HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 5

 *HALIN GIRMA**_Hafsat Rano_*

      *5*

*_Last free page!_*

****

Tana zaune ta idar da sallah, bata tashi daga kan abun sallar ba taji shigowar sa shashen Gajin, gabanta taji ya fadi, tayi kamar bata ji sallamar da yayi ba, tayi tsam a kan sallayar tana kallon gabanta. Da kallo ya bi bayan ta ya samu waje ya zauna a cikin kujerun falon yana kokarin daidaita yanayin da yake ciki. Gajin ce ta fito, 

“Wa nake gani kamar Ibrahim?”

“Nine nan wallahi Hajiya.”

“Lale marhabin, barka da zuwa. Saukar yaushe?”

“Dazu na shigo, mun same ku lafiya?”

“Lafiya lou wallahi, yasu Hajiyan da yan uwanka?”

“Kowa lafiya suna gaida ku.”

“Muna amsawa, sannu da zuwa.”

” Yawwa.” Yace yana yawo da idon sa akan ta, 

” Iman ba magana?” Yace yana son Gajin ta tanka

“Kaji sokonci, wai bata gaishe ka ba?” Tayi maganar da sauri

“Ina wuni?” Tace a gajarce

” Lafiya lou, kina lafiya?”

Shiru tayi bata amsa ba, Gaji ta hau sababi tana mata fad’a, tashi yayi hannun sa cikin aljihu ya zaro wayar ta

“Gashi na tsince ta a kitchen.”

Ya mik’a mata sannan yayi wa Gajin sallama ya fice yana raya ta yadda zai bulowa Iman din, ya gama gane yanayin ta ba irin nasa bane, shirun ta yayi yawa amma duk da haka shi ba damuwar sa bace, yadda ya shiga zuciyar kowa a gidan nan da hakan zaiyi amfani ya kafa kansa, ba zai wani ja lokaci ba zai gabatarwa Gaji da kansa, baya jin ma zai wuce gobe, zai sai fara tuntubar Yaya Hajara idan yaga ba ta goyi bayansa ba zai yi gaban kansa, iya ka tayi masa fad’a shikenan ya wuce.  Be koma shashen ba, sai ya fice daga gidan a kafa yana adana number da ya dauka a wayar ta ta, so yake ya saka number a truecaller yaga ko zai samu wani information akai.

   

Cikin call log dinta ta shiga ta duba amma bata ga number da aka kirata ba, taji babu dadi dan bata so yaga kamar tana sane ta bayar aka daga wayar tasa. Ko da tafiyar su ba zatayi daya ba, ba zata so yaji a ransa dan yana lacking wani abu bane shiyasa hakan ta faru. Kwantar da kanta tayi a saman hannun kujerar ta rufe idon ta tana tariyo zuwan da yayi wajenta, akwai wani abu me girma a muryar sa sai kuma abu daya da ya tsaya mata shine kamshin turaren da taji yana yi, wanda yayi kama da me tsada ne irin ajin farko, domin Allah ya hore mata kaunar kamshi, shiyasa ta kan yi saurin ganewa. Sai dai akwai irin tuurare yan durin nan da suke da kamshi me dadi har ka kasa tantance su, kila irin su ne, abunda ya kara burgeta dashi kenan, duk da yana cikin yanayin da zaka ce kai tsaye babu, amma be bar kansa a wulakance ba. Juya kanta tayi daya gefen ta dora wayar a saman cinyarta ta cigaba da tunani.

***Kiran sallar magriba ya sashi fita daga sashen nasa zuwa masallaci, achan yayi alwala ya shiga sahun farko sukayi sallar. Bubu na ganin shi yaji dadi sosai. Bayan an idar ya wuce bangaren nasa domin ya jira shi, yana zaune sai gashi ko ya shigo, ya tashi tsaye har sai da ya zauna sannan ya zauna shima a k’asa cikin girmamawa ya sake gaishe shi, ya amsa masa sake yana nazarin sa.

“Muhammadu!” Ya kira sunan sa, gyara zaman sa yayi ya tattara hankalin sa waje daya cikin son ganin be yi wani abu a gaban Bubun ba

“Kana ji na Muhammad?”

“Inaji Bubu.”

“Madallah, Muhammad ka san dai a tsarin gidan nan kana cikin lokacin da ya kamata ace ka ajiye iyalin ka kaima, ka nutsu waje daya a kalla hakan zai taimaka maka wajen cikar kamalarka.”

Kansa a kasa yana jin Bubun yayi ta bayani yana gida kansa cike da gamsuwa,

**A kofar ta tsaya tana kallon takalmin Muhammad din dake zube a wajen, ta samu labarin zuwan sa a wajen Kamal amma bata tsammaci irin wannan ganawar da Maimartaba ba, shiyasa ta kasa hakuri tazo ta nemi iso wajen Maimartaba din wajen sarkin kofa amma sai ya nuna mata ba zai yiwu ba, domin an gargade shi akan barin kowa ya shiga shashen maimartaba din har sai ya kammala ganawar sa da Muhammad din, ranta a matukar bace ta koma sashen ta tana jin wani irin tashin hankali, tana tsoron kar Muhammad din ya amsa tayin mahaifin nasa a wannan zaman da zasuyi.

   Safa da Marwa tayi tayi, har wajen sallar isha basu fito ba, tana hangen bangaren ta cikin nata shashen, ta kasa zama tana da yakinin ko menene suke tattaunawa haka me muhimmanci ne sosai.

   Tana tsaye jikin window taga fitowar su, fuskar Muhammad din a sake yana takewa mahaifin nasa baya. Tsaki taja ta saki labulen tana juyawa zuwa gefen gadon ta, ta zauna tana sake jan wani tsakin, tsakin haushin Muhammad din da ya zame mata ciwon ido shi da mahaifiyar sa.

“Ranki ya dade, Maimartaba ya aiko yana da bukatar ganin ki bayan ya dawo sallar isha’i.”

Bata amsa ba, sai ma juya fuskar ta da tayi wani sashen tana sake sakin siririn tsaki.

***Bangaren sa ya koma, ya tattaro abunda ya san zai bukata ya fito, sai kuma ya tuna da maganar Maimartaba ta karshe da suka tattauna, yana son ganin sa da safe kafin ya fito fad’a, komawa yayi ba dan yaso ba, ya ajiye komai ya zauna yana kirga lokacin zuwa wayewar gari. Nisan yayi yawan da yake jin kamar yayi loosing idan har ya kyale shi tsawon wannan lokacin.

   Wayar sa dake ajiye a gefen sa ta dauki sowwa, ya daga ganin kiran da yake ta jira ne tun dazu, 

“Oga na duba maka number din, akwai bayanan sa da komai har da wajen aikin sa, hoton sa da kuma location dinsa a yanxu, na tura maka ta mail sai ka duba.”

“Ok! Thank you, zan neme ka. ”

Ya katse kiran ya shiga mail dinsa, ya hau kan message din ya bud’e. Hoton sa ya bud’e yayi zooming sosai, sai kuma ya fita ya karanta information din. Karamin tsaki yaja ya ajiye wayar yana jin a ransa wannan din karamin kwaro ne be kamata ya hana shi walwalar sa ba, abu daya zai masa ya kama shi a hannun sa, sai dai ba zai hakan ba har sai ya je ya tabbatar da zargin sa.

***Anan sashen Gajin ta shirya, ta wuce islamiyya tana tafe tana satar kallon hanyar ko zata ganshi tunda yace mata yana zama ne domin yaga wucewar ta, har ta isa makarantar bata ga ko me kama dashi ba, sai kawai ta share tayi abinda ya kaita. A dawowa ma haka ta sake yi shima bata ga kowa ba, ta dawo gida ta chanja kayan ta kenan aka shigo aka ce tazo inji Muhammad, Hijab ta dora a saman kayan jikinta ta fito. A tsaye yau ma ta hange shi wajen kujerar, ya rataye hannayen sa a bayan sa yana tsaye kyam akan kafafun sa. 

“Assalamu alaikum.” Tayi masa sallama tana jan kujerar.

“Sannu da zuwa, nan akwai rana bari na saka maka a chan.” Taja kujerar zuwa k’asan wata yar bishiya ta ajiye, 

” Bismillah.” Tace masa tana nuna masa kujerar, be zauna ba, ya zaro hannun sa daga bayan sa, ya dawo dasu gaba ya rungume su a kirjin sa, 

” Bismillah.” Ya nuna mata kujerar da baki

” Zauna babu matsala.” Yace mata

” A ah dan Allah ka zauna, be kamata na zauna kana tsaye ba, ance bakon ka…”

” Kyale fadar hausawan nan, zauna dan Allah.”

Allah da taji ya ambata yasa ta zauna a kunyace, ya zura mata ido har sai da ta dan ji wani iri.

” Na cika kallo ko? Kiyi hakuri.” Yace mata yana murmushi,kallon ta kadai yayi jin sa yake kamar yafi kowa sa’a a duniya

” Ba komai.” Tace tana gyara wayar hannun ta

” Ina wuni?” Ta gaishe shi yana dan zamowa

 

” Lafiya lou, sai kika jini shiru, tafiya nayi zuwa kauye Baba ya kira ni, naso ma na zo kafin na wuce toh tafiyar ce tazo a gaggauce, sauka ta kenan ma.”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button