Uncategorized

MATAR UBA 18

Ad

_____

 💦💦💦💦💦💦💦💦     *MATAR UBA*

💦💦💦💦💦💦💦💦

Daga Alkalamin ✍️

      

       *Milly*

                   Fadilah Yakub

                 *(MILHAAT)*

*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️*

                   *M. W. A*

 *Bismillahir Rahmanir Rahim*

Ad

CHAPTER 18

NOT EDITED

💦💦💦💦💦💦💦💦

Yesmin ganin mahaifiyar ta bata fito ba hakan yasa ta Shiga kicin ta had’a wa kanta breakfast ta wuce makaranta.

💦💦💦💦💦💦💦💦

WASHE GARI

………… Hashim na farkawa bayan ya idar da sallar asuba ya kud’iri aniyar yau sai ya Asiyar sa, shiryawa yayi tsaf a gaggauce ya nufi hanyar gidan su Asiyah, tun karfe shida da minti arba’in yake kofar gidan su Yana zaune a cikin motar sa bai da wani buri sai na ganin ta, har bacci ya Fara d’aukan sa kasantuwar jiya ya kasa bacci, Jin karar mota yasa yayi saurin d’ago kansa dake Kan stairing motar, Murmushi yayi yace “Alhamdulillah makaranta za’a Kai su” bin bayar motar yake har suka Isa makarantar Amma ga mamakin sa Safiya kad’ai ya gani, jikin sa duk yayi sanyi, anan NE ya tuna Asiyah ta tab’a fad’a Masa bad kaita da mota murmushin takaici yayi har ya juya sai Kuma ya dawo cikin sauri ya Isa inda Safiya take sai kaud’i da Rawar Kai take, Sunnan ta ya Kira cikin sanyin murya da sauri ta juya don ta tabbatar was kanta abinda kunnen ta yake jiye Mata, a fad’in ta a tarihin rayuwar ta Bata tab’a gani ko Jin Mai murya irin tasa ba.

Murmushi tayi had’i da dafa kirji race “Na am” Shima murmushin yayi yace “Dan Allah in baza ki damu ba Inna so nayi magana dake.”

A dai dai na bell na assembly ya Fara kara, Murmushi tayi Tace “Ba matsalar mu d’an koma daga gefe.”

Bayan sun gaisa yayi shiru Yana kallon kafarsa ya rasa ta ina zai Fara tambayan ta inda Asiyah take a yayin da ita Kuma sai murmushi take “Finally Allah ya karb’i addu’a ta, idan ya furta kalmar so a gare Ni na bar makaranta Kenan don Wallahi, bazan Bari ya kufce min ba, I love you so much my prince” zancen zuci take, maganar da yayi ne yasa tayi saurin kallon sa Nan da Nan ta had’a Rai kamar bata tab’a dariya ba, Rai a d’an b’ace Tace “me naji kace?”

Gyara tsayuwar sa yayi yace “Cewa nayi, Inna Asiyah take in ta cikiyar ta yau kwanaki uku Kenan ban sa ta a Idona ba.”

Wani abune taji ya rike Mata wuya, kirkiran Murmushi tayi Tace ” Ban sani ba” tayi saurin juyawa don Kar yaga hawayen dake idon ta, cikin sauri ya rike Jakarta Yana fad’in “Dan Allah Safiya ki fad’a min inda take, zan biya ki ko nawa ne, Dan Allah ki taimake Ni” hannu a had’e alamun roko, girgiza kai tayi Tace ” Me zakayi da wata Asiya Hashim kasan fa Ina sonka Kuma ina kaunar ka, harfa gidan ku naje na cire kunyata Amma kai baka gani, dame ta fini ne Dan Allah Hashim ka manta da maganar Asiyah” ta Kara maganar cikin kuka.

Tausayin ta ne ya kamashi don yasan illan rashin abinda kake, yace “ba Wai bana sonki bane ki fahimce ni hankali na ya karkatane a Kan ta, Amma yanzu maganganun ki sun San na fahimci wani Abu, zan Baki number ta sai muyi magana amma da Sharid’i d’aya” Yana nuna Mata Yar yatsan sa, sa hannu tayi ta share hawayen ta Tace “Mene ne sharad’in?”

“Sharad’in shine Zaki fad’a min inda Asiyah take, and I promise za mu zauna mu fahimci juna dake, Akwai Ajiyata a gun ta shiyasa Kika ga ba damu sannan abin sirri ne bawai ita d’in nake son gani ba, kin fahimce Ni?”

Kallon ka Raina min wayo ta Masa a zuciyar ta Tace “Ji d’an raining gabkaliy Ni zai rainawa hankali wai baya sonta, Amma idan Kuma dagaske yake fa? Kai Bai kamata na Bari wannan Daman ya wuce Ni ba, this is my only chance” iska ta hura tace ” zan fad’a maka inda take, Amma ja sani idan na Kira ka baka d’aga ba bazan sake taimaka maka ba, sannan Ina so na San Wace irin ajiya ce”

Murmushin cin nasara yayi kana yace ” Kar ki damu you have my words, Ina zuwa” komawa yayi mota ya d’auko katin sa ya Mika nata yace ” Uhmn Ina sauraron ki Ina take?”

Tsotsa keya tayi irin na Mara gaskiya tace ” Tana asibiti” a takaicw, Hashim Jin ta ambaci asibiti hakan ya tada Masa hankali,  yayi kokarin b’oye tashin hankali da ya Shiga Amma ya kasa, kad’a Kai kawaii Safiya tayi Tace “Sai anjima” ta shige makaranta, Hashim ya d’auki kusan mintuna biyu a tsaye jiki ba Karfi ya shige motar sa, ya kunna key ya bar gun sai da yayi nisa ya taka birki wani Kara naji kiiiikkii, ya daki stairing motar da karhi yace “God damn it, ban tambayeta a wani asibiti take ba, Taya za’ayi na nema ta? Kuma me ya same ta? Hashim me Yake damin ka ne?” Magana yake shi kad’ai Kuma da mugun Karfi da ba don glass din motar a d’age ba na tabbata da mutannen dake wucewa zasu ji abinda yake cewa.

“Dole na koma makarantar, ko da take nasan Safiya zata kirani daga Nan sai na ji a wani asibiti take” Ya tada motarsa Rai a b’ace yana mugun Jin haushin kansa.

*ASIBITI*

“Aunty Badiyya, Baba bai dawo haryanzu ba, na tsorata kamo dai Bai same ta bane yake Jin bazai iya Gaya min ba? Ko Kuma wani mumunan Abu ya same shi?” ta na maganar cikin muryar kuka.

Badiyya ‘dan dafe kafad’ar Asiyah tayi Tace “Always think positive Asiyah, zai dawo karki damu insha Allah Yana cikin koshin lafiya.”

“Ina fatan Haka aunty”

Murmushi tayi Tace “Kar ki damu” a zuciyar ta Tace “Ya salam, Asiyah kina cikin jarabawar rayuwa, gashi Ni wata na shida Kenan da Fara aiki Dana biya Mata kud’in aikin,and now Dole sai an fita da ita kasar waje, Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un Asiyah Allah ya saka Miki” muryar Asiyah ne ya dawo da it’s taga zurfin tunanin da ta Shiga Tace “Aunty ta na ji Kinyi shiru?”

Ad

_____

1 2Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button