Hausa Novels

Lu’u Lu’u 20

*20*

 

Mik’ewa yayi tsaye yana neman kamo hannayenta yace “Kwantar da hankalinki gimbiya, ki ban lokaci kad’an zan tabbatar miki da haka.”

Girgiza kai tayi kamar zata fashe da kuka tace “Yallab’ai ni kawai ina so na koma rayuwata ta baya, wannan labaran da kuke bani zasu iya saka zuciyata tarwatsewa, ta ya mahaifin daya kawoni duniya kamar yanda kuka fad’a kuma zai nemi kasheni?”

A nutse yana tsare fuskarta da ido yace “Saboda ci gaban mulkinshi ne, gimbiya Zafeera tarihin magabata ya nuna ke ce zaki kawo sauyi a k’asar nan baki d’aya, ba kuma zaki kawo wannan sauyin ba har sai mahaifinki baya kan karagar mulkinshi, to da haka ki fad’a min ta ya zai barki bayan ya tabbatar zaki kawo k’arshen mulkinsa?”

Dafe kanta tayi da hannu wasu hawaye masu zafi suka zubo kan kumatunta, cikin nutsuwa da sanyayyar murya tace” Da a ce zan kasance yar wannan sarkin da gaske kamar yanda kuke fad’a min, tabbas da na hak’ura da kawo sauyin nan dan kawar da duk wata hatsaniya tsakanin ‘ya da ubanta, da zan yi k’ok’ari na ga ran mahaifin nan bai b’ace ba bare har na taimakawa son zuciyarsa wajen yunk’urin kasheni.”

Murmushi yayi yace” Haka kike gani, shiyasa na ce ki bani d’an lokaci dan tabbatar miki.”

D’auke hannunta tayi ta kalleshi a marairaice tace” Yallab’ai zaka iya barina ni kad’ai?”

Cike da tabbaci yace” Me zai hana gimbiyata? Na barki lafiya.”

Juyawa yayi ya fita inda ta bishi da kallo har ya fice, a hankali ta lumshe idonta wasu hawayen suka sake gangaro mata, bud’e idonta tayi ta k’arasa gaban tagar ta bud’e labule, inuwar yammacin da shukokin da suka k’awata gidan yasa ta jin son kad’aicewa da kuma samun kyakyawan yanayin nan, sakin labulen tayi da sauri ta shiga takawa ta fita a d’akin.

Kallon fadawa da hadiman take ganin duk wanda suka had’e sai ya sunkuya ya gaisheta a yarensu na Gallois, har ta fita farfajiyar suna gaisheta, zagayawa tayi ta b’angaren hagunta ta k’arasa kusa da shukokin, wani dogon numfashi ta ja idonta a rufe sannan ta sauke numfashin tana mai bud’e idonta akan koreyan shukokin, sanyin mai d’auke da ni’imtacciyar iska sosai ya mata dad’i, rumgume hannayenta tayi tana sake sauke numfashi.

Sannu sannu ta fara shiga duniyar tunani har tayi nisa, a haka kuma tana takawa zuwa ga shukokin, saida ta d’aga k’afarta ta tsallake d’an dakalin da aka zagaye shukokin, shiga tayi ciki tana taka k’ananun ciyayin a rashin sani har ta taka mab’allin pampon dake ba wa shukokin ruwa a duk sanda lokacin ba su ruwan yayi, tana takawa sai kuwa tsinin takalminta ya dannu wasu k’ananun k’arafu na suka bud’e suka shiga feshin ruwa suna juyawa ta ko ina.

Zuwan abun bazata da kuma yanda ruwan ke fita kamar ruwan panpo na sama yasa ta zabura ta waro idonta, da sauri ta kalli k’asa dan tasan tabbas ita ce ta taka, tana ganin wurin ta sunkuya da niyyar kashewa, sai kawai ta ji daga bayanta wani bafaden yace “Ranki shi dad’e ki barshi zan kula da komai.”

Mik’ewa tayi ta fito ta shiga takawa da sauri tana tattaro rigarta tana matse dan har ta jik’e da ruwa, lokaci d’aya kuma tana mayar da gashinta baya tana matseshi shi ma.

Duk abinda ke faruwa tsaf a idonshi yana hangenta daga sashinta ta saman bene, da fari kam dariya ce ta kubce mishi, amma ganin zata koma inda ta fito tana matse kaya sai ya k’urawa duk wani namiji dake wurin ido yana son ya tabbatar da inda idonsu suke kallo, shin sun tsareta da ido sakamakon jik’ewar kayanta suna k’are mata kallo? Ko kuma dai hankalinsu na kan aikinsu kamar yanda suka saba? Saida ya ga shigewarta kad’ai sai kawai ya ji wata nutsuwa ta d’an sauko masa, ko ba komai yasan dai zata canza kayan jikinta.

A wani ikonce ya d’auke kan shi daga gurin yana had’e fuska ya mayar kan k’aramar na’urar dake hannunshi yana ta binciken abinda yake k’ara son tabbatarwa, dan shakkun da yake da akan Haman da wanda Ayam ta k’ara masa a kai yasa ya ji bai yarda da kowa ba hatta ita kan ta hukumar ta su bincike kan miyagun laifuka da hana ta’addanci.

Ko da ta koma d’aki wanka tayi gaba d’aya sai ta canza kayanta, yanzu kam riga da wando ne saidai basu da maraba da irin kayan yan Pakistan, dan har da mayafinsu su ma wanda ta rasa wa ya siyo mata kayan nan haka masu rufe jiki? K’arshe dai mayafin a kafad’unta ta daidaita ta d’orashi sannan ta fito a d’akin dan zaman haka kurum isarta yake, gashi ita ko gudu na tayi bare sauran motsa jiki.

Masu gadin dake tsaron k’ofar d’akin sarauniya wanda yau ne aka sakasu saboda alfarmar data nema gurin sarki Wudar d’in ta kalla tace “Zan iya shiga ciki?”

Jinjina kai d’aya yayi yace “Bayan shugabanmu sarki Wudar da yarima Umad, ke ce ta ukun da aka yarje mana mu barki ki shiga ciki, sai kuma jakadiyarta mai kula da ita.”

D’an murmushi tayi a hankali suka bud’e mata k’ofar ta shiga, yanda dai take da tabbacin zata sameta haka ta samu, kwance amma kuma idonta bud’e alamar ba bacci take ba, murmushi ta d’ora a fuskarta tana k’arasawa kusa da ita d fad’in “Sannu da hutawa madam.”

Zaune tayi bakin gadon daf da ita ta kamo hannunta kamar yanda tayi da safe ta rik’e jim, tsurawa fuskarta ido tayi tace “Kina da buk’atar wani abu ne?”

Kamar d’azu da safe sai kawai ta damk’e hannunta alamar e, jim Ayam tayi alamar tunani sannan tace “Abinci?”

Sarauniya Kossam k’ura mata ido tayi bata damk’e hannunta ba alamar a’a kenan, d’orawa tayi da fad’in “Ruwa?”

Shi ma dai shiru tayi, d’orawa tayi da “Zaki shiga toilet?”

Ganin dai ba amsa sai tayi saurin fad’in “Kin gaji da kwanciyar?”

Matsa hannunta tayi alamar e, murmushi ta fad’ad’a tace “Na gane, bara na samu wanda zai taimaka min sai mu fitar da ke waje.”

Mik’ewa tayi tace “Ina zuwa.”

Fita tayi a d’akin sai kuma tayi katarin had’ewa da wata hadimar, dakatawa tayi tace “Na ce ba, ina za’a samu kujera irin ta masu jinya?”

Jim tayi alamar tunani sai kuma tace “Ina jin akwai a d’akin ajiye kaya, da ana d’ora sarauniya a kai idan za’a kaita d’akin gashi.”

Jinjina kai tayi tace “Ok, ki kawo min.”

Jinjina kai ita ma tayi a ladabce dan dukansu an nuna musu mahimmancinta sannan tace “To ranki shi dad’e.”

Juyawa tayi zata koma ciki tace “Idan kin d’auko ki kawo min d’akin madam.”

Da mamaki tace “Madam?”

Cikin fara’a tace “E, d’akin sarauniya ba.”

Jinjina kai tayi ta wuce da sauri dan cika umarninta, komawa tayi d’akin ta shiga kiciniyar kamata, da k’yar ta tasheta tayi zaune ta gyara mata lullub’in kan ta na kayan da tasa aka d’auko da safe aka saka mata.

Tana dawowa da kujerar masu tsaron k’ofar suka hanata shiga, k’wank’wasa d’akin sukayi Ayam ta lek’o, da kanta ta fad’a musu ita ta nemeta su kuma barta ta shiga dan ta kama mata sarauniya Kossam, suna shiga ciki suka kamata suka ciccib’a suka d’ora kan kujerar, robar ruwan dake aje Ayam ta d’auka ta d’ora kan cinyar sarauniyar sannan ta shiga turata a hankali suka fito.

Duk inda suka wuce sai an kallesu da mamaki, suna kaiwa k’ofar fita sarki Wudar da masu take masa baya zasu shigo ciki, da mamaki ya tsaya yana kallonta yace “Gimbiya ya haka?”

Kyab’e fuska tayi tace “Ta ce ta gaji da kwancin ne wuri d’aya, shiyasa zan fita da ita waje ta sha iska ita ma.”

Da mamaki sarki Wudar ya juya ya kalli waairi shi ma ya kalleshi sannan ya kalleta yace “Amma ta ya ya ta fad’a miki haka ? Ita da ba magana take ba.”

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button