Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 67-68

Episode 67-68

………..WASHE GARI

          Washe gari babu kunya Gimbiya Su’adah tazo har sashen su Anne ta tuntuɓesu batun auren Aynah da Ramadhan. Dan Pa yaƙi bata haɗin kai kwata-kwata.

Ramadhan ko taki cemasa komai duk da tasan yana cikin gidan. Hasalima har zuwa yay ya gaisheta. Yanda bata ɗaga masa maganar abinda ya faru ba a jiya shima

baice komai ba. Yau ma bayan ya dawo sallar asuba yaje ya gaishetan. Nanma bataceba shima kumai bai ceba.
      Koda Bappi ya gama saurarenta cewa yay taje zataji komi da suka yanke shi da su mai-martaba. Ranta ya ɓaci, amma ta danne ta tafi. Duk yanda sukai da

Bappin ta kira Adda Asmah ta sanar mata. Itako daga can gurgun tunaninta bata yay aikin boka ya tabbata kenan. dan dama yace zai rufe bakin kowa ai. Shi

kansa Ramadhan bai isa yin ko tari ba akan batun.

       Hhh ALLAH sarki Addah Asmah. Batasan a yanzu matar Ramadhan da kakaninsa tsaye suke kansa ba. Dan a yau yini Raudha tai aikin karanta addu’oin

warware sihiri dana kariyar ALLAH ita da Ramadhan suna tofawa a ruwa kamar yanda musulinci ya koyar damu. Suka kuma ajiye matsayin ruwan shansu. Yini guda

suna a sashensu. Hatta abinci nan ake kawo musu. Yayinda Anne ta zaunar da shi ta sanar masa dokar Doctor akan Raudha na bedrest. Ya tabbatar mata babu

damuwa zaiyi ƙoƙarinsa na kare hakan. Taji daɗi sosai tai masa nasiha ita da Bappi tare da addu’ar ALLAH ya kiyaye gaba.

    Washe gari gida ya cika da baƙi taf tako ina. Bakajin komai sai hayaniya. Sai dai duk wannan hayaniya da gidan ya dauka babu mai ganin shugaban ƙasa da

first lady. Dan suna can sashensu suna baje kolin shafukan soyayya kamar su kaɗaine a duniyar. Basu da aiki sai zaman garden ɗinsa dake matuƙar ɗaukar

hankalin Raudha takeji kamar a wata sabuwar duniyar take. Abu mafi ɗaukar hankalinta tsuntsaye da ake kiwo a wajen da ruwan da aka kawata mai bulɓulowa

cikin dutse kai kace ba tsarawa akai ba. Sau ɗaya ya barta ta shiga sukai wanka a pool ɗin wai bayaso Unborn ɗinsa ya ɗauka mura tun yanzun. Ita dai

dariyama yake bata. Dan baida aiki saita idan ta haihu babynsa kaza kaza. Kokuma ya kwanta a cinyarta yayta hira da cikin da ko a jikinta bai nuna

akwaishiba dan cikin a shafe yake kamar babu hanji balle ɗa.
        A ɓangaren su Adda Asmah hankalinsu a tashe yake babu ango babu dalilinsa. Gashi har an fara event yau a cikin ukun kawai da mai-martaba ya basu

izininyi tun a waccan ranar. Koda Fulani ta iso tasa a kira mata Ramadhan anƙi ganinsa. Gashi Bappi ya sashi kashe wayoyinsa duka sai mai muhimmanci kawai.

Yo banda abin Fulani ma ganin shugaban ƙasa guda wasane kamar wani ganin Bilyn Abdull haka????.
     Aiko ta shaƙa. Tazo har sashen Anne amma ƙofar sashensa a rufe. Hakan yasata tunanin koma dai raina musu hankali ake baya gidan aka ajiye waɗanan

zaratan securitys ɗin zagaye da anguwa kamar masu gadin wuta. to komadai miye Shugaban kasa Ramadhan ya zama gwal ma ya fisa arhar gani a garesu.
     Dan ko kunshi da yace bilkisu ta kawo mai yiwa matarsa a sashen akai mata cikin garden, yayinda shi yake acan falon hutawarsa zaune shi da Ibrahim da

A.J da sukazo biki suna shan hirarsu, dan Gimbiya Su’adah ta gama turama abokansa invitation kaf ta waya akan zaiyi amarya. Koda suka zo kuma baice da kowa

komai ba akan hakan.

     Koda aka kammala ƙunshin ya gani yayta santi. Kaɗan-kaɗan ya kamo ya sumbata. Harda labarta mata yanda ya dinga satar kallon kafafunta da hannayenta

lokacin da akai mata na bikinsu. Aiko mi zatai inba dariya ba har saida ya ƙulu. Tako shiga masa gwalo da kiransa gulmamme.
     Gyaran kai kam shi ya wanke mata da kansa ya gyara mata shi tsaf har taita mamaki. Yako tabbatar mata tsabar son da yakema gashine kawai ya sashi koya

a wajen Anne. Harda cewa wataran zai mata kitso da sai tasha mamaki.
     

RANA BATA ƘARYA……

       Lallai wannan zance haka yake. Dan kuwa a yau juma’a bayan sakkowa masallaci aka ɗaura aurarrakin yaran Taura Family har su biyar. Sai dai wanda suka

kasa kunne suji da Ramadhan a ciki sukaji tsit. Sai da aka kammala a karshe aka ɗaura na Ayna’u Musaddiq da angonta Aminullahi Ashiru. Ɗa ga tsohon gwamnan

jihar TANDAZA, ya jima yana sonta tana masa ikkanci, dan har kuɗi sun taɓa kawowa ta bijire. Da yake uban baida fus a gidan haka ya hakura duk da kuwa

bokine garesa Alhaji Laminu Tandaza. Sai dai kuma masu iya magana sunce matar mutum kabarinsa. Gashi kuwa UBANGIJI ya tabbatar da hakan.

      Gagarumar ƙurace ta tashi a gidan Adda Asmah jin sunan ango a bakin ƴan ɗaurin aure da ba haka suka saniba tun farko. A cikin kanƙanin lokaci ta

hargitsa kowa. Zata taho Taura House ayi wacce za’ai ita da gimbiya Su’adah da take tunanin ta munafinceta Abban Aynah ya tabbatar mata ko gate ta tsallaka

a bakin aurenta. Wannan tashin hankali ya saka Fulani hana Adda Asmah fita. Dan kowa yanda yaga Alhaji Musaddiq yau babu makawa zai tabbatar da abinda ya

faɗa ɗin.
      Amarya Aynah kuwa suma tayi a take sai da aka nemi likitan ceto ranta.

      A Taura house kam babu wanda yasan mi ake ciki. Dan kuwa koda anguna suka shigo gaisuwa babu wanda yaji wani sabon abu da babu shugaban ƙasa Ramadhan

da ganinsa dama bai zama lallai a idon kowanba.  Dan yanda ya fita tare da Bappi da mai-martaba wajen daurin aure haka suka dawo a mota ɗaya. Yana shigowa

kuma ta ƙofar baya yabi zuwa sashensa dan ya tabbatarma Raudha kartaje ko’ina ana ɗaura aure gida zai dawo.
      Duk da dai taji gargaɗinsa. Anne tazo da kanta ta tafi da ita ta gaisa da wasu aminanta na amana dan ba wani ganin Raudhan sukai sosai ba lokacin nasu

auren. Komai cikin dauriya Raudha keyinsa. Amma jikinta a matukar sanyaye yake tunda tasan yau mijinta zai zama nasune su biyu. A kwanakin nan duka kullum

sai ta buya tasha kukanta. Kuma tsaf Ramadhan na lure da ita batare data sani ba. Sai dai bai taɓa nuna mataba ya barta da lokaci kawai. Zai daibi duk

hanyar data dace ya mantar da ita idan suna tare kafin ta sake samun dama.
          Kasa ɗagowa tai ta kallesa lokacin daya shigo tana zaune ita da Basma da Rumaisa da Fadila a falo. Yayi kyau matuka cikin ɗanyar shadda data

wadatu da jiƙaƙen ɗinki. Sai maiƙo da ɗaukar ido take gamai kallo. Gashi sosai babbar riga ke kawata adonsa da maidashi wani babban mutum. Sannu da zuwa su

Basma sukai masa suna mikewa. Dama Anne ce tace suzo su ɗebe mata kewa kafin ya dawo tunda tasan babu mai shiga sashen nan da sunan yazo biki.
           Bayan ficewarsu ya tako a hankali zuwa gabanta yakai dukunne. Hannayenta ya kamo cikin nasa tare da saka ɗayan ya ɗago habarta. Itama tayi ƙyau

matuƙa cikin wani lass mai azabar kyau da nauyin kuɗi. Ga ɗinkin ya zauna mata ɗas a jiki saboda kibar da tayi da ƙara haske da fresh. Taci kayan ado na ɗan

kunne da sarka da zabba da awarwaraye ga ɗauri daya amsa sunansa ɗauri kai kace itace amaryar.
     Kukan da taketa riƙewa tun ɗazun ta sakar masa. Lumshe idanunsa yayi tare da mikewa ya ɗagata cak ya rungume a jikinsa yana murmushi.
     “Haba ƴar aljanna. Kwantar min da hankalinki Ramadhan B. Hameed Taura na Ameenatu Dawood Hutawa ne ita jaɗai insha ALLAH. Badan bazan iya karawaba

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button