Rayuwar Mace

RAYUWAR MACE 9

RM*
       9

Tsawon lokaci ya dauka kafin ya kyaleta ya fice daga dakin zuwa na kusa dashi, be tsaya duba halin da take ciki ba, sai da yaje ya watsa ruwa sannan ya dawo dakin ya tarar a halin da ya barta, ya dan tsorata ya dinga girgiza ta, ganin da gaske bata motsi ya sashi saurin samo ruwa ya zuba mata, aka yi sa’a ta dawo ta hanyar jan dogon numfashi, kallon sa tayi ganin shi durkushe a kanta ya sakata sake kidemewa har tana yinkurin tashi ta hau masa magiyar dan Allah yayi hakuri a cikin yanayin da duk rashin tausayin mutum sai ya tausaya mata, shi ko gogan ko oho, ganin ta farfado ya saka shi sake tsallake ta yayi ficewar sa bayan ya dalle mata baki na mugunta!
Kasa tashi tayi a wajen, ta dinga jan jikinta da yake mata mugun ciwo zuwa dakin da kayan ta suke, da k’yar ta kai kanta a daidai lokacin taji karar fitar motar sa daga gidan. Toilet ta rarrafa da k’yar bayan ta shiga dakin ta hau gyara kanta tana yi tana kuka wiwi, kukan da sautin sa baya fitowa sai hawaye da yake ta ambiliya a fuskarta, yadda Adam yayi mata ya tabbata har da mugunta a ciki, be lallaba ta balle yayi mata a hankali, tana kuma kyautata zaton yayi mata babbar illa, ta dade aciki tana kuka sosai sannan ta sake rarrafowa ta fito zuwa bakin gadon ta nade a kasan carpet ta cigaba da gurzar kukan ta
Ji tayi an shigo, sai dai ta kasa dagowa balle ta kalle shi, ajiye mata leda yayi a gabanta daga tsaye yace

“Ki sha idan kin gama kukan, bana son raki wallahi. Mtsw!” Ya juya da nufin barin dakin

“Kaji tsoron Allah, duk abinda kayi min Allah sai yayi mana sakayya.”

Tsayawa yayi chak ya fasa fitar, ya dawo ciki yana mata kallon mamaki

“Hakkin nawa da kika hanani tsawon kwanaki shine kike ganin na cutar dake akai!?

Dariya yayi sosai cike da mamakin ta

” You are not serious malama , kadan ma kika gani idan dai nine wallahi, sai kin gwammace baki ja dani ba. “

Ya juya yana sake jan tsakin da yafi na dazu, yayi ficewar sa, yana jin ta tana jaddada masa taji ciwo amma yayi biris, farin ciki na sake mamaye shi, be taba mu’amula da irin ta ba, sai yaji ta daban da duk sauran matan da ya taba Hulda dasu daga fararen fatar har namu na gida bakaken, sai dai a yadda ya dauki aure, da yadda yake ganin mace baa bakin komai ba, ya hanashi ya saukar da kanshi ya nuna mata kulawa, yana ganin bata isa ba! Bata kai wannan matsayin ba, be taba tausayin mace ba, balle har wata aba soyayya ta shiga tsakanin su, abu daya ya sani kawai shine, idan tayi masa sai ya dandana ko ta halin kaka, amma fa daga daya baya karawa wasu ma, idan ba irin Fido da ita kadai ta san logon sa ba, amma kuma Asma’u, ta musamman ce a wannan bangaren, amma baya jin zai iya sauko da kansa har ya nuna mata tausayi ballantana raini ya shiga tsakanin su.
Kuka ta cigaba da yi a wajen ba tare da tasan madafa ba, sai wajejen sha biyu na dare sannan ta sake tashi ta koma toilet, ta fito daure da alwala amma ba zata iya sallah a tsaye ba, sai kawai tayi a zaune tana idarwa ta sake kwanciya a wajen zazzabi na sake rufe ta sosai.
Washegari ta tashi da mugun zazzabi, ita kadai a gidan dan ko motsin sa bata ji ba, bata iya ko mikewa bare tayi ma kanta wani abu, haka ta cigaba da kwanciya a wajen kamar zata mutu, tun tana kuka da hawaye har ta daina idon ta ya soye.
Chan wajen azahar taji ana buga kofa da dan karfi, kofar shigowa falon su, sai kuma taji maigadi na sake tabbatar mata tana nan dan be ga fitar ta ba,tana jin su har zuwa lokacin da taji ana bud’e kofar da key, sai muryoyin su yana mata bayanin ya dan fita ne, Nadeeya ce kila kiran sa tayi a waya, dakin kasan da Asma’un take ciki ta shigo, tayi saurin yin kanta ganin ta a kudundune cikin rawar sanyi.

“Boy!” Ta kwala masa kira tana dagota zafin jikin nata ya bata tsoro,

“Kaji jikin ta kuwa? Baka san bata da lafiya bane? Ko ya akayi?”

“Ban sani ba fa, bata fad’a min ba kuma har dazu da mukayi sallama na fita, zazzabi ne?”

Yace kamar be san komai ba

“Bana son haka Adam, ya zaka fita ka bar matar ka a wannan halin kace sai ta fad’a maka, ya kamata ace ka sani ai, sannu asma’u, zo ka taimaka mata ta kwanta a saman gadon nan na duba ta sosai.”

Kamar ba zai zo ba, sai kuma ya saki kofar da ya toge da ita da ya shigo ya dagata chak ya dora a gadon, zafin kasan ta ya sakata runtse idon ta, tayi yar kara, karar da ta ankarar da Nadeeya din ta kalle shi da sauri ta kalle ta.

“Boy!” Ta kalle shi da sauri a tsorace, sai kuma tace ya fita, ya juya yana bouncing ya fice gami da ja musu kofa cikin nuna halin ko in kula, daga ta tayi ta dora mata kanta a saman pillow, sannan ta dauko ruwa ta bata a hankali tasha cikin tausayin ta tace

“Ya ji miki ciwo ne?” Kasancewar ta nurse ta fahimci komai, da ka Asma’un ta amsa mata hawaye na bin kuncin ta.

“Kiyi hakuri, bari na duba ki.”.

Tace tana gyara wa, ta taimaka mata ta gyara sannan ta duba ta, a tsorace tace

“Naa shiga uku!”

“Amma Adam bashi da hankali wallahi, sai kace mahaukaci.”

Zama tayi dabas a wajen cikin tausayin Asma’un, sai kuma ta dauki wayarta ta kira shi, ya shigo ya tsaya a kofar ta harare shi kamar ta rufe shi da duka tace

“Me kasha? Kana hauka ne ko me?”

“Sis!”

“Ba wani sis, ba zan taba goyon bayan cutarwa ba, Asma’u yar uwarka ce makusanciya, why will you do this to her, wannan pure wickedness ne ban yarda da wani silly excuse ba.”

“Ita ta fad’a miki!? Matsala aka samu fa, ita ta jawo komai.”

Sake hade fuska tayi cikin fad’a tace

“Baka ma yadda kayi laifi ba kake sake bata laifin, lallai.”

Sosa kansa yayi yana dariya kasa k’asa, hakan ya sake kular da Nadeeya ta kuma sake tabbatar da rashin mutuncin kanin nata. Hanya ta nuna masa alamun ya fita ya bata wuri.fita tayi itama ta dauko wayar ta, ta kira wata abokiyar aikinta tace zata zo da patient a duba ta, sannan ta dawo ciki ta taimaka mata suka fito zuwa wajen motar ta, yana kallon su yana tsaye suka fita be ce musu uffan ba, asibitin su ta kaita, aka duba ta sannan tace a bata gado tana bukatar Hutu, aka saka mata drip har yamma suna asibitin sai da ta dan samu karfin jiki ta bata abinci ta dan ci kad’an sannan suka dawo gida, bayan sun dawo ma bata tafi ba sai da ta sake taimaka mata tayi wanka ta bata magunguna sannan ta tafi a zuwa zata dawo da safe ta sake dubata, ta bata shawarwari sosai ta kuma gargade ta akan sake yarda dashi, dan komai zai iya faruwa ta bari ta fara healing shi ma zata masa magana kuma ta sake masa fad’a akan abinda yayi.
Ba karamin dadi taji da abinda Nadeeya tayi mata ba, bata taba tunanin tana da kirki haka ba, babba ce kusan sa’ar Ya Hadiza, tayi aure ta fito bata sake ba tun daga lokacin har kawo yanzu.
Dakin ta sake rufewa dan ta tabbatar da bashi da ishashen hankali zai iya dawowa a kowanne lokaci wanda ta san idan hakan ta kasance zata iya rasa ranta ma ba suma ba saboda ita kadai ta san azabar da tasha.
Satin ta guda tana jinya bata sakashi a idon ta ba, tana jin motsin sa da wayar sa amma be yi ko attempt din zuwa in da take ba, bata sani ba ko fad’an Nadeeya din yaji, ko kuma yana tama ta ne kamar wanchan lokacin oho. Nadeeya kullum sai ta shigo ta taimaka mata ta kuma bata magungunan ta, hakan ya taimaka mata sosai wajen samun sauki da wuri, bata fadawa kowa ba dan wannan ba maganar da zaka fad’a bace, sun yi waya da yan gidan su har da umma amma ta kasa ce musu komai akan irin zaman da take a gidan Adam din, ta dauki hakan a matsayin jarrabawar ta dan kaf gidan su babu wanda yake auren miji irin nata, kowa daidai gwargado suna zaman su cikin mutunci da kaunar juna.
Kwana wajen uku ta daina jin motsin sa, Ashe tafiya yayi bata sani ba, daga fuskanci baya nan sai ta fito ta sake sosai tana harkar ta, gidan yayi mata dadi sosai kamar ta dawwama a haka babu shi. Ranar tana zaune a falon kasan bayan Hajiya Mama ta aiko me aikin ta, ta kawo mata sinasir da miyar taushe ta gama ci kenan ta dawo falon ta zauna sai taji ana saka key a kofar, dama dare ne wajen takwas ma tayi, mikewa tayi dan bata ko ji karar bud’e gate ba bare shigowar sa, shine a gaba tana biye dashi kanta babu rufi ya sha uban attachment har gadon bayan ta, zuba mata ido yayi yana takowa cikin falon, tayi saurin yin hanyar sama ya rigata cikin sassarfa ya riko ta, Fido dake biye dashi ta tamule baki cikin jin haushin shi, kwace hannun ta tayi, ta haye da sauri ya tsaya yana bin bayanta da kallo har ta gama hawa, sannan ya dawo da ganin sa kan Fido da ta hade rai

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button