HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Hajiyan kam ta jinjina abun sosai ta ma rasa me zata ce mai, shin bayan shi zata bi ko kuma bayan su SUHAILA.

Saida tayi gyaran murya kafin ta fara magana”To Habib ni na ma rasa abunda zan ce maka, na farko dai lefin ka ne saboda yaran nan sunyi sunyi su sanar da kai amma kaƙi basu dama ka tsaya kana shirme, abu na biyu kuma shima baban Suhaila yayi kuskure kama ta yayi ace da su kawun ka suka je ya sanar da su halin da ɗiyar sa take ciki koda kuwa ita ɗin ta sanar da kai wannan haƙin sa ne, ka ga matsalar auren wanda ka sani kenan, kuma mutane munayin kuskure be kamata ace wai don ka san mutum ko kuma don wani ɗan uwanka ya san shi ace ba za ayi bincike ba, ina tabbatar maka da me cewar idan da an tsanan ta bincike da duk wannan abun sai ya fito,dumin kuwa na san duk yadda suka kai ga ɓoye wannan zancen sai wani yaji, abu na uku kuma ina da tabbacin labarin da Suhaila ta sanar da kai ba ƙarya take maka ba, amma zaɓi ya rage naka idan ka ga zaka iya cigaba da zama da ita to don ba zai yiwu kazo ka sa musu yarinya a gaba ka dinga jiɓɗar ta ba, sai ka tsaya ka nutsu kayi tunani ka yanke hukunci saboda bani zan zauna maka da ita ba, sannan ka tashi ka wuce gida kaje ka kula da ita mara tausayi kawai.Ai ku maza sai dai fatan Allah ya shirya ku, wato saboda budurcin ta ka aure ta?

Sai da ya tunzuru baki gaba kafin yace “A’a bafa haka bane hajiya”.

“A to, yaya ne? Ganar da ni, idan ba haka ba meye na tayar da hankali baza ka ɗau ƙaddara ba”.

“Ba komai Hajiya bari na tafi”.

“Hmmm Allah ya kiyaye hanya nidai bazan takura maka ba don bani na gano maka ita ba amma Suhaila tana da hankali.Tashi ka tafi Allah ya kiyaye hanya”.

Bayan Habib ya bar gidan Hajiyan shi gida ya wuce direct…

*****

A ɓangaren Suhaila kuwa bayan ta katse wayar kuka tayi sosai har sai da ta fara bawa kanta tausayi. Cikin ranta take ayyana “Shiyasa nake jin kasala, shiyasa nake jin kamar wani abu zai faru da ni ashe wannan babban AL’AMARIN ne zai faru da ni, ya rabbi ka kawo mun ɗauki ya Allah ka san da ni, ya Allah kamar yadda ka jarabce ni ka bani ikon cin wannan jarabawa.

Tafi 30 minute a gurin tana zaune ba tare da tasan lokaci ya tafi haka ba sai ji tayi ana buga ƙofa.

Gabanta ne ya yanke ya faɗi dumin kuwa a tunanin ta Habib ne ya dawo.

Jikin ta na rawa ga zafin da ƙafarta take yi mata, haka nan ta ja ta har zuwa bakin ƙofa. Cikin faɗuwar gaba tace”Waye?”.

Fatima da take tsaye a bakin ƙofa gaba ɗaya hankalin ta ya tashi tace” Nice Suhaila buɗe mun ƙofa mana”.

Ai kam bata san sanda hannun ta ya ƙarasa jikin lock din ƙofar ba nan da nan ta buɗe mata ƙofa.

Fatima kam mutuwar tsaye tayi ganin yadda ƴar uwar tata ta sauya kamanni daga jiya zuwa yau.

Ita kuwa Suhaila da gudu da faɗa jikin Fatima tana sakin wani sabon kukan, ita kam daga wayewar gari zuwa yanzu bata san iya yawan hawayen da ta zubar ba.

Cikin shock ɗin da ta shigeta itama ta rungume ƴar uwar tata tana me shafa bayan ta alamar rarrashi.

Bata ce mata komai ba ta kamo hannun ta suka shigo cikin palon.

Kallon dining arean tayi taga yadda komai yayi kwatsakwatsa.

Kallon ta ta sake mayarwa kan Suhaila taga yadda bakin ta ya kumbura ga kuma wani ciwon tana sake gani a ƙafar ta.

Hawaye ne suka wanke mata fuska, wani mugun tausayin ƴar uwar tata ya taso mata.Cikin sanyin murya tace”Suhaila dukan ki Habib yayi?

Bata samu damar yi mata magana ba sai kai da take girgiza mata kamar wata ƙadangaruwa.

Ita kam Fatima da ta ƙule ganin Suhailan bata da niyyar mata magana yasa ta daka mata tsawa”Wai ba magana nake miki ba! Meye hakan?Open your mouth and talk to me malama!”.

Jikin ta na ɓari tace “Yesss Ya fatima duka na yayi”…………

*_How far????_*

*_We meet tomorrow insha Allah_*

*_Ma’asalam_*????????

*Faɗma Ahmad*✍️

 

????????AL’AMARIN SUHAILAT????????

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*

*page1️⃣4️⃣to1️⃣5️⃣

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*

*~We are bearer’s of so golden pen????~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen????,savour our words, for it will cause you no pain.~*

 

Addu’a A Kan Abokan Gaba

اَللَّهُمَّ مُنْزِلَ الْكِتَابِ، سَرِيعَ الْحِسَابِ، اهْزِمِ اْلأَحْزَابَ، اَللَّهُمَّ اهْزِمْهُمْ وَزَلْزِلَهُمْ.

Allahumma! Munzila-l-kitabi, sar’a-l-hisabi! Ihzimi-l-ahzaba. Allahumma ihzimhum wa alzihlum.
Ya Allah! Mai saukar da littafi, Mai gaggawan sakamako! Ka karya kungiyoyin abokan gaba. Ya
Allah! Ka karya su, ka girgiza su.

 

*Mijin bahaushiya fans group, Al’amrin suhailat fans group, facebook commenter’s, aunty sumiee b, maryam a shahada. Inajin daɗin comment naku sosai. This page is dedicated to you people keep it up.*

 

_*The divorcee paper*_

Jikin ta na ɓari tace “Yess ya Fatima duka na yi”….

Ita kam Fatima ji tayi kamar an soka mata mashi a ƙahon zuciyar ta, me wannan mutumin yake nufi yau kwanan ƙanwar tata ɗaya rak a gidan nashi har ya fara dukan ta, for what reason? Saboda yasan sirrin kenan? Ina bazai taɓa yuwa ba iya wahalar da tasha a baya ma kaɗai ya ishe ta, kama ta yayi yanzu ace SUHAILAN ta huta da duk wata wahala da sha a baya, kamata yayi ace yanzun ne lokacin jin daɗin ta, amma ina taga hakan da wuya.

Kasa furta ko kalma ɗaya tayi saboda tsabar tausayin ƴar uwar tata, rungumota tayi zuwa jikin ta tana rarrashin ta, amma ina abun yaci tura dumin kuwa kamar tana ƙara tunzurata ne.

Suhaila kuwa da fuskarta ta kwaɓe da hawaye da majina tayi saurin raba jikin ta dana Fatima. Tashi tayi tsaye tana me saka duka hannayen ta akan fuskarta kafin ta fara magana”Ya Fatima wannan shine jeki kin gani da Ammi tace mun? Wannan shine halin namijin da tace mun indai shine gani gashi? Ya Fatima ki faɗa mun me nayiwa Ammi da bata so na, bata son ganina, bata son farinciki na, ummm don Allah ki faɗa mun wata ƙila ke kin sani”. Ta ƙarashe maganar tana dasa duka gwiwowin ta bisa carpet ɗin da yake shimfiɗe a ƙasan palon.

Da sauri Fatima ta ƙarasa inda take tana riƙo hannayen ta haɗe da girgiza mata kai alamar ba haka bane ta dena faɗan wai’annan maganganun.

“Suhaila ta ya uwa zata haifi ƴar da tayi tsahon wata tara a cikin ta sannan ta haife ta cikin labour me tsanin azaba, ta mata tarbiya, kice bata son ta ummm? Duk abunda kika ga Ammi tana yi ba wai don bata son mu bane, aa sai don wani ra’ayi nata na can, da kuma yanayin ɗabi’ar ta, kuma ai ba ke kaɗai take gwadawa halayen ta ba. Shi kuma Abbun mu yace me ummm?.

“Ya fatima nawa is worst then naki da Farida, is it because i was raped?

Ta faɗa tana kallon idon Fatima.

Fatima kuwa lumshe idon ta tayi tana ƙara jawo Suhailan jikin ta” Shhhh kar ki ƙara cewa komai kinji ko everything will be fine in sha Allah, and about Habib in sha Allah babu wanda zai ji abunda ya faru zamu shawo kan matsalar”.

Suna cikin haka suka jiyo motar Habib alamar ya dawo.

Suhaila kuwa duk da Fatima tana tare da ita sai da ƴan hanjin cikin ta suka kaɗa.

Ita kuwa Fatima babu abunda ya shafe ta jira take ya shigo ma taji menene hujjar sa na dakar mata ƴar uwa.

Habib kam tundaga bakin ƙofa jikin shi a sanyaye yake, kunyar shiga gidan ma yake saboda yasan koma menene Suhaila bata cancanci duka daga gare shi ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button