ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Suhaila kam da aka je bakin mota nan ta sake fasa wani kukan itama tana tirjewa kamar wata ƙaramar yarinya wai ita a dole sai tayi sallama da Abbun ta ai kuwa ba shiri aka nemo shi kusa..
Yana zuwa ya rungume ta yana faɗin”Mama na ai haƙuri za kiyi shi haka sha’anin aure yake, sai da haƙuri abun da zance miki kawai ki wa mijin ki biyayya, yi nayi bari na bari shine zai kawo miki ɗan sauƙi a zamantakewar ku. Sannna kuma banda yiwa miji rashin kunya, sannan kuma kina kusa da ƴar uwar ki duk wani abu da yake damun ki kafin ki sanar da mu ki fara sanar da ita kinji, Allah ya miki albarka ya kuma kawo haske cikin rayuwar ki”.
Haka nan Abbu ya sa ta cikin mota nan aka shirya wainda za a tafi da su, suka ɗau hanyar zuwa kaduna…..
******
Bayan sun isa sai da aka fara kai amarya gurin maman Habib ta ganta ta sa musu albarka kafin aka kaita gidan ta da yake unguwar hayin ɗan mani.
Gida ne ɗan madaidai ci me kyau sosai safe contain ne, 2 bed room ne sai one palo sai kuma dining ɗin da yake cikin palo, a cikin ko wani bed room kuma akwai toilet sai toilet guda ɗaya a waje. Abbu kam yayi ƙoƙari sosai don ko ina na gidan sai da Abbu ya cika shi da kayan more rayuwa na zamani.
Su Surayya kuwa tunda suka isa gidan take zolayar Suhaila tana mata waƙar ta zama zama ɗakko riga ta zama ɗakko wando,su farida na mata amshi da sauran cousins ɗin su.
Farida ce ta buɗe fuskar ta ta fara mata waƙar”Ke kika ce kina so da baki ce kina so ba da ba a baki shi ba”.
Ita kuwa Suhaila sai ƙara volume ɗin kukan ta take yi. Suna nan suna tsokanar ta while su kuma manyan matan suna ƙara gyara gidan.
*****
Washe gari da safe bayan su Surayya sun yi breakfast suka fara shirin tafiya, don ishaq ya ja mata kunnanen kar ta sake tace za tayi wani yawo a dangi idan su ka gama harkar kai amarya ta biyo motar angwaye kawai ta dawo da ita.
Hakan kuwa akayi bata je ko ina ba aka fara shiri da ita.
Bayam sun gama shiryawa ta sa Suhailan tayi wanka aka kunna wa gidan turare, an share shi yayi tsaf. Zama tayi kusa da SUHAILA tana riƙo hannun ta domin bata shawarwari”Suhaila yau dai gaki na kawo ki gidan yaya Habib, shi mutum me haƙuri amma fa idan kika taɓo shi bashi da sauƙin hali, sannan kuma yana da mita gaskiya sai kici maganin zama da shi, abu kuma na ƙarshe sai kin kama shi hannun biyu biyu kin zama ƙaramar karuwa a gidan ki saboda idon mata akan shi yake sannan kuma ki dage da addu’a kinji ko, zai kula da ke zai baki duk wani abu da kike buƙata ni zan tafi ki kula da kanki don Allah zamu yi waya idan mun isa gida lafiya”.
Tashi tayi tana shirin cire hannun ta a cikin nata amma taji Suhailan ta riƙe hannun nata gam. Komawa tayi ta zauna ta dafa kafaɗar Suhaila ta ce “Me kuma ya faru? Sai addu’a kawai Suhaila da kuma zaman haƙuri don shi aure ɗan haƙuri ne”.
Suhaila na share hawayen fuskar ta da tayi shaɓeɓe da hawaye tace”Ba wannan ba am just scared, kin san bamu sanar da Habib matsala ta ba”.
A hankali ta murza hannun Suhailan tace “Haba mana karki zama raguwa, be positive mana thinks will be okkk, be side duk abunda mu kayi na san ba zai tafi a banza ba, he will understand kuma ba wannan ne dalilin da yasa ya aure ki ba ballantana idan yaga babu shi ya damu”.
Ita dai Suhaila bata gamsu da maganar Surayyan ba amma ya za tayi tunda aikin gama ya gama.
Suna kuka haka suka rabu ita da Farida babu yadda suka iya. Sai da Umman sheka ta ƙara mata nasiha sosai kafin suka kama hanyar komawa garin kano.
******
Haka Suhaila ta gama kukan ta ita kaɗai a gidan kamar mayya ganin dai babu sarki sai Allah yasa ta kama kanta, da lokacin sallar azhar yayi tayi sallar ta.
Har bayan la’asar babu ƙeyar ango, ta gaji da zama ta kira Abbun ta don su gaisa.
_Ni kuwa nace tofa yau na yarda da aka ce wasu sunfi son iyayen su maza akan mata. Yo to soyyaya mana idan ba haka ba in wata ce ai maman ta zata kira_.
A bugu na ukku Abbu ya ɗau wayar “Hello Mama na ya kike?
Suhaila kuwa har ƙwalla ta cika mata ido jin muryar Abbun nata domin kuwa tayi missing ɗin shi sosai da sosai.
Jin muryar ta tayi rauni yasa yace” Kul, kina mun kuka zan kashe waya ta”.
Ai kuwa nan da nan ta haɗiye kukan tace”Abbu nayi shiru, Abbu su Farida sun taho sun barni ni kaɗai”.
“Na sani Mama na har sun iso gida ma ɗazu. Sai haƙuri. Amma me yasa Fatima bata zauna da ke ba?
” Ka san Nihla bata da lafiya shine suka tafi asibiti shiyasa bata zauna ba”.
“To Allah ya ƙara sauƙi ai zata dinga duba ki kar ki damu.
******
Ango be shigo gida ba sai wajen 8:00 bayan anyi sallar Isha’i su Mustapha suka rako shi suna tsokanar shi, suna zuwa dai dai bakin gate ɗin yace” Wallahi baku isa ba daga nan zaku tsaya na gode sosai, Allah ya tashe mu lafiya ya faɗa yana tokare Mustapha da yake shirin biyo sa.
Bayan Mustapha ya koma babu yadda ya iya don har ya shiga gidan ya kara ƙofar zuwa rabin jikin shi.
“Shege sai wani rawar ƙafa kake wai kai zaka ci amarci ko, kai da ka ɗakko ustaziya ƙila ma babu abunda ta iya”.
“Eh naji dai ku tafi, ku dai kuyi ta fama da na titi ni kuwa na kama dahir, ko bata iya ba ma zan koya mata meye a ciki”.
Ya faɗa yana ƙarasa rufe ƙofar.
Suhaila na kan prayer mat taji shi yana rufe ƙofa, nan da nan gaban ta ya yanke ya faɗi, da sauri ta juyawa ƙofa baya ta kwanta kamar bacci ya kwashe ta.
Bayan ya rufe ƙofa ya shigo cikin palon, sai da ya biya ta kitchen ya ɗakko musu plate da cups sannan ya kashe wutar palon ya haɗa da ta dining area kafin yayi sallama cikin ɗakin.
A lokaci ɗaya fargaba da tsoro suka shigi Suhaila, ga kuma zaƙin muryar shi da ya yi amfani da ita ya ƙara sakar mata da jikin ta, ga ƙamshin turaren sa da ya daɗa dagula mata lissafi.
Shi kuwa tunda yayi sallama ya coge a bakin ƙofa yana kallon ta, yana jin wani sonta yana ƙara shiga cikin ranshi.
A hankali ya fara takowa cikin ɗakin yana zuwa ya ajiye kayan hannun shi kafin ya zauna kusa da ita yana tanƙwashe ƙafar shi.
Cikin muryar shi me daɗin sauraro yace”Na san ba bacci kike ba ki tashi kawai don yau duk wata kunyar ki sau na cire miki ita.
A hankali ta fara buɗe idonta kafin ta tashi ta zauna, da ƙyar ta iya cewa sannu da zuwa muryar ta na rawa.
Basarwa yayi kawai yayi ya tashi ya cire babbar rigar jikin ya cire takalmun shi kafin ya janyo plate ɗin ya juye namomin da ya shigo da su don a ƙalla sunyi kala biyar.
Cikin halin ko in kula ya fara cin abun shi yana mata bismillahi.
“Kizo kici abunci plsss”.
Jikin ta a sanyaye ta matsa tasa hannu tana tsakurar naman.
Ganin ba ci za tayi ba yasa ya yago naman yace”Buɗe bakin. ”
Ai kuwa babu shiri ta buɗe ya tura mata ƙaton nana a bakin ta, haka yayi ta bata har sai da yaga alamar ta ƙoshi da gaske.
Lemo ya zuba mata a kofi ta sha, sannan ya tattara kayan zuwa gefe guda, drawer ya buɗe ya ɗakko towel da jallabiyyar shi ya shige toilet, wanka yayi kafin ya fito har ta kwashe kayan ta kai su kitchen.
Kallon ta kawai yayi yana mamakin kunya irin tata.
“Ki tashi kiyi wanka kema ko kinji daɗin jikin ki kema”.
Da sauri ta ɗago ta kalle shi don bata san ma ya shigo cikin ɗakin ba.
Sunkuyar da kanta ta fara yi kafin tace”Bandaɗe da yi ba”.
“To kiyi Alwala” ya sake faɗa.
“Ina da ita” ta faɗa cikin sanyin muraya.