TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Advertisements
*1*
_Bismillahir-rahmanirraheem_.
*B* abban gidane sosai daya qunshi 6angarora acikinsa sbd yawa da zuriar gidan sukeda shi,,
Gidane tsohon gini irin na masu arzikin lokacin baya daya gabata,
Mal Zubair shine mamallakin gidan da ahalin gidan gabaki ‘daya,
Ya rasu shida Mai ‘dakinsa Fatima sunbar ‘yaya hudu duka maza,,
Baba malam hayatu shine babba agidan yanada tsananin zafi da fa’da,
Sam baya kar6ar uzuri ko kuskure duk da kasancewarsu malamai masana addini,
Baba malam shine Mai zartarda duk wani hukunci acikin gidan Kuma ya zartu Koda baiyiwa kowa dadiba.
yanada mata biyu inna hindatu da iya lami,
Inna hindatu bata ta6a haihuwaba iya lami ce keda ‘yaya bakwai, _zayyanu, auwalu, dahiru,Musa,mustapha, abudullahi da sani_.
Baba shehu shine mabiyin baba malam Kuma shima kusan duk halinsu ‘daya da baba malam illai shi Yana da’dewa baiyi fadan ba,
Matarsa ‘daya shi,mama salamatu Sai ‘yaya biyar duk mata,hafsat, Amina, hajaru, zainab da sumayya Kuma duk anyi musu aure.
Sai baba Yusuf Mai sanyin Hali da kawaici dakuma tsananin qaunar ‘yanuwansa, shima matarsa ‘daya fatima da ‘yaya biyu _*AYSHA*_ da nuratu.
Alh Bello shine qaraminsu Kuma fitnannensu Dan masifa da son kansa a fili yake sbd ya ‘dan taba yin arziki abaya Amma yanxu Babu shiyasa ko Abu ka’dan akai saiya maidasa babba akan fitina da fa’dansa.
Matansa biyu mama bilki da umma sakina.,
‘yayansa bakwai _ahmad, isah, Umar, abbakar Sai saudat Salma da husna_
Dukkaninsu a gida ‘daya suke Sai dai kowa da shiyarsa Amma yaransu maza kaf 6angarensu ‘daya hakama matan.
Asalinsu buzayen qasar nijar ne malanci yakawo mahaifinsu garin gombe harya gina gida yazama mazauni.
Malamai ne kaf ‘dinsu Kuma basuda wani aiki bayan malanta hakama ba wani arzikine dasuba Sai rufin asiri.
A rayuwar gidan Sam basa auren na waje saidai atsakaninsu sbd yawa dakuma tsananin kyamar wani yare daba nasuba na buzaye.
Qabilanci ne tsantsa acikin jinin kowane ‘dan Adam dake rayuwa acikin gidan,
Basa qaunar ha’dawa da ko bahaushe bare wani yare har gwara Fulani.
Wannan aladace dasuka gado tun gurin iyaye da kakanni shiyasa duk kwa’dayi da maita ta kyau da ‘yayan gidan sukedashi ba’a tunkararsu da maganarso,
Qiyayyar dasuke fitowa suna nunawa ta rashin son ha’da zuria da wata qabila a qarara yake Dan abin har tsoro da mamaki suke bawa na taredasu.
Yaran gidan kaf dinsu maza da mata ustazai ne kamilallu kullum jikinsu a rufe yake ruf ko qafarsu baka gani fuskarsu ma wani sa’ilin suna rufewa idan zasu fita.,
Mazansu da matansu sun haddace alqur’ani akansu da sauran littafan addini.
Ka’dan ne daga cikinsu sukai karatun Boko sbd bai damesuba sunfi riqe addini shiyasa layin gidan kullum acike yakeda motoci da mashina harda kekuna gurin ‘daukar karatu a gidan.
Ayshah,husnah,saudat da Salma kusan sa’anin juna ne ‘yan kimanin shekaru goma Sha takwas zuwa Sha Tara.
A al’adar gidan mata basa wuce gaba da secondary aure suke musu Amma wannan karon anbarsu Aysha sun wuce sbd ba’ayi Shirin aurensuba Amma antsayarwa kowaccensu da miji.
A university suke karatu yanxu suna two hundred level.,
Aysha medicine take karatu sukuma sauran gabaki ‘daya Islamic sukeyi.
Yaya Umar shine Wanda aka ha’da Aysha dashi sbd sonta daya nuna yanayi qarara,
Ya Umar mutum ne Mai zafin Rai kamar iyayensu Dan kamarma ya zarcesu sbd baida hakuri ko ka’dan ga saurin duka dayakedashi bayada kar6ar uzurinta ko ka’dan shiyasa kullum idan sukai fira kwana kuka take sbd da fa’da suke rabuwa,
Sanyin halinta da sanyin jikinta tareda kasancewarta miskila Mara hayaniya shike wahalarda ita ko acikinsu saudat bare gurin ya Umar.
Halin umminta ne ta ‘dauko Zak harma ta zartata sanyin halin shiyasa mahaifinta da ummin ke tsananin qaunarta da tausayinta sbd ganin kawaici da hakurinta sa6abin qanwarta nuratu dake da masifa ba’a ta6ata ko ka’dan.
Aysha kyakkyawace Mai kyan jiki Dana fata ko acikin gidan tafisu hasken fata da kyau sbd tafisu rashin son fita duk da dama kulle ake musu basa fita.
***********
Yau tun 6 na safe tafara shiri sbd anyi shifting lectures ‘dinsu zuwa sabon site ‘din university Wanda bakowane course ake maidawa can ba gashi yanxu an rabata dasu husnah dansu yanxu tsohon site suke.
Hakanan batajin dadin rabata dasu da’akai sbd batasan ya can ‘din takeba,.
Tsaf tashirya cikin doguwar rigar atampha red Mai adon dark blue saita saka dogon hijab dark blue daya sauka har qasa yanaja danko kalar atampharta ba’a gani bare qafafuwanta,
Jakarta ta ‘dauka tareda ficewa taje tagaida iyayensu kowane 6angare kafin tadawo ‘dakinsu suka fito taredasu husnah.
A qofa suka hadu da ya Umar da ya Ahmad zasu shigo,
Har qasa suka durqusa su duka suka gaidasu
Ahmed ne ya kar6a Yana shigewa cikin gidan
Ya Umar ne ya amsa tareda kallon ayshah
Qasa tayi da kanta Tana wasa da Jakarta su husna kuwa tuni suka wuce sbd Umar ‘din Sam baya wasa yanxune zasuji ruwan bala’i.
Kallonta yakumayi dakyau ahankali yace,
Meyasa baki saka safa ba?
Cikin sanyin murya kanta na qasa tace,
Sunyi dattine na wanke na shanya ruwan da’akayi da dare sun hanasu bushewa.
‘daure fuska yayi yace,
Toki tabbatarda kin dawo kan lokaci.
To””’ tace a hankali tareda wucewa cikin sanyinta.
Ajiyar zuciya ya saki ahankali bayan ta wuce Dan hakanan yakejin Sam hankalinsa yakasa kwanciya da karatun Aysha sbd jiyake kamar zai rasata ne duk dayasan bazata kula kowaba.
A bus stop suka rabu dasu husnah ita ta nufi new site Banda faduwa ba abinda gabanta keyi sbd ita mutum ce Mai tsoron shiga jama’a batareda Wanda tasaniba.
Koda ta Isa kai tsaye hall ‘din dazasuyi lectures ta nufa kanta a qasa cikin nutsuwarta take takawa Dan duk a takure take sbd yanayin students ‘din data gani anan ‘din kamarma ‘yan iskan makarantar ne aka kwaso aka dawo Nan dasu Dan dukanin alamu sun nuna kusan hakan ne,
Lectures suke Amma Sam takasa samun nutsuwarda zata fahimci lectures ‘din Dan wasu samari dake kusada ita suna dariyar shigarta.
Sai kusan six suka fito daqyar taga tafito ta iso gida Dan har wani zuru zuru tayi na fargaba data yini yau aciki.
Tana Isa gida ta tu6e tayi wanka tareda sallah kafin tazauna cin abinci Tana fira da umminta tareda Bata labarin wani fa’da dataga anayi kan hanyarta ta dawowa.
********
Babban gidane dayaji komai najin da’din duniya sbd girma,kyau dakuma haduwarsa..
Babbar mace ce ‘yar gayu da hutu tareda ilimin Boko dayagama ratsata yasa manyancinta qin bayyanuwa sosai,
Babbar justice ce a babbar federal high court dake garin hakama Mai tsananin roqoce da addininta na christian Dan har muqami gareta a church sbd riqoda addininta Dan dukda zamanta babbar Mai kudi hakan bai hanata halarta da kula da aikin church ba kullum.. _justice queen aiden Bellamy_ kenan.
‘yayanta uku rak a duniya,
*FINN* shine babba mum’s boy kenan sbd shine ya ‘daukota sawu da sawu Dan shima law ya karanta yanxu lawyer ne kullum tare suke zuwa office sudawo tare suje church tare,
Duk wani Hali nata ya ‘dauko Dan harma ya zartata musamman yanda ta tsani kowace qabila da addini idan ba nataba toshima haka.
*_NIK_*,,,,Niklaus kenan, shine nabiyu Wanda shida qanwarsu *DAVINA* kwata kwata halayensu sunyi hannun Riga Dana mahaifiyarsu sbd Sam su Babu ruwansu da wani riqo da addini bare zuwa church,,