HAUSA NOVEL

BAKIN CIKIN KISHIYATA Complete Hausa Novel

_______Husna ce ta d’anyi murmushi sannan tace,

“Dan Allah nidai kubar mgnr nan tunda ita tai tafiyartama batasan kunayiba,ita halintane haka kowama hak’uri yakeyi da ita yanzu in kukaci gaba da maganarta saiku kwasarwa kanku zunubi Dan haka kawai kubar mgnr,

Baki Aunty Maryam ta tab’e daga nan suka sako wata firar sunata tsara yanda sunan zai kasance,

Ita kuwa fiddausi bayan komawarta bangarenta zamatai a Bakin gado Amman har yanzu hoton yarinyarne a idonta don tafi faruq kyau sosai balle kuma jiddanta,wani haushinne ya kara tirnik’eta da haka bacci ya d’auketa agurin,

Can cikin baccin taji wani irin ciwon ya taso mata azabure ta mik’e tana rike bayanta jin kamar zai balle, da Sauri ta sauko daga gadon don tasan nak’udace ta taho mata gaba d’aya, ita kadai ta dinga fama a d’akin don yaran basanan suna bangaren husna balle su kira mata wani gashi batasan inda wayarta takeba,

Tasha wuya sosai sai can cikin hukuncin ubangiji ta haihu, zuface ta dinga karyo mata ta wahala don bata tab’a nakudar da ta sha wahalaba kamar wannan,

Ita ta yanke cibiya da kanta Sai bayan ta sami kanta sannan ta gano inda wayar take, d’aukowa tai ta kira mijinta ta sanarmai sannan ta kira yan uwanta
kasancewar ba haihuwar fari bace tasan kan abin da kanta ta gyara babyn ta gyara kanta sannan ta gyara dakin,

Abubakarne ya fara isoea sosai yai far in ciki da haihuwar tamkar ba a tab’ayimai haihuwaba sannu ya dinga mata jin Cewar ita kadai ta haihu, anan ya tambayeta sunan da xa a sawa jaririn,

Taji dadin hakan duk da taso mace ta Haifa asanya sunan mahaifiyarta Amman yanzunma bats b’aciba don haka tace a sa sunan mahaifinta,
Nan take yaiwa jaririn hud’uba da suna Abdullahi,

Nandai aka d’anzo yi mata barka Amman yawanci dangintane sukazo,

HAJIYA jidda ma tazo ganin jikannata anan ta ba da shawarar a had’e sunan ayi komai tare tinda rana d’ayane, ba musu ya amince
ya sanarda Al,amin ma shima yace ayi komai tare har girkin sunan ya sanarda husna itama tace hakan yayi,
saidaifa fiddausin sam tak’i amincewa Wai ita baza a had’a mata suna da husna ba kowa yai taronshi daban ita ta yarda a d’aga nata,

Nanfa shima ya tubure yace tunda Kowa a ya amince dolene itama ta amince don bazasu sab”a maganar mahaifiyarsuba saboda ita,

Ganin ya d’au zafine yasata yin shiru Amman dai ita ba haka tasoba,

Ahaka ranar suna tazo, inda jaririyar husna taci sunan yayar mahaifinta wato FATIMA ZAHRA shi kuma d’an fiddausi yaci sunan mahaifinta wato ABDULLAHI,

Anyi shagali sosai ankashe nera taro ya tashi lfy kowa ya taxi da far in ciki da da kyautuka,
sab’anin fiddausi datai taron cike da takaici da b’acin rai don dukkan yan sunan a bangaren husna suka tare kuma ba Wanda ya bata wani Abu sai yan uwa ta su kadai ne a b’angarenta don ko dangin mijin basu zauna ananba,

Nanfa ta k’ara k’ullatar husna da jaririyarta ta dasawa ranta k’in ZAHRA don tunda aka haifeta ta ganta Sau d’aya bata k’ara zuwa ta gantaba,

Ita kuwa husna kullum saitazo ta gaidata taga jariri ABDUL dukda tana jegon itama Amman bats tab’a gajiya da zuwaba,

Ahakadai zaman basu ya mik’a, husna Na k’ok’arin had’a kan ‘ya ‘yan na su yayin da fiddausi ke janye nata tana nuna musu ba ruwansu da ZAHRA tanason cusa musu tsanarta kamar yadda ta tsaneta,

Shi FARUOQ ma tamkar k’ara mai shak’uwa akeyi da zahran Jidda ma haka cewa suke k’anwarsuce, Abdul ne dai dayake ba wayo shi kuka yake sata insun had’u da yakeshi akwai fad’a ita kuwa hakurine da ita tin tana jariririya,

**”””BAYAN WASU SHEKARU.

Faruoq yana da 18 year s mahaifinshi ya kaishi karatu k’asar waje, su kuma sauran agida sukeyin nasu karatun, alokacin fiddausi yaranta 5 don ta k’ara haifar biyu mace da namiji, ita kuwa husna bata k’ara haihuwaba tindaga Zahra,

Zahra tasha kukan rabuwa da yaya faruoq donsun shak’u sosai, haka shima ya tafi da kewar family d’inshi musamman Zahra da yakejinta a ranshi fiye da kowa,

A yanzu Alhaji abubakar da alhaji Aminu arzik’i yaci uwar Nada don shekara biyu da suka wuce suka d’ebi iyalensu sukaje suka sauke farali daga nan suka wuce MADINA suka ziyarci kabarin Manzo sannan suka dawo gida,

***Haka rayuwa ta mik’a ayanzu FATIMA ZaHRA An zama cikakkiyar budurwa don lokacin shekarunta 18 ayanzu haka sun kusan kammala karatunsu itada Aunty Jidda don tare aka nemar musu shima Abdul haka kannen sune dai ko secondary school basu gamaba ayanzu har an tsayar da bikin Aunty Jidda da sun kammala karatunsu nanda wata biyu,

Abangaren faruq shima a wannan shekarar zai kammala karatunshi ya dawo gida, yana cike da d’okin dawowa yazo yaga masoyiyarshi ZAHRA da yaketa dakon soyayyarta tin tafiyarshi……………..!

Wash

Pls
Comments
And
Share
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️
BAK’IN CIKIN KISHIYATA
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️

Story and written
By
Fatima umar kas
(Mummyn mihal)

*بسم الله الرحمن الرحيم*

®????
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *…*????✍????
[ “`Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women“`]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

*_Z• W• F•????_*
Page 60_65

Shi kuwa faruoq bayan ya shiga d’akinshi rage kayan jikinshi yai sannan ya fad’a toilet wanka yayi sannan ya fito ko mai bai shafaba don yanayin garin akwai zafi_zafi kayan shan iska ya zira sannan ya hau kan makeken gadonshi, wayarshi ya jawo sannan ya fara tura mata gajeran sak’o

“Daman haka ake tarbar masoyi idan ya dawo daga wani guri? Ashe ni kad’ai naii kewarki ke bakiyi kewataba, daman duk abinda kike fad’amin iya bakine? Na gode,”

Tura mata yayi sannan ya k’urawa wayar ido yana jiran reply, ita kuwa a d’aya bangaren murmushi tayi ganin abinda yace amsa ta tura mai itama,

“Wallahi ba haka bane yaya kawai Na kasa yima magana ne a gabansu Momy shiyasa Amman ni kad’ai nasan far in cikin da nake ciki ayau Na dawowarka,

” niban yarda kinyi far in cikida ganinaaba tunda ko kallona kinkiyi balle kiyimin magana ki nunamin kinyi kewata,”

“Allah yaya kunya nakeji shiyasa kuma kaima sai kallona kakeyi agabansu Momy shiyasa duk Na kasa sakewa Amman kayi hakuri nayimurnar ganinka kuma Na tayaka murnar kammala karatunka da fatan ka dawo lfy?”

” lfy kalau my wife da fatan Na sameki lfy? Aike d’ince kika birkitani gaba d’aya shiyasa Na kasa daina kallonki, ni Allah yasa ma su Momy sun gano wani Abu a tsakanin mu don zanyi far in ciki da hakan inma basu ganoba ni da kaina zan fad’a musu, Donni a shirye nake a yauma a d’aura mana aure abani mata ta,
anjima ma dakaina zanyiwa su daddy maganar inmun had’u,”

Ido ta zaro kamar ya Na gabanta jin abinda yace don haka ta turamai,

“Dan Allah karkayi hakan ka bari sai nan gaba Donni inajin kunya da nauyinsu insukasan tun d’ad’ewa munason juna kwara ka bari ad’au lokacin da dawowarka ka ga sai a ga kamar bayan dawowarkane muka fara soyayya,”

Aisaida kiyi hak’uri dani Dan ba zan zauna jiraba su Abba su badake ga wani kinsan ance abari ya huce shi ke kawo Rabon wani Dan haka nibazanyi wannan gangancinba,”

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button