Hausa Novels

Zee Baby Book 1 Page 20

*????????20*

….tana bude kofar Dr Na isowa da Sauri tayi wuff ta fice da gudu jikin Mahabeer ta fada” my zeena meye kike gudu numfashi ta maida ta rikeshi”my heart mutafi please “muje nama Dr godiya kukan shagwab’a ta saka masa tana tsalle sai kallonsu akeyi yada tayi kyau kamar yar tsala gashinta ya zubo har gadon bayanta “OK my zeena muje tunda bakiso ko??” Kai ta daga Sardauna ne ya Iso ransa ab’ace zee ta saki Mahabeer ta koma bayansa “Ah Dar namu menene kuma kake zaro idanu kana fushi? ” bro wlh sai na hukunta yarinyar nan zagina tayi ta gudo daga cewa tabari ayi mata sauran Allura guda shine ta zageni ta gudo kai kuma dan daure mata gindi kake dariya kuma ahakane zaku fita da ita idanu zee ta zaro tana lab’e bayan Mahabeer “wai, Allah kaidai anyi katon banza yaushe na zageka kuma yaushe mijina yayi dariya cikin zafin zuciya yayi kanta Mahabeer ya taresa da sauri “yi hakuri Dr abar Allura bataso fizge hannusa yayi ya nufi cikin room d’in da ya fito”Ya Mahabeer mutafi manta dashi hannuta yaja suka fito”my zee baby wlh kiraba haraka da Dr Sardauna meyasa zakice masa karya yakeyi “to shikenan tunda hakane baka sona kanuna mun matsayi na ta b’are baki tana kuka harda ihu ta fizge hannuta ta dora akai”wayyo na mutu na lalace mijina baya sona saboda kalan dangi jama’ar harabar asibitin sai kallonsu akeyi arikice ya riketa yajata tana tirjewa lokacin Dr Sardauna ya rako mashakurah bayan ya gama sabke mata kwandon masifa tarasa me tamasa wai laifintane da tabar zee ta fita shiru tamasa har yagama ya sabko yace suje ya rakata gun mota suna fitowa harabar asibitin yaga tijara da zee takema Mahabeer yana lalabata ta shiga mota takaici da bakin ciki yasa ya juya ya koma yace mashakurah ta gaida gida zaizo da dare daket Mahabeer ya shayo kan zee da sa bakin wani datijo ta shiga motar tana turo baki shiga yayi yamata key sukabar hospital d’in

driving yake hankalinsa gun zee baby yada tayi fushi “My zeena meyasa ban isa nayi miki maganaba to yi hakuri kinji Amaryata kanta ta kwantar kafadarsa tana masa kukan shagwab’a “,yi hakuri zeezeena please karki samun ciwon zuciya zee rigimarki tayi yawa kalli kayan da kika fito dasu wlh jinake kamar zuciyata zatayi bindiga saboda kishinki ya gangara yai parking ya dago kanta sai shashekar kuka take yana share mata hawayen fuskarta idanunsa sun tara kwalla ya rasa ya zai mata ahankali ya kirata cikin sanyin murya “my zeena mekikeso yanzu ko dan ki tayarmun da hankali”to bakaibane ka batamun rai” ok yi hakuri dagowa tayi takallesa idanunsa sun tara kwalla cike da mamaki ta zaro idanu jikinsa tafada”Ya Mahabeer don Allah yi hakuri kamayar dasu ina sonka karkasa, na tsaneka ni inason jarumin namiji banason lusari ta dago tana gogeme hawayen fuskarsa shima ya goge mata ya saki murmushi “dama wayo namiki dan kibar kuka gashi nayi nasara ajiyar zuciya na sabke na manna masa kiss akumcinsa na koma gun zamana jikina yayi sanyi motar yaja muka tafi yanajana da hira jikina na saki muna hira har muka iso gida, a parlo muka isko yan gidan suna hira da sallama muka shigo direct bedroom na nufa, tana zuwa tayi wanka ta kimtsa jikinta ta saka doguwar riga mara hannu wacce tayi cif cif ajikinta ta gyara gashinta ta daure da ribbon ta fesa turare parlo ta fitokusan ghaisha ta zauna

“Momy sannu ya jikinki?? ” ummina da sauki ta kalli hafeeza”ke baki iya gaishe da mutaneba ne? dariya hafeeza tayi “su manya ina yini ya jiki Aunty amarya tayi dariya”momy ya jikin Ashe cikinki yake ciwo adakile ta amsa khalisat ta rike hannuta “my zee sannu murmushi ta sakar mata”yauwa my khalisat ta kalli ghaisha”ummina bani wayarki na kira my dear ta kawomin wayata da kayana ummina wai kinsan me dan iskan hayatu yaso mun yau wlh kwartacin yaso yi dani fade da rana tsaka dan umma tace ya kaini hospital “innah lillahiwainna’ilaihir raji’un”amma wlh hayatu ya bata wayonsa “ummina kibarshi ai Dr yaci mutumcinsa duk abinda zee ta fada karaf akan kunne mahabeer isowa yayi ransa ab’ace “wlh yau sai hayatu ya gwamce mutuwa da rayuwa ghaisha tace”kanaji Dr ya hukuntashi Mahabeer abi komai asannu kar zumunci ya bace mun godewa Allah da bai cutar da itaba amma bata kara zuwa gidan hauwa ba zaman yayi yana huci zee ta dawo kusansa. “Ya Mahabeer kaje ka amsomun kayana kaji? ” bari yanzu kuwa zan amso miki ya Mike ya fice ghaisha ta rumgumeta tana mata sannu Aunty amarya kallon zee take yada sam bataji kunyar fadar abunda hayatun yaso mataba har tsirara da yayi suna zaune suna hira har aka kira sallah magarib kowa ya tafi yin sallah itako tana zaune tana kallo, tunanin Dr Sardauna ya fado mata yada d’azu ya matseta yana mata masifa sai lumshe idanu takeyi can k’asan makoshi ta kira sunansa ahankali “Dr Sardauna Namijin duniya ta fadi tana kwanciya tsikar jikinta na mimmik’ewa yada ya rinka mata kiss akunne wani irin feelings takeji sanyi na ziyartota jikinta ta kame guri daya tana sabke ajiyar zuciya murya mahabeer ta maidoni haiyacina firgigit na tashi zaune” my heart sannu murmushi ya sakar mata”ga kayanki da wayarki “yauwa angona na gode”ficewa yayi yana murmushi mik’ewa nayi na dauki kayan na nufi bedroom saboda sam banida nutsuwa saman bed na fada na Kira ummina bugo biyu ta daga”ummina ya kukayi dasune? ” zainaba ki ajiye hankalinki karki damu nima insha Allahu ina tafe gwara na barmusu k’asar sati suka bani idan bansa kinzoba zasu d’aura miki aure”wani uban ashar ta lailayo ta dirka saida ummin ta lallasheta”yauwa ummin kizoma cikin satinan zanfi kowa farin ciki”eh zanzo dan Allah zeena yarinyar kirki ki nutsu”zan nutsu amma ko ba yanzuba sai na iske Abbu Rahman saudia “yanzu dai kibari har nazo kinji? ” naji ummina kinada lbrn jannat da manal? ” wlh banida amma zansa amso miki number su, munjima muna hira na kashe tunanin Sardauna ya adabi zuciyata burina najini jikinsa yana tsotsata ganin tunanin zaimun yawa yasa na Mike na watsa kwayoyi abakina na fito parlo,

Bangaran Dr Sardauna tun bayan tafiyar zee ransa ab’ace yake haushinta yakeji da na mahabeer sigari ya rinka zuga babu kakautawa har ya samu nutsuwa saide idan ya tuno yada suka manne juna d’azu tsikar jikinsa ta fara minmmik’ewa yanajin wani iri da muguwar sha’awa na ziyartasa tsaki yaja ya Mike ya fara duba marasa lfy dan ya manta abinda yake damunsa ahaka har karfe shida ya nufo gida yana zuwa ana Kiran sallah magarib agagauce yayi wanka ya shirya cikin jallabi ruwan toka ya taje kansa ya kwanta luf ya dan zubo kamar na mace sai sheki yake turare ya fesa sai zuba kamshi yakeyi yayi mugun kyau kamar balarabe ya nufi masallaci bai dawoba saida akayi sallah isha’i mota ya shiga ya nufi gidansu mashakurah, zee tana zuwa parlo ta isko Daddy na zaune kusansa ta zauna”Daddy oyoyo” momy ya jikinki? ” Daddy da sauki ummina tace zatazo”eh momy wlh naji dadi sosai momy Aunty amaryace ta ISO “Daddy nanah abunci na jiranku mik’ewa yayi “momy tashi muje hannusa ta kama ghaisha ta Mike da sauran yaran dukansu suka nufi dining sai ga mahabeer da Najib suma sun shigo Aunty amarya tayi serving d’insu Daddy yace”ina Dr Mahabeer yace ya tafi zance gun amaryasa dariya sukayi kowa ya fara cin abuncin zee ko tunda akace Dr Sardauna ya tafi zance abun ya tsaya mata arai ta kasa cin abunci haka kawai taji tanason ganin Dr Sardauna adaide wannan lokacin ko zuciyarta tabar zafi sama sama taci abunci ta Mike ta dawo parlo ta zauna Nawwara ta hau cinyarta tana mata surutu jitayi parlon ya isheta ta mik’e zata nufi bedroom wayarta ta dauki ringing taga number saudiya ce

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button