ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

“Kuma ki sani wallahi wallahi bazan bar wannan maganar a iya tsakanin mu ba ki jirayi abunda zai faru”. Ya ƙarashe maganar yana ɗaukan keys din motar shi.
Da gudu taje ta sha gaban shi harda su tsugunawa tana bashi haƙuri amma ina be ko saurare taba daga ƙarshe ma haɓar ta ya kama ya matse mata baki kafin ya hanƙaɗa ta gefe har sai da ta bugu da dining area ɗin da ya ƙawatu da flowers masu shegen kyau da sheƙi, ai kuwa nan komai ya kama gaban shi, flower verses ɗin gurin duk suka fashe tartsatsin kwalba ya fasa mata ƙafa ga kuma bakin ta shima da ya fara futur da jini saboda tsabar matsar da ya sha.
Ko kallon inda take be ƙara yi ba ya fice acikin gidan.
_*Ni kuwa nace ohhhh namiji kenan duk ina su I love you ɗin take? you are my life, can’t leave without you, you are my happiness, idan babu ke bazan iya rayuwa ba, na ƙagu mu kasance tare,duk suna ina? Kenan duk ƙarya ne? Virginity ɗin ta kawai yake yi wa? Ohhh maza kenan sai dai Allah yasa mu dace*_
Ita kuwa SUHAILA bewar Allah abun tausayi da ƙyar ta samu taja ƙafar ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun dining ɗin, tana kuka tana cire kwalbar da ta shegar mata ƙafa ga bakin ta da taji yayi mata wani sumtum alamar har ya kumbura.
Bayan ta cire kwalbar ta samu taja ƙafar ta zuwa cikin bedroom ɗin, babu inda bata duba ba amma bata samu first aid box ba, haka nan ta samu ta ƙara jan ƙafar ta zuwa toilet, shiga tayi ta kunna tap na ruwan zafi nan ta ɗakko towel ta gasa gurin ciwon tana yi tana kuka abun tausayi.
Bayan ta gama ta samu ta sake sabon wanka ta ɗan gasa jikin ta, duk da ita ba virgin bace amma duk da haka akwai gajiya, tunda mara kunyan sai da ya gama biyan buƙatar sa sannan ya wani fara ɗaga kai yana wani haɗe rai kamar be ji daɗin shi ba????.
Bayan ta fito daga toilet ɗin taga wani man zafi akan dressing mirror nan ta ɗauka tayi amfani da shi ta shafa a gurin ciwon. Kallon kanta ta tsaya yi a gaban dressing mirror tana tuno kalaman Ammi.
Wasu hawaye masu zafi ne suka wanke mata fuskar ta nan ta fara tunin wannan shine jeki kin gani ɗin da Ammi ta faɗa mata? me yasa ma bata bi shawarar Ammin nata ba ta yanke wannan hukuncin.
Nan da nan taji wani mugun zazzaɓi ya rufar mata ga wani azzababben ciwon kai da ya saukar mata duk a lokaci ɗaya.
Komawa tayi ta kwanta akan gado tana ƙara tuno maganar Ammi _*” Ba dai namiji bane kije zaki gani”*_
Wannan shine halin namijin kenan? yanzu da abunda Habib zai saka mata kenan? yau kwanan ta ɗaya tak amma har ya haɗa mata jini da majina to yanzu wa ma zata kira Abbun ta ko kuna Aminiyar ta don ko tana shan giya ne baza ta sanar da Ammi ba. Ya Fatima ce ta faɗo mata a arai har ta juya zata kira ta sai kuma tayi tunanin ko ya halin da Nihla take ciki oho, amma duk da haka bata fasa kiran nata ba ko jikin Nihla taji.
Da ƙyar ta miƙa hannun ta ta ɗakko wayar da take kan bed side ta danna kiran yayar tata, ai kuwa a bugu na uku ta ɗauka “Amaryar Habib ba kya lefi”.shine abunda Fatima ta fara faɗa.
Suhaila kuwa sai da idon ta ya ciko da hawaye, da ƙyar ta samu ta mayar da su kafin ta fara magana”Kai oum Nihla, ya jikin baby na?”
“Jikin ta Alhamdullilah taji sauƙi. Yanzu fa nake cewa zan kira ki, ko zuwa anjima daddare ne sai na shigo na duba ya kika tashi”.
Suhaila kam bata san sanda tayi saurin cewa”Aaa karki damu we are good ki bari sai zuwa jibi, ki kula da baby na kawai”.
Fatima kuwa shiru tayi domin kuwa tana gane duk wani yanayi da ƙanwar ta zata kasance a ciki ko da kuwa a waya ne, nan take kuma AL’AMARIN SUHAILAT ɗin ya faɗo mata arai, sai da ta bar kusa da inda Abbu Nihla yake kafin ta fara magana a hankali”Suhaila is everything fine? Yace miki wani abu ne? A wani hali kike yanzu?”
Sai da ta lumshe idon ta hawayen da suke kwance a ciki tuntuni suka biyu saman kuncin ta, saurin tare su tayi da bayan hannun ta tana ƙara saisaita muryar ta.
” Ya Fatima am good, babu abunda ya faru, in sha Allah komai zai yi daidai”.
Ita kuwa Fatima har ranta ya fara ɓaci cikin masifa tace”Abeg malama talk, which kind komai zai yi dai dai, just tell me what is going on there!?”.
Tuni kukan da SUHAILA take riƙewa ya fashe da kanshi ba tare da ta shirya ba, kuka kawai take yi bata iya cewa komai ba daga ƙarshe ma kashe wayar tayi ta sulale a gurin tana sakin wani kukan me cin zuciya.
*******
A ɓangaren goga Habib kuwa yana fita daga gidan ya shige cikin motar shi yayi mata key ya bar ƙofar gidan a million.
Kasuwa ya nufa direct, beyi landing a ko ina ba sai a shagon Mustapha yana shiga ya hango shi a cen ƙarshen shagon yana zaune, daga baki baki kuma yaran shagon suna ta hidima da costomers.
Be wani tsaya ɓata lokaci ba ya nufi inda ya hango Aminin nashi a zaune da alama ma lissafi yake yi.shi kuwa Mustapha yana ɗago kai ya ganshi yana doso shi kamar zai tashi sama, mamaki kwance kan fuskar shi yake kallon aminin angon na shi wanda kamata yayi ace a wannan lokacin yana can yana shan amarcin shi.
Yana ƙarasawa ya jefa mai mukkulin motar shi, ya cire hular da take kanshi ya fara fifita fuskar shi da ita ya wani kama ƙugu sai cika yake yana batsewa, ga wani kumburi da yake kamar kwaɓin fankaso.
Shi kuwa Mustapha dariya yayi yana faɗin”Haba angon SUHAILA, me ya fito da kai daga gida ballantana har wani ya samu damar ɓata maka rai a cikin kasuwar nan?
Ko kallon inda yake bai yi ba ya samu guri ya zauna yana cillar da hular hannun shi.
Mustapha ne ya ƙara cewa”Haba angon Suhaila wai me ya faru ne?”
Wani kallon gargaɗi Habib ya watsawa Aminin nashi, haɗe rai yayi, ya haɗai girar sama da ƙasa.
Shi kuwa Mustapha tun daga nan be ƙara mishi magana ba.
Sai da ya gaji don kanshi kafin ya jefo magana kamar ba shi yayi ba” Yarinyar nan ta cuce ni, ta gama da rayuwa ta, ta munafurce ni Mustapha”.
Takardun da suke hannun shi ya ajiye kafin ya dafa kafaɗar abokin nashi yana tambayar wacce yarinya yake nufi kenan.
Kuka ya sa mai kamar wani ƙaramin yaro.
“Wacce yarinyar nake nufi idan ba Suhaila ba”.
“To me kuma tayi maka daga yin auren ku jiya jiyan nan? “.
“Mustapha yarinyar nan she is not a virgin”.
“What!!!??”
“Ka ga abunda nake fada maka akan ustazan nan ko, ka gani ko, babu yadda banyi da kai ba amma kace mun kai ka ga matar aure. Hmmm habawa da walakin goro a miya, to yanzu wani mataki ka ɗauka? “.
“But then cewa tayi wai she was raped ba abunda nake tunani bane”.
“And so? Ka yarda kenan ko?
” A’a zanyi magana da hajiya tukunna naji me zata ce, na rasa yadda zanyi wallahi, gashi naji mata ciwo kafin na fito shine abunda yafi damu na ma wallahi”.
“Wait a minute, amma dai ba dukan musu ƴa kayi ba ko? don koma menene bazan guyi bayan ka dake ta ba idan ka san baza ka iya zama da ita ba kawai ka sake ta”.
Da sauri ya ɗago kai ya kalli Mustapha”Yace saki fa! yaushe akayi auren da zan sake ta”.
“Da dai ka cigaba da dukan ta gwara kawai ka sake ta wallahi”.
Wani long sigh ya sauke kafin yace”Sai nayi shawara da hajiya gaskiya, bari naje na dawo”.
Ya ɗauki key ɗin sa da yake jikin Mustaphan.
*****
Hajiyan Habib tayi mamakin ganin shi da wannan safiyar a matsayin shi na ango, nan ya gaishe ta cikin girmamawa yana mai sauke kansa ƙasa kamar mutumin kirki.
Be wani tsaya ɓata lokaci ba ya kwashe kaff abunda ya faru tsakanin shi da Suhaila tun kafin suyi aure.