ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Hakanan dai yayi ƙarfin halin zaro keys ɗin shi a aljihu ya buɗe ƙofar gidan ya shiga yana tunanin a wani hali zai samu suhailan.
Yana shiga cikin palon ya hangosu rungume da juna nan fa wata kunya ta kama shi ganin Fatima ji yayi kamar ya nitse a gurin. Nan ya fara shafar ƙeyar munafurci yana gaishe ta, ko amsa gaisuwar tashi bata yi ba.
Miƙar da Suhailan tayi suka koma kan 2 sitter kujera suka zauna.
Shima cikin kunya da fargaba ya samu guri ya zauna sai wani tsilli tsilli da ido yake kamar kare a kwata.
Cikin jin kunya da dana sanin abunda yayi wa Suhailan yace”Sannu da zuwa ummu Nihla, kin zo lafiya?”.
Kallon mamaki kawai take mai sai kace wani mutumin kirki, a fuska baza ka taɓa cewa zai aikata abunda yayi ba kamar wani mutumin arziƙi.
Sai da Fatima ta haɗe fuska babu wani alamar wasa a fuskar ta kafin ta fara magana” Haba Habib yanzu abunda ka aikata ya dace kenan? Baka tausayin ta jiya jiyan nan fa aka kawo maka ita gidan nan amma kalli yadda ka canza mata kamanni kamar ba ita ba, haba ai ko ma menene sai ka kira ni ko kuma ka kira Abbun mu ko kuma ka sanarwa da manyan mu domin asan yadda za a warware matsalar, amma kawai sai ka kama dukan ta, a haka ne zata ji daɗin zama da kai? A haka ne zata girmama ka? A haka ne zata maka biyayya yadda kake so, bayan ka fara mata da duka. Gaskia banji daɗin abunda ka aikata mata ba sam, kalli fuskar ƴar uwata kamar ba tata ba.”Ta ƙarshe maganar tana ɗago haɓar Suhaila.
Ɗago ƙafar Suhailan ta ƙarayi tace” Kalli ƙafar ta har ta kumbura, jibi yadda kayi watsa watsa da gurin nan kamar ba jiya aka sake jera shi ba.”
Shiru ta ɗan yi na seconds tana controlling hawayen da suke zubo mata amma ina ta kasa ruƙe su, cikin kuka tace” Kasan irin wahalar rayuwar da ƙanwata ta ta shiga kuwa, kasan irin azabar da ƙuncin rayuwar da Suhaila ta shiga a shekarun baya,a tunani na wallahi yanzu lokacin hutawar ta ne da kuma jin daɗim rayuwa, amma ina abun ba haka yake ba gashi nan ranar ta ta farko wanda yanzu kamata yayi ace tana kitchen tana haɗa muku breakfast kuna jin daɗin kasancewa tare amma ina gata nan sai kuka take yi tana faɗan maganganun da basu dace ta faɗa ba, am sure babu abunda taci”.
“Habib bazan takura maka ba amma abunda nake so ka sani ƙanwata was raped ko ka yarda ko kar ka yarda she was.. Raped, don haka idan har kasan baza ka iya zama da ita ba, baza ka kyautata mata ba, baza ka ji tausayin ta ba, kuma baza ka dena ganin ta da tazo maka gida babu budurcinta ba, tofa ba dole, ka sawaƙe mata kawai, ka bar ta taji da ɗaya, domin bazai yiwu tana da damuwa kazo ka ƙara mata wata ba. Ai wallahi ni a tunani na ko don saboda Surayya kayi mata kara, yanzu kana tunanin idan Surayya taji abunda ka aikata zata ji daɗi, kullum abunda take cewa shine, shifa ba virginity ɗin ki yake so ba am sure ko da ba a sanar da shi ba ya sani later na san zai ɗau ƙaddara, to gashi tun ba aje ko ina ba kana neman ka watsa mata ƙasa a ido, yanzu idan taji me zaka faɗa mata ummm”.
Habib dai shiru yayi bece ƙala kanzil ba, shi kanshi yasan be dace ba abunda yayiwa Suhaila amma still zafin abunda yake ji a zuciyar shi be ragu ko ɗaya ba shi ya rasa ma mai zai ce, shin sakin Suhailan zai yi ya huta ne, aa ko zai cigaba da bawa kanshi tension ne, shima kan shi a halin yanzu ya yarda da cewar raping ɗin ta aka yi amma still yana jin kamar ba zai iya zama da ita ba.
A hankali ya ɗago kanshi da yake ƙasa tuntuni yana kallon keys ɗin hannun shi, cikin sanyi murya ya fara magana kamar wanda zai faɗin abun arziƙi”ummu Nihla kiyi haƙuri ana asifun jiddan, kuma in sha Allahu bazan ƙara aikata abunda na aikata a saifiyar yau ba, sannan kuma batun Suhaila kin san abun ba farar ɗaya zai wuce mun ba duba da sai jiya na san lamarin ina me roƙon alfarmar karki sanar da kowa wannan AL’AMARIN har sai na ga yadda zaman namu zai kasance, kuma in sha Allahu zan kula da ita Suhailan, yanzu zan kai ta asibiti don a duba ciwon ƙafar nata. ”
Ita kuwa Fatima shiru tayi tana jin maganar da yake faɗa daga ji bazai shika abun kirki ba.
Ba tayi ƙasa a gwiwa ba ta sake cewa” Habib idan har kasan kana kokwanto a zuciyar ka to kawai ka sawaƙe mata faƙat ba a dole”.
Ita kuwa Suhaila tana gefe tana jin su, ita yanzu abunda ya dame ta idan Habib ya sake ta ya zata yi da rayuwar ta, na farko dai zata sha wahala kafin ta samu wani mijin, shikenan ita ta zama victim sannan kuma ta zama bazawara, to wa zai ƙara auren ta kenan, a hakan ma da yaya ta samu tayi auren ballan tana kuma ta zama bazawara, gashi kuma ya Ya fatima sai zance saki take yi, babban tashin hankalin ta yanzu idan ta koma gida wani irin zama zata yi da Ammin nata don ta san ta shiga uku idan Ammi ta dinga yada mata magana sai taji kamar ta bar gidan har a bada, ina that will never happen.
Da sauri ta zabura tace”Ya Fatima ba komai tunda har yayi alƙawari me zai hana ki bari nan da zuwa wani ɗan lokacin, for now i can understand his feelings, with time in sha Allah komai zai wuce”.
Wani kallo Fatiman ta watsa mata sai kuma taji tausayin ƴar uwar tata domin kuwa har ta harsaso dalilin da yasa Suhailan ta faɗi hakan.
Ita kuwa Suhaila for his expression da yake nunawa a fuskar shi ta san ba wai ya yarda zai karɓe ta a hakan bane because she can read his mind a hakan da yake zaune, amma dai kawai abunda ta ajiye a ranta shine zata dinga kyautata mai tana kula da shi yadda yake buƙata har ya sakko komai yayi dai-dai.
_Ni kuwa nace bana jin hakan zata faru_.
Wani long sigh fatima ta sauke kafin tace”Well, sai mu gwada mu gani. Don Allah Habib ka kiyaye idan ba haka ba wallahi da kaina zan ɗauke ta kuma sai ka sake ta ko kana so ko baka so. Ke kuma ki tashi ki shiga ɗaki ki ɗakko hijab ɗin ki mu tafi asibitin.
Ai kuwa babu wani ɓata lokaci ta ɗakko hijabin ta ya kaisu asibiti nan akayi dressing ɗin gurin aka rubuta mata magunguna kafin suka ajiye Fatima a gida suma suka wuce nasu gidan…….
Wannan kenan…..
******
Hajiya Asiya ce zaune kan kujira tana shan tea yayin da kuma tayi zurfi sosai a tunani, da ka kalle ta kasan ba a cikin nutsuwar ta take ba, tunda garin Allah ya waye gabanta yake ta faɗuwa ta rasa meye dalili, sai daga baya can ta tuna ƴar tata nan da nan fa hankalin ta ya tashi ta fara tunanin anya kuwa wani abu be same ta ba, ko dai mijin nata da ya gane halin da take ciki ya tayar mata da hankali, tana ji a jikin ta tabbas Suhailan ba lafiyar ta lau ba, har ta ɗaga waya zata kira ta sai kuma ta fasa wai don kar Suhailan taga kamar ta damu da ita ta ajiye ta a ranta ne.
Tana nan zaune Farida ta fito daga ɗakin su domin ɗaukan breakfast ɗin ta nan take tmabayar ta ko sunyi waya da ƴar uwar tata.
“A’a Ammi bamu yi ba yanzu na tashi daga bacci kuma kin san amare, sai anjima zan kira ta”. Ta faɗa tana ƙarasa shigewa cikin kitchen ɗin..
“To uwar marasa kunya”. Ammin ta faɗa.
Ita kuwa Farida tana kitchen ko a gefan slipper nata ta cigaba da sabgarta kamar ma ba ita Ammin take wa magana ba.
Tana nan zaune a inda take Abbu ya fito daga ɗaki daga gani shima sai yanzu ya tashi daga barci wanda yanzu 12:00pm ta kusa bugawa kasancewar yau week end ne.
Ammi dai kasa haƙuri tayi sai da ta tambayi Abban su Suhailan ko yayi waya da ita.