Hausa Novels

Lu’u Lu’u 25

*25*

 

Waziri Khatar na d’agawa sarki Musail yace “Ka bayar da umarni a fito da Juman, a fito da ita yanzu yanzu.”

Hankali tashe Khatar yace “Yallab’ai ka tabbatar? Wani abu ne ya faru?”

Cikin fad’a yace “Idan ban tabbatar ba na kiraka, na ce ka fito da ita yanzun nan.”

Da sauri ya amsa da “To yallab’ai, yanzu kuwa.”

Aje wayar yayi yana sake rarako idonshi yana tuna abinda ya faru tsakaninshi da Ayam, girgiza kai yayi yace “Kai ina! Hakan ma ba zai faru ba, ba zan tab’a yarda da wannan ba.”

Tana komawa d’akinta ta samu hadiman nan suna jera mata kaya da aka siyo mata daidai ita, falo ta zauna zuciyarta cunkushe saboda rashin jin dad’in abinda ya faru tsakaninta da mahaifinta, ta jima zaune ita kad’ai tana tunanin nan kafin hadiman su fito suka durk’usa gabanta d’aya tace “Gimbiya an gama shirya kayan, ko da wani abu da kike da buk’ata?”

Girgiza kai tayi tace “Ba komai, nagode, zaku iya tafiya.”

Kallon juna sukayi da mamakin jin ta musu godiya, wanda da Zafreen ce saidai ta bisu da tsaki ta musu alama da hannu su fita, mik’ewa sukayi suna fad’in sun barta lafiya kafin suka nufi fita.

Kallonsu tayi suna daf da ficewa tace” Ya maganar wacce ta rasu? Anyi jana’izarta?”

A ladabce ta k’arshen tace mata” Yallab’ai sarki ya sa a kai gawarta ga iyayenta.”

Da d’an mamaki tace” Ina kenan?”

D’aya a ciki ne tace” Nan baya kad’an, mafi aksari iyayenmu sunyi aiki a nan kafin su daina mu kuma mu ka d’ora, to mai akwai babban filin da aka gina musu suke rayuwa anan.”

Da alamar tambaya tace” Kenan a gidan nan babu wanda ya je jana’izarta?”

A hankali wata ta girgiza kai tace” Gaskiya sarki bai bamu wannan izinin ba.”

Jinjina kai tayi tace” Shikenan, d’aya a cikinku sai ta rakani na je.”

Zaro ido sukayi suka kalli junansu, wacce ta rakata d’azun ce tace” Ranki shi dad’e ki rufa mana asiri.”

Fuskarta ba alamar wasa tace” Asirinku a rufe yake, zaman lafiyarku d’aya shi ne muje d’aya a cikinku ta rakani.”

D’aya a ciki kamar zatayi kuka tace” Ranki shi dad’e idan har ya zama dole ki tafi dole mu dukanmu zamu rakaki, sarki ya umarcemu mu kasance tare da ke a ko ina.”

Mik’ewa tayi tsaye tace” To ai sai mu tafi.”

Wacce suka tafi tare ce ta sake fad’in” Duk da haka akwai dogarai da aka ware dan rakiyarki.”

Murmushi tayi ta girgiza kai tace” Ko ma menene dai mu tafi.”

Ita ma kan ta murmishin tayi kafin suka shiga take mata baya har suka fita falo.

A falon suka had’e da Zafreen ta fito ita ma da masu take mata baya alamar fita zatayi, a wulak’ance ta bisu da kallo kafin ta tambayi hadiman da cewa “Ku kuma ina zaku tafi?”

Cikin ladabi d’ayar tace “Zamu raka gimbiya ne babban gida.”

Yatsina fuska tayi tace “What? Babban gida kuma? Me zatayi a can?”

Girgiza kai Ayam tayi tana murmushi tace “Aunty gimbiya ni na ce su rakani, zan je ta’aziyar d’aya daga cikin hadiman da aka rasa da sfiyar nan.”

Wani malalacin murmushi tayi tace “Ke kuma kalar zubar mana da mutumcin da zakiyi kenan? Me ya had’aki da talakawan nan? Me zaki je ki musu har inda suke rayuwa?”

Girgiza kai Ayam tayi tana mamakinta tace “Ko na fad’a miki ba zaki fahimta ba, amma a tak’aice su ma mutane kamar mu, dan bamu fi su da komai ba.”

Tana gama fad’a ta nufi hanyar fita ba tare data sake ji daga Zafreen d’in ba wacce ta bita da kallon mamakin furucinta da kuma jin haushi.

Yanda ta buk’ata haka ya faru, ta isa babban gidan wanda ke da babban filin tsakar gida sai d’akuna a jejere ba adadi, mutuwar da akayi kuma ita tasa kowa na gidan ke waje wasu zaune wasu tsaye suna kallon gawar da aka shinfid’e iyayen yarinyar suna kanta suna kuka da fad’in shikenan sun rasata.

Kusa da su Ayam ta zauna ita ma ta share ‘yar k’wallarta kafin ta shiga jera musu ban hak’uri da fad’in yanda abun ya faru, sosai hakan ya faranta ran iyayen da ma duk wanda suke cikin gidan, dan ko shekara talatin ka b’ata kana ma sarki bauta yau ka mutu ko jaje ba zai yi wa wanda abun ya shafa ba.

Saida aka d’auki gawar dan kai ta gidan kad’ai Ayam ta bar wurin tare da abokatafiyar, suna shiga masarautar daf da k’ofar shiga falon wata hadimar ta ha’de dasu, a ladabce ta sunkuya tace “Ran gimbiya ya dad’e, mai martaba ne ya ce ki zo sarauniya ta iso.”

Da sauri ta kalleta tace “Ta iso? Tana ina? Muje.”

Da sauri ta shiga ciki suka rufi bayanta, rasa hanyar da zata nufa tayi hakan yasa hadimar nan fad’in “Nan ne gimbiya.”

Da sauri kamar zata tashi sama ta bita suka shiga haura matakalar da gudu gudu, saida suka kai k’ofar d’akin sai kuma ta tsaya turus, bud’ewa aka yi hadimar ta kalleta tace “Shiga ranki shi dad’e.”

Kallon k’ofar tayi dake bud’e kad’an, a hankali ta fara d’aga k’afarta tana shiga ciki idonta tsaye wuri d’aya, jin an rufo k’ofar daga baya yasa ta saurin juyawa hakan ya tabbatar mata lallai an rufe k’ofar, sake juyowa tayi gabanta tana mai baza idonta tana son ganin ta inda zata fito.

Sauti tashin muryoyi taji daga wata mashigar,a hankali ta fara takawa zuwa ciki wanda labule ne ya musu shamaki, tana zuwa ta d’aga labulen sai kuwa mutanen suka bayyana, hadimai ne uku da jakadiyarta sai sarauniya Juman tsakiyar su suna caje mata kai bayan tayi wanka tsabar wahalat data shawo a gidan kurkukun nan.

Jin shigowar mutum yasa su ma suka juya, suna ganin Ayam suka kama jikinsu suna mata barka da zuwa, mik’ewa Juman tayi a sanyaye ta juyo gaba d’aya ta zuba mata ido, ido cikin ido suka kalli juna yayin da a tarz sak’on ya isa ga zuciyoyinsu cewa lallai alak’ar mai k’arfi ce wacce ta isa su kira junansu da mai haihuwa da wacce aka haifa.

Ayam data kasa motsawa Juman ce ta shiga d’agowa a hankali tana tunkarota tana k’ara gyara k’aramin towel d’in dake kafad’arta duk gashinta ya kwanta a kai, saida ta tsaya gabanta suka kallon juna, cikin sanyayyar murya Juman tace “Kamar jaririyar ‘yata dana kalla sau d’aya tak a rayuwa?”

Kamar ambaliyar ruwa haka hawaye suka fito daga kurmin idon Ayam suna sauka a kumatunta, cikin muryar kuka ita ma a tausashe tace “Ba zan iya tuna kamannin fuskar ba, dan ban tab’a ganinta ko a mafarki na ba, saidai duk da haka hakk’in haihuwa ne ya jawoni zuwa nan dan tabbatarwa da kai na mahaifiyata na neman taimako na.”

Sark’ar wuyanta ta jawo ta nuna mata tace “Da gaske ke ce kika saka min wannan a wuyana tun ina k’arama?”

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button