A Bari Ya Huce Complete Ebooks

Har goma na dare suna can, yaran suka soma rigima, duk da an basu madara. Uwarsu suke so haikan. Amma
Amiru ya kasa bada su. Saida Habibu yayi mishi alkawarin kafin su tafi gobe zai kai mishi su ofis sannan ya
dauko su har motar Habibu, bayan Hajiya ta cika su da toshi. Daddy ma ya bada check na kudi masu yawa
yace a dinka jamfa, baya son ganin su da daura ‘suit’ irinna Ubansu.
Mairo tayi shirin barci a dakinta dake gidan Yaya Habibu. Ta sanya yaranta a gabanta tana kallon su da fuskar
mahaifinsu. Tana sunsunar su da kamshin ‘miyaki’ wanda ya tuna mata da ‘those precious moments’ da suka
shude a baya. Tana sunsunar su da kamshin ‘miyaki’ da suka kwaso, wanda ya dawo da so da kaunar mijinta
sabo fil a zuciyar ta.
Ta shiga tsakanin su ta rungume kowanne a jikinta. Ta soma sheshshekar kuka a hankali, na tashin tsohon
mikin daya jima da samun sauki. Shiyasa bata so zuwa ba, amma Habibu ya takurata. Ta fadi a ranta Amiru ya
daina son ta…….! Tunda har bai damu daya ganta ba. A karshe ta hakura ta sanyawa ranta salama. Tunda
ance komai yayi farko, to inshallahu yana da karshe WATARANA!
Washegari Habibu ya cika alkawari, ya sake diban Amir da Habib da Esta ya zuba su a mota zai fita da niyyar
kaisu office din Amiru suyi sallama kamar yadda yayi alkawari. Yana kokarin tada mota Amiru na sanyo hancin
motarsa ‘camero’ cikin get din Habibun. Don haka Habibun ya dakata har ya bude motar ya fito.
Ya karbi ‘ya’yansa ya soma ‘kissing’ kamar bazai bari ba.
Daga can saman bene Mairo ta yaye labulen dakinta don iska ta shigo. Nan ta hango su. Ta kurawa Amir ido.
Bayan muguwar ramar da yayi, ya bar lallausar kasumba mara tsari ta cika fuskarshi, abinki da mai yawan
gargasa. Sannan ya saya kwayar idon shi cikin ‘dark-spaces’ wanda ya hana mata gano halin da kwayar idanun
shi ke ciki.
Karan hancin ya kara fitowa, zirit, kamar karas. Wani irin so na fizgarta. Ta saki labulen a hankali ta koma da
baya ta fada a gadonta. Tana mai fidda numfashi da sauri-da-sauri. INAMA ACE…….hannun agogo zai dawo
baya???
***
Washegari suka koma Malaysia. Mairo ta fara karatunta cikin nasara, tana barin yaran a gida wurin mai
rainonsu da yake an fara ba su madara. Kafin su cika watanni tara suna gudunsu ko’ina, musamman Alh.
Abdurrahman ya bude mata ‘account’ a nan ‘Kuala-Lampur’ duk wata yana sako mata makudan kudi na fita
hankali, don lalurorinta da kula da ‘yan jikokinsa.
Bayan kuma ba abin da Ambassada ya rage su da shi, ga na Yaya Habibu. Gaba da baya gata ya lullube Mairo
da ‘ya’yanta, abin sai godiyar Allah.
Shekaru ukku cif, wadanda suka yi dai-dai da cikarta shekaru talatin a duniya, da kwalin digiri, master, da
digiri na kololuwa.
Dr. Maryam Muhammad Bedi, ta tattaro ta dawo gida Najeriya a garin Abuja, zuwa lokacin Habibu ya yi ficce,
bankin ‘Habib Bank’ ya samu habaka zuwa ‘branches’ a dukkan ‘thirty six states’ da muke da su a gida
Najeriya, kamar yadda Amiru Abdurrahman ya yi fata. Yau ga ci gaban ya samu, ba tare da Amiru ba.
A wannan ranar da ake (ten-year anniversary) na cikar bankin shekaru goma da kafuwa, Habibu kuka yake,
maimakon ya yi farin ciki.
A yayin da al’ummar taron suka dauka kukan farin ciki yake yi, amma shi kadai yasan dalilin kukansa, wanda
bai wuce na alhinin samuwar cigaban shikadai, ba tare da Amiru ba.
A kalaminshi na karshe, bayan ya yiwa mahalarta taron godiya mara iyaka. Ya ce,
“Ya tafi ya bar bankin da kewa, bayan shi ya kirkireshi. Ya bar bankin da babban gibin da har gobe bai cike ba.
Na kuma tabbata har abada ba zai cike ba. Sakamakon dumbin ALHERINSA gare ni. A yau na tashi daga
mamallakin ‘Habib Bank’, na kyautar da shi ga ‘ya’yan AMEERU ABDURRAHMAN GAYA”.
Amiru ya daga ido yana kallon shi, extremely puzzled! To haka Alh. Abdurrahman. Ashe wannan shine kudurin
da Habibu yace yana dashi kenan akan bankin, ya ki yarda amaida hannun jarin Amiru cikin bankin?
Ya sanya hannu cikin takardu, lauyoyi suka diba, su ma suka rattaba hannu. Sannan ya ce,
“as a servant, zan ci gaba da juya musu dukiyarsu har zuwa girmansu”.
Hajiya ma ta dauko duk takardun dukiyar Amiru dake tare da ita, ta danka mishi. Ya hada dana wajen Habibu
ya adana a bankin. A wannan ranar Habibu yayi kuka, kawai sabida tausayin AMEERU. Don gabadaya
rayuwarshi ta canza ‘completely’ ta zama ‘no meaning…’ kamar yadda ya fadawa Mairo a baya.
“My life has no meaning……idan ba tareda ke ba”.
***
Habibu ya watsa mata takardun neman aiki, a manyan jami’o’inmu, tun daga Ile-Ife, Ahmadu Bello, Nsukka,
Bayero, Lasu da sauransu, ba don neman kudi ba, sai don al’ummar Najeriya su amfana da ilimin da ta wanzar
da rayuwarta tana nema, don su amfana.
Ba da jimawa ba jami’o’i har biyar suka dauke ta, ciki kuwa har da jami’ar Abuja, wadanda ta bari a baya.
Amma ta zabi BAYERO domin a ganinta al’ummar Kano su ne al’ummarta.
Habibu bai takura mata da zancen aure ba, ko tayin ta koma gidan Amiru. Sai dai shima yana ganin lokacin
yayi daya kamata a maidawa Amiru matarsa sabida yadda zawarawa manya-manyan kusoshi ke yi mishi
rubdugu, a gida ne ko ofis. Alh. Abdurrahman ya fara tsawatar mata da cewa, ba zata koma Kano ba har sai
ta fidda miji ta yi aure.
Sai ta sa musu kuka tana rokonsu, kada su kara yi mata zancen aure, idan ba so suke ita ma CIWON ZUCIYAr
ya kamata ba. Me zata yi da wani da namiji ba Amiru ba? Me zata nema a jikin wani namiji bayan Amiru?
Amiru yasa ta raina sauran maza, ta yadda har basa burgeta, duk ilminsu da mukamin su kuwa.
Gashi da alama Daddy baya son komen nasu. Tunda koda wasa bai taba furtawa ba. Ya kama Mairo da
Habibu ya rungume kamar shi ya haife su, ya jibanci dukkan al’amuransu, amma baya ko son kallon Mairo da
sunan matar Amiru. Itama kuma tunda hakane bazata taba nuna tana son komawar ba, koda hakan na nufin
ta auri wani ne ba shi ba!
Alh. Abdurrahman ya ce,
“Aure ya zama dole Mairo, domin shi ne cikar kima, mutumci da darajar diya mace. Duka wadannan kwalayen
naki aikin banza ne idan babu aure”.
Ta yi masa alkawarin su barta ta fara aikinta, a hankali za ta zabi wanda hankalinta ya kwanta da shi. Ya so ya
karbe yaran, amma ta roke shi ya bar mata, zuwa wani dan lokaci kalilan, don suna debe mata kewa.
Gida guda suka bata cikin ‘new site’, suka tare ita da ‘ya’yanta da mai rainonsu, mai suna Lami. A lokacin
Lawan da Ahmad ‘ya’yan Baffa suna karatu a Bayeron, sai suma suka dawo gidan suna zaune a baskwata.
Baffa yana zuwa duba su akai-akai, su ma suna zuwa idan sun sami lokaci. Mairo ta fara ‘lecturing’ a
‘department of sociology’ cikin nasara da sanin makamar aiki. Ta sanya yaranta a ‘staff-school’ kullum su
Lawan suna kaisu su dauko su, da yamma kuma su kaisu islamiyya da ke nan cikin ‘New-site’.
Ta dade da fara rubuce-rubuce tun tana Malaya akan fannin da ta ke karantarwa, wanda ya kaita ga matakin
zama ‘proffessor’ cikin dan lokaci kalilan.
Kyawunta, zurfin iliminta, sakin fuskarta da yawan taimakonta ga dalibanta, ya sanya ta zamo abar so ga
dalibanta. Sai dai fa kowa yana bin kwakkwafi ya yi mamaki idan aka ce ba ta da aure. Sukan ce kyakkyawar
mace kamar wannan ace ba ta da aure, ai abin mamaki ne sosai. Sannan kallo daya zaka yi mata ka tabbatar
ba da wannan aikin ta ke cin abinci ba. Tana dai yi ne don ra’ayi, amma ba don neman wani abu wai shi ‘kudi’
ba.
Proffessor Maryam Muhammad Bedi, ta zamo daya daga cikin malaman da ake ji da su a jami’ar Bayero, ko
sabida karyayyen harshenta na Turawan America zallah. Don haka da yawa suke bin kwakkwafi akan
rayuwarta, har su san inda ta samo wannan ‘background’ din. Wani dalibinta ya soma rubutu a kanta, sai dai
duk yadda ya so ya ji tana da aure ko ba ta da shi, ba ta bada wannan damar ba.
Dr. Mairo ta shiryawa dalibanta masu fita a wannan shekarar ‘conference’ mai taken, “YADDA ZA A GYARA
AL’ADA TA YI DAI-DAI DA ADDINI” Wanda take so Mai girma sabon V.C ya halarta. Don haka ta je ta nemi
‘appointment’ na ganin V.C a ofishinsa. Aka sanya ta cikin jerin wadanda za su ga V.C a safiyar washegari.
Da ta dawo gida ta tarar Lawan ya dawo da su Habib, Amir yana kwance shiru cikin kujera ba kamar yadda ya
ke ba. Ta dora hannu a kanshi, zafi rau, Lawan ya ce.
“Amir ba ya jin dadi tunda safe”.
Ta ce
“Za mu je asibiti da safe, idan na ba shi ‘paracetamol’ zazzabin bai sauka ba”.
Ta dauko ‘paracetamol’ cikin ‘first-aid box’ dinta ta ba shi da dan kankanin cokali. Har zuwa washegari
zazzabin bai sauka ba. Ga shi kuma tana da ‘appointment’ na ganin V.C, don haka ta sa yaran a bayan mota
suka nufi cikin makaranta da zummar idan ta ga V.C sai ta wuce da su asibiti, don mawuyaci ne daya ya yi
ciwo dan uwansa bai kama ba.
Ba ta barsu a mota ba, sanya su ta yi a gaba suka soma taka matattakala wadda zata sada su da ofishin V.C.
Mutum biyu ne a gabanta, sai da ta jira suka fito, sannan ta kama hannun Habib da Amir suka sanya kai cikin
ofishin, bakinta yana mai furta sassanyar sallama.
Ya juya baya yana zakulo wasu takardu cikin loka. Idanunshi saye cikin farin gilashi, sanye cikin farar shadda
‘excelsior’ dinkin Muhammed Abacha. Hular kanshi na aje bisa teburinshi.
Gaban Mairo ya yi wani irin mugun faduwa, takardun da ke hannunta suka kwace suka watse a kasa. Amir ya
tsugunna yana tsince mata. Shi kuwa Habib tattakawa yakeyi da cambos dinsa.
Ko mutuwa ta yi ta dawo, ba zata mance surar UNCLE JUNAID ba, wanda ke tsaye nan a gabanta. Sai dai
wannan Junaidun, ya sha ban-ban da wanda ta sani shekaru goma sha biyu a baya. Wannan cikakken
magidanci ne, da yasha gwagwarmayar rayuwar neman ilmi cikin fanninnika daban-daban, ba dan saurayi
Junaid Galadanci ba.
Duk da alamun shekaru da suka hau kansa, har yanzu yana nan a Junaidunsa da ta sani, ma’abocin zati da
kamala, gami da kwarjini bayyananne daga Sarkin halitta. Ta rasa cikin halin da ta samu kanta, rudewa ce ko
gigicewa ce? A’a, ko kuwa gaba daya makuwa zata ce ta yi?
Ta juya da baya–da-baya zata bar ofishin, ya juyo a hankali ya dubi mai shigowa.
“Mariama!”
Maironshi da a kullum ta ke zuwa a farke, ko cikin mafarkinshi. Mairon da dai-dai da rana daya cikin shekaru
goma sha shidda, zuciya ba ta taba hutawa da kaunarta ba. Ruhi bai bar mafarkinta ba, haka tunani bai taba
kuskuren manta ta ba.
Ya dago Habib ya dauke shi tare da kama hannun Amir ya zauna a kujerar da mutane suke zama don ganawa
da shi. Cikin wata irin kassararriyar murya, ya ce.
“Ya ya za ki koma? Ko ba ke ce ‘Proffessor Maryam Bedin ba?”
Ta ja tunga a jikin kofa, ba tare da ta juyo ba. Ita bata fita ba, ita bata juyo ba. Hannunta jikin marikin kofa, ta
ce
“Ni ce”.
Ya ce
“To mene ne ajandar?”
Ta ce
“Na zo neman alfarmar V.C ya samu halartar ‘conference’ dina ne”.
Ya yi murmushi yana dauke da Amir ya tako har inda ta ke tsaye. Wani irin sassanyan kamshi da ba zata ce ko
na wanne turare ne ba a duk iya sanin da ta yi wa turare ya kassara mata gabbai.
“Na kasance ma’abocin son ‘twins’ Dr. Mairo, ko za ki bani aronsu? Na dawo miki da su bayan awanni goma
sha biyu?”
Wannan karon ne ta juyo ta dube shi, wasu kibbau na tsohuwar soyayya suka soki idanun kowannensu.
Tsohon tsimi ya tashi, wanda ya yi sanadin tashin tsigogin jikin kowannensu. Da kyar ba tare da ta sake yarda
sun hada ido ba, ta ce.
“Idan iyalinka suka tambaye ka ina ka samo su mai girma V.C me zaka ce musu?”
Babu bata lokaci, ya ce da ita.
“Ya’yana ne, wadanda Mairon Gurin-Gawa ta haifa mini……………”
Kuka ya kece mata, don haka da gudu ta fice daga ofishin tana ji a ranta, ta fasa yin ‘conference’ din, tunda shi
ne ya yi sanadin da ya taso da tsohon gyambon da ya dade da warkewa a zuciyarta.
Gidan Baffa ta wuce kai tsaye, ta nufi dakin Habiba ta kwanta tana sakin ajiyar zuciya mai nauyi. Ta yi juyi a
lallausan gadon Habiba tana tariyo abinda ya faru cikin ‘yan mintina kalilan.
Baffa ya shigo dakin ya zauna a kujera yana fuskantarta, ta goge hawayenta, ya ce.
“Me ya faru? Ke dai har gobe abun kuka ba shi da wuya a wurinki?
Yanzun nan Habiba ta yi min waya ta ce, kin shigo da gudu kina kuka. Idan ka girma sai kasan ka girma, ka
koyi dauriya da juriya irin ta manya. Ba akan kowanne kankanin abu ka bare baki ka yi ta kuka a gaban
mutane ba”.
Ta yi murmushi tana goge hawayen idanunta, ta ce.
“Baffa, Uncle Junaidu na gani, bayan wucewar shekaru goma sha biyu. Ya tuna min da abubuwa da dama da
suka faru cikin rayuwata, shine dalilin kukana, domin na tuna abubuwa da dama da yanayin shekaru da
cigaban rayuwa ba su sani na manta ba”.
Ya ce,
“kwanannan naji a labarai anyi ‘appointing’ din shi matsayin shugaban jami’ar Bayero ai. Har yau har gobe
kuma bai fasa zuwa gidan nan yana gaishe ni ba, bai fasa yi min manya-manyan alhairori ba. Sannan son ki
har yau bai barshi ba.
Ban taba ganin ‘SOYAYYAH’ irin ta Junaidu ba. Don haka ni ma har gobe ban fasa yi mishi addu’ar budi da
nasarar rayuwa ba”.
Mairo ta cika da mamakin jin cewa Uncle Junaidu na zuwa wajen Baffa har yau. Amma koda wasa Baffan bai
taba gaya mata ba. Ba ta gama mamakinta ba su Habib suka shigo suna ta tsalle, kowannensu rike da kit-kit
da leda fal ‘choculates’ suka fada jikinta.
“Mummy mun dawo… Daddy yana gaishe ki”.
Sai Baffa ya tashi ya fita, ya tarbi Junaid a dakin bakinshi.
Habiba ta shigo dauke da kulolin abinci. Su Amir suka makale ta suna ta ba ta labarin inda Daddy ya kai su.
Ta ce,
“Wai wane ne wannan Daddyn?”
Amir ya ce
“Daddyn Mummy ne”.
Mairo ta ce
“Rabu da shirmen su Mama, shugaban jami’armu ne”.
Habiba ta yi murmushi ta ce.
“To ko da shi za a yi ne?”
Ta yi shiru ta daure fuska bata bata amsa ba. Don ba abin da ta tsana a rayuwarta irin a yi mata zancen aure.
Baffa ya dawo dakin yana murmushi, ya same ta tana cin abinci.
“Idan kin kare sai ki je ku gaisa da Alhaji Junaidun. Daga nan ya ce yana so zai kai Amir asibiti, don ya ga
alamun ba shi da lafiya”.
Matsayin Uncle Junaidun da kimarshi da ke zuciyarta, ya fi gaban ta ce ba zata je ba. Baffa ya ci gaba da yi
mata nasiha mai sanyaya zuciya da sanya imani, akan lokaci ya yi da ya kamata ta tsaida hankalinta wuri guda
ta yi aure, domin cikar mutuncinta a duniya da lahira. Tunda Amiru da Daddynshi basa bukatar komen.
Ta yi sallama a kofar dakin, yana zaune cikin kujerun (leather) da suka yi wa dakin kawanya, Habib da Amir
akan cinyoyinsa, yana ta haba-haba da su kamar ya maishe su cikinsa. Ya dago idanunshi da suka yi fari sol,
yana dubanta.
A zahiri Maironshi ce, sai dai fa wannan Mairon babbar mace ce ‘yar shekaru talatin da doriya, wadda kuma a
idanunka da kiyasinka ba zata fi shekaru ashirin da biyar ba.
Wannan bakauyar da aka kawo mishi kafafuwanta jawur cikin lalle tsohuwa ta fada kwata, fatar kamar shuni,
yau idan ka dube ta, tsammani zaka yi Balarabiyar Omman ce, ba wai ‘yar asalin kauyen Gurin-Gawa ba.
Kallonta ya ke, kallon da ke nufin al’amura da dama. Ita ma kallonshi ta ke, kallon da ke tuna mata da
al’amura da dama. Da gaske Uncle Junaidunta ne, sai dai wannan ya kara yi mata GiRMA. Ta TUNA BAYA… ta
tuno ALHERInsa gare ta, ta tuno SIRADIN RAYUWArta, ta yi ALKAWARI ko BAYAN RANTA matsayinshi ba zai
taba canjawa daga zuciyarta ba. Cikin muryar GIRMA ya ce.
“Mairo, ina Amiru Abdurrahman?”
Ta kai gefen mayafin abayarta ta dauke wasu siraran hawaye da suka kawo mata zarya. A hankali tace.
“Mun rabu!”
Duk suka yi shiru na ‘yan dakikai. Can kuma ta kawar da shirun da cewa.
“How comes kai ne sabon V.C dinmu, amma ban taba sani ba?”
Shi ma ya yi murmushi ya ce.
“Ni nasan kina cikin ‘proffessors’ saidai ban tabbatar ba, sannan ban taba tunanin ba kya tare da maigidanki
ba, a wane dalili zan nemeki? Sannan bani da tabbacin ke din ce ko ‘namesake’ dinki ce, na dai ga sunan da ya
tsayamin arai ‘among the proffessors’,
Sannan ai ban dade ba ai, banyi dadewar da zaki san ina cikin makarantar ba” tace “haka ne”. Ta sunkuyar da
kai kafin ta dago ta sake cewa
“Ikon Allah kawai”.
“Ni ma sai ki dauke shi a hakan, wato kudurar Allah, ta fi ga haka”.
Ta jinjina kai, ta ce
“Kwarai kuwa”.
Suka maida idanunsu akan Habib da Amir, wadanda ke ta dabdalarsu cikin dakin, dukkaninsu sai suka yi
murmushi, yaran suka burge su.
“Kuruciyarsu na da ban sha’awa”.
Ya fada a zuci, bai san cewa a fili yake fadi ba.
“Kamar kuruciyar Mairo, Mairon Baba da Inna, Mairon Kausar da Nabilah……..”
Ta yi dariya ta juyar da kanta. Wani ala’amari mai girma na cin zuciyarta. Sai dai ba irin wanda take ji a tsohon
mijin ta ba. Ya kura mata ido, zuciyarshi na harbawa.
“Ina labarin Nabilah da Yaya Habibu?”
“Nabilah tana nan Kano, ‘ya’yanta biyar. Yaya Habibu yana Abuja”.
“Nima na yi aure Mairo. A lokacinda na riga na sallamawa zuciyata cewa na rasa ki, bazan same ki ba, kin riga
kin yimin nisa, kin zama matar wani na. Wanin da nake da tabbacin ko mutuwa yayi bazai tafi ba tareda
igiyoyin aurenki ba.
A halin yanzu Ina da ‘ya’ya biyu, tareda ‘yar uwata Ikhlas. Sai dai har wannan lokacin da tunanin Mairo nake
kwana nake tashi. Sannan dashi nake ‘functioning, will you believe it?”
Ta dago fararen idanunta ta haske shi da su. Tace “sabida me Uncle?”
Babu jinkiri, babu inda-inda ya rausayar da kai ya ce
“sabida Soyayyarki Mairo!
Soyayyar da na ke yi miki a wancan lokacin Mairo, ta zarta hankali, ta zarta duk wani kokarin hankali na ya
fassarata. Mahaukaciyar soyayya ce Mairo, wadda ta makantar da ni daga daga ido na dubi sauran mata. Ta
dakusar da hasken mata ta Ikhlas daga cikin idanuna.
Na tabbatar tunda na rasa Mairo, to bazan samu makwafinta ba. Don haka ne Hajiya tasha wuya da fari
kamin inyi aure. Don nasan ko na yi, to bazan baiwa matar hakkokin da addini ya ce na ba ta ba. Ba zan iya
sallama mata zuciya da gangar jikina ba”.
Ya taso ya tsugunna a gabanta, yana so su hada ido, amma ta ki hakan. Ya dora hannunshi akan tafin kafarta.
Ta lumshe ido a hankali ta bude su akan yatsun hannunshi da ke bisa tafin kafarta. Ya dauke hannunshi ya
zauna sosai a gabanta, ya ci gaba da cewa.
“Hajiyata ta shiga tashin hankali mai yawa, ta yi kuka, ta yi rokon duniya akan na yi aure, na kasa Mairo.
Daga baya sai malamai ta sa suke yi min rokon Allah, sun tabbatar mata da zan yi aure, sai dai da sauran
LOKACI, tunda zuwa yake. Daga baya sai ta koma nasiha, amma zuciyata ta riga ta bushe. Na tabbatar mata
idan dai ba so ta ke na auri matar na dinga daukan alhakinta ba, to ta kyale ni.
Haka ta hakura ta zuba min ido, amma ta ce ba ta fasa yi min addu’a ba. A yau ina da yakinin Allah Ya amsa
addu’arta. For the first time da na ke ji a jikina LOKACI ya zo da zan yi AURE ba irin na Ikhlas da ya zamto
hadin iyayen mu ba. Wanda akayi ba tareda anyi shawara dani ko neman yarda ta ba.
khlas diyar kanin mahaifina ce da Hajiya ta nema min aure bayan na kammala phD dina. A yanzu haka muna
da Maryam (namesake) dinki da Sabir.
Yau ne na ji wani ‘feeling’ a zuciya ta mai tuna min da cewa nima namiji ne KAMAR SAURAN MAZA. Wadanda
ke da buri a rayuwa, da kuma ‘hope’ (fatan) cikar burin nasu. Shin za ki tallafe ni Mairo? Ki auri tsoho in his
fourteeth?”
Hawaye na gudu a kundukukinta, ta ce.
“Uncle Junaidu idan ka kira kanka ‘tsoho’ ni kuma na kira kaina me? Tsohuwa?? (second hand)? Ka
bazawara…???”
Ya yi saurin kai hannu ya toshe mata baki ba tareda yayi niyyar hakan ba. Da sauri kuma ya dauke hannunsa…
“Ni har gobe a Maironki na sanki, koda kuwa ace ke kika haife B.U.K baki dayanta……”
“Idan haka ne, ni ma har gobe a Uncle Junaidu na sanka, bana son kara jin wannan kalmar ta fito daga
bakinka ‘tsoho’.
Ya yi murmushi, ya ce.
“Da dai ana sakewa tuwo suna ne Mairo…”
Ta ce
“Ni ma ban ce a sake masa ba, a barshi a tuwonsa, don haka zauna a Uncle Junaidunka ba V.C Junaid ba, na
zauna a Mairona…….”.
Suka bi junansu da kallo, kallon yarda, so da kauna da aminci. Gaskiyar masu iya magana da suka ce, ‘Soyayya
ba ta tsufa, sai dai msoyan su tsufa’. Don haka sai mu bi JUNAID da MAIRO da fatan ALHERI.
***
Alhaji Abdurarhaman ne ke zarya tsakanin falonshi da falon Haj. Aisha yana duba agogon hannunshi, yana
kuma azalzalarta kan ta yi sauri ta shirya jirgi ya kusa tashi, wanda zai tashi dasu zuwa Kano a sanyin safiyar ta
ranar litinin.
Amiru baya nan ya je China, don shigo da wasu kwanfutoci sabon shigowa, Zuwa wannan lokacin ya yarda da
nadamar ‘ya’yan nasa, da cikar YAKANAH da jarumtakar Amiru. Shekaru uku kenan da rabuwar shi da Mairo
ba tare da ya kara sanya ta a idanunshi ba.
Ya tattara karfin zuciyarshi ya karbi rayuwa ba Mairo, yana ganin lokaci ya yi da ya kamata yai surprising din
sa, da abin da zuciyarshi ke ciwo dominta. Da abinda rayuwarshi ke muradi……… Duk wasu
experiments………. da ya dora shi a kansu…… bai fadi ko daya ba!!!.
Sannan Mairo ta kammala karatunta cikin kwanciyar hankali, duk wasu burirrikan rayuwarta ta cika su,
kamar yadda dan uwanta ke so. Ya kira Habibu a waya ya ce su hadu a Kanon gidan Baffa suma za su taho
yanzu.
Amina ta fito daga daki cikin shiri itama ta ce,
“Daddy don Allah zan biku Kanon, ina son ganin Amir da Habib”. Ya ce “Wuce muje Amina ‘yar albarka”.
(Amina mijinta ya rasu ne, a yanzu haka zaune take a gida).
Hajiya ta fito cikin shirinta, suka nufi cikin chevrolet din Daddy zuwa filin jirgi, inda suka tarar jirgin ya kusa
cika, don haka suna shiga ana rufe jirgin. Ba da jimawa ba ya soma keta hazo ya lula cikin sararin samaniya.
Suna isa Airport din Malam Aminu, suka tarar da Habibu ya riga su isowa, ya kwashe su zuwa Yakasai gidan
Baffa.
Daidai lokacin da Mairo ta yowa Uncle Junaid rakiya zai tafi, tana dauke da Amir yana dauke da Habib. A
kuma daidai lokacin da Habibu ya sanyo hancin motarsa wadda ke dauke da su Daddy harabar gidan. Daga
Habibu, Daddy, Hajiya da Amina babu wanda zuciyarshi ba ta buga ba da ganin Mairo da wannan sankacecen
mutum, ma’abocin zati da kamala, da kwarjini bayananne daga sarkin halitta.
Karo na farko da Uncle Junaid ya dora idonshi a kan Yaya Habibu da baya bukatar a gabatar mishi, sakamakon
tangamemen hotonsa dake sitting room din Baffa.
Shima Habibu a take ya gane wannan shi ne JUNAIDUN MAIRO, da Baffa ya kyankyasa mishi a waya, cewa ya
dawo neman auren Mairo.
Jikin Habib a sanyaye ya fito daga motar, gwiwoyinshi kamar an rarrade su da murfin kwano. Suka yi hannu
da Uncle ya yin da Uncle ya kai gwiwoyinshi kasa yana gaida Alh. Abdurrahaman. Amina ta mika hannu ta
karbi Amir a hannunshi suka hada ido da Junaidun. A take ya ga fuskar Amir da Habib a fuskarta, ita kuma ta ji
wani ‘magnet’ na jan zuciyarta a kan wannan mutum da ba ta sani ba, ba ta taba gani ba. Ya dago suka hada
ido ta yi saurin sunkuyar da kanta.
Mairo na son gabatar da Yaya Habibu ga Uncle amma kunyar su Daddy ta hana ta. Ya shiga mota ya tafi su
Amir na ta kuka sai sun bishi. Hajiya ta kama hannun Mairo, Amina kuwa rungume ta tayi tana hawaye, a
haka suka shiga dakin Habiba. Shi kuma Habibu da Daddy suka wuce falon bakin Baffa.
Cikin dan lokaci Habiba da Hajara sun baibaye su Hajiya da cima ta girmamawa da ruwa da lemu, sun zauna
ana ta gaggaisawa. Mairo da Amina dakin Hajara suka wuce suka bar Hajiya da su Habiba. A nan ne Amina
take labartawa Mairo rasuwar Ghali (mijinta) watanni biyar da suka gabata. Ba tare da Allah ya basu haihuwa
ba.
Mairo har da hawaye na tausayawa Amina, don ita kanta shaida ce a kan matsananciyar soyayyar da suke
yiwa juna. Mairo na so ta tambaye ta AMEERU ba ta so ta bada kanta. Amiru ya yi mata miki mai girma a
zuciyarta. Tunda suka rabu bai taba nema ko sau daya ya ganta ba, sai ‘ya’yansa. To akan me ita zata
nemeshi?
Ta tabbata duk inda yake yanzu ya dade da shafe ta a babin rayuwarsa. Watakila ma ya kara aure bayan
Hanan, ya sallamawa wata wannan gangar jikin da ada ta dauka mallakinta ne ita kadai. Don ta san Dan
Abdurrahaman Gaya, ba zai iya kaiwa tsawon wannan lokacin ba tare da aure ba, in ta yi la’kari da halittarsa,
na mutum mai tsananin yawan bukata. Sannan Hanan, bata da surar irin matar da yake son aure. Ko kuma
watakila ya komawa banasariyar matarshi? Allah masani.
Amina ta ce
“Rayuwa tafe take tare da destiny (kaddara) kala-kala Aunty Mairo, kin manta da brother, kin bude sabuwar
rayuwar da ta bani mamaki, kin kara kyau, kin kara kiba, kin kara haiba da kamala. Sabanin shi da a kullum
yake kara lalacewa.
Cikin shekaru ukun nan ban kara ganin dariyar Yaya Amiru ba, ki yafewa mai kaunarki wanda ya sadaukar da
zuciyarsa ga soyayyarki. Ku tallafi juna, ku baiwa zuciyoyinku abin da suke so.
Hajiyata da ‘yan uwana sun yi kuskure, sun kuma gane kuskuren su, sun yi nadama mai suna nadama amma
ku, (keda Amiru), Daddy da Habibu har yau kun ki karbar tuban su, ban san me yasa ba”.
Mairo ta yi murmushi wanda iyakacinsa fatar bakinta, ta ce,
“Mun karbi tubansu man? Watakila dai iyakar zaman ke nan, babu saura, tunda aka kawo wannan lokacin. Shi
ya gaya miki yana son komen? Yana da mace irin Hanan a gefe?”
Mamaki ya kama Amina, ta tabbata Mairo ba ta san tare suka yi waje ita da Hanan ba. Ta ce,
“A kan sakin Hanan aka yi naki, Allah sarki brother! Zurfin cikin shi na bani mamaki. A halin yanzu Hanan tana
Porthercourt ‘ya’yanta biyu tare da mijinta Ramadan wani ma’aikacin kwastom”.
Mairo ta yi shiru, kamar an zuke jinin jikinta. Tausayin Amiru ya kama ta, Allah kadai ya san halin da
rayuwarshi ke ciki.
Ta tura hannu cikin jakarta ta zaro wasu kananun katina da aka yiwa rubutu da kumfar golden, ta dorawa
Amina a cinya.
A kasalance Amina ta dauka, kati ne na gayyatar daurin auren PROF. JUNAID ATIKU GALADANCHI da DR.
MARYAM MOHAMMAD BEDI, wanda za a gabatar kwanaki goma sha hudu masu zuwa. Ba ta kai karshen
karanta katin bikin ba Amina ta rushe da kuka.
Ashe masu kukan suna da yawa, domin a can falon Baffa ma Hajiya ce ke ta kuka tana rokon Alh. Abbas ya yi
wa Amiru uziri, su ne da laifi ba shi ba. Su kuma ba su yi hakan da nufin A BARI YA HUCE…… ba, sai don a
bawa Mairo dama ta sarara ta cika burin neman iliminta. Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali
Daddy ya ce.
“Idan da mai laifi to ni ne, don ni na hana Amiru yin wani yunkuri na dawo da iyalinsa har tsawon wannan
lokacin. Ina so in koya masa jarumtaka, in nusar da shi cewa;
“kallafa rai a kan abin da ake so, da amanna da cewa samuwar abin nan kadai shi ne samun lafiya da
kwanciyar hankali ba shi ne ba”.
Dauriya, hakuri da juriya da tawakkkali sune halayen da ake son namiji ya suffantu dasu. Kuma na gode
Allah……. DUK WASU EXPERIMENTS DANA YIWA AMEERU BAI FADI KO DAYA BA…………..!!!”
Baffa ya jinjina kai ya ce.
“Nima in son samu ne, na fi son Mairo ta koma wurin mijinta ta tarbiyanci ‘ya’yanta a gabanta. Amma Alh.
Junaidu ya zarta duk yadda kuke tunani a wurin mu. Don haka bana cikin wannan magana….. Zabi yana ga
Mairo, tunda ita Allah ya baiwa damar zaben mijin da za ta iya zama da shi a halin yanzu. Don haka ku bani
kwana biyu zan tuntube ta”.
Habibu bai ce komai ba, don ba shi da ta cewar, bai san me zai ce ba, bayan Allah ya yiwa Mairo zabin alheri,
wannan karon ba zai yi shisshigi ba.
***
SUNA tafe cikin jirgi amma Daddy baya cikin nutsuwa. Tausayin gudan ransa ya ishe shi, ko ma me ya faru ya
tabbata shi ya jawo mishi. Shekaru uku ba kwana uku ba!!! Ya nesanta Amir da iyalinshi a kan laifin da ba
nashi ba. A kan hujjojin sa da basu da karfi.
Don haka suna sauka a jirgi ya bude waya ya kira Amiru yana nishi kamar mai ciwon asthma. Ya ce,
“Ka bar duk abin da kake ka taho, ka wuce Kano ka nemi sasanci da iyalinka in har kana so. Na amince maka
Amiru, da sanya albarkata…. saura kwana goma sha hudu a daurawa Mairo aure!!!”
Ga mamakin Daddy sai ya yi murmushi, wanda har sautinsa ya ratso cikin wayar, ya ce.
“Ka kwantar da hankalinka Daddy, na dade da sanyawa zuciyata salama, na yi amanna da cewa idan akwai
sauran zama tsakanina da Mairo, to za ta dawo mini ko ba dade ko ba jima”.
****
Lawan da Ahmad ‘ya’yan Baffa ne a harabar gidan Dr. Mairo, wanda ke a Area C cikin sabuwar jami’ar Bayero
suna wasan kwallon kwando, ya yin da a gefensu Habib da Amir ne tare da wasu sa’o’insu ‘ya’yan makota
suke wasan tsaren kekuna, yara masu ban sha’awa. Suna sanye da kayan sanyi masu laushi farare sol, an
rubuta I LUV MUMMY, kafafunsu daure cikin farin cambas, sunyi kyau har sun gaji kamar ‘ya’yan SouthWestern.
Daidai lokacin da motar kirar (Camero, 2 Door) ta yi parking and hankali a gefensu, matukin motar ya duba
katin da ke hannunsa ya tabbatar lambar gidan ta yi daidai da wadda ya gani a rubuce. Sai ya kashe ya fito.
Sanye yake da suwaitar ‘Dolce & Gabbana’ mai dogon hannu, da shudin wandon jeans. Ya yin da rigar ta
kasance fari da ratshin ja da blue. Ga duk wanda ya san shi, ba zai yi gaggawar gane shi ba, saboda yadda
fatar jikinshi ta kara kwanciya, tare da goguwa mai nuni da alamun hutu. Ya jawo bakin PRADA ya saya
kwayar idanun shi. Daidai lokacin da idanunshi suka kai ga sanyin idaniyarshi.
Ya dade yana kallon su yana murmushi, har bai san tsayin mintunan da ya bata a tsaye ba, ba tare da yaje
gare su ba, don ganin yadda hankalinsu ya raja’a a kan wasansu. Har sai lokacin da Amir ya karawa Habib
keken shi ya fadi, ya sanya kuka.
Da sassarfa ya karasa garesu, ya mika hannuwa ya dauki Habib wanda ke ta kuka ya rungume a kirjinshi, ya
kuma kama hannun Amir suka doshi kofar gidan. Su Lawan suka gaishe shi suka koma ga kwallon su, Lawan
na radawa Ahmed Baban su Amir ne.
Aikin marking takardun dalibai ya kacame mata, ta yi dai-dai da takardu a tsakiyar falon sanye cikin riga da
wandon da basu kama jikinta ba, kanta babu kallabi, tufkar gashinta a tsakiyar kanta. Fatar nan ta kara zama
fresh ta nuna mace danya sharaf, mai wadatar jini a jika, ta yadda ba za ka yi tunanin ta taba haihuwa ba.
Sassanyan kamshin ‘miyaki’ da ta dade da sani ne ya bakunci hancinta. A razane ta cira kai. Ta sake yin arba,
da dan Abdurrahaman Gaya. Rungume da ‘yan biyunshi masu tsananin kama dashi.
Sai dai wannan AMIRUN ya sha banban da wanda ta bari shekaru uku a baya. Ya sirance, ya bar lallausar
kasumba ta bata kyawun shi da tsarin shi, duk da haka yana nan a Amirun sa, dan gaye, mai kyau, kuma mai
sanyi, wanda idaniya ba za ta taba gajiyawa da kallon shi ba.
Mikewa ta yi tsaye kamar an umarce ta da yin hakan, alama ce ta girmamawa a wajen bature. Ta rasa cikin
yanayin da ta tsinci kanta tsakanin rudewa da gigicewa. Sannan wani sanyi ya tsirga a zuciyarta, ta lumshe ido
ta bude, ta tabbatar shi din ne, ba mai kama da shi ba.
Kafin ta yi wani action ya daga dogayen kafafunshi da sassarfa ya isa gareta, ya hada ta ita da yaran ya
rungume, jikinshi in ban da kyarma ba abinda yake. Ya kankame ta ita da yaran hawayenshi na sauka a gadon
bayansu. Ya ce,
“Mairo kin yi min alkawari…….. ba za ki taba barina ba, kin yi min alkawari…… we are meant for each other.
Me yasa kika karya?
Kin riga kin sani kowanne numfashina yana fita ne tare da sunanki. Me yasa kika amsawa Uncle Junaidu, kika
kasa jirana mu maida auren mu? Kika kasa yi min uziri? Uzurin da zan yiwa Daddy biyayya, kada ya ga rashin
juriyata?
Ya ya zamu yi da ’ya’yan da Allah ya bamu bayan fidda rai da samun su? Baki yi sha’awar ki rayu tare da su
ba? Ki basu tarbiyya irin taki? Jarrabawa ce Allah ya yi mana, kuma mun cinye ta da ikonsa, yanzu ne ya
kamata mu karbi sakamakon mu.
Zan nemi Uncle Junaid in roke shi alfarmar ya bar min ke, ko da hakan na nufin zan durkusa masa akan
gwiwoyina, don na fishi bukatarki, ‘ya’yanmu sun fishi bukatarki.
Kalle ni. Am all alone Mairo, leading a shattered life………!!!
Dukkansu basu ankara da wanzuwar mutum a falon ba, tsayin lokacin da suke rungume da juna suna kuka
dukkaninsu, su suna yi ‘ya’yan na yi. Sai jin karar rufe kofa da aka yi a hankali, suka juyo dukkanninsu, babu
kowa!
Amma kamshin ‘Irresistible Givenchy’ da Mairo ta ji, ya tabbatar mata da ko wane ne ya shigo, ya kuma fita,
ba tare da ya yi wani motsi da zai katse su daga kololuwar duniyar shaukin soyayyar juna da kewar juna da
suka fada ciki ba.
Hankalin Mairo ya tashi, ta tabbatar Uncle Junaidu ya ga Amiru, cikin halin da ita kanta ba ta san wanne ne
ba. Ta zame da karfi, da gudu ta biyo bayan shi amma sai kurar motarshi da hasken fitilar motar shi ta gani.
Ta rasa ina za ta sa kanta, sai ta kifa kai cikin tafukanta ta soma kuka. La shakka maza biyu take so, ba ta san
ya ya za ta yi dasu ba.
Lallashi na duniya, ban baki na duniya Amiru ya yi amma Mairo ta ki ce da shi komai. Ransa ya fara baci,
amma ya danne fushinsa, tunda mai nema…..baya fushi. Ya ce,
“Shi ke nan na tafi Mairo, na ba ki daga yau zuwa gobe ki yi tunani, zan je wajen Baffa daga nan zan wuce inda
na yi masauki, sai gobe insha Allahu”.
Ya dauki Amir ya kama hannun Habib za su fita, ta taso da gudu ta rike rigar shi ta baya cikin kuka ta ce,
“Ina za ka kai su?”
Ya harare ta ya ce, “Gidan ubansu, tunda bakya son ubansu to suma bakya son su”.
Ta ce, “Ni na ce hakan?”
Ya yi mata kallon rahma, sannan ya ce, “Za su taya ni kwana ne”.
Ba ta yi magana ba, ta shige daki ta hado musu duk abin da za su bukata cikin karamar jaka ta ba shi. Suka ce,
“Mummy bye-bye”. Ita ma ta daga hannun tana yi musu bye-bye din har suka fice daga falon.
Cikin hanzari ta dauki waya ta soma kiran nambar V.C Junaidu, bugu daya ya amsa, babu komi cikin muryarshi
sai kulawa ya ce,
“Ya aka yi MARYAMA?”
Ta shafe hawaye ta ce,
“Ka fasa zuwa yin ‘dinner’ din?”
Ya yi murmushi ya runtse idonsa, tsigar jikinsa na wani irin tashi saboda KISHI. Idanunshi na tariyo mishi
hoton abin da ya gani, wani image da bai taba ganin mafi muninsa a rayuwarsa ba, cikin sanyin murya ya ce,
“Na zo na tarar kina da bako, don haka na tafi”.
A raunane ta ce,
“Ba bako bane Baban su Amir ne ya zo ganin su”.
A ranshi ya ce,
“Ka ji rainin hankali irin na ‘ya’ya mata….”. Amma a zahiri ya ce,
“Ki saurare ni, idan na gama da Baffa zan kira ki”. Ya kashe layin.
Damuwar duniya ta ishe ta, ta kuma rasa abin yi, ta shiga halin rudani. Wadannan dakarun maza, jaruman
soyayya sun sanya ta a kwana. Tana neman Dina, tana neman Nabilah….. don neman shawara, tunda an ce
“Aikin mai shawara baya baci”.
Ta kira wayar Nabila, ta ce, “In kina gari zan zo gobe around 11”. Ta ce,
“Ina nan amaryar uncle sai kin zo”.
***
Junaid na yin parking a harabar gidan Baffa, shima Amiru na sawo kai, suka yiwa juna kallon-kallo, bayan
kowanne ya fito daga motarsa. Kwayar idon Amiru har girgiza take saboda KISHI, akwai wani feeling na kishi
iri daya a zuciyar kowannen su, sai dai babu wanda ya bari nashi ya fito fili.
Da sauri Amir da dan uwansa suka balle kofa suka nufi Uncle Junaid suka rungume kafafun shi, ya russuna ya
kama kowannen su da hannu daya ya dauke su, suna ta zuba mishi surutu wai Mummy tana kuka, don Abban
Abuja ya taho dasu. Ya yi murmushi ya ce,
“Zamu je mu lallashi Mummy ta daina kuka”.
An ce “mai Da, wawa….. sai Amiru ya karaso a hankali, ya mikawa V.C hannu, suka yi musabaha, aka rasa
wanda zai fara janye hannunsa. Dai-dai sanda Baffa ya fito, ya yi musu jagora zuwa falon ganawa da bakinsa.
Kallo daya zaka yiwa Alh. Abbas, ka san cewa shima a rikice yake, ya debo gorar ruwa da tambulan cikin firij
ya baiwa kowannen su. Aka rasa mai fara sha, aka rasa mai fara magana. Har shi kansa Baffan kuwa, kafin
Junaid ya yi gyaran murya cike da tausayin Baban Amir da Habib da ya ke ratsa zuciyarsa. Da ganin wannan
‘giant’ kaga wanda ke fama da dingimemiyar soyayya, wadda ta rasa madafa. Yaran sun baibaye Uncle
Junaidu sun kwanta a jikinsa.
Ya ce,
“Baffa na janye niyyata ta auren Maryama! Na hakura har ga Allah na barwa Baban Amir da Habib, ina bayan
Maryama ta koma dakin mijinta uban ‘ya’yanta, don samun kwanciyar hankalin kowannen mu.
Ba lallai sai na auri Mairo ba shi ne zan nuna ina kaunar ta, a’a, ni da Mairo mun wuce haka, Yaya ne da
kanwarsa, alakarmu hadi ne daga Allah, ba don mu yi aure ba.
Ina son ‘yan biyu su tashi gaban uwa da ubansu……kamar yadda Maryama ta tashi gaban Innarta da Babanta,
ta san dadin iyaye, tasan amfanin su. Nikuma ina bukatar addu’arku Baffa, da fatan dorewar zumunci na har
abada a tsakanin mu”.
Baffa ya ce,
“Allahu Akbar! Allahu akbar!! Wannan shi ne halin GIRMA, halin ‘yan aljannah!! Da gaske ne kai da Mairo kun
fi karfin soyayyah!!! Sai ‘yan uwantaka, mun gode da wannan karamci Junaidu, Allah ya biya maka bukatunka
na duniya da lahira, ya kara maka daukaka, ya baka duk abinda kakeso a duniya da lahira……”.
Amiru ya cira kai ya tsura ma Junaid ido ya ce, “In aka yi hakan, ni kuma na so kaina…….”.
Junaidu ya ce,
“Ni kuma ba zan auri Mairo alhalin zuciyarta na ga tsohon mijinta ba”.
Amiru yace
“nayi rantsuwa da Allah! Mairo tayi maka son da ni bata yimin ba, na aure ta ba da son ranta ba, sai a hankali
na koya mata soyayyata. Uncle Junaidu kana da matsayi mai girma a gun Mairo, wanda ni bani da shi…..”
Junaid ya rausayar da kai cikin jin wani irin frin ciki a zuciyarsa, koda wannan ya tsira ya tabbata ya isheshi
rayuwar duniya, yayi murmushi ya ce,
“Kauna ce tsakanina da Mairo Amiru ba soyayyar aure ba tun daga ranar dana fara ganinta, a halin yanzu jin
nauyin junanmu ya fi yawa, wanda da kyar za mu iya sakin jiki da juna mu yi rayuwar aure yadda ya kamata.
Ka yarda ko kada ka yarda, kai Mairo take yiwa soyayyar aure….!”
Amiru ya lumshe ido, ya ce,
“Uncle Junaid, bani da bakin da zan gode maka……. bani da abin da zan biyaka wannan alfarmar da ka yi
min…..” Uncle ya yi murmushi ya katseshi yace,
“Kana dashi Amiru!.
Mairo ta sha bani labarin soyayyar da kanwarka Amina take yi mata, wannan wadda suka zo mai kama da kai.
Ta shaida min cewa maigidanta ya rasu. Ka bani Amina in aura Amiru, don wanzar da dauwamammen
zumunci a tsakanin mu”.
Cikin al’ajabi Amiru ya ce,
“Amina is special a gare ni ko a cikin kannena goma sha biyu, lallai Amina is among the luckiest….
Na taba gayawa Habibu zan roke ka ka bar mini Mairo, ni kuma in baka kannena hudu ba lefe ba sadaki. Na
fada ne kawai a fatar baki, ashe Mala’iku sun amsa. Uncle Allah ya kara GIRMA!”.
Suka hade hannunsu suka cure kamar ba za su saki ba cike da wata shahararriyar kauna daga Allah, Baffa ya ja
su doguwar addu’a suka shafa. Baffa ya ce, su barshi da Mairo, su ci gaba da shirye-shiryen su, yana so zai yi
mata ba-zata ne. Suka yi murmushi. ***
Kwana ta yi tana gwada lambar Uncle Junaid ba ta samu ba. Ta shiga damuwa sosai. Tsoron ta kada Allah yasa
fushi ya yi saboda ganinta da ya yi tare da tsohon mijinta.
Abu kamar wasa Uncle har kwana uku babu wayarshi babu kafarsa cikin gidanta, don haka ta yi tattaki har
office amma ba ta same shi ba. Shima Amiru ko sallama bai zo ya yi mata ba, ya kwashe ‘ya’yansa ya tafi
Abuja dasu ba ta kara jin duriyarsu ba.
Da albishir mai dadi ya tari Alh. Abdurrahaman da Hajiya Aisha, ya kuma gaya musu bukatar V.C na auren
Amina. Daddy da Hajiya suka yi ta hamdala tare da kara yawaita sadaka. Ko da Amir ya tuntubi Amina ya yi
mamakin amincewar ta nan take. Bai san ita tunda ta dora ido a kan Junaidun ba ta kara gane kanta ba.
Ya yiwa gidan Habibu tsinke a daren bakinshi ya kasa rufo, zumudin ya gaza boyuwa. Habibu ya dafa
kafadarshi ya ce
“Angon Harrit ya aka yi?”
Ya harare shi ya ture hannunsa daga kafadunshi, ya ce,
“Kai komi mai muhimmanci sai kasa iskanci da shakiyanci a cikinsa, to bani goro in baka albishir”. Ya ce,
“To bari ina zuwa”.
Ya fito jim kadan bayan shigarsa da kwalin ‘Aspen’ da ‘Lighter’, ya zari daya ya kunna ya manna mishi a baki.
Da sauri ya ture ya bige hannunsa, tabar ta fadi, ya bi ya take da takalminsa, cikin takaici ya ce,
“Wai don Allah Yaya Habibu, yaushe za ka girma ne?”
Ya yi dariya ya ce,
“Sai ranar da son Mairo ya daina kai ka hanyar lahira, ya daina kwantar da kai a asibiti, wato ranar da ka
zama namijin duniya”.
Dina ta yi dariya ta ce,
“Rabu da shi Amiru, muna nan muna jiran nashi turn din, idan ya gano wata ‘yar kwailar. Irin su Habib ba ciwo
suke a kan soyayya ba, rijiya suke fadawa dungurungum su kashe kansu in sun rasa samun wadda suke so….”.
Ya ce,
“Amma kin yanke ni ke da sirikinki bashi kuka ci, akwai ranar da zaku biya shi”. Amiru ya ce,
“Na ma fasa baka albishir din, tunda da Taba za ka hadani, ka jawo min fushin Mairo, ban ji ba ban gani
ba……”.
Ya kamo hannunshi ya fizge, yana dariya ya ce, “Haba dear…. tuni na ji albishir din, ai Baffa ya gaya min komi
yanzun nan, kun yiwa V.C Junaidu fin karfi kun toshe masa baki da Amina”. Ya yi dariya ya ce,
“V.C mutum ne mai saukin kai, yadda na zaceshi ba haka yake ba, ya ji tausayinmu ya tallafi rayuwarmu shima
Allah ya tallafesa. Bani da abin da zan biya shi wannan sadaukarwa da ya yi min koda na bashi my favourite
sister. Wanda na san zai karba ne ba don so ba, sai don kulluwar zumunci a tsakaninmu”.
****
Tana shirin fita office wayar Baffa ta shigo, da hanzari ta amsa cike da girmamawa. Bayan sun gaisa ya ce,
“Kina gida ne yanzu?” Ta ce,
“A’a, ina shirin fita ne zan ba da lacca 8-10”. Ya ce, “To in kin fito ki zo ina son ganin ki”. Ta ce, “Babu damuwa
Baffa sai na iso”. Suka aje wayar a lokaci daya.
Karfe goma na safe ta fito daga ‘twin-theater’ cikin rakiyar zugar dalibanta, wadanda suka riko mata jakar
hannunta da takardunta har zuwa inda ta adana Terrain din ta, ta karbi kayan hannunsu suka yi sallama suka
koma, ita kuma ta zaburo mota sai Yakasai gidan Alh. Abbas.
Bayan sun gaisa da Habiba da Hajara da su Rahama, ta samu Baffa a falonsa, ya nuna mata waje ta zauna, ta
zamo daga kujera ta dira gwiwoyinta a kasa ta gaida shi. Ya amsa yana duban ta sosai, ganin yadda ta ramar
da kanta cikin ‘yan kwanaki kalilan saboda damuwa. Bai nuna mata komi game da zuwan Junaid da Amir ba,
tambaya ta farko da ya watso mata ita ce.
“Mairo maza biyu za ki aura ne???”
Ta cira kai da sauri ta dubi Baffanta, ya girgiza kai ya ce, “Yo maza biyu mana?
Kin amshi maganar Junaidu, an gama komi sai shafa fatiha kadai ya rage, sai kuma ki turo min Alh.
Abdurrahaman da kansa ya zo bikon ki? Sannan shima Amiru ya zo, dukkanninsu da rokon a maida aure.
To dukkansu akwai mutunci da ganin girman juna tsakanina dasu. Don haka bana bayan kowa, zabi yana gare
ki, kamar yadda shari’a ta baki dama. Ina so ki gaya min wanda kika fitar ni kuma ranar da na sanya ba zan
daga ba zan daura aure”.
Kanta a sunkuye ba ta yi magana ba, har sai da Baffa ya gama yana sauraron ta. Ganin ta ki yin magana ya ce,
“Kefa nake saurare Mairo”.
Daga can kasan makoshinta ta ce,
“Baffa ni bani da zabi a cikinsu, kamar yadda ka ce sharia ta bani damar in zaba, ni kuma na baka wannan
damar, ka daura da duk wanda ka ga ya dace. Duka ina son su ina kaunar su, don haka ba zan iya zaben daya
a cikin su ba”.
Baffa ya girgiza kai yana murmushi. Autar Inna Hure, bai san sanda zata daina yarinta ba!.
Ya ce,
“To shi kenan, tunda haka kika ce, na kuma gode da wannan GIRMA da kika bani, ya nuna min cewa kin
amince ba zan yi miki zaben tumun dare ba.
Da fatan duk wanda na zaba miki a cikinsu za ki yi min biyayya shima ki yi masa, ba tare da an tsaya yin wasu
tone-tone da kwakulo laifin da ya riga ya shige ba, za ki zauna lafiya dashi har karshen rayuwarmu”.
Kanta a kasa ta ce,
“Na yi wannan alkawarin Baffa”. Ya ce, “To tashi ki koma kan aikin ki, Allah ya yi miki albarka”.
Cikin zuciyarta ta ce, “Amin”. Ta taso ta fito kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Daga Amiru har Junaid ba ta kara jin duriyar kowa ba. Ta bi shawarar Nabilah, da ta ce dukkansu kar ta neme
su ta rabu dasu.
Sai ana i gobe daurin auren da ba ta san da wa Baffa zai daura ba a cikinsu. Text din Uncle Junaid ya
shigo cikin wayarta da misalin karfe uku na sulusin dare. Ta zaro wayar daga karkashin filonta, hannunta na
rawa ta duba, ga abin da ke rubuce.
SAKON UNCLE JUNAID GA MAIRO!
“Marriage is much more important than mere relationship. It’s the root of all family tree. Any mistake in
sowing the seed will be disastrous…. a mature seed has better chances for germinating than an immature
one…. A garden close to one’s home has to be watered and tendered than that which is very far
away……………….
-Mai son ki.
(wato aure yafi muhimmanci fiye da dangantaka kawai. Domin shine jijiyar bishiyar iyali gaba daya, don haka
hadari ne babba asamu kuskure wajen dasa wannan bishiya…. kosashshen iri zai fi saurin yado fiye da
talalabuwa…. lambun da yake kusa da gidan ka zaka fi bashi ruwa da kulawa, fiye da wanda yake
nesa………….).
Ta karanta ya fi cikin carbi, kafin ta fahimci me sakon Uncle yake nufi. Yanzu ne ta fahimci ashe duk sakonnin
nan da ake turo mata tana Michigan da ‘logo’ na hular ilmi, ashe Uncle Junaidu ne. Ta kifa kai cikin filon ta,
tana kuka mara sauti. Kukan tausayin Uncle Junaidu! A lokacinda ta fahimci Uncle Junaid ya sadaukar da
soyayyarshi ga aurenta da ‘ya’yanta….. Ta yadda har ya kira alakarsu da ‘mere relationship’. Ita ma ta yarda ta
amince AMIRU SHI NE ZABIN ALLAH, ba zabin zuciyarta ba……!!!
Daga kowanne bangare ba su samu matsala ba, sun samu kwarin gwiwa daga Baffa, Yaya Habibu da Alh.
Abdurrahman Gaya. Wadanda burinsu kenan. Hatta Hanan wadda ke da ‘ya’ya biyu a lokacin da mijinta
Ramadan ta samu halartar walimar maida auren Dr. Mairo da Amirunta, Amina da Uncle Junaidu, wadda aka
gabatar a ranar asabar, juma’a, ashirin ga watan maris, daruruwan jama’a suka shaida daurin auren Mairo da
Amiru a karo na biyu, a kofar gidan Alh. Abbas mai goro.
Wannan aure ya ga kusoshin ilmi, daga Kano da wajenta, da daukacin jami’o’in Najeriya. Furofesoshi,
kwamishinoni da daktocin ilmi, abin ba a cewa komi.
Daga Mairo har Ameeru babu mai ra’ayin bidi’o’i, dokance suke da a sake mallaka musu juna. Tsohuwar
soyayya ce ke aiki tare da taimakon sabuwar soyayya. Ta dankawa Alh. Abdurrahman da Hajiya Aisha
jikokinsu kamar yadda suka nemi alfarmarta, sai fatan Allah Ya ba ta wasu masu albarka.
Tana nan zaune a bakin gadonta, tana jiran angon wanda ke can yana ganawa da bakinshi, tare da duba
agogon hannunta.
Rabin awa kenan da fitar Dina, ta fada bayi ta sake sheko wanka mai suna wanka, tunda kuwa ba ta taba yin
irinshi a rayuwarta ba. Ta feshe jikinta da ‘fehrenheit’ da ‘cerruti’ dinta kamar yadda ya ke a al’adarta.
Tana kokarin sanya kayan barci ya turo kofar ya shigo cikin bulalen ‘pyjamas’ yana rike da wani dan fulas mai
tsananin kyau. Kunya ta kama Mairo, kamar bata taba sanin Amirun nata ba, wanda hakan ya janyo ta sanya
rigar a bai-bai.
Amir ya yi murmushi, ya rausayar da kai ya iso gare ta, ya ajiye filas din hannunshi a gefe, ya dora kanshi a
dogon wuyanta. At last! Sa’ar tashi ce a karo na biyu. Gashi ga Maironsa, bayan gushewar shekaru uku
kwarara, cikin duniyar kuntatacciyar soyayya. Shikuwa me zai yiwa Uncle Junaidu, ya biya shi a wannan
duniyar? Babu, sai adduar Alheri.
Kyawawan fuskokinsu suka zahhara cikin mudubin. Dukkansu suka saki sassanyar ajiyar zuciya mai nauyi.
Wadda ke cike da godiya ga Allah!
Cancarakas! Ya dagata ita da filas din da ya shigo da shi sai ‘bed-room’ dinsu. Ya zaunar da ita a bakin gado, ya
mika mata filas din, ya ce.
“Sako ne daga Nabilah, ta ce hannu-da-hannu na baki. Ya zama shi ne cimarmu a wannan daren, sai dai ban
san ko mene ne a ciki ba”.
Ta soma kicin-kicin bude filas din, da kyar ta samu ta bude. Suka bi cikin filas din da kallo dukkanninsu.
“Kwadon Rama” ne wanda ya ji kuli-kuli, tumatur da albasa sai kamshi ya ke. Dariya ta kama Mairo, don ta
lura Nabilah dai na son a TUNA BAYA…….. ne.
Mairo ta soma cin kwadon ramarta sosai, kunnenta kamar ya tsinke don dadi. Ta kusa cinyewa ya rike fulas
din, ya rausayar da ido yana yi mata kallon nan nasa da shanyayyun idanun nan nasa, wanda ya kassara
kuzarin jikinta. Ya tada wani tsohon al’amari, wanda ya riga ya shude a tsammaninta. Amir da Mairo, suka ce
“Takori kauce a nan, yau bama bukatarki”.
***
Washegari Daddy yayi kiransu, ya danka musu ‘passport’ dinsu, mai dauke da visar kasashen duniya guda
uku; Athens, Amsterdam da Pretoria. Yace da Amir yayi amfani da hutun sa na karshen shekara suje su huta
tsayin watanni uku.
Mairo bata tashi dawowa ba, sai da guzurin ciki watanni biyu dan Pretoria. Bayan sun dawo ta nemi chanjin
wajen aiki zuwa jami’ar Abuja, ba da son ranta ba, sai don ta samu kasancewa full-time da mijin ta. Abin son
ta. Uban ‘ya’yanta kuma abin kaunarta; Dan Abdurrahman Gaya.
A shekarar ne kuma akayi bikin kaddamar da Amiru Abdurrahman matsayin gwamnan CBN, bayan gwamna
mai ci a lokacin yayi ritaya. Ba don shekarun shi sun kai ba, sai don kwarewa da sanin makamar aiki da dimbin
tagomashin cigaba da ya kawowa Central Bank of Nigeria a matsayinsa na tsohon ma’aikacin World Bank.
Shima Uncle Junaidu ya samu ‘promotion’ zuwa ‘chancellor’ na jami’ar Bayero bakidaya. Zumunci da aminci
bai taba yankewa tsakanin su ba.
Shekara na zagayowa Mairo ta direwa Hajiyar Amiru wani saitin ‘twins’ din data zabi a bawa sunan (Ilham da
Sagir) kannen Uncle, don bazata taba mantawa da kaunar da Ilham ta nuna mata ba. Uncle yaji dadi kwarai
kuma ya kawo Ilham daga Wales don kawai taga takwararta. Farin cikin Hajiya Aisha abin ba a cewa komai.
Dina ma ta sake samun Hurairah (Hure) bayan fidda rai. Amina ta samu Atiku, Ikhlas ma matar Uncle ta sake
haihuwa. To haka Nabilah duka hayayyafa suke kamar kaji, sai mu ce Allah Ya raya, kuma Allah Ya kara
dankon zumunci.
MASHA ALLAHU LA-KUWWATA ILLA BILLAH…
Maman Safah da Marwah ce….ke cewa.
Sai mun hadu a sabon littafin YAKANAH cikin yardar Maiduka.
Dandano Daga Yakanah
Karfe goma sha dayan dare garin kano yayi tsit, sai iskar hunturu dake kadawa. Malam Ja’afar ya dauko
tabarmar sa ya shigo cikin gida daga soron kofar gida. Zai gitta ta dakin Fati ya jiyo sheshshekar kukanta. Ya
dakata, ya dago labulen yana kallonta.
Tana zaune akan darduma ta kunshe fuskarta cikin hijabi sai kuka take. ya karashe shigowa cikin
dakin yace “Fadimatu kukan me kike yi?
A razane ta cira kai ta dube shi idanunta jawur sun yi luhu-luhu alamar tayi kuka har ta gode Allah.
Malam Ja’afar ya zauna a wata ‘yar kujera dake dakin yana fuskantar diyarsa. Ta share idonta da
hankici, ta ja shashsheka kafin tace “Baba babu komai” ya jima yana kallonta sannan yayi murmushi yace
“kina tuhumar mu dayi miki auren da baki so, auren mijin ‘yar uwar ki. Ki yi hakuri, alheri muke nufin ku da
shi, ba zaki gane ba sai nan gaba. Idan kun gano gatan da muka yiwa rayuwarku”
Fati tayi shiru tana sauraron babansu. Taga wannan itace damarta ta karshe. Daga gobe za’a zarga
mata igiyoyin wanda baya sonta. Ta kai kanta kasa tana kuka sosai tace “ku yi min alfarma Baba. Baba baka
taba sa ni in yi wani abu na shallake maganarka ba.
Amma a wannan karon ina so ka dubi hujjoji na. Baba. Dr Sulaiman baya so na, baba Dr. Sulaiman yafi karfi
na. bani da ilimin da zan jera da shi a matsayin matarsa. Baba sulaiman bazai taba son wata ba bayan son da
yake yiwa yaya Hadiza. Baba kune baku sani ba, amma Dr. sulaiman ya tsaneni ban san laifin da nayi masa ba.
Ban taba gaishe shi ya amsa ba, haka bai taba kallona a matsayini jinin Hadiza ba balle yayi la’akari da wannan
ya kaunace ni. In dai don ‘ya’yanshi ne, ai nima ‘ya’yana ne…zan cigaba da rike su ba sai na zama matarsa
ba……”
Ya ce “Amma zaki zama matar wani ko? Kuma babu wanda zai aureki da zugar ‘ya’yan yayar ki. naji hujjojin ki
Fati, amma nima ina so in tambayeki “wane abu ne Hadiza take da shi wanda ya kaita ga matakin zama matar
Babban likita irin Sulaiman???? Tana ‘yar talakawa kamar ki???
Mu biyo Fati da Babanta a littafin YAKANAH yana zuwa bada jimawa ba!!!! __________-_TAKORI
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na
www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana
soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu
su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu
don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da
wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau – kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi
kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau – manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi,
duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau – Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF
da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book
summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that – we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that
collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that – pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels
through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that – our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with
android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT