Comment on YAR LESBIAN CE Page 91 to 100 (The end) by Unknown

Wani irin mummunan faduwa taji gabanta yayi lokacin data daura Hannunta kan kofar. dafe kirjinta tayi tana maimita kalman innalillah. Jitayi gaba daya batada kuzarin dazata iya bude door din gashi takasa dauke hannunta kan kofar bare Taga mai bugawa. Yazeed da gaba daya Ranshi yagama baci jiyayi kamar ya juya ya bar Wajen, Amma Ina bayajin Zai iya tsallake maganar Abba dayace yatawo tare da iyalinsa. Mtswww Wannan wace irin mace na Aura? Ba mamaki kofar ma batasan yanda Ake budewa va, ba mamaki tunda yar kauye ce. Juyawa yayi Afusace yakoma part dinshi. bejimaba yafito dauke da wani key din a hanunshi. kofar ya Nufa duk da faduwar gaban dayakeji befasa Kai key din kan door dinba, murzawa yayi ya tura kofar da karfi! da Sauri feenah dake tsaye bakin kofar tayi baya tana kara kiran Sunan Allah. tsaye yayi yana kallonta duk da baya ta juya mishi yanason yagane wace yarinyace Wannan? Wacece kuwa banda yar kauyen da inno ta hadaka da ita Xuciyarshi tabashi Amsa. dan tsaki yayi Cikin Ranshi Afili karfin Halin danne Zuciyarshi yayi ya juya baya yafara magana. “Ke wace irin bagidajiya ce, tun tuni Nake Knocking Anan kamar kurma,tun jiya kin Rufe kanki Saikace Aljana, karki damu idan Dan nine basonki Nake ba Umarnin iyayena nabi kuma kisama Ranki Zamanki Cikin gidan Nan na dan lokaci ne. Then kishirya yanzu Zamu fita minti5 Nabaki. feenah da tunda yazeed yafara magana ta juyo da mamaki duk da baya ya juya mata Bazata kasa gane Siffar yazeed ba, bare muryarshi da takeji karara. Shafa idonta tayi dan gasgata ba mafarki bane. Ganin Zai fita tayi Saurin Cewa yazeed! Zaro ido yayi Arazane jin muryar dayaji jiya Amafarkinshi, kasa juyowa yayi Sai wani dan Murmushi dayayi meyasa bazan daina tunanin feenah ba yafada Cikin Ranshi. Juyawa yayi Zai fita Still muryar yakaraji Cikin Sanyi ance yazeed! Wannan karon juyowa yayi gaba daya yana fadin Aljana inno ta Aura mun. Kusan tare Suka fiddo ido Suna jaaa da baya, girgiza Kai Suka Shigayi lokaci daya. Aa dan Allah kiyi hakuri Wlh kakatace tasa Aka Auramun ke,A iya Sanina ban taba Sabani da kowa ba yazakizo kicutar dani da Sufar wacce bazata Iya Cutar da kyankyanso ba bare dan Adam???? da Mamaki feenah ke kallonshi lokaci guda taji tsoron nata yafita ganin duk yanda yazeed yafita hayyacinsa, Abinma yaso bata dariya,Saidai Al’ajabin dake Ranta bazai Bari Tayi ba. turo baki tayi ta goge hawayen face dinta lokaci guda ta Wurga mishi harara. dan Allah Ni Mai yakawoka gidana malan?kazo kamar Wani Wanda yayi Shaye Shaye Kana Surutai,ni Rashin Son matarka da bakayi be Shafeni ba pls kafita bana bukatar Ziyarar ka. ????”She is”! Yazeed yafada Aranshi. Saisaita kanshi yayi feenah har yanzu baki bar tsiwa ba, kinzo gidana Kuma kina fadin Nafita, pls Ce balaraba tafito Zamu fita. Ashe Anan kika kwana,Anfasa kaiki yolan ne kokuma har yanzu mijin naki besamu lokacin dawowa bane? dafe kai Feenat tayi takoma bakin bed ta Zauna. Wai me wannan yake fada ne? Yana nufin gadin matarshi Nazoyi Nan Shine Sukacemun Zama Zanyi kafin Akaini yola Yau? toh Ina balaraba din? Maybe ko wani dakin ta kwana daban. Tabe baki tayi Sorry Na dauka gidan mijina ne,bansan Nan bane Amma Ni bankwana tare da matarka ba. gira yazeed yadaga Sama Ina tunanin tana wanchan dakin. juyawa yayi yafita Zuwa dakin dake kusa Dana feenah. Ganin dakin bude yasa yashiga Kai tsaye. Ware hannu yayi lokacin daya gama dube dube baiga Kowa ba. fita yayi yakoma dakin da feenah take, Sister bata Nan fa kishirya mutafi tare. No feenah ta fada da Sauri ni bazan fita batare da mijina yace ba, katafi ina tunanin ko matarka tana gidan Mamy fa. Shiru yazeed yadanyi na lokaci kafin yadaga baki yayi magana wayarshi tafara kara….dagawa Yayi da Sauri ganin Abba ne ke kira. Hands-free yasa phone din yafara magana. Hello Abba! Haba Yazeed kai kadai fa muke jira. Abba kayi hakuri natsaya jiran balaraba ne kuma banganta ba, Sai Feenah Dana gani A gidana! Shiru Abba yadanyi badamuwa kataho tare da feenah din. Amma Abba tace bazata fita mijinta be Saniba. Bani feenah din idan kuna tare. Mikama feenah yayi ta karba Hello Abba ina huni? Lfy qalau yar Albarka ya bakunta. Alhmdllh. Kibiyo yazeed inason ganinku Yanzu, mijin Naki yana nan. toh Abba insha Allah. Mikama yazeed wayar tayi batajira mai zaice ba tashige toilet. fita yayi adakin yanufa kitchen breakfast yashiga ya hadama feenah mai sauki lokacin dayagama yayi daidai dafitowarta Subhanallah ya furta Cikin Ranshi yayin daya dauke idonshi Akanta. Itama kallo daya tamai ta kauda kai. “Muje ko” Ga breakfast. No bana bukata Ngd. kallonta yazeed yayi tunda yake ba’a taba yimai irin wannan Abun ba, waima meyasa Nake damuwa da ita haka ne? tashi yayi yafita tabishi Abaya.
Karfe10 da Rabi daidai Suka karasa kofar gidan Mamy. gaba daya Kasa fitowa Sukai daga motar domin ji Suke kamar andaura musu dutse Akansu, bangare guda kowanne Zuciyarshi bugawa take ba kadan ba. Tunani kowannesu keyi Cikin Ranshi. Kusan mintuna20 Suka dauka Ahaka…wayar yazeed datayi kara itace ta dawo dasu daga Zancen Zucinsu. duba wayar yayi yabude motar yana kallon feenah Muje ko. Bata tanka mishi ba tafita ya Rufe motar Suka Shiga. Jin parlon dasukai da hayaniya ya tabbatar musu dacewa parlon Cike yake da Mutane. Sallama Sukai gaba daya Hankalin yan parlon yadawo kansu Masha Allah kawai Suke fadi ganin yanda feenah da yazeed Suka jero kai Ka Rantse Kace masoya ne. da gudu Mubeen da Mubeena Sukai kan feenah Suna Oyoyo. Rungumesu itama tayi yayin data jasu Suka karasa parlon. kallon Kausar da leemah tayi Murmushi taga sunayi. Ikon Allah feenah ta furta Aranta kodan Oyoyo din Nan babu,idan Kausar Ciki yahata tashi Leemah fa? Tabe baki Tayi takoma gefe ta Zauna yayin data Shiga gaishe da mutanen parlon. Lallai taron babba ne kenan wannan yawan mutane haka yazeed ya furta Aranshi. Kusan duk familyn bangaren mutanin biyu ne Xaune. inno na hango kusa da innah nafisa ta yola, kusa dasu wata tsohowace, nagane ta Mahaifiyar mumyn feenah ce. Bangare guda Mamy,mumy,Umma da Hajiyar Kausar Su nagani Zaune. Dan nesa dasu Naga dad,Abba da Alhji Suleiman mijin Umma. ( karku manta Alhji Sulaiman tare Suka taso su3 da Abban yazeed da dad din feenah, kuma dad da Abba duk A karkashin Baban Alhaji Sulaiman Suke aiki, wanda mahaifine wajen mumyn feenah. Alhjii Sulaiman Wa ne Awajen mum) Nazir, yusuf Suma duk Suna Wajen. Bayan gaishe gaishe Kakan feenah yafara magana Alhji Ibrahim kenan. Naji dadin kasancewata Acikinku gaba daya. Nayi murna da Allah ya Nuna mun Auren yaranku. Inno kece silar hada Wannan Auren Allah yasaka miki da Alkairi Duniya da lahira. Sanan yusufa kaima inamaka addu’a Allah ya biyaka tunda kaine ka fara daura foundation, Allah yabaka Zaman lfy da iyalinka yabaka Zuri”a dayyiba. Amin Yusuf yafada wanda kanshi ya daure Cikin Ranshi yake tunanin, Ni yaushe na hada Auren yazeed da balaraba, feenah da waye ma Oho? Maganar da kaka yacigaba ta katseshi. Nazeer da Leemah Allah yasama Aurenku Albarka yakareku da Sharrin Shedan,Allah yabaku Zuri’a dayyiba. Amin duk yan wajen Suka fada. Kallon yazeed kaka yayi yazeed Ina jajanta maka Kan Abinda yafaru dakai game da yarinyar nan Mufeeda Allah yakara tsare manaku Aduk Inda kuke, Sannan kacigaba da addu’. insha Allah Kaka ngd Allah yakara girma. Amin yaron kirki. Juyawa kaka yayi wajen feenah. Jikata idan Abu yasameki wanda farin ciki ne wajen iyayenki kekuma Awajenki kila yazama Abin bakin Ciki Sabida yarinta, Wani mataki Zaki dauka Akai?? Shiru Feenah tadanyi daga bisani tafara magana. Kaka farin Cikin iyayena shine nawa, bana tunanin Zasu iya yimun Abinda zai cutar dani dan haka idan Nasamu kaina a irin haka Zan fadi “”Alhmdllh Ala kullin hal”” domin komai Nasan Allah ke yinshi. Masha Allah kawai yan wajen Suka furta. Kaka Murmushi yayi Nazeer in kaine yazakayi? ?kaka Nima yanda feenah ta fada haka Xanyi. Kausar in kece yazakiyi? Kaka nima ina bayan feenah. Yazeed in kaine fa?? Hakan Zanyi kaka. Toh Alhmdllh Alhji Umar yabama yaron Alhji Ahmad Auren yarshi domin farin cikine Awajensu, Sanan Auren ya kullune Sanadiyar yusuf da inno. Allah yamuku Albarka yasama Aurenku Albarka yakarama Rayuwarku Albarka yakuma baku Zuri’a masu Albarka yazeed da feenah. gaba daya yan wajen idan kacire inno dad Abba da innah nafisa Sauran duk kansu daurewa yayi Amma daka gansu Zaka gane farin Cikin dake dauke a face dinsu. tashi yazeed yayi yakoma kusa da yusuf da gaske feenah matata ce? Murmushi yusuf yayi daga bakin da baya karya kaji maganar ai. tsalle yayi yakoma wajen inno kakata da gaske feenah kikasa aka aura mun? Juyar dakai inno tayi kamar batasan me yake fada ba. Tashi yayi yakoma kusa da mamy. Mamy feenah matata ce? Shafa kanshi Mamy tayi Nima yanzu naji Son Allah yayi Albarka karike matarka da Amana. Kwantar da kanshi yayi kan Cinyar Mamy yana Saukar da Ajiyar Zuciya wanda besan fassararta ba. Nasiha kowa yashiga musu idan wannan yayi wannan yayi da haka har Suka Rufe taron da addu’a. Ganin tun lokacin da Akai mgn Feenah batai motse ba yasa Leemah magana. besty bakice komai ba.kamar jira dama take atanka mata take tashiga ihu. Mum Ni Wlh banason Auren Nan, banason yazeed Shima dazun yafadamun baya Sona,dan Allah dad kusa yasakeni, ni Wlh banasonshi bana kaunarshi bazan iya Zama da yazeed Amatsayin mijin Aureba kutaimakeni. Afusace mum ta karasa wajen feenah mari ta dauramata a face dinta takara daga hannu….mamy ta riketa haba hafsat feenah ai tawuce duka, kibi Ahankali. kamo hannun Mamy Feenah tayi Mamy dan girman Allah kisa yazeed ya sakeni. Tsawa dad yabuga mata feenah Xan Saba miki idan natashi. Kabi Ahankali Alhji faruk Abba yafada. tashi feenah tayi Afusace zata fita Saidai ko kofa bata kaiba jire ya kwasheta tangal tangal tayi kadan yarage takai kasa yazeed daya karaso ya tareta. ganin idonta ya kafe yasashi kwala ihu. Inno mamy na Rasa Feenah Wayyo Allah. Gaba daya Sukayo kansu A rikice. Maza Nazeer muje Asiviti. Ku kaita Sama Yusuf ya dubata mamy ta fada. Kasa daukarta yazeed yayi saifaman kuka yake kamar yaro.ganin haka yasa Nazeer daukanta yayi Sama da ita,binshi yazeed yayi yana hurama feenah iska a face dinta. dakin Mamy Nazir yakaita duk sukabi bayanshi.
Akofa inno ta dakatar dasu kumu koma kasa ba yanda Zasu dubata da taron mutane haka. Sauka duk Sukayi dakin yarage yusuf da yazeed Kawai. dubata yusuf keyi yazeed banda Surutai babu Abinda yake. Dan Allah feenah karkimun haka kitashi ko bakyasona muyi Rayuwar Aure dan Allah kada kibari Na rasaki Akaro na2. dan Allah malan kafita kabarni nayi aikina tunda bakada Amfani,tace batasonka ko dole ne? Haba yusuf Kasan inason feenah kabarni Anan banajin Zan iya Rabuwa da ita. Murmushi yusuf yayi Ayanzu koh? Kamance sanda Nake binka Alalama kake Zuba tsiyarka? Kamance yanda kake wulakanci gaban yarinyar Nan? Tayaya kake tunanin feenah Zata soka bayan Ada ita ka tsana fiye da kowa kuma kabari tasan haka? Yusuf mubar wannan Xancen ya huce, tayaya feenah Xata fahimceni? daga kafada yusuf yayi I don’t know. Pls yusuf. ka kyaleni Yazeed kazo kanatamun kuka haba, hope bakamance Mai kafadamun a madina ba lokacin da Kausar tayi Rashin Lfy? Haba yusuf mubar duk wannan yanzu. Ok mubarshi tashi mutafi Xata farka lfy Insha Allah. Yunwa ce Kawai da yawan tunani. tausayinta yazeed yaji matuka tunowa da tunjiya bataci Abinci ba.kai Gaskiya ban kyauta ba Ashe Kaina na cuta. Katashi muje angon balaraba. Katafi ni ina Nan. fita yusuf yayi yana murmushi. Komawa yayi kusa da ita yana kara kallonta Wani irin farin ciki yaji wai Feenah tazama mallakina, da Wani Abu Zan Sakama inno da yusuf Allah yabiyasu kawai. bayan Wasu Awanni Mamy tashigo dakin daidai Sanda yazeed Ke kokarin kai bakinshi kan face din feenah. Sallama tayi da Sauri yazeed yadago kauda kai mamy tayi kamar bata ganshi ba. Bata tashiba har yanzu? Eh Mamy. Kayi Sallah kuwa? Nayi Anan mamy. Juyawa mamy tayi zata fita taji sha2shekar kukan feenah. Da Sauri ta juyo Tayo wajensu
????????????????????????????????
YAR LESBIAN CE
????????????????????????????????
By
Nadeeya mohd Ahmad
(Nadseer)
dedicated to
Xaynab Ummu mahbub
Page…77
Sannu my daughter Mamy ta fada yayin data rike hannayen feenah. Hawaye ne kawai ke Sauka Kan fuskan feenah, ido Rufe tafara magana. Mamy banason yazeed dan Allah kusa yasakeni pls. Runtse ido yazeed dake wajen yayi har Cikin Ranshi bayajin dadin yanda feenah ke furta kalmar kiyayya Akanshi. Murmushi Kawai Mamy keyi kara damke Hannun feenah tayi Kiyi hakuri feenah Ki kwantar da Hankalinki, Babu wanda Zai miki Abinda bakyaso, Abinda nakeso dake yanzu kicire komai kisake jikinki Ni Zansan Abinyi kinji koh. Kada Kai feenah tayi Alaman ta gamsu. Yawwa yar Albarka yanzu me kike So nakawo miki kici. Mamy Ni banason komai. feenah bakici komai ba tun jiya fa yazeed dake gefe ya fada. Kallonshi tayi ta watsa mishi harara ta kauda Kai. dole Zakici inhar kinason Nasa baki Amaganar Nan Mamy ta fada yayin data tashi tabar dakin. tana fita yazeed yadawo kusa da feenah ya Zauna. feenah me Namiki haka dayasa kika tsanene?? Kauda kai feenah tayi gefe Alamar batason maganar. ba Abind yakamata kiyi b kenan feenah kamata yayi muhada Kai wajen yima iyayenmu biyayya, Sanin kankine nima idan bayanzu ba Bansan ke na aura Amatsayin mata ba, ni inada wacce Nake So,Abu daya Nakeso dake kidaure muhadu musaka iyayenmu farin Ciki,lokaci kadan ne Saina Sawwake miki ki Aura wanda kike So. Hawayen da feenah take makalewa Sune Suka Shiga bin face dinta. Kallonshi tayi Cikin kuka tafara Magana, yazeed tunda kaima Kasan baka Sona kaje yanzu kasanar masu Zaka Sakeni dan Allah, Ni Wlh bazan iya Zama dakai Amatsayin miji ba. Runtse ido yazeed yayi Sabida kalaman feenah. bangare guda yanda take kukan ba karamin jinshi yake Arai ba, Karfin Hali kawai yake Ayanzu yandama yasamu tafara kulashi yadanji dadi. feenah idan Nayi haka kamar Na nuna musu basu isa dani b Kenan. Kawai tunda nafada miki Zan Rabu dake Ahankali ki kwantar da Hankalinki. Yaushe Zaka Rabu dani??? Bansa time ba Amma Zaman kankanin lokaci Zakiyi agidana. Wani irin Murmushi feenah tayi wanda yasa yazeed tabbatar da feenah batasonshi ko kadan. Cije baki yayi yafita daga dakin. Karo yaci da yusuf dake kofar dakin. Kama hannushi yusuf yayi Sukabar Wajen. Haba Yazeed wannan wace irin Rayuwa ka daukarma kanka? Ka tabbata Zaka iya Cika Alkawarin daka daukarmata na rabuwa da ita? Menene Aibu Dan kazauna Ka fahimtar da ita kuskuren dakayi Abaya,kakuma fahimtar da ita irin Son dakake Mata Ayanzu! Kasani koma Hakan yasa ta fahimceka tasoka kugina Rayuwarku Kamar kowasu ma’aurata? Me yasa kayi haka yazeed? Why? Why? Cikin karfin Hali yazeed yafara magana, domin Shikadai yasan yanda yakejii idonshi gaba daya yakoma Kamar gauta. Yusuf Na tabbatar Ayanda feenah ke nuna kiyayyarta gareni bazata taba Sauraron Abinda Zan fada mata ba, kawai Zansaka iyayena farin Ciki Ayanzu, kuma Zan Saki feenah kamar yanda ta bukata daga baya, Na Amince koda Son feenah Zai kasheni Saina faranta Ranta da Abinda tafi So. Haka kaga yadace dakai koh yazeed? Inabaka Shawara karka daukarma kanka Alkawarin Abinda bazaka iya Sauke Shi ba! dafa Kafadar yusuf yazeed yayi I promise to you yusuf Zan Aikata Abinda Feenah keso nan da dan lokaci kadan. Hmmm yusuf yafada kenan Wani Auren Zakayi? Nop Nahakura da kowace mace Zanyi Rayuwata ni kadai. Tabe baki yusuf Yayi tunda Haka Mazon Allah S. A.W. Ya koyar damu Saika bada himma. daga haka yabar wajen. dafe kai yazeed yayi lokacin daya Zube Akasa Gaba daya Zuciyarshi wani irin tafasa takeyi bayajin dadin komai. Mamy datazo Wucewa ta lura da yanda yake Zaune kan Step gaba daya taji tausayin dan nata ya Rufeta. dawowa tayi Zuwa wajenshi ta dafashi. yazeed bekamata kana damuwa Akan irin Wannan matsalar ba, tunda dai Kasan bakason feenah mai Zai hana kabata takardarta Ayanzu domin kuhutama Zuciyoyinku, tunda bamu isa daku ba. da Sauri yazeed ya juyo yana kallon mamy kukan dakecinshi ne yashiga Rairawa. kanshi Mamy ta daura kan cinyarta tana maikara tausayawa dan nata. Shafa bayanshi kawai take dan batada bakin bashi hakuri Azatonta duk dan Shima bayason Auren ne yake haka. Saida yayi mai isarsa kafin yadago mamy Abaya Nayi wata irin Rayuwa Wacce bansan kanta ba, . mutane da yawa Sun tsanene Sabida Rayuwar danayi, gashi yanzu Agaban idona ana iya fadamun irin kiyayyar da Akemun. Mamy feenah Itace macen Dana faraso aduniya wacce nakejin idan narasata Zaku iya Rasani. Mamy Menene Aibuna da har feenah ke iya furtamun bata kaunata. dan Allah Mamy kifadamun halina Mara Kyau Wlh Zan gyara. Lumshe ido Mamy tayi tacigaba da Shafa bayanshi. Ya’isa my Son idan na fahimceka Kanason feenah fiye da kowace mace Ayanzu? Mamy Wlh inason feenah da ita kullun nake mafarkin mun Tara yara. Shafa kanshi Mamy tayi ka kwantar da Hankalinka Nan gaba feenah Zatayi Alfahari dakai, Ayanzu kabi komai Ahankali kacigaba da addu”a Wata jarabawace Allah ke jaraftarka da ita. Mamy yanzu menene yakamata Nayi game da feenah? addu’a Itace kan gaba kakuma Rinka Sake Mata kana kyautata mata hade damata Nasiha. Ngd mamy Allah yakara miki kwanciyar Hankali. Amin yarona Allah yabaka farin Cikin ka. tashi Mamy tayi ta nufa dakin da feenah take fira taga Sunayi da Leemah da Kausar Suna dariya kamar ba’itace tagama bori dazu ba. Murmushi kawai mamy tayi ta juya tabar wajen Cikin Ranta take fadin feenah bazatayi wuyar Sakkowaba insha Allah. Misalin karfe8 yusuf yaja Kausar Suka tafi. dakin ya rage Leemah da feenah inda Suka Cigaba da firarsu.duk dacewa yawancin firan vewuce Kan yanda Akayi Shagalin bikinsu ba. Leemah ce takara dacewa Wai Ashe duk Abin Nan brother na kika Aura bamu Saniba. bata Rai feenah tayi ai Wlh danasan Shine tuni da ban Amince andaura Mun Aure dashi ba. Murmushi Leemah tayi tunda kuwa Anriga andaura Sai hakuri ba. Hmmm Zanyi nadan lokaci ba. Magana Leemah Zatayi Mamy data Shigo ta katseta. …Leemah Nazir yace Kije kutafi fa. bata Rai Leemah tayi Mamy Wlh bangaji da Zaman gidan ba. Ai Saiki Zauna lokacin dakika gaji Saiki fito Mamy tafada yayin data bar dakin. yamutsa fuska Leemah tayi ta tashi besty yaushe ke Zaku tafi?? Mtswww Ni ina nan. dariya leemah tayi tabi Hanyar waje kice gidan Mamy Zakuci naku Amarcin kenan. dariya feenah itama tayi wanda yasa Leemah kallonta da mamaki. Lfy kuwa???? dariya feenah takarayi Wannan tafiyan taki Ai dole tasa mutane dariya. bata fuska Leemah tayi tacigaba da tafiyanta har tabar dakin. da karfi feenah ta furta Zankiraki naji dalilin Wannan tafiya haka.
My daughter Wannan dariya duk namiye haka?? Mamy Wlh tafiyan da Leemah keyi yaban dariya. Murmushi kawai Mamy tayi tabar maganar. Kitashi kutafi gida dare nayi. Mamy gidanwa kuma?? Gidan yazeed! Mamy Ni Bazan bishiba Anan Zan Zauna. Kinsan dai Namiki Alkawari koh? Kibi mijinki ni zansan Abinyi Nan gaba. Mamy Idan nabishi wulakanci Zairinka mun Wlh. Bazai miki ba feenah Namishi fada, Sannan Zai Bari kicigaba da tafiya Aikinki lokacin da Leemah Zatacigaba da Xuwa. Turo baki feenah tayi Mamy kifada mishi baruwanshi dani kada yarinka kulani. Zanfada mishi,Zaidai dan rinka miki mgn kadan kinsan gaba ba Kyau. kinji koh? Eh Mamy. Yawwa my feenah yanzu kishirya kutafi, kafin Nan Ki kira mum Awaya kibata hakuri kinga tayi fishi da yawa.toh mamy ita meyasa ta Amince na aura yazeed? Aafa feenah Hafsat batasaniba. Shikenan feenah tafada lokacin data tashi. Nasiha mamy tadan kara mata Asiyasance tare da hadamata Wasu magani kamar yanda tamawa Leemah. Amsa kawai feenah tayi tamawa mamy Sallama. A parlo tasamu yazeed Zaune. turo baki tayi oya. tashi yayi yamawa inno Sallama Suka fita
????????????????????????????????
YAR LESBIAN CE
????????????????????????????????
By
Nadeeya mohd Ahmad
(Nadseer)
dedicated to
Xaynab Ummu mahbub