RAYUWAR MACE 8
RM
8
***Tafiya take ba tare da ta san ina take wurga kafarta ba, kasancewar shi a bayan ta, ya hana mata dukkan nutsuwar ta, har suka isa gate din gidan ta ja ta tsaya, ya karaso yana wuceta ya kwankwasa kofar, mai gadi ne yazo ya bud’e da sauri, ya wuce ciki ta bi bayan sa a darare, be kula taba har suka shiga ciki, yayi hanyar bedroom din sa hakan ya saka ta tunanin ko ya rabu da ita ne, tayi saurin yin hanyar dakin ta, ji tayi an fizgo ta da karfi, har sai da ta bugu da gefen bangon da yake tsaye.
“Dan Allah kayi hakuri!” Tace cikin muryar ta gwanin ban tausayi.
“Ni kika ciza? Ni!?”
Ya nuna kansa still yana rik’e da ita gam.
Girgiza kai tayi da sauri alamar a ah, murmushi yayi ya shiga janta zuwa cikin dakin, yana zuwa ya wurgar da ita a tsakiyar dakin ta durkushe da sauri.
“Kwashe kayan nan dukka ki wanke su a toilet din nan, kuma minti goma kawai na baki, idan kika wuce haka sai na yi k’asa k’asa dake!”
Kallon tarin boxers da singlets dinsa tayi da yace ta wanke a minti goma, ta hau tattare kayan da azama, komawa yayi ya zauna akan couch yana duba agogon wayar sa,
” Kuma su fita sosai wallahi, useless!”
Da sauri take komai, ta tara ruwan ta shiga wanke su da sauri tana kuma saka karfi wajen dirza su sosai. Wayar da ya saba ya shiga amsawa hakan ya mantar dashi duba lokacin da yake har ta gama tas ta fito dasu a cikin bucket. Hada ido sukayi ya harare ta ya cigaba da wayar, ta fita ta zagaya chan baya wajen abun shanya ta shanya su dukks sannan ta gudu dakin ta. Bayan ya gama wayar ya zo ya murda kofar yayi tsaki ya fice daga gidan.
Washegari su Ya Hadiza suka kawo gara suka tafi ba su wani dade ba, tun daga nan da ta ga kafa ta dauke ta daina yarda su hadu, kafin ya dawo ta dauki abinda zata dauka ta shige daki, har ta samu tsarki ta soma sallah ta shiga kaiwa Allah kukan ta, dan shi kadai ne zai yaye mata damuwar ta.
Watarana bayan magriba haka tayi sallah ta idar, ta koma ta zauna ta dauki wayar ta, tana dannawa rabin hankalin ta yana kan chatting din da suke da Rauda har bata ji motsin komai ba, sai ji tayi an bud’e kofar, ta saki wayar ta fadi garin mikewa tsaye. Fuskar sa a hade tamau babu alamun tausayi ko sassauci, wajen da take yayo gadan gadan, tayi yinkurin guduwa ya tarde ta, tayi kamar zata fadi, ya tare ta da hannun sa ta fado jikin sa, ya daga ta chak ya fice da ita daga dakin duk ihun da take da magiya ko gezau be ba, sai da ya kaita dakin sa sannan ya jefa ta a saman gadon, ya koma ya sakawa kofar key ya rufe ya dawo in da ya barta tana kuka ya daka mata tsawa
“Dan rashin mutunci na biya kudi nayi komai amma kice ba zaki bani ba, abun da gashi nan kamar banza kyauta ma ake raba mana shi bama so, ko dan kinga na damu? Taimaka miki nayi kar sha’awa ta kashe ki a gida ba aure, shine zaki dinga wahalar dani a banza.”
Yace yana huci, ya hawo gadon ya sake fizgota, ya murde mata hannu zuwa bayan ta sannan ya zuge zip din rigar ta har kasa ya yi wurgi da ita, idon ta, ta runtse tana cigaba da kuka. Kare mata kallo ya tsaya yanayi, kafin ya shiga sarrafa ta yadda yake so, ya kuma yana mata motsi ko kad’an, ya danne ta ko ta ina, yaci karfin ta, saddakarwa kawai tayi ta dinga jan kuka saboda yadda yake mata, babu digon tausayin ta, hannun ta da yake baya ya sage sosai yayi tsami saboda yadda ya danne su, numfashin ta taji yana sama-sama, ta dinga jin tamkar ranta zai fita daga jikinta saboda azaba. A hankali a hankali komai na jikinta ya saki, ta sume ba tare da ya sani ba!
Afwan! normal posting zai fara in Sha Allah weekends. Nagode