HAUSA NOVELNa Baki Rayuwa Ta

Na Baki Rayuwa Ta, Complete Hausa Novel.

PAGE 1 to 5

Affan ne ya shigo cikin gidansu d’auke da sallama, kai tsaye d’akin mahaifiyarsa ya dosa, ta amsa mishi, tare da fad’in “dama nace tunda hadarin nan ya had’u yanzun nan zan ganka ka dawo.”

Affan ya zauna yana fad’in “wash Allah wallahi kuwa Inna nima hadarin yasa na shigo gida yanzu tunda ko tara batayi ba,” suna cikin magana aka tsuge da ruwan sama kamar da bakin k’warya.

 

Hakan yasa Affan ya tashi da gudu ya fice daga d’akin Inna ya shige nashi wanda yake hanyar fita daga cikin gidan.

 

Yana shiga ya sauya kayan jikinshi, sannan ya zauna gefen ‘yar k’aramar katifarshi, yayi addu’o’i masu yawa har ruwan ya tsagaita sannan ya kwanta tare da jawo wayarshi ya kunna data yana duba sak’onnin dake shigowa cikin wayar.

 

Affan beda budurwa ya d’auki soyayya asarar lokaci, yawanci abokanan karatunshi ne yake chat da su, sai kuma group na ‘yan makarantar tasu da kuma group d’insu na abokananshi na k’wallon k’afa.

 

Abun mamaki shine yana cikin dubawa kawai sai yaga wani group sabo an sakashi a ciki, abun ya k’ara d’aure mishi kai musamman da ya duba yaga group d’in mata da maza ne a cikinsa sai hira kawai akeyi da masu amfani da marasa amfani, kuma yayi iya bincikensa bai gane wanda ya sakashi ba, sai daga baya ya fahimci cewa rabinsu ‘yan makarantarsu ne wanda ya gama, amma yawancin mutanen dake ciki tabbas be sansu ba.

 

To Affan wani irin mutum ne wanda shi ko lokacinda yai rayuwarsa ba ruwansa da mata hatta a makarantun da yayi, hakan yasa wannan group d’in sam be kwanta mishi ba, kuma bazai iya fita ba saboda wanda ya sakashi a ciki amininshi ne me suna Adnan, yana matuk’ar ganin girma da mutuncinshi, amma duk da haka uffan be ce ba a group d’in ya tsallakeshi ya duba abinda zai duba ya bada amsa ga wad’anda zai ba mawa sannan ya kashe datarshi tare da ajiye wayar, sannan ya sake yin addu’o’in kwanciya bacci ya kwanta.

 

Kiran sallar farko na asuba shi ya tashe shi daga bacci ya tashi ya d’auro alwala ya fara nafila har aka kira sallah yaje ya tashi dukkanin ‘yan gidan sannan ya jira k’ananshi maza sukayi alwala dashi da su suka wuce masallaci, bayan sun dawo gaba d’ayansu k’annen nasa suka had’u ya koya musu karatu bayan sun biya na baya ya k’ara musu sannan kowa ya koma yaje ya kwanta, (haka al’adarsu take yin karatu da dare bayan isha’i, da kuma bayan sallar asuba).

 

Affan kuwa bayan ya kwanta wayarshi ya jawo ya bud’e data, kamar jira ake ya bud’e yana bud’ewa yaga message rututu nata shigowa, yana dubawa abun ban haushin duk tarin surutun nan daga cikin wannan group d’in yake, tsaki yaja, sannan ya kashe datan ba tare da ya bud’e ko d’aya daga cikin sak’onnin da aka turo mishi ba, ya ajiye wayar ya kwanta abinshi.

 

Washe gari ya tashi ya fito ya gaisheda Innarsu wato mahaifiyarsa, sannan ya tambayeta ina k’annensa, tace mishi ai sun tafi makaranta, mik’ewa yayi tare da saka hannu a aljihu ya ciro dubu d’aya ya baiwa Innarsu yace “Inna ga wannan ayi cefanen rana insha Allah anjima zan dawo in kawo na yamma.”

 

Inna ta karb’a tare da sa mishi albarka, sannan tace “ai bama sai ka dawo ba, insha Allah wannan dubu d’ayan zata isa tunda munada sauran kayan abinci da ka ajiye cefane kad’ai ya rage, amma ya kamata ka tsaya ka karya ga koko can da na dama na ajiye maka naka,” babu musu ya d’auko ya koma ya zauna, saida ya gama sha sannan ya yiwa Inna sallama Inna ta bishi da addu’ar fatan samun nasara akan abinda aka fita nema har ya fice tana kwararo mishi addu’a.

 

Ada idan Affan ya shiga kasuwa wayarshi ke tayashi hira kafin zuwan kwastomomi, amma yanzu sam be damu da hawa whatsapp d’in ba saboda dalilin wannan group d’in yasa ya dena damuwa da hawa, in kaga ya d’auko wayarshi to kiranshi akayi ko kuma shi zai kira.

 

Ba wani abu yake bawa Affan haushi ba sai kasancewar group d’in akwai mata, kuma abinda yafi k’ular dashi shine yanda suka maida group d’in kamar dandalin soyayya, shi kuma ya tsani yaga namiji ya marairaice duk girmansa yana yiwa mace kalamai ita kuma taita wani yauk’i tana shirme a cewar Affan.

 

Kamar kullum da yamma gab da magrib ya shigo cikin unguwarsu, amma baya shiga gida sai yayi sallar magrib da isha, kuma acan yake tarar da k’annenshi, in sun idar sai su shiga gida tare, to yauma hakan ta kasance.

 

Bayan sun idar da sallar sai suka fito suka hau bayan mashin d’in Affan ya k’arasa dasu gida.

 

Yana zuwa k’ofar gida ya tsaya suka sauka shima sauka yayi, ya cire ledar dake gaban mashin d’insa ya baiwa d’aya daga cikin k’anninsa su rik’e mishi, a haka suka shiga gida ya faka mashin d’in a tsakar gidansu, sannan suka shiga cikin d’akin Inna, bayan sun zauna Affan ya gaisheda Inna sannan ya mik’a mata ledar hannunshi yace “gashi Inna kayan tea ne, tunda naga kin dama koko na gane sun k’arene, kinsan banaso kuna shan kokon nan, burina duk abinda me kud’i zai ci kuma ku ci, kinsan k’annena basa son koko kan dole kawai suke shansa,” ya sake mik’a mata leda wadda take d’auke da dak’wa dak’wan kaji guda biyu.

 

Inna ta dudduba kayan, ledar farko manya manyan gwangwanayen madara ne da bonbita, sai suga da kwalin lipton, d’ayar ledar kuma kaji ne manya manya guda biyu, haka yake yi duk ya fita kasuwa ya dawo sai ya taho musu da tsaraba.

 

Inna ta kalleshi tace “yanzu Affan duk fad’an da nake maka akan ka rage yawan kashe kud’in da kakeyi a kanmu baka ji ko, menene aibun shi kokon, ka koyi tattali fa Affan saboda wata rana, tam.”

 

Affan yai murmushi sannan yace “Inna wallahi samuna beda amfani indai inadashi ban wadataku da komai ba, saboda ku fa nake nema, menene amfanin tarawar bayan kunada buk’atarsu.”

 

Inna tai mishi addu’o’i tare da sa musu albarka dukkansu, bayan sunci sun sha sai Affan ya tara dukkanin k’annensa yaji karatun da akaiwa kowanne daga cikinsu daga kan karatun Qur’ani da sauran litattafan addini har zuwa kan na boko, bayan sun kammala yace suje su kwanta zasu k’ara yin muraji’a da asuba, nan shima yai sallama da Umma ya shige cikin d’akinsa ya rage kayan jikinshi sannan yai addu’a ya kwanta.

 

Saida aka shafe wajen sati biyu Affan be sake waiwayar whatsapp ba.

 

Yau Juma’a da wuri ya sallami Innarsu ya tafi kasuwa, saboda duk ranar juma’a suna samun ciniki sosai, hakan kuwa akayi yanata hada hada da mutane beda lokacin kanshima.

 

Bayan ya dawo gida ya kammala duk abubuwan da zai kammala na yau da kullum wad’anda dama ya saba gabatar da su, be dad’e da kwanciya ba sai wayarshi ta fara ringing, yana dubawa sai yaga ashe babban abokinsa ne koma ince babban amininsa Adnan ne ya kirashi.

 

Fuskar Affan d’auke da murmushi ya d’aga yana fad’in manyan k’asa sai yau ka tuno dani kenan?”

 

Adnan yai dariya sannan yace “kaidai bari mutumina wallahi mun fara jarabawa ne sai shekaranjiya muka gama, shiyasa ka jini shiru kwana biyu, amma ai muna had’uwa a whatsapp ai shiyasa ban damu da kira ba, yanzuma naga kwana biyu bana ganinka online ne nace bari dai in biyo sahu.”

 

Affan yaja tsaki sannan yace “whatsapp d’in ne ya fita a raina tun ranarda ka sakani cikin group d’inku na soyayya, ni kuma kasan bana soyayya bansan shegen karambanin da ya kaika jefani cikinshi ba.”

 

Adnan yai dariya sannan yace “hum dama nai tunanin haka a raina wallahi, wai kai Affan sai yaushe zaka canza ne, yanzu fa kai babba ne ka kusa aure, ko haka kake tunanin zakaita zama, to wallahi karka kuskura ka fita daga cikin group d’in nan, kuma yawanci fa duk mate d’inmu ne daga mazan har matan d’ad’d’aiku ne bare a wajenka, ka hawo yanzuma ni in gabatar dakai.”

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button