DASHEN ZUCIYAHAUSA NOVEL

DASHEN ZUCIYA

1⃣

*FLORIDA united kingdom*

“Bisma Kullun kara kyau kike gashi ana karatu amma ke kaman bakiyi sai wani kiba kikeyi, nikam kaman ana miya da namana, kinsan yau lectures dinnan damukayi wallahi bakiji yadda nikeji ba kamar in zura takalma na in gudu kasata Nigeria
Dayawa mutane suna ganin kaman cin banxane zuwa karatu kasar waje wallahi babu komai sai wahala, dadinshi dayane shekarun karatun badaya bane da gida Nigeria”.

Itadai bisma kallonsa kawai tak’e duk yabi ya rude saboda karatu itakoh koh a jikinta don ita tafison tayita jin chargi a brain dinta, fashewa tayi da dariya lokacin da Hamdan yayi sipping ice-cream ya juyo da sauri kedawa
“Keda lafiyanki kuwa kiketa dariya kamar wata tababba?”.

“Hamdan na lura gaba daya kai ragone, saboda Dan wannan karatun da kak’eyi shine duk’ kabi kake damuna, Allah yabani hakuri nida nake karanta (MBBS Medicine) kuma gashi am still looking more healthier than you, kasan yadda nake kashe dare nake karatu wallahi bana samun cikakken bacci”.

“Naji din ni ragone kek’uma ba Raguwa ba shiyasa naga Kullun tafe kike kamar wacce akayiwa sata, Kullun cikin sauri kike wai shin intambayeki mana?”.

Gyra zama tayi ta juyo tana kallonsa “Ina sauraren ragon namiji”?
Wani littafi ya wurga mata ta tashi tana dariya,
“Joke apart Bisma wai meye dalilin ki na karatun likita?”.

“Hamdan kenan inada dalilai masu yawa, tunda ka bukaci kaji toh yau zan warware maka komai, nak’asance Mara tausayi, sannan da wuya Abu baya sani kuka sai wata rana aka kwantar da Nabil dinmu a asibiti dake zamfara Gusau Wato federal medical centre, da shigarmu naga wata mata tanata kuka tana surutai, rungume da danta amma babu Wanda ya kulada ita bare yasan halinda take ciki, saboda talauci dayake tafe dasu Tuni na shagala da kallonsu wasu zafafan hawaye ne suka gangaro daga k’warmin idanuna”.

“wani wawan shaka nayima wata nurse wacce taketa surfa musu Zagi, nace ke wace irin Mara imani ce? Wace irin dabbace ke wacce batasan darajan mutane ba?
Kina ganin wannan matar kika banzatar da ita bakiga halinda danta ke ciki bane?
Nasha Alwashi saina zama likita don intaimakawa marasa lafya da gajiyayyu”.

“Tuni mutane sukayo kanmu suk’ayi mana cha sai a lokacin Ummi ta hangoni na shake Nurse cikin mutane ta kutso kai
“Bisma da lafiyanki kuwa malamar asibiti kika kama ma wuya?”
Ummi ki kyaleni da ita narasa meyasa wasu likitoci suke wasa da aikinsu Ummi Dan Allah dubi wannan yaron suma yakeyi amma anrasa wanda zai mishi gata? What a pity dagudu nabar asibitin, nayi waje ina kuka Bayan an gama duba Nabil ne muka koma gida”.

“Nanna sanarda Abbeey cewa nidai aikin likita zanyi don in taimakawa mutane musamman ma talakawa masu karamin karfi nayi alkawari koda zan mutu ta hanyan taimakone saina yi karatun likita”.

“Dayake shi mutunne mai son taimako haka ya goyi bayana har nazo kasar Florida USA Dan inyi karatun likita shiyasa kaga bana wasa da profession dina”.

Hamdan shuru yayi yana jinjina k’wazo da jarumta irinnan Bisma,
“lallai kinada kyakkyawan niyya kuma insha Allah, Allah zai miki jagora Allah xai taimakeki”
“Amin” Bisma tace nan suk’ayi sallama da juna kowa ya wuce hostel dinshi cikeda kewan juna, Kullun haka suke haduwa har wata halak’a mai girma tashiga tsakaninsu Wato *LOVE* lokacinda Hamdan ya sanar da Bisma bakutar sa taji wani mugun dadi da mamaki Ashe amintarsu da Hamdan zai iya zama Soyayya?
[1/31, 7:51 PM] Mummy: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

 

2⃣

Nikam nece kwarai, alokacinda suka kusa kammala karatun su ne, suka xama hanta da jini soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu, Wanda tazame musu jiki kowa maganarsu yake dama suyi aure, Hamdan ne mai cewa “ai idan kukaga ban auri Bisma ba toh ajaline yaxomun baka tatan,
“Banda abunka mai sanyina ai rana daya zamu mutu mubar duniya, don inhar katafi kabarni Rayuwa zata kasance mai zafi a gareni”.

“Haka nima Bisma bana fatan ki tafi kibarni inrayu dawa ingawa inji dadii, Dan Allah adaina maganan mutuwa saboda hankalina yana mugun tashi Gashi muna gab da mukammala karatu Mu koma gida Nigeria, Meye next target dinki?”
Bisma kallon soyayya takemai
“Ai banida Wani buri anan gaba saina inganni tareda dakai matsayin matarka halak malak dinka”.

“Gaskiya ne Bisma fatana Allah ya albarkaci soyayyar Mu, Allah yasa iyayen Mu su aminche ma bukatar mu cikin kankanin lokaci donnni ta bangarena banida wata matsala”.

“Nima haka *Hamdan* nasan iyayena bazasu ki abunda nake muradi ba, tun yanzu sunfara yimun maganan aure kuma nasanar dasu cewa nifa nayi gamo da katar a kasar Florida kuma insha Allah shine Wanda za’ayi dashi”.

“Nikam ai Tuni nayi introducing dinki a family na, yanzu haka kowa yakosa daya ganki, Kinsan farin jini gareki da banyi da gaske ba inajin da NURU yamun kafa, dayake jarumine nidin shiyasa na rike fire”.

Dariya Bisma tayi tace, “nikam kana bani mamaki waikai a tunaninka nuru sona yake? Toh koh kafado kawaidai mutunci mukeyi dashi saboda daga gari daya muka fito, Shikafi”
“Bisma kenan kin manta aminta yanasa ayi aure koh a dasa soyayya? Lallai fatana Allah yayi mana jagora”
“Amin”.

NIGERIA SHIKAFI

Shirye shirye akeyi kwarai saboda, dawowar yar gaban goshi hatta fentin gidan sabone, an gyara ko ina donya kawata kallon yar’Gaban goshi,
Inkaga mutane acikin gidan babu Wanda yake zaune kowa sabgar gabansa yakeyi, an shirya liyafa wacce babu irinta a fadin Gusau, abinchi ne kala kala sannan ga yan tarban bakuwa yan uwa sa abokan arzuka duk an halacci gidan, daga birni da kauyuk’a
Ummi kuwa takasa zaune takasa tsaye tilon yarta zata dawo daga USA,
Shikam Abbeey yana chan danasa mukarraban, ana hiran irin cigaba da nasaran da Bisma tasamo daga Florida.

FLORIDA

Acanma bikin yayesu akeyi, lokacin sunrigada sun kammala, hada kayansu dayan tsarabe tsarabe, shikam Hamdan ziri muzin shi zai koma, daman dayawa mata ke jigilan yin tsaraba koda kasa mai Girma akaje dayawa inka leka kasuwanni da dare mata ke hidima.
Bayan an kammala ne, hankulansu duk yabi ya tashi saboda rabuwa da juna da zasuyi, Bisma takasa cin komai gashi garinsu guda amma kowa da shiyarshi, nikaina saida na tausayawa Bisma saboda irin shakuwar dasukayi tun haduwarsu a makaranta.
[1/31, 7:51 PM] Mummy: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

 

3⃣

Haka suka fito kowa kagani hankalinsa a tashe yake ciki har *Nuru* daya kwallafa ransa akan Bisma amma bashida yadda zaiyi tunda *Hamdan* ya rigashi dole ya hakura saboda Bayaso su samu matsala da Hamdan, amma abun takaici Bisma takasa gane cewa *Nuru* sonta yakeyi ita a tunaninta kawai jininsu ne yazo daya shiyasa ya shaku da ita, tafe suke har filin jirgin saman dake US dayake duk gari guda suka nufa, amma Hamdan da Nuru scholarship ne gwamnatin Zamfara ta daukesu saboda kwazonsu da haxaka badon iyayensu sun gaxaba, Nuru ne zan iya cewa dan talaka ne amma kuma mai wadatar zuciya, anyi musu hakanne don kara musu karfin gwiwa, sannan suna fatan idan sukaje suka dawo zasuyiwa gwamnatin Zamfara hidima.

*KASA NIGERIA*

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button