ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

“Ohhh ya Suhaila wallahi duk sai kin ƙara ramewa kafin bikin nan saboda kin sa abun nan a ranki”.
“Hmmm Farida ni kaɗai na san irin matsalar da hakan zata jawo mun shiyasa kika ga duk na damu, wannan fa ba ƙaramar matsala bace Farida”.
“Haba dai wai ke baki san yadda ya Habib yake sonki bane?
” Hmm wallahi Farida duk soyyayar ki da namiji indai akan matsala ta ne tsaf zai ajiye soyyayar nan a gefe yaci miki mutunci shiyasa nake tsoro”.
“To amma ai ko yanzu kika faɗa mai is too late”.
“Duk da haka amma dai at list na faɗa mai ko”.
Haka nan dai suka gama hirar su Farida na ƙara ƙarfafa mata gwiwa.
******
Biki saura sati biyu Suhaila ta shirya zuwa can ƙauyen su Abbun su da yake ƙaramar hukukar gwarzo can cikin wani ƙauye da ake kiran shi da rugoji.
Babban gari ne sosai babu lefi don abubuwan zamanin nan duk ana iya samu a can, kai harma wutar lantarki suna da ita, sai dai fa da ta lalace aka kasa zuwa a gyara musu, wannan dalili ne yasa yau kusan shekarar su goma babu wuta a garin.
SUHAILA ta ji daɗin tafiyar da Abba ya shirya musu duk kuwa da cewa ba kwana za su yi ba, kawai dai za aje ziyara ne da kuma sallama, duk dangin Abbun su SUHAILA suna garin sai shida ɗan uwanshi ne kawai suka fito kasancewar baban su yana da ƙoƙarin ganin sunyi karatun boko, wannan dalili ne yasa suna gama secondary ya nema musu jami’a suka fito don karatu, bayan sun gama kuma ko wannen su ya samu aiki shikenan sai basu koma garin ba kowa yayi aure abun shi.
Farida kam ta tsani zuwa garin saboda bata son halin mutanen ƙauye ita kuwa SUHAILA babu ruwanta gashi duk sanda suka tashi zuwa garin alhaji Muhammad baya barin kowa gaba ɗayan su yake tarkawata ya tafi da su.
Da misalin ƙarfe 6:30 na safiya suka tafi, cikin awa ɗaya kuwa suka isa garin.
Suna shiga cikin garin ƴan garin suka fara murna ganin motar Alhaji Muhammad don gaskiya indai ka ga motar gida to yawanci shine indai ba wani baƙo na mussaman za su yi ba.
Inna shibba kam taji daɗin ganin jikokin nata sai tsokanar su take.
“Aaa ƴan mata na an girma yanzu dai shikenan Allah ya kawo mana lokaci, Allah ya amsa mana addu’a, yo ke ƴan nan ai ni wallahi har na fara tunanin ko dai motanen ɓoye ke ɗawainiya da ke”.
Ta faɗa tana gyaran zanin ta irin na tsofaffafi.
Suhaila ce ta ɓata fuska tace “Haba inna mutanen ɓoye kuma?
” Eh mana yo to abun ne da mamaki, ke ɗin nan fa zaki kai kusan shekara 30 kinga kuwa idan a nan ne ai da tuni kina shirin aurar da ƴar ki ta biyu ko ta uku ma.
Suhaila ce ta zaro ido jin abunda kakar tata tace wai shekara talatin, kin san shi mutumin ƙauye da ka haura shekara 20 sai ya fara ƙara maka shekaru.
“Haba inna shekara ishirin da biyar nake ba daɗi ba ƙari”.
“Affff, ana jika dai, meye marabar? saura ƙaɗan ai”.
“Wallahi inna akwai maraba kuwa”.
Kan farida ta koma wacce tunda suka shigo take game a wayar ta ko a jikin ta”To ke kuma sai yaushe zaki samo mijin? kamata yayi ace tare ma aka haɗa ku wallahi”.
Farida kam ko kallon inda inna take bata yi ba tace “Tabbb ni kam ai sai dai ku kaini bola don sai na ga ƙarshen biro da takarda idan ma zanyi auren, eheee gwara ma kar ku dinga sako bakin ku wallahi, don ni ba ya Suhaila bace kuyi ta sakawa mutum ido”.
“To uwar marasa kunya, idan kin ga dama ma ki zama alhudahuda, dama wa zai kwashi kayan marasa kunya”.
“A to, ai ni dama bana son kowa ma ya kwashe ni”.
Haka dai suka gama wasan su har Abbun su ya gama gaisawa da mutanen cikin gidan.
Shi kuwa Alhaji Nafi’u wato kakan su Suhaila yana can majalisar su ta ƙofar gidan me gari be ma san sun ƙaraso ba sai da aka tafi kiran su.
Bayan ya iso gida aka ƙara gaisawa aka ci abinci kafin suka fita suka fara zagaya dangin nasu ana gaisawa, duk gidan da aka shiga sai Abbu ya musu abun alheri don mutumin ƙauye gwara ko hamsin ce ta raba ka da shi idan ba haka ba duk inda ya zauna sai ya zage ka.
Farida ce ta fara ƙunƙuni tana ita ta gaji da wannan zagayen da akeyi.
“Wallahi shiyasa bana son zuwa garin nan saboda anyita yawo da kai kuma duk sanda kazo abu ɗaya ne dai babu sauyi”.
Karaff kuwa sai a kunnen Alhaji Nafi’u nan fa ya fara surfawa Farida ruwan bala’i dama masifaffe ne na ajin ƙarshe don ko irin wasan kakan nan shi ba ayi da shi dama, sai dai suyi da inna”.
“Ka ji mara kunyar yarinya to ki koma gida mana wa ya ɗaure ki ko an miki dole ne?
Nan fa ya dinga yi har sai da Abbu ya bashi haƙuri tukunna .
Farida ya kalla ya daka mata tsawa sannan ya ja mata kunne da babbar murya.
“Dawo gefe na yadda kina ƙara magana zan kwaɗe ki! Mara kunya kawai”.
******
Bayan duk sun gama zagayen su suka fara shirin komawa gida amma fa ba wanda ya basu ko masara saboda yanayin sai a hankali a watan september ake, an kai abinici gona sannan kuma kaka bata faɗi ba haka nan suka dawo gida.
Tunda suka shigo gida Ammi take jaraba”Kai amma dai mutanen garin nan sunji kunya, yanzu ace ko ƴar daddawar nan da kuka da su kuɓewa babu wanda ya baku”.
Farida ce ta yatsina fuska ta ce “Hmm dama mutanen garin nan ana morar su ne? Ai sai dai kai ka basu, su kuwa basu san wannan ba idan kuma baka basu ba ya zama abun magana”.
“Allah ya kyata tau”.
Ita dai Suhaila bata saka musu baki ba ta cigaba da sabgar gabanta.
****
One week to…….
Gidan su Suhaila ya rikice ya kiɗime shirye shiryen biki kawai ake yi, an shirya komai Abbu yayi duk wani abu da zai iya kuma babu lefi komai ya tsaro, sai dai fa har yanzu hajiya Ammi bata wani saki jiki ba amma duk da haka ba ta nunawa kowa sai dai idan ita da Suhailan ne.
Su Surayya kuwa amara ƙirjin biki tana laulayi amma sam bata ji saboda ana ta bikin ƙawa.
Amarya kuwa tasha gyaran jiki ko ince tana kan sha ma, anyi mata dukkan su dilka ne da dai sauran gyaran jiki amma halawa sai ranar ƙarshe za ayi mata gudun kar jikin ta yaƙi karɓa garin amarya tayi kyau azo a samu matsala.
Saura kwana uku biki Akayi wa Suhaila Halawan ta jiki yayi kyau sosai ta fito amarya sakk.
Washe gari kuma suka je lallai shima haka aka yarfo mata shi yayi kyau sosai sai ta fito kamar wata balarabiya.
A ɓangaren kayan gyaran jikin amarya kuwa Ammi sam bata kula Suhaila ba sai Umman sheka ce(yayar Ammi) ta bata wasu magunguna da zuma da su gumba tace ta dinga shan su amma na infection sun fi yawa.
Itama Surayya ta bata sosai don ita take taya ta gyran jikin ma.
A ɓangaren shirye shirye kuwa Suhaila tace ita idan banda Kamu da walima babu wani event da za tayi, Surayya tayi tayi ayi dinner amma tace no.
Ana gobe kamu Surraya ta dawo gidan su Suhaila don shirya komai.
Zaune suke a ɗakin su Suhaila inda babu jama’a sosai suna tsara yadda abubuwa za su tafi ana kuma ware kayan da amarya zata yi amfani da su.
Ai kuwa nan Surayya taci karo da bra ɗin Suhaila, a hankali ta fara zarota cikin kayan tana ƙara kallon Suhaila sai da tazo daidai fuskar Suhaila sannan ta tsaya cak tana mata kallon meye wannan.
Itama kuwa Suhaila haɗe fuska tayi tana kallon Suryyan kafin cikin masifa ta fizge bra ɗin a hannun ta tana faɗin”Haba Sury meye haka? Ya zaki ɗakko mun kaya kina nunawa jama’a?
Galala Surayya tayi tana faɗin”Cabbbb don kayan lefan ki basu iso ba shine da kika je siyayya kika siyo wannan bra ɗin me kama da slippers?
Suhaila kuwa daɗa haɗe fuska tayi tace “Eh ita nake ra’ayi kar kuma ki ƙara mun magana idan ba haka ba za muyi faɗa wallahi”.