HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

“Alhmadulliha gimbaya ta, irin wannan kyau haka ai sai ki sa na kasa motsi daga inda nake, sai kisa na kasa kai kaina kaduna zuwa gobe. Kin yi kyau sosai na siyi wannan wankan naki, kullum daɗa kyau kike yi wallahi ko meye sirrin.

Murmushi kawai Suhaila tayi tana wasa da ƴan yatsun hannun ta bata ce komai ba.

Shi kuwa ya tsare ta da idanuwa ya hanata sakat da taga dai abun nashi bana ƙare bane yasa ta sake cewa”Yasu Hajiya da fatan duk sana lafiya?
“They are all fine Habibty, sunce na gaishe ki da kyau”.

Shiru Palon yayi na ɗan wani lokaci, amma fa Suhaila da fa ɗago idon ta sai taga Habib ita yake kallo.

Ganin ba shi da niyyar cin abubuwan da ta kawo mai yasa tace”Bimillah mana ga abinci nan kaci, naga ko ruwan ma baka sha ba”.

“Hmmm ina naga ta cin abinci ai ke kaɗai ma abinci ce Habibty”.

“Ummm ni dai kaci abinci don akwai magana me mahimmanci da zamu tattauna”.

“Hmmm ai bazan taɓa manta wannan maganar me mahimmanci da kike ta son faɗa mun ba.

Ya ƙarashe maganr shi yana zuba juice a cup.

Bayan Habib ga gama cin abinci ya kalli Suhaila ya ce” Uhmm na gama ina jin ki Gimbiya ta”.

Sai da tayi shiru tayi jimmm kafin ta ce”Akwai wani abu da nake so ka sani gama da ni ina fatan bazai taɓa maka zuciya ba Habib”.

Saurin ɗaga mata hannu yayi alamar ya isa”Suhaila menene zan sani gama da ke da har zai taɓa mun zuciya umm?

“Abunda zaki faɗa mun wanda zai taɓa mun zuciya shine idan kika ce mun ba kya haihuwa, ko kuma kina da ciwon HIV aids, bayan wa’inan abubuwan babu wani abu da zai girgiza ni akan ki Suhaila, saboda Allah nake son ki kuma ba wani abu na jikin nake so ba, is you that i love, i mean the real you ba wai wani abu da kika mallaka ba and you have to know that, i love you Suhaila to the core, wallahi zan iya yin komai don na Mallake ki you are my world, and i want to be with you till eternity so please ki bar duk wani abu da kike son faɗa mun har sai munyi aure”.

Ita kam Suhaila shiru tayi tana jin kalaman Habib na ratsa gaɓoɓin jikin ta is that how much he loves her, ita kuwa da me zata saka mai. But then baza ta iya barin shi haka ba saboda halarcin da yayi mata.

“Albi, but you have to know the secret”.

Lumshe ido yayi saboda yana jin daɗin wannan sunan da take faɗa mai.

“Habibty i don’t want to know any secret, ke dai kawai ki cigaba da mana addu’a kinji ko, i love you so much”…

“I love you too”. ta faɗa ƙwalla na cika mata ido.

“Kar ki sake inga hawayen ki ko ɗaya Suhaila.

Saurin mayar da su tayi, amma fa zafin da yake taso mata a can ƙasar zuciyar ta babu abunda ya ragu, ba abunda take so irin Habib ya bata dama ta sanar da shi matsalar ta saboda bata so bayan auren su, su zo suna samun matsala, saboda tana son shi sosai itama, but then ta san yayi making up mind ɗin bazai saurare ta ba.

Tana cikin wannan tunanin ya katse ta. “Madam ina kuma kika tafi? Yanzu me kuke buƙata?

” Am here with you Albi bana buƙarta komai duk wani hidima ai ka gama mun”.

“Masha Allah bari nazo na wuce saboda zan biya gidan Surayya muji ita kuma me take shirya mana”.

“Har zaka tafi?
“Yess now, ai na ganki kuma nan da sati uku za ki zama tawa gaba ɗaya babu wata kunya”.

“Allah ya kaimu da rai da lafiya”.
“Amin Habibty”.

*****

Bayan Habib ya tafi Suhaila tayi saurin shiga cikin gida ta sanar da Surayya yadda su kayi da Habib ta kuma jaddada mata idan yazo karta barshi ya tafi har sai ta sanar da shi sirrin abunda yake damun ta.

Ammi ce zaune akan sofa ita kuma farida tana ƙasa a a zaune, Ammin na mata kitso shikuwa Mubarak yana gefe yana buga game ɗin shi a laptop ɗin Suhaila, shi dai idan kana so ka burge shi to ka bashi game.

Suhaila ce ta zauna kusa da Ammin tace”Ammi ga wannan da Habib yazo ya bani su yace wai in ƙara akan hidimar biki”.

“Ko kallon inda kuɗin suke Ammi bata yi ba tace” ki barsu a gurin ki idan wani abu ya taso kinyi kawai”.

Jikin Suhaila a sanyeye ta ce “Haba mana Ammi kiyi haƙuri kisa wa abun nan albarka, tunda aka fara maganar bikin nan baki taɓa sa hannun ki a ciki ba daidai da siyyar kaya tare da umman sheka mu keyi, na rasa me nayi miki Ammi, ƙaddarar mu ce tazo a haka we are mean to be together shiyasa, kuma hakan wataƙila shine mafi alkhairi tunda ina da tabbacin kina mana addu’ar miji na gari ko da yaushe, don Allah kiyi haƙuri”.

“Hmm Suhaila kenan, ai babu abunda zaki faɗa mun, ba dai namiji bane kije zaki gani”.

Zuwa yanzu kuwa Suhaila kasa daurewa tayi bata san lokacin da kuka ya suɓuce mata ba bata sake cewa komai ba tabar palon.

******

Bayan Habib da Surayya sun gama tattauna duk wani abun da ya kamata da wani preparations take ce mai tana son magana da shi akan Suhaila.

“Uhmmm inajin ki what about her ummm?

Dama tace tana son sanar da kai wata magana amma ka ƙi barin ta tayi magana shine nace bari ni na sanar da kai”..

“Kai amma dai da fitina kuke, na fuskanci bakin ku ɗaya. To inajin ki don idan baku faɗa mun ba baza ku barni na huta ba”.

“Dama shekaru biyar da suka wuce Suhaila was………..

Bata ƙarasa faɗan abunda zata faɗa ba kira ya shigo wayar shi, wannan dalili ne yasa tayi shiru don ya gama amsa kiran nashi.

******

_*Tofa ana wata ga wata, ko Surayya zata samu damar ƙarasa abunda yake bakin ta?*_

_*To sai a next page dai zamu sani*_

_*I need your comment shi ke ƙara bamu ƙarfin gwiwa..

_*Asslama alaikum*_

*faɗma Ahmad*✍️

 

*???????? AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*

*Page8️⃣to9️⃣
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*

*~We are bearer’s of so golden pen????~*

*~we write assidiously perceive no pain~no pain.~*

*Abin da wanda ya ji tsoron wasu mutane zai fada:*

اَللَّهُمَّ اكْفِنِيهِمْ بِمَا شِئْتَ.

Allahummak finihim bima shi’ita.
Ya Allah! Ka isar mini su da abin da Ka so.

 

_*The wedding preparations*_

Habib yana gama amsa kiran ya miƙe tsaye baibar Surayya ta ƙarasa abunda take son sanar da shi ba.

Sauri sauri gudu ya ɗau mukullin motar shi haɗe da wayar shi, kallon Surayya yayi da tayi galala tana kallon ikon Allah.

Yana fita daga palon nata yana bata bayani”Surayya munyi magana a waya, don ina tunanin yau zan wuce Kaduna, kiran nan wai kayan da mu kayi order ne suka iso kuma wai sun shigo har garin kaduna daga lagos wai amma drivern ya manta da wobil kinga dole naje muji yadda za ayi”.

Itama miƙewar tayi tana bin bayan shi tana magana”Haba uncle Habib da ka bari mu ƙarasa mana”.

“A’a, kinga a yanzu ma Hajiya tana jira na, munyi waya kawai.

Haka nan dai Habib ya tafi ba tare da Surayya ta samu tayi maganar ba, ta jinjina abun sosai don ta san ba lallai ne idan ya tafi ya samu lokacin da za a sanar da shi wannan zancen ba kuma ya kamata ya sani tun yanzu gudun matsala.

Cikin zuciyar ta take ayyana wai me yasa ma Abban Suhaila be sanar da ƴan uwan shi ba, sai kuma tayi tunanin ai shi Abba zai zata SUHAILA ta sanar da shi shiyasa har ya amince zai aure ta.

Bayan ta yi sallar la’asar ta kira Suhaila take sanar da ita yadda suka yi, SUHAILA kam bata ji daɗin abunba sam saboda ta san shi kaɗai ne zai iya kawo musu matsala da Habib ɗin duk kuwa da cewa yana son ta sosai.

Bayan sun gama waya take ƙara sanar da Farida abunda ya faru.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button