HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

“It’s okay kinji ko, tunda kika dawo daga gidan Suhaila 3weeks back naga gaba ɗaya kin canza”.

Ɗan shiru tayi kafin daga baya ta zabura tace”Yess Suhaila, Suhaila, she is not fine, ina waya ta take?

Da sauri ta sauka daga gadon tayi kan dressing mirror inda wayar tata take, ta ɗauka ta cire key kenan zata danna kiran Suhaila sai taga kiran ta ya shigo, bata wani ɓata lokaci ba ta ɗaga wayar.

“Hello Suhaila are you okay? Yanzu nake shirin kiran ki sai gashi kin kira”.

Cikin kuka Suhaila tace”Ya fatima am dying, ya Fatima ki zo yanzu”.Ɗut ta kashe kiran tana zamewa daga kan gadon da take a zaune duk jini ya ɓata gurin.Wani kukan ta ƙara fashewa da shi me cin zuciya tana dana sanin amincewa da Habib.

Ita kuwa Fatima idan banda Allah yasa Abu Nihla ya bi bayan ta da sai dai ta zube a ƙasa, riƙe ta yayi yana me girgiza ta haɗe da tambayar ta me ke faruwa.

Cikin kuka tace”Ka kai ni gurin SUHAILA, zai kashe ta “.

Cikin rashin fahimta yace”Ban gane zai kashe ta ba, wai me ke faruwa Fatima?”.

Cikin ƙosawa da tambayoyin shi tace”Abu Nihla don Allah ka rabu da ni, just take me to SUHAILA!”

Sakatoto yayi yana ganin ikon Allah duk ta rikice lokaci ɗaya,saurin miƙo mata hijab ɗin ta yayi kafin ya ɗauki car keys ɗin shi. Cikin sauri suka fita daga gidan Allah ya temaka ma sun kai su Nihla School.

Cikin 15 minutes suka isa gidan Suhaila, ai kuwa da gudu Fatima ta fito tana buga gidan kamar zata tashi sama.

Cikin zuciyar ta take ayyana “Ohh Suhaila da baki da ni a garin nan da kin shiga uku, da ko wa zata kira yanzu oho”.

Ni kuwa nace ai Alhamdullilah tunda kina garin.

Suhaila kam tana jin su suna buga ƙofa amma ta kasa tashi, ta ƙyar ta samu ta yunƙura ta fara ɗan takawa. Ji take kamar ta faɗi saboda wani mugun jiri da yake ɗibar ta.

Fatima ce ta kalli Abu Nihla tace”Shikenan ta mutu, ta mutu, na shiga uku na lalace ta mutu wayyo Allah na SUHAILA”.

Saurin riƙe ta yayi yana toshe mata baki”Haba mana Fatima meye hakan ki nutsu mana”.

“Ka kira shi, ka kira wancen mara mutunci ka sanar da shi ya kashe ta ya kawo mana mukulli kawai mu ɗau gawarta”. Ta faɗa tana daɗa fashewa da kuka.

“Wa zan kira Fatima?

” Habib mana!! Habib zaka kira man……

Bata ƙarasa faɗan abunda zata faɗa ba kawai suka ji ƙofa ta buɗe, nan da nan Fatima ta bar jikin Mujahid tana me ƙarasa tura ƙofar.

Bayan su ya kalla yaga har mutane sun fara tsayawa suna kallon su don ma Allah ya temaka Safiya ce.

Fatima kuwa tana shiga Suhaila ta faɗa jikin ta nan suka yi ƙasa a tare suna me rungume junan su.

Mujahid kam da ya shigo ya tsaya yana kallon ikon Allah ganin Suhaila cikin nighty ɗin ta, ga kan ta ko ɗan kwali babu,
Ga jikin ta duk jini, ganin fatima bata ankara da irin yanayin da Suhailan take ciki ba yasa yace”Fatima She is bleeding!!!!.

Ai kuwa da sauri ta raba Suhaila da jikin ta tana me ƙare mata kallo.

Nan taci karo da gurjewar da Suhaila tayi da mugs ɗin nan.

Tashin hankali kwance kan fuskar ta tace”Suhaila me ya faru? Me same ki? Sake dukan ki yayi!?”

Ta jero mata tambayoyi wanda bata bari ta bata amsar ko guda ɗaya ba.

Ita kuwa Kuwa Suhaila cikin azaba tace” Ya Fatima ya sake ni, ya sake ni har saki biyu, shikanen na shiga uku”.

“Ya sake ki fa kika ce!!!??? ????

Shi kuwa Mujahid da suka sa shi cikin duhu ya daka musu tsawa” Could someone tell me what is going on here!?

Babu wanda ya kula shi sai kuka da suka cigaba da yi.

“Fatima will you stop this madness, ke da ya kamata ki daure ki kwantar mata da hankali sai kece kika fita zaƙewa, malama ki tashi ki shiga ciki ki ɗakko mata kaya mu kaita asibiti, idan shi be kashe ta ba ai ke kin kas…….. Be ƙarasa faɗan abun da zai faɗa ba ya shafa ƙeyar shi. Cikin gidan ya shiga kawai ganin Fatiman ma ba jin shi take ba.

Ai kuwa yana shiga ya hango ƙofar bedroom nan ya shi ya ɗakko zanin da ya gani akan bed sa’annan ya ɗakko mata hijabi.

Yana fitowa ya tsaya yana kallon su, ganin ƙara bata lakoci suke yasa ya raba Fatima daga jikin Suhaila ya zura mata hijabin ta kafin ya cillawa fatima zanin, be tsaya jiran ta ba ya saƙalo hanun Suhaila ya kaita cikin mota, ai kuwa da gudu itama Fatiman ta biyo su tana me shiga sit ɗin bayan ta ɗora kan Suhailan a cinyar ta tana cigaba da kuka kamar wata yarinya.

“Ya Fatima mutuwa zanyi, na yi wa Habib alƙawarin yau zan kwashe kaya na a gidan shi plss do this favor for me don Allah, ki ce da Ammi ta yafe mun sannan kuma naje gidan Habib kuma na gani, ki ce da Abbu na ina son shi sosai sannan ya cigaba da haƙuri da Ammi”..

Fatima kam kuka yaƙi tsayawa, saboda yadda take jin kalaman Suhailan kamar da gaske mutuwa zata yi ta bartan.

Cikin kiɗima tace Abu Nihla mutuwa za tayi ka temake ni don Allah Ka yi sauri ka isa asibitin nan……..

 

******

*_Hhhhhhhh????????am tired ohhhhh my eyes dey ache, a haka ma nayi ƙoƙari sosai wallahi manage with this….._*

*_Ma’salam_*

*Faɗma Ahmad*✍️✍️

*????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*

*page 1️⃣8️⃣to1️⃣9️⃣*

*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶????
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶????,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.

*Addu’ar Neman Biyan Bashi*

اللّهُمَّ اكْفِنِي بِحَلالِكَ عَنْ حَرَامِكَ، وَأَغْنِنِي بِفَضْلِكِ عَمَّنْ سِوَاكَ.

Allahummak-finee bihalalika ‘an haramik, wa-aghninee bifadlika ‘amman siwak.

Ya Allah! Ka wadatar da ni da abin da Ka halatta barin abin da Ka haramta, kuma Ka wadatar da ni da falalarka ga barin waninka.

اللّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْهَمِّ وَالْحُزْنِ، وَالعَجْزِ وَالْكَسَلِ وَالْبُخْلِ وَالْجُبْنِ، وَضَلْعِ الدَّيْنِ وَغَلَبَةِ الرِّجَالِ.

Allahumma innee a’oothu bika minal-hammi walhuzn, wal’ajzi walkasal, walbukhl, waljubn, wadal’id-dayni waghalabatir-rijal.

Ya Allah! Ina neman tsarinka daga kunci, da bakin ciki, da kasawa, da lalaci, da rowa, da tsoro, da nauyin bashi, da rinjayen mazaje.

 

*_Heart Breka2*

“Fatima kiyi haƙuri don Allah ki nutsu in sha Allah babu abunda zai samu SUHAILA she will be fine”.

Shafa kan SUHAILA tayi kafin cikin kuka tace”In a
Sha Allah she will overcome this ma”.

Ta cikin mirror ya ɗago kanshi ya kalle ta yace”yeah in sha Allah”.

Nan da nan suka ƙarasa asibitin aikuwa suna zuwa babu wani ɓata lokaci suka kamata suka shigar da ita.

Suna shiga suka ga wata a nurse a zaune, da sauri Fatima ta taya Mujahid suka kwantar da Suhaila akan kujerar da take reception ɗin.

Da gudu ta isa gurin Nurse ɗin tana faɗin”Don Allah ku temaka mun ƙanwata, ku duba ta please. wani kallon rainin hankali nurse ɗin ta watsa mata kafin tace”Tana da file a nan asibitin ne? “.

” A’a bata da shi amma ki duba ta yanzu sai a buɗe mata a biya komai da komai”.

Ƙara haɗe rai nurse ɗin tayi kafin tace”Gaskiya bama haka sai dai ku kaita asibitin kawo, amma mu nan sai ka buɗe file tukunna zamu duba ka indai ba wai haihuwa bace, kuma itama tana da nata sharuɗukan”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button