MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 41 to 50

Ya fi mintuna biyar a cikin motan be fito ba koda yayi parcking ɗin motan a cikin gidaSecurities ɗin sa duk sun zo sun mamaye wurin har ɗaya ya buɗe masa ƙofan motan suna miƙa mishi gaisuwa

Sai dai ya ɗaga musu hannu be ce komi ba. Ɗan numfashi ya ja kafin ya ziro dogayen ƙafafuwan sa ya fito a motan, sannan ya taka ya wuce ya nufi Part ɗin Momy. Nocking yayi da sallama ya shiga ciki

Da gudu Hafsah da Yusra suka yo kanshi ganin mahaifin nasu suna murna

Nan da nan ya haɗa su ya rungume cike da fara’a yana ɗaukar su ɗaya bayan ɗaya yana ajiye wa. Kana kuma ya riƙe musu hannu zuwa kan kujeran yana tambayar su Momy

Kafin ma su ba shi amsar sai ga ta ta fito a ɗaki tana washe baki tace, “ah ah my son ka dawo?”

“Wlh kuwa Momy. Ina wuni?”

“Lafiya lau. Nayi mamaki da aka ce min ka fita, kuma ga shi har yammaci tayi baka dawo ba duk hankali na ya tashi, yanzu nake cewa Luwaira ta kira min kai a wayanta tunda nawa ya ƙi shiga.”

Murmusawa yayi yace, “ayya Momy kiyi haƙuri na tayar miki da hankali. It’s something I do and it’s important that I go out.”

“Masha Allah tunda Babu abunda ya same ka ka dawo gida Lafiya, abun da nake ji dama kenan shiyasa duk na tashi hankali na.” Sai kuma ta kalli su Yusra tace, “an ga Dady ana ta murna ko?”

“Momy dama akwai maganar da zamu yi. Maganar aure na insha Allahu yanzu na samu wacce nake so zan aura.”

Sosai maganar ta zo wa Momy a bazata, wani irin sarawa ƙirjin ta yayi wanda ya hana ta magana, sai da ta ɗan ja seconni kafin ta buɗe baki cike da murnan da iyakan shi fuska tace, “Masha Allah Son, yau ka faranta min abun da na jima ina fatan ji daga bakin ka, ai hakan ya fi shi ne zai ƙara kankaro maka mutunci ka zama babban mutum. Aina yarinyar take?”

Yana murmushi yace, “yarinyar Aunty ce ai, ƴar Yayar Hashim Aboki na.”

“Oh ko wannan yarinyar wacce muka haɗu a asibiti?”

“Eh ita Momy.”

Murmushin yaƙe tayi tace, “Masha Allah sosai kuka dace kuma, ai yarinyan naga kamar babu ruwan ta, yanzu kuma zumunci zai ƙara ƙulluwa kenan kai da Hashim? Abun gunun sha’awa wlh tunda zai baka yar shi ai haka ake so.”

Shi dai murmushi kaɗai yayi

Tace, “alhmadulillah ai komi yanzu ya zo da sauƙi tunda ka samu Matar Aure, ko su Hafsa zasu ji daɗi ai idan aka ce sun sami Mahaifiya. Allah yasa ayi damu.”

“Amin Momy. Abdul be shigo nan bane?”

“Eh ina tunanin ma ba ya gidan, amma na san bazai jima ba zai shigo tunda dare ya fara.”

Miƙe wa yayi yace, “zai tafi.” Sannan yayi mata sallama suka fice da yaran.

              Kai tsaye Part ɗin shi ya nufa, ya saka yaran suyi alwala sannan shima yayi, sai da ya tabbatar sun tayar da Sallan ya bar su a nan falo ya wuce masjid ɗin da ke a cikin gidan.

                 *******

          Momy kasa motsa wa tayi a wurin tun fitan shi gaba ɗaya hankalin ta ya tashi

Fitowar Luwaira daga ɗaki ne ta zauna tana tambayar ta da cewa, “Momy kamar na ji muryan Yaya Umar a nan ina Toilet. Ya dawo ne?”

Kallon ta Momyn tayi bata iya ce mata komi ba domin hankalin ta ya fita a jikin ta tunani ya sha mata kai

Sai da ta sake magana ne tana tambayar ta, “Wai Momy lafiya kika yi shiru?”

“Babu lafiya Luwaira. Ina Abdul kira min wayan shi yayi maza-maza ya zo?”

Yanda ta ga hankalin ta ya tashi ne yasa ta tashi da sauri ta nufi ɗaki ta ɗauko wayan nata ba tare da ta sake furta komi ba, sai da ta kira shi kafin ta sake kallon ta tace, “Momy wai lafiya ki sanar min don Allah?”

“Ki bari Abdul ya zo”.

             Babu jima wa sai ga Abdul ɗin ya shigo tunda dama ya iso gida. Koda ya shigo ya gansu a haka shima tambyar ya soma jeho wa

A nan Momy ta sanar musu da zancen da Umar Faruk ya faɗa mata

Luwaira kasa cewa komi tayi saboda tashin hankali

“Momy wacce yarinyar kika ce zai aura?”

“Wannan yarinyar da suka zo gaishe shi a asibiti da su Hajiyan Hashim.”

Saurin tashi tsaye yayi ya furta, “Whattt..?”

Kallon sa Momy tayi tana karantan yanayin sa ganin yanda gaba ɗaya tsananin tashin hankali ya nuna a fuskar sa. Kafin ma tayi magana sai ji suka yi Luwaira ta faɗi ƙasa a sume. Tuni Momy tayi kanta ita da Talatu wacce ta fito daga ɗakin ta ta hangi me ke faruwa

Shi kuwa Abdul a halin da yake ciki yana ga ya fi ta shiga tashin hankali, shiyasa be bi ta kansu ba ya juya ya fice da sauri ya nufi Part ɗin shi. Yana shiga ya faɗa kan kujera yana mayar da numfashi, sai kuma ya kama kanshi zuciyar sa tana tafarfasa kamar zata faso ƙirjin sa, kawai maganar Momyn ne ke dawo mishi a kwanya, taya zai bari ya rasa yarinyan nan bayan ya rigada ya kamu da ƙaunar ta? Ya za’a yi ma ace Umar Faruk ne zai aure ta? Haba bazai yiwu ba.. sai kuma ya tashi tsaye ya nufi cikin bedroom ɗin shi kamar zai tashi sama.

               Ruwa talatu ta ɗibo aka zuba mata kafin ta farfaɗo

Ganin sambatun da take yi ne sai Momy ta kalli Talatu tace, “je ki kiyi aikin ki.”

Hakan yasa ta tashi ta wuce har tana jiyowa tana kallon su, sai kuma ta taɓe baki a ranta tace, “babban magana. Akwai tashin hankali kenan.”

Momy kuwa tana ganin Talatu ta shige sai ta kalli Luwairan tace, “ke ki yiwa mutane shiru kina hauka ne zaki tona mana Asiri?”

Kuka ta fashe da shi tana cewa, “Haba Momy ke kin san a halin da nake ciki ne? Wlh ji nake yi kamar zuciyata zata faso ƙirji na saboda zancen ki, bazan iya jure wa ba wlh, bazan iya bari wata ta shigo gidan nan a matsayin Matar Umar Faruk ba, Ni ce zan aure shi, idan har ban aure shi ba to babu shi babu wani auren, sai dai duk abinda za’a yi ayi bazan bari ba.” Sai ta sake kece wa da kuka

Dole Momy ta koma rarrashin ta tace, “ki tashi ki wuce ɗaki kiyi sallah, zamu yi maganar daga baya domin nima bazan bari wata ta shigo gidan nan ba gwara ke ki aure shi.”

“Da gaske Momy?” Tafaɗa da sauri jin abinda Momyn tace

“Ki tashi nace ki wuce ban son iskanci.”

Dole ta tashi tana faman hawaye ta wuce ɗakin ta

Ita kuma Momy kasa tashi tayi saboda ruɗu da tashin hankalin da yake cin ranta, duk ta rasa abun yi, daga baya kuma ta miƙe ta wuce ɗakin ta.

                ✳️✳️✳️✳️✳️

               Sai da aka yi sallan isha’i sannan ya dawo gida. Da ya shiga parlour’n su Hafsah suna zaune suna kallo. Yana shigowa suka zo suka ƙanƙame shi suna kiran sunan shi. Ya kama su suka zauna yana cewa, “My babies har Kun idar da sallan?”

“Eh Dady.” Suka haɗa baki wajen faɗa

Shafa kansu yayi ya dubi wajen dainning. Sai kuma yace, “ok to ku tashi mu je ku ci abinci.”

Tashi suka yi suka nufi wajen dainning ɗin. Bayan sun zauna ya zuba wa kowa abinda yake so kafin suka soma ci

Shima abincin yake ci amma hankalin shi na kan wayan shi, laluba Numban MEEMA da Uncle Hashim ya turo mishi yayi, sai da yayi saving kafin ya danna kira. Lumshe idanun sa yayi ya buɗe sanda ya ji wayan ta soma Ring, sai dai har ta tsinke ba’a ɗaga ba sai ya sake kira, nan ma shiru dole ya haƙura ya mayar da hankalin sa kan abincin sa. But ko kaɗan ya gaza ci sosai saboda tunanuka da suka yi masa yawa, surutun da su Hafsah suke mishi ma kaɗan-kaɗan yake amsa musu tunda hankalin shi ba ya wurin. Sai da suka gama yace, “su wuce ɗaki yana zuwa.” Daga baya ya bi bayan su ya ciro musu kayan barci suka saka sannan yace, “su hau gadon su kwanta.” Yayi musu addu’a ya fice ya koma ɗakin sa

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button