BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 34

Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

34

………..A wajen ƴan biki kuwa dawowar ƴan ɗaurin aure ya sake ruɗa gidajen biyu, bakajin komai sai guɗa da kirarin maroƙa tako’ina. Bakin su Daddy ya kasa rufuwa saboda tsananin farin cikin da suke ciki na sake samun damar aurar da yaransu a karo na uku. Hakama Mommy tana a cikin tsananin farin cikin cikar burinta na sake aurar da Maheer ɗinta a ganinta ta raba ƴaƴanta biyu da ƙaya. Shiko ango Maheer ko walwala baka gani a fuskarsa, dauriya kawai yake na amsa gaisuwar jama’a da taya murna a garesa saboda baya son su Daddy suga kamar bai ɗauka shawararsu ba……
        A ɓangaren Mamie da Abie ma duk da wannan rana ta tilon ƴarsu tazo musu a yanayin da basu gama shiryata yanda suke so ba hakan bai hanasu kasancewa cikin ɗunbin farin ciki ba, dan albarkar auren suke nema mata ba wai tsarabe-tsaraben cikinsa ba. Fatansu ALLAH ya bata zaman kafiya da zuri’a masu albarka ita da mijinta. Suna zaune a ɗakin Abie da take barci suna kallonta fuskikinsu murmushi ya kasa sauka, ga ɗunbin tausayinta da ƙaunarta na ratsasu. Abie ya kauda kai gefe yana murmushi ganin Mamie na sharar hawaye, cikin son danne nasa dake ƙoƙarin sakkowa ya miƙe yana kai waya kunnensa tamkar zaiyi kira ya gudu a ɗakin……
        Ƙananun maganar da suka fara fitowa a bakunan mutane saboda jin yanda ɗaurin aure ya kasance suka fara yawaita a gidan har wasu a dangin Mommy ya fara isa kunnuwansu. Da yawansu mamaki suke nunawa jin yanda al’amari ya kasance dan su dai basu san da wannan aure ba. A cikin ƙanen Mommy da abin ta jisa tamkar saukar aradu ta kasa haƙurin shanyewa kamar kowa ta shiga neman Mommy. Da ƙyar ta samota a sashen gwaggo wajen tsoffi na ƴan uwa da ƙawayen ta da suka taru acan.
        “Ke ko lafiyarki kuwa Samira kika shigo mana kamar wadda take a rikice”. Gwaggo ta faɗa ganin yanda aunty Samiran ta shigo har tana cin tuntuɓe. “Gwaggo dole kike ganina a haka, wani mummunan labari nake jiyowa yana tashi a gidan nan dana gaza gaskatawa, Aunty dama akwai auren wata bayan Fadwa akan Shareff?”.
      “Samira ban son takale-takalen masifa ina cikin farin cikina wane aure kuma?”.
  “Humm aunty kenan, aure nawane aka ɗaura a gidan nan yau, kidai bincika dan yanzu naji anata ƙus-ƙus wlhy wai dama matarsa ce sai dai yau aka sanar.” A rikice Mommy ta kalli gwaggo, itama gwaggon kallonta takeyi baki buɗe. Cikin ƙarfin hali gwaggo tace, “Nifa sam bamma gane wannan soki burutsun nakiba wlhy Samira”.
       “Nima da nake faɗa mukun na kasa ganewar, inaga bincikawar dai kamar ya kamata kuyi”.
Suɓucewa plates dake a hanun Mommy sukayi, ƙirjinta na matuƙar bugawa da sauri-sauri. Fitt ta fito ɗakin Gwaggo na ƙwala mata kira amma bata juyo ba. A yanda ta fito ɗin yaja hankalin mutane da yawa suka shiga binta da kallo. Kai tsaye sashen Daddy ta nufa, sai dai koda ta shigo bata samu kowa ba sai kwanikan abinci dake barbaje alamar anci. Har bedroom ta leƙa, nan ma babu kowa a ciki. Da sauri ta shiga laluben wayarta dake cikin handbag ɗin hanunta da take tara kuɗin yinin bikinta dan yau takeyi, hannunta ma rawa yake, tadai samu da ƙyar ta lalubo number Daddy tai dailing. Sai da ta kusan tsinkewa ya ɗauka, babu ko sallama tace, “Daddyn Shareff wani shirme nakeji yanzun, nazo sashenka kuma baka nan?”.
Kai tsaye ya gano abinda taji ɗin, dan haka a dake yace “Ina waje tare da mutane, idan na shigo sai muyi magana…” ƙitt ya yanke wayarsa tana ƙoƙarin dakatar da shi. Tsananin tsoro ne da firgici ya ƙara saukar mata. Tabi wayar da kallo kamar zata gano Daddy ɗin a ciki. Kai ina bazata iya haƙuri ba sam, akalar kiran nata ta maida ga wani yayansu data tabbatar Daddy baya ɓoye masa komai dan abokinsa ne shaƙiƙi tun ƙuruciya. Bugu biyu ya ɗauka, tai ƙoƙarin shanye tashin hankalinta dan tasan saita lalama Yaya Awwalu zai faɗa mata abinda take bukatar. Bayan ta gaishesa yake cemata tayi haƙuri bai shigo ya mata an ɗaura aure ba wani uzirine ya taso masa amma zuwa anjima zai dawo gidan.
“A’a babu komai Yaya ai kai mai yine, yanzuma na kiraka ne saboda inji ko kana tare da abokin naka dan zuwa anjima ina son ka ɗan ƙarama Maheer faɗa kasan yaran nan da taurin kai, Shareff ya fisa haƙuri da biyayya tunda kaga shi duk aurarrakin nan zaɓinmu ne amma ko yau bai tada hankalinsa ba akai”.
Yaya Awwal yay ƴar garan murya irin ta manya da ɗan murmushi, “A’a karki damu shima zai kwantar da hankalinsa ai, kuma hankalinsa aiba ɗaya dashi Mustapha ba. Amma zan shigo ɗin insha ALLAH, yaya jikin shi Mustapha ɗin ma? Dan ina tambayar bangansa ba akace yana asibiti babu lafiya”.
“Eh wlhy zazzaɓine ya kadashi amma da sauƙi, inagama yau za’a sallamosa tunda ba’a kai amarya babu ango ba”.
A karon farko yay ƴar dariya mai sauti da faɗin, “Wannan gaskiya ne, ALLAH dai ya basu zaman lafiya da haƙuri da juna tunda duk gidane, sai dai dan ALLAH kiyita ƙara nusar dashi da tausarsa tunda su duka ƴan uwansa ne kar zuminci ya samu matsala azo ana hai hai babu daɗi. Gaba ɗayansu ɗaya suke a wajensa babu wadda tafi wata…….”
Tunda ya fara jawabin nasa na ƙarshe jikin Mommy ya hau rawa, bazata iya jin ƙarshen zancem ba dan haka ta yanke wayar. Hajijiya taji tana neman ɗibarta, a dai-dai nan Gwaggo da taga shiru bata dawoba ta biyota ta shigo. Salati ta saka da riƙeta da sauri. “Ke ko kina lafiya zaki kashe kanki Nafisa?”.
Kuka Mommy ta fashe da shi, “Gwaggo sun kasheni, wlhy sunyi a banza, har abada jinina dana Usman bazasu zauna a inuwa gudaba. Gwaggo na rantse yau duk masifar da za’ai a gidan nan sai dai ayi sai Shareff ya saketa, ni Muhammad zai cima amana, ni Muhammad zai yaudara ya zalunta…..”
“K wai miya farune kin sani a duhu?!”.
“Gwaggo aure fa suka ɗaurama Shareff da ɗiyar maƙiyana, wai ƴar gidan Usman. Kuma tabbas batun yau ba ma.”
“Ƴar gidan Usman?!!”.
Gwaggo ta faɗa a razane, Mommy bata amsa mataba ta mike fuu ta fito hanunta dafe da kanta dake juya mata. Gwaggo na ƙoƙarin tsaidata yanzu ma bata saurareta ba. kai tsaye hanyar gate tayi, Samira ta biyita da sauri. “Yaya! Yaya miya faru ne? Da gaske ne ko?”.
Bata iya bama Samira amsaba ta fisgi gyalenta tai waje, kasancewar anata ɗaukar ƴan biki da kawosu ta samu a napep. Daddy daya hangota da yake suna zaune a ƙofar gidan cikin runfa ya miƙe, sai dai kafin yazo har napep ɗin tabar wajen…….

      

★Tun ɗazun ya farka saboda zuwan gayyar abokansa da sukaje ɗaurin aure. Shidai kallon mamaki yake musu, dan baiyi tsamanin ganinsu haka da yawa ba a waje ɗaurin auren ƙanin nasa. Suko sai faman washe baki suke da tsokanarsa a sigar daya kasa ganewa dan kowa ya kasa fitowa fili yace wani abu saboda ganin Fadwa tare da shi. Ga kuma dama Dr Jamal ya rokesu kar suce komai anan Please. Basu wani jima sosai ba suka fita acewarsu zasuje cin abinci zuwa anjima zasu dawo duk da Doctor yace maybe ma zuwa dare su sallamesa. Bayan fitarsu Fadwa ta dawo kusa da shi. Ganin yanda tai kicin-kicin da fuska sai yaji wani iri, hannu ya miƙa mata alamar tazo, tai kamar zata noƙe sai kuma ta nufesa ganin yay mata alamar roƙo. Jikinsa ya jawota ya rungume, ya sakar mata sumba a gefen wuyanta tare da ɗaura kansa a kafaɗarta yay shiru. A hankali ta lumshe idanunta da haɗiye kukan dake neman ƙwace mata.
“Shii!!”.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button