Hausa Novels

Lu’u Lu’u 27

*27*

 

Waina idonta tayi tace “Mah, babu wani addini da nake cikinshi a baya, dan abinda su Mah (Habbee) ke bautawa ina ganin hakan kamar b’atan basira, a gani na ba ta yanda zan sassak’a ice da hannu na sannan na ce gareshi zan nemi biyan buk’atoci na, a k’arshe ma sai ta kai da kud’i kad’an zaka iya siyanshi a kasuwar sabah sannan ka kai cikin gidanka, sai nake ganin hakan gaskiya bai dace da mutum mai hankali da tunani ba, duk da ban rayu da su rayuwa mai tsayi ba saboda makarantar kwana dana dinga yi, amma dai a haka suna min fad’an na samawa rayuwata madogara, dan rayuwa babu addini tamkar rayuwa ne babu alk’ibla, amma kullum sai na fad’a musu zan yi idan har na samu addinin daya dace, dan kullum a jikina da kuma hangena nake samun yak’ini tabbas akwai wani buwayi gagara misali wanda ya cancanci dukanin mai rai da numfashi yayi bautarsa gareshi, and…a k’arshe dai na samu ta dalilin yallab’ai Umad, yana bautawa ubangijin daya dace, gareshi ni ma na karb’a, saidai yanayi yasa babu abinda ya koyar dani game da addinin, amma kakata ta koyar dani wankan tsarki, sannan ta fara min bayani akan rukunan musulunci guda biyar.”

Cike da farin ciki marar misaltuwa Juman ta rumgumota tace” Wow! Masha Allah, a gaskiya na ji dad’in haka sosai, sai kuma yanzu na fahimci kuskuren da na yi saboda rufewar da ido na sukayi na son ganin na ceci rayuwar ki, sam na manta da madogararki, na manta nayi tunani akan jigon rayuwarki, zan nemi gafarar ubangiji na kuskure na, sannan daga yanzu zan fara d’oraki daga inda kika tsaya.”

Cikin jin dad’i ita ma tace” Nagode Mah.”

Da sauri kuma tace” Dakata, dakata, na ji kin ce kakarki? Wace kakarki kenan?”

K’urawa fuskarta ido tayi tace” Mahaifiyarki, sarauniyar Egypt.”

Zaro ido tayi tace” Ina kika had’u da su Ayam? Iyaye na fa kika ce?”

Jinjina kai tayi tace” Yallab’ai Umad ne ya kai ni wajensu.”

Da mamaki tace” Umad? Wai me yake nema ne?”

Girgiza kai tayi tace” Ban sani ba ni ma Mah, amma ni yanzu babu ruwana da shi, dan yau da zan taho na shiga d’akinshi sai na samu wasu abubuwa da ke nuni da kamar wani ne ke shirya mana wani abu, ko kuma dai ana aiki a kan mu.”

Jim tayi tana tunani kafi’ daga bisani tace” To ko dai shi ma…”

Sai kuma tayi shiru, da sauri Ayam tace” Shi ma me? Mah ki fad’a min idan kinsan wani abu a kan shi.”

Girgiza kai tayi idonta na kallon k’asa tace” Um um! Ba lallai abinda nake tunani ba ya zama gaskiya.”

Cikin zumud’i tace” Duk da haka Mah fad’a min.”

Kallonta tayi tace” Kin gane ko? Zuciyata ce na ji ta raya min wasu abubuwa a game da yawan maganarsa da na ji kinyi, uwa uba kuma kika ce ya had’aki da iyayena, ina tunanin to ko dai shi ma ya shiga aiki irin na yayansa Urab ne?”

Kallon tuhuma Ayam ta mata tace” Mah, tambayarki fa nayi kuma ke ma kin tambayeni, wane aiki kenan?”

Cikin rashin tabbas tace” Jami’in sirri ne, a waccen lokacin jami’in sirri ne dake binciken manyan laifuka na k’asa.”

Jim tayi alamar tunani sai kuma ta jinjina kai tace” Lallai biri yayi kama da mutum, hakan na iya faruwa.”

Da mamaki Juman tace “Amma kum…”

Bata gama fad’a ba aka bud’e k’ofar aka shigo, Juman na jin haka ta tabbatar da sarki ne, Ayam kuma juyawa tayi da sauri, tana ganinshi ta shiga k’ok’arin sauka daga kan gadon, da fara’a ya k’araso yana fad’in “Kaga ‘ya da uwarta, ana tattaunawa?”

Murmushi Ayam tayi a ladabce ta juya ta kalli Juman data had’e fuska tace “Mah zan fita, sai anjima.”

Da kai ta amsa mata alamar to, sannan ta mayar da dubanta k’asa tana sake cije fuska.

Saida ya ga fitar Ayam ya haura kan gado tare da fizgo gashin Juman cikin b’acin rai yace “Me kuke tattaunawa da ita haka tsawon awa d’aya? Gulma ki ke koya mata? Ko wani abu ki ke fad’a ma ta game da ni dan ta bijire min?”

Cike da bushewar zuciya ta fizge gashinta tana fad’in “E d’in, sai me? Tsoro ka ke ji ne kar ta san wani abu a kan ka?”

Hab’arta ya rik’o ya matse yace “Ki saurare ni da kyau, ko ki fad’a ma ta ko kar ki fad’a dai mutuwa za ta yi, dan haka ki shirya ganin gawarta gabanki.”

Murmushin mugunta tayi tace “Ka jaraba ka gani mana, me ye na fad’a min idan ka yarda za ka iya kasheta d’in, ka je ka jaraba ka gani.”

Jinjina kai ya yi yace “Shikenan za ki gani.”

Ita ma jinjina kai tayi tace “Za ka gani mana in shaa Allah.”

Sakinta ya yi ya sauka daga kan gadon ya juya zai fita sai kuma ya tsaya cak ya juyo yace “In shaa Allah? Ki sani na hane ki da yin duk wani abu daya danganci addininki, daga yanzu kuma bana so na sake ji.”

Da sauri ta sauko daga kan gadon tace “Saboda me? Ka fara jiyo k’amshin sub’utar mulkinka daga hannunka ne?”

Bushewa tayi da dariya tace “To ka ji wani abu da ba ka sani ba, ita kan ta wannan addinin take bautawa, kuma ina mai tabbatar ma ka lokaci kad’an ya rage ka fara ganin sahu sahun masallata a farfajiyar gidan ka.”

D’aga murya ya yi yace “Ba zai yiwu ba, sam haka ba za ta faru ba Juman, idan kuma haka ta faru sai dai in bayan ba rai na.”

A hankali ta d’auke kan ta ta furta “Ai dama haka aka fad’a ma ka, komai zai faru ne bayan ba ranka d’in.”

Da azama ya yi kan ta yana d’ga sandarshi da niyyar maketa, sai kuma wata zuciya ta horeshi tare da tuna mi shi Ayam, da k’arfi ya sauke hannunshi ya juya ya bud’e k’ofar da k’arfi ya fita kamar zai tashi sama.

Tana ganin fitar shi ita ma tab’e baki tayi ta gyara zaman mayafinta da kyau sannan ta fita, jakadiyar ta da hadima d’aya za su rakata tace “Ku barshi kawai, wajen ‘yata zan tafi.”

A ladabce suka amsa ma ta ita kuma ta wuce, dake ta san b’angaren sai gashi ta iso a sauk’ak’e, zaune ta samu Ayam kamar mai lissafin kud’i sai nuni take da hannaye, zaune tayi tana murmushi tace “Me ki ke yi haka?”

Murmushi tayi ita ma tace “Ba komai Mah, sannu da zuwa.”

Numfashi ta sauke kafin tace “Yawwa sannu.”

A tsanake ta kalleta tace “Yawwa Mah! Ina so ki d’ora min karatun nan daga inda kakata ta tsaya min.”

Jim tayi tana kallon fuskarta tace “Ayam, ya ki ka ga iyaye na? Suna cikin k’oshin lafiya?”

Cike da tabbaci tace “Mah suna cikin k’oshin lafiya, saidai na tabbata suna kewarki, zai fi kyau ki ware rana ki had’u da su ko da sau d’aya ne kafin waninku ya bar duniya.”

Jinjina kai tayi tace “Zan yi k’ok’arin haka In shaa Allah, ganinki ya haifar min da k’warin gwiwa.”

Da fara’a tace “Ni kuma idan za ki tafi wajensu to zan tafi tare da ke.”

Dariya tayi tace “To shikena’, yanzu mu fara karatunmu ko, dan ya kamata ki san mahaliccinki da kuma yanda zaki bauta masa.”

Daga haka suka shiga karatu ta dinga sanar da ita abinda ya kamata ta fara sani a farko.

*Giobarh*

 

Tunda suka had’u bai ce masa komai ba, yanda ya zuba masa ido tuni ya gigita tunaninshi yasa jikinshi kwasar b’ari da tunanin ya gama gano manufarshi, coffee da yasa aka kawo musu ya kasa kurb’ashi saboda baya da nutsuwa.

Ganin dai shirun ba zai fishesu ba yasa shi muskutawa yace “Umad ina saurarenka, me yake faruwa ne wai dan Allah?”

Ba tare daya daina binsa da kallon nan ba hannunshi tallabe da hab’arshi yace “Wani sabon aiki za mu shiga.”

Wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace “Haba Umad, yanzu abinda zaka fad’a kenan amma ka min shiru duk ka d’aga min hankali, ina jinka to me ye aikin?”

Gyara zamansa yayi ya d’auke hannunshi daga hab’ar ya sauke numfashi, cikin nutsuwa yasa hannu yana juya kofin dake d’auke da coffee yace “Na fad’a ma ka Ayam tana masarautar nan, kuma kafi kowa sanin had’arin hakan, shiyasa ni da kai zamu je fadar da nufin masu neman aurenta.”

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button