ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

” Haba ya Suhaila don Allah kiyi shiru ya isa haka mana, kar ki zama raguwa ki jure mana, kin jurewa shekarun baya ma ballantana yanzu da na san ko rabin su baza ki ƙara yi a gidan nan ba”.
“Farida Am confuse, bana son wani abbu yazo ya faru, kuma kinga har yanzu ba muyi magana da Habib akan matsala ta ba, am scared idan na faɗa mai yace ya fasa aure na”.
“No Ya Suhaila ai ba wani abu a jikin ki yake so ba, ki ɗin ya gani yake so, so plss don Allah ki cire duk wata damuwa a ranki, mu kuma zamu cigaba da miki addu’a in sha Allah”.
“Na gode sosai da kika kwantar mun da hankali da bani da ƙanwa irin ki da ban san ya zan yi ba”.
“It’s okk ya Suhaila, idan ban miki ba wa zanyi wa. Kuma please karki faɗawa ya Fatima abunda ya faru yau karma ki tayar mata da hankali”
“In sha Allah”.
******
Ummi ce zaune akan gado ta rafka uban tagumi tana jiran Alhaji muhammad ya fito daga toilet, tunda ta shiga ɗakin yana ciki be fito ba.
Tana nan zaune y fito da towel a ɗaure a ƙugun shi ko kallon inda take be ƙara yi ba ya cigaba da sabgar shi, har yayi shirin bacci ya kwanta abunshi, tana nan zaune a gurin kamar wacce aka dasa.
Sai da ta gaji da zama sannan ta koma kusa da shi ta zauna.
“Abban Suhaila”.
Shiru be amsa mata ba kuma be motsa ba.
“Na san kana ji na don Allah ka tashi magana za muyi”.
“Hmm Asiya indai kin san tayar mun da hankali zaki yi to please ki rabu dani kawai”.
“Ka tashi don Allah”.
Ta faɗa tana ƙara matsawa kusa da shi.
Be mata musu ba ya tashi ya zauna, kallon cikin idon shi tayi ƙwalla na ƙara cika idon nata, mayar da su tayi ta rufe nan da nan hawayen da suke kwance a cikin idon nata suka zubo, a hankali ta fara magana.
“Yanzu har zaka iya ɗaga hannu ka mare ni yaran mu suna ji?
Wani wawan kallo ya watsa mata, yana ƙara jin wani takaici na kama shi.
” Hmm ke kuma tijarar da kike yi mun ai basa ji ko?
“Ai wannan daban ne, amma ya za ayi ka mare ni a gaban su”.
“Daban ko? Saboda kin saba mun irin wannan sunajin ki, ke yanzu ba kya jin kunyar suje gidan miji suna wa mazajen su abunda kike mun umm?
” Ban isa na miki magana ba yanzu zaki hau kaina ki fara faɗa da bala’i da masifa”.
“Indai akan bikin Suhaila ne wallahi bazan ƙara sa muku baki ba, tunda abun har ya kai ga mari”.
“Hmm da dai kin samawar kanki sauƙi”.
“Allah ya baku sa’a kuma zaku ce na faɗa muku”.
“Dama addu’a kika yi da yafi miki tunda ƴar kice ba ta wani ba”.
“Hmmm Allah ya bada zaman lafiya”.
Amsa mata yayi da tau sannan ya juya mata baya yayi kwanciyar shi abunshi.
Sai da itama tayi wankan ta shirya cikin pyjamas ɗin ta itama tabi lafiyar gado.
Suhaila kam da ƙyar tayi bacci sai jiyar zuciya take saukewa saboda kukan da ta sha abun tausayi.
Washegari da safe haka gidan ya tashi shiru babu wani motsin arziƙi.
Ranar ne kuma dangin su Habib su ka kawo kuɗin auren Suhaila.
******
Farida ce zaune akan kuje sai rolling spring rolls ta ke, daga gani kasan ta sha aiki babu lefi.
Bayan sun kammala ta shige toilet tayi wanka ta fito, ita kuwa Suhaila tana kwance akan gado zazzaɓi ya kama ta sai rawar sanyi take.
Farida ce ta zauna a gefan gadon ta ɗora hannun ta akan goshin ta.
“Haba ya Suhaila wai me yasa kike irin haka ne, kina ganin komai ya wuce, ita kanta Ammi ta haƙura kina kallon duk tare mukayi aiki da ita”.
Kallon Farida tayi nan da nan ƙwalla ta cika mata ido.
“Farida ina fargabar sanar da Habib halin da nake ciki gaskiya”.
“Haba ya Suhaila ai ya zama dole ya sani ko da kuwa zai fasa auren ki ne. Idan ma be aure ki ba ba za ki rasa mijin aure ba, akwai wanda zai zauna da ke tsakanin shi da Allah, ya kuma kula da ke sosai kamar ma lafiya lau sumul ya same ki.
” Ya Suhaila ba duka aka taru aka zama ɗaya ba ki faɗa mishi kawai”.
Tashi tayi ta zauna ta jingina a jikin fuskar gadon ta kalli farida sannan tace”Ina ji a jiki na wani abu zai faru da ni nan ba daɗewa ba, ko mutuwa zanyi ne, don gaskiya bana jin abun mai kyau ne”.
“Haba ya Suhaila mutuwa kuma ana zaune ƙalau”.
“Farida am weak wallahi, ko na faɗawa Surayya ta fara sanar da shi?
” Uhmm yadda kika gani. Bari naje muyi arranging kayan nan”.
Bayan Farida ta fito daga ɗakin ta ɗauki wayar ta kira Surayya.
“Hello amaryar yaya Habib bakya lefi”.
“Hmm Allah ya shiryaki. Surayya magana nake so muyi da ke please”.
“Okk am all ears me ya faru ne?
” Don Allah ki faɗawa Habib matsala ta, he have to know the secret tun kafin maganar nan tayi nisa”.
“Year Suhaila kuma da gaskiyar ki, duk da na san bashi da matsala amma kuma ba a shedar namiji a wannan fannin, bari zan yi mai maganar, amma kema kiyi mai please saboda kwana biyu bana jin daɗi sosai”.
“Kice mun samu Nu’aman”.
“Ban sani ba ƴan sa ido kawai, sai anjima ki gaida Ammi”.
Nan ta kashe wayar ta.
******
Ƴan uwan Habib sun zo anyi baiko an saka rana, nan da wata uku masu zuwa za ayi bikin saboda ba sa son abun yayi nisa sosai.
Abbu shima yaji daɗi sosai don babu abunda yake so irin Suhaila tayi aure itama ta huta.
Ranar kam Habib kamar ya zuba ruwa ƙasa ya sha don murna itama Suhaila taji daɗi sosai.
A ɓangaren Ammi kuwa babu lefi ta kwantar da hankalin ta sannan kuma tana kula Suhailan sai dai fa har aka gama kawo ƙuɗin bata ce uffan ba tun dai da ta gama aikin abinci.
Suhail da Habib soyyaya suke sosai sai dai fa har yanzu ta kasa sanar da shi sirrin da yake ƙasan zuciyar ta wanda tasan dole ne ta sanar da shi, idan ba haka za a samu babbar matsala.
Shima kuma Habib ɗin a nashi ɓangaren da tace tana son magana da shi sai yace mata ta bari sai yazo kano sunyi a tsanake. Bayan wani ɗan lokaci aka yi posting ɗin su zuwa camping Allah ya temake ta akayi posting ɗin su Kaduna har da Surayya kuwa, amma sai dai mijin Surayya ya nemar mata alfarma aka barta a nan kano ita kuwa SUHAILA haka nan ta fara shirin zuwa can kadunan, a nan ne kuma Habib hankalin shi ya tashi har nemi a sakko da bikin indai ba wai akwai wata matsala bane saboda bazai so Suhailan ta tafi gurin da babu me kula da ita ba duk da ya san zata yi iya bakin ƙoƙarin ta,a lokacin kuma bikin nasu saura kusan wata ɗaya da sati biyu haka nan aka cire sati biyun kau bikin ya dawo saura kwana 30 cif.
Biki saura sati uku Habib ya diro garin kano saboda abubuwa sun mai yawa sosai shiyasa be samu damar zuwa da wuri ba amma kuma duk wani preprations suna yi ta waya ya ba ta kuɗin komai harda na gyaran jiki ma.
Da misalin ƙarfe 1 na rana Habib ya isa gidan su Suhaila.
A sit room aka yi mai masauki be daɗe da shigowa ba Suhaila ta shigo cikin palon da tire wanda yake ɗauke da kayan ciyeye da kuma kayan marmari sai lemuka masu mugun sanyi.
Sanye take cikin black jilbab tayi rolling da army green ɗin mayafi fuskarta babu wani make up daga kwalli sai lipstick, amma kuma ba ƙaramun kyau tayi ba a hankali ta ƙarasa shigowa cikin palon cikin nutsuwa .
Guri ta samu ta ajiye farantin kayan abincin kafin ta zauna akan kujerar da take kallon shi.
A kunyace ta ce”Sannu da zuwa ina wuni ka iso lafiya?
Shi kuwa Habib tunda Suhaila ta shigo yake kallon ta babu ko ƙifta ido saboda ba ƙaramun tafiya tayi da imanin shi ba, ji yake kamar ya sata a aljihu ya gudu da ita, ji yake inama ace a halin da suke ciki a matsayin matar shi take, babu abunda yake gani sai ita. Duk cikin ƴan matan da yayi soyyaya da su babu wacce yake so yake ganin mutuncin ta irin Suhaila, itace rayuwar shi ita ce komai nashi.Sai da ya tattaro nutsuwar shi kafff sannan ya samu damar yin magana.