HAUSA NOVELWANI LABARI Complete Hausa Novel

WANI LABARI Complete Hausa Novel

1__
abun yana matukar bani mamaki hade da
bani dariya musamman idan naji al’umma
suna kuranta soyayya. Abun har kunya yake
bani musamman idan naga wani ya shiga
bacinrai akan soyayya. Ban sani ba ashe nima
soyayya ba mantawa tai da shafinaba sai dai
kuma soyayyar data tashi budo shafina saita
budomin bakin shafi wanda bansan ta ina zan
fara sarrafa linzamin soyayyar ba. Lokaci daya
khadeeja ta shiga zuciyata ko kuma ince muku
ummey domin dashi a saba kiranta. Duk da
cewar unguwarmu daya kuma layinmu daya
da ummey bamu cika yima juna magana ba
domin ni ko kadan banason raini ya shiga
hanyata sai bayan ummey ta dan tasa nima
shekaruna sunja. Sai na fahimci ummey ba
yarinyace mai raini ba kawai tsantsar
alkunyace a tattare da ita. Hakika ummey tana
da fasalinta na kyau dolene nasata a jerin
masu kyan diri bawai dan zuciyata tana
bukatar kasancewa a tare da itaba na tabbata
duk wanda yai ido biyu da ummey dolene ya
yaba surarta. Ummey bata da wata abokiyar
yawo wadda ta wuce anti zainab yayata kenan
wannan al’amarin yana matukar burgeni ganin
yadda zainab ta dauki ummey tamkar
kawarta. Ummey takan shiga gidanmu tayi duk
abunda taga dama kamar yadda antita zainab
take gudanar da harkokinta a gidanmu.
Tabbas zuciyata tayi matukar kamuwa da son
kasancewa a tare da ummey a matsayin
wadda zata kasance uwar yayana. Amma sai
dai nakasa samun hanyar da zata kasance
mafi sauki wajan cimma burina na samun
tabbataccen wajan zama a zuciyar ummey.
Tabbas ni kaina nasan ummey tafi karfin ajina
ganin hakane yasa na nemi tausar zuciyata ta
hanyar mantawa da ita amma ina hakan bazai
taba yuwuwaba domin ako wace rana nakanyi
ido biyu da ummey fiye da sau talatin kai
banmasan iyakaba kuma duk sanda zanganta
sai shaukin sonta ya sake sabon toho a
zuciyata. Gaisuwace kawai take hadani da ita
idan ba wannan ba bazan iya cewa ga wata
maganar data taba hadani da ummey ba
tabbas zuciyata tana matukar girmama
ummey fiye da anti zainab amma saidai
zuciyar tawa bata da ikon fito da wannan
girmamawar a fili ta yadda ummey zata
fuskanta a wannan lokacinne na fahimci
girman soyayya. A yayin danabi duk wata
hanyar data dace wajan mallakar numbar
ummey saina sayi sabon layin MTN ako wace
rana nakan tura mata da sakonnin jan hankali
kamar sau ukku domin cimma burina sai da
na dauki kimanin sati ukku ina aika mata da
sakonni iri-iri amma ban taba ganin replay
dinta ba furucin da taimin a karshe ba kadan
yasani kukan zuci ba. Da sassafe na dakko
layin dana saba aika mata da wannan sakonni
da kudurin aika mata da sakon barka da
safiya koda na dora layin sainai arba da
sakonta cikin yanayin shauki na bude sakon
abunda tace shine “dan Allah dan Annabi
idan kana ganin girman iyayenka kayi hakuri
ka daina aikomin da wadannan sakonnin. Nan
take naji duk ilahirin jikina ya mutu kamar
wanda aima dukan kawo wuka. Duk da haka
ban hakuraba. A wannan lokacin karamar
wayace dani kirar nokia E72 duk da cewar ba
wani dadin hawa social network zanji da ita
ba haka na bude sabon account a shafin
facebook da boyayyan suna nayi amfani kafin
kowa ya sanni dashi a yanzu wato Young
Uzee ummey itace farkon wadda na farayin
adding kaina tsaye nashiga bangaran search
dayake bansan cikakken sunan da take
amfani dashiba sai nayi amfani da numbar
wayarta wato waddana saba aika mata da
sako a baya kenan saboda ina kyautata zaton
dashi ta bude account din koda na rubuta
numbar nan take nayi ido biyu da account
dinta cikin gaggawa na aika mata da frnd rqst
saida a dauki tsawon kwana takwas sannan
na samu karbuwa a matsayin frnd dinta duk
da hakan dai ban tsiraba domin bansan
adadin maganar da nai mata ba amma shiru
babu replay har raina ya fara kuna saina tuna
ummeyfa kyakkyawace dolene al’umma suyi
mata katutu/yawa ta hanyar aika mata da
sakonni iri-iri wanda hakan zaisa taki tsayawa
dan karanta sakon kowa daya bayan daya.
Ganin hakane yasa na aika mata da sakon da
zai jawo hankalinta zuwa gareni. Abun da
nace shine {“haba malan sam wannan ba
halin mutun nagari bane kaji tsoran Allah ka
rufe wannan account din. yanzu a matsayinka
na musulmi meye amfanin bude account da
sunan mace hade dasa hotan wadda bakasan
ko waceceba kaji tsoran Allah ka daina amma
kayi hakuri idan na batama rai”} bayan 7
minutes da aika mata da wannan sakon. Sai
replay dinta ya shigo wayata abun da tace
shine {“subhanallah dan Allah karkayi tunanin
wannan account din na wanine to bana kowa
bane face nawa kuma ni macece kuma hotan
daka gani a profile dina bana kowa bane face
nawa”} sai nayi mata replay nace {“dan Allah
ummey kiyi hakuri wallahi nasan wannan
account din nakine banawani namiji ba kawai
na rasa yadda zanyine domin naga kin kulani
a matsayina na frnd dinki a kalla nayi miki
magana tafi ashirin ba tare da nayi kacibus da
replay dinkiba hakane yasa nayi miki wannan
maganar sai gashi kuma nayi sa’a kin kulani
dan haka wallahi ko yanzu kiyi blocking dina
bazan wani damu ba tunda har nayi nasarar
magana da kyakkyawar mace kamarki”}
hakika na dauka zata fadamin wata
mummunar magana sannan tayi blocking din.
Amma sai naga sabanin haka. Murmushi tayi
tace {“humm”} ba tare da furta wata kalmaba.
Sai nace {“to amma ummey ko zan iya sanin
abunda yasaki murmushi haka cikin kankanin
lokaci mai makon ki nuna bacin ranki akan
abun da nai miki?”} Sai tace {“kawai
salankane ya burgemi.} Wannanne yasa
najawo hankalin ummey zuwa gareni. Yanayin
yadda nake chating da itane yasa ta kagu taji
muryata numbarta ta turomin tace dan Allah
na kirata ko kuma nayimata plashing domin ta
kirani anannefa na fashinci wannan hanyar
bazata taba bullewa dani ba domin muddun
nayi kuskuran kiran ummey a waya to babu
makawa saita ganeni ni kuma hakane banaso
domin kuwa so nake sai munyi matukar
shakuwa da juna sannan zan bijiro mata da
ainashin kudurina a kanta. Hakane yasa gaba
daya nayi forget din facebook dina domin
canza wata sabuwar hanyar wadda kuma
nake kyautata zaton zata bulle dani. Kwatsam
wata ranar asabar musalin 5:00pm nayi
wankana kamar yadda na saba zan fita kenan
sai nayi kacibus da abbana ayayin da yashigo
gida wani kallo naga yaimin hade da cewar
kasan yaune za’a fara aikin gyaran gidannan
amma saboda tsabar wulakanci tun dazu nake
nemanka ban samu ganinkaba gudun karna
batawa masu aikin lokacine yasa na daga
aikin zuwa gobe saboda key din dakin da’a
aje simintin yana wajanka dan haka maza kaje
ka dakko key din ka fito da gaba daya
simintin dake dakin ba yadda na iya duk da
wankan da nayi haka na bude dakin na fara
fito da simintin dake dakin tabbas buhun
siminti ba karamin nauyine dashi ba a yayin
dana dakko na farko dakyar na iya fitowa
dashi waje koda ummey tazo wucewa ta kusa
dani tare da anti zainab sai Allah ya jarabceni
ta hanyar taka wani dutse bansan lokacin da
wannan simintin yaje kasba koda kurar
wannan simintin ya dan budesu cikin yanayin
wasa ummey tace “kash dadina da yaran
zamani sun fiye gaggawa kasan karfinka
baikai ba taya zaka dauki wannan simintin
gashi har kana neman batamu da kura. Koda
na dago kai na kalleta sai nayi dariya hade da
cewar zan ramane yarinya tun daga wannan
lokacin sai wasa ya fara shiga tsakanina da
ummey.
=> 2
haka naita nazarin hanyar da zata haifar da
wasa a tsakanina da ummey amma kwata-
kwata na rasa. Kwatsam wata rana ina zaune
a falon gidanmu ranar banje ko inaba haka na
tasa set light da kallo. Karar bude kofa naji
dubawar da zanyi sai kuwa nayi ido biyu da
ummey bayan tayi sallama na amsa mata
kanta tsaye ta wuce dakin anti zainab ko
cikakken 3 minutes da shigarta ba aiba sai
gata ta fito da zuwanta gareni kamar zata
zauna a kusa dani sai tace “kaga dan
komacan inason nai kallone. Kallonta nayi tun
daga sama har kasa sannan nace ” ummey
idan har na tashi rama wulakancin da kikemin
to babu makawa sai kin koka dani. Murmushi
naga tayi sannan tace “au da yayar taka kake
sa’insa to dan Allah karka janye wannan
kudurin naka mu fara daga yau. Saina jinjina
kai sannan na tashi na bata wuri. A kalla an
daki kimanin 1 week da faruwar haka kwatsam
da musalin karfe 8 na dare nazo wucewa a
kan hanyata ta komawa gida dayake layin mu
daya da ummey a yayin da nazo dai-dai kofar
gidan su ummey sai kuwa muyi ido biyu da
juna a yayin da take tsaye da wasu samari
biyu a matsayinta na wadda nake so kokuma
ince wadda nake kauna ko kadan ban waji ji
haushin kasancewarta a tare da wadannan
mutanan ba domin duk mai kaunar abunda
nake kauna shima masoyinane amma sai nayi
amfani da wannan damar dan rama abunda
tayimin da isata gida ba inda naci burki sai a
dakina wasu tsofaffin magungunan da wani
doctor ya taba rubutamin na dakko kati biyu
wadan da nima kaina na manta adadin
dadewarsu a wajena cikin yanayin kwarin
guiwa na fito daga gida da zuwana inda suke
nai sallama kamar yadda addinin musulunci
ya tanadar mana cikin yanayin sakin fuska na
mika musu hannu mu gaisa. Haka nasa
hannuna a aljihu na dakko wannan maganin
koda na kalli ummey sai nace “ummey dama
dazune anti zainab ta aikoni wajanki domin na
karbar mata sakon data baki, sai kuma ayi
rashin sa’a a wannan lokacin bakyajin dadi
sakamakon gudawar da take damunki hakane
yasa ban samu damar ganinki ba sakamakon
a wannan lokacin kina toilet saboda gudawar
ta matsa miki shine abbanki ko kuma ince
abbanmu ya aikeni domin na siyo miki
wannan maganin saboda yasan bakya shiri da
allura. Nanfa ummey tamin wani kallo cikin
yanayin bacin rai tace ” kaga karka sake
yimin irin wannan. In banda tsabar wulakanci
yaushene na kamu da wata rashin lafiya balle
ayi batun gudawa ina gudawarne zan dauki
tsawon wannan lokacin a waje. Koda naga
alamun bazata karbi maganin ba kaina tsaye
nashiga gidansu. Saidai kuma na dauki
tsawan lokaci rabona da shiga gidan da
shigata sai kuwa nayi kacibis da mahaifinta a
harabar gidan bayan mun gaisa cikin yanayin
sakin fuska yace “yau kuma kaine a gidan ai
na dauka ka manta damune sai nayi dariya
nace ” abba ai ba yadda za’ai na manta daku
nima kaina nasan ban kyautaba yanzu nazo
wucewa saina hadu da ummey anan kofar
gida shine take cewa ai bani da mutunci
kullun zataje gidanmu ammani banason zuwa
gidansu hakane yasa na shigo domin na
wanke wannan laifin a idonta sai yai dariya
hade da cewar aikon ta kyauta. Haka na
karasa ciki na gaisa da mahaifiyarta sannan
na fito koda na dawo gareta sai nace “ummey
abba yace kije yanason ganinki ba yadda ta
iya haka tayi bankwana dasu ranta a bace.
Bayan sun tafi sai nace ” ummey ai bai
kamata ki nuna bacin ranki akan wannan
kankanin wulakancin ba domin tun farko ke
kice muzuba mugani. Sai ta jinjina kai hade
da cewa “hakika kayimin wulakancin da yai
matukar konamin rai amma kasani muddun
ina raye babu abunda zai hanani rama
wannan cin mutuncin da kaimin a wannan
lokacin saida mu dauki kimanin wata daya ba
tare da mun sake yima juna maganaba
kwatsam wata rana zamu garin kaduna daurin
auran wani kanin mahaifiyata mutuncin da
yake tsakanin gidanmu danasu ummey ne
yasa ummey ta bimu wannan bikin ashe raban
za’a samu dai-daito tsakanina da ummey ne
muna cikin tafiya sai nace ” anti karfa ki
manta da kudin da kice zaki cikamin domin
siyan wayar da nake bukata budar bakinta sai
tace “kaga karfa ka takuramin tunda nace zan
baka kawai ka zuba ido mana da isarmu
kuwa haka na sake tambayarta batun kudin
domin na kagu naga iPhone 6 ta shiga
hannuna nan take ta hauni da masifa hade da
cewar na bari saimun koma gida ganin hakane
yasa ummey ta nuna tausayawarta a gareni
koda ta kalleni sai tace “nawane cikon kudin
da zata baka cikin yanayin bacin rai nace 8
thousands ne sai ummey tayi dariya sannan
tace “indai dan 8 thousands ne to karka damu
ni zan cikama da yake akwai wani shagon
saida wayoyin dana sani a kasuwar bacci
dake kaduna haka mutafi tare da isarmu
bayan anyi cinikin waya iPhone 6 akan kudi
naira dubu 67 sai kuwa ummey ta karbi kudin
dake hannuna ta cika naira 8,000 sannan ta
mikawa mai waya nannefa na gane cewar
ashe ummey gadar zare ta shiryamin domin
daukar fansar wulakancin da nai mata a baya
domin kuwa sunanta naji tace asa a resit din
haka na zuba ido a kammala komai a gaban
idona sannan ta kalleni tace ” nagode yayana
kasiyamin waya. Cikin yanayin nadama nace
dan Allah ummey kiyi hakuri nasan nayi
kuskure amma daga yau babu yadda za’ai na
sake aikatamiki abunda zai haifar da bacin rai
a tattare dake murmushi naga tayi sannan
tace da zakayi hakuri ka cire wannan wayar
daga zuciyarka zaifiyema komai dadi domin
wahalar da kanka kawai kakeyi koda taga
alamun zan takura mata nan take ta damka
wayar a hannun wannan mutumin tace “malan
ka’ajemin wayarnan na tsawon wata biyu
sannan ta damkamai 2 thousands a matsayin
kudin ajiyarshi inaji ina gani haka nayi
bankwana da kudina ba tare da cikon burina
ba. Bama wannanne yafi damuna ba illa
rashin sanin hanyar da zan bullo mata dan
ganin sakon zuciyata ya isa gareta abunda
nake nufi shine nasamu soyayyarta. Amma
duk da haka ban ja da baya ba haka muci
gaba da yima junanmu wulakanci mai kama
da rashin mutunci.
=> 3
Haka ummey taita min dariya domin tasan
dolene raina ya baci ganin yadda mu koma
gida ba tare da ummey ta karbi wayar bane
yasa na tabbatar da cewar eh lallai babu
yadda za’ai ta bani wannan wayar balle ayi
batun dawowar kudina. Duk da irin wannan ta
addancin da ummey taimin baisa taja da baya
wurin ci gaba da yimin abunda taga dama ba
bazan taba mantawa da wata ranar monday/
litinin ba ranar mahaifiyata da abbana
basanan sunyi wata tafiya garin bauchi haka
na dawo gida a yunwace koda na duba inda
asaba ajemin abinci banga komaiba face
emptying plate haka na shiga dakin anti
zainab cikin yanayin damuwa nace “wai anti
baki girka mana komai bane? Budar bakinta
sai tace ni baiwarkace da zan zauna naima
girki. Cikin yanayin sakin fuska nace ”
ammafa zainab baki da mutunci. Wani kallon
hadarin kaji taimin hade da cewar a ina kuma
ka manta antin da zaka kira sunana kaitsaye
ba girmamawa? Budar bakina sai nace “ai
idan har kiga yara suna kiran yayarsu da anti
to ki tabbata tana kyautata musune ammake
ko kadan wannan sunan bai kamaceki ba
domin bana samun wannan kyautatawar daga
gareki. Koda naga alamun ranta ya baci sai
nace ” haba antita dawasafa nake miki domin
nasan bazaki rasa yan kudin da zaki baniba
domin naje na samu dan abunda zanci.
Dakyar na shawo kanta ta dauki two hundred
#200 ta bani domin naje naci abinci ba yadda
na iya haka na karbi wannan kudin
majalissarmu na nufa domin nasan acan
bazan rasa abunda zan siya ba da isata ko
zama banyi ba nace da maryam mai shin kafa
ta kawomin ta dari hade da coke mai sanyi da
kawowarta ko faraci banyi ba saiga musta
bangis abokina kenan yazo gareni a gaggauce
wayar dake hannunshi naga ya mikomin hade
da cewar wata yarinyace mai suna aisha
takeson magana dakai haka na tashi na koma
lungu domin jin ko wacece ban saniba ashe
tun daga nesa ummey taga lokacin da’a
kawomin wannan abincin da zuwanta ta dauki
wannan abincin hade da coke din ta
damkawa almajirai tace “ku karbi sadaka.
Tabbas bayanin da naji daga bakin aisha
wadda nai waya da ita kenan ba kadan ya
jefani a rudani ba. Haka na dawo wurin
abincina kaina a daure. Koda na duba naga
ba abinci kuma ba coke sai na kalli bangi
hade da sauran abokaina nace ” ina kuma
abincin nawa? Budar bakin bangis sai yace
“gashican a hannun almajirai cikin yanayin
fusata na daka musu tsawa! Cikin yanayin
dariya nuhu ya dafa kafadata yace ” kaga
abokina karkaga laifinsu domin ummey ce ta
dauka da hannunta ta basu. Saina jinjina kai
nace “ammafa wannan yarinyar tafini
wulakanci. Haka bangis ya karbarmin wani
abincin daga wajan maryam. Inacin abincin
ina tunanin maganar da aisha ta fadamin
bayan naba bangis wayar sannan nace ” dan
Allah ya tabbata yayi saving din numbar
domin ina bukatar sake magana da ita bayan
kwana ukku da faruwar haka musalin karfe
5:00pm ina zaune a kofar gida saiga ummey
tazo gareni kaida ganin fuskarta kasan akwai
damuwa a tattare da ita kusa dani ta zauna
koda naga idanuwanta duk sun canza daga
yadda na saba ganinsu sai nace “amma
ummey ban taba ganinki a cikin irin wannan
yanayin ba ko zaki iya sanar dani abunda
yake faruwa? sai tace “tabbas na aikatama
laifi mafi muni domin abbana ya fasa wannan
wayar daka siya a garin kaduna. Kuma wallahi
ban hanaka wayar domin ta zama mallakinaba
kawai na hanakane domin na gane shin
soyayyar da kakemin gaskiyace ko kuma wasa
kakeyi domin tun daga lokacin daka fara
aikomin da wadannan sakonnin na gane
cewar ba kowa bane yake aikomina da
wannan sakon illah kai cikin yanayin mamaki
nace amma ummey taya ai har kisan da
cewar nine nake aikomiki da wadannan
sakonnin?
=> 4
Ummey tace wata ranar juma’a lokacin ina
zaune tare da zainab a falon gidanku koda
zainab taji karar horn din motar abbanku cikin
yanayin tsoro naga ta afka dakinka da sauri
ganin hakane yasa nabi bayanta dan jin
abunda yake faruwa cikin yanayin mamaki
nace amma zainab lafiya kuwa naga kin shigo
nan a tsorace? Budar bakinta sai tace
“wallahi tun dazu abba ya kirani a waya yace
na dakkomai wasu takaddu a durowarshi
kuma shaf na manta nasan idan yai ido biyu
dani sai nasha fada da shigowar abbanku
bayan yai sallama sai ya fara kiran zainab
amma zainab sai tai shiru ba tare data
amsaba Allah cikin ikonsa sai kira ya shigo
wayarta cikin yanayin furgici ta jefar da wayar
haka wayar tai watsa-watsa ba tare da sanin
wa yake kiranta ba ashe tuni karar wayar ta
isa kunnan abbanku a wannan ranar ba kadan
zainab tasha fada ba bayan abbanku ko kuma
ince abbanmu ya dauki abunda zai dauka ya
fita sai zainab tace naje na dakko mata
wayarta a tsakar dakinka naga wayar batirin
hade da marfin kuma a karkashin gadonka na
dakkosu amma Allah baisa naga naga layin ba
wani littafin geography na gani a kasa koda na
dagashi sai naga layin MTN ya fado kasa
kasancewar bansan layin da take amfani
dashi bane yasa na dorashi a wayar tata da
yake wayar irin karamar nokiyar nance ina
kunnata ta kawo bayan na damka wayar a
hannunta sai tayi kokarin duba wannan
numbar da’a kirata kafin ta jefar da wayar
kenan amma bataga numbar kowaba face
numbata koda ta shiga bangaran message sai
taga sakonnin da ba ita ta turasuba sai ta
kalleni tace “ummey wannan ai ba layina
bane kuma ni ai airtel nake amfani dashi ba
mtn ba duk yadda ai wannan layin brother
dinane domin na tabbata wadannan sakonnin
babu wanda zai turasu face shi. dariya naga
tayi a yayin data kalleni sannan tace ummey
yashe ku fara soyayya cikin yanayin mamaki
na karbi wayar na duba hakane ya
tabbatarmin da cewar kaine kake aikomin da
wadannan sakonnin a wannan ranarne na roki
zainab akan karta nuna wata alamar da zatasa
kagane mun duba wannan layin naka. Sannan
na bukaceta data kauda kanta akan duk kan
wani abunda zai faru a tsakanina da kai. Haka
naita yima abubuwan da zasusa ranka ya baci
amma domin auna mizanin soyayyar da
kakeyimin a zuciyarka wanda hakan ta
tabbatarmin da cewar lallai kana matukar
sona a karshe saina yanke shawarar komawa
kaduna domin karboma wayarka haka na tafi
ba tare da kowa ya saniba domin ko
mahaifiyatama bata sani ba balle abbana sai
a samu akasi a yayin dana isa garin kaduna
ba inda na tsaya sai a shagon damu sayi
wayar akasin da’a samu shine ban samu
shagon a bude ba domin a rufe na sameshi da
yake ya rubuta numbar wayarshi a gaban
shagon sai nayi kokarin kiranshi koda ya daga
bayan mun gaisa hade da sanar dashi dalilin
kiranshi a wannan lokacin sai yace to gaskiya
yanzu haka yana zaria daurin auran wani
abokinshi haka na zauna zaman jiranshi har
ya dawo ba kuma shi ya dawo ba sai musalin
karfe 5 ban saniba ashe abbana ranshi yayi
matukar baci sakamon rashin ganina in
takaicema dai bani na dawo gidaba sai
musalin karfe 8 na dare da shigata falo sai nai
kacibus da abbana cikin yanayin damuwa
hade da bacin rai yace “ummey daga ina
kike? Sai nai shiru ba tare dana bashi amsaba
domin na tabbata idan na sanar dashi inda
naje raina ba karamin baci zaiyi ba gudun kar
raina ya bacine yasa naimai karyar zainab na
raka zaria. Jinai ya daukeni da mari hade da
cewa munafukar banza kawai ni zaki rainama
hankali a kalla na kira wayarki yafi a kirga
amma sam bata shiga. Muryata tana rawa/
bari. Nace “abba babu cajine. Jinai ya
dakamin tsawa hade da cewa ina wayar take?
Cikin rawar jiki nasa hannuna a aljihu domin
dakko wayar sai a samu akasi na dakko
wannan iPhone din koda abbana yaga iPhone
a tattare dani sai yace ” ummey a ina kuma ki
samo wannan wayar? Cikin yanayin kidimewa
nace “au! Abba ba ita bace wannan. Wani
kalar kallo naga abbana yamin hade da cewar
ummey a sanina wannan wayar mai matukar
tsadace kamar yadda nasan bana baki kudin
da zasu sa har ki sayi wannan wayar haka na
tabbata bazaki samu kudin wannan wayar
daga wajan mahaifiyar kiba dan haka ki
gaggauta sanar dani yadda ai ki samu kudin
da kisayi wannan wayar. Cikin yanayin kuka
nace ” wallahi abba ajiyarta abani. Ban tashi
auneba sai jinai ya bugata da kasa sannan ya
nunani da yatsansa yace ko wayar uban waye
ya sake ganinta a tattare dani to babu
makawa sai ya fasata kuma yaci mutuncina.
Bayan ta gama bani wannan labarin sannan ta
kalleni hade da cewa bansan wane irin hakuri
zan bakaba a dalilin faruwar wannan
al’amarin. Sai nayi murmushi nace “haba kefa
tamkar kanwata na daukeki dan haka zan iya
sadaukar miki da koma menene. Sai dai kuma
ummey akwai wani bakon al’amari wanda ya
jefa zuciyata a rudani ko kuma ince sarkakiya
wanda nake ganin muddun hakan ya kasance
gaskiya to zuciyata zata iya cutuwa. Cikin
gaggawa ummey tace ” yayana dan Allah kayi
gaggawar sanar dani wannan sarkakiyar. Sai
nace “ummey akwai wata yarinya kokuma
ince budurwa mai suna aisha wadda ta kira
wayar abokina bangis da bukatar magana
dani bayan bangis ya kawomin wayar
maganar da naji daga bakinta ba kadan ta
girgizani ba. Bayan mun gaisa sai tace ” kai
dan uwanane dan haka bazan taba bari ka
cutar da zuciyarka wajan fadawa soyayya da
wadda aure bazai taba kasantuwa a
tsakaninka da ita ba dan haka ina mai
tabbatarma da cewar har abada babu aure a
tsakaninka da wadda kake shirin fadawa
soyayya da ita wato ummey domin addinin
musulunci yayi hani da hakan na bude baki
zanyi magana kenan sai ta yanke wayar.
Saina kalli ummey nace “babban abunda
yake dauremin kai shine taya ai tasan akwai
soyayyarki a cikin zuciyata kafin na bayyanata
a gareki kuma ta wace hanya ta samu numbar
abokina bangis sarkakiyar da nake ciki itace
shin dagaskene babu aure a tsakanina dake?
Sai ummey ta girgiza kai hade da cewa
meyasa kake kokarin haifarma zuciyarka da
damuwa kafi kowa sanin cewar babu wata
dangantakar da zatakawo batun hana aure a
tsakanina da kai dan haka kamar yadda na
dauki wannan maganar a matsayin shirme
zanso kaima kayi kokarin daukarta a matsayin
hakan.
=>5
Tun daga wannan ranar komai ya sauya a
tsakanina da ummey lokaci daya ta janye
kanta dangane da batun yawo tare da anti
zainab sai ya zamto ba kowane abokin
rakiyartaba face ni tun ina dan nuna jin kunyar
jerawa tare da ummey a matsayina na bakon
soyayya rannan kuwa sai ummey ta kalleni
tayi murmushi hade da cewa na fahimci kana
matukar jin kunyar jerawa tare dani
musamman a yayin dana bukaci rakiyarka a
gareni to amma ni a ganina hakan ba wani
abun kunya bane a matsayinmu na masoyan
juna kuma ta wani bangaran ni tamkar
kanwarka nake domin gidanmu da naku ya
zama tamkar daya duba da yadda iyayanmu
suke mutunta junansu wanda hakan yasa nake
aikata duk wani abunda naga dama a gidanku
ba tare da ahalinka sun nuna wata damuwa
ba abun yana matukar bani haushi ganin
yadda kai baka damu da zuwa gidanmu ba
kamar yadda na maida gidanku tamkar
gidanmu zanso kaima kayi kokarin daukar
gidanmu tamkar gidanku kamar yadda
nakeson ka cire duk wata kunyar da take
tsakanina da kai haka dai soyayyarmu taita
bayyanuwa a idon kowa ko wace safiya
mukan turawa junanmu da sakon barka da
safiya ta waya idan dare yayi bama taba yin
bacci ba tare da munyi waya da juna ba.
Kwatsam wata rana muna cikin fira nida
ummey da musalin karfe 8:30pm sai calling..
Ya shigo wayata. koda naga bakuwar
numbace ban wani bata lokaciba cikin
gaggawa na daga kiran muryar mace naji
ayayin da tai sallama a gareni. hakane yasa
na gane ko wacece domin ba wata bace illa
aisha. budar bakinta sai tace wato har yanzu
kananan akan bakanka kenan to bari kaji
wallahi wahalar da kanka kawai kakeyi domin
ummey bazata taba zama matarkaba. Cikin
yanayin bacin rai nace kinga wallahi muddun
nayi ido biyu dake wallahi ina mai tabbatar
miki da cewar sai kinyi matukar raina kanki.
Dariya naji tayi sannan tace “ai bansan zaka
iya aikata hakanba domin yanzu na wuce ta
kusa daku nan take na sauke wayar daga
kunnena na fara waige-waige domin tabbatar
da maganarta koda ummey taga ina waige-
waige sai tace ” yayana lafiya kuwa, me kuma
ya faru? cikin yanayin mamaki nace ummey
kinga wata ta wuce tanan yanzu sai ta danyi
shiru na dan wani lokaci sannan tace kwarai
kuwa akwai wadda ta wuce ta nan kusan
tsayinmu daya da ita tana sanye da wasu
kaya ruwan madara sanye da wani farin
gyale. Sannan ta kalleni tace “wai me yake
faruwa? Bayan na sanar da ita duk abunda ta
fadamin driya naga ummey tayi sannan tace ”
ko wacece wannan to babu abunda zata karu
dashi face bakin ciki hade da takaici. Haka
mu dauki wannan maganar a matsayin shirme.
amma duk da hakan zuciyata bata gaza wurin
afkawa cikin katafaran rudanin yadda ai har
wannan addababbiyar yarinyar ta samu
numbata ba. maimakon mutsaya muyi dogon
bincike a kanmu kawai sai muci gaba da
soyayyarmu ashe maganar aisha tana kama
da gaskiya koda a tsakanin iyayan ummey da
iyayena mahaifiyatace ta fara gane cewar
akwai soyayya a tsakanina da ummey. Cikin
dare musalin karfe 11:00pm mahaifiyata ta
shigo dakina. koda ta tasheni daga bacci cikin
yanayin mamaki nace “umma lafiya kuwa? Sai
ta jinjina kai tace ” lafiya kalau nazo garekane
da wata bukata a matsayina na mahaifiyarka.
Cikin gaggawa nace “umma ki fadi duk wata
bukatarki nayi miki alkawarin zan biya miki ita
domin nasan bazaki taba tunkarata da bukatar
da zatafi karfina ba. Budar bakin mahaifiyata
sai tace ” meye alakarka da ummey? Nan
take na sumkuyar da kaina kas, na dauka
wannan ita kadaice bukatarta a gareni. cikin
kwarin guiwa nace “umma ba wani abu bane
a tsakanina da ummey illa soyayya. Sai tace ”
to indai har kanajin maganata a matsayina na
mahaifiyarka zanso daga yau ka dakatar da
wannan soyayyar taku kuma karka bari ta
fahimci cewar nice makasudin faruwar hakan
balle wasu daban kai ko yayarka zainab
banason tasan da wannan maganar domin
banason hakan yai sular daina shigowar
ummey gidannan. Cikin yanayin rudani nace
“to amma umma ni a sanina mafi yawanci
iyaye sukan hana yayansu auran wadda
sukesone saboda wasu dalilai ko wani dalili.
Amma sai gashi ke da kanki kin nemi na guji
ummey ba tare da kin sanar dani dalilin
hakanba kuma ta wani bangaran sai naga
kamar ummey bata aikata wani laifin da zaisa
ki nemi rabani da itaba saboda naga alamun
kina matukar kaunarta wanda hakan yasa
bakyason wani dalilin da zaisa ta daina
shigowa gidannan. Sai na kalleta nace ” dan
Allah umma ki sanar dani abun daya faru? Sai
ta girgiza kai hade da cewar na riga na
daukar wa mahaifinka da iyayan ummey
alkawarin bazan taba sanarma kowa wannan
sirrin ba dan haka kawai kayi hakuri ka
biyamin wannan bukatar tawa ba tare da kaji
komai ba. Nan take hawaye ya kwaranyo
daga idanuna. Cikin yanayin kuka nace
“umma karkisa zuciyata ta fara zarginki da
aikata ba daidai ba. Nan take tasa hannunta
ta share hawayen dake fuskata. Hade da
cewa ko kusa karka taba barin zuciyarka ta
zargeni da sabama ubangijinsa domin ban
taba aikata fasikanci ba kamar yadda kake
tunani. Sanannan ta tashi tayi waje ta barni
cikin rudani.
=> 6
Haka na kwana cikin rudani hade da
matsanancin tunani washe gari da sassafe
saiga ummey ta shigo kamar yadda ta saba
kanta tsaye ta shigo dakina a kwance nake
amma idona biyu duk da cewar babu wani
annuri a tattare dani haka na dan saki fuskata
cikin yanayin sakin fuska nace “ummey kardai
kice kinzo tashina baccine? Murmushi naga
tayi sannan tace “amma ya ai kasan abun
daya kawoni? Budar bakina sai nace ” ai
saboda zukatanmu sun riga da sun zama
dayane shine dalilin da yasa na fahimci haka.
Sai tace “kaga malan tashi kazo muje kayi
breakfast domin akwai inda nakeson ka
rakani. Bayadda na iya haka na fita ba’a son
rainaba domin ko kadan banason na batawa
mahaifiyata ranta gudun kar ummey ta fahimci
na fara ja da baya da itane yasa na fito.
Bayan nayi brush haka na zauna a falo ina cin
abinci ga kuma ummey ta zauna kusa dani
tanamin irin kallon da masoya sukewa junansu
mai kawar da kunci da bacin rai bayan na
kammala saina fita tare da ita domin rakata
inda take son zuwa bayan na dawo gida sai
na fahimci ran mahaifiyata yayi matukar baci
gaba daya saina rasa hanyar da zanbi
danganin na ciwa mahaifiyata burinta ba
tareda ummey ta fahimci komai ba duk da
cewar nasan hakan ba abune mai yuwuwaba
amma ko kadan zuciyata bata daina nazarin
neman mafita ba. rana daya nayi duk wani
shirina na tafiya garin jigawa amma sai dai
kuma ina duba yiwuwar tafiyar da zanyi zata
dauki dogon lokaci domin bana tunanin cewar
zan dawo har sai lokacin da ummey tayi aure.
Koda na sanar da iyayena batun tafiyata da
kudurin bazan wuce sati daya ba. Sai suyimin
fatan alkairi hade da sa albarka a gareni.
Ummey har zubar da hawaye tayi a dalilin
wannan tafiyar tawa inaji ina gani haka nayi
bankwana da abar kaunata wadda ko tuntube
batason taga nayi a yayin da muke tafiya tare
da juna. Tafiya nake amma ina tunanin irin
soyayyar da mukewa junanmu hade da
tunanin halin da ummey zata tsunci kanta a
yayin da taji shiru ban dawoba. Duk da irin
wannan tunanin da zuciyata take ciki bai
hanani tafiyaba badan komaiba sai dan
cikawa mahaifiya burinta saboda kokadan
banason mahaifiyata ta shiga damuwa a
dalilina amma sai dai kuma a zuciyata ba
jahar jigawa nake da kudurin zuwaba domin
kuwa jahar kebbi ce a zuciyata. Musalin karfe
1 na dare na sauka a kebbi state. Da saukata
nayi calling din abokina faruq wanda na hadu
dashi a social network wato facebook kenan
cikin kankanin lokaci faruq yazo gareni cikin
girmamawa ya saukeni a gidansu a wannan
ranar ne na sanar da faruq duk abun daya
faru dani hade da makasudin barowata gida.
Daga karshe kuma sai nace “faruq bana
muradin komawa gida har sai lokacin da
ummey tai aure shiru naga yayi na dan wani
lokaci zuwacan ya kalleni cikin tausayawa
yace ” tabbas kayi matukar burgeni tunda har
ka zabi farantawa mahaifiyarka fiye da son
zuciyarka dan haka zakaci gaba da zama dani
har zuwa lokacin da wannan burin naka zai
cika. Duk da cewar na nisanta da ummey
amma hakan baisa mun fasa yin waya da
junaba domin kullunne sai ummey tayi calling
dina hade da aikomin da sakon text message.
Nanfa na rasa hanyar da zanbi dan ganin
hakan ta daina faruwa kwanana biyar da zuwa
kebbi sai wata mota (kano line) tai accident/
hadari a yayin da take gaf da fita daga cikin
garin kebbi zuwa jahar kano abun takaici duk
jama’ar ciki basu rayu ba domin kuwa
konewa tai gaba daya babu wanda zaka iya
shaida fuskarshi. Sai nayi amfani da wannan
damar dan ganin na batar da rayuwata a idon
ummey ta wani bangaran kuma ina tunanin
irin hawayan da iyayena zasu zubar a yayin
da sakon mutuwata ya isa kunnansu amma
naji hausawa suna cewar da ruwan ciki akanja
na rijiya, domin kuwa sai an fuskanci wani
bacin ran sannan ake samun wani farin cikin.
Bayan mun shira komai ni da abokina faruq
saina damka wayata a hannunshi a gaban
idona ya damka wayar a hannun daya daga
cikin jami’an yan sandan dake wannan wajan
hade da cewa “yallabai ina tunanin wannan
wayar daya daga cikin mutanan da wannan
hadarin ya auku dasune. Ta wannan wayarne
sakon barina duniya ya isa kunnuwan iyayena
saboda wannan ita kadaice hanyar da zatasa
ummey ta auri wani ba tare data fahimci
komai ba.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button