Nancy Yar Karya

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*
PAGE *ONE AND TWO*
_____Wata kyakyawar budurwa na hango sanye da , riga da zani kod’ad’u , da ‘alamu sunji jiki sosai , amma kasancewar wanan budurwa kyakyawa, yasa ko yagaggun kaya tasa baya yimata muni , budurwar zatakai shekara goma sha biyar , tafiya takeyi cikin yanga da iya taku, duk a ganinta kaf cikin k’auyen (ZANKANA) itace wayayya, tunda ta doso gurin wasu samari suna shan rake, naji suna cewa saike Duduwa , 6ata rai tayi kana tace “wallahi duk wanda yakuma fad’amin wanan sunan saiyayi dana sani , cikin tsiwa take maganar, wani matashin saurayi ne ya taso yazo kusada ita yace ” saike kyakyawa , washe hak’ora tayi tana dariya tace”yauwa Yasir ai kai kafisu mutunci,
Suna tafiya suna hira, har suka zo daidai k’ofar gidan su Duduwa , gidane mai zagaye da galan galan saboda bazaka kira gidan masu kud’iba saidai ace talakawa , bayan sunyi sallam da Yasir ta shige gida, tasami Umman ta ‘tana tuk’a tuwo , yamutsa fuska tayi kana tace” waike Umma bakya gajiya da cin tuwo ? kullum tuwo ,wallahi ni nagaji cikin masifa take maganar , Umman ta da ko kallonta batayi ba tacigaba da tuk’a tuwon ta , Duduwa ce ta wuce d’akinta daya kasance mai katifar yayi ,ta janyo wata leda data mak’ale a mararta ,dan tasan hardai Umma ta ganta da ledar to saitayi mata nasiha , awara ce da yaji cikin farar leda , tanaci tana karkad’a k’afa tana mita, Umma ce ta k’wala mata kira ,seda tad’au lokaci sanan ta ‘amsa , bayan ta goge hannunta ta fice zuwa gurin kiran Umman,
Tana zuwa Umma tace” ga tuwonki nan , kamar zata fasa ihu tace ” ba yanzu zanciba sai zuwa anjima, tsayawa kallonta Umma tayi , tana tunanin girman kai ‘irinna Duduwa, bayan Umma tagama tattare kwanukan abincin data zuba ta koma d’aki, bata ko kalli gurinda Duduwa ta tsaya ba , bayan sallahr isha’i , yaro yazo yana sallama , Umma ce ta amsa sallamar tare da cewa , waye? yaron yana daga k’ofar gida yace” Duduwa ake kira , kafin yaron ya k’arasa fad’ar sunanta ta fito cikin masifa Umma na tsaye tace” dan uwarka wacece Duduwar ? rik’e baki Umma tayi tana kallon ikon Allah tace” inkin gama masifar saiki tambayi waye mai kirannaki, bayan ta gallawa yaron harara tace”wai’ injiwa ? yaron da tsoro ya kamashi yace ” inji Yasir ne, da fara’a d’auke a fuskarta tace kace ina zuwa,
Bayan yaron ya fice, Umma ta dubi Duduwa tace”nidai nasihata dake shine kirik’e mutuncinki , wlh ke y’a mace ce mai rauni , tunda Umma tafara nasihar Duduwa ta had’e rai tace”Umma kullum kekenan fad’a kuma kinsan ‘ niba k’aramar yarinya bace, sanin halinta da Umma tayi yasata komawa d’aki , ita kuwa Duduwa kwaskwarima tayi tayi kwaliya tasa kayan sallanta ta fice zuwa gurin Yasir , tunda ta doso yajiyo k’amshin turarenta yafara fad’in, maraba da kyakyawa saike y’ammata murmushi takeyi tana sunkuyar da kai ,ammafa tak’i bud’e baki wai, saboda kar janbakin ya goge , bayan sund’an ta6a hirane yayi mata sallam , ganin bai mik’o mata komai ba yasata 6ata rai , shikuwa saboda tsokana yazagayo yace”kawo hannunki , a hanzarce ta mik’o , ganin wainar k’awai ce a leda tahau dariya , daganan sukayi sallama cikin farinciki,
Washe gari da safe , bayan Duduwa tayi sallah tazo gaida Umma , bayan sun gaisa ne Umma tace” maza tashi ki had’a wanke_wanke kiyi mana saboda yau inason zuwa anguwa ,da har ta6ata rai , amma jin Umma tace zataje anguwa yasata fara’a ta mik’e da sauri dandanan ta gama , lokacin Umma tagama shiri , dari hud’u ta bata kud’in cefanen abincin rana , tace “kafin ta dawo tasamu tagama , aikuwa Duduwa jiki na rawa tace” Umma insha Allah zan kammala kafin kidawo , Umma tayimata sallama ta wuce unguwa,
Duduwa na kwance tun k’arfe tara na safe har shad’aya na rana tana bacci , k’arar dabbobin gidansu ne ya tayar da ita daga baccin, gyalenta ta d’auke da kud’in da Umma ta bata ta nufi shagon mai saida kayan shayi , bredi d’an nera d’ari ta siyo sai madara ta hamsin sai k’wai na d’ari takuma siyo maggi na goma tasiyo indomie ta ragowar canjin , tana tafiya ne sukaci karo da wani saurayin dake kusada gidan su yace”ah kyakyawa ina zuwa ? naga kamar kayan dad’i kika siyo mana , tana dariya tace”Abdul yunwace ta isheni shine nazo siyan kayan shayi , Abdul daketa lek’en ledar yace”to sammin burodin inci ,mak’ale kafad’a tayi tana dariya,
Tunda ta koma gida tafara had’a wuta bayan ta d’ora shayin ta had’a takuma d’ora indomie , bayan ta kammalla girkin ta d’auko plet d’inda tasiyo a kasuwa , a cewarta bazata dinga cin abinci a kwano mai tsatsa ba , bayan ta d’ibarwa Umma tata ta shige d’aki da sauran tanaci hankalinta kwance , bayan tagama ci taji bata k’oshiba , komawa tayi kwanonda
tazubawa, Umma ta d’ebo kad’an tarugo da gudu taje ta wanke kwanukan duka ….✍️✍️✍️
*TABBAS ALK’ALAMI ✍️YAFI TAKOBI????*.
_Alk’alamin mom islam✍️._
*Please share ????*
*Comments*
*vote*✔️
????????NANCY Y’AR K’ARYA????????.
_labari mai d’auke da nishad’i tareda fad’a karwa._
_story and writing_
By
*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*
PAGE 3_4
___Umma na dawo wa tasamu ankai mata abinci a kwano k’ato , ganin haka tafara sawa Duduwa albarka , Duduwa na ganin haka tafara mur mushi, bayan Umma ta bud’e kwanon ‘ne taga indomie da k’awai a k’arshen kwano , zaro ido Umma tayi kana ta dubi Duduwa tace” wato fad’an danake yimiki baya shigarki kenan? kina y’ar talaka amma kin d’auki buri kin d’orawa kanki , kuka Duduwa ta k’a k’alo tana bawa Umma hak’uri ,
Suna cikin haka ne sai ga sallamar dillaliya nan , Duduwa najin muryar ta aikuwa ta rugo a guje tana oyoyo hajiyar mu ,
da fara’a dillaliya ta tari Duduwa tana cewa zuwan danayi yau gurinki nazo ,
Washe baki Duduwa tayi tace “wallahi dama ina nemanki ‘ido rufe sekuma gaki , dillaliya ce tace” to mu k’arasa ciki , cikin fara’a suka k’arasa d’akin Umma ,
Bayan sun gaisa da Umma ne dillaliya take gayawa Umma maganar zuwan Duduwa birni ya taso , farinciki ne ya lulu6e Umma tace ” alhamdulilah haka akeso ,
Dillaliya ce tace” kinga gidan da Duduwa zata sauka sunbada kud’i dubu hamsin , zaro ido Duduwa tayi kana tace ” har anfara biyana kud’in ‘ ne tunkafin infara zuwa?
Dariya dillaliya tayi kana tace ” a’a sunce dai za’a siya miki kayan sawa masu kyau , dakuma hijabai da gyalu luka suma masu kyau,
Tsalle Duduwa tayi tana dariya , Umma dake gefe tace”nidai nasihata kullum itace ki kulada mutuncin ki , insha Allah Duduwa ta amsa , bayan dillaliya tabawa Umma kud’in , Umma tak’i amsa tace”Duduwa ta shirya suje kasuwa suyi siyayya , tunda tafiyar gobe ce ,
A yaudai farincikin da Duduwa take ciki baya fad’uwa saboda yau ko rashin kunya bata yiwa Umma ba , nan tafara had’a kayanta tana kyautar wa saboda duk sun kod’e ,
Shirin zuwa kasuwa tayi , bayan sunje ne dillaliya ta za6o mata wasu riga da skirt na kanti masu kyau sunkai kala goma , sai atamfa kala biyar sannan pants da bra sukuma rabin dozin tasiya mata yadin hijab suka tsaya aka d’inka da takalmi masu kyau , tunda suka dawo gida bakin Duduwa yak’i rufuwa saboda ita burinta taganta cikin kayan ba zuwa birni yin aikin ba ,