HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

“Abbun su SUHAILA nace kayi waya da ƴar taka kuwa?

Guri ya samu ya zauna a kujera kafin yace” Eh munyi waya da ita amma tun jiya bayan tasowar su Farida”.

Taɓe baki tayi tace”Ummm daya ke kai kaine ai ta kira ka, amma ni ko flashing”.

Be ce mata ƙala ba sai ma bagarar da zancen da yayi da “Ina breakfast ɗina?”.

Ammi kuwa kawai dai ta jefo maganar ne amma ita kaɗai ta san me take ji a ranta jin kowa be yi waya da ita yau ba.

Bayan ta gama kawo mai breakfast ɗin ta shige ɗaki tana dialing no. Fatima.

Fatima tana cikin yiwa Nihla wanka tajiyo ƙarar wayar ta, sai da suka kammala sannan ta duba wa ya kira ta, sai da gaban ta ya buga ganin no. Ammin nasu.

Tana shirin ajiye wayar wani kiran ya sake shigowa, jikin ta a sanyaye ta ɗauka tana kara wayar a kunnen ta”Hello Ammin ina kwana”.

“Lafiya Fatima, ya Suhaila kuwa take kunyi waya yau?

Ji tayi gabanta ya buga dummm, hmmm habawa duk inda Ammi takai ga basar wa ai baza ta iya ba, ɗa fa, wanda ka haifa da cikin ka amma duk da haka Fatiman tayi mamaki, kenan hankalin ta ya kasa kwanciya? Tana ji a jikin ta wani Abu ya samu Suhaila. Cikin dakiya da nuna farin ciki tace”Laaaaa yanzun nan kinga ban fi 30 minute da dawowa daga gidan ta ba, lafiya lau sumul suke”.

Ɗan jimmmm Ammin tayi yaushe gari ya waye har ta shirya taje gidan mutane da safiyar Allahn nan kuma ma amare.

“Anya kuwa Fatima babu abunda kike ɓoye mun?

” Ba komai Ammi ki kira ta ma zaki ji ta lafiya lau”.

“To ai shikenan ki gaida Su Walid” ta katse wayar.

Ammi dai kawai tayi shiru ne amma ba wai don hankalin ta ya kwanta ba.

********

Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya inda Habib yana bawa Suhaila duk wani kulawa da take da buƙata tun daga kan harkar abinci ne da dai sauran su amma sai dai har yanzu mu’ammala ta aure bata ƙara shiga tsakanin su ba, itama kuma anata ɓangaren tana iya ƙoƙarin ta wajen ganin ta kyautata masa, don kafin ya tashi an haɗa mai ruwan wanka an haɗa mai breakfast da dai sauran su ga kuma lafuzuka masu daɗi, sai dai shi Habib ɗin har yanzu be yi freeing mind ɗin shi ba, ita kuma anata ɓangaren bata taɓa nuna mai cewar abunda yake mata naƙin ma’amalar aure ya dame ta ba. Satin ta ɗaya a gidan ta fara zuwa gurin Service ɗin ta kuma alhamdullilah yanzu ta rage damuwa sosai.

After 3 weeks…

A cikim sati ukun nan abubuwa da yawa sun faru inda Ammi da Suhaila sunyi waya yakai sau Bakwai, shi kuwa Abbun ta kusan kullum sai sunyi waya da shi.

Habib kam har yanzun bata canza zani ba yana dai ƙoƙarin kyautata mata amma har yanzu be sake da ita ba, ga kuma ziga da yake samu daga gurin abokin shi, na cewar idan ma bazai sake ta ba to ya ƙaro aure domin ya morewa abunda ya rasa a gurin matar tashi, shi kuma a ɓangaren Habib yasan ƙarya da ciwo mari da zafi ba zai iya zama da mata biyu ba a halin da yake ciki.

*******

Tsaye yake a gaban shower inda ya sake ta gaba ɗaya, da ƙarfita take tahowa tana dukan kan shi zuwa fuskar shi kafin ruwan ya gangara zuwa jikin shi, ga kuma ruwan da mugun sanyi domin kuwa be saka showern a tsakanin heat and cold ba ballantana ta bashi ruwa me ɗumi
akan blue color kan showern yake wanda yake nuni da ruwan sanyi yake amfani.

Yafi tsawon 30 minute yana wankan yayin da gaba ɗaya tunanin ya baibaye mai zuciya, shin abunda zai aikata daidai ne, shin takardar da ya rubuta jiya da misalin ƙarfe ɗaya na dare zai iya bawa matar tashi kuwa, kai anya Suhailan shi ta cancanci haka daga gare shi, duk kyautata mai da take yi amma ya rasa hukuncin da zai ɗauka sai wannan, wata zuciyar kuma sai ƙara tuno mai da shawarwarin da abokin shi yake bashi take.

Ɗifff ya kashe showern ya ɗora towel a ƙugun shi ya fito daga toilet ɗin ba tare da ya tsane jikin shi ba.

Yana fitowa ya shirya cikin maroon ɗin shadda wacce ta sha aiki da milk ɗin zare, turare ya fesa a jikin kafin ya janyo side drawer yana ɗakko takardar da ya rubuta, yafi 10 minute yana juya ta kafin ya fito daga ɗakin, yasan dai dole ya bayar da ita tunda ya riga da ya rubuta.

Yana fitowa yaji gidan gaba ɗaya ya baɗe da ƙamshin abincin da gimbiyar tashi take girkawa, a nan ma sai da zuciyar shi ta sake karyewa amma ina ya riga da yayi niyar bata takardar, bakin kitchen ɗin yaje ya tsaya yana kallon yadda take sauri cikin aikin nata daga gani saboda shi take yi.

Sanye take cikin dogowar riga ta bacci wanda ta kasance iyakar ta gwiwa, tayi parkinga gashin ta a tsakiyar kan ta , sai sauri take cikin aikin nata, ai kuwa tana juyowa suka yi two eyes da shi, tun daga sama har ƙasa yake kallon ta kamar wani maye ko me shirin yin wani abun arziƙi, itama shi take kallo saboda ya mata kyau sosai shaddar ta ɗau jikin shi tana son mijin nata ko sai yaushe ne zai sakko oho.

Langwaɓar da kai tayi tana mai irin abun shagwaɓar nan, da sauri ta ƙaraso inda yake ta bashi peak a gushin shi tana faɗin”Kai Albi duk saurin nan da nake yi sai da ka riga ni shiryawa? ka bani two minute zan jera komai a dining ta faɗa tana komawa cikin kitchen tana me fara haɗo kan kayan breakfast ɗin, guri ya samu ya zauna yana kallon yadda take komai cikin ƙorewa gashi sai wani nan take da shi kamar ta cinye shi, shi kuwa sai kallon ban kwana yake mata.

Bayan ta gama haɗa komai ta sa mai napkin a wuyan shi ta kawo na cinya ma ta sa mai gudun kar ya ɓata kwalliyar tashi.

Kafin ta koma ta zauna tace”Now we are good to go, bismillah”.

Babu kunya ba tsoran Allah ya fara cin abincin shi, sai da yaci ya ƙoshi har da ɗorawa da ruwa, kuma tunda suka fara be ce mata ko ci kanki ba.

Baya ta fara tattara kayan da suka yi amfani da shi ya zaro takardar daga aljihun shi, gaban shi yana dukan taratara don ta bashi tausayi sosai da sosai amma ba yadda ya iya tunda zai aikata son zuciyar shi.

Bayan ta dawo ta kwashi mugs wanda ya zama sune na ƙarshe ya miƙa mata takar dar, ita kuwa bata kawo komai ba ta haɗe mugs ɗin a hannu guda tana ƙoƙarin buɗe takardar haɗe da tambayar shi ko meye a cikin takardar, be amsa mata har ta ida buɗe takardar.

 

Abunda tayi tozali da shi a cikin takardar yasa ta saki mugs ɗin suka faɗi ƙasa ji kake tassss…

Abunda ta gani ba komai bane kuwa illa *”NI HABIB MANSUR NA SAKI MATATA SUHAILA MUHAMMAD SAKI BIYU, A DALILIN BAYAN AUREN MU NA GANO ITA BA CIKAKKIYAR BUDURWA BACE*”…………….

 

******

*share and drop a comments*

_*wayyo yau kam bani da magana*????????

_*Assalama alaikim uhhhhhhhh*_

*fadma Ahmad*

*????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*

*page1️⃣6️⃣to1️⃣7️⃣*

*✍✍ GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION ✍✍*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶????*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.*
*α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶????,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

Addu’ar Neman Biyan Bashi

اللّهُمَّ اكْفِنِي بِحَلالِكَ عَنْ حَرَامِكَ، وَأَغْنِنِي بِفَضْلِكِ عَمَّنْ سِوَاكَ.
Allahummak-finee bihalalika ‘an haramik, wa-aghninee bifadlika ‘amman siwak.

Ya Allah! Ka wadatar da ni da abin da Ka halatta barin abin da Ka haramta, kuma Ka wadatar da ni da falalarka ga barin waninka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button