ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Ta ƙarashe maganar kamar za tayi kuma.
“Kuma kin san lafazin Ammi, kuma wallahi indai haka zan yi aure ba tare da wanda zan aura yasan halin da nake ciki ba, to wallahi zan mutu banyi auren ba”.
“Hmmm Suhaila kenan, ba sai ya samu aikin ma baki yi auren ba, yanda kike wannan abun, amma kuma kina da gaskiya ko nima ina bayan ki wallahi, duk wanda zai aure ki dole yasan halin da kike ciki.
” Amma fa ya kamata ki san halin da kike ciki don 25 years old ba wasa bane.
” To wai Surayya so kike inje in janyo mazan su zo su aure ni, ko kuma so kike in fara tallan kaina ina ga matar aure ga me so”.
“Ga malam habu nan yana ta magana ana yonƙwana shi, ni dai wallahi idan kika ruɓe a gidan nan, dena zuwa zan yi eheee gwara ma ki sani”.
Ta faɗa tana tuntsurewa da dariya.
“Bana son wulaƙanci Sury, idan lokaci yayi zanyi in sha Allah”.
They both burst into laugh….
“Kinga ni kam bari na wuce gida zan yi girki kar habibi na ya dawo babu abun sawa a baki”.
Kallon Surayyan tayi with admiration tana cewa dama ita ma tana da auren, amma ta san lokaci ne yana yi za tayi.
” To shikenan ki gaida gida, kice ina gaishe da Abbu nu’aman..
” Hhh Allah ya amsa bakin ki, zai ji in sha Allah.”
“Gobe ni dai bazan shiga school ba, sai na zo zancen yadda zamu tsara convocation ɗin, muji yadda za ayi”.
“Okay sai kin zo, nima na san gobe ina shiga zan ƙarasa clearance ɗin, da wuri zan fita in sha Allah “……..
****
_*Ni kam wani abu ne yake damun Suhailat da yasa tace indai Ammin ta bata bari ta bayyanar dashi ga mijin da zata aura ba she is not getting married har abada…*_?
*_Who can guess it.._*?
_*Ya kuke gani, shin zaku so littafin kuwa…*_?
_*Ku biyo ni zuwa next page don jin alot of drama, we are just starting…*_
_*To mun haɗu da Ammi due bamu san other side nata ba. we are meeting Abbu next page in sha Allah, and it will be epic…*_ ????
*_Assalama alaikum_*
*Faɗma Ahmad✍️*
*???????? AL’AMARIN SUHAILAT????????*
*Bintu Ahmad*
*Wattpad@cynosure3*
Page2️⃣
*Day of typing 28-May-2020.*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*
*~We are bearer’s of so golden pen????~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen????,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Abinda Wanda Ya yi Mafarki mara kyau Zai Karanta.*
أَعُوذُ بِاللهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ ثَلاَثٍ مَرَّاتٍ.
a’uzu bi-l-lahi mina shaytani r-rajeem (3)
Wanda ya ga abu mummuna a mafarki, to sai ya yi wadannan abubuwan:-
– Ya yi tofi ta gefen hagunsa sau uku.
– Ya nemi tsarin Allah daga shaidan da kuma sharrin abin da ya gani, sau uku.
– Kada ya gaya wa kowa wannan mafarkin.
– Ya juya daga kwibin da ya kasance yana kwance a kansa.
Idan ya so, ya iya tashi ya yi sallah.
_*The preparations*_
Tunda Surayya ta fita take tunanin maganganun da suka tattauna, ita kanta tana so tayi auren amma abubuwan gidan nasu ne sai a hankali, sai addu’a kawai.
“Allah sarki Surayya kina son gani na cikin farin ciki, in sha Allah kwanan nan zanyi auren nima, very soon”.
Ta ƙarashe maganarta tana goge hawayen da ya zubo mata.
Kitchen ta shiga ta zuba tuwan shinkafa da miyar egusin da Ammi tayi ɗazu, kaɗan ta zuba saboda ita ba me cin abince bace sosai.
Bayan ta gama ta ɗakko wani littafin *Yasmeen Mughahid*,me suna LOVE AND HAPPINESS ta cigaba da karantawa tana yi tana jotting. Ni kam da naji ance love and happiness na zaci wani littafin soyyaya ne, ashe littafin kalamai ne masu daɗi na tsarkake zuciya da haƙuri da kuma juriyya kan tafarkin addinin musulunci.
****
Bayan tayi sallar la’asar ta nufi zuwa ɗakin Ammi, da sallama ta shiga ɗakin.
“Salamu alaikum”
“Walaikumsalam”
“Barka da yamma Ammi”.
“Barkan ki dai Suhaila, ya gajiyar makaranta?
” Alhamdullilah, dama cewa nayi gobe idan Allah ya kaimu zan kammala clearance ɗina”.
“Masha Allah, Allah ya kaimu da rai da lafiya”.
“Dama cewa nayi bari na tuna miki ranar monday ne fa convocation ɗin namu”.
“Aaaa wai har lokacin ya ƙarato haka, lallai kwanakin ba wuya sun ruske mu, masha Allah kice muna da biki”.
Kallon mamaki Suhaila tayiwa Ammin nata…
_”Hmmm wai muna da biki_” ta maimata maganar cikin ranta.
“Bari Abbun ku ya dawo sai mu tattauna zancen muji yadda za ayi ko?
“Eh haka ne Allah ya kaimu da rai da lafiya, amma fa Ammi ba sai kun takura kan ku ba, saboda ba wani abun biki bane, kawai dai za aje da ƴan uwa da abokan arziƙi ayi hotuna sai kuma abinci da zamu dafa”.
“To ƴar ƙa’ida, uztaziyar kawai, maƙogwaran liman, sai abunda na gadama za ayi, kina nufin ki kammala karatun degree kice baza muyi biki ba, ko ɗan memo da photo calendar ɗin nan ba za ayi ba, to ai kuwa abunda bazai yuwu ba kenan, ki zauna a gefe kawai ki sha kallo babu ruwan ki da mu yauwa, idan kuma baso kike mu fara raba abun faɗe acikin gidan nan ba “.
“A’a Ammi, in sha Allah ma hakan bazai faru ba, ba haka nake nufi ba, Allah ya huci zuciyar ki”.
“A to wai ma in hakan kike nufi.
“Me zamu dafa da daddare?
” Ba sai kun dafa komai ba, tuwo na har dare nayi shi”.
“Okay to shikenan Ammi bari na koma ɗaki ina da ɗan aikin da zan ƙarasa”.
“To Allah ya bada sa’a”.
Wani zubin duk abun Ammin
nata be fiya damun ta ba saboda tana musu addu’a ko da yauahe.
****
Bayan magrib, suna zaune ana ta hira sai ga Abbun su yayi sallama.
Kayan da yake hannun shi Suhaila ta karɓa tayi mai sannu da zuwa.
“Abbu ya hanya, ya kuma ɗalibai ?
” Alhamdullilah mama na muna ta fama kam, sai dai godiyar Allah. Ina Ammin taku take ne naga sai ku kaɗai a palon?
“Tana ciki, may be yanzu zata fito”.
“Mama na sai dai fa yau ban siyo inibin nan ba, nayi ta nema ban samu ba”.
Ya faɗa yana mayar da dariyar da ta taso mai.
Ɗan tinzuro baki tayi kafin ta ce”Na jiya fa da ka siyo kaɗan nasha wallahi, naje clearance kafin na dawo Mubarak ya shanye mun”.
“Ohhh Mama na har an canza fuska, da wasa nake miki na siyo amma sai dai bashi da yawa na yau ɗin don ƙaramar roba ne”.
“Ba komai Abbu hakan ma na gode sosai”.
“So now tell me ya clearance ɗin naku, amma dai kun gama komai ko?
” A’a ban ƙarasa ba Abba, na library ne kawai banyi ba kuma shima in sha Allah gobe zan kammala”.
“Abbu na san ma ka manta, ranar monday ne fa convocation ɗin namu”.
“Afff ai kuwa kinga na manta wallahi, Allah ya kaimu da dai da lafiya, abun ba wuya ga lokacin har ya zo, lallai su Suhaila an girma an zama psychologist burin ki dai ya cika”.
“To yanzu me ake shirya mana ne mama na?
” Ummm tau gashi nan dai Ammi tace zaku yi magana, duk ita zata tsara komai”.
Da sallama Ammi ta shigo cikin palon.
“Aaa Abban Suhaila yaushe ka shigo cikin gidan?
” Ban daɗe da shigowa ba, na tambaya ai suka ce kina ciki”.
“Ina ciki wallahi sannu da zuwa”.
“Yauwa, ya yaran? Ya kuma gidan? Da fatan kowa lafiya lau ko?
” Gamu nan duk Alhamdullilah muna cikin ƙoshin lafiya”.
*****
Fruit ɗin da ya shigo da shi aka juye a plate, nan Suhaila ta ɗauke grapes ɗin ta don ita bama kallon sauran kayan za tayi ba.
“Ohhh ya Suhaila har kin ɗauke zaki shige ɗaki ko, ko sammun baza kiyi ba”.
“Eh ɗin, a wanda ka sha ban baka ba ɗazu”.
Farida kam tana gefe sai faman danne danne take a laptop wanda ban san me take yi ba.