ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Yauma kamar kullum ya dawo daga aiki ya shigo cikin gidan yana ta sallama amma bata ji shi ba saboda yadda tayi nisa a cikin tunanin nata.
Zama yayi a kusa da ita ya rungumo ta ta baya ya saka haɓar shi a gefan wuyan ta yana busa mata iska,jin shi a jikin ta yasa ta lumshe ido alamar hankalin ya dawo jikinta, juyo da ita yayi tana kallon shi, a hankali yayi pecking lips ɗin ta sannan ya saka hannun shi ya ɗago haɓar ta kafin a hankali ya fara magana.
“Ohhh Shadineyy menene?har yanzu baki cire abun nan a ranki ba?”
Kallon shi tayi idonta duk ya ciko da ƙwallo tace; “This is not funny Cynosure ya kamata ace muna da baby zuwa yanzu gaskiya ummm shekara ɗaya fa kenan harda wata ɗaya amma shiru, me kake tunanin mutane za su faɗa a kaina ummm?”
“Babu wani wanda zai faɗi magana Azizateyy, naga mu kaɗai muke rayuwar mu ba Ummi ba Daddy ballantana kice suna so suga jikan su”.
“To kasan me Ammi take cewa ne? Wai har yanzu bani da ciki wai anya kuwa bamu da matsala wai muje muga likita”.
Lakuce hancinta yayi sannan ya rungume ta tsam a jikin shi yace; “Shagwaɓaɓɓiya kawai gobe da safe sai muje muga doctor ko?”
Rungume shi tayi itama tace “To” tana jin farin ciki sosai a wani ɓangaren kuma tanajin tsoron kar ace matsalan daga ita ne.
Washegari ko da suka je asibiti anyi musu duk wani gwaje-gwaje amma babu abunda yake damun ɗaya daga cikin su, haka suka dawo gida gaba ɗaya jikin su a sanyaye.
Haka suka cigaba da rayuwa kullum cikin rarrashin ta yake, Suhaila kuwa bata da aiki sai na tashi cikin dare tana addu’a, ko lokacin Ahmad bata fiya samu ba yanzu saboda da daddare kullum cikin sallah take ganin bata jin maganar shi yasa shima yake taya ta suna sallah suna kaiwa Allah kukan su.
Bayan wata shida.
Yauma kamar kullum Ahmad yana tsaye a bakin toilet yana jiran ta ta fito daga banɗaki don test take yi, sai addu’a yake Allah yasa suga positive idon ba haka ba ya shiga uku da Suhaila ba irin yadda ta ɗaga hankalin ta saboda watan ta biyu kenan bata yi period ba kuma tanajin tsoron yin test taga negative saboda ya taɓa mata haka, da murnarta, tana yi taga negative.
Fitowa tayi daga banɗakin idon ta duk ya ciko da ƙwalla yana ganin haka ya girgiza mata kai, yana tahowa zuwa gurin ta hannun ta kuma ga tsinken gwaji.
Yana ƙarasowa ta faɗa jikin tana sakin ihu.
“Yeeee, ya Ahmad.. I mean my cynosure, positive ne, finally i am pregnant, Alhamdulillahi zamu samu baby”.
Sama yayi da ita yana faɗin “Allah?”
Gyaɗa mai kai tayi hawayen farin ciki na gangaro mata.
Sauke ta yayi ya haɗe bakin su yana bata wani kiss me wuyar fassarawa kafin ya rungume ta tsam a jikin shi.
Kallon ta yayi yace; “Yau sai an bani, a bani abinci na gaskiya”.
Dariya tayi tace; “Kana so in baka sau uku yau?”
Saurin gyaɗa mata kai yayi yana haɗe goshin su waje ɗaya.
“Sai kaci grapes guda uku tukunna”.
Ɓata fuska yayi yace; “Ai kema kinsan bazan iya ba, please a bani wani aikin amma banda wannan don Allah”.
Dariya tayi sannan tace ; “Sai ka goya ni kayi yawo da ni a cikin unguwar nan tukunna”.
Dariya yayi sannan ya buɗe drawer ya ɗakko mata abaya da dogon wando ya saka mata sannan ya ya yafa mata mayafi, ya goya ta suka fita, sun daɗe suna yawo suna hira sannan suka dawo gida.
Ranar kuwa yini suka yi suna shan soyayya kamar za su cinye junan su.
Washegari da safe tana zaune sai lallaɓa kanta take sun gama waya da Surayya kenan ta sanar da ita tana da ciki taji bell yana ƙara.
Tayi mamaki don tasan Ahmad baya dawowa da rana haka, a hankali ta tashi ta buɗe musu ƙofa.
Turus tayi ganin Kausar da Ummi sai Jibril a bayan su.
Da gudu ta rungume Kausar hawaye na cika mata ido.
Yayin da Ummi take gefe tana kallon yadda Suhailan ta canza tayi kyau ta kuma ɗanyi ƙiba babu lefi.
Sunkuyar da kai tayi sannan ta faɗa jikin Ummi tana sakin kuka.
Ɗagota Ummi tayi suka shigo cikin gidan suka zauna a kujera.
Cikin sanyi jiki tayi musu sannu da zuwa sannan ta tashi ta kawo musu ruwa da lemo, kafin ta dawo ta zauna kusa da Ummi tana sunkuyar da kai.
“Ummi ina wuni”. Ta faɗa cikin sanyi murya.
“Lafiya lau daughter”.
Sai kuma tayi shiru saboda gaba ɗaya kunyar su take ji, Jibril ta kalla ta gaishe shi, cikin sakin fuska ya amsa mata yana tambayar ta ya gida,jikin ta duk a sanyaye ta amsa mai da lafiya lau.
Ummi ce ta kalle ta tace; “Ashe ƴa zata iya fushi da mahaifiyar ta har na kusan tsawan shekara biyu ban sani ba?”.
Shiru Suhaila tayi sai kuma ta saka kuka.
“Wallahi Ummi ya Ahmad ne ya karɓi waya ta ya goge numbers ɗin ku ya saka ku a black list yadda baza ku iya samu na ba amma Allah ba lefi na bane”.
“Ke kuma ƴar daɗi miji ko? Kin samu gidan ki sai kika biye mai kuka zauna ku kaɗai kamar mayu baku da dangi ko?”
Shiru tayi ba tare da tace komai ba, haka Ummi tayi ta mata faɗa tana nuna mata abunda suka yi sam basu kyauta ba domin kuwa iyaye sun fi ƙarfin a wulaƙanta su haka.
Can after magrib Ahmad ya dawo yana shigowa ya gansu sun baje a palo sai cin abinci suke, Kausar ce taje da gudu ta rungume shi ita kuwa Ummi ko kallon side ɗin shi bata yi ba ballantana ta san da zaman shi.
Jikin shi a sanyaye ya ƙaraso ya tsuguna har ƙasa ya gaishe ta.
Ko kallon shi bata yi ba ballanta yasa da ran zata amsa gaisuwar shi,haka ya gama rara gefan shi ya haye sama yayi wanka sannan ya sake sakkowa, sai dai yana zuwa yaga suna shirin tafiya Suhaila kuwa ita da Kausar sai kuka suke wai basa son rabuwa da junan su.
Ummi ce tace; “Malama zo ki wuce mu tafi, dama amanar mutane da na karɓo ita nazo dubawa tunda tana cikin ƙoshin lafiya tare da mijin ta daya hure mata kunne yake nuna mata yadda zata raina iyayen shi ai shikenan ko?”.
“Zoki wuje mu tafi”. Ummi ta ƙarashe maganar tana fizgo hannun Kausar.
Da gudu ya ƙarasa ya rungume Ummin ta shi ta baya yana bata haƙuri shi kanshi yasan abunda yayi mata sam be kyauta ba amma yaya zai yi, haka yayi ta bata haƙuri yana lallaɓata har ta haƙura.
Jibril kuwa sai dariya yake saboda dama shi suna waya da Ahmad sosai.
Haka aka koma aka sha hira after 11 suka koma masaukin su Washegari kuma za su koma gida don Daddy be san sun zo ba yayi tafiya na ƙwana uku ne shine suka sato hanya.
Bayan sati ɗaya da zuwan su Ummi. Suhaila ce zaune kan kujera sai game take yi a wayar Ahmad shi kuma yana toilet yana wanka, kamar daga sama taji saƙo ya shigo cikin wayar tashi haka kawai ta tsinci kanta da son karanta saƙon nashi.
Buɗewa tayi ta fara karanta saƙon kamar haka _”Salama alaikum Ahmad kun tashi lafiya ya Suhaila take? masha Allah, dama cewa nayi bari na tuna maka zancen kuɗin littafin nan na Farida ta sake yi mun magana gashi Abban su har yanzu ba ayi albashi ba kuma wai zuwa jibi ake so su siya, nace ta tambayi Jibril wai ita baza ta iya tambayar shi ba,na gode sai anjima._”
Gaban tane taji ya buga damm, sai kuma ta kalli no, tabbas number Ammin ta ne me hakan yake nufi kenan Ahmad Ammi take tambaya kuɗi ko me.
Kanta ne taji ya buga nan da nan taji ya fara mata ciwo, sai kuma ta fara bin messeges ɗin Ammin tundaga farko har zuwa kan wannan, jefar da wayar tayi ta haɗa kai gwiwa hawaye na zubo mata ta rasa wace irin uwa Allah ya basu ita dai kuɗi shine rayuwar ta kuma abun ya wuce kan Abbun ta ya tsallako har kan Ahmad ga wani tallan wulaƙanci da tayi ga ƴar uwar ta, ko haka tace mata bata taɓa saurayi ba oho.