi mata”.
Dina ta kyafkyafta ‘yan idanunta ta sato kallon Mairo, cike da fargabar Allah Ya sa ba ta jiyo abin da Yayanta
ya ce ba. Ta ga hankalinta ba ya kanta, ya tafi ga lallashin Little Mairo ta ci abincin da ta ke ba ta da dan
kankanin cokali. Ta godewa Allah da abin da ya darsu a ranta (mutuwar Amiru) ba shi ne ba. Ta kawo
gwauron numfashi ta ce “Kano za mu taho ko Abuja?”
Ya ce
“Ku biyo jirgin Abuja, idan kun sauka ki kirani zan zo na dauke ku”.
Don haka a daren yau bakidayansa Dina ba ta samu isasshen barci ba. Tausayin Mairo ya cika mata zuciya. Irin
yadda ta ke wahala akan karatun nan, ta kwallafa rai a kansa, kullum cikin ‘solving assignments’ ace ya tashi a
banza! Shekaru biyu cur! Sai dai kwarin gwiwar da ta ke da shi, shi ne Habibu ba zai kai ‘yar uwarsa inda za ta
tozarta ko ta wulakanta ba. Duk son da ta ke yi mata ta tabbata bai yi rabin-rabin wanda shi yake yi mata ba.
Sannan akan Amiru ba abinda bazai iya ba.
Da safe karfe takwas ta yi shirin fita don yi musu booking din tickets na jirgin ‘Lufthansa’ wanda zai tashi karfe
goma na daren ranar. Sannan ta dawo, ta cimma Mairo ta fito daga wanka tana shafa akan stool ta ce (tana
mai kawas da kai) “ki hada kayanki masu dan yawa, gida Najeriya zamu tafi, ban san kuma ranar da zamu
dawo ba”.
Tana mai kawas da idanunta daga gare ta, don ba zata iya fada mata abin da Habibun ya gaya mata ba.
Cikin mamaki Mairo ta ce
“Me ya faru? Irin wannan tafiya haka unexpected?”
Dina ta ce
“Bai fada min ba, amma dai ya ce lallai mu tafi”.
Kamar ta yi kuka, ta ce “Ina da ‘test’ yau, kuma jibi za mu fara jarrabawa, kuma Yaya Habibu ya sani, yaya
yake so in yi?”
Dina ta ce
“Hakuri za ki yi, haka Allah Ya shirya miki. Wani hanin ga Allah baiwa ne”.
***
J
irginsu ya sauka a Abuja karfe biyar na asubahi. Ban da kunci da kumburi ba abin da Mairo ta ke yi. Dina sai
lallabata ta ke tana ba ta hakuri. Idan takaicin ya yi takaici, sai ta kai hankici ta tsane hakwayen da ke ‘racing’ a
fararen kundukukinta.
Idan Dina ta ce “Ki yi wa Allah Mairo ki yi hakuri…”
Sai ta ce
“Haba Aunty Dina? Shekaru biyu ina wahala, in fadi, in tashi amma ace sun tashi a banza?”
Wani farin dattijo, dan kimanin shekaru sittin da biyar, wanda alamun jin dadi, tsantsar ilimi da gogewar
rayuwa ya boye shekarun nashi. Sanye cikin kaftan na wata irin farar sassalkar shadda da akalla ta baiwa naira
dubu dari baya, yana da tsagin biyu-biyu a gefen fuskarsa na Fulanin Gaya. Biye da shi escort ne har guda biyu
cikin bakaken suit wadanda harsashi na kowacce irin bindiga ba ya huda su, sun maka ‘dark-spaces’
fuskokinsu kamar hadari, sabanin dattijon wanda kyakkyawar fuskarsa ke yalwace da ni’imtaccen murmushi
wanda da alama tabbatacce ne akan fuskarsa cikin kowanne yanayi.
Abin nufi, cikin halin bakin ciki da farin ciki, kwanciyar hankali da tashin hankali, wannan sassanyan
murmushin ba ya gushewa daga fuskarsa. A takaice dai na halitta ne, watau ‘nature’, shi ne a gaba wajen
tarbar su Habibu a baya.
Don haka kwarjininshi da haibarshi ya sanya dole Mairo ta daina kukan da ta ke, ta tsugunna har kasa ta gaida
shi. Ya dora hannun damanshi a kanta ya ce
“Barka da zuwa Maryamu. Godiya ga Allah da Ya sauke ku lafiya”.
Yaya Habibun kuwa ko arzikin kallo bai samu ba, sai matarshi ke binshi da kallon mamakin muguwar
zabgewar da ya yi cikin kwanaki biyar kacal.
Mairo ta sha mamakin ganin ‘chebrolit’ yau a gida Najeriya. Motar da ko a America, sai wanda ya ci ya tada
kai. Ba wannan ne kadai ya razanata ba, sai tangamemen ‘gate’ irin wanda ake kira ‘Mahdi ka-ture’ da aka
wangame musu a lokacin da motarsu ta sawo kai cikin unguwar Asokoro. Ta hango wani irin ‘American billa’
mai kama da jirgin ruwa.
Ita dai Mairo ido ne nata, sai kuma ta cilla kafa duk inda ta ga an cilla. Tana cewa a ranta, watakila Yaya
Habibu siyar da mu zai yi. Dama ni kudin nan nasa ai ban yarda da su ba. Sai dai kuma babu dar ko tsoro ko
yaya cikin kalbinta, wadda ke cike taf da takaicin rabota da karatunta da aka yi babu gaira babu dalili.
A kofar wani kayataccen falo mai kofar gilashi Yaya Habibu, dattijon da sauran mutanen da ke take mishi baya
suka tsaya. Su kuma aka sa wata mace wadda ga dukkan alamu mai aiki ce, ta yi musu jagora cikin gidan. Ta
nuna musu dakin da za su sauka, sannan ta sanar da su cewa, matar gidan tana asibiti, idan sun kimtsa su
danna ‘bell’ za a shigo musu da abinci. Dina ce ta amsa, amma Mairo ta zama hoto.
Dina ce ta fara yin wanka, sannan Mairo. Suka dauro alwala suka bada faralin sallar subhi da ta riske su a jirgi.
Suka shirya tsaf, Mairo cikin ‘swiss lace’ ruwan madara da yarfin kananan duwatsu, riga da ‘wrapper zani’, ta
yi ‘simple’ nadin kallabi a kanta. Dina cikin atamfar ‘super’ shudiya ita ma riga da zani da yalwataccen mayafi.
A tsaitsaye suka ci abincin sabida kiran Yaya Habibu cikin wayar Dina cewa, su fito za su wuce asibiti.
A babban asibitin koyarwa na Abuja, ita Mairo ta sha wajen matar gidan suka zo da ta ji an ce tana asibiti, sai
raba ido ta ke cike da son ganin wace ce mamallakiyar wannan ‘bungalow’ din. Wanda aka yi amfani da
hikima, ilmi da tunani wajen sarrafa shi. Kai ita a iya yawonta cikin U.S ba ta taba ganin irin wannan ginin ba,
wanda ta fahimci cewa gidan wannan farin dattijon ne, da ya je tarbo su filin jirgi.
Dattijon ne a gaba, sai ‘escort’ dinshi, sannan Habibu da Dina biye da shi, Mairo ce karshen shiga dakin,
wanda ya kasance ‘amenity’. Sabida cikowar da dakin ya yi da kyawawan mata masu kama daya, kuma masu
kananan shekaru akalla daga mai talatin sai mai kasa da haka, sai kuma ‘yammata tsararrakinta, wadanda ga
dukkan alamu ko auren fari ba su yi ba, ta rasa inda tasan fuskarsu kamar ta sansu a wani wuri. Daga can gefe
wata dattijuwa ce kyakkyawa cikin kyakkyawar suttura zaune bisa darduma, ta yi nisa cikin sujjadarta ba ta
san me ake a dakin ba.
Cikowar da dakin ya yi, shi yasa Mairo ba ta yi nasarar hango ‘patient’ din ba, wanda ke ta kelayo aman jini,
har da guda-guda. Daya daga cikin matan ta rike shi tana kuka, sauran ma duk sharar hawaye suke yi da gefen
mayafansu, wanda ke nuni da cewa kauna ce mai tsanani tsakaninsu da dan uwansu.
Da sauri dattijon ya karasa gaban gadon ya tallafe shi cikin kirjinsa. Ya danna wani abu, da gudu likitoci biyar
suka shigo. Nan suka yi umarnin kowa ya fita.
Mairo dama tana bakin kofa, don haka ita ce ta farkon fita. Dattijiyar ma tana sallarta ko dagowa ba ta yi ba,
su ma likitocin ba su ce ta fita ba. Daga likitocin sai dattijon sai Habibu, wanda idanunshi suka kada suka yi
jajur, zaka iya hango tsabar tashin hankalin da ke kwance cikinsu. Don ma yana dauriya ne, amma da fashewa
zai yi da kuka.
Cikin gaggawa kowannensu ke ba shi taimakon da zai iya. Masu jona abin janyo numfashi na yi, masu auna
bugun zuciya na yi, da ya ja wata doguwar ajiyar zuciya su dukka suka kalli juna suka girgiza kai, sannan suka
ci gaba da aikinsu cikin kwarewa da sanin makamar aiki.
Kafin su cire ‘odygen’ din su yi wa Habibu da dattijon alamar su biyo su ofishinsu. Fitarsu ke da wuya leburori
suka shiga dakin suka soma tsaftace wajen. Har zuwa wannan lokacin dattijuwar nan ba ta daina sallah ba. Ba
ta daina kai goshinta gaban mahaliccinta ba, domin ta yi imanin Shi kadai ne zai tashi kafadar danta, amma ba
wadannan tarkacen nasaran ba.
A can ofishin Dr. Fredrick Engles (consultant) na bangaren zuciya, bayani yake musu dalla-dalla na bugun
zuciyar ba-zata da ‘patient’ dinsu ya samu, wanda ya yi mugun yi wa zuciyarshi illa farat daya.
Ciwon zuciya na lokaci daya ya yi mishi mugun kaye, wanda idan ba a yi gaggawar magance mishi
damuwarshi ba, daga yanzu zuwa kowanne lokaci komai zai iya faruwa. Ya kare da tambayarsu, shin ko sun
san hakikanin abin da ke damun mara lafiyan? Domin su sunyi-sunyi ya fada musu, amma ya ki cewa komai.
A nan ne dattijon ya soma yi wa babban likitan bayanin duk abin da Amirun ya fada mishi ranar da ya dawo,
kafin ciwon ya ci karfinshi. Wato kanwar Habibu yake so, ita kuma ta ce ba zata aure shi ba.
Habibu kuma ya dubi likitan ya ce
“Ni kuma na yi alkawarin zan aurawa Amiru Mairo, ko da a gobe ne, idan hakan shi ne zai zamo FANSA ga
lafiyarshi. Ko da kuwa ace wannan shi ne abu na KARSHE da zan gabatar a rayuwata”.
Dattijon ya ce, “A’a Habibu, ba za a yi haka ba, a bi-ta a hankali, domin dai da na kowa ne, ban yarda a
tursasata bisa abin da ba ta so ba”.
Dr. Fredrick ya ce
“Yanzu ina yarinyar?”
Habibu ya ce “Tana waje, sun zo tun dazu. Sai dai ba tasan abin da ke faruwa ba. Da kyar ma idan tasan
Amirun ne kwance a gadon asibiti”.
Likitan ya ce “A kirawo ta”.
Habibu ya fita, jim kadan suka shigo tare da Mairo, duk da ranta a bace yake, amma ba zaka karanci hakan a
fuskarta ba. Ta nemi kujera gefen Habibu ta zauna, kanta a sunkuye, Dr. Fredrick ya yiwa su Habibu
alamar su fita, yana mai ci gaba da rubuce-rubucensa cikin ‘file’. Ofishin ya rage daga shi sai Mairo, har zuwa
lokacin bai gama rubutun da yake yi ba. Daga bisani ya dago, ta karkashin farin gilashinsa yake kare mata
kallo. Cikin ranshi ya ce, Dole maza su kwanta ciwo.
Ya yi gyaran murya, sannan ya yi murmushi, ya ce “Maryam”.
Ta dago a hankali ta dube shi cikin fararen idanunta ba tare da ta ce dashi komai ba.
Ya mike zuwa dan karamin firij da ke gefenshi ya fiddo gorar ruwan (Faro) ya bincire murfin ya sha, ya maida
robar. Maimakon ya koma mazauninshi, sai ya ja kujerar da ke fuskantarta ya zauna. Ya sake yin murmushi
kafin ya sake kiran sunanta. Wannan karon kam ta amsa, ta ce
“Na’am”.
Ya ce “Sunana Dr. Fredrick, ni ne likitan da ke kula da lafiyar iyalin ABDURRAHMAN GAYA. Ina so ki ba mu
hadin kai mu ceto rai, wanda ke cikin halin ha’u’la’i akan soyayyarki. Shin za mu samu wannan taimakon
Mairo?”
Cikin murya mai sanyi ta ce
“Ni Doctor?”
Ya ce “Ke fa Maryam”.
“Ta ya ya zan taimaka?”
“Ta hanyar tayamu jinya, har sai ya samu lafiyarshi, domin a halin yanzu ba ya bukatar komai Maryam, sai
soyayyarki, sannan ne mu ma za mu samu namu aikin ya yi kyau. Mai zai hana ki yarda ki auri mai sonki
Maryam? Har ya ke neman rasa kyakkyawar rayuwarshi a dalilinki?”
Cike da matsanancin mamaki ta ce “wai wanene?”
Yayi murmushi ya ce
“Taso mu je”.
Dr. Fredrick ne a gaba, Mairo na biye da shi. Ya tura kofar dakin dazu ya shiga, ita ma ta sa kai. Dakin babu
kowa, sai mara lafiyan, wanda ke barci sadidan. Sai dai fa da ganin irin barcin da yake yi kasan ba na Allah da
Annabi ba ne, na karfin allurai ne.
Ba karamin bugawa zuciyarta ta yi ba (kamar wancan lokacin da ta fara ganinsa) a lokacin da ta sake yin arba,
da dan Abdurrahman Gaya. Sai dai fa wannan Amirun ya sha ban-ban da wanda ta gani satittikan da suka
gabata, ma’abocin kuzari da koshin lafiya, hadi da wasu nasibobi da ba duk maza Allah Ya mallakawa ba.
Wannan Amirun ya rame fiye da tunaninta, sannan ga dukkan alamu ba karamin jin jiki yake yi ba.
Ta tsaya jikin gadon kawai ba ta ce komai ba, sai dai zaka iya karantar karyewar da zuciyarta ta yi, hadi da
tausayi tsantsa, da shi ma ya bayyana bisa kyakkyawar fuskarta. Tambaya ta ke cikin ranta, ita kuwa wace ce
da Amiru zai kwanta ciwo a dalilinta?
Kamar an ce da shi bude idonka, a hankali ya ke bude idonshi a kanta. To ita ma din kallonshi ta ke, sai ya
dauka ko mafarki ne da gizon da ta ke mishi dare da rana, don haka ya dauke kanshi daga kanta, don bai
gasgata idanunshi ba. Ya mayar da su kan Dr. Fredrick, wanda ke ta murmushi.
Shi kam al’ummar Hausa suna ba shi mamaki akan soyayya, shi wallahi har duniya ta nade, bai ga macen da
zata kwantar da shi a gadon asibiti ba. Balle mutun irin Amiru, dan gata gaba da baya, wanda duk irin macen
da yake so a duniya zai iya aura. Ganin abinnasu yake kamar irin a fina-finan India. Ya kama hannun Amirun
yana murmushi, ya ce
“Kana da bakuwa fa? Wadda tayo tattaki tun daga U.S domin ta duba jikin ka!”
Bai juya ya kara kallon Mairon ba, wadda ganinta ya kara haifar mishi da faduwar gaba. Kirjinshi in banda
bugawa ba abin da yakeyi. Zuwa yanzu ya yarda ita din ce, ba gizo idanun shi ke mishi ba. Likita ya kama
hannun Mairo ya dora mishi kan kirjinshi, dai-dai santar zuciyarshi. Tana jin yadda zuciyarshi ke bugawa fatfat-fat! Amma don karfin hali bai fasa magana ba cikin nishi.
“Ba wajena ta zo ba, ta biyo bayan Yayanta ne”.
Mace mai rauni da saurin karaya, sai ta soma kuka.
Tun fil’azal Mairo mace ce mai tausayi, abin kuka bai da wuya a gurinta, bare an ce a dalilinta ne Amir ya
kamu da ciwon zuciya. Wato wannan ne dalilin Habibu na yanke mata karatunta, Allah sarki Yaya Habibu, a da
har ta kullace shi tayi fushi dashi mai tsanani. Ban da abinsu ita wace ce? Da kasancewarta tare da shi zai sa
ya samu sauki?
Likita ya daga mata gira, ya rausayar da kai, ta gane yana lallaminta ne ta rarrashi Amiru. Ta janye hannunta
daga kirjinshi, cikin sassanyar murya ta ce
“Ni na fada maka cewa ba wajenka na zo ba?”
Ya lumshe ido a hankali, tsayin mintuna biyu bai bude ba. Dr. Fredrick ya zame ya fita, don ya lura Amirun ba
zai iya yi mata magana ba idan yana kallonsu.
Ya sake bude ido a hankali ya dubeta, da wani irin sassanyan kallo. Ta yi hanzarin sunkuyar da kanta, sabida
wasu irin allurai da ta ji suna bin jinin jikinta. Hawayenta na diga a kasa dis-dis.
Ya tara hannu ya taro hawayen, ya ce “Wannan hawayen kuma na mene ne? Ni da kika ce ba kya so na? Ban
yi kuka ba, sai ke?”
Muryarshi bata fita sosai, ba don tana kusa da shi sosai ba, da ba zata ji shi ba.
“How dare you want to me to believe you (ta yaya kike so in yarda da ke cewa) kin zo sabida ni ne? Bayan kin
fada min ga wanda kike so, ni ba kya so na? Na hakura na tafi, don me Habibu zai takuraki ki biyo ni?
To me kika zo ki yi min? Kin zo ne ki kara min ciwon, ko kin zo karasar da ni zuwa kushewata ne?”
Ta dago sosai ta dube shi, ya yi saurin kauda kai, don ba zai iya jurar kallon tsakiyar idanunta a wannan
lokacin ba, wadanda suke kamar ‘magnet’ cikin nashi idanun, suke kuma sanyaya mishi zuciya, tare da karya
karfin zuciyar duk da yake rikewa da jarumtar zucin duk da yake takama da ita. Har yake ganin zai iya jayayya
da ita, ga shi tun ba a je ko’ina ba, ta fara karya lagon zuciyarshi.
Ta ce a sanyaye
“Har airport na bika, dai-dai lokacin da jirginku ya tashi. Ban ce lallai ka yarda da ni ba, amma Allah shaidata
ne!”
Ta juya zata fita, har ta kai bakin kofa, ya tattara iya sautin da ya rage mishi a makoshi ya ce
“Mairo!”
Ta dakata, hannunta jikin marikin kofar, amma ba ta juyo ba. Ya yi tari kuful-kuful! sau uku, kamin ya ce
“Fushi kika yi? Za ki sake tafiya ki barni? Ciwon sonki ya karasa ni?
Ki yi hakuri idan na fadi wani abu wanda ya bata miki rai, zafin sonki ne ya kawo hakan. Dawo ki zauna tare da
ni, ina jin wani sanyi cikin zuciyata, a dalilin tsayawarki tare da ni.
Ki yi wa Allah, kada ki sake barina, har zuwa karshen rayuwarmu. My life has no meaning…… Idan na rasa
soyayyarki. I’m impotent….idan ba tare dake ba!
Bana son Habibu ya takuraki ki aure ni, soyayyarki na ke nema, ba da tursasawar wani ba”.
Wannan lokacin ba ta ce komi ba. Ta rasa abin da zata ce, ta kasa tantance shin abin da ta ke ji game da
Amirun cikin zuciyarta da illahirin gangar jikinta a halin yanzu, soyayya ce ko kauna ce? Idan kauna da
soyayyar ne baki daya, to shi kuma Uncle Junaidu fa? Shi kuma me ta ke masa idan ba so da kauna ba?
Idan haka ne ke nan MAZA BIYU ta ke so ko yaya ne? Soyayya guda daya ce, wadda a halin yanzu ba ta san ko
ta waye ba, don haka ba zata ce ba. Amma data tuna halin da Amirun ke ciki, yana bukatar lallashi da kauna
daga gareta a daidai wannan lokacin kamar yadda likitanshi yace, sai ta dawo kujerar da ke fuskartarshi ta
zauna kanta a kasa. Kamun kai da kunyar Mairon, su ne manyan al’amuran yarinyar da suke kara masa
kaunarta.
Ya tabbatar ba zata taba bude baki ta ce, tana sonshi ba, sai dai idan su kwana a hakan, wannan din ma ba
karamin burge shi ya yi ba. Domin duk yarinyar da zata budi baki gatsar ta ce da namijin da bai zamo mijinta
ba, ina sonka. To wallahi ba matar aure ba ce.
Inda Allah Ya ceceta daga kaifafan idanun Amirun, shi ne shigowar Yaya Habibu, Dr. Fredrick da dattijon da a
yanzu ta gane shi ne Alh. Abdurrahman Gaya. Mahaifin Amiru.
Cikin murmushin jin dadin ganin dan nashi cikin yanayin da ya bashi mamaki, zaune sosai bisa gadon ya zuro
kafafunshi kasa. Fuskarshi cike da walwala da yalwataccen murmushi ya karaso gare su, shima Amirun
murmushin yake yi.
“A’ah sauki ya samu, lallai, kai Mairo ta iya jinya!”.
Amiru ya harare ta, ya ce
“Ni ba wani jinyata da ta yi, sai kuka ta ke yi mini. Kai Yaya Habibu mai yasa ka takurata ta zo? Me ya hada
ciwona da zuwan Mairo Nigeria? Alhalin karatu take yi? Da ka kyale ta ai zan samu sauki ne a hankali cikin
yardar Allah”.
Habibu ya harare shi ya ce
“Kwarai fa, shi yasa na ga kamin ta zo ana ta janyo maka numfashi”.
Duk suka yi dariya ban da shi Amirun. Da kalaman Habibu suka jefa shi a tunanin anya ya cika namiji? Anya
shigowar Mairo rayuwarsa bata maida shi mace ba?
Dr. Fredrick ya ce
“Ya ci abinci Mairo?”
Ta girgiza kai, sannan ta dubi kular abincin da ke kan lokar jikin gadon, ta dauko ta bude, farfesun kaza ne da
ya ji kayan kamshi, a daya kular ‘chips’ ne da soyayyen kwai. Tana son ta tambaye shi wanne zai ci a ciki,
amma kunya ta hana ta, don haka ta zuba kowanne kadan cikin faranti daban-daban ta mika mishi.
Dai-dai sanda ya debo shanyayyun idanunshi ya dora a kanta, sannan ya mika hannu ya karba. A hankali ta ce
“Ba zaka wanke baki ba?”
Cikin kankanuwar murya shima ya ce
“Kin bani abin wanke bakin na ce ba zan wanke ba?”
Ta ce
“Ai ban san inda ya ke ba”.
Alh. Abdurrahman da kansa ya bude lokar ya fiddo sabbin burushi da makilin ya mika mata, ta bude ta shafa
jikin burushin, Yaya Habibu ya mika mata roba. Tana zuba mishi ruwan robar ‘swan’ yana wankewa har ya
gama, sannan ya soma cin abincin. Shi kanshi likitan ya yi mamakin yawan abincin da Amiru ya ci, wanda
tunda aka kawo shi sai yau ya ci, “lallai so ba dama”. (Ya ce a zuciyarshi) sai ruwa ake kara masa mai dauke da
sinadaran abincin maras lafiya.
Hajiyar Amiru ta shigo, bakinta ya kasa rufo, ganin Amirunta na cin abinci, alamun sauki sun bayyana sosai a
gare shi.
Ta ce
“Kai masha’Allah, har abinci ake ci? Lallai sauki ya samu (don ita ba ta san musabbabin ciwon Amirun ba)”.
Ta kalli Mairo da fuska ma’abociyar walwala, ta ce
“Ina muka samo ‘yar kyakkyawar budurwa?”
Mairo ta dukar da kai, Alhajin ya ce,
“Kanwar Habibu ce, kuma surukarki insha Allahu”.
Murmushinta ya fadada sosai zuwa dariya, ta ce
“Da gaske?”
Ta juya ta kalli Habibu
“Na ce da gaske ne Habibu?”
Ya yi murmushi ya ce
“Idan Allah Ya yarda”.
Kunya a wajen Mairo, kamar ta nutse cikin kasa. Hajiya A’isha ta kamo hannunta ta rike cikin nata cike da
matsananciyar kauna da kulawa.
Ana haka Dina da wasu daga cikin kannen Amiru suka shigo, don haka dakin ya yi albarka, ba masaka tsinke,
wanda ke nuni da lallai Amiru dan dangi ne. Kowa na fadin albarkacin bakinshi. Akan yanayin jikin Amirun. Ba
su bar asibitin ba sai dare, aka barshi da Habibu wanda shi yake kwana da shi.
***
C
A kwanaki bakwai da suka biyo baya, Mairo ce ke jinyar Amiru, wata irin shakuwa da soyayya na kara
wanzuwa a tsakaninsu. Ta saba da daukacin kannensa wadanda suke nan ban da wadanda ke aure a kasar
waje da sauran biranen Najeriya, musamman Rayyah, Sabah da Amina wadanda ba a yiwa aure ba. Dukkansu
suna karatu ne a jami’ar Abuja (Gwagwalada), sai dai kuma kowaccensu da sa-ranar ta a kanta.
Yau satin Amiru uku ke nan kwance a asibiti, ya samu sauki sosai da taimakon Mairo, wadda dare da rana ba
ta gajiyawa da hidimarsa. Ita ce cinshi, ita ce shanshi, ita ce walwalarshi kamar yadda likitocinshi ke so duk da
cewa ba ta sakewa su yi hira sosai, musamman idan ya kasance daga ita sai shi a dakin, to maganar duniyar
nan da zai yi da kyar zata ba shi amsar da ‘eh’ ko ‘a’ah’.
Tun kunyar na burge shi har ta soma ba shi haushi, ga shi shi bai iya zama yana wani tsarata da zancen
soyayya ba. Don haka idan Habibu da Dina suka fita, sai kurum ya kwanta ya lumshe idonsa. Ita kuma ta
dauko dan littafin ‘Alma’asurat’ dinta tana karantawa, ko ta makala sautin Sudaith cikin kunnuwanta.
Shi dai tunda tana zaune yana kallonta yana jin motsinta cikin dakin, to babban kwanciyar hankalinshi ke nan.
Yau da asubah bayan Habibu ya dawo sallar asubahi daga masallacin cikin asibitin. Ya tadda Amirun ya idar da
tashi sallar yana lazimi bisa darduma. Ya ja kujera ya zauna bai katse shi ba, har ya gama ya mike.
Ya zauna gefen gadonshi yana lallatsa wayarshi da alama wani yake son kira. Habibu ya dube shi sosai, ya ce
“Wai kai ina Harrit ne? Tasan kana nan kwance kana ciwon soyayya?”
Ya harare shi ya ce “Au ciwon soyayya ma nake yi? Kai mai yasa ka faya rainin wayau ne?”
Habibu ya ce
“Idan ba shi ba ne mene ne? Ka bi ka daga hankalin kowa, ka daga hankalin iyayenka da masu kaunarka. Idan
dai Mairo ce na baka, to ka tashi hakanan mu fuskanci al’amuran da ke gabanmu. Duk wasu ayyuka na saita
kwamfuta nake shigar da su, bari Fredrick ya zo a san wacce ake ciki, tunda ka warke sabida ni kana bata min
lokaci”.
Ya ce
“To ka tafi mana? Na rikeka ne? Tunda ba ka tausayina, har yanzu ko ranar auren ba ka sa min ba”.
Ya ce “Mun gama wannan maganar da Daddy. Na kuma fada mishi zancen Harrit…….”
Amiru ya fiddo ido kuru-kuru, carbin da ke hannunshi ya fadi. Habibu ya yi dariya ya ci gaba da cewa
“Imagine yadda kai ka zaci zai karbi al’amarin shi ba haka ya dauka ba. Shi dai ya ce, idan ta kawo masa jika, to
ba zai karbe shi ba, har sai ta tsarkaka, ta amshi musulunci da zuciya daya. Sai dai fa duk laifin ya fi dora shi a
kaina, da ban sanar da shi tun lokacin ba. Na fada mishi ba zan iya cin amanarka ba. Yanzu ma da na yi mishi
zancen, to dalilin auren mairo ne, ya kuma zama dole ya sani, don haka idan ya zo sai ka san yadda zaka yi ka
amshi laifinka, ka ba shi hakuri…….”
Habibu bai kai ga rufe bakinshi ba, Daddyn ya turo kofar ya shigo, shi kadai ya shigo, ‘escort’ din suna waje,
hannunshi rike da doguwar cazbaha ga dukkan alamu daga masallaci bai koma gida ba, nan asibitin ya zarto
kai tsaye.
Amiru ya rasa inda zai sa kansa, sabida yadda Daddyn ya tsura mishi ido. Ya sunkuyar da kanshi kasa bai ce
komi ba. Ya karasa shigowa cikin dakin sosai, ya ce
“Da gaske ne Amiru abin da Habibu ya sanar da ni?”
Ya sunkuyar da kai cikin amsa laifinsa.
Ya sake cewa
“Ba magana nake yi ba Amiru?”
Cikin raunanniyar murya ya ce
“Na yi laifi Daddy, amma ka yi hakuri”.
Abinka da mahaifi, mai sassanyar zuciya, sannan ga shi Allah Ya halicce shi da son mutum mai amsa laifinshi
nan take, balle kaunarshi da Amiru duk cikin ‘ya’yanshi daban ce. Ya ce
“Ni ba ka yi min laifin komai ba. Amma maganar aurenka da Mairo, na cire hannuna. Idan kai Habibu ka
amince ka ba shi tilon kanwarka arniya ta kashe ta a banza, to sai ka ba shi. Idan kuma za ta musulunta ne ta
zauna lafiya da ita, to sannan ne zan amince Habibu ya aura maka Mairo.
Dama ko ba ka ce ka dawo Najeriya ke nan ba, to ba zaka koma ba. Mu ma nan muna bukatar ku a
ofisoshinmu, don haka idan ta ga zata bar kasarta ta biyoka ta zauna da mu cikin amana, to muna maraba da
ita, idan ba haka ba kuwa babu hannuna cikin aurenka da Mairo”.
Daga haka ya juya ya fita. Daga shi har Habibun an rasa mai kwarin gwiwar dakatar da shi balle su ba shi
hakuri yadda ya kamata.
Amiru ya ce
“Ni ai ka taimake ni, tunda ka riga ka fasa kwan da bazan iya fasawa ba. Tunda kwan ya fashe shi ke nan,
barin shi zan yi sai YA HUCE…… Sannan na je na ba shi hakuri, don a yanzu ya yi fushi ba zai saurare ni ba.
Yau alhamis, ya yi dai-dai da cikar Amiru kwanaki talatin cif a asibiti. Likitocinsa suka sallame shi tare da
dankawa Mairo ragamar shan magungunanshi akan lokaci. Zuwa lokacin Daddy ya sauko sabida yadda ya ke
binshi da nacin ban hakuri dare da rana. Ita Hajiyarshi har ta fi Daddy fushi, amma da yake lafiyar shi ce ta fi
damunsu a yanzu, dole ta yi hakuri ta yafe mishi, ta kuma bi shi da irin kalaman da Daddy ya bishi da su.
Washegari juma’a suka dungumo suka yo Kano, Daddy da Hajiya suka wuce garin Gaya domin fara shiryeshiryen auren, inda su kuma su Habibu suka yo Kano.
Baffa ya yi farin cikin jin cewa auren Mairo ya zo, wanda abin da yake kwana yana addu’ar Allah Ya nuna mishi
ke nan kamin ya dau ransa.
Wato ranar da zai aurar da Mairo. Ya cika burin dan uwansa, sai dai ganin Mairon cikin rashin walwala ya
dame shi, don haka ya leka dakin Ladidi inda ta sauka ya yi kiranta ya ce ta same shi a dakinsa. A lokacin Dina
da Habibu ba sa nan, sun shiga gari.
Baffa ya tirke Mairo yana son jin hakikanin damuwarta, amma Mairo ta ce “Babu komai”. Can karkashin
zuciyarta kuwa, kuka ta ke tana karawa, ba don komai ba, sai don tunanin, ashe Allah Ya rubuta Uncle Junaid
ba mijinta ba ne a gidan duniya?
Ikirarin Inna da Nabilah, bai zamo gaskiya ba!
Ashe tausayi da kulawa daban, soyayya daban? Kenan gara ta karbi mai sonta, ta rabu da wanda ta ke so.
Mace kamarta, bai kamata ace ta zauna jiran tsammanin warabbuka ba. Har sai kuruciyarta ta kode.
Kyakkyawar fatarta ta tattare. Gashin kanta ya canza launi daga baki zuwa fari. Da gaske Dina ta ke, Amiru shi
ne ZABIN ALLAH! Da gaske Dina take, data ce ta kama mai son ta , ta rabu da JIRAN TSAMMANIN
WARABBUKA. Don haka ta rungumi mijin da Allah Ya rubuta mata da hannu bibbiyu, don cimma rayuwa mai
amfani a duniya da lahira.
Ta daga kai sama a hankali, tamkar mai karanto abin da ke zane jikin silin, sannan ta sunkuyar, tana mai tariyo
rayuwarta dalla-dalla tamkar a majigi. Ta amince ta kuma yarda cewa ta rabu da Junaid ke nan har abada! Ta
amince cewa kaddararta ke nan, wani ba ya auren matar wani, kamar yadda mijin wata ba ya auren matar
wani. Tana fatan Allah Ya ba ta ikon cinye jarrabawarta. Ya ba ta ikon yi wa mijin da Ya zaba mata biyayya, har
zuwa karshen rayuwarta.
***
Duk kafafen yada labarai na radiyo, talabijin da jarida sanar da auren Amiru Abdurrahman Gaya da Maryam
Muhammad Bedi ake yi. Tun a farkon satin baki suka soma tuttudowa daga ciki da wajen gida Nigeria, wasu
ta bangaren mahaifin Amiru ne, wanda yake fitacce kuma sananne a Najeriya gaba daya, wasu ta bangaren
Habibu, wasu ta bangaren ango. Abin kam sai sam-barka.
Ranar asabar biyu ga watan biyu na shekarar miladiyya dubban jama’a suka shaida daurin auren akan sadaki
mafi kankanta, wato naira dubu goma a kofar gidan Alh. Abbas mai goro, da ke cikin unguwar Yakasai a Kano.
Daga nan angwayen suka zarce da walima, a gidan saukar baki na ni’ima.
Tun ranar kamu Nabilah na tare da Mairo, kullum ta zo tun safe sai dare ta ke tafiya. Kullum kuma
shawarwari ne da nasihohi masu ratsa zuciya ta ke binta da su, tana mai ba ta misalai na rayuwa kala-kala.
Tana nuna mata ba lallai abin da kake so dole shi zaka samu a rayuwa ba. Dina kam hidima ta ke sadidan, don
tun ana ya gobe daurin aure kannenta da mamanta suka iso daga Malaysia, hatta Hajiyar Dutsinma ta iso
Kano domin halartar bikin Mairo da hakan nan Allah Ya dora mata kaunarta.
A BARI YA HUCE…
A can wani bangare kuma na cikin Kanon, wato filin saukar jirage da tashinsu na Malam Aminu Kano, jirgin
(cathay pacific) ya sauke Junaid Atiku Galadanci da shi da sauran malamai abokan tafiyarsa daga Ukrain
(Russia). Idan har ba ka yi wa Junaid kyakkyawan sani ba, to mawuyaci ne ka gane shi a halin yanzu. Ya kara
GIRMA, ya kara kyau na ban mamaki.
Tun daga nesa ya hango Ilham dauke da jaririnta tana daga mishi hannu, a gefe mijinta ne Abdurra’uf harde
da hannuwa a kirji yana yi mishi murmushi. Junaid sanye ya ke da farar shadda sol, dinkin Muhammed
Abacha kanshi babu hula, wanda hakan ya bayyanar da kwantacciyar sumar kanshi baka wuluk, sai sheki ta
ke. Daure a hannunshi na hagu, agogon ‘polo’ ne ruwan azurfa, sai sheki ya ke.
Suka rungume juna shi da ‘yar uwarshi, kamin ya yi ido biyu da mahaifiyarshi wadda siraran labbanta ke
dauke da murmushin kauna. Zaka iya karanto tsantsar farin cikinta akan kyakkyawar fuskarta na murnar
Ubangiji Ya dawo mata da Junaidunta lafiya.
Yana shiga gida wanka ya fada, bayan idar da sallar asubahi wadda ta riske shi a hanya. Ya fito cikin wata
shaddar ‘dark green’ sai zuba kamshi yake na turaren ‘212’, bai ko kalli garar abincin da Ilham ta jere mishi ba
ya yiwa Hajiyarshi sallama ya ce, zai je ya dawo.
Cike da murmushi ta ce
“Ina zaka haka? Har da ba zaka iya tsayawa ka ci abinci ba ko kadan ne?”
Ya girgiza kai cikin wani irin yanayi da shi kanshi ya kasa tantance ko na mene ne da ya samu kansa a ciki
“Gabana ne ke faduwa Hajiya, zan fara zuwa na ga MAIRO”.
Ta yi murmushi, ta ce
“Junaid mai Mairo! Allah dai Ya tabbatar mana da ALHERI”.
Ya ce
“Ameen”.
Acaba ya tare ya hau zuwa kofar gidan Alh. Abbas. Sai dai kuma me? Tun daga nesa yake hango cincirindon
jama’a a kofar gidan. Faduwar gabansa ta kara tsananta, ya soma addu’ar Allah Ya sa ba Baffan Mairo ne shi
ma ya bar duniyar ba. Cike yake da tunanin, ya ya zai ga Mairo a yau ne? Wane irin girma ta kara? Wane irin
ci gaban rayuwa ta kara samu a tsayin shekaru biyu da watannin da ya yi bai ganta ba?
Ya san a yanzu ta saba da gwagwarmayar rayuwa, da yake so ta fuskanta, kafin ya bayyana mata soyayyarshi.
Mai mashin ya sauke shi a farkon layin sabida yawan ja’amar da yake hangowa a dai-dai gidan Alh. Abbas, sai
dai kuma tun daga nesa ya nemi gidan Alh. Abbas ya rasa, sai wani katafaren gini kawai yake iya hangowa mai
dauke da fenti ruwan kasa da ratsin ruwan madara.
Ya soma tunanin ko ya yi batan kai ne? Sai dai kuma duk sauran gidajen layin da ya lura da su a zuwanshi na
farko suna nan yadda suke, don haka da kafarshi ya karasa wajen wasu masu sayar da rake da ke daura da
gidan ya yi musu sallama.
“Don Allah ko ina ne gidan Alh. Abbas mai goro?”
Daya daga cikin samarin da ke shan rake ya yi mishi nuni da wannan gidan da yake kokonto. Ya kara da cewa
“Ka zo daurin aure ne? Ai tuni an daura angwayen sun wuce walima a Ni’ima, sai dai ka bisu can”.
Ya yi musu godiya ba tare da ya tambaye su daurin auren wa ake yi ba.
Ya karasa ‘gate’ din gidan, dai-dai lokacin da Lawan daya daga cikin ‘ya’yan Alh. Abbas ya fito sanye cikin
babbar riga yana ta sauri ga dukkan alamu wajen walimar zai je, saura kadan su yi karo da juna. Ya mika mishi
hannu suka yi musabiha.
“Don Allah samari ko maigidan yana nan ne?”
Lawan ya ce
“Eh, yana nan, amma shi ma yanzu zai fito mu tafi wajen walima”.
“Taimake ni don Allah kamin ya fito ka ce da shi yana da bako”.
Lawan ya juya ya koma cikin gidan. Jim kadan ya fito ya ce
“Ka shigo mu je”.
Ya yi mishi jagora har ‘sitting room’ na Baffan. Junaid ya sa kai tare da sallama.
Cike da fara’a Baffa ya amsa, yana mai gyara zaman hular (Zanna Bukar) da ke kanshi. Yaci ado har ya gaji da
tsadaddiyar shadda. Ya tsurawa Junaid ido, yana mai son tuno inda yasan fuskar. Junaid ya zube kasa yana
gaida shi, Baffan ya ce
“Haba-haba samari, hau kujera ka zauna”.
Amma Junaid ya ki, surukuta sosai yake nunawa.
Baffa ya koma ya zauna ya ba shi hankalinsa suka kara gaisawa cikin mutunta juna.
Baffa ya ce
“Na so na san fuskar, amma na sha’afa”.
Junaid ya yi murmushi, ya ce
“Ni malamin su Mairo ne, a can makarantar da ta yi a Minjibir. To bayan sun gama karatun a ranar ba mu
samu damar yin sallama ba, aka yi kirana a gida da gaggawa cewa, kanina ya rasu.
To bayan nan kuma ba da dadewa ba aka turani karo karatu a Ukrain, sannan ina da wasu uzurirrika da suka
sa ban nemeta a wancan lokacin ba. Na bari ne sai na dawo, sabida shekaru biyu kacal zan yi. Ga shi yau Allah
Ya nufe ni da dawowa. Baffa na zo ne ina so zan auri Mairo”.
Baffa ya yi shiru na lokaci mai tsawo, har Junaid ya fara shan jinin jikinsa, cewa amsar da zata fito daga
bakinsa ba mai dadin ji ba ce.
Baffa ya ja doguwar ajiyar zuciya
“Kai ne Junaidun Mairo dama?”
Bai amsa ba, kanshi yana kasa
“Na so na tuna inda na sanka, sai a yanzu na tuna a wajen jinyar Malam Bedi.
Dan uwana ya bar min wasiyya a kanka cewa, duk ranar da ka zo ka ce kana son Mairo, to na aura maka ita
ba tare da na karbi ko sisin kwabonka ba. Amma Junaid muna namu ne, Allah na naShi.
Na yi jiranka Allah Ya gani tun lokacin da Mairo ta kare makaranta, ina tunanin bada dadewa ba zaka zo min
da zancen aurenta kamar yadda Malam Bedi ya yi zato, amma shiru. Don haka da Yayanta ya dawo ya tafi da
ita can inda yake aiki a kasar Amurka, a can ne Allah Ya hadata da abokin Yayanta, ga shi yau har mun daura
aure……..”
Ya wani irin dago cikin ‘slow-motion’ yana duban Baffan Mairo. A lokaci guda kuma zufa (gumi) ya soma
bubbugowa daga kowannen sashe na jikinsa. Duk da na’urar sanyaya daki da ta maida dakin kamar firinji,
wannan bai hana shi zufa ba… Idanuwanshi sun kankance sun yi jazur har sai da Alh. Abbas ya tsorata.
Cikin rawar murya Baffa ya ce, “Hakuri zaka yi Junaidu, hakika ka yi abin nan da mutane ke cewa, A BARI YA
HUCE…… Wanda shi ke kawo da rabon wani”.
Cikin sarkakkiyar murya mai dauke da rishin kuka, ya ce
“Amma Baffa ai itama gaggawar ba ta da amfani… Itama gaggawar daga shaidan ce…”
Baffa ya ce “Na san haka Junaidu, amma ni ma ina so ka yarda da cewa ‘matar mutum….. kabarinsa ce’. Kamar
yadda mijin wani ba ya taba auren matar wani, ka yarda da kaddara, ka amince haka Allah Ya hukunta muku.
Ita kanta Mairo na lura ba son auren ta ke ba, don dai tana da zurfin ciki da biyayya ne kawai. Sannan kai ma
ka yi kuskure. Abin da kake so ba ka yi mishi rikon sakainar kashi ba.
Nasan ka yi ne don kana da tabbacin soyayyarta, to abin da nake so ka gane shi ne, soyayya daban, mijin aure
daban. Shi mijin aure da matar aure tun a haihuwar dan Adam ake rubuta mishi, wato rubutacce ne a lauhulmahfuz.
Ka dauki hakan a matsayin jarrabawa ce daga Allah! Sai ka yi JURIYA ka roki Allah Ya ba ka ikon cinye
jarrabawarka!! Ba ka san musayan ALHERIN da Allah zai yi maka a dalilin yarda da hukuncinSa ba.
Ina mai baka hakuri Junaidu…… Junaidu Allah Ya huci zuciyarka…!!!”
Duk dauriyar Baffan shi ma sai ya fashe da kuka. Ganin babatu yake shi kadai Junaidun bai san yana yi ba. Ya
tafi can ga wata duniyar tunani mai zurfin da ba ya misaltuwa. Bai san cewa hawaye suna gudu a
kundukukinsa ba, duk da jarumtakar da yake nunawa kuwa. Al’amarin yake tunowa filla-filla, wato rayuwarsu
cikin Minjibir ta lokaci mai tsawo.
Ashe Allah Ya rubuta, Mairo ba matarshi ba ce, those tears… those emotions will forever remain GREEN in his
memory. Ya mike zai fita, juwa ta kwashe shi ta warbar a tsakiyar dakin. Ko kafin Baffa ya mike. Junaid ya yi
dogon suma.
Baffa mutum mai hankali, bai yi kururuwa a kawo mishi dauki ba, ya taso daga kujerarshi ya kama tsintsiyar
hannun Junaid ya tabbatar ba mutuwa ya yi ba. Sai ya bude firinji ya dauko robar swan mai sanyi ya yayyafa
masa ya shafe fuskarsa. Yana mai karanto mishi duk addu’ar da ta zo bakinshi, yana tofa mishi.
Ya ja doguwar ajiyar zuciya ya bude kyawawan idanunshi. Baffa ya kama hannunshi ya zaunar da shi ya ci
gaba da ba shi baki, amma Junaid ya tabbatar ya yi RASHIN da har abada ba zai iya mayarwa ba.
Ba wai ba zai samu mace mai kyau kamar Mairo ba, a’a, Mairon ce daban ta ke a zuciyarshi. Allah Ya riga Ya
halicci zuciyarshi da soyayyar Mairo. Ya tabbatar shi da wani abu wai shi ‘AURE’ har duniya ta nade! Zai iya
jurar kowanne irin hali ya samu kansa a ciki, amma ba zai iya jurar hada rayuwa da wata diya mace ba
Maryam Muhammad Bedi ba.
Ba tare da ya iya furta kalma ba ya mike zai fita, Baffa ya rike gefen rigarsa,
“Ungo ruwa ka sha”.
Ba musu ya karba ya kafa kai, ya soma kwankwada. Amma ji yake kamar yana shan madaci, sannan saukar
ruwan a makogwaronshi tamkar digar dalma ne a zuciyarshi, amma hakan bai hana shi ci gaba da sha ba, don
tabbatarwa da Baffan cewa, ya bi umarninshi.
Baffa ya ce
“Dakata in kirata ku gaisa”.
Ya ce
“A’ah Baffa, bana son ganinta. Na rasa mahaifina ma na hakura balle MAIRO?”
Baffa ya yi murmushi, ya ce
“Shi din zaka iya rasa shi ka manta, ka hakura, amma ita din ba zaka iya mantawa ko ka hakura ba,
kasancewar (mata) wani bangare ne na gangar jikinmu, ba zamu iya rayuwa ba su ba.
Kada ka ce rashin Mairo zai hanaka aure, a kul, kada ka fara. Zauna nan in kirata ku gaisa, tunda ita ba ta da
laifi, mu ma kuma ba mu da laifi, daga ni har Yayanta, don babu wata kama ko shaida mai nuna kayi niyyar
auren Mairo. Sannan shima yana da babbar hujjarshi na yin hakan. Duk laifin naka ne. Daga yau ya kamata ka
san cewa ba a daukar abin da ake so da wasa”.
Bai saurari amsarshi ba, ya fita ya nufi cikin gidan kai tsaye domin kiran Mairo.
Duk da cikar da gidan ya yi da jama’a, hakan bai hana Baffa kutsawa har dakin su Mairo ba. Suna zaune ita da
Nabilah, Amina, Rayyah da Sabah kannen Amiru da Iman, Radhiyyah da Hafsat kannen Dina dukkansu babu
wacce ta kai shekaru ashirin. Suna ta hirarrakinsu cikin hankali da nutsuwa kamar ba a gidan biki ba, sabida
ilimi da gata da ya ishi kowannensu.
Su Habiba da Hajara ana ta daura manyan tukwane ana saukewa, hidima sosai babu kama hannun yaro,
Ladidi tana asibiti don haihuwa ta zo don haka ba ta samu halartar gidan yinin ba.
Dina da mamanta da sauran jama’arta suna dakin baki inda aka yi musu masauki, an wadata kowa da duk
wani nau’i na kayan ci da sha na gargajiya ne ko na bature.
Baffa ya tura Hajara ta kira masa Mairo, ta sha kwalliya cikin wani tattausan leshi cotton beig colour, mai
ratsin baki ba ta sa goggoro ba, don duk yadda Nabila ta kashe kudi wajen nadin bakin goggoron Mairo ta ki
ta sanya. An yi mata siraran kalba yiri-yiri sama da guda dari biyu, wadanda jelunan suka kwanta a dogon
wuyanta.
Daurin kallabin da ke kanta ya dace da zubin kwalliyar tata, daga wuya, kunne, hannu har kafafunta wasu irin
siraran ‘english gold’ ne masu sanyin kyau a ido, inda duk ta gilma sai walwali ta ke, haka inda duk ta gitta
kamshin turaren ‘fahrenheit’ da ‘cerruti’ ke tashi a jikinta. Sanye a kafarta wani ‘flat’ takalmi ne samfurin
‘Gucci’. Amarya dai sosai mai wani irin fitinannen kyau na daukar hankali da ban mamaki.
Ta bi bayan baffa har zuwa dakin ganawa da bakinsa, wanda ke daga wajen gidan. Zuciyarta cike da tunanin
ko kiran me Baffan ke mata haka cikin mutane? Ta lura shi dai ya fiya damuwa da damuwarta, har tausayi
yake ba ta. Son da yake mata ko diyanshi su Ladidi ba su samu 20% ba.
Lokacin da suka shiga Junaid ya juya baya ne, hannuwanshi sarke a bayanshi. Ya tsurawa wani ‘family picture’
na al’ummar gidan gaba daya ido, ciki har da Mairo, da wani magidanci mai masifar kama da ita, wanda a take
ya ba shi sunan YAYA HABIBU.
Juyawar nan da zai yi, idanunshi cikin na Mairon da zuciya ba ta taba hutawa ba ko na second daya tsayin
shekaru takwas da sonta da kaunarta.
Mairo dai idanunta kankancewa suka yi, sannan hanjin cikinta ya dunkule wuri daya. Cikin kowanne hali ba
zata mance wannan fuskar da a kullum ta ke kara-kaina cikin mafarkinta ba.
Ba zata mance wannan kyakkyawar fuskar da ke sanyata cikin farin ciki da jin cewa ita ma cikakkar mutum ce
kamar kowa a duk sanda ta samu kanta cikin (inferiority complex). Ba zata mance wannan Junaidun, da har
gobe babu mai kima da darajarshi a zuciyarta ba.
Ganin sun mance da shi a dakin ya sanya ya fita zuciyarshi babu dadi (Baffa). Mairo ce ta fara sunkuyar da
kanta (feeling guilty), idanunta suka ciko da hawaye.
Ta kai tafukanta bisa fuskarta ta soma kuka. Bai katse ta ba, sai da ta yi mai isarta. Kuka ta ke, kukan sabo,
kauna da kewa. Kuka ta ke, don sanin cewa yau ta RASA abu mafi muhimmanci a rayuwarta. Wato wannan
Junaidun, da har gobe babu kamarshi a zuciyarta.
Wani bangaren na zuciyarta ya tunasar da ita cewa
“Akan me za ki yi kuka? Junaidu ba sonki yake yi ba.
Da yana sonki da ya neme ki. Sai da ya ji kin yi aure sannan ya zo, to me ya zo ya yi miki a halin yanzu?”
Don haka ta juya zata fita, ba tare da ta ce da shi komai ba. Ya zo ne ya yi mata yawo da hankali kawai. Cikin
muryar da a kullum ta ke mafarkin sake ji a rayuwarta, ya ce “Congratulations Maryamah”.
Shi kadai yake kiranta da wannan sunan, don haka sai ta juyo ta dube shi cikin ido, ta ce, “Na gode”. Sai ta sa
kuka.
Ya ciro hankicinshi cikin aljihun rigarshi ya mika mata, “Share hawayenki Mairo, ni ban zo don na saki kuka ba.
Na zo wa Baffa ne da maganar aurenmu, ya ke sanar da ni cewa, NA BARI YA HUCE….. ya zamo RABON WANI.
Amma hakan bai sa na fidda rai ba, mai yiwuwa wata rana Allah Ya hadamu aure a aljannah. Rabon duniya
mai karewa ne, na lahira shi ne dauwamamme.
Ba zan ce laifina ba ne ya sanya kika zama rabon wanina, sai dai na ce hukuncin Allah ne. Amma ban taba
tunanin zan dawo na samu kin yi aure ba.
A kullum zuciyata na fada min, karatun nan da na sanki da shi shi kike yi. Na sha yi miki email da address
dinki ba ki replying ba. Nima kuma ban sanya suna ba. Don banaso in shiga cikin karatunki da soyayyata. Bana
so na daguka miki lissafi sabida nima lokkacin karatu nakeyi. Na rasa Sagir a ranar candy dinku, don haka na
tafi………”
Ta yi saurin dagowa ta dube shi, furucin Nabila ta tuna “Uncle ba zai tafi haka kawai baku yi sallama ba, sai dai
inyi mishi UZURI da wani babban al’amari mai muhimmanci da ya faru da shi”.
Ya ci gaba da cewa
“Bayan sadakar ukkun Sagir ya kama zan tafi Ukrain yin masters dina da federal ta dauki nauyinmu. Sannan a
wancan lokacin na yi tunanin gara na bari ki yi zurfi cikin karatunki n jami’a kafin lokacin ni ma na hada
masters dina.
Kuskuren da na yi shi ne, ban zo na samu Baffa da maganar tun a wancan lokacin ba. Sannan ke ma ban fada
miki ba, don alkawari muka dauka kamin mu fara aiki a makaranta cewa, babu SOYAYYA tsakanin malami da
dalibi. Amma Mairo ai ko ban furta ba ke ma kin san INA SONKI…!!!”
Ta lumshe ido a hankali, duk wani bacin rai da ke zuciyarta sai ya yaye, ko ba komai abin da ta ke kokonto,
ikirarin Inna da Nabilah yau ya zamo gaskiya, ko da wannan ta tsira ya ishe ta rakiyar rayuwar har zuwa ranar
da muka daina numfashi.
Hankicin sa ya miko mata. Ta karbi hankicin ta share hawayen idonta, ta dago ta dubi Uncle Junaidu, ya yi
mata murmushin da bai taba yi ba. Ita ma ta mayar mishi da martanin murmushin da har abada ba zai taba
gushewa daga zuciyarsu ba.
Da baya-da-baya ta ke fita daga dakin. A yayin da ta cimma kofar ta kama marikin kofar ta rike, sai ta daga
hannu a hankali tana yi mishi bye-bye. Ba shi da kuzarin da zai daga na shi hannun, shi ma ya yi mata.
Tsayin mintuna ashirin da fitarta, amma bai motsa daga inda yake ba, har Baffa ya dawo falon ya dora hannu
a kafadunshi, ya soma yi mishi kalami, masu sanyaya zuciya.
Da taimakon Allah Junaid ya iso gida. Tun daga Yakasai har Galadanci a kafa, shi kanshi bai san inda yake cilla
kafarshi ba. Mai yiwuwa ne don kasancewar ita kafar ta riga ta san hanyar.
Yadda ya zube a falon Hajiyarshi ya yi bala’in tayar mata da hankali, to haka kanwarshi Ilham da ta cillar da
babynta ta taho ta tallafi dan uwanta, duka tambaya daya suke kwararo mishi, wato
“Lafiya?”
Cikin dauriya ya ce “Kada ku damu Ilham. Amma na rasa Mairona, Hajiyata Mairo ta yi aure!”.
Ilham sai ta sa kuka sabida karyewa da zuciyarta ta yi. Cikin rishin kuka ta ce
“Ni dama Yaya Junaid ai na fada maka tun a wancan lokacin cewa, hujjarka na Maryam na sonka, ba hujja ba
ce da zata hanata yin aure ba”.
Hajiya ta yi murmushi ta dubi Ilham, “Kada ki zamo mai jayayya da kaddara mana? Allah Ya riga Ya rubuta
Mairo ba matar Junaid ba ce. Sai mu taru mu yi addu’a, Allah Ya sa hakan shi ne mafi ALHERI a gare mu baki
daya”.
Tayi wani dan tunani, tace “kai, yarinyar nan ta taba zuwa gidannan, lokacin duk bakwanan, naso na ganeta
don na taba ganinta a wajen makokin mahaifinta, ta gayamin sunan ta maryam, amma sai tacemin ke
kawarta ce. Allah sarki, haka Allah ya rubuta.” Shidai baiyi magana ba, sai Ilham ce ta kara tsananta kukanta.
A kwanakin da suka biyo baya, Junaid shirye-shiryen komawa Russia yake ba tare da sanin kowa ba, domin
neman kwalin PhD dinsa, ba shi Kano ba shi Abuja, sai da ya kammala shirye-shiryenshi tsaf, sannan ya sanar
da Hajiyarshi. A cewarshi ba zai iya zama a cikin kasar da Mairo ke rayuwa da waninshi ba.
Da fari ta so ta ki amincewa, amma daga baya sai tausayinshi ya rinjayeta, ta ce
“Junaidu idan hakan ne kwanciyar hankalinka, to ka tafi, Allah Ya bada sa’a. Junaidu Allah Ya yi maka albarka”.
Da wannan kwarin gwiwar da addu’a gami da fatan alherin na UWA-mahaifiya Junaid Atiku Galadanchi, ya
durfafi karatun PhD dinsa a babbar jami’ar Ukrain da ke kasar Russia
***
D
Awashegarin daurin aure, wato lahadi, tun safe motocin daukar amarya zuwa garin Gaya suka iso. Dina ta
shirya amarya cikin fararen liffaya na Larabawan Mouritania, ta fesheta da turarukan ‘gibenchy’ su Habiba da
Hajara suka sanyata a tsakiya, Dina na gidan gaba suka nufi garin Gaya.
Anyi musu tarba ta GIRMA, a gidan sarkin Gaya na lokacin, wanda ya kasance kaka ga Amiru, tunda kuwa shi
ya haifi Alhaji Abdurrahman, dangin Mairo sun tabbatar Mairo ta yi aure da dan dangi, wanda ake so, ake
kauna kwarai, ake kuma son abin da yake so, sannan aka san mutumcin dan Adam.
Kwanansu uku ana shagalin biki irin nasu na masarautar Gaya, kuma fulanin usli. Mai martaba Sarki
Abdulkarim Sarkin Gaya III ya yi wa amarya kyautar bajimai uku da sabuwar mota.
Washegari suka nufo Abuja inda aka shiryawa amarya gidanta cikin gidan surukanta, bangare guda, wanda
dama tun sanda za a gina gidan an gina shi ne musamman sabida Amirun.
Duk da dai gidan ba ya bukatar komi, wannan bai hana Habibu da Alh. Abbas yi wa Mairon su gata ba. Dakuna
uku manya-manya aka ba su suka shakewa Mairo da dukiya.
Sai dai fa ba wai rambatsau ba, a’ah, komi ya dace da muhallinshi. Cikin tsari mai burgewa da ban sha’awa,
sannan sun kawota da gararta (trailer) guda. Lokacin da suka shigo wajen Hajiya Aisha aka fara kai Mairo, inda
dukkan dangin ango suke tare da Hajiyar a babban falonta.
Duk kannen Amiru guda goma sha biyu na ciki da na waje sun hallara, suka karbi amaryarsu cikin mutuntawa
da kamala. Daga nan sai sassan Daddy wanda ya dade yana yi musu addu’a ta neman dacewa a duniya da
lahira.
Daga nan aka taho da amarya bangarenta banda kuka da shessheka ba abin da ta ke yi. Ta kama Dina ta rike
tamau, ta rantse ba zata tafi ta barta ba, sai dai su koma tare.
Dina na dariya ta ce
“Ina kika taba jin anyi haka Mairo? Ai auren ke nan, YAKIN MATA…… Ko ba ki ganin nima namu gidan na baro
na ke zaune da Yayan ki, a inda ba ni da kowa? Ke kuwa fa? Ga ki ga su Hajiya, ga su Amina, ko su kadai sun
isheki debe kewa. Duk lokacin da kike son zuwa Kano za ki je”.
Cikin kuka ta ce
“Yanzu Aunty Dina ni da ku shi ke nan? Ni da su Little Mairo shi ke nan? Sannan ba zan koma makaranta ba?”
Dina ta ce
“Idan na ce za ki koma makaranta, ko ba zaki koma ba na yi karya, sabida a halin yanzu ba mu da iko da ke, sai
abin da mijinki ya hukunta a gare ki. Yara kuwa na yi miki alkawarin da zarar sun samu hutu zan kawo miki su.
Ki kwantar da hankalinki ki zauna da mijinki Amiru is a nice person”.
Sabah ta yi murmushi, ta ce
“Sai ma kin zauna da shi for a little while…”
Dina ta ce
“To kinji ba, kannenshi ma sun shaida”.
Wayarta ta hau ruri ta yi murmushi
“Ni ma nawa tsohon angon kirana yake yi in mishi tausar gajiyar da kujuba-kujubar aurenki ya sanya shi. Don
haka amarya sai ince, asubah ta gari”.
Tana ji tana gani Dina ta fice, ji ta ke kamar ta dora hannuwa aka ta ce “Wayyo Allah”. Ko ta sami sa’idah.
Ya rage daga ita sai su Amina, don su Hafsat kannen Dina duk sun tafi tun dazun. Nabilah dama ba ta taho
Abuja ba, daga Gaya suka nufi gida ita da Isma’il.
Suna so ta yarda su yi hira, amma amaryar tasu ta ki sakin jikinta. Ganin abin ta ke kamar a mafarki, wai yau
ita ce a gidan wani mijin ba Uncle Junaidu ba.
Ta yi saurin yin istigfari da wannan mummunan tunanin ta amince, ta yarda da kaddararta. Ta amince haka
Allah Ya rubuta musu dukkaninsu. Zata koyawa zuciyarta juriya da karbar rayuwa a duk yadda ta zo mata.
Hajiya ta yi kiran wayar Amina, ta ce duk abin da suke yi su bari su taho gida haka dare ya yi. Dukkansu suka
mike suna yi mata sai da safe Hajiya na kiransu. Ta rike mayafin Sabah tana kuka sosai har ta karyawa Sabah
zuciya, ta ce su tafi zata taho.
Ta koma ta zauna ta ce “Haba Antinmu? Ya ya kike abu kamar karamar yarinya ne? Amare yanzu ba sa kuka,
sakin jiki suke a sha soyayya. Kuma ni kinga idan ban tafi ba zan yi laifi wurin Hajiyarmu, don haka ki yi hakuri
na tafi na yi miki alkawarin gobe da safe zan dawo idan Allah Ya kaimu”.
Haka ta kalallameta da dadin baki ta samu ta gudu. Ya rage sai Mairo kadai cikin katafaren gidanta, daga ita
sai halinta. Ji ta ke kamar an kawo ta kabarinta. Don haka ta ce bari kawai ta yi ibada ko ta samu sanyin
zuciyarta.
Ta mike a hankali, ba tare da ta ajiye nadin laffayar da ke jikinta ba. Ta nufi kofar da jikinta ya ba ta bandaki
ne, ba don ta saba da ire-iren wadannan wuraren ba, da hakika ta tsaya kauyanci. Komi na bandakin wanda
ya kasance (Jacuzzi) kalar ruwan hoda ne, watau ‘pink’ kamar yadda makeken bed room din shi ma ruwan
hodar ne da ratsin fari.
Ta dauro cikakkiyar alwala ta fito. Ba tare da ta tsaya neman darduma ba ta nemi wani gefe a can wani korido
na dakin ta tada ikama. Sallolin neman biyan bukatar duniya da na lahira da neman dacewa a rayuwar
aurenta ne ta ke yi. Cikin sujudunta tana mai yi wa Babanta da Innarta addu’ar samun rahma da gafarar
Ubangiji.
Cikin tahiyarta ta ji alamun ana taba kofa, kafin cikin nutsuwa ta ji an murda kofar an shigo. Angon ya
bayyana a dakin cikin fararen kayan barci.
Dai-dai lokacin da ta yi sallah ta mike ta kara tada sallah, ya aje kwali da tambulan din da ke hannunshi, shi
ma ya shiga ya dauro alwalar ya cimmata suka ci gaba da sallar tare. Agogon bango ya buga karfe biyu dai-dai
na sulusin dare lokacin da kowane mai rai yake neman hutu, amma ga wadannan ma’auratan abin ba haka
yake ba.
Sun fada wata duniyar tunani ta daban, ba wannan tamun wadda muke ciki ba. Abin nufi, kowanne da
tunanin da ke cin ranshi. Ba auren sha’awa ya yi ba, auren so da kauna ya yi. Don haka babu sha’awar Mairo
ko yaya a tare da shi a daren yau.
Ya dauko kwalin ‘fresh milk’ na madarar ‘oldenburger’ da ya shigo da shi ya tsiyaya a kofin ya mika mata. Ba
tare da ta tashi daga inda ta yi sallar ba, ta mika hannu ta amsa. Ya sauko daga gefen gadon ya yi zaman
rakuma a gabanta. Ya dauki dukkan hannuwanta ya rike cikin nashi. Wannan ya haifar da tashin tsigogin
jikinta duka a lokaci daya.
Ta samu kanta cikin matsananciyar sha’awar mijinta Amiru, wanda sassanyan kamshinsa na turaren ‘Miyaki’
ke kara dagula mata al’amura, dama yaya lafiyar kura, balle an tsokaneta, amma ga shi Amirun, abin ba haka
yake ba.
Zuciyarshi ta kasa amincewa Mairo na sonshi, a ganinshi Habibu ne ya takurata ta aure shi, don haka akan me
zai sallama mata soyayyarshi? Yana son ya koyar da ita sonshi da kaunarshi, ba wai sha’awarshi ba kamar
yadda ya karanto karara cikin fararen kwayar idanunta.
Haka suka yi ta zama dungur-gur bisa kafet har aka yi kiran assalatu, kowanne na ji da miskilanci. An rasa
wanda zai fara keta billensa, ya kwantar da kai ga dan uwansa. Ya rausayar da kai, ya ce
“Mu je mu sake alwala”.
Ba musu ta mike domin dama ta tsauwala da wannan zaman na babu gaira babu dalili.
Don haka koda suka idar da sallar Mairo gefen gado ta koma ta takure. Shi kuma ya ja filo ya jefa bisa kilishi
ya kwanta. Ta leka ta hango idonshi a rufe ta dauka barci ne ya dauke shi, don haka ta mike ta warware
laffayarta, yadda zata ji dadin yin barci, ta nade a gado ta ja bargo ta rufa. Wani irin fitinannen barci na
fizgarta, hakan yasa ba da dadewa ba sarkin barayin ya yi awon gaba da ita.
Mairo ba ita ta farka ba sai wajejen karfe goma na safe. Shi ma din sakamakon feshin ruwan da ta ji akan
fuskarta ne. Ta juya a hankali saitin da feshin ruwan ya ke, Amiru ne ke taje sumarshi. Ya yi shiri cikin bakaken
‘suit’ masu ban sha’awa.
Ta zuba mishi ido kurr kamar mayya, har yawun bakinta na tsinkewa, sakamakon wata matsananciyar
sha’awarshi da ta kara saukar mata. Wannan mutum kamar Romeo ya ke, kamar an ce da shi ‘juya’ ya juyo
suka yi ido hudu da ita, ya daure fuska sosai, ya ce
“Lafiya kike kallona? Ko na yi kama da tsohon saurayinki ne mai sunan aljanu? Haka kawai yarinya kin zama
kurma, in dai ni ne to mu zuba, shege ka fasa”.
Ya kuta, ya sake cewa
“Halan Dina ko gayar da mutane ba ta koya miki ba?”
Ta dauke kai ba ta ba shi amsa ba, sannan ta yunkura ta mike ta fada bandaki ta yi wanka tare da wanke baki
ta fito. Yana tsaye jikin sif dinta yana amsa waya, ga dukkan alamu da Harrit yake wayar, wani kululun bakin
ciki ya taso ya tokare ta. Ta yi saurin komawa bandakin don ta dauka ya fita ta aje tawul din ta maida kayan
jikinta. Ta sake fitowa wannan karon ya gama wayar yana sanyata a aljihun wandonshi.
Ya bi-ta da wani irin kallo kasa-kasa ya girgiza kai, ya fita yana cewa
“Abinci za mu ci, ko yau ma ba za a ci da ni ba?”
Ko ta tafas ba ta ce masa ba, don ta lura neman baki yake yi da ita.
Ta shirya cikin shadda ‘orange’ babbar riga ‘senegalese’, ba ta yin kwalliya rankacau don haka kullum fatarta
ta ke danya shar (fresh). Ba kankanuwar yunwa ta ke ji ba, don haka ta nufo falon ta cimmashi a ‘dinning area’
na falon. Kallo daya ya yi mata ya dauke kanshi, zuciyarshi na bugawa. Wannan yarinya kamar Juliet ta ke.
Ta ja kujera mai fuskantarshi ta zauna, sannan ta fara bude ma’adanan abincin, sinasir ne da waina, sai
hadaddiyar miyar agushi wadda ta ji naman rago, a gefe farfesun hanta da Koda ne sai Shawarmah da snacks
dangin su meat-pie, samosa, spring rolls da sauransu.
Cikin sassanyar murya ta ce “Can I serve you?”
Hakika ya ji wannan muryar har cikin kokon ransa. Bai iya ya amsa ba, illa kai da ya gyada mata, don haka ta
fara da hada mishi ruwan ‘lipton’ mai zafi da ganyen ‘Hemorrhoid tea’, sannan ta zuba mishi Sinasir din da
farfesun a faranti daban-daban.
Ya yi mata wani sassanyan kallo ba tare da ta sani ba, sannan ya soma ci. Ta hada ‘lipton’ ta sha, amma ta yitayi ta ci abinci a gabansa ta kasa. Ta mike ta ce
“Zan shiga wajen Hajiya”.
Ya ce
“A’a, sai kin ci abinci na gani tukunna”.
Ta koma ta zauna, ta dauki sinasir guda daya, ta sanya a faranti ta soma ci cike da kunya. Ya tura mata
farfesun gabanshi ya ce, “Cinye shi”.
Ba musu ta karba don ba zata iya yin jayayya da shi ba. Sai da ya tabbatar ta cinye, sannan shi ma ya mike
yana cewa
“Mu je na rakaki wurin Hajiyar”.
Tare suka jera har gidan Hajiya. Tana sallar walha sanda suka shiga a karamin falonta. Sai da ta idar ta shafa
addu’o’inta sannan ta juyo gare su, cikin matsananciyar kauna ta mikawa Mairo hannu
“Zo dawo nan kusa da ni diyata”.
Sai ga su Sabah su ma sun fito, suka gaida Yayansu wanda ya maida hankali ga amsa kiran da ke shigowa cikin
wayarshi.
Daga karshe ma fita ya yi ya barsu, bayan ya fadawa Hajiya zai je ya raka bakinshi airport. Su Amina kamar su
hadiye Mairo. Nan ta wuni sur tare da su.
Bai dawo ba sai bayan la’asar, lokacin da ya shigo tana kicin ita da su Sabah suna hada abincin dare. Hajiya na
falo ta ce
“Sai yanzu?”
Ya ce
“Wallahi kuwa, ai bakin nawa ne suna da yawa, kuma jirage daban-daban za su shiga, amma dai
alhamdulillah duk sun tafi sai fatan Allah Ya sauke su lafiya”.
Hajiya ta kwalawa Mairo kira, ta fito ba tare da ta iya hada ido da Amirun ba. Wanda ya bita da kallo kamar
bai santa ba. Ta russuna gaban Hajiya cike da girmamawa, Hajiya ta ce, “Shi miji idan ya dawo yana bukatar
kulawar matar sa, ta hanyar yi mishi sannu da zuwa, da ba shi abu mai dan sanyi ya sha kafin a gabatar mishi
da abinci. Don haka bi shi ku tafi, su Amina za su shigo muku da abincin idan an karasa”.
Cikin jin nauyi ta ce
“to Hajiya”.
Shi abin ma dariya ya ba shi, wai wannan katuwar ake koyawa kula da miji, Hajiya ba ta san yaran zamani da
wayonsu ake haifarsu ba, balle Mairo rainon Dina, kula da miji sai dai ta koyawa wasu, sai dai in ba ta sa kanta
ba.
A ‘bedroom’ dinta ya cimmata, tana kokarin sauya kayan jikinta. Duk dauriyarshi da jarumtakarshi ya kasa
sarrafa kanshi, don haka ya yi hanzarin komawa da baya ya ja mata kofar. Ta yi saurin juyowa amma ba ta ga
kowa ba, sai karar rufe kofa.
Ta ci gaba da abin da ta ke yi kamin ta jiyo sallamar Amina da Rayyah a falo. Ta fita suka aje abincin a ‘dinning.
Suka yi ‘yar hira ba su jima ba suka fita. Ba ta san dakin da ya shiga ba, ko ta sani ma ba zata shiga ba, don
haka ta zauna nan falon tana jiran shi sai zuba kamshi ta ke.
Zamanta da wajen mintuna ashirin sannan ya fito, da alama wanka ya fito. Wannan karon cikin shigar
kananan kaya, farar shirt din (Tommy Hilfiger) da bakin wando Tokyo. Sai ‘miyaki’ ke tashi. Mairo ta daga kai a
hankali tana kallonshi. Wani irin abu na tsirgawa cikin jikinta yana tada tsigogin jikinta. Kallo daya ya yi mata
ya karanto halin da zuciyarta da ma gangar jikinta ke ciki.
Ya murmusa ya daga gira ta kara rikicewa, a ranshi ya ce “munafuka! Idan dai wannan Amirun ne yarinya, to
kwalelenki har sai kin so shi, kin kaunace shi don Allah, tunda kiri-kiri kin fada mishi cewa ba kya sonshi, akwai
wanda kike so, don haka wannan jikin ma da kike wa marmari ba zaki same shi ba”.
Abincin da Mairo ba ta iya ta ci ba ke nan, sabida gani ta ke kamar Amirun yana karanto zuciyarta. To da
gaske hakan ne, tunda yake shi din ba yaro ba ne. Ya fita ilmi da hankali nesa ba kusa ba. A kwayar idanunta
ya gama gane ta tsaf.
Yana kallonta sai caccaka cokali ta ke cikin abinci ta kasa kai ko loma guda. Shi kuwa cin abincinshi yake cikin
nutsuwa da kwanciyar hankali yana kallonta a kaikaice. Wani zubin ya yi murmushi, wani zubin ya girgiza kai.
Wannan karon bai takurata da lallai sai ta ci ba, don ya tabbata ba zata ci din ba. Dan Abdurrahman Gaya,
kadai ta ke so a jikinta.
Kararrawar kofar shigowarsu ta yi kara, wannan ne ya ceci Mairo daga kaifafan idon Amiru. Da azamarta ta
mike ta nufi kofar ta bude. Ta sha mamakin ganin Daddy da kansa. Cike da girmamawa ta ba shi hanya ya
wuce.
Sai da ya zauna a ‘seater’ ta zube a kasa tana gayas da shi. Ya ce
“Yaya bakunta Maryamu?”
Ta ce
“Alhamdu lillah”.
“Babu wata matsala ince ko?”
Ta ce
“Babu Daddy”.
Amiru ya baro kujerarshi ya iso inda Daddyn ya ke ya zauna a gefensa suka soma hirarsu. Ta mike ta je kicin ta
kawo mishi ruwan (Eva) mai sanyi da lemun ‘shany’ sannan ta gabatar mishi da abinci.
A nan ne ya yi murmushi, ya ce
“Lemun kadai zan sha Maryamu, na Hajiyarku yana can yana jirana, kada inci a wajenki inje in kasa cin nata”.
Ta yi murmushi ta ce
“To Daddy babu komai”.
Ta koma daki ta barsu don su gana.
Yau ma irin kwanciyar jiya suka maimaita, wato shi yana bisa kilishi ita tan kan gado. To haka kwanakin da
suka biyo baya. Idan ka gansu a gaban Hajiya da Daddy. ko su Amina, ba zaka taba zaton cewa zaman ‘yan
Marina suke ba. Kowanne na ji da miskilancinsa ya kasa kwantar da kai ga dan uwanshi. Ga ita Mairo, a
ganinta shi ne namiji, shi ya kamata ya nuna mata kulawa irin ta kowadanne ma’aurata amma ba ita ba.
Sannan ba haka Dina ta gaya mata ana yiwa amare a renakun su na farko a gidan aure ba. Ba haka kuma ta ga
Yaya Habibu yana yiwa Dinan ba. Amiru yace yana son ta baka da zuci, amma bayan aurensu ta ga ba haka ba.
Wannan al’amari yana sanya ta cikin wani irin tunani mai zurfi da wuyar fassarawa. Har ta kasa jin dadin
rayuwar gabadaya.
Shi kuma Amirun, a nashi bangaren, ya riga ya saba samun tarairaya ta karshe daga banasariyar matarshi,
kamar ta goya shi. Bai san cewa matar Bahaushe da matar bature akwai wasu manya-manyan banbancebanbance ba. Hakika mu Allah Ya ba mu wannan darajar ta kamun kai da alkunya, wanda ya zamo kowanne
irin namiji, duk kyau, aji, mukaminsa da iliminsa dole ya lallame mu idan har yana son ganin yadda ya ke so.
Yau juma’a ta tashi da kewar Dina kwarai a ranta, ba abin da ta ke so irin ta ji muryarta. Ya dawo daga sallar
juma’a shi da Daddy daga babban masallacin Abuja kamar yadda suka saba kowanne sati idan suna nan. Ta
rasa yadda zata yi ta roke shi ya ba ta aron waya. Dabara ta fado mata don haka ta nemo biro da ‘yar takarda
ta rubuta mishi, ta soke a jikin kofar dakin da ta tabbata shi ne nasa.
Ya zo shiga dakin don sauya manyan kayan da ke jikinsa ya cimma sakonta. Ya yi murmushi ya sumbaci
takardar ya share ta bai ce mata komai ba.
Sai da daddare sun yi shirin kwanciya, bayan ya jefa filonshi ya mike. Ta zuba tagumi a gefen gado abin duniya
ya dame ta, idan jurinta miskilanci ta gamu da wanda ya fi ta miskilanci. Ta juyo kadan, ga dukkan alamu barci
mai nauyi ya tafi da shi. Cikin sanda kamar barauniya ta iso gabanshi don ta dauki daya daga cikin wayoyinshi
sai caraf! Ya damke hannunta tareda wayar ya kuma bude lumsassun idanunshi sannu a hankali a kanta.
Kunya ta duniya Mairo ta gama jinta. Ashe ba a yi komai ba sai sanda ya fizgota ta fada gaba daya a jikinshi.
Ta rasa inda za ta sa kanta don kunya, fargaba da wani bakon tsoro da ya ziyarce ta duk a lokaci guda.
Jikinta ya soma rawa kamar mazari, amma hakan bai sa ya cikata daga sassaukan rikon da ya yi mata ba. Duk
yadda ya so da su hada ido cikin dan sauran hasken fitilar baccin dake dakin amma Mairo ta ki. Runtse idon ta
shiga yi da karfi. Wani sabon Son mijinta AMIRU da kaunarsa ne farat daya suke tsirgawa a zuciyarta.
Wadanda bazata iya tantance tun tsahon wane lokaci hakan ya soma ginuwa a zuciyarta ba. Yana danne
wancan feeling din mai karfi da dukkan tasirin sa, wanda zuciyarta ta dade tana kallon Amiru dasu. Tareda
gina mafarkanta da shi a kansa.
Ya dago fuskarta daga kirjinsa, a wannan lokacin ya yi nasarar hango cikin kwayar idanunta, cikin murya irin ta
wanda ya tashi daga bacci ya ce
“Sata ko Mairo?”
Ta ce
“A’a, ina so in kira Anti Dina ne, kuma na fada maka ai ba ka ba ni ba”.
Ya ce
“Ni ban kai kararki wajen Anti Dinan ba, sai ke za ki kai karata?”
Kamshin ‘mouth fresh’ dinshi na fizgarta, yana sanya mata rashin kuzari ta ce,
“Me ka yi min da zan kai kararka, kuma nima me na yi maka da zaka kai karata?”
Ya ce,
“Kin yi min laifuffuka da yawa Mairo, wadanda idan na fadawa Anti Dina sai ta zane ki wallahi”.
“Dame-dame ne laifuffukan nawa?”
“Ai ba ki ma sansu ba?”
“Da na sani bazan tambaye ka ba”.
“To sunkuyo nan na fada miki”.
“Kinga na farko ba kya gaishe ni da safe, sannan ba kya zuwa dakina taya ni kwana, sai dai ni na biyo ki
dakinki. Sannan idan na biyo ki ba kya hada makwanci da ni, sai ki bar ni a kasa ki dare gadonki. Haka Dinan ta
fada miki tana yi wa Habibu? Ko ba ki ga har kaya ita ta ke saka mishi ba? Amma ke bana jin ko inda nake
wanka kin sani a gidan nan ko don har yanzu ba kya sona?”
Taji zafi a ranta da kalamansa. Da zai taimake ta da ya daina zancen rashin so a tsakaninsu. Ta ce
“Maganar ina sonka ko bana sonka, tunda mun riga mun kasance cikin inuwar AURE, to bata taso ba, bare
kuma ni wallahi ban taba jin kiyayyarka a raina ba. Ko wancan lokacin da na fada, na fada ne kawai don ban
amince da irin son da zuciyata ta ke yi maka ba”.
Ya lumshe ido a hankali, tare da sake yi mata muhalli cikin ni’imtaccen kirjinshi mai cike da gargasa.
Yace “wane iri ne shi wancan son?” Ta dan rufe ido kafin tace “irin na shirme!”.
“Wane irin so ne irin na shirme?”
Amiru ya tambaya cikin mamaki.
Mutsu-mutsun kwacewa ta hau yi, ko zai kashe ta bazata iya yi masa wannan bayanin ba.
Sako riko ta yayi da karfin da yafi na dazu, ya juyo ta sannan ya sa hannu ya dago habarta. Yana iya ganin
kyallin dake cikin idanunta wadanda ke cike taf! Da soyayyar data mamaye su. Soyayya mai cike da kauna
mara algus or material attachement. Zaiyi rantsuwa bai taba ganin wannan yanayin cikin kwayar idanunta ba,
wani yanayi da yake matukar jira, yake kuma da yakinin zai iya cigaba da jiran zuwansa cikin idanun Mairo har
nan gaba da shekaru goma kafin ya yarda ya hada shimfida da ita.
“To yanzu fa? Mairo! Mairo yanzun kina sona?”
Amiru ya tambaya, da wata murya tamkar ba tashi ba.
Sai ta yi murmushi, irin wanda bai taba gani bisa siraran labbanta ba.
Wannan kadai ya tabbatar mishi da cewa, ya gama mallakar soyayyar Mairon, saura da me? A take shi ma ya
soma mallaka mata ta shi. Cikin wani irin salo mai ban mamaki da Mairo ba ta taba tunanin akwai irin wannan
soyayyar a duniya ba. Koda a duniyar karance-karancen novels dinta kuwa.
Su Hajiya Mairo, tun ana dauriya, ana cijewa, cikin bin shawarwarin uwardakin ta Dina, har lissafin ya soma
kwace mata……aka kai ga gejin kiran Anti Dinah, Baffa, da Yaya Habibu su zo su kawo taimako. Yau har Ladidi
da Nabilah sun sha kira don tana ganin karshen rayuwarta yazo! Shi kanshi Amirun ya rasa control din kansa,
ta yadda har zai yi tunanin cewa Mairon virgin ce, ba kamar matarshi ba. Tunda yake a rayuwarsa bai san
akwai Hurul-eeni tun a duniya ba. Bai san aure iri-iri ne kuma suna ya tara ba. Don haka bai farga da aikaaikar da ya yi ba, sai da ya duba ya ga Mairon ta sume mishi.
Ba ita ta dawo hayyacinta ba sai da sanyin ruwan ‘ragolis’ ya ratsa kwanyarta, da sauran sassan jikinta. Ya
rungume ta sosai, tamkar ya tsaga kirjinsa ya sanyata, cikin shauki ya ce
“Mairo kar ki gudu ki barni! Mairo ki ci gaba da zama da ni ko ba kya sona, ni ina sonki da dukkan ruhi na! Ki
rike naki son ko bazaki bani ba! Zan zamo ‘impotent’ a duk ranar da kika guje ni, ko kika juya min baya…!”
***
MAIRO A GIDAN AURENTA!
Zuwa yanzu, wato watanni biyu a gaba, Mairo an zama manyan mata, an iya komai na kula da miji. Ta iya
daukewa mijinta lalurar da mata hudu ba zasu iya dauke masa ba. Soyayya, kauna da shakuwa ke kara kamari
tsakaninta da mijinta. Ga kauna da kulawa da ta ke samu daga surukanta kamar su suka tsugunna suka haife
ta.
Cikin wannan dan tsukin Amirun ba ya samun zama sosai, sabida shirye-shiryen bude bankinsu da suke yi shi
da Habibu. Shi Habibun ke tafiyar musu da komi ta can, shi kuma yake tafiyar da komi ta nan.
Gaba daya ya mance da wata Harrit da ya sanya lambarta a (divert call), sannan a ka’idarshi bai daukar wayar
da bai san lambar ba. Al’amuran gabanshi kadai sun ishe shi, sannan Mairon shi kadai ya sanya a gaba, a
yadda yake ji cikin ransa, ta ishe shi rayuwar duniya da lahira.
A wannan daren na ranar talata shiri yake don tashi zuwa Washington a washegari, domin mika takardar yin
retire daga aiki a World Bank, a gefe guda kuma ga Mairo ta dira shagwaba ita dai sai ya tafi da ita ta ga Yaya
Habibu da Dina.
Ya kamo hannunta ya ce
“rigimarki yawa gare ta Mairo, na fada miki Washington za ni ba Michigan ba. Kuma ba dadewa zan yi ba,
karkari na yi sati biyu. Ina duba yiwuwar komawarki makaranta, idan komi ya dai-daita gidan Habibun zan
barki ki zauna gaba daya”.
Ai da jin haka ta yi tsalle ta dane shi cikin nuna farin cikinta a fili. Inda shi kuma ya juyo ta gareshi ya bi ta da
deep-kisses tsakiyar bakinta, wuyanta, da idanunta; mai nuni da cewa, lallai zai yi kewarta.
Ita da Sabah suka yi mishi rakiya filin jirgi a asubahin washegari. A gaban Sabah ya rungume ta yana fada
mata wasu irin kalamai masu rikirkita kwakwalwa cikin kunnuwanta. Sabah sai ta sa mayafinta ta kare
fuskarta tana murmushi. A zuciyarta kuwa addu’a ta ke, Allah Ya ba ta miji irin Yayanta.
Yana sauka a Washington ya tarar tuni Raymond da Franklyn suna jiran isowarshi, don haka suka zubo
jakarshi a bayan mota suka nufo cikin gari.
Kai tsaye gidanshi suka nufa suna tafe suna yi mishi bayanin muhimman abubuwan da suka gabatar (in his
absence), ci gaban da aka samu da shortcomings din duk da ya biyo baya. Suna sanyo hancin motarsu a
farfajiyar gidan ya ga bakuwar mota kirar (Ferrari 458) kusa da ta Harrit.
Bai kawo komi a ranshi ba, don ya yi zaton baki ne Harrit din ta yi kasancewarta ma’abociyar hulda da jama’a,
don haka ya yi amfani da mukullinshi ya bude kofar. Su Raymond suna daga waje suna magana. Ya ratsa falon
babu kowa, ita ba musulma ba, balle ya yi mata sallama don haka kai tsaye ya sanya kai ‘bed-room’ dinsu.
Idanunshi kuwa suka yi kyakkyawan gani.
Harrit ce kwance tare da wani bature dan uwanta haihuwar uwarsu-ubansu cikin halin turmi da tabarya.
Ya tsaya kawai yana kallon tashin hankalin da bai taba gani a rayuwarshi ba, wanda a take ya tabbatar ba
komi ba ne, hakkin iyaye ne da son zuciya suka jawo mishi (al’ummar musulmi irin Amiru sai a yi hattara,
kafiri har gobe kafiri ne, duk soyayyarsa gareka kuwa, kuma babu soyayya ta hakika tsakaninshi da musulmi
sai yaudara da soyayyar manufa).
Jikinsu ne watakila ya ba su ana kallonsu, su duka suka juyo a razane, amma abinka da nasara da babu digon
kunya ko tsoron Allah a tare da shi, sai suma suka zuba mishi idanun.
Ya yi saurin dauke idonsa ya fito falon ya barsu a nan. Ya zauna cikin kujera yana fidda wani irin wahalallen
numfashi yana fesarwa da kyar, yana shaka da kyar.
Idan wani ya fada mishi Harrit zata yi mishi haka ba zai taba yarda ba, ya godewa Allah da bai taba kusantar
Harrit ba tare da ya yi amfani da kwaroron-roba ba. A take ya fiddo takarda ya dora biro ya rubuta mata sakin
aure kamar yadda addininshi ya tanada.
Ya leka waje ya kira Raymond da Franklyn ya ce, ya ba su minti goma su fitar da duk wani abu da ke cikin
gidan su loda mata shi a waje.
Ya leka dakin ya cilla mata takardar sannan ya kara fadi mata da bakinsa cewa ya sake ta saki uku. Ko babu
sakin dama auren ya riga ya gurbata a nashi addinin. Ya kuma sanar da su minti goma suka kara yi mishi cikin
gida ‘yan sanda ne za su raba shi da su.
Harrit sai kuka ta ke tana ba shi hakuri, ta kama kafafunshi ta rike tamau! Jan gashinta (blonde) ya baje a
bayanta da fuskarta kamar na mahaukaciya. Tuni kwarton nata ya gudu, ta gaban Amiru ya rarrafa ya wuce
da rigarsa a hannu, da ya ga ya iso kofa lafiya sai ya taka da gudu iya karfinsa ko motarshi bai dauka ba. Su
Raymond ne ke cika umarnin ubangidansu. Masu fushi da fushin wani. Fatali kawai suke da komai dake cikin
gidan. Ya fizge kafarshi cike da kyama yana ja da baya tamkar ta dana masa garwashin wuta, a baya in Habibu
ya ce kyamar Harrit yake mugun haushinsa yake ji, amma a yau ji yake har zuciyarshi na tashi da kallonta, ya
fice babu waiwaye yana mai kara jaddada mata cewa, kada ta sake ya dawo ya ganta ko wani tsinkenta a cikin
gidanshi.
Bai kara bi ta kan Harrit ba, don ya lura idan ya ce bakin cikinta zai sa a ranshi shi ne zai cutu a banza. Amma
alal hakika Harrit ta sanya kasar America ta fice mishi a rai. Dan burbushin kewar kasar da ya rage a baya ya
kara zagwanyewa
Ya samu kanshi da rashin yarda da kowa, hadi da shi kansa kuwa. Mairo ce kadai yake tunawa ya ji sanyi a
zuciyarshi. Itan kam ya yarda da ita da wata irin yarda da bai taba yiwa kowa ba bayan Habibu in ka cire
iyayensa, bayan budurcinta data kawo masa cikin girma da daraja, yana da wata irin yarda akanta, yana
samun wata irin nutsuwa a duk lokacin da yake tareda ita. Amma ita kanta Mairon a yau sai yaji bazai iya
magana da ita ba. Don haka ya kashe dukkan wayoyinshi.
Cikin sati daya rak! Duk abin da ya kai shi ya gama shi, hankalinshi ya yo gida kwarai, amma dole ya biya
wajen Habibu maganar karatun Mairo.
Don haka daga Washington kai tsaye Michigan gidan Habibu ya nufo a Detroit. Habibun ya je da kanshi filin
jirgi ya taho da shi.
Hakika idan ka dube shi zaka lura cewa, a razane yake, a firgice da al’amarin mata. Ita ma Mairon sai yake
ganin kamar kafin ya koma zata yi mishi haka! Don haka ya kulle kanshi a hotel din (RAMADA INN) tare da
kulle wayoyinshi don ya samu daidaituwar kwakwalwarshi da tunaninshi. Ba abin da ke tashinshi daga
shimfidarshi sai sallah da cin abinci, shi kansa Habibu bai san inda ya shiga ba.
Tsayin sati guda sannan ya samu ya yi ‘regaining consciousness’. Sannan ya nufo gidan Habibu. Habibun ya
ganshi kamar daga sama, koda wasa bai yi gigin fada mishi abin da ya faru ba, don yasan dariya zai yi mishi,
dariya har da ta keta, tunda babu yadda bai yi ba ya nuna mishi illar da ke tattare da auren mushrikiya, amma
Amirun bai gane hakan ba, sabida giyar soyayya na dibanshi a wancan lokacin, don haka idan yana da kunya
ai ba zai neme shi ba. Da ya tambaye shi Harrit sai ya ce da shi, sun rabu ta koma Philppines, bayan idan za a
kashe shi bai san inda ta nufa ba.
Dina na kicin tana hada musu abincin dare, a yayin da su kuma suke baje a falon suna aikin takardunsu cikin
systems.
Kallo daya Habibu ya yi mishi ya tabbatar yana cikin wani bacin rai mai zurfi, ya yi tambayar duniyar nan
amma zurfin ciki irin na Amiru ya hana shi fadar abin da ke damunsa.
Shi kuma Habibun ya takura sai ya ji, daga karshe ya yanke shawarar fada mishi ko da kuwa zai yi mishi
dariyar ne, akalla ya samu rangwamen radadin da zuciyarshi ke yi da nauyin da ya danne ta.
Habibu ya yi shiru, can kuma ya ce
“Ban yi mamaki ba. Shi arne wannan (adultery) a wajenshi ai ba wani abu ba ne extraordinary. Sai a yi
hattara, Allah Ya kara tserar da mu daga kutungwila da kaidin ZUCIYA.
Amma ni a ganina wannan ba wani abu ba ne da zaka sanya shi a ranka har ya haifar maka da hawan jini,
tunda ka san abin da ka aura ai ka aura din. Sannan sabawa mahaifa ai ba abin da ba zai janyo mana ba mu
‘yan Adam, don haka sai mu yi fatan Allah Ya kiyaye gaba, Ya sa mu gama da duniya lafiya”.
Ya ce.
“Ina son farantawa Mairo Habibu, kamar yadda ta ke haifar min da nau’o’in farin ciki a kullum. Don haka nake
ganin zata dawo nan ta karasa karatunta kamar yadda ta faro shi cikin nasara.
Ba zan bari ya kasance ni din na yi silar rabata da burin rayuwarta ba, da tubalin da ka jima kafin ka assasa.
Don ko a yanzu na fita na dawo kullum sai na ganta tana bitar littafanta, duk da cewa bata taba yi min korafi
akan hakan ba. Ni da na yi mata na ga farin cikinta fiye da kullum, tayi min abinda bata taba yi ba, idan na
samu sarari zan dinga lekowa akai-akai insha Allahu”.
Habibu ya ji dadin wannan karamci da Amiru ya yi mishi, don shi ma abin yana damunshi, don bai san tsarin
sa bane shi yasa tun farko bai neme shi da zancen ba. Don haka a washegari suka nufi Michigan State
University tare don gyara mata registration dinta.
Ya rage saura kwana uku Amiru ya dawo, Hajiya ta yi kiran Mairo, ta hadata da wasu jarkokin magani da zuma
roba guda da Mairo ba ta san ko na mene ne ba. Ta ce, ta je ta yi ta kwankwada, ta kawo mata jarkokin kafin
kwana uku.
Ta bi umarnin Hajiyar don tasan ba zata ba ta abin da zai cuce ta ba, bare wannan magani mai shegen dadi da
zaki.
A’ah! Ai tun a washegari ta ji yanayin jikinta na sauyawa, ba abin da ta ke bukata sai dawowar Ameeeru, da
yake saukar karfe shidda na yamma za su yi, don haka tun safe tana kicin dinta tana hada abincin tarbar
angon nata.
Da taimakon daya daga cikin masu aikin Hajiya da Hajiyar ta bata don su Sabah duk sun koma makaranta,
komai ya hadu.
Babu yadda Hajiya ba ta yi ba ta je airport ta tarbo shi ba, amma kunya ta hanata. Wannan na daga cikin
halayen yarinyar da suke kara mata kaunarta.
Ta lura bayan kunya, tasan mutumcin kanta, kuma ta iya zama da kowa da wata mu’amala ko ya ya ta hadata
da shi.
Tana sassan Hajiya suna sauraron labaran MBC a lokacin da ya iso, daga bakin kofa ya tsaya, ya tokare kofar
da hannunshi na dama yayin da na hagun ke dauke da falmarar din ‘Italian suit’ ruwan toka, wato ‘grey’ da ke
jikinshi.
Ya rausayar da kai yana kallonta, da kyawawan idanunshi, ba tare da ita din ta sani ba. Sassanyan kamshin
‘miyaki’ da ya bakunci hancinta shi ya ankarar da ita tsayuwarshi a bakin kofar n wasu mintuna.
Ji ta yi kamar an yi mata gafara sabida farin cikin dawowarsa cikin koshin lafiya. Ta lumshe ido ba tare da
tasan lokacin da ta yi hakan ba. Hajiya tana ta magana, amma ba ta ji Mairo ta bata amsa, sun yi nisa a kallon
junansu kamar yau suka fara ganin juna.
Ta juyo don ta dubi Mairo, a sannan ne ta ankara da inda Mairon ta kafa wa ido. Ta ce “Au, ashe mijinki kika
gani kika manta da ni nake ta sambatu ni kadai?”.
Ya yi dariya ya idasa shigowa dakin. Ita kuwa don kunya sai ta zame ta gudu gidanta ba ta kara lekowa sassan
Hajiya ba.
Tana shafa a gaban mudubi, ga dukkan alamu daga wanka ta fito. Daure da tawul iya cinyoyinta. Ya bude
kofar ya shigo cikin bakaken pyjamas, tana hango shi ta cikin mudubin a lokacin da ya iso gare ta. Ya dora kai
a hankali kan kafadunta ta baya, kyawawan fuskokinsu suka bayyana cikin mudubin a jere, a hankali ya
sanyata cikin jikinshi ya lullube da hannayenshi, yana shakan sassanyan ‘bathrobb’ dinta na ‘rasasi’ yana
lumshe ido. Ya ce
“Tell me how much you misses me, ko ba ki yi kewata ba ne Mairo? Don na ga ke har wata kiba kika kara
abunki, ni kuwa ina can tunaninki ya hana ni sukuni”.
Murmushi kawai ta yi har ‘beauty point’ din mai kara mata kyau ya lotsa ciki sosai. Ya sumbuci wajen with a
very warm kiss, kana a hankali ya soma warware mata tawul din suka soma aikin lada.
***
Wata guda da dawowarshi, suka yi shiri suka nufo Kano don yi wa Baffa sallama, kasancewar a cikin satin ne
zata koma Michigan. Su Habiba an shiga makarantar ta nutsu don yanzu Mairon da suke wulakantawa ta
zame musu uwargijiya da bazarsu suke rawa.
(To ina ruwan Allah!)
Tuni aka sa Lawan ya gyare musu dakin baki, ya kunna ‘burner’. Abinci kam sai wanda suka zaba. Baffa ya ji
dadin ganin yanayin da Mairon shi ke ciki, ta cika ta yi bul, ta zama babbar mace, kamar kajin Agric jawur da
ita.
Ya tarasu duka ita da Amirun ya yi musu kyawawan nasihohi akan rayuwa, da kuma yadda za a yi a ci ribarta.
Ya kare da yi masu nasiha akan muhimmancin riko da sallah akan lokacinta.
“Ita ce idan ta yi kyau dukkan ayyuka za su kyautata”. Amiru na son Baffan Mairo, sabida sauran mazan jiya
ne ba na yau ba, irin wadanda kyale-kyalen duniya ba sa gabansu. Ya cika su da alheri duk gidan, a washegari
suka nufo Michigan.
Dina ce ta zo ta tarbe su, domin Habibu ya yi balaguro zuwa New-Jersey. Mairo ta rungume ‘ya’yanta kamar
ta tsaga kirjinta ta sanya su. Suna fada mata,
“Mun yi missing dinki Anti Mairo, da gaske ne da Daddy ya ce anyi miki aure da Uncle Amiru???” Inji Bedi.
Murmushi ta yi, cikin matsanancin nishadi tana shafa kan yaron, amma ba ta amsa musu tambayar ba.
Amirun ne ya ji, ya juyo daga maganar da suke yi da Dina ya bashi amsa cikin daga gira.
“yes Muhammad da gaske ne, Daddy is absolutely right! Har ma ta kusa ta kawo wa little Mairo kanwa, nan
da wasu watanni kadan”. Da sauri Mairo ta bace a wurin.
A ranar Amiru ya juya Washigton don karasa wasu hidimominsa tare da jaddawa Dina amanar rayuwarsa,
wato Mairon da ta dusar da hasken sauran matan duniya baki daya daga idanunshi.
Sun kulle a daki ita da Dina ana labarin bayan rabo. Dina ta kura mata ido ta ce
“Anya Mairo? Jikin nan naki babu bayani? Irin wannan fari da kyau haka sai ka ce mai shafe-shafe? Ko dai
kwanan nan za fara goyo ne? Naji Amiru na fadawa yara dazu na dauka wasa yake”
Mairo ta rufe fuska da tafukan hannunta, ta ce “Kai Anti Dina, wallahi ba ni da komi. Karewa ma yanzu haka
period nakeyi. Ni fa tunda na je gidan dakina daban nashi daban. Kuma ba sai ana kwana daki daya ne ake yin
cikin ba?”. Dina ta kyalkyale da dariya ta ce.
“Amirun? To abar kazar cikin gashinta tunda ba kya son a fige ta kada in zama babbar banza”.
Ta jawo lokarta ta soma fiddo mata magungunan mata masu kyau da tsada ‘yan Indonesia data ke saya tana
yi mata bayanin tsarin shan su.
Mairo ta ce
“Maganin mene ne?”
Dina ta murmusa, ta ce, “Maganin basir ne, ke dai ki dinga sha don da alama akwai basir a jikinki tunda ga shi
nan duk kin yi fari”.
Mairo ta yi dariya. Ta rasa dalilin da yasa kullum Dina ke treating dinta yarinya kamar Little Mairo.
Idan dai wadannan magangunan ne ai tunda ta zo gidan ta ke ganin Dinan na shansu, sai dai ba ta taba
tambayarta ko na mene ne ba. Amma yanzu ai ta yi girma da hankalin da zata san amfaninsu.
Daga baya ko me Dinan ta tuna? Ta zaro ido ta ce “Ke! Bani magungunan nan bai kamata ki fara amfani da su
ba, sai mun je asibiti anyi checking dinki don ban yarda da ke ba. Mai juna biyu ba ta amfani da irinsu”.
Mairo ta bata fuska kamar ta yi kuka, don gani ta ke kamar Dinan na kallon abin da ta ke yi a goshinta. Ta
tashi gudu tayi dakinta.
Dina sai ta yi dariya, kuruciyar Mairo da halayenta na alkunya suna burge ta matuka.
Satin Amiru daya da tafiya sai ga shi kamar an jefo shi. Tana kicin tana hadin salad don haka Dina ce kadai a
falo, ita ma ba ta jima da dawowa aiki ba, ta sanya Mairon ta hada mata salad zata ci.
Kararrawar kofar shigowa ta yi kara, ta umarci Lynder ta bude. Amiru ya bayyana a falon cikin bakaken suitspanish. Ta daga kai tana kallonshi tare da amsa mishi sallama, ganinshi wani ‘as a smart pace’ (afujajan) ya
bala’in ba ta dariya.
A gajiye ya zauna cikin kujera idanunshi a kwance ya ce “Dariyar me kike yi min?”
Ta ce “Ganinka na yi kamar an jefoka, lafiya dai ko?”
Ya ce “Da babu lafiyar ai ba za ki ganni ba, sai dai sako. Ina kanwar takin nan ne? Yanzu haka kina nan kina
hadata da wadannan girke-girken naki na tsiya”.
Ta ce “Au na tsiya ne, amma idan an baka kake ci?”
Bai amsa mata ba ya nufi kicin inda ya jiyo motsin tangaraye.
Ta juya baya ta takarkare tana bude gwangwanin ‘heinz-beans’ ya mika dogayen hannuwanshi ya rungume ta.
Ya soma sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Kwanaki bakwan nan da ya yi ba tare da ita ba, jinsu ya yi kamar
shekaru bakwai. Ka zalika ita ma Mairon, don dai ta kasance mai zurfin ciki da kawaici ne. Amma ta yi missing
din mijinta yadda harshe ba zai iya bayyanawa ba.
Sun yi nisa cikin duniyar faranta ran junansu, kafin Mairo ta ankara da inda suke, ta yi kokarin kwatar kanta.
Ya dago habarta da hannun damanshi yana son kallon kwayar idanunta, amma bai yi nasarar hakan ba sabida
matsananciyar kunyarshi da ta lullube ta. Ta yi azamar hankade shi sabida warin ‘aspen’ da ta tsinkaya cikin
bakinshi.
Ya sake kamota ta fuzge, ya ce, “Haba Mairo? Mairon Dina, Mairon Yaya Habibu?”
Zata fice ya sha gabanta a galabaice, ya ce, “Kina so Mala’ikun rahma su soma tsine miki ko, bayan da kina ta
kwasar lada?”
Inda abin da Mairo ta tsana to wannan furucin ne, kamar ta yi kuka ta ce,
“Ni na ce ka sha taba?
Tun a gida ka ce min ka daina sha, amma ai ga shi nan na ji-ta a bakinka”.
Ya rufe mata baki, ya ce, “Wallahi bazan kuma ba. Wannan din ma a jirgi aka ba ni. Ba kudina na sanya na siya
ba. Ce miki nayi “bazan kuma sayen taba ba”, ba “bazan kuma shan taba ba..” Sun ba ni ‘wine’ ne, ni kuma na
ga da na shata ai gara na sha tabar”.
Ta zumbura baki, tana toshe hanci ta ce.
“Ni don Allah ka ba ni hanya na wuce…”
Amma fa banda kaduwa ba abinda jikinta ke yi, Amiru ya bala’in sanin ‘weakness’ dinta. Karfin halinta da
jarumtakarta suna ba shi mamaki. Kiri-kiri ga shi tana cikin kewar mijinta, a idanunta da gangar jikinta, amma
a fatar baki ta nuna ba haka ba ne.
“Ko in baki (hanky) ki toshe hancin da kyau??”
Kanshi ya tura cikin gashin kanta ta baya, bayan ya cillar da ‘bound’ din da ta daure gashin da shi. Yana shakar
kamshin kumfar ‘pert-plus’ da ta ke amfani da shi ba tare da ta sa wa gashinta ‘relaxer’ ba. Amma sai ka
rantse kullum ‘relaxer’ ta ke shafa mishi.
Can cikin kunnenta yake rada mata. “Rakiya za ki yi min Mairo”.
Da sauri ta ce
“Zuwa wajen budurwarka?”
Ya yi dariya, ya ce.
“Ga budurwata nan ina tare da ita, shopping zan yi”.
Ta ce “Ni ba zan bika ba kullum kana yawo da wadannan gardawan masu shegen kallon tsiya kamar wasu
‘body-guard’ dinka”. (Raymond da Franklyn).
Yayi dariya. Ya ce
“To zan sallame su. Mu biyu zamu yi tafiyarmu, sannan ba shan Aspen a hanya, in kin ganni zan saya ki kwace
credit card din, hakan ya yi miki?”
Ta gyada kai cikin gamsuwa.
“Amma kai zaka fadawa Anti Dina”.
“Idan don wannan ne, ta kwana gidan sauki, uuwata ce ita ko kanwar ubana? Daga kawo ajiya?”
Abin ya bata dariya amma ta gimtse.
“To bari na karasa hada mata salad din, yunwa take ji”.
Har zuwa lokacin bai sake ta ba, ya bi ya kankane ko’ina na jikinta. Sai faman sunsunarta yake yi kamar zai
hadiyeta. Sai da ta hada da magiya sannan ya sassauta rikon da ya yi mata.
Tare suka fito ta isa ga Dina ta mika mata farantin, ta nufi dakinsu don ta kimtsa.
Wanka ta sake ta zuba riga da siket na wani material yellow mai santsi, ta nada dan bakin mayafi a kanta, ta
matse da fil ta kara feshe jikinta da turaren (fahrenheit). Tana kokarin saka takalmi ta jiyo Dina na kwala mata
kira, don haka ta dauki jakarta ‘polo’ mahadin takalmin da ke kafarta ta fito.
Ba ta san me ya fadawa Dina ba, ta ce
“Amiru ya ce za ki raka shi shopping ko? To sai kun dawo”.
Suka hada ido ya daga mata gira, ya kashe ta da murmushi. Ta yi hanzarin sunkuyar da kanta.
Ya mike yana kiran Raymond ya fada mishi su je sai ya neme su, yana tare da Madam dinshi. Ya karbi
makullan motar Mairon hannun Dina, suka fito.
Tafiya suke sannu a hankali, irin tafiyar da ke sanya nishadi a zuciyar ma’aurata, kuma irin tafiyar da ke kara
wa masoya kusanci da juna. Babu wanda ke cewa uffan sai zuciyoyi kadai suke magaba. Ya mika hannu yana
karo sautin Abdurrahman Sudaith da ke tashi a hankali cikin radiyon motar, cikin suratul Anfal.
Hankalin Mairo na kara nutsuwa da mijinta, wanda dan zaman da suka yi na tsayin watanni ya sanya ta ke
fuskantar kyawawan halayensa a hankali. Wadanda ada bata yi tsammani ba. In tayi la’akari da irin tsarin
rayuwarsa da bigiren da yake rayuwa a ciki, da kuma irin mutanen da yake hulda da su. Ko su Raymond sun
isa su dulmiyar dashi cikin dabi’un nasara. Sai ta tadda akasi ga tunaninta.
Da farko dai ta fahimci Amirun ba’a kada shi a magana, ko me ka gaya masa zai baka amsa daidai da
maganarka, ko ya baka wadda ta fita daraja, kuma ba shi da munafunci, kai tsaye yake fadin abin da ke cikin
zuciyarshi ba tare da la’akari da cewa, zai yi wa mai sauraronsa dadi ba ko a’ah?
Sannan Amiru mutum ne mai kula da sallah, da ba ta dukkan hakkokinta. Har ga tabon sujjada nan rangadede
a kan goshinsa. Ga son ‘yan uwansa da iyayensa da kulawa da su, irin mazan da duk son da suke wa mace ba
sa hada shi da na iyayensu.
Yana da ban dariya, yana da barkwanci, sai dai idan miskilancin ya motsa ya fi mahaukaci ban haushi da
takaici.
Ba ta kai ga gama tunaninta ba ta ji yana zungurin kugunta da mukullin mota.
Ta juyo a hankali tana kallonsa, soyayyarshi na kara kamari a tare da ita. Kamar yasan me ta ke tunanin, ya
kamo hannunta ya rike cikin nasa, ya kwantar da kai a kafadunta, ya dora mata dukkan nauyin jikinshi…
“Mairo kada ki bar ni. Ba ni da harshen da zan fada miki adadin soyayyarki da ke cikin zuciyata.
Ban taba son wani abu a rayuwata kwatankwacin yadda nake sonki ba, idan kika dauke iyayena. Ban taba yin
soyayya ba Mairo sai a kanki. Nasan kin aure ni ne ba bisa son ranki ba, amma……”
Ta yi hanzarin kai yatsunta ta toshe mishi baki. Ta kankame shi sosai jikinta yana rawa.
“Kayi min alfarma kada ka kara yi min wannan zargin, domin kuwa Allah shaidata ne akan cewa na aureka ne
da zuciya daya, cikin amincewa kaina cewa, kai ne mijin da Allah Ya zaba min; kai ne zabin Allah a gare ni.
Daga lokacin da na fara ganinka, na ji wasu abubuwa sosai a zuciyata. Duk da soyayyar Uncle dina da nake
fama da ita a wancan lokacin hakan bai hanani ba ka wani muhimmin gurbi a zuciyata ba, gurbi na ‘auratayya’
ba soyayya ba.
Na kalubalanci tunanina ne a lokacin da cewa yaudara ce. A hankali na gane hakan ma ba ya zuwa sai da
soyayya! Soyayya ta da Uncle Junaid wani abu ne da ya shude a wata rayuwata ta can a baya…, Past is past
Ameeru, and you are my present…!!!”
Amiru ya wani irin kankame Mairo yana mata sumba mai tsayi da zurfi, tsayin wani lokaci mai tsawo, kamin
su samu nutsuwa cikin zuciyoyinsu. A yau ya samu wani irin kwanciyar hankali irin wanda bai taba samu ba
tun haduwarsa da Mairo. Tada motar yayi suka harba kan titi. Ba su tsaya ba sai a shagunan da ke karkashin
‘Sommerset mall’.
E
Shi kadai ya shiga ya yo musu duk sayayyar da zai yi. Ta duk abinda zasu bukata na kwana uku. Ya bar Mairo
cikin motar. Tsabar kishi irin na Ameer bai yarda da shiga da Mairoßs irin wadannan wuraren ba, bai tsaya a
ko’ina ba sai a otel din ‘Hyatt Regency’ inda Amirun ya yi masauki. Hotel ne na manya, na daga wane sai
wane. Ta dube shi a razane, a sanda ya kashe motar, sanda ta fahimci cewa a otel suke. Kamar ta yi kuka ta
ce.
“Haba don Allah? Me zan ce da Anti Dina?”
Ya langwabar da kai abin tausayi a masangalin kujerarsa, tsayin lokaci bai ce mata komai ba, a cikin lumsassun
idanunshi kadai ta gama samun amsar duk wani uzurin sa da dalilinsa, da kyar ya ce. “Ba kya tausayina ko
Mairo? For quite a week kenan ina suffering. Sabida ke nazo, tun daga Nigeria har Michigan. Sannan idan na
tafi na barki zan jima ban zo ba, sai kun yi hutun karshen semester, ban sanki da halin rashin tausayi ba. kada
ki fara ta kaina……!!!”
Kalaman sa sun gama kashe duk wani kuzarinta. Kwayar idanunsa sun gama kassarata. Ba yadda ta iya, dole
ta zuro kafafunta ta fito. Zuciyarta na gaya mata ko akan titi Ameeru yakeso su rayu yau zata kasance tare
dashi, gata dama da rarraunar zuciya, wadda ta afu ga son Ameerun with infatuation. A kwanaki ukun da suka
yi cikin otel din ‘Hyatt Regency’ tamkar wani sabon babin amarci ne Amiru da Mairo suka balle.
Mairo ta ga soyayya a gun Ameeru irin wadda a duk karance-karancen Novels dinta, ba ta taba katari da irinta
ba, domin Amiru karshe ne, a fannin nuna soyayyah.
A yau zai maida ita gida, domin jirgin karfe hudu na yamma zai bi zuwa gida Najeriya. Tunanin Mairo na yadda
za ta fuskanci Dina ne da Yaya Habibu idan ya dawo ya ji ta bi miji, kwana da kwanaki ba a gansu ba.
Har kuka ta yi saboda damuwa, don ta lura shi ko a kwalar rigarshi. Ba karamin tausayi da dariya Mairon ta ba
shi ba. Don haka ya shiga lallashinta, yana nuna mata wannan ba wani abu ne na tada hankali ba.
“Shi Yaya Habibu da Dinar ba daki daya suke kwana a gabanki ba? Su ba su ji kunyarki ba, sai ke ce mai jin
kunyarsu akan haka?”
Ta balla mishi harara cikin hawaye. Ya tarairayota ya rungume yana dariya, ya ce.
“Shikenan ki barni da su, ni zan fitar da ke”.
****
Lokacin da suka iso gidan Habibu da Dinan ne suke ‘lunch’ tare da su Muhammad. Cikin bagararwa Yaya
Habibu ya saci kallon Mairon da ke bin bango tana son ta shige dakinta, ya ce.
“Ai na dauka kun wuce gida Najeriya ne?”
Amiru ya yi dan murmushi, sannan ya ce.
“Idan mun wuce ina ruwanka? Ni bana son aikin sa ido wallahi”.
Dina ta yi murmushi tana jinsu suna ta yi, Amirun na cewa.
“Sa ido sana’ar banza, Yayan banza, Yayan kwabo”.
Habibu ya dube shi, ya ce.
“Na ji dai, tunda ni dai mace ba ta taba kwantar da ni a gadon asibiti ba”.
To a nan ya kashe bakinsa, don bai kuma tankawa ba.
***
C
ike da himma Mairo ta dasa karatunta daga sabuwar shekara, duk da su Ir’eesh sun wuceta, ya kasance ta
koma farkon shekara ta biyu.
Habibu ya ba ta wayarta, bayan wadanda Amirun ya mallaka mata guda biyu irin wadanda ba ta taba gani ba.
Don haka duk dare suna makale a waya suna fadawa juna how much they miss each other.
Yadda ba ta iya sakewa su yi hira fuska da fuska, a waya idan ka ji su, sai ka sha mamaki. Kullum tambayarshi
shi ne, har yau babu ajiyarshi ne?
Da ya fadi hakan zata yi sauri ta kashe wayar, sabida kunya.
To haka rayuwarsu ke tafiya, cikin so da kauna, ba sa taba gundurar juna. A Najeriya ne ko a Michigan, har
Mairo ta kare karatunta, ta fiddo kwalin first class degree a B.Sc Sociology.
Har zuwa wannan lokacin shiru, babu haihuwa babu alamarta, don ko batan wata Mairo ba ta taba yi ba. Tun
abun na damunsu har suka hakura suka fauwalawa Allah.
Sai dai kuma kamar yadda kowanne dan Adam ba ya rasa makiya, to hakan ce ta faru da Mairo daga dangin
Amiru, musamman a Gaya da suka fara kishin-kishin Amiru ya auro musu juya, don ma Hajiya tana
tsawatarwa ne amma har su Sabah sun soma sauya mata fuska.
Aka soma yi wa Amirun tushen ‘yammata, ‘ya’yan gata, kyawawa wadanda suke ganin zasu iya gogawa da
Mairon da duk abin da ta ke takama.
Zuwa lokacin shi ma Habibu ya yi ‘retire’ daga ‘barclays’, haka Dina ta bar kotun da ta ke aiki. Sun tattaro da
‘ya’yansu duka sun dawo gida Najeriya garin Abuja, cikin unguwar colorado close.
Don haka Mairo cikin farin ciki ta ke, ga ta ga iyayenta, wadanda su ne kadai ta ke gani ta ji dadi, kasancewar
Hajiyar ma ta soma daukar hudubar ‘ya’yanta da ‘yan uwan mijinta na Amiru ya kara aure.
Daddy bai san abin da ke faruwa ba na matsalolin da Mairo ta soma fuskanta cikin gidan ba. A lokacin tana
hidimar kasa a nan jami’ar Abuja, ta kai ga ko ta gaida Hajiya a ciki ta ke amsawa don gani ta ke Mairon ta
mallake mata da, yadda har ba ya damuwa da samun dan kansa.
(Matsalarmu ke nan al’ummar Hausa, babu ta yadda za a yi a ga mace na zaune lafiya da mijinta yana sonta,
yana gudun bacin ranta, sai a ce ta mallake shi.
An fi so a ji kullum yana kawo kararta ana yi musu sasancin sulhu, ko ya dinga aura yana saki, ko ya dinga
aibatata cikin yan uwansa, Allah Ya sa mu gane mu gyara zuciyoyinmu, amin).
A yau ne Amiru ya shirya musu ‘wedding anniversary’ na cikarsu shekaru biyar da aure. Taro ne da ya tara
manya-manyan ma’aikatan bankunan Najeriya, bankunan kasar America, irin su World Bank, Barclays, Bank
of America, Comerica, Citigroup, HSBC, Chase… da sauransu. Abokansu na karatu ne da yawa da suka watsu a
wadannan bankuna suka gaggayyato. Taron wanda aka gabatar da shi a wani conference hall na ‘hotel’ din
‘Nicon Noga’ ya yi matukar yin armashi, kowane bako da maidakinsa, wato by couple’.
Mairo da Amiru sun samu kyaututtuka na ban mamaki daga ‘yan uwa da abokan arzikinsu. Kudi wannan
tsurarsu da Mairo ta samu sun tasarwa lissafi mai girma, ba’a maganar sauran kadarori irinsu gidaje, hannun
jari da sauransu.
Daddy kadai abin da ya bayar ya girgiza kowa, wai! Ina wuta a jefa marainiyar Allah Mairo a wajen kannen
Amiru, dangin Hajiya da dangin Daddy da suka zo daga Gaya.
Sun sha alwashin idan Habibu a tafe yake yana tsaface musu Da ta yadda har ba ya jin shawarar kowa sai
tashi, baya ganin owa nasa da gashi sai shi, to su a can suka kwan, kuma acan suka wuni.
Gadararsu shi ne Amiru shi ne silar arzikinshi, wannan bai ishe shi ba, sai da ya kakaba mishi kanwarshi da a
yanzu ta zame musu alakakai, karfen kafa.
Don haka sun sha alwashin sai Amiru ya yi auran dangi, kuma sai sun raba shi da Habibun koda za su yi yawo
tsirara ne.
A wannan dan tsukin Mairo ba ta samun zama, sabida shirye-shiryen fara karatunta a ‘Wayne State
University’ da ke Michigan. Komawa karatun da ya janyo mata kace-nace da dama har ta gwammace dama ba
ta tarki zancen ba.
Domin Hajiya ta kira Amiru kai tsaye ta fada mishi cewa ba ta yarda ba. Idan ba zata yi karatun a nan ba, to ta
bar shi, amma sun daina daukar wannan rainin hankalin na Habibu da mace tana gidan aure zata tsallake ta
tafi wata uwa duniya wai karatu.
Amiru ya sha mamaki kwarai, don bai taba ganin ranar da wani sabani ya gitta tsakanin Hajiya da Mairo ba.
Biyayya ta ke mata tamkar ta yi mata sujjada. Hajiyar da ke fada da shi idan ya batawa Mairo rai, amma yau
ita ce ta ke mishi magana kamar ba ta taba sanin Mairon ba. Bai san ba abin da ‘zuga’ da ‘karfar baka’ ba sa
jawowa ba. Cikin nutsuwa ya soma yi mata bayani cewa.
“Hajiya babu hannun Habibu a cikin wannan lamari. Idan ma da wanda yake da ruwa a ciki to ni ne. Don ni na
amince mata, Mairo tana karatunta na aure ta, wanda hakan har ya janyo mata asarar shekara guda, kuma
Hajiya wanda ya saba karatu a waje ba zai iya karatu cikin gurbatattun jami’o’inmu ba. Da wannan dalilin da
kuma wasu da yawa ya sa…..”
“Kai! Rufe min baki!! Shirmen banza shirmen wofi, sallamamme , bawan mace. Da dai ba a san asalin balbelar
ba ne zata zo ta ce da mu daga Makkah ta zo, kuma kowa ya samu rana ai sai ya yi shanya inda yake so.
Don haka ka tashi ka ba ni waje, maganar karatu na soketa. ‘Ya’yan Abdurrahman Gaya ma a nan suke
karatun, bare wata ‘yar karkarar da ko kwalta babu.
Allah dai Ya isa tsakanina da Habibu, tunda ya mayar min da da sammatacce. Ya kanainaye dukiyarka,
kanwarshi ta kanainaye zuciyarka ta tsiyata ka, don ba na jin abin da ta samu din nan kai ka samu rabinrabinsa. Sabida haka wannan hadin gwiwar da aka yi aka bude Habib Bank raba shi za a yi, wallahi ba zan
yarda ba. Ku biyu ke da banki, amma sunasa ne shikadai keda bankin. Sabida kai wawa ne. Don haka na ba ka
kwanaki bakwai ka kawo min takardun komi mai nuna ka raba dukiyarka da ta Habibu, idan ba haka ba,
wallahi TSINE MAKA ZAN YI!!!”
Haka ya taso ya fito ko gabanshi ba ya gani. ya yi taga-taga zai fadi, ya yi saurin dafa bango. Kanshi ya kulle
tamau, kwakwalwarshi ta daina aiki. Bai san yaushe Hajiya ta koma haka ba, bai san laifin da Habibu da Mairo
suka yi mata haka da zafi ba. Bai san me zai cewa Habibu ba.
Ya yi tunanin ko ya samu Daddy ya fada mishi ya ba ta hakuri, kuma ya yi tunanin kada haka ya janyo ya kara
laifi a wajenta.
Don haka a kwanakin da suka biyo baya duka Mairo ta kasa gane kan Amirun nata. Kullum yana kwance a daki
yana tunanin ta inda zai bullowa al’amarin ba tare da ya batawa kowannensu ba.
Don ta Mairo mai sauki ce, yasan ba ta musu da shi, idan ya ce bai yarda ta koma Michigan ba yasan ba zata
nuna bacin rai ba, zata bi umarninshi.
Amma Habibu fa, me zai ce mishi? Mutumin da ke dawainiya da dukiyarshi dare da rana tana kara bunkasa
tana kara habaka shi yana kwance a gida, sai ya ga dama ne zai dan tabuka wani abu. Ba ya son sunan Hajiya
ya fito ko kadan cikin lamarin kada mutuncinta ya zube a idanun Habibun.
To wannan tunanin su ne suka hadu suka haifar mishi da ciwon kai mai tsanani, wanda ya kai shi har tsayin
kwanaki biyar da yin maganarsu da Hajiya amma ya kasa yin wani yunkuri. Ga shi yau saura kwana biyu
kwanakin da ta deba mishi su kare.
Mairo ta shigo cikin shirin barci dauke da dan karamin faranti a hannunta. Ta zauna a gefen gadon ta dauko
kanshi ta dora a cinyoyinta, bayan ta ajiye farantin da ke hannunta bisa durowar jikin gadonsu. Ta daura
kanta akan nashi tana jin yadda ya yi zafi rau. Cike da tausayawa ta ce.
“Don Allah A.A (kamar yadda ta ke kiransa idan ta so nishadi, wato Amiru Abdurrahman) ka daure mu je
asibiti tunda ka ki yarda na kira Dr. Fred, ya kake so na yi? Jin ciwon kan nan nake kamar a cikin jikina, sannan
ka ce ba zaka hadiyi magani ba? So kake nima ciwon ya kamani sabida damuwa?”
Sai ta sa kuka sosai, ta tura kai cikin kirjinshi. Ya mika hannu yana shafar gadon bayanta a hankali. Amma bai
ce komi ba. Shi kadai yasan halin da zuciyarshi ke ciki. Kukanta na tsuma mishi zuciya, yana kara gigita shi.
“Ya isa Mairo, ya isa don Allah, ba ni maganin na ji zan sha”.
Ta dago da idanunta jage-jage da hawaye tana kallonshi, kwanaki biyar kacal, duk ya rafke, ya rame, ga wata
kasumba mara tsari ta fara bayyana, kamar ba Amiru mugun dan kwsalisar nan ba.
Ta mike zuwa lokar jikin mudubi, ta dauko kwayoyin paracetamol ta ciri biyu ta hada da gorar ruwan ‘swan’
mara sanyi ta ba shi. Da kyar ya ke hadiya yana bata fuska don shi sau dubu gara a yi mishi allura goma da dai
ya hadiyi kwayar magani.
Ya tura yatsunshi cikin sumar kanshi yana cudawa a hankali. Mairo ta gane kwarai, akwai muhimmin abin da
ke damun Amirun nata. Wanda zurfin cikinshi ba zai bari ya bayyana ba. Sai ita ma ba ta takura da lallai sai ta
ji ba. Yinin yau ma ya kare baki daya ba tare da ya hassala komi ba.
Ya rage gobe ne wa’adin da Hajiya ta dibar mishi zai cika, suna kwance kankame da juna kamar masu jin
tsoron kada wani abu ya gitta a tsakaninsu. Ya yi gyaran murya ya ce, “Maryam”.
(Sunan da bai taba kiranta da shi ba).
Ba ta amsa mishi ba, illa ta kalli kwayar idanunshi ta cikin dan hasken fitilar barci (dim light). Ya sake kiranta a
karo na biyu, ya ce.
“Alfarmarki nake nema Mairo, za ki yi mini?”
Ta ce
“Babu alfarma tsakanina da kai, sai biyayya da bin umarni. Don haka fadi abin da kake so, ni kuma ji da bi shi
ne nawa”.
Ya kara lullube ta da katafaren kirjinshi, ya sarke ‘yan yatsunsu cikin na juna, ya ce.
“Maganar komawarki karatu Michigan, na ke so ki bari, ki yi hakuri, ki yi a nan Gwagwalada ya fiye min
kwanciyar hankali”.
Ta ce
“Idan don wannan ne ai babu komai. Sai dai na fi son na yi karatu a jami’a mai nagarta da tsohon tarihi,
kamar Ahmadu Bello ko jami’ar Bayero”.
“Duka ki hakura, ki barsu, tunda kika ji na ce ‘alfarma’ to alfarmar nake nema da gaske. Kin san haka kawai
bazan sa ki yin abin da ranki bai so ba, don haka ki yi min uzuri”.
“Na yi maka A.A, Allah Ya ba ka lafiya”.
***
A yau ne Hajiya ta yi kiranshi don jin inda suka kwana. Ta tsare shi da dara-daran idanunta, kafarta daya akan
daya cikin luntsumemiyar kujerar falonta. Ta ce.
“To yaya, kai nake saurare?”
Ya ce, “Maganar tafiya karatu ai an barta Hajiya, tunda ba kya so”.
Ta mika mishi hannu, ta ce.
“To ba ni takardun”.
Ya yi wuki-wuki da ido, can ya ce.
“Habibun ne ba ya nan, idan ya dawo za mu zauna a ware a kawo miki……..”.
Sai hawaye sharr-sharr wasu na korar wasu, domin gani yake Hajiya ta gama tozarta shi, a duk ranar da ya
doshi Habibun da wannan zancen. Domin Habibun zai yi zargin abubuwa da dama, ciki kuwa har da tunanin
ko Amirun na zarginshi da cin amana ne, ba zai taba kawowa ranshi Hajiya ce ta sa shi ba sabida yadda ta
dauke shi kamar dan cikinta, shi ma yake daraajjata kamar mahaifiyarsa.
Hajiya ta kama baki, tana cewa.
“Yanzu sabida ina so na rabaka da abin da zai cuce ka, shi ne za ka sanya ni a gaba kana yi min kuka?”
Ya dago sosai yana dubanta da idanunshi da suka kada suka yi jawur. Muryarshi abin tausayi ya ce.
“Hajiya, Habibun ne zai cuce ni?”
Ta girgiza kai.
“A’ah, ba zai cuce ka ba. Ni uwarka ni ce zan cuce ka. Habibu sai ya je kauye ya biya malamansa. Tashi ka je,
na yafewa Habibu da kanwarshi Mairo kai, idan har ba zaka kawo min takardun komi na dukiyarka ba. Kuma
zan maka Habibu a kotu sai ya ba ni dukiyar da na!”
Zuciyarshi ta bushe da etsoro da al’ajabi. Ya ce, “Hajiya me ya yi zafi da za ki kai Habibu kotu? Ki kara min
alfarmar kwana biyu. Na yi alkawarin zan cika umarninki ko da hakan shi ne aiki na karshe da zan gabatar a
rayuwata”.
Fitowa ya yi zuciyarshi na suya, ya zaburi mota bai tsaya a ko’ina ba sai a kofar gidan Habibu.
A lokacin Habibu na shirin shiga mota zai fita, shi kuma yana danno hancin motarsa (Camero, 2 door) cikin
‘gate’ din Habibun. Don haka ya fasa shiga motar ya jirashi har ya karaso ya fito daga motar.ŕ
Ba karamin faduwar gaba ce ta samu Habibun ba ganin irin halin da aminin nashi ke ciki. Suka rankaya suka
koma cikin gidan. Dina ba ta nan, ta je Malaysia ita da yara, duba jikin mahaifinta da ba shi da lafiya.
Habibu ya isa ga firij, ya dauko mishi gwangwanin ‘coke’ ya bincire hancin ya mika mishi ba tare da sun gaisa
ba. Ya karba ya yi kurba daya, amma ya kasa wucewa a makoshinsa. Dole ya furzar da na bakinshi idanunshi
sun kara kadawa sun hargitse.
Habibu ya zauna a gefenshi, ya ce
“Be a man, plz! idan kana raye ba abin da ba zaka gani ba”.
Ya rausayar da kai cikin amincewa da kalaman Habibun. Ya ce
“Alfarmarka nake nema, sai dai bana son ka tambaye ni dalilina, na yin hakan”.
“Ba zan tambaye ka ba Amiru. Fada min komi tsaurinta”.
“So nake na janye komi nawa daga cikin ‘Habib Bank!!”.
Habibu ya yi shiru, domin Amiru ke da kaso 60% wanda hakan ke nufin durkushewar bankin da ya faro da
nasara cikin shekaru biyu kacal da kafuwarshi, wanda ke nufin shi kadai (Habibun) ba zai iya ‘running’ bankin
ba.
Ya tabbatar makiya sun shigo cikin al’amarinsu, amma bai ga laèèifin Amirun ba, wanda da gani kasan tursasa
zuciyarshi yakeyi, wajen furta kalaminshi.
Ya ce “Idan don wannan ne, ai babu damuwa Amiru. Idan har hakan zai samar maka kwanciyar hankali, ka ba
ni kwana goma, insha Allahu komai naka zai dawo hannunka. Sai dai ina so ka samu lauya, wani daban, ba
Dina lauyar bankinmu ba”.
Ya ce
“Ni ba ni da wani lauya”.
Habibu ya ce
“Dole sai ka nemo”.
Ya juyar da kai yana kwararar da hawaye, ya ce
“Daga yau ba zan kara neman kudi ba, tunda su din fitina ne. Ta yadda har wasu suke ganin su din (kudi) sun fi
mutumci da amana, Ya Allah Ka tsiyata ni………..”
A gaggauce Habibu ya toshe masa baki.
“Kana hauka ne?
Kada ‘frustration’ (bacin rai) ya sanyaka fita daga imaninka. Ka je ka samo lauya, mu yi abin da zai kwantar
maka da hankali”.
“Ni na ce da kai hakan kwanciyar hankalina ne?”
“Ba ka ce ba, don haka abar kazar cikin gashinta ba sai an fiffigeta ba”.
Cikin satin Habibu, tare da taimakon Barrister Dalha wani abokin aikin Dina daya daga cikin lauyoyin ‘CBN’ da
Barrister Mujahid lauyan ‘starling’ sun hattama komi na dukiyar Amiru, ta koma hannunshi da sunanshi da
sanya hannunshi.
Ya kwashi takardu cikin ‘briefcase’ ya yi sallama a dakin Hajiya. Kallo daya ta yi mishi ta ga yadda ya zabge, ya
yi zuru-zuru sai karan hancin da idandanun kadai, amma hakan bai sa ko kadan zuciyarta ta russuna ba, da dai
ta kyale Habibu da kanwarshi su yi galaba a kanta. Tunda sanda ta ke nakudar abinta bayan rainonshi cikin
mahaifarta, har wata tara da dawainiyarshi zuwa girmanshi, ai ba su zo sun tayata ba.
Don haka ta kudure sun daina cin arzikin Amiru, kowa ya ci gashin kansa.
Ya zauna a kujerar da ke fuskantarta, kwakwalwarshi na juyawa. Ya mika mata ‘briefcase’ ba tare da ya iya
hada ido da ita ba.
Ta bude ta zaro takardun ciki ta sanya ‘medicated glass’ dinta tana dubawa daya bayan daya. Ita kanta ta
razana da ganin abin da Amirun ya mallaka a ‘yan kananan shekarunshi.
Bayan ta gamsu da ingancinsu, ta maida su inda suke tana murmushi, ta ce.
“To ko kai fa?
Ba ga shi ba yanzu sai yasan zafin nema ba ya tashi daga cima-zaune? Yanzu wane kasuwanci zaka soma da
wadannan din?”
Ya kalle ta kawai bai yi magana ba. Ta dauka bai ji ba ne, don haka ta sake maimaitawa.
Ya ce ba tareda ya dubeta ba,
“Sadakar da su zan yi”.
“Au fushi ka yi, sabida ina yi maka gata Amiru?”
Ya ce
“Ya ya za a yi na yi fushi da ke Hajiya? Ina juya su, kin ce in kawo miki. Na kawo miki kuma ki ce me zan yi da
su?
Ban iya wani kasuwanci ba, bayan wanda nakeyi, ni ma’aikaci ne. Aikin banki shi ne wanda na iya tsawon
shekaru goma.
A yau kin ce na barshi, don kada Habibu ya samu dan wani abu a jikina, wanda bai taka kara ya karya ba.
Bayan kin san duniyar cudarni in cudeka ce, kuma shi ma ba matsiyaci ba ne, yana da rufin asirinshi wanda da
kadan ne bai kai nawa ba.
Haba Hajiya! Shekarata nawa da Habibu bai cuce nin ba sai yanzu da muka zama daya?”
Hajiya ta ce
“Rabi (half) kuka zama ba daya ba, sallamamme, bawan mace. Tunda ba ka so ka yi zuciya har kana cewa
sadakarwa zaka yi, ni ina so, zan yi maka sadakar, amma ba duk ba. Ranar da tsiya ta isheka ka waiwaye su,
nima ina da ‘account’ din da zan adana maka su su hayayyafa ba Habibu ne kadai ya iya juya sisi ya koma
kwabo ba”.
Duk abin nan da ake Daddy bai sani ba, don shi ba mazauni ba ne, sannan ko da wasa Hajiya ba ta yi gigin
sanar da shi abin da ta yi ba, don tasan bazai goyi bayanta ba. Sai su Khalisa da Nina wadda ke aure a Lagos
sune ‘yan abi yarima a sha kida, duk suka yi ta tsalle.
Nina ta ce
“Mun gama da wannan, saura ‘yar kauyen Gurin-Gawa, don Allah Hajiyarmu ki yi mana waje-road da ita”.
Hajiya ta ce
“Ku barni da su, duk na ishe su, ko ba ta yi waje ba, ai ta yi zaman boranci idan na aura mishi wadda zata cika
min gida da ‘ya’ya”.
*****÷
F
An debi watanni biyu kwarara, Hajiya na tarairayar danta don dai ta wanke dattin ta dake idanunshi, tana
kuma nuna kulawarta akan Mairo, wadda ita kuma ba ta san tana yi ba, karatunta kawai ta sa a gaba.
An yi bikin su Sabah tun shekarar da ta gabata, bayan sun kare karatunsu. Don haka yanzu sassan Hajiya babu
kowa, daga ita sai ‘yan aiki. Watakila hakan ne ya sa ta kwallafa ranta ga son ganin ‘ya’yan Amirun, tunda
sauran jikokinta iyayensu maza ba za su ba ta ba.
Yau da ya shigo gaishe ta da safe, cikin sakin fuska ta amsa. Bayan sun gaisa ta janyo wata dirkekiyar jarka irin
wadda ake zuwa da zam-zam daga Saudiyyah din nan, cike ta ke taf da ruwan rubutu bakikirin da shi ta girgiza
ta tsiyayo a kofi ta mika mishi.
“Ungo shanye ka ba ni kofin”.
Ya ce
“Na mene ne Hajiya?”
“Maganin sammu da tsarin jiki ne, ko ba zaka sha ba? Idan ka shanye shi duk wani makaru da ke jikinka zai
karye, don haka shanye ka ba ni kofin”.
Bai yi musu ba ya karba ya soma sha a kyankyame, don kam shi Amiru tun fil’azal mutum ne mai kyankyami
matuka, ko (spring water) ba kowanne ya ke sha ba.
Tun yana kyankyami har ya zamo masa jiki. Don ka’ida ne kullum ta Allah ya zo gaishe ta, sai ta cika kofi ta ba
shi tsawon sati biyu suna hakan. Ya ji ya fara jin wasu sauye-sauye a zuciyarshi akan Mairo, sai dai ko kusa bai
alakanta hakan da cewa rubutun da Hajiya ta ke daddaka masa ba ne.
Yau da yamma da ya dawo daga ofishin Daddy inda ya koma zuwa yana taya shi da wasu ayyukan, sabida
nauyin Habibu da yake ji ya sanya alakarsu yanzu ta ja baya.
Duk da cewa shi Habibun a nashi bangaren, ya maida komi ba komi ba, amma Amirun gani yake Hajiya ta riga
ta gama tozarta shi a idon Habibu, ta yadda har abada ba zasu koma kamar da ba.
Ya yi sallama Hajiya da ke harde cikin kushin tana sauraron labaran Al-Jazeera ta amsa mishi. Ya samu kujera
mai fuskantarta ya zauna. Ya dan zamo daga cikin kujerar yana gaishe ta.
Ta amsa mishi da sakakkiyar murya, can kuma ta ce.
“Anya Amiru, rayuwa zata yiwu da hakan? Ace mutum ya yi ta zama, ba ya tunanin samun dan kansa, duk
tsararrakinka daga masu ‘ya’ya uku sai masu hudu amma kai ba abin da ya dame ka, sabida idonka ya rufe da
son matarka. Alhalin kuma ba zata iya ba ka sanyin idanu ba, sai dai a cika maka masai da kashi, to wallahi
bazan yarda da wannan ba”.
Ya dago idanunshi a kankance ya dubeta.
“Hajiya mun isa mu ba wa kanmu abin da Allah bai ba mu ba ne? Sannan ba ki san matsalar nan daga gare ni
take, ko daga gare ta ba? Don haka bai kamata ki dau zafi akan al’amarin ba, don Allah Hajiyata”.
Ta ja dogon tsaki tsiiit!
“To ku je asibiti mana? Ko haka za mu yi ta zama cikin jiran gawon shanu? Ai gara a banbance, don a san
matakin dauka”.
Da wannan tunanin na maganganun Hajiya ya kwana, har ya soma jin kamshin gaskiya a cikinsu. A
shekarunshi ya ci ace shi ma ya aje masu yi mishi addu’a. Har ya soma zargin Mairo ko tana amfani da
‘contraception’. Tunda dama ai tun farko ba sonshi ta ke yi ba.
Ya yi gaggawar kwabar zuciyarshi daga wannan mummunan zargin da ta darsa mishi. Ya yarda da matarsa
100% (Azzannu zambun, wa lau kana hakkun), sai dai rashin damuwarta akan al’amarin ma ai abin dubawa
ne, bokonta kawai ta sa a gaba, da son ganin kwalayen ilimi, tare da son hango kololuwar biro da takarda.
Ta murda kofar ta shigo cikin sallama cikin sassalkar doguwar riga baka sid, kirar Dammam, fararen
duwarwatsu na ta walwali a jikinta, sannan ni’imtaccen kamshinta na din-din-din ya doki hancinsa.
A kwance yake ‘flat’ bisa makeken gadonsu ya lumshe ido kamar mai barci. Har ta zauna gefen kafafunshi ta
soma ja mishi yatsu bai juyo ba. Haka nan ya samu kanshi da jin haushinta babu gaira babu dalili. Ta yi
kiranshi cikin tattausar murya, amma bai bude idonshi ya dubeta ba.
Karewa ma kara runtse idonshi ya yi, tareda janye kafarshi dake ciin hannunta, don ba ya son ganinta, ba ya
son kamshin turarenta.
Ta yi wa kanta kyakkyawan matsugunni a kirjinshi, ji ya yi kamar ta dosana masa wuta. Ya yi azamar angijita
ya ce
“Leave me alone, please!”
Cikin mamaki ta ke dubanshi, idanuwanshi sun hargitse kamar ba Amirun nata ba. Ta ja gefe ta zauna jikinta
yana rawa, don ko kadan bai taba yi mata magana cikin tsawa irin haka ba, sannan ita a rayuwarta ba ta iya
tashin hankali ba.
Zuwa can kuma ya mike ya soma shiri, ya dan juyo a kai-kaice ya kalle ta.
“Ki shirya, asibiti za mu”.
Ta yi ta maza cikin sanyi ta ce.
“Waye ba lafiya?”
“Idon matambayi ne”.
Abin da ya ce da ita ke nan.
Kamar ta ce, ‘to ba zani ba’, amma kwarjinin Amirun da kimarshi dake cikin idanunta ya hana. Soyayyar da ta
ke mishi wata kaddara ce daga Allah da ita kanta bata san adadin ta ba. Ta yadda ba ta iya fushi da duk abin
da ya yi mata. To balle ma bai taba yin ba. Idan haka ne ya dace ta yi mishi uzuri, ba kullum ne mutum yake
kasancewa cikin dadin rai ba.
Suna tafe a motar amma ba mai ce da dan uwansa uffan, kowanne abin da yake sakawa a zuciyarsa daban ne
da na dan uwansa.
Tunanin Mairo shi ne, shin laifin me ta yi wa Amiru haka da zafi, da har ba zai iya budar baki ya fada mata ba
don ta gyara?
Shi kansa Amirun ya rasa laifin da ta yi mishi ya ke ganinta bakikkirin da jin zafinta babu gaira babu dalili.
Amma ransa na gaya masa rashin haihuwar tane, yazo wani limit na kasa jurewa. Har suka iso babban asibitin
Abuja, kalma daya ba ta hada su ba.
Kai tsaye ofishin Dr. Fredrick suka nufa, Amiru ya ce da shi.
“Doctor mun zo ne yau ka duba mana dalilin rashin haihuwarmu, al’amarin ya fara damuna. Sannan Hajiya ta
tada hankalinta, idan ba asibitin nan muka zo ba, ba zata barni na zaun lafiya ba”.
Sai a sannan ne Mairo ta cira ido ta dube shi. Yanzu ne ta gano dalilin bacin ranshi. Wato sun fara damuwa da
rashin haihuwarta, wanda ita ba ta isa ta bai wa kanta ba.
Dr. Fredrick ya hada su da Gynaec Doctor da za su gani, wato Dr. Ma’u. Bincike iri-iri Dr. Ma’u ta yi amma ba
ta gano wata matsala a tare da Amiru ba. Da ta zo kan Mairo, sakamako ya nuna cewa, ita ce bakin
mahaifarta yake a tsuke sosai. Idan har tana son haihuwa, dole sai an yi mata aiki, an bude bakin mahaifar.
Ya roki Dr. Fredrick da Dr. Ma’u lokacin da Mairo ta nufi mota cewa su taimake shi su bar wannan sirrin a
tsakaninsu, ba ya son Hajiya ta ji.
Dr. Ma’u ta ce da shi.
“Ai ko ba ka ce ba, amana ce tsakanin likita da ‘patient’ dinsa, insha Allahu ba za a fada mata ba”.
Ya yi godiya ya barsu da alkawarin idan sun dai-daita ranar da za a yi mata aikin za su dawo.
Mairo ta shiga cikin tsananin damuwa. Tashin hankali da rudani. Yadda farat daya Ameeru ya sauya mata.
Kamar ba shi ba. Babu wannan murmushin, babu wannan soyayyar tashi mai kidimata. Kullum daga fada sai
hantara. Duk ta bi ta kare a tsaye, ta soma samun tangarda a karatunta. Amma don zurfin ciki irin nata, ko
Dina ba ta taba tunanin fadawa ba.
Hajiya ta samu yadda ta ke so, domin ta janye hankalin tilon danta kanta. Duk abin da ta ce da shi dashi ya ke
amfani, jikin shi har rawa yake wajen bin umarnin ta, ta himmatu da yi wa surukarta karfar baka, mai wuyar
magani, wadda ta fi kiyayyar zahiri lahani a zuciyar wanda ake mawa.
Duk yadda ya so ya lallame ta su koma asibiti a yi mata aikin amma Mairon ta ki. Idan ya takura mata da nacin
maganar sai ta sa kuka. Ga shi shi kuma ba abin da ya tsana irin kukanta da ke soya zuciyarshi.
Ta dage akan cewa, ita Allah ne kawai bai nufe ta da samun cikin ba. Ranar da ya nufa Ya ga damar ba ta zata
samu ne.
“Amma Shi Ya ce ‘tashi in taimake ka. Sannan babu cutar da Ya saukar ba tare da ya saukar da ita tare da
maganinta ba.
Idan ke ba ki damu ba, ni ina son ganin dan kaina. Tun da rayuwar ba jiranmu ta ke ba, mu muke jiranta”.
Tana so ta yi tsaki, amma kimarshi da martabarshi sun wuce hakan a idanunta. Dole ta maida tsakinta.
“Ni fa babu inda zan je”.
Duk inda ranshi yake idan ya yi dubu, to ya baci. Ba ta taba yi mishi musu a rayuwarshi irin na wannan lokacin
ba. Ya rasa abin da zai mata YA HUCE… Gaba daya ya soma tunanin bokon da ya barta tana yi ne ya sanya ta
raina shi… Wannan ne karo na farko da ya kai kararta wajen Habibu tun bayan aurensu. Habibun ya ce, ya
kawo mishi ita.
Daga ita sai Yaya Habibun a babban falonshi, don Amirun da ya kawota bai zauna ba ya wuce ofis wajen
Daddy. Dina na kicin tana kacaniyar shirya abinci.
Habibu ya ce
“Mairo me nake ji haka? Wai mijinki bai isa ya sa ki abu ki yi ba?
Idan ke ba kya son ‘ya’yan, to shi yana so. Muma muna so, me kike nufi da ba zaki yarda a yi miki aikin ba?”
Ta fashe da kuka, ta ce
“Da da ne ya ce na yi abin da yake so, ai zan yi ne, ba tare da kowa ya ji ba. Amma ni ma yanzu ban san me
yake nufi da ni ba. Babu magana mai dadi tsakanina da shi sai hantara. Kuma yadda ya ke nunawa kamar ta
karfi yake so na haifo mishi dan, sannan ni gaskiya tsoro nake ji, lafiyata kalau inje a jagwalgwala min
mahaifa”.
Habibu ya ce
“Likitoci ba za su yi miki karya ba Mairo. Maganar canzawarshi sai ki yi mishi uzuri, yanayin rayuwar kenan,
wata rana a sha zuma, watarana a sha madaci! Ba kullum ne mutum yake kasancewa cikin dadin rai ba!”.
Da kyar Habibun ya rarrashe ta, ta yarda za su je ayi aikin. Ranar litinin Dr. Ma’u ta yi mata aikin.
***
Tsawon shekara guda har da doriya, babu wani bayani, wato ba abin da ya sauya bayan yin aikin. Babu ciki ba
alamarsa.
Dai-dai lokacin da ta kammala rubutun ‘project’ dinta na kwalin master, sabida kwazon da ta nuna kai tsaye
suka ba ta gurbin zama daya daga cikin malamansu, wato ‘lecturing’ a jami’ar Abuja.
Mairo ta debi kudi masu yawa, ta dankawa Yaya Habibu aka soma ginin makarantar firamare da sakandire a
kauyen Gurin-Gawa. Sannan ta dauki sauran gaba daya ta mallaka mishi halak-malak, bayan ta warewa Baffa
nashi kason.
Habibu ya saida gidanshi na kasar America da wasu manyan kadarorinsa ya tada kafadar (Habib Bank) wanda
ke gaf da durkushewa. Cikin taimakon Allah sai al’amuran suka soma dai-daita. Amma a ranshi ya dai karbi
kudin Mairo ne kawai bai ce mata komi ba, sai dai cikin ranshi ya kudurce juya mata zai yi.
***
Hanan Abdulwahab, diyar kanin Hajiya ce, wato Uncle din Amiru da ke garin Gaya. ‘Yar kimanin shekaru
ashirin da hudu, kyakkyawa ce matuka, kuma tana da irin tsagin su Amiru a gefen hagu da dama na fuskarsu.
‘Yan asalin garin Gaya ne su ma, don da Babanta da Hajiya ubansu daya. Mahaifinta tsohon soja ne, wanda ya
rike manya-manyan mukamai a aikin soji, har zuwa matsayin da yake kai a yau, wato Major Genaral
Abdulwahab Gaya.
Gaba dayan karatun Hanan tun daga firamare har jami’a ta yi shi ne a garin Lagos, inda mahaifinsu ya yi aiki a
wancan lokacin. Daga baya da ya yi ‘retire’ suka dawo garin Kaduna da zama, inda suke zaune a halin yanzu.
Direban Hajiya Mr. Kademi ne ya je ya dauko Hanan daga filin jirgi, wadda ta sauka karfe hudu dai-dai na
yammacin ranar ta Laraba.
Hajiya ta yi mata kyakkyawar tarba bayan ta rungumeta tana lale da diyarta. Kamar yadda Hajiyar ta nemi
izinin mahaifin Hanan di n kan ya barta ta zo ta yi mata kwana biyu.
Sun baje a falon Hajiya suna labari, Hanan ta ce.
“Ina labarin brother, yanzu yaran shi nawa ne Hajiya?”
Hajiya ta kyabe baki, ta ce.
“Babu ko daya”.
Hanan ta yi murmushi, ta ce.
“To ai kin san Turawa ne, watakila ba su shirya fara tarbar ‘ya’yan ba”.
Cikin rashin walwala Hajiyar ta ce.
“Ke raba ni da abin haushi, kada ke ma ki bata min rai yanzun nan. Turancin yaci abu kazan ubansa. Ba wani
tsarin iyali, juya kawai ya je ya auro”.
Kwanan Hanan biyu a gidan, amma ba su hadu da Amiru ba, sabida sanda yake shigowa gaida Hajiyar da safe
ita ba ta tashi daga barci ba, sabida dai Hanan ‘yar hutu ce ta karshe.
A rana ta uku ne da ya shigo Hajiya ta je har dakin da ta sauka wanda ya kasance dakin su Rayyah ne kamin su
yi aure, ta tasota ta ce ta zo su gaisa da Yayanta. Ta ba ta wani farin kwalli ta ce, ta zizara a idonta, ta yi duk
kokarin da zata yi ta tabbatar sun hada ido.
Hanan ta cika da mamakin mene ne dalilin Hajiya na yin hakan? Sai dai kuma ba ta jin zata iya kin bin umarnin
Hajiyar.
Tsaye ya ke a baranda yana amsa kiran Habib cikin wayarshi, a lokacin da Hanan ta fito falon. Ya juya baya
hannunshi daya dafe a bayanshi, yayin da ya yi amfani da dayan wajen rike wayar.
Hanan ta tsura mishi idanu, wani al’amari mai karfi na fizgarta. Rabonta da Amiru tun wani zuwa da ya yi
Kaduna gaida mahaifinta a lokacin yana Washington. Zuwa yanzu ya kara girma da haiba. Duk wasu kamanni
na ingarman namiji ya mallake su, kuma kyakkyawa na karshen-karshe. Ya zama ‘giant’ mai wani irin kyawun
halitta na burgewa da ban mamaki. Irin mazan da ba kowacce lafiyayyar mace ce zata iya dauke ido a kansu
ba.
Gwiyoyinta suka yi sanyi, kuzarin jikinta ya kare, wata irin soyayyar Amirun na tsirga zuciyarta. Ba ta iya ta
dauke ido a bayanshi ba har ya juyo.
Da farko kallo daya ya yi mata, amma ya rasa dalilin da ya sanya ya kasa dauke idonshi a kanta. Don sai ya
ganta kamar Mairo, idanunta, bakinta da karan hancinta duk sun rikide sun koma na Maironshi sak! Har ya ke
jin yafi son wannan Mairon, akan wadda ya baro a gida.
Sakon Hajiya ya yi aiki sosai, ya hada wata matsiyaciyar soyayya, mai wuyar fassarawa.
Duk da haka bai saki fuska ba, jan ajin yana nan. Tuni ya soma kokarin nemo notin kanshi domin ya kulle. Ya
koma kujerar da ya tashi ya zauna, dai-dai lokacin da Hajiya ta fito tana ta murmushi.
Ta dubi Hanan fuska cike da fara’a, ta ce
“Hanan kina ta tsayuwa ba ki gaida Yayan naki ba”.
Ta ja ta suka zauna a kujera daya. Ta sake cewa.
“Ba ka gane ta ba ne Yayansu?”
Ba tare da ya sake duban Hanan din ba, ya ce.
“Na gane ta mana, ba Hanan ba ce?”
Ta ce
“To ke ki gaishe shi mana? Ko haka ake yi wa babba a garinku?”
Hanan ta ji kunya, ta ce
“Ina wuni?”
Ya ce, “Bana so, tunda ke ba ki san ya kamata ba”.
Ya mike zai fita, Hajiya ta ce.
“Sai ina kuma?”
Cikin takaicin raba shi da aikinshi da ta yi ya ce a raunane.
“Ina da wani wurin zuwa ne da ya wuce ofishin Daddy?”
Ta ji ba dadi cikin ranta. Ta ce.
“To ka nemi wani aikin mana?”
Ya yi murmushi kawai, ya sa kai ya fita ba tare da ya ce da ita komi ba.
Ya yi juyi a makeken gadonsu, wani abu na tsunkulinshi a zucci. Ya rasa abin da ke damunsa. Ya juya a hankali
ya dubi matarshi abin sonshi, Mairo. Barcinta ta ke sadidan cikin kwanciyar hankali. Sanye ta ke cikin bakaken
(pjs) masu taushi. Duk inda ake neman kira ta halitta (natural) ta fita tsara, ta nunawa sa’a, kuma mai gamsar
da da namiji ta kowacce fuska to matarshi ta zarce.
Biyayya, hankali, ilmi babu wanda Allah bai hore mata ba, ta yadda a baya ya yiwa zuciyarshi alkawarin ta ishe
shi rayuwar duniya da lahira.
Wato ba zai taba yi mata KISHIYA ba, amma kuma yana matukar son ganin kwanshi a duniya kamin Allah Ya
dau ransa. Yana son ganin ‘family’ mai ban sha’awa kamar na Habibu. Idan haka ne, yana bukatar kara AURE,
wanda ba ya cikin ra’ayinsa. Bai san kuma abin da ke tunzura zuciyarshi ga son yin hakan ba. Musamman da
ya ga Hanan a yau. Sai dai fa babu buurbushin sonta ko kankani a zuciyarshi, sai wata fitinanniyar sha’awa da
bai san dalilinta ba.
Maironshi kadai yake so har cikin kashi da vargo, sai dai kuma bai san hakikanin abin da ke kassara soyayyarta
a zuciyarshi a wannan dan tsukin ba. Da ta haihu, da kada ta haihu yana sonta, amma hakan ba ya nufin zai ci
gaba da zama da ita a hakan ba tare da ya bi wata hanyar da zai iya samun dan kanshi ba.
Amma anya Habibun ya cancanci hakan? Mutumin da ya tserar da rayuwarshi daga soyayyar da ta kusa
hallaka shi, ya yankewa kanwarshi burin rayuwarta (karatu), ya rabata da dadaddiyar soyayyarta ga waninshi,
ya wanke ta ya ba shi ita ba don tana so ba, har zuwa lokacin da ta koyawa zuciyarta kaunarshi a hankali, ba
don wata tsiya da ya mallaka ba, don ko lefenshi Habibu bai karba ba, cewa ya yi ya ajiye, idan ta je can
gidanshi ya ba ta.
Anya ta cancanci ya yi mata kishiya don ta kasa haifa mishi da? Wanda ba ta isa ta bai wa kanta ba.
Ya san Mairo ba zata hana shi yin aure ba, sabida hankali da kyakkyawan tunaninta, amma yana jin kunyar
Habibu a karo na biyu ya je mishi da wannan zancen, wai zai yi wa Mairo kishiya.
Ya matsa a hankali ya janyo matarshi ya rungume ya yiwa kanshi matsugunni a dogon wuyanta, yana mai
sakin ajiyar zuciya mai nauyi.
A wani bangaren kuma da ke can karkashin zuciyarshi, ana kawata mishi Hanan ne da sanyin muryarta kamar
Mairo.
A hankali ya ke cewa… “Am sorry Habibu da Mairo, ina son kara aure, amma ba don bana son Mairo na ba”.
Kamar an ce da ita ‘bude idonki’. A hankali ta bude fararen idanunta. tana jin wani ruwa mai dumi a wuyanta,
kafin ta mika hannu ta shafo hawayen Amiru, a hankali hawayen ke gudu a dokin wuyanta. A razane ta mike,
ta lalubi makunnin lantarki ta kunna, haske ya wadaci dakin. Ya kauda kai daga idanunta, don ba ya son ta ga
hawayen soyayyar da yake yi mata.
Binshi ta yi ta kwanta a bayanshi, ita ma ta soma kukan da ba tasan dalilinshi ba. Ba ta taba ganin Amiru yana
kuka ba, domin mutum ne mai taurin zuciya da juriya bisa duk wani al’amari da ya samu kanshi ciki, mai dadi
ne ko mara dadi? Abin da zai sa shi zubar da hawaye, hakika ba karamin abu ba ne.
“Me ke faruwa A.A? Don Allah ka fada mini.
Zubar hawayenka na nufin tashin hankali na. Idan dai ‘ya’ya ne Allah zai ba mu Amiru, har yau ban fidda rai
ba. Domin jikina da zuciyata, suna ba ni mun kusa cinye jarrabawarmu.
Idan kai ka yi kuka, kai da zaka iya auren wata ka samu, ni kuma in yi yaya? Ko kuma wani laifin na yi maka, za
ka sa Ubangijina Ya yi fushi da ni ta dalilin zubar hawayenka?”
“Ni ba ki yi min laifin komi ba. Ni ne ma zan yi miki, ba bisa son zuciyata ba, sai don wata jarabta da na samu
kaina a ciki, da nake son ke da Habibu ku fahimce ni.
Ba zan yi don gajen hakuri ba, ko don na samu ‘ya’yan da nake mafarkin samu daga gare ki ba, sai don wata
masifa da na samu zuciyata a ciki, da ni kaina ban san dalilinta ba.
Mairo so nake zan auri ‘yar uwata Hanan!!!”
Jin maganar ta yi tamkar saukar aradu cikin kwakwalwarta, tun daga kanta har zuwa yatsar kafarta babu
wanda bai amsa kuwwar sautin Amirun, cikin gangar jikinta ba.
Sai ta janye jikinta a hankali daga jikinshi. Kumallon matan wanda kowacce mace kedandana ya motsa, ba
tasan tana son Amirun har haka ba, sai yau da ta ji farat daya ta tsane shi ko son ganinshi ba ta son yi.
To amma wacce hujja gare ta, ta hana shi yin aure tunda ita Allah bai ba ta abin da yake so ba? Lokaci daya ta
ji ta zargi Hajiya, wato wannan ne dalilin ajiye Hanan din cikin gidan, tana da yakinin cewa zama da mace
sama da daya ba tsarin Amirunta ba ne.
Sai dai kuma ai an ce MAZA BA SU DA TABBAS! Sannan kuma sauyawa suke kamar hawainiya!! Hajiya ta yi
nasara ta karya alkadarinta a zuciyar mijinta, tunda dama ta fada mata baki-da-baki cewa, sai ta aurawa
Amiru wadda za ta cika mishi gida da ‘ya’ya, ko ba dade ko ba jima.
Hawayenta na sauka a hankali bisa cinyoyinta, ya mika hannu yana tare hawayen suna sauka a tafukansa,
daga bisani sai ya sa harshe akan kuncinta yana side hawayen da ke zuba kamar an bude famfo.
“Tunda ba kya so Mairo na hakura, wallahi ba zan yi ba. Zan rayu tare da ke ke kadai har zuwa karshen
rayuwata, da kin haihu ko ba ki haihu ba………”
Ta yi saurin toshe mishi baki, ta ce.
“Idan na yi hakan na so kaina, kuma karya nake ba sonka nake yi ba. Farin cikinka shi ne nawa. Don haka with
my 100% go ahead, ka je ka yi aurenka.
Hawayena na zuba a bisa dalilai guda biyu ne, na farko na so na kasance ni ce mace ta farko da zan ba ka
sanyin idaniya, amma Allah bai nufa ba.
Na biyu ina KISHINKA iya yadda ban san adadinsa ba. Iya yadda harshena ba zai iya bayyanawa ba. Hawaye ne
na radadin cewa, zan daina mallakarka ni kadai, wanda hakan ba zai sa komi ba, kuma ba zai hana ba.
Don haka kar ka damu da wannan, Ameer, ka je ka yi aurenka, Allah Ya sanya albarka, a sami abin da ake so”.
Ya rungumota sosai yana cewa.
“Na gode Mairo, sai dai kuma ni ma jikina yana ba ni cewa, kafin kowa ya ba ni sanyin idaniyar ke za ki fara ba
ni…”
Ya sauya akalar al’amarin zuwa wani irin nau’in soyayya mai ban mamaki da bai taba nunawa kowacce ‘ya
mace ba. Ba a kuma haifi wadda zai nunawa ba. Mairon kadai yake ji har ruhi da bargon jikinsa. Bai san
dalilinshi na fadawa a soyayyar wannan yarinyar ba, wadda a da ko kallo ba ta ishe shi ba.
Ta kara kankame mijinta kamar ta tsaga kirjinshi ta yi wa kanta muhalli, don ta saddakar idan yau ta samu
wannan alfarmar, to gobe ba zata samu ita kadai ba. Sannan ji ta ke kamar lokaci ya zo da zata sake RASA
wani abu mai muhimmanci a tare da ita.
Wanda kuma shi ne Soyayyar wannan Amirun, da a yanzu ya kurda cikin kowanne sako da kowanne lungu na
zuciya da gangar jikinta. Tunda kuwa wata zai auro wadda zata samu irin wannan muhallin, da a da ta ke
tunanin ita kadai Allah Ya mallakawa, kuma ita kadai za ta ci gaba da mallakarsa, har zuwa karshen
rayuwarsu. Ashe tunanin nata ba zai zamo gaskiya ba?
Ta cira kai a hankali ta cikin hasken farin wata, wanda ya ratso ta tsakanin farin labulen dakin, tana kallon
yadda Amiru yake barci cikin kwanciyar hankali, bayan ya tsarkake jikinsa.
Ita kuwa ko motsin kirki ta kasa, har aka yi kiran assalatu tana mai tariyo rayuwarta daki-daki, dalla-dalla.
Gaskiyar yaya Habibu ne, haka yanayin rayuwar yake, wata rana zuma, wata rana madaci. Idan haka ne ya
kamata mu daina jayayya da nufin Allah. Idan Allah Ya rubuto mata hudu Amiru zai aura a duniya ba ta isa yin
komi ba, tunda abu ne da Allah Ya halatta.
Ba ta so ta zamo daya daga cikin matan da ke azabtar da mazajensu ta hanyar amfani da soyayyar da suke yi
musu. Amiru ranshi ne kadai bai mallaka mata ba, don so da kauna. Idan haka ne kenan ita ma ya dace ta yi
mishi halarci, watakila Allah Ya dube su Ya ba su abin da suke nema ta tsatson wata ba ita ba, tunda matsalar
daga gare ta take. Sannan mai yuwuwa ne kara auren nasa ya sa kiyayyarta ta ragu a zuciyar Hajiya, tunda
jigon kiyayyar tata akan rashin haihuwa ne, idan ta samu shi ke nan watakila su koma kamar yadda suke a da.
Allah Sarki! Bata san al’amarin Hajiyar ya fi gaban nan ba.
Da safe ko kalaci bai tsaya ya yi ba, ji yake kamar ana ingiza keyarshi akan ya je ya ga Hanan, ko da bai ce
mata komi ba, ya samu yin tozali da kyawawan idanunta.
Ya yi wanka ya zuba wagambari fara kal, ya taje sumarshi. Mairo ta dauki Miyakinshi tana fesa mishi, ta kara
da ‘outspoken intense’ wani kululun bakin ciki na cinta a zucci, don ta tabbatar wannan kwalliyar ba ta kowa
ba ce ta Hanan ce.
A ranta kuwa cewa ta ke, ko ba ka yi kwalliya ba ai zata so ka ne. A zuci ta fadi haka, amma ba ta san har
furucin ya subuto ya shiga kunnensa ba. Ya yi murmushi, ya ce
“Me kika ce, Mairo?”
Ba ta ba shi amsa ba, ta nufi kicin da sauri ta hado mishi ruwan ‘lipton’ da ganyen shayin ‘beyond comment’
tana firfita mishi yana kurba, jikinshi har rawa yake kamar wanda anka sanya cikin sanyin kankara. Sai ta fara
jin tausayin kanta, lallai ba karamar kauna yake yi wa yarinyar nan ba.
Bai ida shanye ‘lipton’ din ba ya yi mata sallama ya fita. Yau Hajiya wani irin turare dan duri ta bata, ta ce ta
mutsuttsuke hannayenta da shi, ta san duk yadda zata yi ta shafi hannun damanshi da hannunta.
Hanan ta ce
“To”.
Bayan fitar Hajiyan ta zauna a gefen gado tana tunani. Ta gane Hajiya na son hada soyayya tsakaninta da
danta ta hanyar ‘asiri’ wanda ita ba haka ta ke so ba. Kauna ta fisabilillahi ta ke mishi, idan har zata samu ya
aure ta. Ta yi mamakin yadda UWA da kanta ta ke asirce abinda ta Haifa, don kurum son cimma wata manufa
ta duniya. Shi yasa aka ce, ‘AL-MAAL WAL BANUNA ZINATUL HAYATUD-DUNIYA’ (wato:- ‘ya’ya da dukiya fitina
ne), don kurum tan son jikoki, sai ta dinga yi mishi asiri?
Ba ta san yaushe Hajiya ta koma haka ba, domin mutum ce mai takawa da riko da sallah da ibada, kowa ya
san hakan, amma ga shi yanzu sharrin zuciya yana neman dakusar da imaninta.
Ta bude kwalbar ta kai hancinta, turaren babu dadi kamar na ‘yan bori. Ta ce a ranta, ‘Idan na bari ya ji
wannan kamshin a jikina, ai sai ya raina ni ya ce ni ‘yar kauye ce’.
Don haka ta dauki turaren da aka narkar da naira dubu dari biyu da tamanin aka hada shi da zuciyar tunkiya
ta bulbule a masai. Ta dauki nata ‘eternal magic’ ta fesa ta yi kwanciyarta a daki ba ta da niyyar fitowa.
Ya jima a dakin suna hira da Hajiya yana duban kofar dakinta a sace ko za ta fito, amma bata ba alamarta.
Hajiya kuwa ta cika fam da Hanan da ta ki fitowa, balle ta gabatar da aikin da ta sanyata, ga shi kuma ba ta
son Amirun ya fahimci tuttura masa Hanan din ta ke so ta yi da ta kwala mata kira. Ta dauki waya tana dannedanne kamar tana son kiran wani nan kuwa text ta tura mata.
“Don abu kazan ubanki ki fito ki kawo mishi kalaci”.
Hanan ta zumbura baki ta fito tana kunkuni cikin ranta tana cewa, “ba dai ubana ba”.
Da shi da Hajiyar suka daga ido suka dube ta. Yadda ta ke tura baki kamar Mairo, idan tayi fushi, sai ta kara
burge shi. Ya yi kasa-kasa da ido yana kallonta a sanda ta ke tambayarshi.
“Ko za a kawo maka break-fast?”
Kamar ba zai amsa ba, can kuma ya ce.
“Shin ke wace irin IDIOT ce ne? Da ba ki san ki gaida mutane ba za ki wani tsaya musu aka wai a kawo musu
break-fast, an ce da ke ciki suka kawo?”
Ta sake zumbura bakin Hajiya na kyaf-kyafta mata ido, wai ta shafa masa turaren, amma ita ta ma manta da
wani zancen turare. Zata koma daki ya ce.
“Zo nan”.
Ta zo ta tsaya mishi kerere a kai, ya kuwa sa kafa ya kwasheta ta fadi tim! A tsakar dakin.
Hajiya ta yi salati ta kwaso jiki da gudu ta tada ita, Hanan ta dasa kuka sosai tana rike da kafarta.
Hajiya ta ce
“Mene ne haka Yayansu? Wannan ai ba wasa ba ne, idan ka karyata fa?”
Ya ce
“Da na ce da ita wasa nake mata? Tarbiyyar da ba ta da ita ne, ni ba za a gwada a kaina ba”.
Ta ce
“Fice ka ba ni waje mutumin banza. Kuma ko ka ki ko ka so sati mai zuwa daurin aurenku, duk da rashin
tarbiyyar tata”.
Ya ce
“A aura min din ina so, amma wallahi duka zata ci idan ta yi min ba yadda nake so ba”.
Hajiya ta yi murmushi cikin jin dadi, ta tabbatar ba ta yi asarar kudinta ba.
Yana fita ta kira Nina (mai bin Amiru) a waya, ta ce
“Komai ya yi kyau, ki je ki kai mishi cikon kudinshi, da bakinshi ya furta yana sonta, zai aure ta”.
Nina ta yi tsalle ta dire duk da Hajiyar ba ta ganinta, ta ce
“Da gaske Hajiyarmu?”
Ta ce
“Ina miki wasa ne? Sai ku fara shirye-shiryen biki”.
Nina ta cillar da waya, ta rasa inda za ta sa kanta don farin ciki, sun yi nasara, sun gama da Habibu, sun gama
da Mairo. Ba su san fadarta a zuciyar mijinta ya zarce yadda duk suke tsammani ba.
A washegari Hajiya ta iske Daddy a turakarshi. Yana sauraron muryar BBC cikin ‘yar karamar radiyonshi. Tana
murmushi ta zauna a gefenshi.
Daga ganin irin zaman da ta yi ya tabbatar wata magana ce mai muhimmanci zata yi mishi, don haka ya
tattara hankalinshi ya ba ta, ya ce.
“Yaya aka yi ne Maman su Nina?”
Ta kalmashe kafa tana murmushi, ta ce.
“ALHERI ne zai karu cikin gidan namu”.
Ya ce, “Ina sauraronki, fada min na ji”.
“Kasan Hanan ta zo hutu gurina. To Yayanta ya ganta yana so sun sulhunta kansu ya ce, yana so zai aure ta,
kuma karshen satin nan idan Allah Ya ara mana rai da lafiya”.
Daddy ya dube ta sosai, ya ce.
“Wane ne Yayanta?”
Ta ce
“Ka ji ka Alhaji da wani zance, suna da wani Yayan ne bayan na gidan nan?”
“Kina nufin AMIRU?”
Ta ce
“Shi fa”.
Ya tsura mata ido cikin al’ajabi.
“Ko ni ban yi mata biyu ba, sai shi ne zai rikitowa kanshi abin da zai hana shi kwanciyar hankali? Ta ina
Maryam ta kuskuro shi da zai kara auren?”
Hajiya ta hade fuska sosai, zaka iya karantar bacin ranta akan kyakkyawar fuskar tata, ta ce
“Amma ai ba ta haihuwa, don ta yi mishi komai ba ta ba shi magaji ba me ta yi mishi ke nan?”
Daddy ya kafa mata ido cikin rashin yarda da al’amarin, ya ce
“Wa ya fada miki ba ta haihuwa? Ko shi ya zo ya same ki ya ce zai kara auren sabida matarshi bata haihuwa?”
Hajiya ta yi duru-duru irin na rashin gaskiya, sabida yadda ya tsareta da manyan idanunshi, ma’abota hankali
da nutsuwa. A daburce ta ce.
“To ya yi ta zaman jiran tsammanin warabbuka kenan?”
Ya ce
“Ba wannan na tambaye ki ba. Cewa na yi shi ya zo ya same ki ya ce da ke, yana so zai auri Hanan din sabida
matarshi ba ta haihuwa?”
Muryarta na rawa ta ce.
“Eh, shi ya ce yana so”.
“To kirawo min shi”.
Ta yi ‘yan danne-dannenta a waya ta kara a kunne, ta ce.
“Ta ki shiga”.
Ba musu ya fiddo tashi ya kira layinshi, bugu daya ya dauka.
Cike da ladabi ya gaida mahaifinshi, kamin ya ce.
“Ka zo falona yanzu, in son ganinka”.
Minti goma ba su cika ba sai ga shi ya bayyana a falon. Ya yi sallama ya nemi wuri can gefe ya zauna.
Hajiya zuciyarta in banda zabalbala ba abin da ta ke. Cike da fargaba kada ta ga samu ta ga rashi. Don haka ta
ke ta addu’a cikin zuciyarta, kan Allah Ya dorata a kansu dukkansu. Lokaci guda kuma tana jifan Amirun da
harara, cikin fararen idanunta.
Daddy ya fuskance shi sosai, ya tabbatar Amirun ya ba shi dukkan hankalinsa.
“Kwana biyu, ina yawan ganinka a ofis dina, sannan kana yawaita zaman gida, sannan abokaina da sauran
jama’a suna tambayata akan wata jarida da aka buga cewa, ana zaton ka janye hannun jarinka daga Habib
Bank, wanda hakan ya janyo durkushewar shi, sai daga baya ne ya soma mikewa, mene ne gaskiyar
al’amarin?”
Ya daga kyawawan idanunshi yana kallon Hajiya, wadda fuskarta ta yi kamar ta fashe da kuka. Ya yi duba ga
wahalar da ta yi ta yi da shi tun yana yaro, haihuwa da RAINO. Da kaunar da ta ke mishi har a GIRMANSA, da
sa idonta akan TARBIYYARSA. Ya tuno halin da ta shiga na kwana sallah a lokacin da ba shi da lafiya,…….
Wannan UWA ce da ba zai iya tozartawa ba……!
Don haka ya sauke kwayar idanunshi a kasa, a hankali ya ce.
“Daddy ba duka na cire ba. Na dai ciri wani kaso ne, sabida sabbin kwamfutoci samfurin ‘laptop’ da nake son
yo odarsu daga China, amma ka tambayi Habibun, ko shi zai gaya maka komai yana nan yadda yake, sai ma ci
gaba da aka samu ta fannoni da dama”.
(Ya fadi hakan ne don yasan daddyn ba shi da lokacin da zai tsaya yana tambayar Habibun, don shi ba mutum
ne mai bin kwakkwafi da sanya idanu akan abin da ba nashi ba).
Daddy ya ce, “Na ji wannan. To mene ne dalilinka na son kara aure, alhalin kuna zaman lafiya da matarka?”
Ya yi shiru yana cizawa yana busawa, don ba a fadawa Alh. Abdurrahman maganar banza, mara hujja da
makama. Yanzun nan zai yi watsi da al’amarin komai muhimmancinsa kuwa. Gashi shi kansa bai san dalilinsa
na son kara auren ba. Kawai ya ji yana so ne kawai, amma babu ta inda Maironshi ta rage shi. Mace daya ce
tamkar da dubu, abin alfaharin kowanne da namiji duk mulki da ilminsa.
Watakila dalilin son kara auren nasa ba zai wuce don ya samarwa Hajiya jikokin da ta ke so daga gare shi ba,
wanda Allah bai ba wa Mairon ba. Sai kuma fitinanniyar sha’awar komi na Hanan din, wanda ake kara kawata
mishi a zuci, a bayan kowacce dakika. Har yake jin ba zai taba samun kwanciyar hankali ba, idan har bai aure
ta ba.
Daddy ya dade yana nazarinsa, a yayin da shi kuma ya ke tattauna amsar da ya dace ya ba shi. Bai katse shi
ba, har sai da ya gama tattara kalamanshi suka daidaitu akan harshensa.
“Daddy ba wani dalili ba ne, da ya wuce umarnin UBANGIJI (S.W.T) na cewa, “Ku auri abin da ya fi muku dadi
daga daya-daya, biyu-biyu, uku-uku ko hudu-hudu idan har za ku iya adalci”. To hujjata ke nan. Sannan na
yarda da kaina, ina da yakinin zan zamo mai adalci a tsakaninsu”.
Daddy ya ce,
“Tunda ka jawo aya ai shikenan. Ba ni da ta cewa, Allah Ya sa a yi a sa’a. Ya ba da zaman lafiya, sai dai ina
dada jadda maka amanar Mairo. Bar ganin tana da Habibu, ita MARAINIYA ce.
Rikon amanar maraya kuwa sai an yi da gaske. Sannan ba zan yarda kowa ya wulakantata ba cikin gidan nan,
don takamar ka auri ‘yar uwarka. Ba zan mance halarcin da yarinyar nan ta yi mana ba, ta ceto rayuwarka
daga cikin halin ha’u’la’i, ta sadaukar da soyayyarta da ta ke yiwa waninka.
Ba zan mance furucin Habibu ba, ‘ko wannan shi ne aiki na karshe da zan gabatar a rayuwata, sai na aurawa
Amiru Mairo. Idan hakan zai zamo FANSA ga lafiyarshi’. Don haka tashi ka je ka yi shawara da Habibu, domin
masoyinka ne, ba na wasa ba”.
Daga shi har Hajiya jikinsu ya yi sanyi. Amma da yake shaidan ya riga ya samu muhalli mai GIRMA a zuciyarta,
sai ba ta ji ko dar na yin abin da ta yi niyya ba, wato samun jikoki ko ta halin kaka. Ai ba cewa ta yi a saki
Mairon ba. Ita jikoki kawai ta ke so. Daga jikin Amiru. Sannan ba zata lamunci Mairo kadai ta mallake mata da
ba. Dole nata ‘yan uwan su shigo su ma su ci abin da Mairon ta ke ci a Amirun.
Da wannan taron ya tashi. Hajiya tana mai godiya ga Allah da Ya ba ta da mai kaunarta da kaunar duk abin da
ta ke so. Tareda gudun wulakantar ta. Shin wannan bai isa ta kyale shi haka nan ba?
A’ah, zuciyarta na ci gaba da kitsa mata sabbin abubuwa daban-daban, wanda bai fice na raba Mairo da
Amiru ba. Idan ta samu ta shigar da wadda ta ke so, ta haifa mata jikoki, kamar yadda ta ke tunanin ya rabu
da Habibu, koma bai rabu da shi din ba, ya daina morar dukiyar danta, babu dangin Iya babu na Baba.
A daren ya tunkari gidan Habibu, jikinsa a matukar sanyaye. Sai dai ya yi rashin sa’a, Dina ta ce tunda ya fita
da safe bai dawo gidan ba. Don haka ya fiddo waya ya kira Habibun.
“Ina gidanka ina jiranka”.
Mintuna ashirin ba su cika ba, Habibun ya bayyana a falon, cikin shigar ‘suit’ na alfarma, da ganinshi ka ga
baturen banki tsantsa. Ma’abocin fara’a da haba-haba da jama’a. Sabanin shi da kwakwalwarshi ta ke a
hargitse, duk ya bi ya susuce sabida rashin kwanciyar hankali da kuma dalilin muggan asirin da uwarshi ke
dankara masa babu gaira babu dalili.
Jama’a ina UWA zata kai wannan hakkin? Tunda yake akwai hisabi tsakanin ‘ya’ya da iyayensu?
Duk irin ‘delicious’ din da Dina ta hada musu shi da Habibun ko loma daya bai iya ya ci ba. Habibu a nutse ya
ke karantar Amirun gaba daya ya birkice masa, Amiru dan gaye danye sharaf, ma’abocin yawan saisaye da
‘shaving’, amma yau ga shi fuskarshi ta cika da lallausar kasumba, bai damu da ya gyara ba.
Ya rasa abin da ke damunshi. Ga shi kuma da shegen zurfin ciki kamar Mairo. Da zai daure ya fada mishi da ya
taimaka mishi da duk wata hanya da yasan zata gusar mishi da damuwarshi. Ba karamar kauna yake wa
Amiru ba, ta yadda har ya ke jin damuwar shi as his own problem (kamar tashi).
Ya tsiyayi ruwan ‘ya’yan inibi da Dina ta tace mai sanyi cikin tambulan ya mika mishi. Bai yi musu ba ya karba
ya soma sha, sanyin lemun na kwantar mishi da zuciya. Ya daga idanunshi da suka kankance ya dubi Habibu,
ya ce.
“Yaya Habibu, na zo zan kara yi maka laifi”.
Habibu ya ce, (cikin girgiza kai) “Har abada! Babu laifi tsakaninmu, sai fahimtar juna, gaskiya da amana. Don
haka ‘be a man’ (ka zama jarumi) ka fada min abin da ke damunka”.
Ya yi hucin wani numfashi mai zafi ya fesar, ya yi sassanyar ajiyar zuciya ya ce.
“Aure nake so na kara Habibu”.
Ya sunkuyar da kai yana mai sauraron amsar da zai ba shi.
Wani abu ya dan daki zuciyar Habibun, kamin ya ce.
“Ko ba ka zo min da wannan maganar ba, na yi tunanin na ba ka shawararta. Sabida lokacin ba shi yake
jiranmu ba, mu muke jiranshi. Kwata-kwata rayuwar ta yanzu, bata da yawa, gajeriya ce. Sittuna ce, au
saba’una. Don haka (at 44) ya dace ace mun ajiye kwayayen da zamu kyankyashe mu samu sanyin idaniya,
kuma masu yi mana addu’a.
Bana jin Mairo sai halinmu na maza! Na idan mun samu sabon abu, hasken tsohon sai ya dushe a
idanunmu……..”
Ya katse shi da sauri da cewa.
“……. Har abada wannan tsohon hasken, shi zai ci gaba da haskaka min rayuwa. Abin da nake so ka fahimta
shi ne, ba ni da wani nufi cikin wannan kaddararren auren face wata jarabtar Ubangiji da ta same ni. Ta yadda
nake jin idan har ban yi ba, I cannot regain my fullest self (ba zan iya komawa yadda nake ba).
Ina bukatar goyon baya, da hadin kanka Habibu kamar kullum”.
Cike da tausayin Mairo, da kuma kaunar aminin nashi, wadda ta sha gaban komi, Habibu ya ce.
“Idan don wannan ne Amiru kai ma kasan ba zaka rasa hadin kaina ba. Tunda abu ne da Allah Ya halatta
mana, idan har muna so. Kuma muna da iko. Sannan Mairo ba kanwata ba ce ni kadai, kai ma kanwarka ce,
kuma matarka, da ke karkashinka.
Kana da damar da zaka yi abin da ka so a kanta. Ni dai matsalata wannan damuwar da na ke ganinka a ciki
kullum, tun daga lokacin da ka amshi dukiyarka a hannuna, ka kasa sakin jiki da ni kamar da. Idan dai ba wani
abu ne daban a zuciyarka ba kuma, ina so ka cire duk wata kunya ko jin nauyi da ka sanya a tsakaninmu, don
ni wallahi wallahi har na manta. Sannan Banki alhamdu lillahi komi yana daidaita a hankali.
Ka yi ta zama ke nan haka ba ka aiki? Ka mikawa Daddy takardunka mana? A san abin da ya dace, amma
zaman haka ai ba shi da amfani”.
Amiru ya yi ajiyar zuciya, ya ce.
“Har yanzu fa Daddy bai san na janye hannuna daga Habib Bank ba. Ta yaya zan ce dashi ya samomin aiki?”.
“Dalili?”
Habibun ya bukata cike da son karin bayani.
“Kai dai share kurum. Amma ni tunda na rabu da aiki tare da kai, bana jin zan kuma neman wani aiki”.
“Shi ne kuma har kake kara rikito aure? Wa zai ije maka nauyin matan naka?”
Ya ce
“Allah na nan, kuma tunda na yi BIYAYYA na tabbata ba zan tabe ba”.
Habibu ya so ya tambaye shi wa ya yiwa biyayyar? Sai kuma ya yi tunanin tunda bai furta ba, bari kawai ya
kyale shi, don ba mutum ne da ya fiya son a yi mishi kwakkwafi ko tirkiya a kan al’amarinshi ba.
Bayan fitar Amirun Habibu kwance ya yi cikin doguwar kujera ta katafaren falon shi. Dina na yi mishi tausa
kadan-kadan, kanshi bisa cinyoyinta.
Ta lura tun bayan tafiyar Amiru Habibu na cikin damuwa. Ta tausasa harshe ta ce.
“Me ya faru ne Habib? Don Allah fada min”.
Ya runtse ido ya ce.
“Wai Mairo Amiru zai yi wa kishiya!”
Ba karamin razana ta yi ba, amma don ta ba shi karfin zuciya, sai ba ta nuna razanar ba. Ta ce.
“Ni dama nasan wata rana wani abu makamancin wannan zai faru. Don ba tun yau ba na lura Hajiyar Amiru ta
daina shiri da Mairo. Don duk sanda na je gidan na gaisheta a ciki ta ke amsawa, sannan Mairo ko kallo ba ta
isarta, sai wani duba na kaskanci da wulakanci wanda kuma na tabbata akan rashin haihuwarta ne.
Duk da Mairo ba ta taba fada min ba na taba tambayarta cewa, ko ta yi wa Hajiya wani laifi ne?
Ta ce, ita kam ba ta sani ba, ita ma haka ta ga ta sauya mata”.
Habibu ya yi shiru cikin tunani, can ya ce.
“Idan haka ne Hajiya ce ta raba Amir da bankinmu, duk da cewa an ce zato zunubi ne. Kina da masaniyar
yanzu bankin nawa ne ni kadai?”
Dina ta bude baki cikin matsanancin mamaki.
“Amma ya aka yi bankin ya ke ‘running as earlier?’ Da fatan ba bashin wani bankin ka ci ba?”
“Ko daya, taimakon Allah kawai, amma don Allah kada ki dau wani ‘action’ don kafin ya janye sai da ya roke ni
alfarma kada na tambaye shi dalili, ban kuma tambaye shin ba. Ko Mairo kada ki bari ta ji wannan maganar.
Amiru yana cikin wani hali da yake bukatar duk wani masoyinshi daya taimaka mishi da addu’a. Kwata-kwata
ba ya cikin nutsuwarsa da hayyacinsa.
Son Mairo ya janyo ya shiga wasu matsaloli da dama, don haka don Allah duk lokacin da kika yi sallah ki
sanyamu cikin addu’arki.
Maganar aurenshi ki lallashi Mairo, ki nuna mata ta dauki komi ba komi ba, don ni shaida ne akan cewa Amiru
yana sonta. Don kin san adadin son ka ga mace, adadin kiyayyarta a zuciyar iyaye da ‘yan uwanka, sai masu
tsananin tsoron Allah kuma sauran mazan jiya irin su Alh. Abdurrahman wanda ba ya shiga rayuwar kowa.
Sai kuma ya kasance shi Amirun bai iya boye abin da ke karkashin zuciyarshi ba, har kowa nashi ya gane, bashi
da abin so sama da Mairo.
To wannan shi ya janyo mata kiyayya, ko wannan auren na lura na kuma fahimci tursasa shi ake yi, amma ba
ra’ayinshi ba ne”.
Dina ta jinjina kai, ta ce.
“Gobe insha Allahu zan je na lallashi Mairo. Idan dai aure ne wai ‘yan magana suka ce A YI DAI MU GANI…
GABA MU BADA LABARI… Idan dai Amirun-Mairo ne”.
***
Ranar juma’a uku ga watan uku shekarar dubu biyu da biyar, daruruwan jama’a suka shaida daurin auren
AMIRU ABDURRAHMAN GAYA da HANAN ABDULWAHAB GAYA a garin Gaya, da ke cikin jihar Kano. Sai dai
kuma kamar yadda kannenshi mata ‘ya’yan Hajiya Aisha da Abdurrahman suka so a yi biki na kece raini,
angon ya taka musu birki. ya ce ba zai yi ba, kuma bai da ko sisi, ko yana da shi ba zai bayar ba, balle ba shi da
shi.
Aure ya ce yana yi, kuma an daura, to su lullubo matarshi su kawo mishi ko lefe ba zai yi ba, akan wannan
amaryar da suke ta yi wa rawar kafa mai kama da tattabara don suna takamar ‘yar uwarsu ce.
Sai Hajiya ce ta hada lefe na gani a bada labari ta kai. Biki suke sosai a bangaren Hajiya babu ko mai leken inda
uwargida ta ke, sai AMINA. To dama haka ne, cikin makiya dari ba zaka rasa daya kwakkwara da ke sonka ba.
Mairo na tare da Dina, Nabilah da Ladidi da suka zo daga Kano, musamman don su yi mata dannar kirji. Sai
harkokinta ta ke kamar ba abinda ya dame ta, amma a zahiri can kasan zuciyarta suya yake tamkar zuciyarta
ta hudo allon kirjinta ta fito. Ba ta san tana son ‘Ameerun’ har haka ba, sai yau da ya zamo mallakinsu su biyu.
Duk da dauriyar da ta ke sai da hawayen suka balle a lokacin da ta ji gudar an shigo mata da amarya gidanta.
Nabilah da Dina har suna hada baki wajen cewa.
“Haba-haba Mairo? Kada ki bada mu mana?”
Suna goge mata hawayen da tafukan hannayensu.
Ko irin amanar nan da ake kawo amarya wajen uwargida su Sabah ba su yi ba, ita ma ta godewa hakan don ta
kasa ‘controlling’ hawayen idanunta, sai dai kuma sun yi taronsu sun gama lafiya ba tare da an zagi kowa ba.
Kafin karfe goma na dare, duk mazajensu sun zo tafiya da su. Ya rage saura Mairo ita kadai a dakinta.
Madadin ta zauna tana kunci da kunar zuci, sai ta dauro alwala ta dasa sallah. Sallah ta ke ba tare da tasan iya
adadin raka’o’in da ta ke yi ba.
Lallai da gaske Dina ta ke, soyayya a hankali ta ke rikidewa ta zama kauna. Ji ta ke kamar ta dora dukkan
hannuwanta a kanta, ta kwarara ihu. Son mijinta ya game ko’ina na sassan jikinta da zuciyarta. Tana neman
sassauci wajen Ubangiji daga wannan mugun KISHIN da ke cin zuciyarta. Daga wannan fitinannen son
AMIRUN, da ba ta taba ji a rayuwarta ba.
Dan halak din sai ya turo kofar ya shigo, cikin ruwan tokar ‘pyjamas’. Yau harda sanja turare maimakon
‘miyaki’, kamshin ‘incandessence’ ne ya doki hancinta. Ya zauna a bakin gadon yana lallatsa wayarshi yana
jiranta, sai dai kuma babu alamar tana da niyyar idar da sallar, tana sallame wata, zata sake tada wata. Don
haka ya kishingida sosai akan gadonta yana lumshe ido a hankali alamar barci na son fizgar sa.
Ba ta yi niyyar katse sallarta ba, amma dole ta katse. A lokacin da agogon bango ya buga karfe biyu na sulusin
dare. Ta kunna fitilar da ya kashe ta dube shi har ya fara bacci. Ta ja babban yatsan kafarshi ya bude
lumsassun idanunshi a hankali a kanta.
Ta yi saurin dauke nata idon kada ya gano ‘weakness’ dinta.
“Ya kamata ka tafi, ina so zan rufe kofa na kwanta”.
Ya lumshe idon a karo na biyu.
“Na hanaki rufe kofa ki kwanta ne?”
Ta ce
“Amma ai kai ma kasan ba a nan ya kamata ka kwana ba”.
Ta fada cike da haushin gulma, da kinibibin MAZA, da bata fatan AMIRUN ya kasance daya daga cikinsu.
“Ke da kika san ya kamatan ai sai ki kaini inda zan kwanan……….”
Ta dalla mishi harara, ya yi dariya ya mike ya cilla kafarshi.
“Na tafi wurin (sweet 16) dina tunda tsohuwar korata take yi”.
Ta ce
“Idan ka je don Allah ka take ta 16 times, gobe na ganta da ‘ya’ya 16”.
Ya sake yin dariya ya kama baki, ya ce
“Yarinyar nan ashe kina da baki? Kalamanki sun girmi kakana, bari in tafi kada (sweet 16) din ma ta rufe min
kofa in zama marayan karfi da yaji alhalin ina da gatana, mata cancada-cancada har guda biyu?”
Ya kama kugunta ta buge mishi hannu, ya kawo kisses ta goce ta hankade shi.
Ya ce
“Allah Ya danne kirjinki, Uwargida sarautar mata, tunda Dina da Nabilah sun kasa danne min shi. Sai da safe,
me zan ce da ‘sweet 16 idan na je?”
Ko amsa ba ta ba shi ba. Ta kara tsare gida sosai. Ya lura babu wargi, don haka sai ya ja tsumman rayuwarshi
ya yi gaba.
A zaton Mairo, yana can yana shan amarci, don haka Allah kadai yasan halin da zuciyarta ke ciki. Ba ta iya ta
runtsa ba, har aka yi kiran assalatu.
Da kyar ta dauro alwala ta fara gabatar da raka’atainil fajr kafin ta gabatar da faralin asubahi. Tana rokon
Allah Ya rage mata kishi, Ya ba ta juriyar da zata baiwa mijinta hadin kan da zai samu nutsuwa har ya iya yin
adalci a tsakaninsu.
Da safe ba ta fito da wuri ba, sai misalin karfe sha daya. Ta tambayi Jummai mai yi mata aikace-aikace, ko ina
ne dakin amaryar? Ta yi mata nuni da daya sassan gidan wanda yake a kulle.
Ta yi sallama ta shiga falon babu kowa, sai ta matsa kofar ‘bed-room’ din ta sake yin sallama. Hanan ta fito
cikin rigar wanka da ‘showercap’ a kanta. Yarinyar kyakkyawa ce ba ta da makusa, sai dai sirintarta ta yi yawa.
Ga shi shi kuma Amirun ba ya son macen da ta fiya kashi ba mamora. Amma don kyau kam zallarshi Hanan za
a shiga da ita ko ina a duniya, a nunawa sa’a ba tare da an ji kunya ba. Wato dai tana daga cikin matan
‘fashion’ irin su Saliman Saifuddeen Dan Aliyu Dambatta’. (Alheri)
Sai suka dan tsaya suna kallon juna. Kowacce zuciyarta ta buga da ganin ‘yar uwarta. Sai dai kuma duk abu
daya suke fadi ckin zuciyoyinsu, ‘Ai ba ki fi ni ba’.
Sai dai kuma da yake dukkaninsu ‘yan birni ne, sai suka saki fuska. Mairon ce ta fara cewa.
“Amarya kin tashi lafiya?”
Ta ce
“Lafiya lau, amma ai ba ki kawo min angon ba, ko keyarshi ban gani ba har yanzu. Kin kama abinki kin saka a
daki, don haka bai kamata ki kirani da amarya ba, ke ce dai amaryar”.
Jikin Mairo ya yi sanyi, ta ce.
“Kada ki yi min wannan zargin, ni bai kwana a dakina ba”.
Cikin raha da yanayin zolaya Hanan ta yi maganar, kasancewarta (frank), amma ita Mairon cikin jin ciwon abin
da Amirun ya yiwa Hanan din ta yi maganar, don ko ita aka yi wa haka ba zata ji dadi ba.
“Kuma da kika ji shi shiru, ba sai ki bishi ba? Ko ba ki san dakinshi ba ne? Ni ma ai an yi min laifi, ba a kawo
min ke ba, balle ni ma in san da shigowarki na dauko angon naki na kawo miki”.
Hanan ta yi dariya har siririyar wushiryarta ta fito, ta ce.
“Kin san ba kowacce uwargida ce ta ke karbar wannan amanar ba. Watakila shi yasa aunties dina ba su yi
hakan ba”.
Kamin ka ce meye wannan sai ga kishiyoyin biyu sun zube a kujera suna hira rai-rai-rai kamar ba kishiyoyin
juna ba.
Cikin wannan dan zaman da Mairo ta yi da Hanan, ta fahimci wasu halaye a tare da ita. Na farko ta fi hanan
kishi, sai dai kuma watakila don abin da ke hada kishin bai faru da Hanan din ba. Sannan kuma gabuwa ce,
mai tabbatar da cewa ita ‘yar fari ce, sannan zuciyarta mai kyau ce, da alama za a yi zaman lafiya da ita.
Bai dawo gidan ba sai misalin karfe uku na yamma. Ya duba dakinta a bude amma ba ta ciki. Ya leka bayi, nan
ma ba ta nan, don haka ya fiddo waya yana kiranta, amma layin a rufe yake. Ya yi kiran Jummai ya tambaye ta
ina matar gidan ta je ne?
Ta ce
“tana sassan amarya”.
Cikin mamaki ya nufo sassan Hanan din. Da gaske suna falon suna ta hira abinsu. Da alama sun ci abinci tare,
don ba a kai ga kwashe kwanukan abincin da ke wurin ba. Zuciyarshi ta yi dadi, don bai tsammaci hakan daga
Mairon ba. Ya rausayar da kai yana kallonsu bai ce musu komi ba.
Hanan ce ta yi mishi sannu da zuwa. Inda Mairo ta maida hankali ga hada mishi abinci. Ya kama hannunta ya
rike yana yi mata wani irin kallo da ya sanya Hanan barin falon, kishi na cinta, amma sai ta ke tambayar kanta,
‘Ni me ya kai ni shigowa gidan mutum da matarshi, alhalin ba rasa masoya na yi ba?’
Amsar ita ce, ‘Amirun shi ne mijin da Allah Ya rubuta mata, koma dai yaya ne, da sanya hannun Hajiya a ciki.
Don tun sanda ta ba ta kwallin nan da ta saka ta samu kanta dumu-dumu da soyayyar Amiru, wanda a da ta yi
alkawarin ba zata auri mai mata ba, sai yaro dan uwanta.
Har kwanaki bakwai da addini ya bai wa Hanan suka cika, Amiru bai san hanyar dakinta ba. Don gani yake
idan ya yi hakan ya ci amanar Maironshi, wannan yarinyar ta raina shi, sannan ba zai iya hada jiki da wata diya
mace ba a tun bayan da ya auri Mairo.
Ita ce kadai ta mallaki duk wasu abubuwa da yake so a diya mace ta kasance tana da su, amma ba wannan
mai kama da kazar fingi-fingin ba.
Sannan kallon Hanan yake kamar su Amina. Idan har zai iya hada jiki da ita, ashe kuwa zai iya hadawa da
Rayyah. Kafin a yi auren kam, fitinanniyar sha’awarta ce ta sanya ya aure ta, sai ga shi bayan auren duk wasu
‘feelings’ da yake ji a ransa game da Hanan din ‘including’ sha’awar, ya neme su ya rasa.
Ita Mairo ba ta san cewa ba a dakin Hanan din ya ke kwana ba, sai yau da girki ya zagayo kanta. Tun safe ya
kasa fita, sai zarya yake mata a kicin tana aikin hada abinci yana bi yana nanikarta da sunsunarta, jikinsa na
masifar rawa kamar yau aka kawo mishi ita.
A can dakin Hanan kuwa kayanta ta ke hadawa tana kuka. Ta dauko akwati ta koma sassan Hajiya, ta sa mata
kuka ta ce ita gida za ta tafi, ba zata iya jurar wannan wulakancin ba.
Ran Hajiya ya yi masifar baci, me hakan ke nufi? Mairo da Habibu suna nufin cewa, duk kudin da ta kashe ta
kulla auren Hanan da danta don cikar burinta, sun tashi a banza? Ta damu Hanan da tambayar abin da Mairo
ta ke yi mata, ta ce.
“Ni bata yi min komai ba, lafiya nake zaune da ita. Shi din ne dai bai taba shiga dakina ba.
Bai taba yi min magana ba, kuma ko gaishe shi na yi ba ya daga ido ya dube ni. Gaskiya Hajiya bazan juri
wannan wulakancin ba, da kuruciyata da komi”.
Hajiya ta ba ta hakuri, ta ce ta zauna nan sai ya shigo zata yi mishi fada, sannan za ta dauki mataki akai.
Don haka ko da ya shigo da safe gaida Hajiya, ba ta amsa ba. Ya sha mamakin ganin Hanan ta fito daga dakin
su Rayyah, don shi kwata-kwata ma bai san ba a cikin gidan ta kwana ba. Ko kallonshi ba ta yi ba ta yi abin da
ya fito da ita ta koma daki. Hajiya ta dube shi sosai, ta ce.
“Na dauka ko wani ne ka gani zai wulakanta Hanan sai inda karfinka ya kare, balle kai kanka. Me ye dalilin da
ya sanya ba ka shiga dakinta?”
Cikin takaici ya ce da ita.
“Au karata ta kawo?”
Hajiya ta kulu sosai, ta ce.
“Ta kawo din, sai ta zauna kuna cutarta kai da matarka ko?”
Ya yi shiru bai tanka ba, can kuma ya ce.
“A gaskiya Hajiya ki yi mana adalci ni da Hanan. Ki bar kowa ya zauna da wanda yake so. Hanan ba sona ta ke
yi ba, don ba tasan ma hakikanin mene ne son ba. Sannan ni kaina na aure ta ne ba bisa hayyacina ba. A
yanzu da na dawo cikin hankalina ba zan iya rayuwar aure da ita ba”.
Hajiya ta rasa abin da zata ce don takaici. Ya sake kaskantar da murya, ya ce.
“Maimakon na dinga daukar hakkinta Hajiya, na gwammace a samu maslaha ta fahimta a tsakaninmu. Don
haka na saki Hanan saki biyu, idan ta samu miji ta yi aure. Ni kuma zan yi mata duk abin da dan uwa na ciki
daya zai yi wa kanwarshi. Dama kuma babu iddata a kanta”.
Hajiya Aisha sai ta sa kuka, tana cewa.
“Tsakanina da Habibu da kanwarshi sai Allah Ya isa, ban ga laifinka ba, kuma bazan yi fushi da kai ba, tunda ba
cikin hankalinka ka ke ba, ba yin kanka ba ne.
Sai dai kuma yadda ka saki Hanan haka nake son ka saki Mairo yanzun nan ba sai anjima ba, ko kuma na tsine
maka duniya da lahira wallahi”.
Da ya san abin da hukuncinsa zai janyo kenan, ko kusa da bai fara ba. Wani irin zazzafan gumi (zufa) ya soma
bubbugowa daga kowane sashe na jikinsa. Jikinsa ya soma wani irin rawa, labbanshi suka soma karkarwa,
hankoranshi suka soma karo da juna kaf-kaf-kaf kamar wanda aka fiddo daga cikin kankara
Ta dauko biro da takarda ta dora mishi akan cinyarshi. Ya manta yadda ake sarrafa alkalami, har ya bada
kalma, kalma ta bada jumla balle ya rubuta mata abin da ta bukatan. Ta daka mishi tsawa mai firgitarwa, ta
ce.
“Zaka bi umarnina ko ka zabi Mairo a kaina?”
Cikin sarkewar harshe ya ce.
“Na zabe ki Hajiya,……. wallahi na zabe ki”.
Ta ce
“To rubuta ka ba ni”.
Yatsun hannunshi suna karkarwa ya rubuta abin da bai san me ya rubuta ba. Ya mika mata, ta duba ta
tabbatar ya rubuta din, sai dai ita kanta ta kasa karanta wannan cakudadden rubutun. Ya mike ba tare da
yana ganin abin da ke gabanshi ba, har ya tarar da kofar dakin Mairo.
Durkushe ta ke a tsakiyar dakinta tana kelayo wani irin koren amai fatau kamar zata amayar da ‘ya’yan
hanjinta. Ya isa gare ta da gudu ya tallafe ta. Ta kuwa sake kelayo mishi wani koren aman a farar sassalkar
shaddarshi. Wannan bai dame shi ba kamar mugun zafin da ya ji jikinta ya dauka, kamar an jefata a wuta.
Babu bata lokaci ya sunkuceta ya yi mota da ita. Bai shimfideta a ko’ina ba sai a ofishin Dr. Fredrick, ko nurses
da suka so su taimaka masa wajen daukarta a keken tura marassa lafiya, bai karbi taimakon nasu ba.
Dr. Fredrick ya dora mata ‘drip’ sannan ya shiga bincike a kanta. Zuwa can kuma ya ba ta umarnin da ta yi
mishi fitsari a roba. Bada jimawa ba sakamako ya fito na karamin ciki dan watanni biyu da ‘yan kwanaki. Ya
rasa a halin da ya tsinci kansa ciki, farin ciki zai yi? Ko kuwa hannu zai dora aka ya rusa ihu? Ba shi da sauran
buri a rayuwa, tunda ya rasa Mairo, Hajiya ta raba shi da farin cikin rayuwarshi ta hanyar da baisan ya zaiyi ya
fassara ba.
Ga shi kuma shi kansa bai san abin da ya rubuta ba, don haka bai samu kanshi da yin murna da abin da ake
neman samuwarshi shekara da shekaru ba, wanda kuma rashinshi ne silar duk kasancewarshi cikin halin da
yake ciki a halin yanzu, dama wanda ya gabata.
Ina amfanin ‘ya’yan ba tare da uwarsu ba? Ba dan Mairo yake so ba, ita Mairon yake so kanta, ba abin da za
ta haifa ba. Da ba Hajiya ce ta haife shi ba, cewa zai yi ba ta kaunarsa…….
A tsaye yake jingine da garu, ya harde hannayenshi a bayanshi. Idanun shi a rufe. Numfashi ya soma yi mishi
wuyar shaka. Idan ya tuno shi da Mairo shi ke nan? Yanzu ta zama haramiyarshi? Ga albarkar haihuwa Allah
ya kawo, sai hawayen su sake shatata.
Kafin Dr. Fredrick ya dago daga kan Mairo, Amiru ya sulale a tsakar ofishinsa, babu alamun numfashi ko
kankani a tare da shi. Ya danna wani abu akan tebur dinsa, likitoci biyu da ma’aikatan jinya suka bayyana a
ofishin cikin sauri. Suka kwashe shi suka aza bisa gado, kasancewar akwai ‘file’ dinshi tare da su suka shiga
kokari don ceto numfashinsa.
Dr. Fredrick ya dauki waya cikin aljihunshi ya kira Alh. Abdurrahman. Ko kafin ya iso the condition has become
worst! Ya gamu da abin da suka kira ‘heart stroke’, zuciyarshi sauran kiris ta buga, don haka yana isowa ya
nemi da su hada mishi ‘report’ din komai zai fitar da shi New York.
Duk inda hankalin Daddy ya ke idan ya yi dubu to ya tashi. Bai nemi kowa da zancen ba, sai da ya kammala
shirye-shiryensa sannan ya nemi Habibu a waya ya sanar da shi asibitin da suke a New York.
Don haka a washegari Habibun ya yi shiri shi ma ya bi su, ya bar Dina cikin damuwa mai yawa. Hankalinshi ya
yi matukar tashi da ganin halin da aminin nashi ke ciki, bai san inda kansa yake ba, baya shaida kowa, yana
cikin injina rankatakaf, kafafunshi ne kawai ba a sanya cikin inji ba.
Kwanan Mairo biyu a asibitinsu Dr. Fredrick yana sanya mata karin ruwa sannan ya sallame ta. Babu waya
tare da ita don haka shi Dr. ya kira Hajiya ya ke sanar da ita a zo a tafi da Mairo ta ji sauki. Hajiya ta ce
“Ina Amirun?”
Dr. ya tuna umarnin da Alh. Abdurrahman ya ba shi, na cewa kada ya sake ya sanar da kowa dan shi ba shi da
lafiya ko ya tafi da shi wani wuri. Don haka ya ce da ita yana tare da Alhaji tunda ya kawo ta bai dawo ba.
Hajiya ta ce, ya ce da Mairon ta jirata ga ta nan zuwa.
Mintuna ashirin suka shude, Mairo ta yi zugum cikin tunanin halin da mijinta ke ciki, tun faduwar da ya yi
akan idonta ba ta kara ganin shi ba, tun sanda likitoci suka yi waje da shi. Ta soma yi mishi addu’a cikin ranta
cewa koma mene ne sanadin ciwonshi to ya kasance mai sauki ne.
Dr. Fredrick bai kara fada mata wani abu akan Amiru ba, baya ga cewa ba shi da lafiya. Hajiya ta banko kofar
dakin ta shigo, babu ko sallama, dai-dai lokacin da Dr. Fred ya sawo kai zai shigo. Ta dauko takarda cikin
jakarta ta dora mata akan cinyarta. Ta ce.
“Yadda kika sa Amiru ya saki Hanan, to kema ga naki tikitin nan. Amiru ya sake ki! Ki fadawa Habibu idan a
tafe yake, ni a can na kwan!! Kada ki sake na kara ganin farar kafarki a gidana, duk wata allurarki da ke cikin
gidan na aunata cikin akori-kura, an kai muku tsiyarku, matsiyatan banza. Hanan na zabawa Amiru, matsayin
matar aure, kuma da ita zai zauna don haka sai ki san inda dare ya yi miki ba dai GIDAN AMIRU BA!”
Ta juya ta fita, daga Mairo har Dr. Fredrick suka bi ta da kallo cike da wasu-wasin anya lafiyarta? Don kwatakwata basu fahimci kan zancenta ba, balle shi da ba ya jin harshen Hausa. Mairo ta dawo da idanunta akan
takardar da Hajiya ta aje mata bisa cinyarta.
“Na saki matata Maryam saki daya… ba da son raina ba… ..” Sa hannun
Amiru Abdurrahman Gaya.
“Daga Allah muke! Kuma gare Shi za mu koma!!”
Abinda Mairo ta fada ke nan a fili da boye, kafin wasu irin dunkulallun hawaye su mirgino a kundukukinta.
‘Ya’yan hanjinta suka dunkule waje daya, cikinta ya murda jini ya kece kamar da bakin kwarya. Ta yi baya
luuu…! Ta fadi akan dandaryar kasa, ba ta kara banbance abin da ke faruwa cikin duniyar ba.
***
Dr.Fredrick, Dr. Ma’u, da sauran likitoci ne tsaye a kanta, a lokacin da ta farfado, kowanne yana aikinsa cikin
kwarewa da sanin makamar aiki. Ga ledojin jini da na ruwa duka ana kara mata. A lokacin ne abin da ta
karanta cikin takardar ya soma dawowa cikin kwakwalwarta.
Da gaske ne Amiru ya sake ta! Wannan sa-hannun nashi ne ba na kowa ba.
Wasu dumammun hawaye suka soma fito daga idanunta, Dr. Fred ya soma ba ta baki, yana cewa ta yi hakuri,
ta dauki komai ya faru da ita da sauki idan har tana son dan cikinta ya zauna, wanda ke gab da ficewa. Ya kara
da cewa ta ba shi wata lamba ya kirawo mata wani, duk da bai san me Hajiya ta fada mata ba, ya lura ba abin
arziki ba ne.
Tana kuka ta ce, ita kawai ya kai ta gidan Yayanta. Ya ce, ba zai sallame ta ba, sai cikin jikinta ya zauna sosai,
don haka ta ba shi lambar Dina.
Karfe hudu na yammacin ranar Dina ta iso tare da babban danta Muhammad, hankalinta a masifar tashe.
Mairo tana ganinta ta fada jikinta ta fashe da kukan da ke cin ranta, Dina ma kuka ta ke tana fyacewa, don
yanzu suka yi waya da Habibu, yana kuka riris kamar ba namiji ba, ya ke fada mata rayuwar Amiru sai wani
babban ikon Allah.
Sai ta dauka kukan da Mairo ke yi kenan, wadda ita bata san abin da ke faruwa da Amirun ba.
Ta ce
“Ki yi hakuri, ki kwantar da hankalinki Mairo, da yardar Ubangiji, Allah zai ba shi lafiya”.
Mairo ta saki Dina, hawaye ba su bar gudu a kundukukinta ba. Ta dauko takarda karkashin filonta ta ba ta.
Cike da mamaki Dina ta warware takardar ta karanta, sannan ta ninke, Allah kadai Ya san halin da ta tsinci
zuciyarta a ciki.
Tsayin mintuna goma ba ta ce komi ba. Ta yi tagumi, ta zubawa Mairo ido. At last! Akalla Hajiya ce da nasara
ba su ba! Idanunta jawur ta ce.
“Ki kwantar da hankalinki Mairo, wannan ba shi ne karshen rayuwar ba”.
Ta mike ta nufi ofishin Dr. Fredrick suka tattauna akan matsalar Mairo. A nan ne ma Dinan ta ji ciki gare ta. Ta
ce.
“Ikon Allah! Ga samu, ga rashi!!”
Dina ta fada a fili, wani kududun bakin ciki na tokare mata a zuciya.
Dr. ya ce, ta lallaba Mairo idan har ta kwantar da hankalinta ko gobe sai ya sallame ta.
Dina ta dinga jinjina al’amarin a zuciyarta. Tausayin Mairo da Amiru ya ishe ta. Ba ta ga laifinshi ba ko daya, ta
tabbata silar shigarshi cikin halin da yake ciki ke nan. Tana tausayin Mairo, kasancewar abin da ya fi muni ga
diya mace (zawarci) ya same ta a ‘yan kananan shekarunta da ba su kai ga cika talatin ba.
Da asubahin ranar juma’a Amiru ya bude ido ya ganshi rungume a kirjin mahaifinsa da amininshi Habibu a
gefe, yana mai furta Alhamdulillahillazi Ahyana….baada ma amatana wa ilaihinnushour…..”. Ya sake maida
idonshi ya lumshe. Kalmomin dake fita daga bakinshi a wannan lokacin cikin gushewar hayyaci sune ;
“Habibu ka yafe mini……. Na sake yi maka gagarumin laifi ba da son raina ba……..!!!”
Sannan ya dubi Alh. Abdurrahman hawayenshi na zirara, yace “Daddy ka taya ni bashi hakuri, abotata da shi
bata kare shi da komai ba, sai tarin tozarci da kaskanci a gareshi, alhalin shi ya kasance aboki nagari, wanda
babu kamsrsa a wannan zamanin, mai yawan uzri da sadaukarwa a gareni, wannan karon na mishi laifi mai
girma Daddy…..”.
Kallon tambaya Daddy yabi Habibu dashi, don son jin laifin me Amirun yayi masa? To shi kansa Habibun ya
shiga rudu, bai sani ba. Don haka ya sunkuyar da kanshi kasa. Kuka riris Amiru yake yi. Likitocinsa suka rufu a
kansa suna gwaje-gwajen daya dace. Suka tabbatar ayyukansu sunyi kyau lafiya ta soma samuwa. Bacin rai ne
kawai yayi masa yawa.
Saidai fa ga dukkan alamu patient din nasu na son maido musu da aiki baya, sabida yadda ya kuntata
zuciyarshi. Suka shiga bashi shawarwari masu amfani ga lafiyar shi. Wadanda idan ya bisu zai tserar da
rayuwarshi. Ciwon zuciya in ya riga ya sameka ya same ka kenan kai zaka cigaba da kula da kanka. Lafiyarka
tana hannunka su taimako kawai suke yi. Bayanin da likitocin ke masa kenan cikin tattausan lafazi, amma ta
inda suka shiga, ta nan suke fita ba sauraron su yake ba.
Habibu ya kira Dina. Zuciyarshi ta bushe rayas kamar soyayyiyar gyada marau-marau. In banda wani irin suya
da zogi, ba abin da ta ke yi. Sabida damuwar halin da aminin nashi ke ciki.
Ya sanar da ita ciwon Amiru na baya ne ya tashi suna tare dashi a New York. Don haka tashin hankali kan
tashin hankali wajen Dina yau ba’a magana. A take zazzabi ya rufeta amma bata gayawa Mairon ba.
Bayan sati biyu aka dawo da Amiru gida, ba don ya warke ba sai bisa tursasawarshi, bayan ya karbi taimako
na kwararru daga likitocinsa. Ya dage lallai a maida shi gida, zai iya jinyar kansa. Ya amince abinda ya faru da
shi, kaddara ce daga Allah!
A babban masallacin Abuja suka yi sallar juma’a shida Habib da Alh. Abdurrahman Gaya, amma shi a zaune
yayi sabida rashin karfin jikinsa. Tareda dubban al’umma daga cikin Abuja da wajenta, ciki har da Alh. Abbas,
wanda Habibu ya yankarwa tikitin jirgi ya zo, musamman don kawai yaga lafiyar Amirun. Shi Amiru kunya
bata bari ya iya hada ido da Baffan ba, duk Alh. Abdurrahman na hankalce da shi. Ya lura Amiru kunyar
Habibu da Alh. Abbas yake ji. Ko ido baya iya hadawa dasu. Baya hira dasu. Ga dukkan alamu sukuma basu
san dalili ba. Sababbin halayensa garesu sun jefa su rudani.
Hajiya Aisha ta idar da sallar azahar ke nan su Daddy suka shigo da Amiru a rirrike. Yana tsakanin kafadunsu.
Suka kwantar dashi a doguwar kujera. Ta dubi mijinta, sannan ta dubi Habibu ta maida idonta ga Amirun dake
kwance, ta tabbatar Amirun ta ne yayi wannan lalacewar cikin dan lokacin kalilan. Ta yi neman duniya ta rasa
shi tun ranar data tursasashi sakin Mairo. Bata san tare sukeda Daddy ba don tasan Daddy yayi tafiya. Sai a
lokacin Daddy ya gaya mata cewa a binciken likitoci ciwon zuciyar Amiru bai rabu dashi ba, a wancan lokacin
kwanciya yayi sabida samun kwanciyar hankali, a yanzu yazo matakin da dole a guji daga masa hankali, yana
so yasan neye matsalar Amiru daga ita da Habibu tunda Amiru ya ki gaya masa? Sannan ina Mairo?
Maimakon ta bashi amsa sai ta dora hannuwanta duka biyu aka tana kuka, ta ce.
“Kaicona, ni Aisha! Na cuci kaina!!”
Duk yadda Daddy ke lallashinta kan ta nutsu tayi masa bayani ciwo ba mutuwa bane amma ta ki, sai kuka ta
ke tana fadin ta cuci kanta. Wannan ya su su fitar da Amirun daga gidan zuwa nashi gidan. Anan Daddy da
Habibu suka ga wayam, babu Mairo babu ko allurar ta. Cikin tashin hankali Daddy ya dubi Amiru, yace
“ina Maryama?”
Ya sunkuyar da kai wani dunkulallen abu mai kama da sasari na daure kirjinsa yace “NA SAKETA Daddy!”
“What?????”
Inji Abdurrahman Gaya.
***.
Ita dai Mairo tunda tazo gidan, Yaya Habibu ya dawo daga tafiyar da yayi, tana ganinsa yana shigowa gidan
yana fita baya magana, ita ma Dinan ba ta magana, wanda ya haifarwa da su Muhammad rashin walwala,
koda yake su rabin rayuwarsu duk a makaranta suke yinta safe da yamma. Ta tabbatar bakin cikin sakin
aurenta da Amiru yayi ya taba zuciyar Yaya Habibu fiye da tunanin mai tunani. Fiyeda kintacen mai kintace.
To ita ma ai ta damu, damuwa irin wacce bazata fassaru ba, amma damuwar Yaya Habibu da Dina, tana bata
mamaki. Tana tsorata ta. Domin ta wuce hankali.
Ba tare da shawara da ita ba, Habibu ya soma yi mata shirin tafiya Malaysia gidan su Dina. A cewarshi ya
samar mata jami’ar Kuala-Lampur (inda yayi), idan ta haihu a can zata yi PhD dinta.
Ko kadan ranta ba ya son wannan tafiyar. Bata son gusawa daga kusa dasu. Su kadai take gani taji sanyi a
xuciyarta, ta ji tanada sauran masu son ta a duniya. Iyalin Abdurrahman Gaya sun sa ta a zargin kanta da
kanta da halayenta bayan rashin haihuwa. Rashin haihuwa kadai bazai sa ayi mata nnan tozarcin ba, saidai in
halayenta ma ababen kyama ne. Ta rasa dalilin da yasa ita ma ba ta jin dadin ranta, kewar mijinta da
soyayyarsa sun shafe duk wani burin da ta ciwa rayuwarta, gaba daya karatun ma ta tsaneshi. Me zata yi da
kwalayen babu Amiru mai nuna soyayya, kauna da karfafawa?
Duk da haka ba ta yi mishi musu ba, kada ya ce ta faya kulaficin mijin da ya riga ya sake ta, ko ta zauna zaman
jiran ya maida ita. Don haka ta bi umarnin shi ba tare da musu ko nuna bacin rai ba.
Habibu da Dina ne suka kai ta airport ta bi jirgin ‘MEA International’ zuwa ‘Kuala-Lampur’.
Baban Dina da kanshi da Hajiyarta suka zo suka dauketa a filin jirgi. Su Hafsat duk an yi musu aure a garuruwa
daban-daban, don haka babu kowa gaban Hajiya da Daddyn Dina.
Irin yadda Daddyn da Hajiyar ke tausayinta, sai ta ji ita ma tana tausayin kanta. Idan haka dacin mutuwar aure
yake, to ba ta fatan shi koda akan makiyarta.
Irin kulawar da Hajiyar Dina take bata ko Innarta iyakarta ke nan. Tana ganin likita akai-akai, (awo) domin
kulawa da lafiyarta da ta abin da ke cikinta.
A yau Daddy ya yi musu sallama zai wuce gida Najeriya. Hajiyar Dutsinma babu lafiya. Ashe zai je ne duba
Amiru a Abuja. Wanda ciwonshi ya kara tashi kamar bazai kai labari ba. Hajiyar Dina ta yi mishi rakiya har
bakin mota. Mairo daga saman bene inda dakinta ya ke ta bude taga tana hango su suna magana fuskokinsu
babu annuri. Kanta ya yi masifar daurewa, kada dai Hajiyar Dutsinma mutuwa ta yi shi ne Daddy zai tafi
Nigeria?
Don haka bayan fitarshi ta samu Hajiya a daki, wadda ta yi tagumi da dukkan hannuwanta biyu a bakin
gadonta. Yanayin Mairo take nazari a ‘yan kwanakin nan. Magana take ita kadai inta shiga daki. Ba dama ta
kadaice sai taji tashin sunan A.A a bakinta ko bacci take yi. Ta yanke shawarar fadawa Mairo halinda Amiru ke
ciki don ta dinga yi masa addu’a, amma ba don wani abu ba.
Mairo ta yi sallama cikin dakin, sanye da doguwar riga mai hade da hula samfurin Oman, ta zauna a gaban
Hajiyar Dina, cike da damuwa ta ce.
“Don Allah Hajiya me ya faru da Hajiyar Dutsinma ne?”
Hajiya ta ce, “Ciwon suga ke damunta, don haka Daddy zai taho da ita idan zai komo don ta samu kulawa
sosai daga kwararrun likitoci”.
Sai yanzu ne hankalinta ya kwanta da ta tabbatar Hajiyar ba mutuwa ta yi ba. Amma wannan damuwar da
kowa a gidan yake ciki tana damun ta, don ya wuce ace akan mutuwar aurenta ne kadai.
Hajiya ta dubi Mairo cikin tausayi, ta ce.
“Maryam ina so ki ba ni hankalinki, tunaninki da nutsuwarki. Nasan saki a zuciyar diya mace ba abu ne mai
sauki ba. Nasan zafin sa nasan radadin sa. Ki dauki abin da za ki ji daga bakina ba wani abu daban ba; so nake
ki yafewa Amiru duk wani kullacinsa dake ranki da zuciya daya ba tareda shi din ya sani ba, ki taya kowa
addu’ar nema masa lafiya”.
Shiru Mairo tayi, kamar ruwa ya cinye ta. Anya tabon da Amiru ya ji mata a zuci abinda zata iya yafewa ne???
Hajiya ta ce
“Amiru ya kamu da ciwon zuciya a bisa tafarkin soyayyarki. Irin ciwon da yayi kafin ya same ki, shi ya dawo
mishi a lokacin da ya rasa ki. Wato bacin rai da tashin hankalin da ya samu kanshi a ciki, a dalilin ya sake ki.
Wannan abin alfaharinki ne Mairo, mijinki na son ki, soyaya irin wadda babu a wannan karnin, kaddara ce ta
raba ku,, yana mai yarda da ke, da sa miki albarka. Na fada miki ba don komi ba, sai don ki dubi Allah ki yafe
masa, ki dinga yi mishi addu’ar samun sauki, albarkacin soyayyar sa gareki…….”.
Hajiya magana ta ke, a sanda ta lura Mairo ba ta jinta. Tun sanda ta ambaci kalmar ciwon zuciyar Ameeru ya
dawo….’ ba ta kara fahimtar abin da ke fita daga bakinta ba. Damuwoyin sun yiwa zuciya da kwakwalwar ta
yawa. Ji tayi kamar Hajiya tace Amiru ya rasu…Ji ta ke kamar ana mata ihu a cikin kwakwalwarta. Can anjima
kuma taji kamar ana gudun famfalaki a cikin kanta. Hajiya ta ga idanuwan Mairo sun birkice. Tamkar ba’a jikin
ta suke ba.
Ba karamin tsorata ta yi ba, ta soma nadamar karambaninta. Kawai sai taji Mairo ta soma yi mata sambatu.
Sambatu iri-iri.
“Don yayi aure sai ya sake ni? Nayi duk iya kokarina don ya samu kwanciyar hankali a auren da yake so yayi,
na bashi dukkan go ahead, na bashi amana da soyayya ta, na sakankance we’re to live for life! Na san Hajiya
ta daina so na tunda banna haihuwa amma ai na yarda ta aura masa mai haihuwa meyasa bazata barmu tare
ba?”
Can kuma ta kara duban Hajiya, ta ce.
“Ai Hanan din tana da kirki, ni bazan cuce ta ba! Hajiya ki mayar dani in ba ni na yi jinyar sa ba bazai mike
ba!!!”
Ta mike da sauri tayi hanyar kofa.
Hajiya sai ta sa kuka ta kamota ta rungume ta, tana tofa mata duk addu’ar da ta zo bakinta. A wannan gabar,,
tana gujewa Mairo haduwa da psychological problem kowanne iri, wanda damuwa ke yin sanadin sa.
A daren ta yi asibiti da ita, aka soma ba ta treatment din da ya dace.
Ko da Daddy ya dawo tare da Hajiyar Dutsinma a can asibitin suka isko su, sun ba ta gado sun ce za su yi
‘treating’ dinta tsayin sati biyu. In banda surutai ba abin da ta ke kwana tana yi, duk akan Amiru da
damuwarta kan halin da yake ciki, sosai Daddyn Dina ya yiwa Hajiya fada kan abinda tayi. Wani zubin kuma
sai ta sa kuka, tayi-ta-yi ba kakkautawa. Likita yana zuwa har gida yana duba Hajiyar Dutsinma don bata yarda
tazo asibiti cikin sati biyu ta warware.
Daddy Ya yiwa Habibu waya ya sanar da shi halin da Mairo ke ciki. Bayan kwanaki biyu ya iso. Tana ganinshi ta
fizgo daga gado ta rungume shi tana hararar Hajiya, ta ce.
“Ba ga shi ba Amirun kika ce ya mutu! Allah Ya isa tsakanina da ke!!” Sai ta sa kuka.
Ma’aikatan jinyar asibitin suka zo suka yi mata allura, nan da nan ta kama barci. Habibu ya yi ajiyar zuciya ya
dubi Daddy. Suka zauna a kujeru masu fuskantar Mairon suna kallonta cikin tausayi. Habibu ya kebe da
babban likita ya kara yi mishi bayanin komi.
Ya ce kada su damu, bacin rai ne da damuwa kawai ya hargitsa ta, amma da ta kare shan maganin da suka
dorata a kai zata dawo dai-dai insha Allahu.
***
Tsayin watanni biyu Alh. Abdurrahman na jinyar tilon dansa, ya na kwantar masa da hankali ta hanyar bashi
misalai da al’amuran rayuwa kala-kala. Don ya yaye wa kanshi damuwar daya sanyawa zuciyar shi. Yana kuma
karantar abubuwanda ke faruwa a cikin gidanshi musamman Hajiya A’isha daya digawa gundumemiyar ayar
tambaya. Sabida yadda ta fita hayyacinta da rashin lafiyar Amiru, sai surutai take mai tonawa kai asiri, wani
zubin ta hada da su Nina tace su suka angizata, ta zazzagesu tayi musu mugun kalami tana cewa sun cuce ta.
Bai tambayeta komai ba, kuma bai tambayi Amiru mai yasa ya saki Mairo ba. Wanda rayuwar sa ke hannun
Allah. Dr. Fred yana zuwa gida akai-akai yana kula dashi. Ya ki yarda a maida shi New-York. Yace da Daddy in
ma mutuwarce, to yafi so ta dauke shi a dakin da yayi rayuwa da Mairo.
A yau Ambasadan Malaysia yazo ganin sa, ta dalilin Habibu da Amiru Daddyn Dina da Alhaji Abdurrahman
suka kulla abota. Alh. Abdurrahman yayi masa kyakkyawar tarba, shikansa saida ya zubda hawaye ganin halin
da Amirun ke ciki. Ya koma Malaysia cike da alhini inda ya tarar da Mairo da tata sabuwar matsalar har yau ba
sauyi.
A wannan satin da surutan Hajiya suka ishi Alh. Abdurrahman, yayiwa ‘ya’yan shi mata gabadaya waya, na ciki
dana waje, yace yana so su hallara a ‘family meeting’ ranar asabar mai zuwa. Sannan ya kira Alh. Abdulwahab
Baban Hanan shima yace yana so Hanan tazo ranar asabar. Alhaji Abdulwahab wanda ke cike taf da fushin
sakin da Amiru yayiwa Hanan sati daya da aure ya gintse fuska yace
“ince ko lafiya? Bayan an riga an saketa?”
Daddy yace lafiya kalau, ‘meeting’ zasu yi tare da ita. Ya gaya mishi bai san abubuwanda suke faruwa a gidan
ba, yana so ya sani ne, inda halin gyara ayi gyara. Yace Hanan zata zo albarkacin ka, amma babu batun gyara.
Don dama Hanan tana da mai sonta tuni, mutunci da ‘yan uwantaka aka diba aka bawa Amiru. Tunda kuma
yace baiyi, to Allah ya hada kowa da rabonsa na ALHERI.
Jikin Daddy a masifar sanyaye, da mamakin wai itama Hanan an saketa. To shi yana ina aka yi duk wannan
kazamin aiki? Lallai Hajiya ta bashi mamaki. Ya kuma soma zargin koma menene itace ummul-haba’isi, haka
kawai za’a kashe masa Da a banza.
Habibu bai bar jinyar Amiru ba, duk da tabbacinsa na sakin Mairo da yayi. Duk da zafin hakan dake ranshi.
Duk wai wata kusan tafi wata kusan. A wurinshi ba Mairo ce ta hada shi da Amiru ba balle ta zamo silar
rabuwarsu. Allah ne ya hada su, ya sanya kaunar juna da soyayya a tsakaninsu, ba kuma zasu rabu a dalilin ta
ba. Ko ba komai Amiru ya wanke mishi zuciya da baiyi mummunan saki ba wanda Allah baya so. Yayi kokari ya
karanta hargitsatstsen rubutun ya ga saki daya ne. Kullum kafin ya fita ofis zai zo, haka in ya tashi yana nan
tare dashi har goman dare.
Amiru yana shaida kowa, amma baya magana. Sai bin kowa da ido. A ganin shi rayuwar bata cancanci a
cigaba da itaba, ba tare da abinda zuciya da gangar jiki ke so ba. In za’a bashi zabi gara mutuwa da rayuwa
babu Mairo.
Kasancewar Daddy da Habibu na kula da shan magungunan sa akan lokaci, ya sanya kullum sauki na kara
samuwa.
Daddy ya shigo falon da ‘ya’yan sa, Hajiya da Hanan ke zaune, kowanne kai a kasa. Jiki yayi la’asar babu laka.
Ita kanta Hanan ta tsorata da ganin yadda Amiru ya koma cikin dan lokaci kalilan. Sau daya ta shiga part
dinshi, tausayi bai barta ta kara komawa ba. Ko babu soyayya Amiru dan uwanta ne wanda take ji har cikin
kashi da bTa kuma alkawartawa ranta fadiwa Daddy gaskiyar duk abinda ya tambayeta ba tareda shayin
Hajiya ba, don Yaya Amiru ya samu lafiya, ya samu abinda yake so, ita tayi hakuri, ta auri Ramadan wanda ke
son ta kamar ya kashe kan shi.
Amina kadai ake jira a falon wadda bata karaso daga Switzerland ba har yanzu. Don haka ganin ana batawa
‘majority’ lokaci, akan mutum daya, Daddy ya yanke hukuncin ayi taron bada ita ba.
Ya bude taron da cewa kowa yayiwa Annabi salati goma. Ya ja doguwar addu’a suka shafa. Yasa gilashi ya
soma duban ‘ya’yanshi mata su goma sha daya da fuska mara walwala. Ya maida dubanshi ga Hajiya A’isha
yace
“Hajiya, keda Hanan kune a gidannan sanda abin ya faru, don haka ku zan fara tambaya. Yaya aka yi Amir ya
saki matansa biyu duk a lokacin daya?”
Hajiya tayi shiru, ta soma share ido da gefen mayafinta, abinda ya riga ya zame mata jiki tun ranar da aka
dawo da Amiru wai yana fama da ciwon zuciyar data yi tsammanin yayi hannun riga da shi. Tararradinta shine
idan ta rasa Amiru ina zata tsoma ranta? Mutumin da ke yi mata biyayyar da duk cikin ‘ya’yan ta babu mai yi
mata kwatankwacinta?
Mutumin da ya sadaukar da farin-cikinshi akanta. Bama wannan ba, ina zata kai hakkin Mairon da bata ci
mata ba, bata sha mata ba, biyayya take yi mata tamkar tayi mata sujjada, kawai don Allah As-samadu bai
bata haihuwar da bata isa ta baiwa kanta ba? Ta tabbatar ba komai ya kai ta yin umarnin data yi ba, bacin ran
sakin da yayiwa Hanan ne. Wadda ita bata damu ba, kamar dama jira take, yana sakinta ta hada ya-nata-yanata tayi tafiyar ta, babu ko cikakkiyar sallama. Sai yau ta ganta cikin taron da bata zata ba.
Amma ko waya Hanan bata kara yi mata ba. Gatanan da ranta da lafiyar ta ba abinda ya dameta. Sai nata dan
data jefa cikin halin ha’u’la’i. zaiyi-ba zaiyi- ba Allah masani.
Ta dubi Nina, kamar ta tsinka mata mari, domin dai ita ta kaita ga abinda bata taba tsammanin yi a rayuwarta
ba. Wato bin malaman tsafi Yarbawan Lagos, haka-kawai zasu fidda ita a imanin ta. Kukanta ya tsananta ta
kasa baiwa Daddy amsa.
Don haka ya juya akalar tambayarsa ga Hanan. Ta sunkuyar da kai ta soma fada masa duk abinda ya faru, tun
ranar da Hajiya ta aika ta zo, abubuwanda ta rinka bata wai tayiwa Amiru amfani dasu, har zuwa ranar daya
saketa, da tirkeshi data yi ya saki Mairo. Daddy ya jinjina kai cikin al’ajabi da mamaki, yaushe Hajiya ta koma
haka?
Ya ce da Hanan ya gama da ita, kuma ya gode. Kuma menene ra’ayinta kan zama da Amiru? Tana so idan
Allah Ya bashi lafiya zata dawo dakinta ne ko a’ah?
Ta sunkuyar da kai tace “ka fahimce ni Daddy. Ba wai bana son Yaya Amiru ba, amma shi wallahi-wallahi baya
so na. Matarshi kadai yake so Daddy. Kuyi kokari ku dawo mishi da abarshi cikin gaggawa in har kuna son
lafiyar shi fakat. Nikam har ga Allah na hakura, zan auri mai so na. Daman kuma babu iddarshi a kaina”.
Daddy ya sake jinjina kalamanta, yayi mata godiya ya sallameta ta fita ta koma wurin Amiru. Inda aka baro su
shida Habibu. Daddy ya dubi Hajiya cikin wani irin fushi da ‘anger’ da bata taba gani daga gareshi ba. Fuskar
shi tayi jawur abinki da bafulatani, jijiyoyin kansa sun fito rada-rada, idanunshi sun canza launi daga farare sol
zuwa jajaye. Jikinshi na tsuma, tsigar jikinshi na tashi yace
“A’isha! Hanan gaskiya ta fadi ko karya ne?”
Ta juya kai cikin tsoro da tashin hankali, nadama da yin kaico da kai, don bata taba ganin shi cikin wannan
halin ba. Tace
“batayi karya ba anyi haka. Sai dai kuskure ne da ajizanci irin na kowanne dan adam. Na tuba Alhaji na bi
Allah na bika. Sai dai komai ya faru ne da zuga da taimakon wadannan……….” Tana nuna Nina, Ni’ima da
Khalisa.
“Su suke karbo komi a Lagos wallahi ban taba zuwa ba. Don nasan zuwa wajen irin wadannan mutanen
haramun ne. Na roke ka, kada ka bari Habibu yaji wannan magana don GIRMA NA ZAI FADI A IDANUN SA don
ba iyakarta kenan ba…….”
Cikin nishi Alh. Abdurrahman yace “sai kuma me?”
Ta yarfe hawaye da majina tace
“Na sanya shi ya janye hannun jarinsa daga bankinsu shida Habibu……duk takardun dukiyar shi suna hannu
na yanzu, bari inje in dauko…”.
Tana shirin mikewa ya daga mata hannu “bayan Nina, Ni’ima da Khalisa sai kuma wa?” tace “sai mutanen
Gaya. Su suke cewa “juya” ce. Don haka ne na kulla auren shi da Hanan don ya samu ‘ya’ya kawai wallahi,
amma ba don in raba shi da matarsa ba….. kai shaida ne akan cewa tsakani da Allah ina son Mairo”.
Ya kalli Nina da Khalisa da suka yi tsuru-tsuru, jikinsu sai kyarma yake. Don sun gigice da ganin ‘tension’ din
mahaifinsu mai son su da gudun bacin ransu, tareda kyautatawa rayuwarsu tun daga yarinta har girma.
Rayyah tace “wallahi babu ruwana……” Sabah tace “wallahi babu hannu na…..” Mami tace.
“ni Daddy da ba a kasar nake ba, wallahi bani da masaniyar komai…….”.
Juyawa yayi gefensa ya fizgo wayar talbijin. Ya soma binsu yana tsula musu. Duka na tashin hankali. Da masu
ruwan, da wadanda suka ce babu ruwan su. Yana hawaye yana tafkarsu, yace
“Kun yi asara! Kun kashe auren mutumci da amana da soyayya ta gaskiya!!
Bazan yi muku baki ba. Amma kuji tsoron hakki. Kuje duniya kadai ta isheku, tunda kuma mata ne kuma aure
kuke kamar yadda Mairo ke zaman aure.
Sannan abinda kuka yiwa Mairo, kuka sa aka yi mata, zai iya faruwa da kowaccenku. Dan uwanku kuma idan
yana da hakkinku Allah zai fitar masa, muddin ya mutu bai yafe muku ba.
Kuma sai kun maimaita wannan magana agaban Habibu, sai Habibu yaji wannan maganar.
Ke kuma Hajiya ki tattara ya-naki-ya-naki ki tafi Gaya, sai na nemeki…….bana bukatar ganin ki a cikin gidana
yanzu……”. Kowa a falon kuka yake, yana rokon gafara. Basu kara tsananta kukansu ba, saida suka ji wannan
danyen hukuncin da Daddy ya zartas akan Hajiya. Suka rirrike kafafun shi suna bashi hakuri yace
“ni baku yi min komai ba. Wadanda kuka yiwa su zaku nema gafara amma ba ni ba. Sannan bazan taba sanya
baki Mairo ta dawo gidan dan uwanku ba. Tunda bakwa son ta.
Ku aura mishi duk wadda kuke so tazo ta cika muku gida da ‘ya’ya. Ko ya mutu, ko yayi rai, na barwa ALLAH!
Ku bace min da gani dabbobin banza. Hajiya ina kara gaya miki, kada in dawo in ganki cikin gida na….”.
Ya yarda wayar ya fice, yana share hawayen da suka cika mishi ido.
***
Wasa-wasa sai da Mairo ta kwashe watanni uku cur cikin wannan halin, a lokacin cikin jikinta ya fito sosai,
domin ya shiga cikin watanni na biyar.
Rannan daga ita sai Hajiyar Dutsinma a dakin, ta farka daga barci, ta kurawa silin ido, al’amuran suka soma
dawo mata tar-tar.
Ta tuna wai Amiru ya sake ta, ba tareda ta yi mishi laifin komi ba, alhalin suna tsaka da son junansu. Bayan ta
mallaka mishi duk wata soyayyarta.
Sannan ya auro Hanan, ba ta fita daga wannan bacin ran ba, ya dankara mata saki, ta tabbatar bisa
tursasawar Hajiya ne, amma Amirun ba zai taba yi mata haka akan-kanshi ba, ko giyar wake ya sha.
Tana mai sa ran bada jimawa ba za su dai-daita da mijinta ya maida ita ta zauna lafiya da Hajiya Aisha, tunda
abin da Hajiyar ta kwallafa rai, har ta tsane ta a kanshi, ga shi Allah Ya bayar.
Sai kuma ta tuno wai an fada mata ya kara kamuwa da ciwon zuciya irin wanda yayi a baya, aka samu
rayuwarshi da kyar da taimakon ta. Gashi yanzu basa tare. Kai ita ji tayi ma kamar ance ya rasu! Daga bakin
Hajiyar Dina da ba zai taba yi mata karya, ko zolaya ba.
Ta soma kuka a hankali, kukan sabo, soyayya, kauna da kewa. A tsayin zamansu na shekaru takwas, bai taba
bata mata ba, sai bisa kuskure. Soyayyar da ya wanzar da rayuwarshi a nuna mata, wani abu ne da ba zai taba
kankaruwa daga zuciyarta ba.
Tunda ya aure ta ya haramtawa kanshi sauran mata. Bai kara hada jiki da wata diya mace ba, bayan ita, har
inda yau ke motsi. Har kuwa wadda ya aura da auren sunnah. Taji wannan a bakin Hanan ba a bakinsa ba.
Duk da matakin rayuwa irin nashi, wannan bai shagaltar da shi daga rudin duniya ba.
Ta tabbata ta yi babban rashin da har abada ba zata mayar da makwafinsa ba.
Ta mika hannu ta shafi kasan mararta, inda babynshi ke kwance, yana wutsil-wutsil cikin koshin lafiya. Ta
lumshe ido a hankali, hawaye masu dumi suna zirara ta gefen idonta suna shiga cikin kunnuwanta. Ba ta
damu da ta share ba, haka zuciyarta ba ta daina kokawa ba.
A wannan halin Habibu ya tarar da ita. Ya ja kujera ya zauna yana fuskantarta. Ya ce.
“Mairo, Mairon Dina, Mairon Yaya Habibu…”
Ga mamakinshi sai ta fado jikinshi tana kuka mai tsuma zuciya. Ta ce.
“Yaya Habibu da gaske mun rasa AMEERU?”
Ya ce
“Mun rasa auren shi dai Mairo, da gaske mun rasa auren mai kaunarmu da gaskiya da amana. Amma Ameeru
yana nan a raye.
Duk wanda yace dake ya rasu, ya fada miki ne kawai don ya tayar da hankalinki. Ko kuma baki tsaya kin
saurara dai-dai ba. Amma yana gida, kwance a dakin ki. Akan gadon ki.
Kwanciyar shi ciwo da rabuwar auren ku ya barni da kewa, da katoton gibi a zuciyata. Wanda mayar da shi
wani abu ne da ba zai taba yiyuwa ba. Don haka ki dage da yi mishi addu’a. Allah ya bashi lafiya cikin
gaggawa.
To lose a friend like him, will be the GREATEST lose of all losses. To lose a husband like him, is another GREAT
loss. (rasa aboki kamar sa, ba karamar asara ba ce daga manyan asarori, kuma rasa miji kamar sa, shima
babbar asara ce.) Sai dai mu cigaba da yi mishi addu’a. Allah ya bashi lafiya.
Wannan ne kadai babbar sakayyar da zamu yi wa masoyi irinshi. Amma ba da son ranshi ya sake ki ba.
A matsayinmu na musulmi, ma’abota imani da yarda da kaddara, muna da tabbacin cewa, duk abinda ya faru
damu da sanin Allah. Shine mai sanya cuta, kuma shine mai yaye ta. Don haka muna da kyakkyawan zaton Zai
tashi kafadar Amiru, a lokacinda ya so. Ya cigaba da gudanar da al’amuran kyakkyawar rayuwarshi. Inda
rabon zaku komawa auren ku, to da yardar Allah zaku koma. Amir bai yi haka ba Mairo, sai bisa tirsasawa.
Ya kamo hannunta ya rike cikin nashi, ya ce.
“Mairo mun rasa Baba, mun rasa Inna, amma mun hakura kan ba yadda za mu yi. To haka da muka rasa auren
Amiru, zamu yi hobbasar yin tawakkali. Mu ci gaba da jure jarrabawoyin da Ubangiji ke yi mana a rayuwa, har
mu cinye jarrabawarmu.
Don haka ki yi hakuri kamar yadda na yi hakuri, iyayenshi da ‘yan uwanshi suka yi, kan halinda yake ciki. Kuma
Alhamdulillahi yana gane mutane yanzu saidai ya ki asibiti.
Hajiyar Amiru dasu Nina suna can suna ta nemanki, suna neman inda za su ganki su nemi gafarar ki sun rasa.
Ta yi nadama/sunyi nadamar abin da suka yi mana.
Yafiyarki su ke nema Mairo. Afuwata suke nema da hawayensu. Sun gurfana kan gwiwoyin su a gabana don
na yafe musu. Sannan sun samu Daddy sun bayyana mishi duk abinda suka yi mana, yayi mamaki nima nayi
mamaki, ya saba musu sosai kuma sunyi nadama ta gaskiya akan ki Mairo. Yace dasu ai ga sakayya nan sun
soma gani tun a duniya, tunda Amirun na neman rasa ransa a kanki. Wallahi Mairo tun bayan tafiyar ki ko
kofar gida Amiru bai kara takawa ba, yana gidan ki, daga dakin ki sai falon ki.
Hajiya in kin ganta a halin yanzu dole ki tausaya mata, watanta daya a Gaya ya koreta, kiris ya rage ya saketa
saida nasa baki tukunna ya hakura.
Ta ce ki yi wa Allah ki kula mata da abin da ke cikinki. Sabida na gayawa Daddy kina da ciki shikuma ya gaya
musu.
Sabida haka ki kwantar da hankalinki, don a samu daidaituwar B.P dinki, don hawan jini hatsari ne ga mai juna
biyu, kuma jininki ya hau, don haka ki taimake ni Mairo, kada kema na rasa ki………bani da Uwa, bani da Uba,
sai ke da abinda zaki haifa….”
Hawaye sharrr! Suka zubo daga idonsa.
Ta kai hannu tana share masa, ita ma nata suna zuba. Cikin rishin kuka ta ce.
“Ka daina kuka Yaya Habibu, na yi maka alkawarin zan kwantar da hankalina tunda yana raye”.
Ya ce,
“To tashi ki ci abinci, ko dan cikinki ya samu. Bai kamata ki dinga zama da yunwa ba, plzzz… Mairona!”.
Ta ce
“To ba ni in ci”.
Ya bude kular da ke gabanta, ya zuba mata faten dankalin Turawa, wanda ya ji tsokar naman kaji ya yi lugub.
Ya mika mata a faranti, ya cika tambulan da (fresh milk) mai sanyi ya mika mata. Ta karba ta soma ci sosai har
tana taune harshenta sabida yunwa.
Dina ta shigo rike da kwandon kayan abinci, suka zauna akan kilishi suna ci ita da Habibu. Mairo na kallonsu
tana raya abubuwa a ranta, wato ranar da aka kaita gidan Amiru ya takura mata sai ta ci abinci akan idonsa.
Ta kai hannu da sauri ta goge hawayen da suka kara shimfido mata, don ba ta son Yaya Habibu ya gani, ranshi
ya baci. Amma ta riga ta san kuka ta dinga yinshi kenan, har karshen rayuwarta. Tunda yanzu itada Amiru sai
dai a TUNA BAYA……Yaya zatayi da dimbin soyayyar shi data kankanewa zuciyarta????
An sallami Mairo ranar wata asabar bayan likitocinta sun tabbatar komi nata ya koma dai-dai. A lokacin
cikinta ya cika watanni shidda cif, wanda ya yi dai-dai da cikar Amiru watanni hudu yana jinya.
Suka dawo gidan su Dina, inda a washegari Habibu da Dina suka yi shirin tahowa gida Najeriya. Gidan ya rage
daga Mairon sai Hajiya da masu aiki, don Abban Dina bai cika zama ba sai a weekend, kullum yana ofis.
Bata tashi daga inda ta yi sallolin farilla guda biyar, ba tareda ta yiwa Amiru addu’ar neman lafiya daga
Ubangiji ba.
Hajiyar Dina na kula da ita yadda ya kamata, ko Innarta iyakacin kulawar da zata yi mata kenan.
Watan Hajiyar Dutsinma biyu tare da su jikinta ya yi kyau ta koma gida.
Kwanaki na mirginawa su zama watanni, har watan Aprilu ya kama, wanda shi ne EDD dinta. Sai dai Mairo ba
ta yarda anyi mata ‘scan’ ba. Ranar wata alhamis nakuda ta tashi cikin dare, haihuwa gadan-gadan. Don haka
ba da bata lokaci ba Hajiya ta tuka su da kanta suka nufi asibitin da ta ke awo, nan da nan aka karbe ta a
(labour ward), nakuda ta tsayin awanni uku cur, kan Hassan ya bullo, kamin likitocin su yi wani yunkuri, shi
ma Hussaini ya biyo dan uwansa.
Aka turota dakin hutu, Hajiya na rungume da jariran tana yi wa Allah sarkin halitta tazbihi, sabida kamar
Amiru ya yi kaki ya tofar. Sannan ‘identical twins’ irin wadanda banbacesu zai yi wuya.
Sai dai da alama Hassan kalar Babanshi ne, wato (choculate), yayin da Hussaini ya debo hasken fatar Mairo.
A take Hajiya ta yi waya ta sanar da Habibu, ya yi hamdala ya kuma nemi wayar Alh. Abdurrahman ya sanar
da shi, don haka a karshen satin suka dungumo har Hajiyar Amiru dasu Sabah suka iso Malaysia.
Farin ciki a wajen Hajiya Aisha da Alh. Abdurrahman abin ba’a cewa komi. Hajiya har da kukanta na nadama,
ga dai ‘ya’ya ba daya ba har biyu Mairo ta Haifa, duk kunyar Mairon ta isheta, ta kama ‘yan jikokin ta
rungume tana yi musu addu’a, ji take kamar Amirun ne ta rungume a ranar data haifeshi, sai dai dukkaninsu
babu mai ra’ayin a yi wani taro sai addu’a da kowa yake yi wa mahaifinsu, wanda har zuwa lokacin ke kwance
cikin halin jinya.
Yara sun ci sunan Habib da Amir, babu kuma wanda ya yarda da a sakaya. Ana kiransu da sunansu abinsu.
Bayan su Hajiya sun koma Mairo ta ci gaba da rainon ‘yan biyunta cikin koshin lafiya da taimakon (Nanny)
Bamaleshiya da Hajiya ta daukar mata.
Kamin watanni hudu sun cika sun yi kiba, sun yi bul kamar ‘yan watanni goma sabida samun kulawa da ruwan
nono isasshe. A lokacin ne kuma ‘addmission’ dinta na yin PhD ya fito a ‘university of Malaya’.
A satin da zata fara karatu, Yaya Habibu ya zo Malaysia. Yace tayi shiri suje Najeriya ta kaiwa Amiru ‘ya’yan shi
ya gansu. Don ya samu sauki har ya soma zuwa ofis. Daddy ya samo mishi aiki a CBN. Don shi Habibun bai
yarda su sake yin hadin gwiwar ba kamar yadda Daddy da Amirun suka bukata, yace saboda halin rai. Ya
kuma ce da Daddy akwai kudurin da yake dashi a kan bankin nan bada jimawa ba. Amma ba wai don yayi
fushi da abinda Hajiya tayi ba.
Mairo bata son wannan tafiyar sai don Yaya Habibu ya matsa mata. Amirun ne bata son gani, don bata son
duk wani abu da zai taba zuciyar ta a halin yanzu. Ta riga ta sanyawa zuciyarta YAKANAH (sunan littafin Takori
mai zuwa). Ta koya mata dangana, ta koya mata rayuwa ba AMIRU. Karatun ta kawai tasa a gaba, da rainon
‘ya’yan da Allah ya bata.
Lokacin da Daddy ya gayawa Amiru mairo ta haihu har ‘ya’ya biyu, bai nuna wani farin-ciki ba, don yana
kullace da Mairo, da bata taba zuwa ta dubashi ba har yayi ciwon sa da jinyarsa ya gama ya gaji ya mike. Bashi
da wani sauran buri a rayuwa, tunda ya rasa Mairo.
Sannan Daddy yace babu maganar biko, ba zancen kome, don bai yarda sun gama horuwa ba, Amirun yayi ta
zama a gwauro, ko su aura masa mai haihuwa. Ya kuma ce da Amiru in zai mike ya fuskanci sabuwar rayuwa
to ya mike, in bazai mike ba, yayi ta kwanciya soyayya ta kassara shi. Don shima yana da nasa laifin. Na kin
gaya masa duk abinda ke faruwa saboda tsoro da son Hajiyarsa. Har saida komai ya lalace. Daddy yace
“ita tana son ka ta lalata maka rayuwa?”
A fannin ita Hajiya, zaman Amirun haka babu iyali ya fara damun ta. Tana so tayi zancen biko a maida aure
tunda saki daya ne, babu fuska daga Habibu da Daddy. Don haka tasa ido, don ganin hukuncin da suke nufi.
Saidaifa rayuwar Amiru ta canza sosai. Ya zama babu murmushi babu far’a sai ‘dark-spaces’ kusan koyaushe
make a fuskarsa. Sai ayyukan dake gabansa. Ya kudire a ransa idan ba Daddy ne da kansa ya bude baki yace
ya maida Mairo ba da bakinsa, to ya hakura da ita har karshen rayuwarsa.
Yamma lis, suka iso filin jirgin saman Abuja. Dina dasu Muhammad sukaje tareda direba filin jirgin suka dauko
su. Suna zuwa gida Dina ta karbi yaran tayi musu wanka ta shiryasu da kaya na alfarma. Habibu ya dura su a
mota tareda su Muhamnmad da mai rainon su Esta da suka taho da ita daga Malaysia sai Asokoro.
Kasancewar ranar Lahadi ce, Daddy yana gida shida Amiru a karamin falonsa, suna aiki cikin takardu da
kwamfuta. Habibu ya yi sallama rike da mai sunan sa yayinda Muhammad ya biyo bayansa dauke da Amir. Ya
saki takardun hannunsa ya bisu da kallo. Ba zaka iya karantar halin da zuciyarshi ke ciki ba.
Suka yiwa kansu mazauni a falon Esta tana waje, Daddy sai murmushi yake yayinda Amiru ya zamo
mutummutumi, tsigar jikin shi na tashi cikin kauna da shauki. Ya matso ga Habib dake zaune a cinyar Habibu,
ya durkusa a gabansa ya mika mishi hannu, siraran lebbansa dauke da wani irin ni’imtaccen murmushi, da bai
taba yi a rayuwarsa ba.
Wata irin kauna ta da da mahaifi ke fizgar zuciyar shi. Amma sai Habib ya noke a kafadar Yaya Habibu wato,
bai san shi ba.
Yaji ba dadi, ya koma ga Amir yana karkada mishi ‘ya’yan mukullai, da wayo da dabara ya samu ya yarda ya
dauke shi. Ya rungumeshi sosai a kirjinshi yana sunsunar shi. Yana shakar kamshin turaren Mairo (Fahrenheit)
daya kama jikin yaron. Ganin dan uwanshi a hannun shi sai shima Habib ya miko hannu, ya hadasu su duka
biyun a kirjinsa, sai yaji kamar Mairo ce ya rungume. Amma don mazantaka, bai yarda ya zudda hawayen da
suke son bashi kunya ba.
Daddy da Habibu suka bisu da kallo cikin tausayi. Daddy yace “saukar yaushe?” Yace “dazunnan muka iso”.
Dai-dai lokacinda Hajiya ta shigo falon cikin kwalliya ta alfarma. Bakinta ya fadada da far’a da murmushi. Tace
“A’ah! Sababbin masu gidan sun zo, tsofaffi sai su zo su fice…” tana kallon Daddy tana dariya. Ya harareta don
yasan dashi take, yace “da tsohuwar zuma ake magani. In dai wadannan ne da ba mazauna ba ai gaki gasu, da
sun tafi zaki dawo min ne kina rara-gefe”.
Ba yadda bata yi ba don ta dauke su amma sun like jikin Ubansu. Ta fita ta kawo ‘teddy’ na ‘ya’yan Nina da
suka zo hutu sannan suka yarda da ita. Daddy yana son ya tambayi Habibu mai yasa Mairo bata zo ba? Yaga
babu dalilin da zai yi masa wannan tambayar sai yayi shiru. Shikuwa Amiru Allah kadai yasan abinda ke cin
zuciyar shi. Mairo ta daina son sa……! Mairo bata son ganin sa…..!!

1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button