Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

1-2

 

 

Gidane madedaici me dauke da dakuna shida du da dakunan da bawasu manya bane ciki dai daine se shago daya daga kofar gida Wanda Shima bawani girma gareshiba samarin gidanne suke kwana aciki da Kuma Baki maza in anyi gidane me Mata hudu aciki duka miji Daya suke aure Kuma ko wance na da Yara gidane da kullin Sana,a akeyi aciki Babu hutu daga safiya har dare abincine kalakala ake dafawa asiyar agidan kullin cikin sallama ake Yan siyan abinci Yara da manya suke zuwa su siya du da haka Kuma yammatan gidan see andora musu sun fita tallah arana kowace budurwa tindaga safe zuwa dare mahaifiyarta na Dora Mata talla sau uku arana

 

Budurwace Wanda zatakai shekara ashirin da bakwai aduniya tafito daga Daya daga cikin dakunan gidan tasaka dogwan hijabu har kasa da yarinyar ta dago fuskarta na kallah se Da nace Masha Allah tubarkallah saboda kyau budurwar me suna sadiya karasawa tayi gaban mahaifiyarta da take girki abakin murhu

Tace umma nafito Zan tafi isilamiya su kalifa har sunyi gaba sun barni

Mahaifiyar Tata ummu tace anfito sadiya Allah yatsare Allah yaimiki Albarka se kin dawo maza kidaga kafarki ki karasa Kinga kin makara saboda aikin da Kika tsaya yi

Tace to umma

Sauran Matan gidanne atsakar gidan kowance aikin gabanta take suka bushe da dariyar da shewa kamar hadin Baki sukace aikin kenan ahaka zaakare ana yawo atiti da sunan makaranta ake zuwa ana fakewa da karatu ana fita karuwanci wayaga tsohuwar guzuma du kanne da saanni da kawaye sunyi aure Banda ke saboda kwantan da kikayi saboda mugun bakinjinin ki tinda Kika taso agidannan ko kare betaba zuwa yayi sallama da keba kullin ana fita da sunan zuwa makarantar boko da ta isilamiya ana fama da katan hijabi se yamma tayi afita kofar gida asoya awara da zunan ana siyarwa nankuwa samarine suke lalubeta acikin katan hijabin da take sawa da Kuma tallan kanta da takeyiwa mutane ko zasu auri saura heeehheehe awai ai gara yaranmu da su kulin talla suke zuwa ba makaranta suke zuwa ball Kuma du da haka Allah yabasu farin jini kullin cikin sallama ake samari na zuwa zance wajansu har da masu sa Rana akansu Kuma du kannankine ko muce yayanki Allah mun godema Ni Ina mamakin malam da ko sadakane beba da itaba da aiko wani tsohun yasamu yaroka ya aureta sadaka tinda anyi kwantai tafa yi talatin alinsafin da mukayi rannan suka dada kwashewa da dareya

Sadiya da idanta yake ta zubar hawaye har tabude Baki zatayi mgn mahaifiyarta tace shige kitafi karnaji kinyi mgn ai in da sabo kin Saba jin haka abakinsu da yaransu Allah yaimiki Albarka maza yi tafiyarki aishi mahaukaci meja da ikwan Allah in katsaya kulashi kaima kazama mahaukacin wannan ba da ke sukeba da Allah suke Kuma Yana jinsu shi ze Mana maganunsu

Ficewa sadiya tayi tana ta goge hawaye tace Allah Kaine Allah kaji du abinda ke faruwa Kuma Kai ka halincemu Allah kakara min hakuri da juriya Ni da mahaifiyarta da Yan uwana Allah kabumu ikwan cinye wannan kandarar umma narasa wana irin hakurine da ke tinda nataso agidannan nake ganin irin cin kashin da ake Miki Amma bakya mgn se dai ki kau da Kai naso yau Daya ki barni na maida musu da martani haka tashiga makaranta Rai abace

Matan gidanne sukahau Kan umma da masifa Wai tace musu mahaukata se zage zage suke ai bamuyi karyaba du abinda muka fada ba sharri mukai mukuba abune afili baro baro kowa yasani ai ba gullarku mukayiba agabanku muka fada in karyane abudi Baki akaryata

Umma tace ai base na karyataba bakuma tsoranku nakeba na barkune da Wanda yahalincemu Kuma Ni nasan jinina in har Ni nahaifa insha Allah baze taba aikata zinaba daga Matan har mazan da yardar Allah adduar da nakewa yayana tana binsu adu inda suke da Kuma tarbiyar da na basu Ni bani da lokacinku wlh na tsaya muna fada Amma kusani akwai ranar mai da martani in takama nasa hannu Kan mace wlh zansa Dan anfara kaini bango na gode Allah Ni yarana makaranta suke zuwa bakuma talla nake Dora musuba tin safe har dare wataranma har Sha Daya da wani abin ana kaiwa baa dawo gidaba Allah ngd maka da nake da lokacin tarbaiyar yayana kunga Ina da abin yi

Tai shigewarta daki tabarsu Baki sake Daya daga cikinsu tace Abu mgnfa tagaya Mana Wai yaushe ma har matarnan Tai Baki haka kun bani mamaki da bamu hadu mun rufeta da dukaba mun karkarya shegiya mun zubar kuka tsaya Kuna kallanta har ta shige daki yanda kike da jikinnan lami ai da zaune Mana ita kikayi

Lami tace bar irin mutanannan sirara da kike gani wlh Kashi dayane da su ke inmun daketa manyan yaranta da Yan uwanta zasu hakurane musamman wannan sojan da yashiga iakin kwanannan kinsan shegen zuciyace da shi Kuma karki manta Yan uwanta masifanfune basaso ataba musu Yar uwarsu ga yaranta maza shegen zuciyane da su du da basa gidan wlh suna Jin labarin mun Dakar musu uwa se sunzo sun Rama Mata ko sojannan ze iya kwaso Mana Yan uwanshi sojoji su tafi da mu barki aimana dukan tsiya koma a karkaryamu kun dai ga rannan da sukazo da abokansa da kakin soja jikinsu su kasamu su asabe sun rufe su kalima da duka akofar gida dukan tsiya sukaiwa su asabe tin daganan na tsorata da su ai kome muke Mata ko dawasa kar mu samata hannu da bakin dai ya Isa bakijiba ita yanzu dukanmu takeso tafara ai takamarta kabiru da yake soja gashi har tasamu bakin mayar Mana da mgn wlh mubi ahankali nagaya muku Danni yanzu ko Ido banaso na hada da kabiru soja gashidai kwanannan yashiga aikin Amma yarikide yazama wani mugu ko fuskarshi baka iya kalla sosai saboda kullin fuskar hade take kamar hadari bakiga itama sadiya ba mgn takeso ta mayar Mana wlh in da Wanda nabudi Ido nagani a idona itace sadiya wlh na tsaneta indai Ina numfashi ita da aure har abada sedai taga anayi ahaka zata Kare agida da bin maza suna latseta

Dayar mesuna talah tace ashedai du raayinmu daya Akan sadiya Nima yanzu na kulla makaman yaki Akan sadiya se naga bayanta Ni nayi mamaki da danta kabiru yasamu aikin soja bakiga kudin da na kashe Akan yaranta maza Amma abanza shegiyar inaga wani banban bokan tasamu yake Mata aiki akan yaranta ga isama kuga yanzu yasamu aiki Naga Kuma kamar Yana samu ko matarsa da yaransa kagani kasan suna jin dadi

Kafin sukara mgn Megidanne me suna malam musa amma matansa da yayansa malam suke kiranshi yai sallama yashigo Baki suka hada suna Masa sannu da zuwa ya amsa musu

Yace me ake tantaunawane haka naganku awaje Daya haka Ina ita Khadija ko bacci take

Baki suka hada wajan bashi Amma su kace wannan Yar mulki me ishansha. Iko wannance zatazo cikinmu tazauna yanzu ta shige daki da ta gama Mana rashin mutunci tazagemu tass Dan haka ka jamata kunne wlh karta Kara zaginmu in bahakaba wlh zamu dau mataki dama jira muke ka dawo mukawo maka kararta

Malam yace Kai ba dai Khadija ba saunawa ko agabana zaku Bata Mata Rai Bata muku mgn yau dinma bango kuka kaita inaga

Sukace ai Daman munsani bayanta zakabi Dan munga kwanannan wani rawarkai kake akanta da yaranta saboda yaranta maza sun samu aikin yi har da me aure da Yara in baka jamata kunneba wlh watarana zaka dawo kasamu matarka akarkarye Wai yau harmu takewa Gori yaranmu basa zuwa makaranta se tallah aigara mu talla tarufa mana asiri har Yara mun aurar da kudin talla itafa me karatun bokwan yatsinanawa yaranta in banda kwantai ma da akayi agida ba mashinshini du kanne sunyi aure da kawaye da saanni ana gida azaune ai itace me abin Gori zamuga ranar auran tsohuwar guzuma in yatashi me za ai Mata na Kayan daki baa Sana,a ana zaman kashe wando bareba ba auruwa zatai ba Waze kwashi jangwan sauran wasu yakai gidansa

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button