Rayuwar Mace

RAYUWAR MACE 10

RM*
       10

***Da asubah Fido ta bar gidan bayan ya sauke ta a gidanta da take zaune wanda shine ya kama mata shi yake biyan kudin hayar gidan tsawon lokacin da suka sauka a tare. Gida ya dawo direct ya wuce daki ya kwanta babu batun sallar asubah a lokacin burin sa kawai yayi bacci dan ba wani isashen bacci suka samu a tafiyar da sukayi ba ta bikin abokin sa Chairman shiyasa yake jin tamkar idonsa zasu rufe saboda bacci.
Sallar asuba ta idar ta zauna a wajen tana karatun al’qur’an har gari yayi sha sannan ta tashi ta gyara dakin ta koma ta dan kwanta zuwa takwas ta mike, so take ta shiga gidan Hajiya Mama shiyasa ta ki bari ta koma baccin safen. Wajen goma ta gama abinda take ta bud’e kofar ta dan leka ta tabbatar baya nan sannan ta fito ta rufe kofar a hankali ta fita. A harabar gidan suka hadu da Nadeeya zata fita, tsayawa tayi suka gaisa ta sake tambayar ta jikin ta, a kunyace ta amsa mata tayi godiya ta fice ita kuma ta shiga ciki. Hajiya Mama na zaune a falo tana breakfast, ta saki fuskarta sosai ta hau yi mata sannu da zuwa

“Dama ina shirin yi wa Adam korafi, idan ya fita kiyi tahowar ki nan kiyi zaman ki, chan ai sai kadaita ta dameki.”

“Ina kwana?” Tace tana durkusawa k’asa

“Lafiya lou wallahi, zauna mana.”

A kunyace ta tashi daga tsugunan ta zauna daga gefe, Hajiyan ya turo mata tray din dake gabanta

“Maza ci abinci, bari na watso ruwa nazo.”

“Naci abinci Mama.”

“Gidanku, maza dauki ki zuba kici wani abincin kirki kake iya ci ne, Nadeeya ma tace min baki ji dadi ba, ban sani ba wallahi sai yau take fad’a min, ni dai nace Allah yasa addu’a tace Allah ya amsa min.”

“Uhumm…” Tace cike da kunyar Hajiyar, fuskar ta cike da farin ciki ta shiga ciki, ta bar Asma’un da tunann maganganun ta, bata jima ba ta dawo ta zauna, ta shiga jan Asma’un da hira cikin sigar son bugun cikin ta ko taji wani abu dangane da zaman nasu, dazu take maganar Asma’un anan Nadeeya take ce mata ai bata ji dadi ba ma, daga haka kuma bata sake ce mata komai ba, shiyasa tayi tunanin ko cike ne da Asma’un, tayi niyyar dama anjima ta shiga gidan nasu sai kuma ga Asma’un ta hutashsheta ta shigo, bata samu amsar dukkan bayanan da ta nema wajen Asma’un ba dan kamar kunyar Hajiyan take ji sosai hakan ya sake tabbatr wa da Hajiyan Asma’un cikin ne.
Har sha biyun rana suna zaune a falon in da Hajiyan ta saka aka ajiye mata abubuwa masu yawa a gabanta duk wani abu da tayi tunanin zata ci sai ta saka an ajiye mata, ita abin ma sai ya dinga bata dariya da mamaki, bata dai nuna komai ba, ta dai jinjinawa kokarin Hajiyan da kuma irin soyayyar da take wa Adam din nata. Cikin shigar dakakkiyar shadda coffee colour ya shigo falon, sosai shigar ta karbe shi ko dan be saba irin ta ba? Kallo daya Asma’un tayi masa ta kauda kai dan ita sam bata ga abun kallo a wajen mutum irin Adam ba, wanda yake da kyawun dan miciji.

“Shine kika taho kika barni ko? Bayan nace ki jirani mu zo tare.”

Kallon baya asma’u tayi a tunanin ta da wata yake, sai kuma taga ya nufo ta, yana sake son tabbatar mata da itan yake, yak’e ta hau yi ganin idon Hajiyar na kansu tana ta murnushin jin dadi, dungure mata kai yayi yace

“Punishment dinki kenan na tahowa ki barni, gobe ma kin kara.”

“Gidanku Adam, karka kara dungure mata kai, wani ya hanaka tashi da wuri?”

“Toh ai laifin ta ne fa, ita ta hanani baccin jiya, shine kuma ta taho ta barni.”

Mutuwar zaune tayi, bata taba sanin akwai maza makirai ba sai yau, kallon sa take shima kuma ita yake kalla idon sa fes a kanta, ya harare ta, ga gefe ba tare da Hajiyan ta gani ba, tayi saurin sauke kanta k’asa mamakin sa na sake girmama a ranta, ya wuce duk in da take tunanin sa. Be sake bata mamaki ba sai da taga ya zo ya zauna daf da ita yana cigaba da tsokanar ta, wanda ta lura ba karamin dadi hakan yayi wa Hajiyar ba.
Anan suka ci abincin rana, ko da tace zata tafi sai Hajiyan ta hanata, ganin su a tare a hakan yayi mata dadi ainun, ta dinga hasaso yadda komai zai daidaita a rayuwar Adam din ta. Sai da akayi la’asar ta barta ta tafi lokacin shi ya ma riga ya fice wai zai raka wani abokin sa neman aure.

***Gidan su take son zuwa, gashi bata san ta ina zata fara sanar dashi ba, tasan haramun ne ta fita bata tambaye shi ba, amma kuma bata san ta ina zata fara tambayar ba, ita kadai take sakawa da warwarewa har tara na dare be shigo ba, ba jiran sa take ba dama, amma kuma tana ankare da duk motsin sa. Bacci ne ya soma daukar ta, ta mike daga zaman chatting din da tayi da su Hidaya ta je ta dauro alwala tayi shafa’i da wutri tazo ta kwanta bayan ta rage kayan jikin ta, ta daga curtains din dakin yadda iska zata shigo sosai.
Bata san yaushe ya shigo ba, cikin bacci bacci taji ana taba ta, ta tashi a firgice, ya rik’e ta gam yana toshe mata baki.

“Hakki na nazo karba, kikayi gardama na sake miki kacha-kacha.”

Gumi ne ya shiga karyo mata, tana tuna bakar wahalar da tasha a wajen sa waccar ranar, magiya ta soma masa da hada shi da Allah amma babu alamun zai ji ta balle ya tausaya mata, tunanin yadda zata kwaci kanta ta hau yi dan kuwa idan bar ta amince masa akwai matsala bata gama warkewa ba har yanzu dan kusan kullum sai ta shiga ruwan dumi take jin dadi, dukkan karfin ta, ta tattaro ta hankade shi, ta mike tayi hanyar barin dakin duk da duhun da ya mamaye ilahirin dakin, shaf ta manta gaba daya da kafar benen dake wajen, burin ta kawai ta tsira da ranta, ji tayi kamar ta taka abu me tsantsi, sai kuma taji ta zame ta kwalla kara gami da zamewa ta fadi a wajen, kanta ya bugu da karfin stairs din ya fasa mata saman goshin ta!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button