ZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

Kuka take rusawa mai tab’a zuciyar duk wani mai sauraronta ,babu kuma alaman tayi niyan tsagaitashi, dan abinda yake damunta, yake ci mata rai yayi zafin da a ganinta idan ba kukan tayi ba baza ta samu sassaucin damuwarta ba.
Kawunta dake zaune bisa kujeran palourn ya zuba mata ido cikin k’unar zuciya da matsanancin b’acin rai, wannan Kuka da take yi ba k’aramin tab’a mishi zuciya yake yi ba.
Ji yake inama da zai iya magance mata damuwarta da yayi ko da kuwa shi zai zame masa damuwa. Yanzu babbar matsalar shi bai wuci rashin sanar dashi takamemmen damuwarta ba.
Cikin dak’ushewar murya wanda yake ji kamar Shima yasa kukan yace “Rumaisa, Kiyi wa Allah ki fad’a min damuwar ki, kukan ki yana d’agan hankali ,ki taimakeni ki fad’an damuwarki ko Zan samu kwanciyar hankali. ”
Volume na kukanta ta k’ara har tana shid’ewa ta kuma dad’a dukunkune kanta cikin katon hijabin da ke jikinta.
Cikin k’arin b’acin rai kawunnata ya dunkule hanunshi ya naushi kujera “Bull shit,”yace cikin karaji, Rumaisa Kiyi magana mana. ”
D’ago kanta tayi da niyyar yi mishi magana wani kukan ya sake sarke ta tayi saurin mai da kanta.
Tasowa yayi daga kujeran yazo ya durkusa a gabanta, cikin sassauta murya yace “Maisa, kasheni kike son yi ko? ”
Kai ta girgiza alamun A’a.
“To, Kiyi magana, fad’a min damurki Maisan Kawu. ”
Ya k’arashe maganar da rarrashi.
Cikin cin zuciya da sarkewar murya tace,” Kawu, Bobbo zai kasheni ,bazan iya ba na gaji ,wahalar ta min yawa kasheni yake son yi, bazan iya ba, bazan iya ba, na gaji Kawu, na……. ” Tana fad’a tana jujjuya kanta.
Numfashinta ne taji kamar zai d’auke ta yanke maganar taci gaba da shessheka.
“Me KABIRUn yake miki, Maisa, fad’a min me ya ke miki. “cikin tashin hankali da tafasar zuciya yake magana idanunshi sun rine da b’acin rai.
Ci gaba yayi da cewa “Maisa fad’amin abinda ya ke miki Wlh zan kashe aurennan, dole zan karb’a miki takardarki. ”
Maganarshi ta k’arshe tayi dadai da shigowar Kabeer, palourn idonshi a kansu.
Wani irin bugawa zuciyar Kabeer takeyi kamar ta fito, Kallon tsana ya bisu dashi dukansu biyu kafin ya yi hanyar d’akinshi.
“Kabiru! Kabiru!! kabiru!!!
Duk Wannan kira da yake jera mishi cikin b’acin rai da zafin zuciya baisa ya juyo ba shigewa d’akinshi yayi ya rufo k’ofa.
Bishi ya farayi Rumaisa tayi saurin tare shi “Kawu ka kyale shi zuciyarshi ba kyau kar Kuyi b’atacciya dashi. ”
“Zuciya? Waye bashi da shi, muyi abinda yafi b’atacciya ma in yaga dama, ba fa Zan kyale shi ba, Wlh akanki Zan iya aikata komai Maisa. ”
Ya na gama fad’ar haka ya tasamma d’akin Kabeer. Kwankwasawa ya shigayi yana kiranshi, idan ya amsa dutse ma ya amsa.
K’arshe ya shiga jijjiga kofar har ya gaji dan kanshi ya koma ya zauna yana huci yana surutai “Zaka fito ka sameni anan dan ubanka, ni ba sa’anka bane, badai kace kai d’an iska ba, Zan gwada maka kalar tawa iskancin. ”
ita dai Rumaisa ganin abin yana neman yafi karfinta ta shige d’akinta ta takure gu d’aya.
Saida Kabeer ya gama duk abinda zaiyi tukun ya fito, ga mamakinshi sai yaga Kawu bai tafi ba yana zaune.
D’auke kanshi ya yi ya wuce zai fita, cikin zafin nama Kawu ya sha gabanshi ya rike kwalar rigar shi.
Kallo Kallo suka shiga yiwa juna cikin tsantsan tsanar juna.
kawu ne ya fara magana “Wato ga d’an iska ko, ina maka magana, Kayi wucewar ka, yanzu kuma kazo ka d’auke kai kamar bakasan da mutum a nan ba, wai kabiru me kakeji dashi ne? Ko Ubanka bai tab’a min rashin mutunci haka ba balle kai. ”
Sai a snn Kabeer yayi magana “Shi dama mai mutunci ne, rashin mutunci kuma a wurinka na d’auko.”
Fizge jikinshi yayi da karfi daga rikon da Kawu ya mishi yana cewa “Mind u, kada Ka sake yi min irin wnn abin, ko baka ga wanka nayi yanzu ba kake son b’ata min jiki da datti. ”
Yana gama fad’an haka yayi waje da sassarfa ya bar kawu nan tsaye yana huci.
Motarshi ya shiga ya bata wuta.
Shiko kawu Kwafa yayi yace “Sai na raba aurennan dan Ubanka daga nan yasa kai Shima ya fita…
*Toh ????wai me yasa Kawun yake son kashe auren Maisan shi?*
*Me Kabeer yayiwa Maisa me zafinnan.?*
*Me yasa kuma yake cutar da ita?*
*Snn me yasa ya ciwa kawu mutunci?*
*Wnn amsa sai ‘yar mutan Jalingo. Ku biyo Mmn Nuraini kusha labari.*
*Luv u all*????????????
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
*Aunty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*Allah ya k’ara miki lafiya swt sis, Halima Auwal (Mmn Aisha.)*
*2*.
Gaba d’aya ya rasa yadda zaiyi Tunani yake wani irin mataki ya Kamata ya d’auka akan Kabeer, gida ya koma ya shige d’akinshi ya kwanta duk maganar da yaran shi da matarsa ke masa babu wanda ya kula cikinsu.
Kwanciya yayi, yayi pillow da hannayenshi, yana tunanin hanyar da zaibi ya raba auren Kabeer da Rumaisa.
Fitan kawu ba da jimawa ba Kabeer ya dawo gida, direct d’akin Rumaisa ya shiga, kwance ya sameta tayi rub da ciki ta kifa kanta a kan pillow.
kare mata Kallo ya tsaya yi daga k’ofar d’akin, wando ne dogo bak’i ta saka ya Matse ta sosae kamar zai fashe, rigar jikinta kalar pink ce mai doguwar hanu, ta d’an nad’e hanun rigar , rigar ta kama ta dam ,bak’in dogon gashinta d’aure da pink ribbon, sai kyalli gashin yakeyi. Tayi kyau iya kyau, duk inda kake neman kyakkyawar mace mai cikar halitta Rumaisa ta had’a.
Bakinshi ya hura ya fesar da iska, cikin taku Irinna zaratan maza ya taka ta isa gaban gadon.
D’ago ta yayi ta hanyar Jan wuyar rigarta ta baya ya finciketa da k’arfin da ya sata mugun razana.
Kuka ta fara, tana rokanshi yayi hakuri, saida ya sharara mata Lafiyayyun Mari guda biyu snn ya sake ta ya fara zare belt .
Cikin b’arin jiki ta durkusa a gabanshi, ta kama kafafunshi”Bobbo dan Allah Kayi min rai kada ka dakeni bani da lafiya Wlh. ”
Ball yayi da ita wanda yayi sanadiyyar kifuwanta, tsugunawa yayi ya d’ago ta, cikin husky voice d’inshi yace “Ban hana ki saka wad’annan kaya a gidannan ba,? kuma uban me Bappa yazo yi min a gida, ehh?”
Rikon da ya mata da yadda yake bud’e mata ido ya hanata magana.
“Ba dake nake ba? Munafuka, sai zura ido take kamar mayya. Wato ke taurin kai ko? bakya jin magana ko? Yau Zan yi maganin rashin jinki a gidannan munafukai marasa mutunci. “ya fad’a cikin zafin rai.
“Bobbo Kayi hakuri bazan sake ba. ”
Maganar da tayi ya k’ara harzuka shi tuni ya fara labta mata belt d’in hannun shi, tun tana kokarin Kaucewa har abin ya gagareta, Dakyar ihunta yake fita dan kukan da tasha, dukanta yake har suka fito palour, daga k’arshe ya takarkare yayi ball da ita wanda yayi sanadiyyar d’aukewar numfashinta.
Dadai shigowar yayarsa wacce yake bin mai bimata.
Cak ta tsaya tana binshi da Kallo ganin yadda ya ke huci idonnan jazur ga kuma belt a hanunshi.
Maida kallonta tayi kan Rumaisa’un dake kwance kamar ba rai a jikinta.
“Subhanallah, me Zan gani yau ni Binta. “Ta fad’a cikin rawar murya tana dafe kirji tare da durkusawa kan Rumaisa.
Tab’a ta tayi tana kiran sunanta amma shiru ba amsa.
Kallonshi tayi taga ya juya ya kama hanyar d’akinshi, da gudu ta isa wajen shi ta kama shi tana jijjiga shi “Ka kasheta Kabeer, ka kasheta ka huta, Wannan wani irin rashin imani ne? Ashe abinda ake fad’a min akanka gaskiyane? me yarinyar nan ta maka da ta cancanci Wannan hukunci daga gareka, Kabeer baka da imani. “ta fad’a tana matsanancin Kuka.