ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

A haka ya fito ya same ta da sauri ya ƙaraso yana ajiye towel ɗin hannun shi ya rungomata zuwa jikin shi sannan ya fara tambayar tq me ya same ta.
Cikin kuka ta cilla mai wayar shi kan cinyar shi dai-dai inda saƙon Ammin nata yake sannan tace; “Me yasa tuntuni baka faɗa mun ba han? Wato kallon da kake mu kenan ko, uwata me son kuɗin bala’i shiyasa baka taɓa faɗa mun ba kake kallo na da abun, sannan ta saka ka haɗa Jibril da Farida amma baka taɓa faɗa mun ba itama Faridar da yake munafuka ce ai bata sanar dani ba ko, wallahi sai naci ubanta, nasan Abbu besan duk suna ƙulla waƴannan abubuwan ba zanyi maganin su wallahi”.
Ɗan murmushi yayi ya tashi ya nufi gaban mirror ya fara shirin shi kafin yace; “To shadineyy so kike nace miki Ammi na tambaya na kuɗi? ko kuma so kike naƙi bata kuma alhalin ina da shi? babu komai na fuskance ta kuma nasan irin ta so, karki wani damu kanki shiyasa ma ban taɓa miki maganar ba all this while, Jibril kuma da Farida su suka ce kar na faɗa miki don haka ba ruwa na, yanzu ma ba ni na faɗa miki ba binciken ki ya kaiki kika gani so, i am out”.
Ko kallon shi bata sake yi ba tayi kwanciyar ta abunta har ya gama shiri yayi kissing fore ɗin ta sannan ya girgiza kai ya fita yasan kafin ya dawo ta dena fushin.
Yana fita ta kira Ammin ta ranar kuwa sai da suka yi faɗan da suka daɗe basu yi ba.
Sannan ta kira Farida ta zage ta tasss, sannan taji ranta ya ɗan mata sanyi.
Da yamma bayan ta gama gyare gidan ta kunna ragowar turaren wuta wanda shine na ƙarshe, ta gama girgirki tayi kwalliya tana jiran shi ya dawo.
Ganin ta gaji ta jiran shi yasa ta shiga library da duk yayi ƙura tana kallon abubuwan ciki zanukanshi da ta gani a London taga wasu daga cikin su a nan ga kuma littafai ba adadi sai wanda ka zaɓa, ɗan dafa wani shelf tayi ta ɗan saka effort sai taga ya motsa ƙara dannawa tayi sai kawai taga ya fara juyawa, wani ɗan guri ya bayyana, pappers da abubuwa da yawa ta gani a gurin sai wasu pictures marasa kyaun gani wanda saida gabanta ya buga dam, don hotunan ƴan mata ne kala-kala, wani shida abokanan shi sun rungume ƴan mata wani kuma shi kaɗai ne, wani da kaya wani babu kaya, wani ya saka short wando da uban sarƙa gashi nan dai pics ɗin gangs wanda da ka kalle su kasan sai ahankali, hotunan shi ta gani da Suraj da ƴan mata a club, gashi nan dai abun ba kyaun gani sai addu’a.
Wani CD ta gani a gurin kamar an saka ta dole ta ɗakko su guda uku, ta mayar da gurin ta rufe sannan ta sakko ƙasa ta saka ta fara kallo.
Na farko competition ne su kayi na shan koken kuma Ahmad yafi kowa sha, na biyu kuma giya ce kawai suke sha kamar wasu mahaukata, sai na uku kuma a club ne shida suraj sai rawa suke da mata ana musu video.
Ko ƙarasa kallo bata yi ba ta saka pause ta haɗe kai da gwiwa tana kuka kamar ranta zai fita duk da tasan a baya yayi waƴannan abubuwan kuma ya dena it’s still hurt and baza ta iya jurewa ba ji take gaba ɗaya komai nata ya tsaya mata ga kanta da yake mugun juya mata ta rasa yadda za tayi ita kam taga ta kanta jarrabawa kala-kala daga wannan sai waccen.
Nan da nan zazzaɓi ya kamata ta takure a kan kujera ko sallar magrib ta kasa tashi tayi.
Haka ya shigo ya same ta da sauri kuwa ya ƙaraso yana taɓa jikin ta, sai dai kuma yana ɗora idon shi akan screen ɗin tvn ya mayar da su ya runste yanajin zuciyar na mishi zafi.
Play ya saka don ya ƙara tabbatar da ta kalla sai kuma ya tashi ya kashe tvn a nan yaga ragowar CD’s ɗin alamar duk ta kalla.
Da gudu ya ƙaraso ya Ɗagota ta dawo jikin shi ya rungume ta tsam sannan ya fara magana”Azizateey wallahi duk abunda kika gani bana yi yanzu na roƙe ki don Allah ki fahimce ni don sonki da annabi kiyi haƙuri wallahi, wallahi na dena Allah kuwa tunda na fito daga *Rehab* na zama criminologist wallahi na dena please ki yarda da ni don Allah”.
A can Nigeria kuwa tun ranar da Suhaila ta samu ciki boka ya sanar da Umma hakan ne yasa tace kota wace hanya ce a ɓarar da cikin.
A dai-dai wannan lokacin kuma boka yake shirin aiko da aljanin shi.
Suhaila barin jikin shi tayi tace; “Naji kuma na yarda, kuma na sani tunda na gani da idanu na, amma still ba zuciyar dutse gare ni ba don haka i need some space so please leave me alone”.
Ta ƙarashe maganar tana tashi daga kan kujerar shi kuwa sakin baki kawai yayi yana kallon ta yasan sam be kyauta mata ba dama ya faɗa mata tuntuni da bata zo ta gani ba daga baya.
Shikuwa aljani yasan bazai iya taɓa ta ba hakan ne yasa ya zuba yawon shi sannan ya saka wani Abu wanda tana faɗuwa marar ta zata sauka akai, ai kuwa tana takawa ta sule jikake dahm ta faɗi akan stairs ɗin.
Rumtse idon ta tayi saboda zafin da taji amma kuma sai ta daure, da sauri ya ƙaraso ya riƙeta amma ta fizge ta cigaba da tafiya.
Bata ganin hanya ko kaɗan don duhu-duhu take gani sai da ta kusa gama hawa sannan ya hango jini yana bin cinyoyin ta saboda rigar da ta saka ko gwiwa bata zo mata ba.
Wani irin ihu yayi yace; “Azizateey you are bleeding!”
Ihun da yayi kawai kunuwanta suka ji bayan haka babu abunda taji, da gudu ya ƙaraso ya tarota ta faɗa jikin shi, kuka ya saka yana ƙara rungume ta shikenan saboda shi za su rasa babyn su.
Cikin tashin hankali ya ɗauke ta suka wuce asibiti suna zuwa aka karɓeta aka shigar da ita ciki, yayi kusan 1 hour yana jira sannan suka fito da ita nan suke sanar da shi ai tayi miscarriaging babyn dama kuma 9 weeks take so, beyi wani ƙwarin kirki ba, kuka ya saka yana zubewa a gurin shi yanzu idan ta tashi me zaice mata tayi ɓarin cikin kenan, ya shiga ukun shi ina zai saka kanshi.
Haka ya dinga kuka daga baya dai ya tashi ya shiga ɗakin ya zauna yna kallon innocent face ɗinta, buɗe idonta da yayi mata nauyi tayi sannan ta kalle shi..
Tashi ta soma ƙoƙarin yi nan ya temaka mata ta tashi.
“Me muke yi a hospital?”
Sai kuma taji jikin ta is wet.
Daka mai tsawa tayi, cikin rarawar murya yace; “Ou..r baby”.
“Uhmmm what happen to the baby”?
“Shadineyy i am sorry but we lost our baby”.
Komawa kawai tayi ta zube a jikin shi tana sakin kuka, rungume ta yayi shima yana kukan kamar wani wawa aka rasa me rarrashin wani……….
******
*A gaskiya sai kun zo jamun ɗan yatsa don sosai na gaji wallahi, kai typing is not easy*
*I love you all, my WhatsApp fans, facebook, wattpad inaji da ku irin sosai ɗin nan*
_*Ma’asalam, Faɗma Ahmad*_
[9/4, 12:57 PM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*
*Bintu Ahmad*
*Watpadd@cynosure3*
*Page9️⃣1️⃣to9️⃣2️⃣*
[ad_2]