ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Be sake ce mata komai ba ya gyara musu abun sallar ya miƙa mata hijabin ta yace”Tashi muyi sallah”.
Ba musu ta karɓa ta saka nan ya jasu suka yi sallah raka’a biyu.
Bayan sun idar ya juyo ya dafa kanta yayi mata addu’a kamar haka” *Allahuma inni as’aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha, wa a’auzibika min sharraha wa sharraha ma jabaltaha alaihi*.
Amin ta amsa masa da shi kafin ya ɗan mata tambayoyi wanda yasan indai ba wani ikon Allah ba yana da yaƙinnin duk zata amsa su.
Tashi yayi ya cire jallabiyar shi babu ruwan shi daga shi sai gajeron wando ya haye gado abunshi ita kuwa Suhaila tafi 15 minute a zaune akan daddumar ta kasa motsi samm.
Sai da ya gaji kafin yace mata”Wai duk kunyarce haka? An fa ɗaura mana aure igiya uku ma kuwa amma shine kike mun wannan abun kamar wata bafulatana irin ta rigar nan”.
Ɗan tinzuro baki tayi tana faɗin”Aa ni ba ta riga bace ba wallahi”.
“A to ai abun su kike yi, kuma ko suma idan suka waye baza su yi abunda kike yi ba”.
Daurewa tayi ta tashi ta cire hijabin dake sanye a jikin ta, ta ninke shi gefe kafin ta buɗe durowa ta ɗakko wasu pyjamas ta shiga toilet ta sako su a jikin ta.
Bayan ta fito ta zauna a kan gadon can nesa da shi tana neman gurin kwanciya,ai kuwa ya janyo ta jikin yana placing kanta a ƙirjin shi kafin ya saki wani long sigh, ita kuwa ji tayi zuciyar ta ta buga dummmm kamar an buga mata wani ƙaton dutse saboda tsabar tsoro duk da ta san wannan ba lallai ya kai wancan ba.
Nan Habib ya zare hular kanta ya fara massaging gashin kanta da ya kwanta yayi baƙi sosai, a a lokacin ne na fara ganin gashin ta baƙi wuluk wanda ban taɓa ganin shi ba sai yau, ɗan madaidaici ne ita ba mara gashi ba sannan kuma baza a ce tana da gashi har gadon baya ba amma duk da haka zai kai kafadar ta.
Ƙoƙarin barin jikin shi tayi sai kuma naga ta fasa ku tunanin me tayi oho.
Shi kuwa nan fa ya ƙara samun dama yana kashe ƙishin ruwan sa, tun daga nan na tattara takalma na na bar wajen nace gobe da safe naji kadun zancen.
******
Da safe kuwa da na koma ɗakin abunda nayi expecting gani bashi na gani ba dumin kuwa idan ka kalli fuskar angon nan sam babu wani annurin farin ciki gashi kuma ya shirya cikin kayan aiki shi da ya kama ta ya tsaya ya kula da ɓarnar da yayi a daren jiya.
Ita kuwa Suhaila a gefe na hango ta tana ta kuka kamar ranta zai fita, shi kuwa ko a gefen slipper nashi.
Fita yazo yi naga ta tare mai hanya tana faɗin”Don Allah Habib ka tsaya ka saurare ni, i have been trying to tell you amma kaƙi bani dama, ko da yaushe cikin tunani nake, haka ma Surayya tayi yunƙurin faɗa maka amma kaƙi sauraron ta kace a bari sai munyi aure ka sani, kuma dama abunda nake jiye mana kenan misunderstanding gashi kuma tun ba aje ko ina ba mun fara samu.
Wani wawan kallo ya watsa mata gaba ɗaya veins ɗin kanshi sun tashi idanun shi kuwa sun kaɗa sunyi ja babu wani anurin tausayi a fuskar shi, ga wani ɗaci ɗaci da yake taso mai a can ƙasan zuciyar shi.
“Kinga ki shirya kawai ki tafi camping ki bar maganar nan Suhaila kin riga da kin cuceni kin gama da rayuwa ta, kin zubar mun da mutunci kin kuma rufe ni, yanzu ace har Abbu ya kasa sanar da ƴan uwa na wannan lamarin, sai da kuka cuce ni sannan zaki zo kina bani haƙuri”.
Runtse ido tayi tana jin yadda maganganun shi suke ratsa ɓargwan jikin ta, ga ɗacin maganar da ya faɗa wanda yayi referring ɗin ta zuwa ga Abbun ta.
Bata gama jimamin abunda ya faɗa mata ba ya sake cewa”Kinje kin gama yawan iskancin ki a duniya sannan zaki zo ki rufe ni, dama duk ustazan nan haka kuke, sai kuyi ta ɓoye fuska a zuwan mutanen kirki, ina ashe abun ba haka yake ba, ba abunda ba a gaya mun ba a kan ki amma naƙi ji, yanzu gashi gaskiya tayi halin ta”.
Jin ɗacin maganar da ya gaya mata yasa ta daka mai tsawa tare nuna shi da ɗan yatsa tace”Ni ban taɓa yawan banza ba kuma bazan taɓa ba har na koma ga mahallici na”.
Hawayen da yake zubo mata ta share kafin tace”I WAS RAPED BY 3 MEN A SHEKARU SHIDA DA SUKA WUCE, don haka don’t ever call me a prostitute”.
*****
_*Tofa yau ƙwan ya fashe*_
_*muje dai zuwa*_
_*Assalama alaikum*_
*faɗama Ahmad*✍️
*???????? AL’AMARIN SUHAILAT????????*
*Bintu Ahmad*
*Wattpad@cynosure3*
Page1️⃣2️⃣to1️⃣3️⃣
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*
*~We are bearer’s of so golden pen????~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen????,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Addu’a A Kan Abokan Gaba*
اَللَّهُمَّ مُنْزِلَ الْكِتَابِ، سَرِيعَ الْحِسَابِ، اهْزِمِ اْلأَحْزَابَ، اَللَّهُمَّ اهْزِمْهُمْ وَزَلْزِلَهُمْ.
Allahumma! Munzila-l-kitabi, sar’a-l-hisabi! Ihzimi-l-ahzaba. Allahumma ihzimhum wa alzihlum.
Ya Allah! Mai saukar da littafi, Mai gaggawan sakamako! Ka karya kungiyoyin abokan gaba. Ya Allah! Ka karya su, ka girgiza su.
*_EMBER????_*
Hawayen da yake zubo mata ta share kafin tace” I WAS RAPED BY 3 MEN A SHEKARU SHIDA DA SUKA WUCE, don haka don’t ever call me a prostitute!”.
Komawa tayi ta zauna a bakin gado tana cigaba da kuka, ji take Ina ma ace irin wannan ranar bata zo mata ba. Duk wani baƙin ciki da azaba, da hantara da kuma wariya a lokacin da abun ya faru da ita suka dawo mata sabo fil.
Shi kuwa ya tsaya a bakin ƙofa kamar wani gunki ya kasa motsawa kuma ya kasa ce mata komai.
Ganin dai alamar ba shi da niyyar neman ƙarin bayani yasa ta share hawayen fuskarta ta dawo bakin ƙofar inda yake tsaye ko motsawa be yi ba.
Hanun shi ta sa cikin nata tana me murza su alamar rarrashi, ɗayan hannun nata tasa ta shafo gefan kumatun shi kafin a hankali tafara tafiya da shi zuwa palo.
Shi kuwa sai binta yake kamar wani wawa, yayi wani sakato sai ka ce irin down syndrome ɗin nan.
Akan 2 sitter kujera tayi musu mazauni, bayan ta zauna tayi placing kanta a ƙirjin shi tana me cigaba da murza hannun wanda take jin daɗin sofness ɗin shi.
Cikin nutsuwa da kwantar da hankali ta fara magana”Am really sorry Albi na san munyi lefi duk kuwa da cewa nayi insisting amma kaƙi sauraro na, sannan kuma Abbu shima yayi nauyin baki da be sanar da su kawu Alhaji ba, kuma nasan shi tunanin da yayi na riga da na sanar da kai shiyasa har ka yarda zaka aure ni. Albi i was raped by arm robbers a shekaru shida da suka wuce, and then ban san dalilin su nayin hakan ba dumin kuwa ko kuɗi basu tambaya ba they just raped me and leave, kuma bayan ni babu wanda suka taɓa a gidan”.
*_”But then this is not the end of the story, wannan kawai kake da haƙƙin sani”. ta faɗa a cikin ranta_*
Ƙara gyara kwanciyar ta tayi tana daɗa shigewa jikin shi, shi kuwa gogan ko gezau be yi ba kuma babu wani abu da yaji ya sauya a can ƙasan zuciyar shi
Jin shirun yayi yawa yasa ta ɗago kai ta kalle shi, nan ta ga fuskar nan babu ko alamar tausayi ko kuma wani change of emotion.
Tashi tayi ta zauna, tafi 10 minutes tana kallon shi amma be ce mata komai.
Hannun ta takai zata ƙara shafar gefan kumatun shi ya riƙe hannun gam yana watsa mata wani kallo me kama da gargaɗi.
Yasar da hannun gefe yayi kafin ya tashi akan kujerar ya nuna ta da hannu yana faɗin”Kina tunanin wannan labarin ƙanzon kuregen da kika bani shi zai sa na yarda da ke? Never wallahi, you cheated me,kin gama da ni, kuma wallahi Allah ya isa tsakanina da ke, soyyayar da nayi miki da damuwar da na shiga saboda ke ban yafe ba”.