GURBIN IDO CHAPTER 2
GURBIN IDO????????????
Free page 02
“Migodake” ta fada a hankali tana sharce ruwan fuskarta,dubanta yayi,ya sakar mata murmushi,wani abu me suna nutsuwa da sanyin halin daya karanta tattare da ita na dan qaramin lokaci yana burgeshi
“Karki damu,ba komai” kai ta jinjina,saita juya tana nufar cikin gidan tana qudundune jikinta waje daya saboda yadda sanyi ya fara ratsata,da alama akwai damuwa kenan,yayin da shi kuma ya juya ya dauki torch dinsa ya fara gangrawa yana barin wajen,saidai sau kusan uku yana waiwayarta kafin ta qule masa yabar ganinta,ya sauke ajiyar zuciya yana maida hankalinsa sosai ga hanya,zuciyarsa na qissima masa ita,tsahon wanzuwarsa a rugar bau taba kula da ita ba,hakanan bai taba ganin macen da Allah ya zubawa kyau me sanyi da tsari irinta ba,ko wacece ita?,da wannan tunanin ya isa kofar wani gida,wanda shi dayane kaf kafin wajen dake dauke da ginin qasa da bulo.
Babban tsakar gidane daya kasance wayam babu kowa saboda ruwan daketa sauka,yakai dubansa ga dakunan dake jere a tsakar gidan,har ya nufi wani daki daga ciki,sai kuma ya dakata ya juya akalarsa zuwa wani daki dake daura dashi,muqullin ya taba,a rufe dakin yake dole dai ya karbo muqullin,abinda yasa ya juya da dan sassarfa ya nufi daya dakin,yasa hannu ya dage asabarin da aka saukema qofar dakin saboda kaucema shigar ruwa.
Dumine ya fara dukan fuskarsa kafin hasken fitilar aci bal bal dake dakin ya cika masa idanu,matasan mata ne guda biyu da yaro namiji guda daya zagaye da fitilar,kowannensu d kwanon tuwo a gabansa yana ci,sai babbar mace guda daya da alamu suka nuna mahaifiyarsu ce zaune gefe daya tana dubansu,jikinta nannade da mayafi me kauri,da alama sanyi takeji
“noi saare daada”
“Jam….alhamdulillahi,ina ka tsaya?,inata taraddadi ruwan nan sai daya dakeka” murmushi ya saki
“Zan canza kaya daada,a bani maqulli” hannu ta miqa wata qwarya dake kusa da ita da alama a nan take ajjiye ajjiyenta ta dauko,ta miqawa daya daga cikin yaran
“Nabugol(karbi)” ta fadi,sai yasa hannu ya karba din,sannan ya miqe zuwa inda yayan nasa ke tsaye
Cikin girmama ya miqa masa muqullin yana cewa
“Hamma…..” Dakatar dashi yayi
“Micanjato kayaa sadam,ina zuwa”
“To” ya amsa yana murmushi,saboda ya qagu ya bashi labarin dake bakinsa,a nutse ya juya ya fice daga dakin ya sake nufar dakin da yayi nufin shiga dazu.
Batayi wani hanzari ba wajen isa dakinsu,saboda ta riga data jiqe,kuma koda ta isa dinma tasan bata da wani wajen zama daya wuce bakin qofa,dakinsu ne su biyu,amma kuma ya zama gaba daya kamar mallakin mutum guda,wato ‘yar uwarta gaaje.
Cikin kula da takatsantsan ta dage assabarin dakin,hasken fitilar dake dakin ya bayyana,motsin shigowarta ya sanya matashiyar dake amsa sunan gaje din daga kanta tana dubanta,gabanta akushi ne madaidaici cike da dambu tana ci,wanda shine yawa yawan cimarsu,tuwo ko dambu,ba kasafai zaka gansu da shinkafa ba
Wani kallo ta watsa mata kamar wadda taga qullin kashi
“Dirdutu malama(matsa malama)” tasan neman bala’i ne kawai irin na gaje,amma inda take tsaye ma sam bashi da alaqa da wajen da gajen ke zaune,sai ta matsa gefan don kawai a zauna lpy,ta miqa hannunta zuwa ga wata tsohuwar baqar jakar bacco dake saqale jikin bango,darajarta wajen maimunatu dai dai yake da akwati a wajen kowa,duk kuwa da cewa duba daya zaka yimata kasan cewa ta sha duniya ta kuma ji jiki,a nan din take ajjiyar duk wani abu nata,duk da dewa ba komai ta mallaka ba face kayan saqinta kala daya da take boyansa saboda sallah ko wani sha’ani idan ya tashi,duk da cewar ita din ba shiga jama’a take ba,rayuwarta na maqale da wani tabo da ya hanata duk wani ‘yanci da walwala da kowanne dan adam kan samu,laifin da bata da masaniya a kansa,bata kuma san sanda aka aikatashi ba.
Kayan jikinta ta zame ta matsesu da kyau daga bakin bukkar tasu,sannan ta dawo ta daura wani fallen zani guda daya da take rufa dashi,ta tara hannu a ruwa bunun dake sauka ta dora alwala,sannan ta dawo ciki ta tada sallah.
Sallar magrib ce kawai a kanta,saboda koda wajen kiwo bata wasa da sallarta sam,duk da ba ilimin addini gareta ba mai wani zurfi,amma tun kafin takai haka,zamanin da take rayuwa da mahaifiyarta ta koyar da ita yin salla da zarar lokacinta yayi,abu guda daya da ba zata manta da shi ba,ta kuma riqeshi har yau da kyau,kasancewarta mutum da bata da yawan mantuwa da kuma qwaqwalwa mai yawan riqe abu.
Da kyar takai sallar da takeyi din saboda tsananin yunwa,takai dubanta ga kwanon da gaje ke cin abinci,tuni ta hallakeshi,dan abinda yayi saura a ciki bazai wuce loma biyu ba,ya tabbata bata da abincin dare kenan duk da dan karen yunwan da take ji?,ta rasa wanne irin azanci ne wannan….tare inna ke hada musu abinci ita da gaje,bayan bambancinsu da gajen kwatankwacin bambacin sama da qasa ne,saboda gaje irin mutanen nan ne masu shegen cin abinci,kamar ci suka kawo duniya,duk yawan abinci sai sun tasheshi….yayin da maimunatu ta kasance wata irin mace,duk yawan yunwar da takeji dan abinda zata ci maka bai taka kara ya karya ba,har wani lokacin ma idan kawai nono tafi ganewa tasha shi ko ajiyayyar madara idan tana da sauranta,kusan duk sanda aka hada musu abinci da gaje sai gaje ta kusan cinyewa ko ta cinye ma sannan take tunawa da ita,duk da cewa a yawancin lokuta bar mata take yi,amma duk lokacin data ratso da tsautsayi irin haka tana jin yunwa tofa saidai ta lashi walqiya ko ta nemi ma duk abinda zata ci din,gajen duka duka sa’anni suke da maimunatu,har maimunatun ma ta bata tazarar kwanaki masu dan dama a duniyar.
“Gaje ya baki ragemin ba?”
“Idan kina da wani ma ki qaro min” ta bata amsa tana sude hannu tare da ture kwanon da qafa ta gicciye anan wajen tana sakin gyatsa.
Fararen idanunta masu sheqi ta dauke daga kan gajen,dan qaramin bakinta mai dauke da jajayen labba yana motsawa kamar zata ce wani abun,saidai ba komai zata fada din ba,zallar bacin rai ne qasan ranta,wanda bata isa ta furta ba,bata jun a daren zata iya runtsawa matuqat bata sanyawa cikinta wani abun ba,ga gajiya da takeji tana nuqurqusar qashinta tare da qaramin zazzabi da taji ya fara lasarta,wanda dama tana tsammanin zuwan nasa.
Tsam ta miqe tana leqen waje ta qaramin window din cikin ginin bukkar,ruwan yadan sassauta,amma yana sauka kadan kadan da dan qarfinsa,saita dage qofar ta sanyo kai zuwa waje.
Gabanta na faduwa amma ta daure ta qarasa qofar dakin inna,sallama tayi,shuru ba’a amsa ta ba,ta sake sallama,a sannan aka amsa daga ciki a tsawace
“Wai waye!?”
“N…..nice inna?” Kamar ba za’a fito ba sai kuma ta jiyo motsinta,ta dage labulen ta fito tana mata wani duba daga sama zuwa qasa
“Menene kuma?” Sunkui da kanta maimunatu tayi
“Yunwa nakeji inna”
“Shine kika zo ki cinyeni?” Amsar data sanya maimunatu daga kanta da sauri tana duban innar hadi da girgiza mata kai
“A’ah inna”
“To meye?,bayan kinsan na hada muku abinci da gaje?”
“Ta cinye inna”
“Kina kallonta ta cinye?,to babu wani sauran abinci cikin gidan,saiki kwanta haka,kyaci gobe”
“A’ah,ba za’ayi haka ba” sukaji an fada daga bayansu,rabewa maimunatu tayi gefe daya,ko bata juya ba tasan waye,mutumin da shi kadai yayi saura wanda yake dubanta da idanun rahama,ya qaraso garesu yana sanye da rigar ruwa,da alama dawowarsa gidan kenan.