HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

“Caɓɓ wallahi sai dai muyi amma you are not wearing this thing, wannan ai ko ni da breast ɗina yayi rabin kanki bazan saka wannan ba ballantana ke da ko dunƙulin hannu na be kai ba. To wallahi you must wear a padded bra”.

Ta ƙarashe maganar tana wani cin magani kamar ba daga bakin ta maganar ta fito ba.

Suhaila kam ji tayi kamar zata nitse a gurin don akwai cousin sisters ɗin ta a gurin.

Cikin fushi tace”Hmmm wallahi am not wearing any padded things, or push up bra, ko ma dai me kuke ce musu be dame ni ba. Wa zanyi wa push up ɗin? Wai mutane? Cabbb sun daɗe basu ga slipper breast ɗina ba, badai shi wanda zai aure ni yace yaji ya gani ba, a haka yake so na ba, to ai shikenan “.

” Ke ni wallahi a dole zan sa wannan ɗin ma sai me?

Surayya kam ta zama speechless tana mamakin boɗaɗɗen hali irin na ƙawar tata.

Farida ce ta saka musu baki tana faɗin “Ki rabu da village yayar nan tawa duk wani abun gayu bata san shi ba, jiya ma inajin su suna yi da ya fatima amma tace ita Allahn bur baza ta sa ba”.

“Surayya ce ta matso kusa da ita tace” “To bari ki ji namiji sai da gyara yarinya”.

Ture ta Suhaila tayi tace”look he is my husband zan saka abunda yafi push up ma, ke idan da akwai push high ma zan saka,amma fa bazan sa ba don na burge can wata ƙatuwa ba”.

“Idan an gadama ma ace basu taɓa fitowa ba a gurin”.

Ƴan matan da suke gurin ne gaba ɗaya suka sa dariya suna faɗin Allah ya ja da ran ya Suhaila amaryar ya Habib in sha Allah.

Kallon su tayi ɗaya bayan ɗaya tace “Munafukai ku faɗi duk abunda zaku faɗa amma no going back”.

Surayya kam takaici ya hana ta magana.

******

*KAMU*

Tun daga nesa nake hango ƙyallin wata lufaya wanda ta kasance pitch sai kuma kwalliyar baƙi a jikin ta, sai ƙyallin golden wanda shine abunda ya fito da ainahin kyan lufayar da take sanye a jikin Suhaila. Ban kai ga ganin fuskarta ba saboda lulluɓin da ta sha, amma dai na samu damar ganin hannun ta zuwa ƙafar ta, henna ɗin ya fito sosai ya kuma ƙara kyau ga hanun nata ya sha wani agogo me tsadar gaske ɗayan kuma bangles ne guda biyi na gold, ƙafar ta kuma sanye take cikin wani arnen takalmi me kama da na gidan sarauta wanda kwalliyar shi ta kasance golden kalar takalmin kuma pitch ne.

Bridal mates na kalla naga suma sun fito cikin ankon doguwar riga wanda aka ɗinka da wani net me shegen tsada, sai dai fa kwalliyar ta burge ni don maroon da golden suka yi, sun yi kyau sosai don zan iya ce muku ma ni kalar su ta fin mun ta amayar kyau ko don color na ne.

Su Ammi na hango manyan mata an sha riga da skirt anyi mata make up ansha ɗauri ga lace ɗin ya ɗauki kalar ta sosai don coffe ne da kwalliyar light brown abunka da farar mace, itama umman sheka irin kayan Ammi ta saka sai suka fito kamar wasu ƴan biyu sun haɗu.

Amara ƙirjin biki kuwa kayan ta complete golden ne kuma ita kaɗai tayi kayan ta ta fita daban kuma tayi kyau sosai ba ƙarya.

Cikin hall ɗin aka ida shegar da amarya aka ajiye ta a mazaunin ta nan fa guri ya haɗe aka fara hidima sai da akayi hotuna sosai sannan aka samu aka zauna don cin abinci.

Inda abun nasu ya burge ni kamun nasu babu namiji ko ɗaya don ko Mubarak ban gani ba, har me ɗaukan hoto ma mace ce ba irin kamun da akeyi yanzu ba ka ango yayi wani ƙwam su kuma abokanan sa suna bin shi kamar wani jela.

Bayan anci an sha aka ƙara ɗaukan wasu hotunan,

Amarya kam tayi kyau don very light make up aka yi mata babu wani hayaniya.

Bayan antashi daga biki,
Suka fito bakin gurin a nan ma sai da aka ƙara wani bikin don duk mazan family ɗin sai da suka zo lokacin, a nan kuma aka sake sababbin pictures….

******

_*Tofa ko ya zata kaya a next page oho… Ba dai muji ɗuriyar ango ba kuma da alamun daga amarya har aminiyar ta babu wanda ya sanar da ango halin da ke ciki*_

*_wai shin readers baku ƙagu kuji abunda yake damun Suhaila bane? Naji baku tambaya ba.._* ????

*_Har yanzu be fara daɗi ba wollah ko farawa bamu yi ba, ku dai ku cigaba da bin alƙalamin Bintu Ahmad(ɗiyar Ahmad)_*

_*ma’asalam*_????????

*faɗma Ahmad*

 

*???????? AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*

page1️⃣0️⃣to1️⃣1️⃣
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*

*~We are bearer’s of so golden pen????~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen????,savour our words, for it will cause you no pain.~*

Addu’ar Neman Biyan Bashi

اللّهُمَّ اكْفِنِي بِحَلالِكَ عَنْ حَرَامِكَ، وَأَغْنِنِي بِفَضْلِكِ عَمَّنْ سِوَاكَ.
Allahummak-finee bihalalika ‘an haramik, wa-aghninee bifadlika ‘amman siwak.

Ya Allah! Ka wadatar da ni da abin da Ka halatta barin abin da Ka haramta, kuma Ka wadatar da ni da falalarka ga barin waninka.

اللّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْهَمِّ وَالْحُزْنِ، وَالعَجْزِ وَالْكَسَلِ وَالْبُخْلِ وَالْجُبْنِ، وَضَلْعِ الدَّيْنِ وَغَلَبَةِ الرِّجَالِ.
Allahumma innee a’oothu bika minal-hammi walhuzn, wal’ajzi walkasal, walbukhl, waljubn, wadal’id-dayni waghalabatir-rijal.
Ya Allah! Ina neman tsarinka daga kunci, da bakin ciki, da kasawa, da lalaci, da rowa, da tsoro, da nauyin bashi, da rinjayen mazaje.

*NIKAH*

Washe gari ta kama juma’a da wuri dangin ango suka iso haɗe da kayan lefan su, da misalin goma zuwa sha ɗaya akayi walima.

Bayan an sakko sallar juma’a kuma aka ɗaura auren HABIB MANSUR da kuma SUHAILA MUHAMMAD akan sadaki naira dubu 100 cif.

Tun da aka ɗaura auren bakin Habib yaƙi rufuwa sai wage shi yake yadda kasan gonar auduga. Ita kuwa amarya SUHAILA tana can tana shan kuka kamar ranta zai fita don tunda aka gama walima shikenan fuskar ta, ta cakwaɓe da majina da hawaye anyi anyi tayi shiru amma kamar daɗa tunzurata suke yi.

Dangin ango kuwa sun dage a ƙarfe 3:00 nan za su wuce da amarya zuwa kaduna babu yadda su umman sheka basu yi ba akan a bari sai washe gari amma ina angwayen nan suka shafawa fuskar su hudar rashin kunya suka ce ina ai su a ranar za a basu amarya.hakan ce kuwa ta faru nan da nan aka fara shirya SUHAILA ita kuwa kuka take kamar ranta zai fita har da shashheka.

Bayan an gama shirya ta tsafff aka kawo ta wajen Ammi don suyi sallama amma buɗar bakin ta sai cewa tayi”Babu abunda zan ce miki sai da Allah ya kaiki lafiya ya kuma baki haƙurin zama da abunda kika aura, tashi ki tafi Allah ya miki albarka “.

Duk cikin kalaman Ammi Allah ya miki albarkan nan ne kaɗai ya ɗan sa zuciyar Suhailn ta ɗan yi sanyi amma kuma duk da haka ji take kamar tace ta fasa auren, gashi wani sabon yanayi take ji a jikin ta, ji take kamar idan ta tafi wani abu zai same ta.

Umman sheka tayi mata faɗa sosai da nasihohi da kuma jan kunne kafin ta fara sallama da sauran mutane.

Da gudu mubarak ya taho ya rungume ta itama rungume shi tayi tana kuka kamar ranta zai fita shi kuwa Mubarak ya kasa ce mata komai sai ƙwaƙumar ta yake ƙara yi.

Sai da aka ga dai basu da lokacin rabuwa kafin da ƙayar umman sheka ta ɓanɓare Mubarak a jikin Suhaila, ai nan take ya fasa wani uban ihu yana faɗin”Wayyo Allah ku dawo da ya Suhaila ta don girman Allah kar ku ɗauke mun ita, ina son ta ita kaɗaice take so na a gidan mu”.

Haka dai ya dinga ihu kamar wani ƙaramun yaro yana dirjewa wanda ina tunanin yayi shekara 17 har da ɗoriya amma shine yake sirfa wannan uban kukan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button