HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

اللّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْهَمِّ وَالْحُزْنِ، وَالعَجْزِ وَالْكَسَلِ وَالْبُخْلِ وَالْجُبْنِ، وَضَلْعِ الدَّيْنِ وَغَلَبَةِ الرِّجَالِ.
Allahumma innee a’oothu bika minal-hammi walhuzn, wal’ajzi walkasal, walbukhl, waljubn, wadal’id-dayni waghalabatir-rijal.
Ya Allah! Ina neman tsarinka daga kunci, da bakin ciki, da kasawa, da lalaci, da rowa, da tsoro, da nauyin bashi, da rinjayen mazaje.

 

*_HEART BREAK_*

Abunda ta gani ba komai bane kuwa illa *”NI HABIB MANSUR NA SAKI MATA TA SUHAILAT MUHAMMAD SAKI BIYU, A DALILIN BAYAN AUREN MU NA GANO ITA BA CIKAKKIYAR BUDURWA BACE”*…….

Suhaila kam ji tayi kamar an luma mata wuƙa a ciki, nan da nan jinta ya ɗauke, yawun bakin ta ya ƙafe, idanun ta kuwa kamar an zuba mata yaji domin wani raɗaɗi suke mata gashi nan da nan ta fara gani dusu dusu, babu ƙwalla ko a ɗaya a cikin idanun nata, tana daga tsaye inda take ta saki takardar hannun ta kafin ta faɗi daɓas, Allah ma ya tamaketa bata faɗi akan mugs ɗin da suka fashe ba.

Wani irin ihu ta fasa wanda ni da nake gurin sai da na girgiza tsabar tsoro, shi kuwa gogan yana tsaye kamar an dasa bishiya ko motsawa be yi ba amma fa sai dai akwai tsantsar tausayin ta a idon shi, ji yayi gaba ɗaya zuciyar shi ta karaya kamar shima ya fasa ihun irin nata, ganin ba zai iya jurewa ba yasa ya juya mata baya yana me runtse idanun shi da suka kaɗa suka yi jazur. A hakali ya fara furta”Am really sorry SUHAILAT ki yafe mun amma bazan iya cigaba da zama da ke a gidan nan ba, ba zan iya jurewa ba, bazan iya mantawa da daren mu na farko ba, duk kuwa da cewa ba don budurcin ki na aure ki ba amma na rasa me yasa na kasa jurewa. Suhala bana son na shiga haƙin ki ko kaɗan shiyasa kawai naga wannan hukuncin shi ya kamata na ɗauka, ki yafe mun don Allah, Allah ya baki mijin da ya fini komai da komai,ba abunda zan iya ce miki yanzu sai dai Allah ya haɗa kowa da rabon shi, and also, you can stay here har sanda zaki yi iddar ki, na tafi ki yafe ni don Allah”.Ya ƙarashe maganar yana bin hanyar da zata sada shi zuwa tsakar gidan.

Ita kuwa Suhaila da tunda ya fara magana ta tsaya tana kallon shi with her dry mouth, abun ma abun mamaki really Habib ya sake ta, shikenan yanzu zata koma gidan Ammi, shikenan yanzu ta zama bazawara, shikenan shikenan.

Jin ya ɗau hanyar barin palon yasa ta fara rarrafowa tana bi ta cikin broken mugs ɗin da suke zube a ƙasan carpet ɗin gurin ba tare da ta sani ba, ba tare da ta ji zafin da yake ratsa ta ba, wanda idan mutum yana cikin hayyacin sa sai da kawai muce Allah ya kikaye. Gudu gudu sauri sauri ta ƙarasa inda yake tana me riƙe ƙafar shi.

Cakk ya tsaya yana jin yadda ta ƙaƙume mai ƙafa kamar her life depend on it.

Cikin gushewar hankali da rashin sanin abunda take faɗa tace”Don Allah, don son ka da soyyayar fiyyayen halinta kayi haƙuri, ka janye maganar sakin nan, wallahi ban san irin halin da zan shiga ba idan har ka barni, Habib sai da nayi shekara ishirin da biyar kafin na samu nayi aure, Habib idan na koma gidan mu ban san wacce irin rayuwa zanyi ba, Habib idan ka rabu da ni zan shiga cikin wani yanayi, Habib you are my cynosure, my first love, my first husband, Albi ina sonka don Allah ka bar zancen sakin nan mu cigaba da rayuwar mu plsss don Allah, wallahi a shirye nake na maka duk wani abu da kake so amma don Allah kar ka rabu dani na roƙe ka don Allah”. Ta ƙarashe maganar ta sakin wani kukan me cin zuciya.

“Habib am breaking into pieces”.

Shikuwa gogan tuni yaji Ƙwalla ta cika mishi ido amma duk da haka ba zai iya zama da ita ba,ba abunda yake tunawa sai maganganun Mustapha.

_”Haba! me zaka yi da wannan? ga mata nan masu aji suna binka, dube ka kyakkyawan saurayi amma ka rasa wacce zaka aura sai wannan bakidajiyar, wanda bata zo maka da budurcin ta ba haba malam kawai ka sake ta ka buga ƙara’i_.

Lumshe idon shi yayi hawayen da yake riƙewa suka samu daman zubowa, saurin saka hannun shi yayi ya goge fuskar shi kafin ya juyo ya tsuguna daidai inda take, kissing ɗin goshin ta yayi kafin ya ɓanɓare hanun ta a jikin ƙafar shi”Am sorry” shine kawai abunda ya furta, yana me fita daga cikin Palon.

Wani sabon kukan Suhaila ta saki tana yunƙurin ƙara bin shi amma ina taji ƙafar ta ta riƙe.

Cikin second biyar wani tunani ya saukar mata kamar daga sama.

Suhaila me kike shirin yi ne? me kike nema kuma bayan yace baya son ki ya sake ki, ba saki ɗaya ba har saki biyu, ya nuna ya tsane ki, ya nuna budurcin ki kawai daman yake so, ya nuna miki halin mazan da Ammi take cewa kice zaki gani inda namiji ne, ya wulaƙan ta ki, dubi yadda ya tafi ya barki cikin jini ko a jikin shi ko tausayi baki bashi ba, kuma don rainin hankali har da wani kissing goshin ki. Ya kamata ki farka daga baccin da kike this is not the end of the world kuma zai wuce, nayi overcoming raping ɗina da aka yi ballantana kuma don Habib ya sake ni.

Wani nauyayen ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ƙwala mai kira”Habib!!!!!!!”.

Da sauri ya juyo ya kalle ta jin irin kira da ta kwaɗa mai.

A hankali ta fara tashi daga inda take tana me ɗingisa ƙafar ta har ta ƙaraso inda yake, kafaɗar shi ta dafa kafin ta fara magana cikin saukar da murya ga hawayen da suke wanke mata fuska” Habib meye amfanin na tsaya nayi idda a gidan ka, inace saboda Sulhu ne, ko za a samu daidaito a tsakanin mata da miji shiyasa annabi ya umarce mu da muyi idda a gidajen mazajen mu, to tunda ba ka da buƙatar haka ko kaɗan kuma ka yi making mind ɗin ka baza ka zauna da ni ba, to ka ga kuwa zaman iddar bashi da amfani, nayi maka alƙawarin kafin ka dawo zaka zo ka tarar da gidan ka kamar yadda yake nayi maka alƙawarin har kaya na sai na kwashe su a yau ɗin nan, sannan kuma ina so ka sani bazan taɓa yafe maka abunda ka mun ba, bazan taɓa mantawa da kai ba, ka cuceni ka gama da rayuwa ta ina cikin zaman zama na kace kana so na har ka aure ni ashe ba ni kake so ba jiki na kake so, kaje ga duniyar na iya abunda zance maka kenan, indai mata ne gasu nan kala kala duk inda kabi, don haka daga ƙarshe ina maka fatan alheri Allah ya baka irin matar da kake so, sai wata rana”.

Ta ƙarashe maganar tana me juyawa zuwa cikin gidan tana ɗan cangala ƙafarta har ta isa zuwa bedroom.

Shi kuwa Habib jikin shi a sanyaye ya fita a gidan, cikin motar shi ya shige be tsaya ko ina ba sai shagon aminin na shi.

****

Abu Nihla ne zaune akan gado while Fatima kuma tana kwance tayi matashi da jinyar shi, idanon ta a lumshe suke kamar me bacci amma kuma ba baccin take ba, shi kuwa massaging kanta yake amma kuma yasan ba baccin take ba, a hankali ya ɗago ta ta dawo bisa ƙirjin shi yana me sumbatar gashin ta, daɗa lafewa tayi a jiki shi tana jin yadda gaban ta yake ƙara faɗuwa.

Cikin lallashi da nuna kulawa yace”Ummu”. Amma shiru bata amsa mai ba.

Cikin harshen larabci yace”tisma’ini Ummu Nihla? (kina ji na ummu Nihla? )”.

Ɗan motsawa tayi kafin tace” Ehhh sama’atak(Eh naji ka)”.

Ɗan ƙara ɗago da kanta yayi kafin yace” Maza hadath? Mal mushkila? (me ya faru meye matsalar?).

Ɗan buɗe idonta tayi kafin tace”Bani da lafiya kuma ban san me yake damu na ba, tun da na tashi nake jin jiki na babu daɗi ga kuma faɗuwa da gaba na yake yi”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button